yana gama katsewa ya juya ya nufi cikin hotel din Inda wani Kiran ya shigo bai dauka ba har sai daya shiga d'aki, yana shiga d'akin ya d'auka " hello ! jaguwa ya fad'a a hankali daga can bangaren enamdi Sunday yace "hello how are you doing my friend ?"am fine inamdi jaguwa ya fad'a idanunshi na kallon Inda tanweer ke kwance ."
"daman na kiraka ne akan sakon dana turo maka d'azu hope kaga sakona ? "Bangani ba me sakon ya kusan ? gobe akwai makudan kudaden da za'a shigo dasu murtala international airport wani abokin
mai gidana ne alhj aminu zai yi harka shine nace na sanar daku jaguwa yay murmushin gefen baki yayi "infomer " daga can bangaren enamdi yayi murmushi yana tsotsa keya ya cigaba da mgn " Kuna shigowa office din dake kallonku nan office dinsa yake dan Allah kuyi aiki da fasaha kmr yadda kuka saba kar a samu matsala domin aikinku akwai hatsari sosai any singul mistake komai zai iya faruwa saboda jami'an tsaron dake gurin "you don't have to worry inamdi komai zai tafi dade aikina dana d'auki tsawon lokaci Ina yi bana tunanin akwai matsala idan ma matsalar tazo nasan yadda zanyi handover din komai jaguwa ya qarasa maganar yana sham kamshi kmr yana gabansa ."
"yauwa friend ai Ina alfahari da Kai sai maganar percentage dina karka manta kasona yana nan kamar da dai ko ?" ai muna da cika alkwari inshallahu sosai I bet you wannan karon ma zakaji dadin muamula damu zamu baka kaso d'aya cikin uku " to to shikenan na gode sosai inamdi ya fad'a "ni ne da godiya ". Inji cewar jaguwa ,alright bye thanks yana kokarin katse wayar wani Kiran ya shigo haka yayita receive calls na tsawon lokaci madadin ya koma gurinsu jabir su cigaba da holewa sai ya karasa kusa da tanweer ya yaye bargon da take ciki ya shige jikinta ya lullubesu yana jin wani irin abu na yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa da tsananin sha'awa hannunsa d'aya ya d'aura akan ruwan cikinta yana lumshe sexy eye's dinsa yana sauke numfashi cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dashi ."
*****"
bangaren Zahra kuwa daren ranar kasa bacci tayi tana zaune cikin tsananin tashin hankalin data tsinci kanta dan gbdy ta kasa runtsawa data runtse idanunta da zumar bacci jaguwa take gani tare da yarinyar da bata san ko sunanta ba , daf da asuba bacci ya fixgeta a matukar firgice ta farka ta zauna tana haki , jikinta ya d'auki zafi kmr garwashin wuta tsinuwa kuwa ta tsinewa yarinyar yafi sai babu adadi daga karshe ta rushe da matsanacin kuka "wayyohhhly Allah naci amanar kaina , na yaudari kaina dana d'auki soyayyar duniya na daura ma Adnan kuka take sosai har da shesheka, bazan taba barinka haka ba sai na tabbatar da na kawar da hankalin kowace mace akanka tsam ta sauko daga kan katifa ta jingina jikinta da bangon d'akin ta runtse idanunta masu zubar da zafafan hawaye masu zafin gaske tana Neman mafuta.
wata zuciyar na bata shawarar ta hakura dashi yayinda wata zuciyar ke karfafa mata gwiwar tabi kowace hanya dan ta mallaki jaguwa sosai tayi zurfi cikin tsananin tunani da tashin hankali ,babu wacce tazo mata sai kawarta blessing da suka had'u a shurem blessing yar asalin edo state ce akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu blessing ta sha bata shawara ta dinga binta zuwa garinsu idan zata domin ta had'ata da manyan bokaye dan ta qara samun d'aukaka a harka karuwanci amman taki naunayen ajiyar zuciya ta sauke na samun mafuta dan kuwa tasan blessing zata taimaka mata tun da asuban fari ta kirata tana kuka ta sheida mata halin da take ciki take blessing tace "ki shirya kawai ki zo muje garinmu na gode blessing ai muddin kika min wannan taimakon bazan taba mantawa dake ba "karki damu zahra ai wannan ba wani abu bane amman Ina tabbatar miki muddin na Kai ki gurin malamai sai yadda kikayi da jaguwa sai ya zamo tamkar bawanki "na gode na gode ",Kai haba Zahra ai mun zama daya tuntuni kece dai baki d'auki hakan ba ki shirya mu hadu a iyanapaja dan Ina royal stream hotel nan kwana zan k'arasa na siya mana ticket kafin kizo "okay sai nazo cikin saurin ta soma shirinta tana jin sanyi da natsuwar zuciya."
Mika jaguwa yayi had'e da salati Ya sake kwakumeta tsam ajikinsa yana sauke numfashi a hankali kmr bazai bud'e Idanunsa ba amman dole ya bud'e sakamakon wayarsa dake Kiran sallah alamun lokacin sallah yayi ya bud'e tsumammamun idanunshi ya kunna wutar d'akin wanda yasa ta d'an motsa tana shigewa jikinsa hade da d'aura hannunta akan chest Kuma daidai nipples dinsa sauri d'auke numfashi yayi gabansa na faduwa yayi shiru na tsawon lokaci yana tunaninta abubuwa dayawa akan yarinyar ya d'an dade kwance idanunshi biyu sannan ya cire hannunta a chest dinsa ya sauko a natse ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d'auki daya yana dubawa karfe bakwai saura na safe bai so wannan lokacin ya taddashi a hotel din ba shi daya so tun asuban fari ya bar hotel din Kai tsaye bayi ya shiga ya fara da sakarwa jikinsa ruwa sannan ya dauro alwala ya fito ya saka kayansa ya Kalli gabas ya tadda sallah byn ya idar ya mike ya Isa Inda take kwance ya Kai hannuwansa tsakiyar kafafunta yana shafawa a hankali ta bud'e idanunta sakamakon jin damshin ruwan hannunsa na ratsata idanunshi cikin nata yace "tashi kiyi sallah lokaci na tafiya ta janyo bargo ta lullu'be jikinta sosai dan babu komai ajikinta muryarta can kasa tace "okay ka miko min towel na d'aura "Dan Allah malama ki tashi kije dauka karki bata min lokaci ya k'arasa maganar a fusace shagwabe fuska tayi kmr zatayi kuka "babu komai ajikina fa tsaki yaja ya mike ya janyo towel ajikin kofar bayi ya jefa mata a fuska ta d'aura ta soma k'okarin saukowa "kiyi sauri please Ina da appointment ya fad'a kwayar idanunshi na kanta bata ce Komai ba ta nufi bayi yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her komai nata dabam ne ta had'u sosai ilarta dai rashin kunya har ta shige bayi idanunshi na kanta itama sai data yi wanka sannan ta dauro alwala ta fito a lokaci da yake waya da anas "karka damu ku bani minti ashirin yanzu zaku gani murmushi yayi yace "Kai anas me yasa ka fiyye damun kanka nace maka ba abinda kake tunani bane shikenan koma dai menene ba abinda kake zato bane ya katse Kiran ya kira ammina Inda yake sheida mata Yana da aiki me mahimmancin da zashi shi da abokan aikinsa yana bukatar adduarta"Allah ya tsareku yasa ayi aiki cikin nasara amman dan Allah kabi a hankali kasan Kai ne rayuwarmu sannan da zarar ka kammala da komai kazo
naganka karka ce sai karshen sati zaka zo gbdy "karki damu ammi inshallahu bazan Kai ba me zan taho Miki dashi ?".Shiru tayi tana tunanin kafin daga baya tace "komai ka kawo amminka zatayi farinciki murmushi yayi yace "shikenan my happiness murmushi tayi daga bangarenta ta sake Aiko masa da addua komai dare idan na dawo zan kiraki karki yi bacci har sai Kinga kirana kinji ammina tace "to Adnan inshallahu zan jira kiranka sun d'auki minti biyar suna waya har da kannensa ,sanda tanweer ta kammala shirinta taja ta tsaya tana kare masa kallon tsab yana matukar burgeta yadda bai wasa da lamarin mahaifiyarsa da kannensa a dan zamanta dashi ta fahimci yadda yake mugu mugun son mahaifiyarsa har sanda ya k'araso gareta ya riko tsintsiyar hannunta tana can duniyar tunani kumatunta ya ja kadan tayi firgib ta dawo natsuwarta tana sauke ajiyar zuciya tsurawa juna idanu sukayi batare data ce masa komai ba
ya nufi hanyar fitowa daga d'akin daita tana biye dashi ."
Yana fitowa haraban hotel din idanunshi suka ci karo da motar alqali murfin motar a bude wasu mutane na tsaye suna duba cikin motar ,sai lokacin ya tuna da yasa a tsare masa shi ,Kai tsaye gurin motarsa ya nufa ya bude wa tanweer gaban mota ta shiga ta zauna ya rufe ya zagaya ya shiga bangaren direba ya shiga ya zauna ya tadda motar yana fitowa ya sawa motar wuta kamar Wanda zai tashi sama "kabi a hankali please Ina matukar son rayuwata domin tana da matukar mahimmanci ga iyaye saboda nice duniyarsu "Ina da mahaifiya da kanne day day har guda uku mafi soyuwa a zuciyata bazan so suyi maraicina ba bare ki fada min maganar banza yayi mgnr a tsawace yana dukan stearing motar shiru tayi tana zance zuci kafin daga bisani ta motsa labbanta a hankali "kana son mahaifiyarka da kannenka sosai ?" tayi maganar tana kallonsa da gefen Ido da kmr bazai yi mgn ba sai dai mahimmancin su ya wuce ya banzatar da amsar dan haka yace "kwarai kuwa ina matukar son mahaifiyata da kannena so na gaskiya son da bana Jin akwai wani mahalikin da yake wa ahlinsa "Amman shi ...." maid your thought karki sake furta komai akan ahlina ya fad'a yana cigaba da murza stearing ,dole taja bakinta tayi shiru ".
cikin kankanin lokaci ya k'araso gida Kai tsaye bangarensa ya wuce da tanweer ta tsaya tana dubansa "ki kwanta ki cigaba da baccinki nasan bai isheki ba "batun komawata gida fa ?"zan maidake amman ba yanzu ba ki bani lokaci tayi kicin kicin da ranta kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa "gsky nifa na gaji wallahi gida nake bukata idan baka yarda ka maidani ba zan bi ta kowani hanya na bar gidan nan "ki gwada ki kigani idan hakan abu ne me sauki yayi mgnr tare da yin shiru yana dubanta dan tuni idanunta sun cicciko da ruwan hawaye "ban San me yasa kake min haka ba ,idan km kasan kana da dalilin rikeni ka fad'a min nasan zaman da nake yi amman bawai ka rikeni ba alhalin ni din ba muharamarka bace ta k'arasa maganar tana jan numfashi da danne kukanta tabbas jikina na bani akwai sirrin da kake boye min meye shi Ina son sani ?".Tayi taku daya biyu ta qaraso gabansa qirjinta na dokawa da matsanacin karfi ta cigaba da magana a natse zuciyarta na rawa "zuwa yanzu ya kamata ka sanar dani menene shi abinda kake k'okarin boyewa " take jikinsa yayi sanyi kmr Wanda aka jefa cikin kankara "zuciyata ta fara jefo min abubuwa masu wuyar misaltuwa akanka sai dai na shirya jin koma menene ta k'arasa maganar tana kuka dan ta kasa rike kukanta ."
ya Kai hannuwansa duka yana qokarin zagaye kugunta ta zame jikinta ta koma bakin gado ta zauna ta kife Kanta akan cinyarta tana cigaba da kukanta ya k'araso ya janyo stood ya zauna a gabanta ya riko hannunta daya cikin nasa ta d'ago runannun idanunta ta zuba masa tana sauraron abinda zai ce sai daya furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya fara magana a natse kmr me koyon mgn "kunnewanki bazasu iya Jin dalili
ko sirrin dayasa nake rike dake a gidan ba , hankalinki bazai iya dauka ba wallahi zuciyarki zata buga idan kikaji mafi alkhairinsa ki bar wannan maganar "na bar wannan maganar saboda me byn kana rike da rayuwata ka tsareni ka hanani naje ga iyayena alhalin suna cikin damuwar rashina ta k'arasa maganar tana fixge hannuwanta ya sake riko hannuwanta da sauri "shikenan ki bani lokaci kad'an nasan dai bazaki sake d'aukar lakacin da kikayi tare dani ba a gidan nan ". ya qarasa mgn Yana goge mata hawayenta dake tsiyaya a idanunta tare da yin shiru yana kallonta itama shi take kallo zuciyarta na zafi "to shikenan amman kayi min alfarma ka bani waya Ina son Jin muryar iyayena ,Ina kwadayi jin muryarsu dan Allah karka ce a'a".
" ya mike tsaye yana cewa "zanyi nazarin akan haka yana gama fad'ar haka ya fita daga d'akin ta kwanta sharaf akan makeken gadonsa tana kuka tana tunanin yadda zata bar gidan ta kowani hali .Kai tsaye d'akin ajiya makamansa ya nufa Inda ya iske abokansa da yaransa suna zaman jiransa a hankali ya shiga yi musu bayanin Inda kowannensu zai tsaya da zarar sun Isa airport ya d'auki sama da awa biyu yana musu bayanin har sanda karfe goma shabiyu ta buga ya d'ago yana duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa a natse ya d'auke kyawawan idanunshi ya d'aura akan Scorpio tare da bashi umarni "kaje ka siyowa tanweer abinci ya lumshe sexy eye's na second biyu sannan ya Bude ya jiyo ya Kalli eku "Kai Kuma kaje ma'ajiyin kudi ka diba ka siyo kayan d'anye abinci da duk abinda kasan za'a bukata na abinci ka tabbatar ka siyo "okay boss ".
gbdy abokansa suka zuba masa Ido kawai suna kallonsa cike da tsananin mamakinsa " kamil ne yayi karfin halin tambayarsa "me za'a yi da d'anye abinci Kuma ?""Wa wannan yarinyar ne ya bashi amsa atakaice yana furzar da iska , duk da yaki yarda da son yarinyar yake amman su sun fahimci matakin soyayyar da yakewa yarinyar , soyayya ce me zafi da wuyar bari, soyayya ce da mutun bai Isa ya iya barinta ba cikin dadin rai " jaguwa amman dai ...." saurin d'agawa anas hannu yayi saboda yasan me zai fito daga bakinsa "ya zaka katseshi ka barshi yayi magana mana ?".bazan barshi ba dan nasan maganarsa iska ce da shirme ya fad'a yana runtse idanuwanshi tare da shafa sumar kanshi . kamil yace "kenan mu din yan iskanka ne sannan mashiririta ? tsuke bakinsa yayi yana kallonsu d'aya byn daya yana girgiza musu Kai alamun a'a "haka ne mana jubi ya fad'a "ada Kai din mai son a fad'a maka gsky ne amman me yasa yanzu duk ka canza bafa ayi haka damu ba ,ba'ayi damu zamu d'auko yarinyar mutane mu ajiyeta ba meye ma amfanin rike musu yarinya idan kana son yarinyar why not ka fada mana mu san abunyi ?"no no jubi Sam babu wannan a raina ta ya ma zan d'aukarwa kaina soyayya soyayyar ma da diyar minster Sam Sam hakan ba me yiwu bane ?
"me yasa zaka fadi haka byn zuciya gareka kamar kowani halitta "kunga dan Allah ku bar maganar nan haka, bama zan iya wata soyayya ba a yanzu kawai dai Ina gudar mata sharrin wannan mutumin ne me Katon ciki ban San wani tuggu zai sake had'a mata ba Ina tausayinta Ina Jin kamar zai cutar daita ne Idan na mayar daita ",saboda zunzurutun qaunar da kake mata ba shiyasa kake Jin tausayinta ",oh my god jubril wai ya kuke min haka ne ?"idan Ina son yarinyar nan wallahi zan fad'a muku dan bamu Saba boyewa juna komai ba , ku yarda bana son yarinyar nan " shiru sukayi suka cigaba da kallonsa ba dan sun yarda dashi ba har ya juya ya kusan kofar fitar sannan yace " eku Scorpio "zaman munafurcin me kukeyi dan Allah ku tashe kuje kuyi abinda na sakaku bamu da lokaci " da sauri suka mike suna shafa kansu ."
Cikin takun Isa da Jin shi wani ne ya nufi haraban gidan hannunsa d'aya soke cikin aljihun wandonsa eku da Scorpio suka fice da sauri suka nufi Inda ya aikesu , yana nan tsaye yaga fitowar tanweer tana karewa haraban gidan kallo fuskarta d'auke da murmushin jin dadi ba kamar d'azu ba , a kallon da yake mata ya lura hankalinta na kan shukokin gidan ne ,yana kallonta ta cigaba da takawa a hankali har ta Isa Inda shukokin suke tana shafawa a hankali tana lumshe idanu , a natse ta karya kwana tabi hannunta na hagu ,cike da natsuwa ya biyo bayanta , bata tsaya koina ba sai gurin fararen fure dake shuke cikin ruwa har lokacin fuskarta da murmushi , ya k'araso ya tsaya a bayanta yana sauke numfashi, saukar numfashinsa yasa ta juyo a tsorace har qirjinta na ta'ba nashi saurin d'auke numfashi yayi qirjinsa na tsananta bugu , ganin shine tsaye yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta juya ta cigaba da kallon fararen fure muryarta a sanyaye tace " ina son fararen fure ko zaka tsinko min? ta fad'a tana duban Inda yake tsaye har lokacin hannunsa na soke cikin aljihunsa " kina son fure ne haka ? ya tmbyeta yana kare mata kallo tsab " sosai Ina qaunar fararen fure arayuwata ya qara taku biyu yayi kusa daita sosai yana cewa "yarinyar da nake so itama tana matukar son fure " qirjinta ne yayi wani irin bugawa da karfi , taji saukar maganarsa kamar saukar aradu ,zafi ta dinga ji a qirjinta tamkar ana diga mata ruwan dalma nan take ta nemi natsuwarta ta rasa idanunta na kan furen tace "wacece ita yarinyar da kake so ? ta tambayesa kwayar idanunta cikin nashi ,bai bata amsa ba duk da ya lura da canzawar da tayi a lokaci daya sakamakon jin yana son wata dariya taso subuce masa dan yadda ta had'e rai abun babu sauki kace shi din mijinta ne .
ranta a 'bace ta soma tafiya zuwa wani bangaren "ke Ina zaki ?itama banza tayi masa kamar yadda yayi mata "ba dake nake magana ba kina jina ? still banza ta masa " ki koma ciki kar na sake ganin kafafunki kin fito haraban gidan nan bare nan. "dan me yasa bazan fito ba ? ta fad'a a fusace tana Jin wani irin zafi mara misaltuwa sannan ta juyo ta fuskancesa fuskarta a had'e tamakr ba itace take murmushi a sakwanin da suka wuce ba , ta rasa dalilin wannan so da take masa , soyayyarsa me karfi ce agareta ,bata ta'ba sanin tana da kishin irin haka ba sai yanzu daya furta yana son wata ba ita ba yace baya son zahra sannan baya sonta to wacece wannan daya furta da bakinsa ? Ido cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun juna kamar ta rufesa da duka ko zata samu sausauci ,k'okarin danne kishin tayi ta sanyawa jikinta jarumta "ko bazanje koina ba ka barni na dinga fitowa Ina ganin fararen fure tayi mgnr kmr zatayi kuka ,bai ce mata Komai ba ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita bai tsaya a koina ba sai d'akinta ya bud'e kofar ya turata "iya nan na yarda kiyi rayuwa aciki ko falon gidan nan ban yarda ki fito ba idan Kuma kikayi kuskuren fitowa zaki ga abinda zan miki ya k'arasa maganar tare da ya janye kofar ya rufe garam , ita duk wannan abun da yayi bai dameta ba akan zance budurwa da yayi mata shi yafi komai ta'ba zuciyarta da d'aga mata hankali, tsaki taja yafi sau goma ajere " Allah! Allah !! ka tsi ...." shiru tayi ta kasa tsine masa shi da budurwar da yake so ta koma karshen gado ta zauna tare da zuba tagumi ."
ya shiga d'akinsa ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya tsaya shiru cikin bathtube ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa yana tunanin maganar abokansa akan yarinyar "duk suna min kallon d'an soyayya alhalin ba haka bane acikin zuciyarsa ," taimako ai ba soyayya ce? ya tambayi kanshi ya d'an dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d'aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya riga blue wanda a gabansa aka rubuta polo 1967 yayinda wondon da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa yake , tsintsiyar hannunsa d'aure da agogon rolex ya rufe idanunshi da glass baki ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita, falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d'akin da tanweer take ."
tana Jin shigowarsa amman taki d'agowa daga kwance da take dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa "ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje wani aiki me mahimmanci zan dan dade kafin na dawo batare data d'ago ba tace "a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya ". "ki daina damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy idan lokaci yayi ya juya ya fara tafiya cikin hanzarin wannan karon d'akin dake gefen d'akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d'aya yayi sautin muryar scopio ya fito dashi "boss komai ya kammala "okay kana iya tafiya ya fad'a d'akin tanweer yana cewa " nasa a kawo komai na kayan abinci muje kiga kitchen din ". banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba ya zuba mata Ido har kusan minti biyar kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had'ad'd'en kitchen din ."
a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen din very Niet kamar mace ce ke amfani dashi babu abinda babu na kayan abinci komai gashin nan ajiye yasa an kawo," ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so ". idanunta da suka canza kala sukayi jazir tsabar kishi ta d'ago ta sauke su akan fuskar jaguwa dake tsaye a gabanta yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin matan nan ne masu shep din cocakola "dan tani da baka tanadin wad'an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na .." ".shiiiii ya d'aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma rungumeta ajikinsa yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .
wani irin haushi ne da bata ta'ba jin irinsa ba ya diran mata a kahon zuciya ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar iskar karfi da yaji ta soma mutsu mutsun kwatar jikinta domin zuwa wannan lokacin zuciyarta ban da zafin kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin karfinta amman yaki sakinta ya kamkameta tsam yana son yaga karshen karfinta "Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya quntatawa kannenka ". cak ya saketa yana furzar da numfashin mai zafi daga bakinsa idan akwai abinda ya tsana bai wuce a ta'ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa a tsarke yace"tan ...."bata d'ago ta kallesa ba "karki sake sako kannena cikin shirmenki idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake ."
"Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu muddin baka maidani ga iyayena ba wallahi na dinga ma kannenka mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni ne sai dai a yanzu taunina ya Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa "waye Kai Adnan ? Ka fad'a min waye Kai Ina son sani kai din waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din zuciyarsa na rawa bai ta'ba Jin tsoron wani yasan sana'arsa ba ko sanin ko shi waye sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta bazai ta'ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa haraban gidan , tuni su kamil ,anas, jubi, da jabir da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya bud'e
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 67