mata amfani daita gurin lallabata "kace Baka bukatar cikin Ko"?
Shiru yayi na tsawon minti goma kana a hankali ya fesar da numfashi ya kwantar da murya "ba wai bana son cikin bane matsala zai zame mana arayuwa bare ke da kike matsayin mace "ni dai gsky Ina son kayana "a hankali ya d'aura tafin hannunsa a goshinsa ya dafe tare da lumshe idanunshi cike da kulawa yace "nima Ina son abuna amman kiyi hakuri acire zamu samu wasu nan gaba.
"Da gaske kake ?"
Yayi shiru yana cigaba da cizan lips dinsa .
A hankali ta Kira sunansa "Adnan !"a hankali ya motsa lips dinsa "na'am tan ."ka tabbatar zamu samu wasu ? da kyar ya fixgo mgn "eh idan kika bi umarnina kika cire ba ya k'arasa maganar yana shafa sumar kanshi "tunda muka rabu ban kara samu sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nake kullum cikin damuwar soyayyarka nake da zazzabin cikin nan bana wani cin abincin kirki gashi Kowa ya gane halin da nake ciki a gida ".
"oh my god tanwer me yasa kikayi haka me yasa kika bari suka sani ?
"saboda ina qaunarka ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka ..
Qirjinsa yayi masa nauyi tausayinta ya lullubesa duk da bai son yawon surutu amman haka yayi shiru yana biye mata "gsky banso kika sanar dasu ba "to yazanyi da rayuwata dole ce . ya dunkule hannunsa sosai yaji ya Shiga damuwa" ina sonka Adnan Allah idan bakayi wani abu ba tunanika zai kasheni "
ki daina yawon tunanina .
tace "bazai Yiwu ba yanzu ma Na fara idan kaga na rage tunaninka to ina gidanka ne "
"Ki rage yawon tunsni yana kisa ,dan Allah kiyi kokari kije asibiti gobe acire cikin nan sannan su rubuta miki magani. "nifa bazan zubar ba .
Ki yi abinda nace shine kwanciyar hankalina sun dade suna magana akan ciki duk yadda yayi daita taki amince masa da zata cire cikin, wanda ita a zuciyarta tuni ma ta yarda kuma ta amince ma zuciyarta zata cire ta hutawa ranta tunda shima bai so amman bazata yarda ta bari yasan zata cire ba sai ta d'aga masa hankali.
"ki kwanta ki huta zan Kiraki zuwa gobe amman ki tabbatar kin amincewa ranki zaki cire "
Tace "to !
"karkiyi tunani komai kinji "
ta sake cewa " to ! ta fad'a tana jin zafi aranta saboda gbdy ta gano rashin sonta da bai mata sai tana jinshi ya katse Kira ."
zuciyarta ta kasa samu natsuwar tunanin daya gargade shi ta cigaba da yi, bata da burin da wuce ta mallakesa a matsayin mijin aurenta , tunani kala kala tayi ta saka wancan ta kwance har ta shigo tunanin rayuwar da sukayi agidansa a farkon zuwanta suna lullube dashi cikin bargo d'aya babu kaya ajikinsu tana makale a gefensa yayinda hannunta d'aya Ke Saman faffadan qirjinsa shi kuma yana shafa sansar jikinta tare da sarrafa albarkatun qirjinta nan take tsigar jikinta suka tai mikewa ,ta dinga jinsa ajikinta a hankali jikinta ya kama kyarma ta kankame jikinta guri daya tana jin kamar jijiyarsa na shiga jikinta ,yayinda taji tafukan hannunsa na yawo sansar jikinta da wannan tunanin bacci barawo ya dauketa ."
Washegari da misalin karfe biyar da rabi ta farka had'e da yin mika , jiki a sanyaye ta sauko daga kan gadonta tashiga bathroom tayi alwala ta fito ta gabatar da Sallah byn ta Idar bata tashi ba ta kwanta akan sallaya tana azkar tana kuka har ta gama ta kama addua "rabbi Inni Lima Anzalta Ilaiya min khairin faqeer ta dade kwance tana tunani da fargaban zafin cire ciki ahankali baci ya dauketa sai gurin karfe goma ta farka ta mike tare da nade dadduma Sallah ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya ta nufi d'akin mumy anan ta samu mumy har dasu uncle bashir byn ta gaishesu ta gaishe da mumy sannan ta roketa tare da bata hakurin damuwar da ta sakata jiya, sannan Kuma ta tabbatar mata Da ta amince a cire cikin .
nan take mumy taji ta warke daga ciwonta ta ji jikinta ya dawo normal damuwa ta bar gangar jikinta sai faman saka mata albarka take "inshaallah sai Allah ya yaye Miki abinda kike ji akan dan iskan mutumin nan ,
Allah ya yaye miki gbdy suka amsa da" ameen".
cike da farinciki suka dauketa zuwa babba asibitin kudi batare da bata lokaci ba suka Samu ganin likita suka fad'a masa taimakon da zai musu ,dake yasan minister bai tsaya bata musu lokaci ba yayi mata gwaje gwaje dan ya gano cikin Ko na wata Nawa ne dan yasan me za'a mata ganin karamin ne yace "za'a Iya bata kwaya tasha amman fur dady yace a'a ayi mata abortion Kawai zaifi samun natsuwa , dan haka batare da bata lokaci ba aka Shiga daita Wani d'aki .
ta sha wahala sosai Kamar zata mutu har aka gama kuka take tana Kiran "wayyo Allah zan mutu nurse ta d'auki sama da minti talatin tana aikinta bayan an gama nurse ta fito ta barta ta dan huta .
byn kmr awa d'aya ta fito tana d'aga kafa da kyar tana jin jikinta kmr ba nata ba sai dai ta daina jin nauyin da jikinta yayi mata amman kallo d'aya zaka mata ka tausaya mata dan taji jiki sosai , duk tayi wuri wuri Kamar wacce tayi shekara tana ciwo.
sai dai ciwon bai kai zafin rashin son da jaguwa yake mata ba office din doctor ta shiga inda ta iske su dady zaman jiranta doctor ya rubuta mata magugunan da zasu taimaka mata sannan suka dawo gida .
Kai tsaye d'akinta suka nufa daita suka kwantar daita akan gado suka zagayeta suna mata Sannu "doctor yace abata ruwan zafi ta sha kafin ta sha magani inji cewar uncle Jamil.
mumy najin haka ta mike da sauri ta fita ta shiga kitchen da Kanta ta dafa mata ruwan zafi ta juyo a cup ta dawo d'akin "Tashi ki sha kinji tanwer dina ,tan ta soma k'okarin mikewa uncle bashir ya taimaka mata ta zauna tana fidda zazzafan numfashi ya janyo pillow ya saka mata abayanta ya jinginata yana mata "Sannu!"
Mumy ta mika mata cup din ruwan zafi tana sake mata "Sannu"! tanweer ta gyada mata kai Kawai dan ita kad'ai tasan ciwon da zuciyarta ke mata .
a hankali ta dinga kurban ruwan zafin ,kadan ta sha tana k'okarin mikawa mumy cup, ta miko mata magani ta karba ta sha da kyar ta mika mata cup ta koma ta kwanta lamo had'e da kunna wayarta dan tun safe a kashe take ta tura karkashin pillow .
Ko minti biyar batayi da kunna wayar ba,ta soma babriting alamun ana Kira ta lalubo tana duba screen din wayar number jaguwa ne dan haka ta maida wayar inda ta dauko batare data dauka ba ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafin gaske wanda take jin zafinsu har cikin jikinta .
"ya kiranta yanzu saboda yana bukatar ta zubar da ciki amman ita kira nawa tayi masa bai d'auka ba ?"tana jin Kira na sake shigowa wayar amman taki d'auka "ciwon abun taji sosai bata san meye matsala arayuwarta ba sai da qaddara ta hadasu ,wani Kiran ne ya shigo aranta tace "duk ka gama kiranka bazan dauka ba sai na ganar da kai kuskurenka .
Ahankali duk suka watse suka barta a d'aki ranar yini sukai cikin farinciki bini bini sun shigo dakin dubata har dady yayinda wuni jaguwa yayi yana Kiran number tanwer amman taki d'auka a karshe ma ta kashe wayar gbdy."
Haka yayita damunta da kira acikin kwanan biyu ya hanata sakat da batun zubar da ciki ita kuma taki yarda ta fad'a masa ta zubar tun su mumy basu fahimci mai Kiran ba har suka zo suka fahimta haushi kamar ya kashesu ganin tana sauraronsa.
Bayan kwana biyu su uncle Jamil suka fara Shirin komawa uncle bashir yace zai wuce da tanwer dan ta kara samun natsuwa ko hankalinta zai bar mutumin da take so "ki shirya kinji tanwer muje Katsina.
uncle Jamil ya gyara zama yace gaskiya gara ka tafi daita dan ni Zan iya Mata Dukan mutuwa idan naga tana nacin wancan banzan mutumin," kai dai kayi hakuri komai qaddara ce fa ni dai idan zata bini zan wuce daita.
dady yace "kuyi hakuri bazata koina ba ta cigaba da zama tare damu shine kwanciyar hankalina Ku cigaba da yi mata addua.
Allah ya tsare mana zuria inji cewar mumy uncle bashir yace ", inshaallah da sannu zata manta komai hawaye suka cika mata Ido bata Jin zata manta da Adnan, yayi mata tabon da bazata manta dashi ba ta yunkura zata tashi tana kuka sai kuma ta kasa tashi dan haka ta rarrafa jikin dad dinta ta kudundune ajikinsa ta rushe da kuka nan da nan ta Karya masa zuciya to daman Shi akwai sanyi da tsananin jin tausayi mutun bare tanwer dinsa daya fi qauna akan komai , idanuwansa suka cika taf da ruwan hawaye a hankali ya d'aura hannunsa a Saman Kanta muryarsa na rawa yake cewa "da zan iya tanwer da na Karbi number yaron nan na aura miki Shi ,wallahi Ke abar tausayi CE amman bazan Iya ba, bazan iya wannan Imani ba ."
"Please dad ....."Sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganar
Ahankali ya janyota yace"dubeni mamana da kyar ta dubesa hawaye na zuba "ki daina kuka yana daga min hankali ,baki dace kiyi soyayya da irin wadan nan mutane ba ,bare har ta kai ga aure jikinki bai dace dasu ba rayuwarsa rayuwar wulakacin CE "dady Allah zai daina wannan rayuwar "bazai daina ba ".
ta zuba masa Ido ta kasa cewa komai ta kankame Shi tana kuka washegari haka su uncle Jamil suka tafi sukar barsu cikin Wani yanayi kafin rana ta fadi duk sun isa gidajensu .
Sati biyu Kenan jaguwa na Kiran layin tanwer kwata kwaya bata d'auka ta danne zuciyarta ta cigaba da abubuwan gabanta a karshe ma ta koma bakin aikinta .
*******"
Fitowar nazifi Kenan daga d'akin tiyata yaga wasu mutane su biyu a bakin kofar office dinsa suna k'okarin bud'e kofar office din , gabansa ne ya fadi .
wani irin bugawa had'e da tsalle zuciyar nazifi yayi har ya haifar masa da tsayawar numfashi haka nan yaji bai yarda dasu ba nan take Kuma maganganun alhj Tahir suka shiga dawo masa suna masa kuwa acikin kwaluwarsa da kunnuwansa "kwana biyu kawai na baka matata da dana su dawo Idan ba haka zan sa adaddatsa min kai sannan na aika ka lahira "ai Ko bai sa an daddatsa shi ba yasan zai iya sawa a nemishi a rasa na har abada take tsoron haka yake nema yi masa barazanar da tarwatsa masa kwakwaluwa da zuciyarsa, kallonsu yake yana tunanin abunyi .
yaje police station da sheidu daya tattara sai dai gbdy bai ga wanda ya dace ya mikawa sheidun ba, dan akan idanunsa yaga anyi rashin adalci muraran " wani mashayi ne ya buge wata mata da tsohon ciki ta mutu har lahira shine aka kamo mutumin aka kawoshi office din yansanda aka nufi office din wani ma'akaci dashi , alokacin da shi kuma yake k'okarin shiga office din , abinda ya d'aga masa hankali bai wuce yadda police din Ke k'okari son su gyarota Kawai ya kama gabansa "
Kamar nawa zan bayar yallabai a kashe maganar ?"ka bada million dari "million dari yallabai ?"eh muddin kana son akashe case din Kamar bayi ba domin duk wanda yasan da wannan batun sai an bashi kudi "gaskiya ni bani da wadan nan kudadade "a she kuwa zaka gidan yari".
cike da sanyin jiki ya juya ya bar station din zuciyarsa cike da bakinciki ya koma gida ranar kasa bacci yayi bai ya suka kare ba amman jikinsa na bashi zaa gyarota .
Naunayyen ajiyar zuciya nazifi ya sauke yana k'okarin juyawa domin tsiratar da rayuwarsa dan yasan idan sun kashesa sun kashe banza yaji an buga masa wata hadadiyar tsawa tare da cewa "ga mutumin da mukazo nema karka kuskura ka kara taku d'aya ."
" nan take jikinsa ya kama rawa" ya zubar da abinda ke rike a hannunsa ya falla da mugun gudu, aiko kamar jira suke suka biyosa aguje.
gudu yake suna binsa domin k'okarin kamasa amman ina tazararsu da nisa gudu yayi sosai yana haki yana neman inda zai boye kuma har lokacin suna biye dashi akan titi wannan karon har da garbi yana gocewa mutane sai kallonsu suke yana
K'okarin shiga wani super market domin buya yayi tuntube da gangar jikin mutun nan take ya zube a jikinsa yana haki yana furta "ka taimakeni dan Allah kasheni zasuyi zasu kasheni yana gama fadar haka numfashinsa ya dauke su kuma mutanen na ganin haka suka juya suka koma da gudun kar asirinsu ya tono dan basu san matsayin mutumin ba .
Nazifi bai sake sanin inda yake ba sai farkawa yayi ya gansa a wani hadadden daki hannunsa daure da drip a hankali ya karasa bud'e idanunsa yana kallon d'akin ya zabura ya mike ya cire drip yana k'okarin durowa daga saman gadon, sallama yaji Da k'okarin shigowa d'akin shiru yayi tare da bin kofar da kallo ganin mutumin daya fad'a jikinsa ne ya sauke ajiyar zuciya .
"Sannu Ko ,ya ka cire drip din tun bai kare ba ?"numfasawa yayi wallahi rashin samun natsuwar zuciya ne dan ban san a hannun da nake ba ya fada yana maida drip din.
ya gyada masa yana duban wanda suka shigo tare "dan Allah Kawo masa abinci "okay yallabai !"ya fad'a tare da juyawa cikin kankanin lokaci ya dawo d'akin hannunsa rike da food flake da plet da spoon ya ajiye ya zuba masa abincin a plet ya saka masa spoon ya mika ma nazifi ya karba.
da hannun daya ya fara ci ya karasa inda fridge yake ya d'auko masa maltina mai sanyi ya bud'e ya ajiye masa ya samu guri ya tsaya yana dubansu .
A hankali nazifi ya d'ago yace "na gode fa ranka ya dade "karka damu me kayiwa wadan can mutane suka biyoka suna neman rayuwarka ?"naunayyen ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye spoon din hannunsa a natse ya shiga Koro masa komai dayasani har zuwa sanda aka fara farautan ransa mutumin ya gyada kai Kawai sannan ya soma magana a natse "ka natsu ka kwantar da hankalinka zaka cigaba da zama anan har na tsawon sati zansan abun yi da fatan bakada iyali ?
"girgiza masa kai yayi alamun bai da"okay !ya fad'a tare da mikewa suka bar d'akin ."
****
Tanweer na zaune a falo tare dasu rukayya suna kallon zeeworld Kiran jaguwa ya shigo ta mike tsam ta koma d'akinta ta d'auka tana d'auka yace "dan iskanci me yasa kika d'aukar wayata kwana da kwanaki ?
"abinda yasa kake d'aukar tawa wayar kwanaki shi ya hanani d'auka .
"okay haka ma zakice? tace "eh!
Idan na bari kika haifi cikin nan mahaifiyata janyowa abun kunya ,wannan abu zai sata jin kunya ".
ai babu abun kunyar daya wuce satar da kakeyi aboye batasani ba wallahi sai tafin jin kunya idan ankamaka akan wannan cikin dan hakan ni dai bazan zubar ba sai kaje kajira ranar da Zan haifa maka danka Ko yarka ka Samu dan aike Ko magajin fashin ba sai kayi training yayan wasu ..."
"Enough tanwer ki maida hankalinki jikinki kinsan irin maganar da zaki dinga fad'a min "bangane na maida hankalina ba gsky ce na fada kaima kuma ka sani ."dan nawa ne zai yi fashi ?"to meye aiki har ma sai yafika tunda magajinka ma fiyinka ".
Shiru yay kanshi na Kasa Kamar yana gabanta cikin sanyin murya yace"ni dai ki zubar Kawai idan Kuma kikaki zubarwa ..."
"Me zakayi "?
"Nace Mai zakayi idan naki zubarwa ?babu abinda zaka iya yi Kuma ciki baza'a zubar ba kayi abinda zaka yi ina jira ta k'arasa maganar tana jan tsaki tana gama fadar haka tai disconnecting din Kiran ...."
Shiru yayi rike da wayar a kunnensa yana jin zafi da ciwon abinda tayi masa, babu abinda yafi masa ciwo Kamar tsakin da tai masa .
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️25
zama jaguwa ya cigaba da yi rike da waya zuciyarsa na zafi da farfasa a qalla ya kusan minti goma yana tunanin maganganunta," bai san me yasa zai damu kansa akan cikin ba , cikin ma da bashi da tabbacin tana d'auke dashi .
wani dogon tsaki yaja yana sake kiran layinta , babu 'bata lokaci ta d'auka qirjinta na bugawa fat fat "Ke ni zakiwa wulakacin ? "
shiru tayi taki ce masa komai sai dai zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri .
"har kin isa ki dinga farfad'a min magana son ranki ?"
ya sake tmbyrta tare da jan tsaki "har ma da kashe min waya ? "shiru tayi still cikin tsananin tashin hankali tana tunanin abinda zata sake fad'a masa wanda zai sake d'aga masa hankali sai dai bata kai ga tattara abinda zata fada masa ba ta tsikayi muryarsa na dukan dodon kunnenta.
"dan kinga ina lalla'baki shine zaki d'auka ko ina jin tsoron ki haifi cikin ne ? "to kar allah yasa ki cire cikin ai cikin ba ajikina yake ba idan akwai shi kenan dan haka ko ki cire ko Karki cire ruwanki sannan matsalarki ce bata Adnan .
ba Adnan za'a dinga kwatance dashi ba , sannan ba shi zai rasa mai aurensa ba . aurenki ne dai bazan yi ba kije ki nemi abokin rayuwarki dan ni tuni na amince da zabin mahaifiyata aikin banza Kawai ki jira ki gani idan zan sake nemanki".
ya k'arasa maganar yana jan dogon tsaki sannan ya katse Kiran yana fidda wani wahalallen numfashi ,yasa hannunsa d'aya ya dafe goshinsa yana jin zafi da ciwo a ransa, shiru yay na second goma qirjinsa da gangar jikinsa na rawa gbdy sai yaji kimai ya tsaya masa guri daya ya shiga tunanin abinda yayi mata a ganin zuciyarsa bai kyauta mata ba daya farfad'a mata son ranshi dan bata cancaci ya fad'a mata magangun daya fad'a mata ba ,ita din wata aba ce mai daraja da kima a rayuwarsa. amman daya tuna irin maganganun data fad'a masa da irin mugun fatan da tai masa a mintunan da suka gabata sai ya dawo haiyacinsa , komai ya dawo masa daidai, qirjinsa da gangar jikinsa da suka d'auki rawa suka daidaita yaga mai ma yayi mata ai bai mata komai ba . "
Bangaren tanwer kuwa maganganunsa sun daki Kunnuwanta sosai sannan sun wuce har cikin zuciyarta, gbdy ya kunno mata wutar damuwar da take dannewa acikin zuciyarta ,Kawai sai ji hawaye yazo idanunta ya fara zuba akan kuncinta, a hankali ta fara rare kuka mara sauti qirjinta na zafi "Allah ka gani ba wai nayi masa haka dan na wulakatanshi bane , "na yi dan na raunata zuciyarsa,na yine ko zai saduda ya zubar da makamansa ya canza rayuwarsa darajan tace bata zubar ba suyi aure ,ashe wata sabuwar maseefa ta jefa kanta ciki tayi maganar a fili tana sheshekan kuka "wayyo Allah ka d'auki raina na huta da wannan rayuwar da nake " wani zafi take a kahon zuciyarta sam ba taji kashi daya na son da take masa ya rugu sai ma qaruwa da son shi yayi acikin zuciyarta , tana sonshi muddin zai aureta zatai confuse din iyayenta akwai hanyoyi da dama da idan ta bullo dasu dolensu su hakura su rungumi nata qaddarar su aura mata shi amman shi kuji abinda yake fad'a mata har ma ya amince da zabin mahaifiyarsa ita ko oho zama tayi ta cigaba da rera kukanta tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa ."
tana cikin wannan halin rukayya ta shigo d'akin ganin idanun tanwer na zubar da ruwan hawaye yasa ta karasa shigowa d'akin da sauri tana cewa "lafiya tanwer menene Kuma ?"
Rukayya ta samu guri gefenta ta zauna ta riko hannuwanta duka cikin nata tana dubanta cike da tausayawa , runtse idanunta tanweer tayi sai ga wasu hawayen sharrrrrr."
"wallahi ina cikin damuwa rukayya ,ina cikin tashin hankali na rasa yadda zanyi da wannan rayuwar da nake ciki , komai ya canza min rukayya ina ma rayuwata ta baya zama dawo , "ina ma ban dawo kasar nan ba"..
Rukayya ta numfasa tace" haka ne kina cikin damuwa da jarabawar rayuwa tanwer amman kiyi hakuri da sannu komai zai daidaita ,"sannan kiyi kokari ki rage damuwar nan duk da tasan komai dake faruwa daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
" ki kara imani da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne kawai dai Allah ya bamu Ikon cinye jarabawarmu rukayya ta fadi haka ne dan takaita maganar .
"nima ina son na rage tunanin Adnan acikin zuciyata amman na rasa dalili da tunaninsa kullum sai gaba yake , wallahi ina masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi ba sai ranar dana ji an shafa fatihan aurensa ta k'arasa maganar tana mai runtse idanunta."
"Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa "? tanweer ta gyada mata kai alamun "eh! "gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi .
Tanweer ta gyara zama tana kallonta "na fahimceki yar'uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki "to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace "na gode rukayya inshallahu zan daina .
." Ki kwantar da hankalinki kinji dan Allah karki sake daga hankalinki akansa Ki fara nemi zabin Allah kiyi k'okari kiyi istahara domin neman zabin Allah "rukayya ko ya min wani irin adduar istaharar da zanyi".?
"zan koya miki , mu nemi zabin Allah bamu sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku idan babu idan kinyi zaki ga komai ya tafi daidai amman Karki yarda ki bari wani yayi miki kiyi da kanki ,zaki iya yi kullum idan zaki kwanta raka biyu zaki yi sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki hatta wannan radadin da kike ji akanshi zaki rage jinsa ."
Jiki a sanyaye tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta amsa ta fara rubuta mata adduar "Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as'aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta'alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi."inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure "na gode rukayya inshallahu zanyi ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta'ba sanin zama da mutun guri d'aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k'okarin kawar mata da dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau ."
Da misalin karfe goma na dare kowa ya shige d'akinsa tanweer ta shiga bathroom dinta tayi alwala ta fito ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 67