Ina kaskantar da kaina ba, kasan fa mata idan suka ga ka damu dasu sai salo da iskanci ya tashi babu ma abinda ke bani takaici kmr kaga katon nmj a gaban karamar yarinya yana rage murya da kaskantar da Kai wai duk akan a amsa masa soyayyarsa Kai Allah bazan iya ba ni kawai idan ma ya zama dole Allah umarni kawai zan bata tunda ya fara mgn sadiq da kannensa mata har ma da ammi suke dariya.
Shi kuwa jaguwa yayi dip kmr anyi ruwa an d'auke ,duk yadda sadiq ya so acigaba da mgnr tanweer jaguwa yaki sai ma ya kawar da hirar ya shiga tmbyrsu abinda basu dashi a gida anan yayi sallahr magrib da isha'i
Hira sukayi sosai har lokaci yaja ya duba agogon hannuna karfe shadaya saura ya mike yayiwa ammi sallama byn ya ajiye mata bandir din kudi yan dari biyu biyu suka fita tare da sadiq domin yi masa rakiya ya shiga motarsa ya kunnata ya bata wuta sai da sadiq yaga tashinsa sannan ya koma gida ya rufe .
Koda ya koma gida bai bi ta kan kowa ba har ma tanweer ya shareta ,ita Kuwa idanunta shi suke son gani ta sake neman afuwansa amman yaki shigowa Inda take ranar da kyar ta runtsa kwana tayi juyi da kuka .
Washegari ta shigo d'akinsa bakinta d'auke da sallama yana kwance a akan doguwar kujera a falonsa dan tun bayan daya dawo sallah asuba yake kwance agurin ta ra'be gefe guda tana dubansa ,a hankali ta k'arasa ta tsugunna a gabansa tana kallon gefen fuskarsa Inda ta maresa ,saukar numfashinta akan fuskarsa yasa shi bude Ido eyes to eye's suke kallon juna "sorry for my active kayi hakuri nasan har yanzu kana fushi dani "ya juya mata baya yana jan tsaki ta sake matsowa sosai ta Kai hannunta jikinsa ya buge mata hannu da karfi ta rike hannunta tana runtse idanunta dan taji zafi sosai har cikin ranta taji dukan .
take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta muryarta a shagwa'ba tace "yanzu bazaka yafe min ba ?banza yayi mata kamar bai san da wani halitta agurin ba "ki tashi ki bar d'akin nan tun kafin na tashi nayi miki abinda banyi niyya ba . "ka yarda nayi nadama "dan ubanki karkiyi nadama maza ki tashi ki bar d'aki ya fad'a yana mikewa tsaye da sauri itama ta mike tsaye"oya out of this room "dan murmushi gefen baki tayi tare da matsoshi sosai ta rungumeshi tsam ajikinta kamar za'a kwace mata shi, jinta ajikinsa yasa shi Jin wani iri muguwar kasala ,tayi lif a faffadan qirjinsa tana shakar numfashinsa da kamshi turarensa me d'aga hankali.
a hankali kowannensu ke sauke ajiyar zuciya muryarta a matukar sanyaye tace "karka sake zagin ubana ko zan d'auki komai ban da zagin mahaifina ka kiyaye harshenka " shiru tayi tana jiran abinda zai ce hannusa yasa ya zareta ajikinsa "tunda shine abinda kika fi tsana daga yau shi zan dinga fada miki "zan kuwa rama tunda uba bai fi ba "bar d'akin nan ya fada a fusace yana nuna mata kofa "karki sake shigo min daki "Kai ma haka karka sake zuwa Inda nake "wai ni sa'anki ne da ina fada kina fad'a?yayi mgnr a matukar hassale yana kokari damkota ta zame tayi baya da sauri tare da yi masa gwalo da karkad'a masa kunnuwanta.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai ya kasa cewa komai taku d'aya yayi ta kwasa da gudu ta bar d'akin ya ja dogon tsaki "zanyi maganinki ne ."Tun daga ranar bai sake shigowa Inda take ba hatta abinci ya daina kawo mata , lura da so yake yayi punishing dinta da yunwa yasa hankalinta ya tashi sosai ta shiga damuwar halin da zata shiga idan ta wuce kwana daya nan gaba batare data sakawa cikinta wani abu ba .
Sai da yayi kwana biyar yana fushi daita sannan ya sauko ya shigo domin kawo mata abinci ya ajiye mata farar leda zai fita tace "malam ka dawo ka d'auki abincinka bana ci duk kwanakin nan da baka kawo min abincin ba na mutu ne ?"ban mutu ba dan haka ka dauki kayanka ba zanci ba zan cigaba da zama haka har na bar gidan nan.
wani murmushin gefen baki yayi sannan ya juyo ya fuskanceta sosai yaga ta rame acikin kwanakin da yayi bata ci komai ba taku d'aya ya K'ara ya fara mgn cike da dakiyar zuciya "Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba ,saboda bana sonki bakya cikin rayuwata bakya gabana ,kisan Allah ko nemanki na sake yi na rasa yanzu bazan damu ba saboda na lura baki da mutunci, bakida kirki ,baki da biyayya biki san komai ba sai zallar rashin kunya ,ada Ina matukar jin tausayinki da gudun abinda zai cutar dake amman a yanzu duk babu wannan , zan cigaba da rikeki ne dan na musguna miki dan fahimci kina qaunar komawa gida kamar yadda kike qaunar rayuwarki". yana dasa aya ta fashe da kuka tana cewa "Allah ya Saka min wallahi sai hakina ya bibiyi rayuwarka ni wallahi dama kasheni kayi na huta .
"bazan kasheki ba zaki zauna ki cigaba da ganin rayuwa a gidan nan , sannan babu abinda zai bibiye rayuwata bakinki bazai kamani ba danke ba uwata bace
yana gama fad'ar haka ya fice daga dakin ya barta tana kuka yana fita ta hau share hawayenta da hannuwanta duka ta Isa Inda ledar takeway yake ta bud'e ta fito da takeway jikinta har rawa yake ta soma cin abincin tana zubar da hawaye ."
jaguwa na fita daga d'akin gidan ya bari gbdy zuwa asibiti Kai ziyara sai dai tafiya kad'an yayi ya fahimci ana binsa abaya , ilai kuwa yana duba mirrow din motarsa dcp lawan numan ya gani zaune yana biye dashi nan take ya qara gudu shima ya biyosa a guje sunyi tafiya me nesa dcp na biye dashi daf da zai sha gaban jaguwa ya ciro bindigar ya harbi tayar motar dcp cak motar ta tsaya daga mugun gudun da take Allah ya taimakesa motar bata hantsila ba , yaja tsaki yana cewa zaku rasa ranku akaina idan baku daina bibiyata ba ya canza hanya ya cigaba da tafiya yana sauke numfashi ."
Cike da rashin kuzari dcp ya dawo office ya tara yaransa gbdy ya Kalli Inda babban yaronsa yake zaune "meye nazarinka akan wannan lamarin na kwamushe diyar minister da danfashin nan yayi yaki dawo daita sannan yaki bukatar komai daga hannun iyayenta ?"ni fa bansan abinda zance ba wannan lamari yafi karfin tunanina" kana ganin shigowar yan fashi gidan minister hakan bashi da halaka dana jikin minister ?
"Nima na fara tunanin akwai saka hannun wani dake tare da minister dan mutun abun tsoro ne zasu iya aikata komai amman Kuma bai zama lallai zarginka ya zamo gaskiya ba dan idan da saka hannun wasu zuwa yanzu zamuga alama" "haka ne Kuma nan suka shiga nazari akan abubuwan dake faruwa suna nan zaune har karfe shida kira ya shigo wayar dcp ya d'auka "Yana d'auka sautin jaguwa ya karad'e gurin dake a handsfree ya Saka wayar "barka da yammaci masoyina "masoyinka Kuma ?eh mana masoyina dake bbiyata a duk Inda na Saka kafa kaga dole na kiraka da masoyi yakamata ace kasan Koni wanene shiyasa ma na kiraka na sanar da Kai wani Abu da baka sani ba .
cike da zakuwa dcp yace "Ina jinka a she dai kana bukatar mu tautauna kenan ? ya mike cike da hanzari yana cewa "Ina saurareka me yasa kake aikata abinda kake aikatawa ?"so kake kasan dalilin da yasa nake aikata hakan? dcp ya gyada masa kai kmr yana gabansa " amman Kuma sanin dalilin ba fa shine me mahimmam ba sanin mahimmam aikina yafi ."
"yanzu har aikin fashi da garkuwar da mutane yana da wani mahimmanci ? Sannan Kai fa masheki ne "kwarai kuwa mahimmancinsa ne ma yasa nake aikata shi da kwarin gwaiwa ,kace masheki a karshen maganarka waye na sheke ?
"ban sani ba amman Kai ai kasan me laifi ne ? "Kenan har yanzu ana kan kirana da me laifi ? Idan ni an kirani da mai laifi su tanko gote da tawagarsa fa me za'a kirasu dashi ? gskiya Kai din mai baseera ne ya kamata na tayaka murna sosai amman meye laifina akan abinda nake aikatawa ?"
"shikenan na yarda baka da laifi amman Ina son na had'u da Kai mu tautaunawa abu me mahimmanci nima yanzu zan goyi banyanka dan nasan akwai jami'an tsaro da dama da suke aiki karkashin ikonka masu kawo maka rahoto akanmu' "dakata dcp har yanzu ba'a haifi uwar d'an da zai min wayo ba" dcp ya runtse idanunshi yana shafa goshinsa " ni nan da wayona aka haifeni idan kaga na bar mutun to naga dama ne , dcp ya furzar da iska sannan yace "Kai karka dauka wannan takamar da kake samun sauki ne ko mafuta ,karka manta har yanzu Kai din me laifi ne a kasar nan "na dauka yalla'bai dan ka kirani da me laifi amman kasani masu aikata laifin irin nawa basa ta'ba shiga hannun yansanda domin a idon alumma ba masu laifi bane idan da naso da Kai kanka bazaka iya bincike akaina ba sannan da na kawar da Kai a dazu dan ba tayar motarka zan harba kwakwaluwarka zan fasa .
"ya kamata ka taimaki rayuwarka data iyalinka ka hutar da kanka da tunaninka akaina dan bazaka iya komai ba."
"ka min shiru barawon banza kawai Kuma me garkuwa da mutane " yalla'bai ka dai kirani da kwararren d'an fashi wannan nasan Ina yi amman garkuwa da mutane wannan ba aikina bane gurinsu tanko gote zaku samu cikakken bayanai masu yi ,ku daina bibiyata dan ga dukkanin alamun Kuna sa Ina Kara yin suna a duniya kunsa koina acikin garin nan sunan jaguwa kawai ake kira .
"idan aiki kuke bukata karku manta akwai yaran da kullum ake musu fayde sannan akwai yaran da kullum ake maidasu marayu saboda basu da gata arayuwaarsu da talakawan da basu ji ba basu gani ba aka sakasu shiga tashin hankali ,
aikin ne da yakamata Kuna tsaye akansu amman duk kun kasa daukar mataki Kuna zaune a office sanye da uniform din sharri ?"bari Kuji Ina kan zuwa kan aikinsu domin na hukuntasu bisa laifinsu tunda ku cin hanci ya hanaku bawa kasarku tsaron daya dace ".
"Ina ruwanka da wannan bangaren ?baka da hurumin hukunta ko ma wanene dan Kai ba kowa bane tamkar matacce dan kana shigowa hannu mutuwa ce zata tarbeka .
"nasani yalla'bai ni ba kowa bane Kuma duk daren dadewa zan mutu ko baka fad'a ba,Amman kasan da cewa Ina kishin kasata ni d'an kasa ne me kishin Kai Kuma na zabi farinciki al'uma akan mutuwa da komai Kuma zan hukunta azzaluman sannan na kawo karshen rayuwarsu.
"wallahi Kai sheidan ne "kwarai kuwa ka kirani da abinda yafi haka indai akan gaskiyata ne na yarda ."me ! dcp ya fad'a a razane shine dansanda Amman yafi shi shiga tashin hankali.
"Eh tamkar mota haka zamu cigaba da karawa da Kai Amman kasani a koda yaushe Ina gabanka daga nan har izuwa lokacin da zaka gane ba kuskure nake aikatawa ba domin kuwa ko za'a fito da gaskiyar a yanzu bazai shafe *KUSKUREN BAYA BA* shiru dcp yayi da sauran mutane suna sauraronsa "da zaku gane da Kun daina bincike akaina Ina fatan ka fahimta masoyi "tur da Hali irin naka yanzu yaushe zaka dawo da diyar minis ...."ai kafin ya karasa mgnr yaji kit wayar ta mutu tsaki dcp yaja yace "yanzu kenan bazamu iya kamashi ba ?da alama kam inji cewar daya daga ciki police din dake gurin "aikin banza kama wannan dan fashin dole ne Koda zan rasa rayuwata dole mu cigaba da bibiyarsa tunda da alamun har yanzu bai fahimci mun tura masa jami'n sirri ba dole zai shigo hannunmu a lokacin zai gane kuskuren da yake aikatawa sai yayi dayasani mara amfani wai shi me hukunta masu laifi , nida Kai ba masoya bane makiyan juna ne yadda kake bibiyar komai namu muma hk muna bibiyar komai naka ."
********
Tanweer zaune a bakin gado tayi shiru ta zuba uban tagumi tana tunanin shikenan ta sadaukar ita da iyayenta sai alahira idan da rabon zasu had'u dan bata ga al'amun zata koma garesu ba ta barwa Allah komai komai yayi zafi maganinsa Allah
a tsakanin wannan lokacin ta lura Kullum gidan cike yake da mutane da yammata kala dabam dabam , wasu masu fasali wasu marasa fali ga shaye shaye baka jin kamshi komai a gidan sai na wiwi da ta'ba da sauran kayan shaye shaye, wannan Abu na matukar daga mata hankali idan ta tuna da irin qaunar da take wa Adnan kullum kokari take taga ta yakicesa a rayuwata dan ingata nata rayuwar amman abun ya cutura kullum soyyarsa sake nunkuwa yake amman hakan bai hanata son komawa gida ba .
ganin yadda gidan ya rikice yasa take kulle kofar d'akinta dan bazata zauna akaita a baro ba .tun da jaguwa ya lura tana kulle kofar ya tsareta yayi mata gud warning "karki sake kulle kofar nan ko da kudin ubanki na gina gidan ?"
ranta a matukar bace tace " ba da kudin ubana ka gina ba hakazalika Kai ma bada kudin ubanka ka gina ba da kudin ubannen mutane ka gi... "bata k'arasa ba taji saukar mari akan quncinta "zaki sha wahala matuka a hannuna muddin zan dinga fada kina fad'a Kuma na rantse na sake ganin kin kulle kofar d'akin nan zaki ga yadda zanyi dake ."
Ya sake d'aukar fushi me tsanani daita bata damu ba duk sanda ya fad'a sai ta fad'a masa haka rayuwar tanweer ta cigaba a gidan jaguwa cikin rashin Jin dadi da kwanciyar hankali domin kuwa a maimakon abubuwansa yayi sauki sai yayi gaba tayi fushin tayi zagin tayi rashin kunya duk abanza dan bai canza ba sannan bai sauko daga fushin da yake daita ba dan haka ta sauko daga nata fushin tayi k'okarin shawo kansa amman ya faskara ta bishi har d'akinsa ta bashi hakuri amman yaki nan itama ta fita hanyarsa ko kallon kofar d'akinsa ta daina kullum cikin addua take Allah ya kawo mata d'auki ,adduar da batayi ada shi ya zamo abokin hirarta a yanzu ."
*****
Hajiya Zainab zaune cikin halin damuwar da take kawarta hjy saratu ta kawo mata ziyara tare da diyarta mardiyya wacce ta kasance Kawa ga tanweer byn sun gaisa suka samu guri suka zauna nan ta fara bawa hjy zainab hakuri" addau zamu cigaba dayi komai zai daidata inshallahu karki sa tunani a ranki ,Allah bazai ta'ba had'a mana dadi gbdy ba idan Kuma ya had'a to wallahi mu tambayi kanmu ".hjy zainab ta kalleta cike da rauni ta girgiza Kai kawai bazan iya daina tunanin tanweer ba Allah na gode maka ban ta'ba tsammanin zan shiga tashin hankali irin haka ba a she haka iyayen da suka rasa yayansu suke ji idan akayi kidnapping dinsu ? Allah ka juyo da hankalin yan fashin nan suji tausayina dan zuciyata bazata juri rashin tan ba "hjy saratu tace" Ameen inshallahu zasu dawo daita cikin koshin lfy hjy zainab tayi shiru ta ma rasa mai zatace lamarin yan fashin Nan ya isheta hjy saratu ta Kalli hjy zainab tace "ki Kara hakuri ."
bayan sati d'aya taga alamun jaguwa ya dan fara saukowa dan har d'akin da take yake shigowa , bata kallonsa haka zalika bata ce masa komai har yayi abinda zai yi ya fita.
da yammacin ranar juma'a a bakin kofa suka yi karo dashi zata fita shi Kuma zai shigo d'akin garin ta matsa masa tayi baya zata fad'i da sauri ya Kai hannunsa ya taro bayanta , ita dake jiran ta ji bayanta ya daki kasan tayis taji saukar hannunsa ya tare ta sauke wahalalle numfashi suka tsurawa junansu Ido suna kallon kwayar idanun juna cike da shauki ko kifta idanunsu basa son yi yayi mata kyau matuka cikin shigarsa ta kullum yake wando da riga sai kamshi turare yake.
sun kusan minti biyar a haka sannan yayi k'okari janye kwayar idanunshi acikin nata
ya tsaidaita bisa kafafunta yana cewa"kin dinga kula ki daina wannan haukan tafiyan "
"haka zalika kaima ka dinga lura da naka haukan shigowan tana gama fad'ar haka ta wuce ta barshi nan yana kallon bayanta tsaki yaja ya gyara zaman rigarsa sannan ya shiga d'akin ya d'auki abinda zai dauka ya zauna zaman jiran dawowarta d'akin ya samu damar cin ubanta la'ada waje amman taki dawowa mikewa yayi ya biyota Kai tsaye falo ya nufa har zai wuce yaji motsin ta a kitchen ya k'araso ya tsaya a bakin kofa ya rike kugunsa da hanun daya wani irin kallo yayi mata na rainin wayo fuskarsa babu alamun wasa ya had'e girar sama data kasa tunda ta waigo taga irin kallon da yake mata Tasha jinin jikinta tare da rikicewa ta d'auke idanunta ta juya masa baya muryarsa a harzuke yace . "ni kike cewa mahaukaci ?
"to menene kake mamaki ?tayi mgnr a dake tana kokarin cire tsoro yayi taku d'aya yana ƙoƙarin damkota ta juyo da sauri qirjinsa ya hade danata atare suka sauke numfashi wani irin abu sukaji ya bakuncin zuciya da gangar jikinsu sakamakon haduwar da jikinsu yayi ,kasa yayi da sexy eye's dinsa suka sauka akan qirjinta tsurawa qirjin Ido yayi yana kallon tudun dukiyar fulaninta duk da cikin riga suke amman a zahiri yake kallonsu .
wani zirrr yaji lokacin daya tuno yadda yayita murzasu a wancan ranar Ina ma zai sake samun dama irinta ranar ? iya murzasu ma kawai ya ishesa ba sai ya Kai ga saduwa daita ba .
a hankali ta soma k'okarin juyawa ganin yadda yake ma qirjinta kallon kurrilla, yasa hannu ya juyo daita ta sake fuskantarsa ya hade fuskarsa tamau "har Kin isa ki juya min baya ?batace umm ba bare Uhm uhmm illa qirjinta dake dokawa fiyye da kaida "ba'a min back to back sai dai nayiwa mutun ya Bude Baki zai sake yin mgn kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya soma received call yana mata gargardi da hannunsa alamun zai ka mata sannan ya fara amsa wayar "okay to shikenan gani nan just give me 10 minit yanzu zaka gani ya juya da sauri ya fita wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da abinda take .."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️19
Da misalin karfe tara na daren ranar laraba tanweer tana bathroom tana wanka jaguwa ya shigo d'akin hannunsa rike da tabar wiwi yana zuga a hankali cikin kwarewa ,warin bai tsaya iya d'akin ba har sai daya iskota bayi , abinda tafi tsana kenan ta gansa yana shan wiwi Kuma ta lura ya fahimci bata son hakan shi yasa cikin kwanakin dan iskanci idan zai shigo sai ya shigo mata daita yana sha ,Idan ta kulle kofar d'akin ya zama balai . "
cikin fushi ta fito sanye da doguwar riga hannunta rike da towel tana cewa "dan darajan Allah ka daina shigo min kana Shan wannan abar bana son warinta "kana da ilimi amman kullum kamar dabba kake abubuwanka, tsabar shagala kullum cikin aikata abinda Allah ya haramta kake , wallahi Koni da bani da wani sani akan naka ba zanyi lalacewa irin taka ba, Kaine Zina , Kaine sata , Kai ne sha......."
Wani gigitacen mari ya wanka mata yana huci ta dafe kuncinta daidai Inda hannunsa ya sauka tana dubansa Ido fal da hawaye "akan na fad'a maka gaskiya shine ka mareni ?" to karya ne baka sata ,baka bin mata , baka..."a tsawace yace " Kada ki sake fad'a min maganar banza idan kika sake fad'a min maganar banza wallahi zanyi miki abinda har ki mutu ba zaki manta dani ba ko ubanki bai Isa ya Kalli idona ya fad'a min maganar da kika fad'a min ba bareki" .
tayi shiru tana kallonsa ta kasa cewa komai kafin daga bisani tayi kasa da muryarta ",Allah ka saka min " ya sake d'aga hannu zai sauke mata wani marin tayi saurin kaucewa ta dube shi Ido cikin Ido "da gatana da komai amman ka d'aukoni ka rabani da gatana ka maidani jaka to wallahi na barka da Allah duk abinda ka min ka jira sakamako " tana gama fad'ar haka ta juya zata bar d'akin ya biyota ya shakota ",Ina zaki ki dawo ki gama tsine min ",ni ka sakar min wuya ,bazan saka ba muddin kina son zaman Lafiyarki a gidan nan ki iya bakinki akan abubuwana dan wannan halin naki yana d'aya daga cikin abinda yasa na tsaneki yanzu sam baki da kunya ".
"naji kaima ka daina abinda zai sa na dinga maka rashin kunya , da kyar ta sanya gbdy karfinta ta kwaci kanta tana haki fixgota yayi ya maka akan gado yana mata wani irin kallo mai firgitarwa bayan second biyu ya sawa kofar key ya d'auki towel din data fito dashi ya wuce ya shiga bayi yana jan tsaki .
tanweer ta dafe kanta tana jijigawa "na shiga uku ni tanweer wani irin iftilai ne haka ya fad'a min ? yawon zagin ubana da yake yana mugun bata min rai kusan yafi duk wani wulakanci da yake mata ,da kyar ta rarrashi kanta ta kwanta tana tunani adadin kwanakinta a gidan a lisafinta ta share wata biyu kenan zata shiga na uku a hannunsa tana kwance lamo
ya fito kungunsa d'aure da towel yana goge jikinsa da alamun wanka yayi gajeren wondo ya d'auka ya saka ya kwanta kusa daita tana ganin haka tayi saurin ta matsawa daga kusa dashi dan har lokacin warin wiwi bai bar jikinsa ba ."
ganin abinda tayi yasa haushi ya kamashi cikin fushi ya fixgota jikinsa da karfi ta sake janyewa
ya sake rikota sosai "ke kin isa na kwanta kusa dake ki tashi ? "dame kike takama dashi ? ta bud'e idanunta sosai "bana takama da komai Amman gaskiya ka daina taba min jiki dan ni ba matarka bace sannan ba karuwa bace da zaka dinga had'a jikinka da nawa bazan iya irin wannan rayuwar ba, kawai ka kyaleni idan bazaka maidani gidanmu ba zan hakura na zauna amman bazan iya wannan shirmen da haukan ba wallahi idan baka farga ka tuba ba ka jira mako.." "ya Isa ! ya isheki haka jaguwa ya fad'a a fusace "ke ni zaki gayawa maganar banza akan abinda isana ya bani dama ba".tayi saurin tashi daga jikinsa ta zauna tana dubansa tace "ban fahimceka ba ? menene Isan naka ya baka ba ? Yayi mata kallon banza kana yace "ke mana ni gani nake kin zama mallakina duk da bana sonki kuma dole nayi abinda na gada dama dake ".ranta ya dugunzuma a fusace tace "wallahi karya ne , wiwin da kasha ya fada maka karya baka Isa kayi abinda kaga dama dani ba, Kuma daga yau ka daina taba koina a jikina har sanda zan bar gidan nan tunda bana Uba.. ..."
Ji tayi ya zabga mata mari a fusace tare da durowa daga kan gadon Yana dubanta" Ina gargadinki da ki iya bakinki da furta min duk Kalmar da kika ga dama domin idan ba haka zan miki rashin mutunci dan ni ko kusa ban d'auki mace a komai ba illa abun bukatata ki sani Ina da halin da zan aje irinki guda hamsim idan naso dan ma Kinga na barki haka batare da na aikata wani abun asha dake ba shine zaki kawowa mutane salo ?
"to ni Ina ruwana idan kaga dama ka cika gidan nan makil da karuwai wannan matsalarka ce ni dai karka tabani ".
Ya Isa Inda ya ajiye wayoyinsa ya d'auki daya daga ciki ya duba lamba pretty ya kira ya sa a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 67