You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
mayafi baki haka ka'fafunta sanye suke cikin baby shoe baki masu matukar kyau tsintsiyar hannunta d'aure da agogo fata baki duk jaguwa ne ya bata su a wannin da suka gaba tare da yi mata albishir din maidata gidan iyayenta , kayan sun amshi jikinta sosai kamar dan ita aka yisu .
a hankali itama ta juyo cike da natsuwa fuskarta d'auke da murmushin jin dadi zata gida taga iyayenta cikin sa'a shima ya Kalli Inda take idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin bugawa qirjinsu yayi , alokaci d'aya sukai shiru tare da tsurawa juna idanu gbdy suka kasa d'auke idanunsu .
a cikin zuciyarsa yake yabawa kyawunta "hakika tsarki ya tabbata ga ubangiji daya halicci wannan yarinyar , kallo d'aya zaka mata kasan kyakkyawa ce ajin farko ."
a natse ya d'auke kyawawan idanunshi acikin nata sakamakon ganin yadda ta kafe shi da nata idanunta da suka wadatu da zararan gashi Ido gashi ko kifta su bata yi shi kuma mutun ne da bai fiyye son kallo ba bare kallo irin nata dake saukar masa da kasala tare da sha'awa me tsayawa arai , dan nan take kallonta kesa yanayin mutun ya sauya batare daya shiryawa hakan ba." kasa d'auke idanunta tayi daga kallonsa saboda baiwar kyau da Allah yayi masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika idan ta Kalli kanta a mirrow tana tabbatar da abinda mutane ke yawon fad'a akan tsarin jiki da kyawunta sai dai ko kusa bata kai shi komai ba , dan idan tana gabansa raina komai nata take domin gani take ya fita komai bama za'a a had'a ba .
muryarsa a kasalance ta fito kmr baya son yin magana "ki daina yiwa namiji irin wannan kallon domin duk macen dake kallon nmj haka yana nuna alamun bata da cikakken tarbiya ,mace da kunya da kauda Kai aka santa " ya qarasa maganar yana jan dogon tsaki dake 'batawa duk wanda akayi dominsa rai , runtse idanunta tayi gam tana zance zuci "nice mara tarbiya sannan mara kunya ?"tayiwa kanta tambayar ranta na quna da tuttukin bakincikin daya maye gurbin farincikin dake kwance a fuskarta , idan akwai abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce wulakanci irin wannan ba , kusan second biyu tayi idanunta na runtse kamar bataji abinda yace ba , cikin natsuwa taje d'aura laulausan tafin hannunta saman kushin din kujera domin gyara zamanta taji ya sauka akan laulausan hannunshi nan take yaji qirjinsa ya cigaba da bugawar da yake , itama qirjinta ya shiga dukan uku uku dan wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa .
ya sauke wani zazzafan ajiyar zuciya da numfashi alokaci d'aya ,
a hankali tayi karfin halin d'auke hannunta dake saman nashi a dalilin jikinta dake kyarma ta soma magana cikin fushi da bacin rai "karka sake furta min wannan kalmar domin kuwa kallon nmj bashi ke nuna rashin tarbiya ko rashin kunya ba dan haka bana son sake jin kalmar gareni domin ni din macece me tarbiya da kima idan Kai baka ganin kimata akwai dayawa masu gani ta k'arasa maganar hawaye na gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai tana goge hawayenta dake tsiyaya "wani kallon banza ya watsa mata mai hade da harara " lallai yarinyar nan ma ta sameshi yadda ya kamata ,shi take maidawa magana ?ai duk laifinka ne da baka gyara mata zama ba ka tsaya kana tattalinta, yarinyar da yaka mata ka wulakantata ta hanyar keta mata haddi tunda abinda yasa ka d'aukota kenan " zuciyarsa ta fad'a masa
haka numfashi ya fesar yana jin zafin acikin zuciyarsa , sam bai ji d'acin Kalmar daya fad'a mata ba, dan haka yayi tunani sake musguna mata jikinsa a sanyaye ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta yana sake watsa mata kallon bazan tayi saurin gocewa tana furzar da numfashi tare da hura hanci sannan taki waigowa ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta barshi tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda ya sha fad'a mata ."
ya matso kusa daita Sosai yana busa mata iskar bakinsa , bakinciki da takaici yasa tayi saurin janye jikinta daga nashi tana kallon gefen titi ,shiru yayi yana kallon gefen fuskarta numfashi ma da kyar take fesarwa bai san yadda akayi ba ya sake matsowa sosai ya d'aura kanshi a saman kafad'arta ,shiru tayi taki motsi sannan taki waigowa, jin shiru taki motsawa ya tabbatar masa da lallai fushi tayi dashi tsintar Kansa yayi da rashin jin dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had'e da jan dogon tsaki "me yasa zan ji babu dadi araina dan tayi fushi dani ?ya jefawa kwakwaluwarsa tambayar " Kiran daya shigo wayarsa ya katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu'bo wayarsa daga cikin aljihun wandonsa ya mannata a kunnensa batare daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar amminsa ce yasa shi barin jikinta da hanzarinsa dan yana expecting jin dadd'adan labari daga bakinta dan jiya da sukayi waya yake sheida mata ya kamata ace yaron dake son shefiqa ya turo iyayensa ayi maganar aure ,a lokacin ammi ta tabbatar masa da zatayiwa shafiqa din magana , ai kuwa abinda yake expecting ji shi ta fara fad'a masa yasa wayar a hands free ya d'aura wayar a kafad'arsa ya jingina jikinsa sosai a kujera."
"yaron nan gali wai zai turo iyayensa ranar lahadi tare da saka rana gbdy " murmushi jaguwa ya saki na farinciki yana cewa " Allah ya nuna mana ranar lafiya so nake na aurar dasu gbdy kafin nawa auren . "a'a ban yarda da wannan tsarin ba ,idan ma son samu ne a had'a auren da naka ba qaramin farinciki zanyi ba "shinkenan ammina yadda kikace haka za'a yi bani da za'bin da ya wuce naki zanyi k'okari naga anyi auren da nawa sai dai ki qara addua akan wanda kike min Allah yasa na samu me sona tsakani da Allah "zaka samu da iKon allah dan baka da makusar da wata diya mace zata kika ni dai fatana kayi kokari ka cika min alkawarina Ina son kyakkyawar suruka me nagarta idan son samu ne wacce ta fika kyau". wani narkakken murmushi ya saki kamar yana gabanta kana yace "kin samu kin gama ammina dan sai na kawo miki irin matan hurul'ain dan irinta kike bukata ta zama surukarki ya k'arasa maganar yana dariya tare da matsowa ya kamo yatsun hannun tanweer ya rike gam cikin nashi yana massaging a hankali , itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan take so , ita Kuwa tanweer gbdy ranta a dagule yake sbd haushin abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa dan duk tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa sannan tana Jin amsar da yake Bata cike da fushi ta soma k'okarin zare hannunta cikin nashi tana sauke wahalalle numfashi sai dai ta kasa kwatar hannunta dan haka tayita jan tsaki babu kaukautawa ganin hk yasa yayi sallama da ammi tun kafin ta tunhumeshi ,ya katse Kiran yana cewa "ki daina wahalar da kanki bake ba ko namiji dan'uwana na rike bai Isa ya kwace ba bare ke " ko kina tunani ni din irin lusaran samarinkanki ne da zaki gwada karfi dani ..?"ya karasa tmyr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."
danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi tana zance zuci" shi take mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace , tunda suka had'u yake kyautata mata ta hanyar bata kulawa sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce ya 'bata mata rai ta hanyar fada mata baqaqen maganganu . tasan ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata kyau sama sama ta dinga fidda numfashi tana danne damuwarta "dan Allah direba ka taka motar nan da sauri Ina son d'aura kwayar idanuna akan iyayena wad'anda suka zamo min bango abun ma jingina kuma farincikina nasan suma nice farincikinsu rashina baqaramin babban tashin hankali bane garesu suna can suna mararina"
"shiiiii......." munafurcin banza kawai kina dai son kije kiga wad'an can rubabbun samarin naki barin wancan me murya gangarin da bata dadin saurara "ya Allah ta furta dan sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace "kafa san irin maganar da zaka dinga fad'a min dan ni din ba motar haya bace bare kayi tunanin Ina tara kwashe kwashen samari Ko da yake yau ne final kasancewata da kai zaka mayardani gidanmu na gode da taimako ta k'arasa maganar tana murgad'a masa 'karamin bakinta "karki gode min ki godewa Allah sannan na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace " aikin banza kawai Nima daga yau ai bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan dogon tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke fuskarsa yace "wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa'anki ne da zaki dinga ja min tsaki yayi tmbyr yana murd'e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa "a'a kayi hakuri hannuna zafi bai mata magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun tare da bud'e tafin hannun ya tsurawa tsakiyar hannunta kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d'aura dayan hannunsa ciki ya fara mata tafiyar tsutsa wani irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin da take saukewa da kyar tare da jin wani sauyi na dabam a sansar jikinta. Shima wani irin abu yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu ,wayarsa ya d'auka ya soma danne danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake tukasu ."eku ka duba wayarka na tura maka sako eku yace "noted boss ya tura wa su anas dake bayansa Sako kamar yadda ya turawa eku sannan ya koma ya jingina bayansa ya runtse idanunshi .."
motar bata tsaya a koina ba sai gaban katon get din Rita Lori hotel dake onipan , get din already a bud'e yake kamar Koda yaushe security's ne tam ciki da wajen hotel din saboda manya masu kudi da kusoshin gwanati dake zuwa da manya manyan yan fashi da makami , gurin fitowa daga ciki hotel din dabam haka zalika gurin shiga dabam , eku ya sanya hancin motarsa cikin Rita Lori, d'aya daga cikin security's din gurin ya mike da sauri ya zare karfen da sakale Wanda ke bawa mutun damar shiga, eku ya samu guri ya soma k'okarin parking adaidai lokacin da motar alqali danasu anas ya shigo
haraban hotel ne dake da bangare dabam dabam dan shakatawa sam tanweer bata fahimci Inda suke ba saboda ranta dake 'bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune ya bud' mata kofa "fito ko ".ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa
ta yunkura a hankali ta fito tana jiran ta ganta a haraban gidansu kawai ta ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar hannunta ya fara tafiya daita zuwa cikin had'ad'd'en club din dake ciki, banda sautin kidi da waka baka Jin sautin komai "Ina ne nan ka kawoni ? tayi masa tambayar muryarta a tsarke "gurin shakatawa yayi maganar a dake yana cigaba da tafiya daita yayinda har lokacin hannunta na cikin nashi jikinta na rawa taja ta tsaya qirjinta na wani irin bugu fiyye da kaida juyowa yayi ya tsaida idanunshi a kanta take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke "gida mukayi da Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau sotsan lips dinta ." ni gaskiya gida nake son zuwa ba nan ba ka Kai gidanmu tayi maganar kamar zatayi kuka dan tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace "Kinga dan Allah ki kwantar da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d'aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin maganrsa " kennan idan ta fahimci maganarsa shine d'an fashin daya d'aukota daga gaban iyayenta ? wani irin bugu gabanta ya sake yi da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k'okarin tsayawa hankalinta yayi matukar tashi ta dinga maimaita kalmarsa ta karshe daya furta ."
a hankali ta shiga girgiza Kai "no no impossible bashi bane sam bai yi kama da irin wad'an nan mutane ba dukkanin alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne zuciyarta ta tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba da tafiya cikin Isa da izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa wani yawu ta hadeye tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta shiga d'aga ka'fafunta kmr walkiya ya nemeta ya rasa Yana nan tsaye su anas suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa kowanne ya kama gabansa kasancewar kowannensu akwai bangaren da yafi so ."
*******
Tsaye tanweer tayi aguri d'aya kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda ta tsinci kanta a yau din nan , ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya samu guri ya zauna akan d'aya daga cikin fararen kujerarun dake gurin ta waiga bangarenta na dama tsaye taga wasu matasan mata su biyu akan stage daya sanye da kaya wando da riga yellow dinki gbamu gbamu ka'fafunta sanye da sander shima baki hannunta rike da speaker tana rera waka yayinda yaranata ke mata amshi dayar mata itama sanye da wando da riga sai dai nata kalar ja ne gbdy haraban gurin shirye yake da fararen kujeru da table a tsakiya ."
tun daga nesa mawakiyar ta fara bud'e hakoranta dan ganin anas na shigowa nan take salon wakar ya canza salo ta soma masa waka tana sake fad'ada fuskarta da murmushin irin nasu na gogaggun yan duniya Shima murmushi ya sakar mata sannan ya soma qarasowa Inda take itama ta nufo shi suka rungume juna har da kiss ta manna masa a goshi kana ya nufi gurin empty chairs ya samu guri ya zauna zamansa ke da wuya ma'aikatan gurin suka qaraso garesa tare da kwalaben giya da soyayyen nama da yaji yaji domin sun san irin abinda yake bukata kenan sa'banin jaguwa da malt kawai yake sha idan yazo.
"subhanallah tanweer ta furta a ranta tana mamakin "wai yau itace a irin wannan gurin wasu hawaye ne masu zafi sukayi nasarar biyo gefen fuskarta tana k'okarin sharesu jaguwa ya qaraso gabanta yana girgiza mata Kai alamar kartayi kuka sannan ya rungumota jikinsa ta kwantar da kanta a faffadan qirjinsa dake fitar da sihirtaccen kamshi , cikin tsananin tashin hankali yasa hannunsa ya share mata hawaye ya sake rungumeta tsam yana zagaye weist dinta da hannunwansa duka wani irin tsalle hade buguwar zuciya tanweer tayi Wanda har hakan ya haifar mata da tsayawan numfashi na wasu yan mintuna haka duk wani tunani dake tafiyar da bugun zuciyarta sai daya motsa ta dinga Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta.
yau ce rana ta farko da jaguwa ya rungume mace acikin mutane batare daya ji komai ba ajikinsa hasalima wani sanyi yaji yana bin jijiyon jikinsa ,bakinsa ya Kai cikin kunnenta yana mata rad'a wanda hkn yasa tsigar jikinta tashi "kukan ya Isa haka please kar zazzabi ya kamaki " cike da muryar kuka tace "me yasa ka kawo ni nan ? shiru yay mata tausayinta na kamashi ya d'ago fuskarta suna kallon kwayar idanun juna can ya motsa lip's dinsa "baki so mu wuce na mai dake gida yanzu ?shiru tayi ta cigaba da kallonsa yayinda zuwa lokacin idanun mutane sunyi caa akansu ciki kuwa har da abokansa da alqali daya samu nasarar shigowa "kiyi min magana idan baki bukatar kasancewa damu anan na mayar dake " nan ma shiru tayi hawaye na sake zubo mata masu zafi da radadi "wai kasancewa dasu ko su dawa oho masa ?tafiya ya soma yi daita tana makale ajikinsa har ya Kaita kan table din daya fara zama ya zaunar daita a hankali .
kuka tayi sosai taki yin shiru yayi mata magana yafi sau goma dan gbdy ya manta Kansa a gabanta sai wani narke mata yake zuciyarsa na sanyi akanta sannan baya son rabuwa daita shiru tayi kawai tana makale ajikinsa tayi yawo kasashen duniya sosai amman bata ta'ba Kai kanta irin wad'an guraren ba sai gashi a kasarta ta tsinci kanta da kyar ya rarrasheta tayi shiru ya bude mata kwalban malt ya Kai bakinta idanunshi na kanta . suna nan zaune mawakiyar ta fara bin Site by site tana waka yayinda mazauna kan table suka dinga mata liki har ta k'araso table din da jaguwa ke zaune bai daga idanunshi ya kalleta ba sai anas ne ya taso daga mazauninsa ya shiga lika mata 'yan dubu day day ta dan durkusa tare da furta "thank you sir shiyasa nake son ganinka sannan ta tsaida wakar tare da cewa ayi mata tafi nan take gurin ya d'auki tafi raf raf banda jaguwa da tanweer , sautinta ne ya cigaba da karad'e gurin anas ya tashi yana layi ya shiga rawa bayan ya gama rawa ya nufi gurin zamansa Yana rawa aikuwa makiyar ta biyosa nan gurin ya hargitse da dariya har shi anas din dariya yake sakamakon ya fahimci abinda take bukata daga garesa kudi take so ya fito da bandir din kudi ya shiga lika mata yana rawa irin tasu ta mashaya ."
Yammata ne su uku zaune acikin runfa me zagaye da wutar lantarki sai tsirarun bishiyoyi kowacce daga cikinsu hannunta rike da karan sigari da glass cup dake cike da ruwan giya "Kalli d'an iskan mutumin nan , ai na sha fad'awa sweet zahra ta fita hanyarsa ta tsaya taci lokacinta taki kamar jijiyarsa ce kadai ke da dadi , "ai Ina ganin sai ta tsinci kanta a lahira zata gane matakin daya dace daita , sam taki yarda tayi muamula da masu bukatarta inji cewar helen "kyale banza yanzu dey kirata tazo ta ganewa idanunta wata Killa tasan Inda ke mata ciwo wallahi tunda ta had'u da mutumin nan komai nata yayi qasa Ina dalili inji cewar hafcy no-no suna cewa mata haka kasancewarsa tana da dukiyar Fulani over "haka za'a yi hafcy bari na kira shegiya ta bud'e jakarta ta ciro wayarta kira d'aya zahra ta d'aga wayar cikin fara'a" sweety nah dake haka suke Kiran junansu dashi "yes sweet Helen meye labari ne ? ta amsa mata ciki fara'a.
"sweety kina ina ?" Ina gida kwance wallahi Ina hutawata " bazaki fito bane ma yau ? cikin Marairaicewa murya Zahra tace "da wahala na fito Ina son na cigaba da kame kaina a gida dan ta haka ne kawai burina zai cika akan Adnan idan ya daina ganina a guraren shakawata ko hotel hotel may be zai yi kewata har ya nemini ,ni Kuma ta haka zan bijiro masa da lallai sai dai muyi aure "wani dogon tsaki helen taja "Kinga ki raba mutane da zance wani Adnan mutumin nan ba aurenki zai yi ba sau nawa yana fad'a miki bazai aureki ba amman da yake ke karamin brain gareki kin kasa ganewa? "me Kuma ya kawo wannan maganar sweety ? kin kirani ne dan ki ta'ba zuciyata ko me ? Ko d'aya na kiraki ne dan na fahimtar dake wani abu me mahimmam na tura miki Sako ta what's app dinki ki shiga ki duba idan km zaki iya zuwa Rita Lori hotel yanzu kina iya zuwa ki ganewa idanunki komai tana gama fad'ar haka ta katse Kiran .
zahra tayi shiru sororo da waya a hannunta tana tunanin maganar Helen what's app dinta ta shiga nan idanunta suka ci karo da mugun Abu domin kuwa adana dinta ne rungume da wata yarinya da bata san kowacece ba , ta sake bude wani hoto su din ne yarinyar na tsaye a gabansa shi km yana rike da kugunta wani irin abu taji yayi mata diran makiya a qirjinta nan take ta fara jin zafi a zuciyarta tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta adalilin bugawar da take .
take gumi ya shiga karyo mata ciwon daya dade yana damun zuciyarta ya sake taso mata ya mamaye kahon zuciyarta , wannan alamarin akwai ciwo, ciwon da mikinsa ke azabtar da zuciya da gangar jikinta ,ciwon da kullum yake qara girma acikin zuciyarta, tunda ta fara son Adnan ta tsani ganinsa da kowace mace sannan Kuma zuciyarta ke cikin tashin hankali , ta zabura ta mike ta sauya kaya riga fara sol iya gwiwarta ta sakala jaka fara , haka ma takalimi fari ta fito cikin sauri tana Uber ,cikin kankanin lokaci mai Uber ya k'araso dan yana kusa daita, ta shiga gidan baya ta kame zuciyarta na wani irin zafi da ciwon da batasan ranar dainashi ba "why Adnan? me na
rasa ? "me kake so ajikin mace da bani dashi ?.me wannan yarinyar ta fini dan Allah karka bari bakincikinka ya kasheni Ina sonka fiyye da komai ta k'arasa maganar tana goge hawayenta .."
tana gama karasowa Rita Lori ta sallami me Uber sannan ta kira layin Helen kira daya ta d'auka tayi mata kwatance gurin da suke zaune ."ta k'araso ciki hankalinta a matukar tashe tana baza idanu taga ta Inda jaguwa yake da yarinyar dan idanunta babu abinda suke son da burin gani agurin kamar tagansa aiko cikin sa'a idanunta ya sauka akansa makale da tanweer kamar zai mata numfashi ita Kuma ta d'aura kanta a saman kafad'arsa saboda baccin data soma ji ga sanyi gurin dake ratsa jikinta ta shige masa sosai har suna iya jiyo numfashin juna tuni idanun Zahra suka kawo ruwa wani tunani yazo mata ko dai yayi aure ne ?" kai impossible ace Adnan dinta yayi aure Kuma ko yayi aure bazai ta'ba zuwa da matarsa gurin nan ba sai dai idan sabuwar karuwa yayi wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke ,hankalin zahra yayi kololuwar tashi gadan gadan ta nufi Inda suke zaune tana gama Isa gurin tasa kafarta d'aya ta take kafar tanweer qara ta saki mara sauti tana furta " subhanallah tare da runtse tsamammun idanunta dake cike da mayen bacci ,a hankali jaguwa yabi inuwar da ya gani tsaye akansu itama tanweer ta d'ago domin taga abinda ya take mata kafa kafin tanweer ta gama kare mata kallo har zahra ta cakumi wuyan rigarta da iyakacin karfinta "dan ubanki me kike yi tare da mijin da zan aura ? nan da nan jikin tanweer ya d'auki rawa wata razananniyar tsawa zahra ta buga mata wanda yasa jikin tanweer ya sake d'aukar qyarma zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa kuncinta muryarta na rawa tace "ki...kiyi hakuri wallahi babu komai a tsakaninmu kawai tai ..."
"Shut up useless kawai hakurin uwarki zanyi ko da yake da ganin nasan kema sabuwar shigowa karuwanci ce bancin haka da Koda millioyoyin kudi ba zaki Kalli Inda
Book Chapters
Chapter 11
Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67