Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rana ta kwalle kuma taga babu jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da take kwance sai ta mike zaune zumbur a lokacin da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai ta sauko daga kan gadon da sauri ta leka bandaki don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma sai ta iske bandakin wayam babu kowa a cikinsa a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan ta kimtsa gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata kofa saiga wata kuyanga ta shigo, kuyangar ta zube kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata sarauniya ta turoni nayi miki jagora zuwa can turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki shadila ta dubi yadda rana ta kwalle ta cikin tagar dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har yanzu sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun dade da tafiya kallon GASAR JARUMTAKA, koda jin wannan batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta ji babu abinda take so sama da ta ganta a filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da kuyangar yi maza ki kaini wajan sarauniya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin shardila na biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin dake falonta ita kadai tana jiran sai ga kuyanga tare da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike tsaye da sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin har suka kusan gama cin abincin dayansu baice kala ba a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai ta dubi luzaira tace yake kawata ki gafarceni na bata miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi kalaci ba domin barcina ne yayi nauyi, kafin shardila ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai kallonta cikin murmushi tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa akan hakan domin danki ya gaya mini cewar yana zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata matsala dake damunki koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu abinda yake damuna kuma bani da wata matsala haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da daddare wata kila bakunta ce ta janyo hakan koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda domin ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace ko dai kewar sarki shardas ce ta hanaki barci kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin na san cewa yanzu tuni an dade da fara wasa babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike tsaye saboda dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka tanadar musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun da zasuyi musu rakiya tun daga nesa shardila ta hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta ba face a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi ta kallonta, abinda bata sani ba shine tsananin kyawun fuskarta da kyan surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin GASAR JARUMTAKA. . NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba Nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square nake cewa Ku zama lafiya TSATSUBA Littafi Na Hudu (4) Part D. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan da yawa daga cikin yan kallo dai sun firgice ne da al amarin siyama kai harni Al amin da nake wannan typing din na rikice da lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri acikin lamarin Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka ne a nono kuma tun tana da shekaru hudu kacal a duniya mahaifinta ya far bata horon yaki Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin tashin tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya Luzuraina nan ta iso, take farinciki ya kama sarki hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar bakuwarmu koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma sai ya kasa sakamakon ganin wani irin mugun naushi da darkus ya yiwa siyama a fuska cikin tsananin shammace, saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga cikin hancinta kuma ya yi feshi daga cikin bakinta ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da tsananin juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama ta doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta duro kasa ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon jini har shima yaji wani jiri ya kwashe shi ya tafi luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya tokare jikinsa da hannu guda ya taso sama kamar sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki kamar ma lokacinne suka fara yakin, A dai dai wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila suka shigo cikin filin gasar suka durfafo inda su sarki ke zaune dakaru na take musu baya , tun daga nesa Abul siyama ya hango shardila sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji ba a rayuwarsa koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa domin a sannan ne ya tabbatar da abin da yake zargi duk da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don komai ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari domin ta gusar da wasu wasin dake cikin zuciyarta bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata ga mutum mai hannu daya da nakasashshiyar kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta tabbatar da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take zata shaidashi, amma har suka iso inda su sarki hulbasu ke zaune amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan hankalinta bai kawo kan Abul Siyama ba shine ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu ya zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma fuskar Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da wanibabban mayafi na alfarma, luzuraina da shardila suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga hagunsa shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa tun da suka zauna abul siyama bai yarda ya kalli inda suke ba shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma yana kan gumurzun da ake yi a tsakiyar filin gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko tunanin gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan su Luzuraina Al amin Ahmed Misau, Guyson Ko kuma A square nake yayin da shardila ta kyalla ido ta hango siyama a tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki tayi arba da fuskarta sai taji zuciyarta ta buga da karfi ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama tana matukar kama da mahaifinta, nan take shardila ta gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta ce wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru bakwai baya lallai hakan ya tabbatar mata da cewar kenan Hailur na nan a raye kuma a cikin wannan gari koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko zataga Hailur shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin da take ciki sai ya noke yana mai sunkuyar da kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya tabbatar da cewa suna hada idanu zata shaidashi duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani idan kuwa ta shaidashi a gaban kowa zata fashe da kuka ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa zai tonu su sadauki Murzanu su shaidashi idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan domin sai labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar hakan ta faru kuwa hatta sarki hulbasu ya shiga cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki shardas Cewa zaiyi ya boye babban makiyinsa a birninsa don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya mallake kasar ma gaba daya, nan take idanun Hailur suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye domin shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga ta alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki Murzanu na take mata baya sai ya kamu da tsananin bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai a yanzu ta zama matar sarki shardas, aikuwa bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila ya rungumeta nan take zuciyar hailur ta sake bugawa da karfin gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin zuciyarsa yace ' shin wannan yaro dana ne ko kuwa dan sarki shardas ne tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama don haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas shardila na dauke da cikin dana, wai shin kana zaton cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife danka a cikin gidan sarautarsa, kai hailur ! Idan ma mafarki kake yi toka farka '' wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa nan fa yaji cewar babu abinda yake bukata sama da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta bashi amsar wadannan tambayoyi dake yi masa yawo a cikin zuciya lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku uku ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas siyama tana tsananin kama da tsohon mijinta hailur babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta shine ganin irin yanayin yadda take yin yakinta Al amin ahmed nake Guyson, iri daya ne sak dana tsohon mijinta Hailur kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle kalle da waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta hailur amma shiru kamar maye yaci shirwa ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da ita duk da cewar fuskarsa a rufe take cikin rawani kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana tare da luzuraina abarin hagun sarkin, Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa wanda zai iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin damtse irin na darkus sai gashi naci da juriyar siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen mahaifinta yasa ta iya kwatar kanta awajensa tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban hannayansu har sai da suka gaji ainun makaman nasu suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar juna da hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa irinsa kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar masifar yaki sai da takai ga sun durkushe kasa a tare kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu a hakan kowannansu ya kama layi kamar wanda ya sha giya suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin wannan hali daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya luuu ! Suka baje a kasa tare suna numfarfashi kamar ransu zai fita........... . A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe Marubucin Littafin yace.... . YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN SADAUKI DARKUS DA JARUMA SIYAMA ??? . WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR JARUMTAKA A TSAKANINSU ? . MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA HAILUR DA SUKA RABU TSAWON LOKACI ? . SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI YA KAI KUNNEN BABBAN MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN YA AURI MASOYIYARSA KUMA MATARSA? . MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ? . Marubucin littafin yace mu hadu a littafi na 5 donjin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari Daga mai debe muku kewa a ko yaushe Ni Al amin Ahmed Misau Wanda keda inkiyar Guyson ko A square nake cewa Mu zama Lafiya. Amma Ku meye kuka hango a haduwar Hailur da shardila wata irin Dambarwa za a yi ne kam sai naji daga gare ku... TSATSUBA Abdulaziz s madakin gini Hausaebooks Made:- by shuraih Usman Domin samun wasu kayatattun littatafan hausa amatsayin hausa ebooks sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan wannan adireshin http://shuraih.waphall.com TSATSUBA Littafi Na Biyar (5) Part A. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus suka bingire kasa suna fitar da numfarfashi kamar ransu zai fita a dai dai wannan lokaci ne aka buga gangar tsayar da yaki sannan alkalin gasa ya rugo izuwa cikin tsakiyar fili ya fuskanci jama a yace yaku jama a kuyi sani cewa wannan gumurzu tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama babu zakara a tsakaninsu wato sunyi MUTUWAR KASKO don haka zasu sake haduwa a zagayen karshe na wannan wasa wanda za ayi rana i ta yau don haka yanzu zamu kirawo jarumai na gaba domin aci gaba da wannan gasa, gama fadin hakan keda wuya sai aka dauke sadauki Darkus da jaruma siyama daga cikin filin aka kaisu can gefe daya maimakon a shigar dasu cikin wannan asibiti wanda aka tanada domin yiwa jaruman gasar magani, dalilin da yasa kuwa ba a shigar da su cikin wannan asibiti ba shine babu mai wani babban rauni a cikinsu akan hancinsu da bakunansu ne kadai jini ke diga lokacin da jaruma siyama ta dawo cikin haiyacinta sai ta dubi inda su sarki hulbasu ke zaune tana mai mamakin dalilin da ya hana mahaifinta zuwa inda take a lokacin da hankalinta ya gushe bayan an tsayar da wasansu, bisa mamaki sai siyama taga babu mahaifinta a inda yake zaune amma kuma sai taga shardila ta kura mata idanu ko kiftawa batayi duk da cewa kuwa ta rufe fuskarta da bakin kyalle idanunta kadai ake gani nan fa hankalin siyama ya dugunzuma ainun in ba don ma ta hango mahaifiyarta ba ta taso daga inda take zaune ta taho wajenta ba da mikewa zata yi ta bazama mahaifin nata Hailur, da isowar zalima wato mahaifiyar siyama sai ta rungumete cikin murna tana mai yi mata jinjina bisa bajintar da ta nuna a wannan wasa da tayi A dai dai wannan lokaci ne wani likita yazo garesu da nufin zai duba tafiyar siyama amma sai zalina ta tsaidashi tace babu wani likita da zai duba lafiyar yata face ni don haka mun gode bama bukatar taimakonka, koda gama fadin hakan sai zalina ta bude wani kullin tsumma dake hannunta ta dauko wani ruwan magani a cikin wata yar doguwar kwalba ta mikawa siyama siyama ta karba ta bude murfin kwalbar ta sa abakinta tasha mukurwa biyu kacal sannan ta rufe kwalbar ta mai dawa zalina Faruwar hakan keda wuya sai jinin dake yoyo a hannun siyama da bakinta ya tsaya cak kamar bai taba diga ba kuma nan take taji duk gajiyar dake jikinta ta dauke fuskarta ce kawai da idanunta a dan kumbure sakamakon naushin da darkus ya yi mata a can gefe daya kuma likita ne ke duba sadauki darkus ana sa masa magani a kan hancinsa don tsaida jinin dake yoyo koda darkus ya dawo cikin hayyacinsa ya waiga bayansa yayi arba da jaruma siyama sai ya daka mata harara yaji ya tsaneta fiye da komai a rayuwarsa, nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone bisa ganin cewa yarinya karama ta gagareshi a filin gasa, nan fa ya fara tunanin cewa ta kowanne hali sai ya kaita kas a zagaye na biyu da zasu hadu wato a wasan karshe da za ayi na gasar idan rana ta zagayo kuma babu abinda zai yi ya dawo da kimarsa da mutuncinsa a birnin face ya kashe wannan karamar yarinya siyama ya zamana cewa ta mutu murus har lahira a cikin filin gasa kuwa mai gabatarwa yazo tsakiyar fili yaci gaba da jawabi sannan ya kirawo sunayan jarumai na gaba wadanda zasuyi fafata a wannan gasa A dai dai wannan lokaci ne sarki hulbasu ya dubi Hailur yace yakai abokina hakika ka baiwa yar ka horon yaki na ban al ajabi domin ta bani mamaki matuka kuma akwai alamun cewa zata iya lashe wannan gasa amma ka sani cewa lashe wannan gasa ba abune mai sauki ba saboda babu irin abinda jaruman gasar nan basayi don ganin sukai gaci, suna yin tsafi tuggu da makirci iri iri don ganin sun sami nasara ta kowacce hanya don haka dole ne kasa ido akan yarka domin daga yanzu rayuwarta na cikin hadari kada ka tafi izuwa gida kai tsaye daganan ina son ku biyoni izuwa cikin gidan sarautata domin ku dauke hankalin makiya dolene ku sauya gidan zama kuma nima zan baku shawarwari da taimako wai shin ma kasan kuwa irin ladan da yarka zata samu idan ta lashe wannan gasa ta jarumtaka ? Koda jin wannan tambaya sai hailur ya sunkui da kansa kas saboda yaga shardila ta kalleshi don kada taga kwayar idanunsa ta shaidashi sai yaki yarda ya dago kansa sa ar ma da yayi ko kadan bata jin abin da suke tattaunawa shi da sarki kasancewar suna magana ne cikin kus kus yadda babu mai iya jin abinda suke tattaunawa hailur ya risina cikin girmamawa yace yakai abokina wane irin lada za a baiwa yata idan ta lashe wannan gasa sarki hulbasu yayi murmushi sannan yace da farko dai za a bata babbar gona guda daya daga cikin manyan gonakan garin nan gami da dinare dubu dari bakwai sannan kuma zan bata mukamin shugabar dakarun dake tsaron lafiyata muddin zata iya rantsuwa bisa rike amanata da kuma siyar da rayuwarta don kare tawa idan har ta sami wannan mukami zata rinka samun albashi mafi tsoka a kan duk albashin da ake biyan dakaruna daga wannan matsayi kuma zata iya zama sarkin yakin birnin nan gaba daya bayan ta fuskanci wadansu jarrabobi da matakai Al amin Ahmed Misau, Guyson . Duk mutumin da ya sami wannan dama wacce yarka ta samu dole ne ya fuskanci makiya da yawa daga cikin manyan fadawana domin sun san cewa zaizone yafi su matsayi da arziki, lokacin da sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya dugunzuma ainun take yaji yayi nadamar sanya siyama a cikin wannan gasa saboda dalilai guda biyu dalili na farko shine yanzu ya sanya rayuwar siyama a cikin hadari domin zata tara abokan gaba wadanda za su rinka farautar rayuwarta kamar yadda mai jin kishirwa ke neman ruwan sha, abu na biyu kuma idan ta tsallake kowanne hadari da dukkan matakai da zata nisanta dashi inma bai yi sa a ba ya rasata gaba daya kamar yadda ya rasa matarsa shardila wacce ya tabbatar da cewar tana dauke da juna biyu a lokacin da suka rabu A yanzu da hailur yaga yarima hulkas sai ya fara tunanin ko dansa ne wannan yaro ko kuma dan sarki shardas ne tabbas babu mai bashi amsar wannan tambaya face shardila da kanta kuma yana shakkar ya sadu da ita domin idan wani daga cikin dakarunta ya gansu komai ya dagule kenan domin sai sarki shardas ya samu labarin cewa yana raye to ba mashi ba matarsa zalima da yarsa siyama ma rayuwarsu ta shiga hadarin da shiba zai iya kare suba hailur ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace ta yaya zan iya saduwa da shardila a sirrance ba tare da kowa ya ganni ba ko yaji babu wanda zai iya taimaka mini na iya ganawa da shadila asirrance face sarki hulbasu, hailur baya son sarki hulbasu ya san cewa shine ainihin abokin gabar sarki shardas wanda tuni aka dauka cewa ya mutu tun shekaru bakwai baya, hailu na cikin wannan tunani ne yaji an ruguntsume da wani masifaffen azababben yaki a tsakiyar filin gasa koda ya daga kansa yayi arba da jaruman biyu dake fafatawa a filin gasar sai ya cika da mamaki, ba komai ne ya sashi wannan mamaki ba face ganin cewar dayansu amintaccen yaronsa ne sadauki Ruhaisu jarumin da ya aminta dashi dari bisa dari a cikin dukkanin yaransa lokacin a yake kan matsayin shugaban kabilarsu koda hailur yayi arba da ruhaisu sai farin ciki ya lullubeshi domin indai ruhaisu na tare dashi zai iya nemo masa ire iren sauran jama arsu da sukayi saura a raye domin su sake tayar da kabilarsu kuma su taimaka masa wajan bashi kariya dashi da iyalansa jarumin da yake karawa da ruhaisu kuwa wani narkeken katone wanda ya ninkashi girma da tsayi sau uku kuma a zahiri ma yafi shi surar sdaukantakada jarumtaka ana kiransa da suna Jamar, amma suna fara artabu sai jamar ya raina kansa domin ruhaisu yafishi zafin nama da iya yaki nan da nan ya rikitashi kuma ya kuntatashi sai gashi Jamar yana ta ja da baya kuma yana ta kokarin kare kansa baya ma iya kai hari koda ruhaisu ya tabbatar da cewar yafi jamar iya yaki da fadan hannu sai kafa sai ya shammaceshi ya daka tsalle sama ya doki habarsa da guiwarsa ta dama saboda karfin dukan sai da jamar yayi sama a lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa yana saman kafin ya fado kasa sai ruhaisu ya kara dukan kirjinsa da karfin gaske kawai saiji akayi jamar ya fado kasa tim kamar giwa ta fadi kuma ya baje kas a sume ko kyakkyawan motsi ba yayi koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewa aka kama yiwa ruhaisu tafi da jinjina ba don komai ba sai don saboda shine jarumi na farko da ya fara lashe wasansa na farko a cikin kankanin lokaci da fara gasa tunda ko rabin sa a ba ayi ana gumurzun ba ya sami wannan nasara ana cikin wannan yanayine hAilur ya dubi sarki hulbasu yace hakika wannan jarumi ya burgeni matuka zan so na gana dashi, koda jin haka sai sarki hulbasu ya yi murmushi yace ai wannan mai saukine zan shirya duk yadda zaka gana dashi nan ba da dadewa ba yanzu ina so kaje ka ruko yarka da matarka ka shigo cikin tawagata domin mu shiga cikin gidan sarautata tare koda jin haka sai hailur ya dubi sarki hulbasu cikin alamun damuwa yace bana son na shiga cikin filin nan ranka ya dade ka taimaka min ka aika wani daga cikin hadimanka ya taho da siyama da zalina koda jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi murmushi yace shikenan an gama, nan take sarki ya kira wani hadiminsa ya turashi yaje ya taho da jaruma siyama da mahaifiyarta suka shigo cikin tawagar sarki hulbasu koda hailu ya yunkura zai mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune sai santsi ya kwashe shi ya zame zai fadi kasa a lokacinne rawanin da hailur ya rufe fuskarsa dashi ya zame kafin ya mayar da rawanin kan fuskarsa shadila ta yi arba dashi domin ya hada idanu da ita cikin kaduwa yai sauri ya mayar da rawanin ita kuwa shadila sai ta kame a inda take tsaye saboda tsananin mamaki da kaduwa da murna bata san sa adda hawaye ya fara zubo mata ba.... Nima dai saboda tsananin farin ciki da murna bansan lokacin da na ajiye typing dinnan ba nake cewa A huta lafiya kafinann Nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square daga Zauran Labarai nake magana SATSUBA Littafi Na Biyar (5) Part B. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Duk da cewa itama ta rufe idanunta da bakin kyalle sai da sarki hulbasu ya lura da halin da take ciki amma sai ya basar yayi kamar bai fahimci komai ba ita kuwa luzuraina sam bata lura da duk abinda ke faruwa ba yarima hulkas ne ya lura da irin satar kallon da mahaifiyarsa ke yiwa abul siyama kuma yaga sa adda hawaye ya zubo mata, nan take hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa dalilin faruwar wannan lamari don haka sai zuciyarsa ta kama zargi da wasu wasi amma ya kasa gane abin ma da yake zargi da wasi wasin a kansa haka dai sarki da mukarrabansa suka mimmike tsaye a cikin filin gasar aka kawo musu dawakansu suka hau sannan suka fice daga cikin filin gasar dakaru na zagaye dasu gaba da baya da kuma tsakiyarsu Ashe Tun sa adda aka gama fafatawa tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama tuni sadauki darkus ya kebe da wadansu zakwakuran yaransa ya basu umarni akan cewa da zarar sun ga jaruma siyama da iyayanta sun fito daga cikin filin gasar a kashe su a sirrance ba tare da kowa ya gane abinda ya kashe sun ba baya ga wannan mugun abu da sadauki darkus ya shirya ashe shima sarkin yakin sarki hulbasu ma ya tura wadansu yaran nasa ma a sirrance sun je can hanyar bayan gari sun labe rike da da kwari da baka sun dana kawai jira suke suga giftawar jaruma siyama da iyayenta akan hanyarsu ta komawa gida su sakar musu harbi su kashesu lokacin da shi sarkin yaki wanda ake

Chapter 9 of 21