Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kira suna RINZALU da kuma sadauki darkus suka ga cewa siyama tare da iyayanta sun shiga cika da mamaki kuma hankalinsu ya tashi saboda sun san cewa lallai dukkan shirinsu ya watse, nan take sarkin yaki rinzalu ya nufi tawagar ta sarki da nufin ya shiga cikinsu amma sai yaga dakarun sarki na musamman masu tsaron lafiyarsa sun shiga gabansa sun hanashi shiga cikin tawagar, Al amarin da yai matukai baiwa sarkin yaki rinzalu mamaki kenan kuma ransa ya baci saboda ba a taba hanashi shiga cikin tawagar sarki ba sai yau nan take ya fara tunani a cikin zuciyarsa yace wai shin wane irin matsayi ne da jaruma siyama da iyayanta a wajan sarki hulbasu haka har da yake kare rayuwarsu wai shin ma yaushe ya san su har da suka sami matsayi a wajansa kamar haka amsoshin da rinzalu ya kasa baiwa kansa kenan haka dai ya hakura yana ji yana gani ya juya da baya yaje ya shiga cikin sauran yan uwansa -- Al amin Ahmed Misau Lokacin da aka iso cikin gidan sarautar sarki Hulbasu sai ya kama hannun hailur ya jashi har izuwa cikin kuryar turakarsa suka zauna aka kawo musu abinci da abinsha shi kansa hailur yayi mamakin yadda sarki hulbasu ya aminta dashi haka cikin kankanin lokaci alhalin sau daya rak suka taba ganin junansu ma wannan haduwar ta yau itace ta biyu amma ya aminta dashi kamar haka Hailur yace a cikin ransa wata kila saboda abin karamcin da nayi masa ne a daji shi yasa ya saka mini da irin wannan tarba, bayan an kawo musu wannan abinci da abin sha na alfarma sai sarki yayiwa hailur tayi amma sai hailr ya kasa cin abincin ya kura masa idanu kawai a lokacin da tuni sarki ya gabatar da wajan loma biyu yana shirinkai ta uku kenan sai ya lura da cewa hailr baya cin abincin kuma yayi shiru fuskarsa na nuna alamun tunani koda ganin haka sai sarki Hulbasu yai murmushi a gareshi yace kwantar da hankalinka ya kai abokina kayi sani cewa a halin yanzu matarka da yarka jaruma siyama suna can tare da matata da kuma gimbiya shadila matar sarki shardas cikin aminci suna cin irin wannan abinci dake gabanmu koda jin haka sai hailur ya saki ajiyar zuciya tare da jinjina kai alamar gamsuwa da furucin da sarki Hulbasu yayi masa nan ya saki jikinsa ya fara cin abincin, har suka ci suka koshi dayansu bai kara cewa uffan ba sai bayan sun nutsu sannan sarki ya dubi hailur yace yakai abokina kayi sani cewa hankali shine yake gani amma ba idanu ba tabbas akwai boyayyen al amari a tare dakai wanda kake boye mini amma ina so ka sani cewa ba a boyewa abokin kuka mutuwa yakamata ka gane cewa shi masoyi na kwarai har abada masoyi ne shi kuwa masoyi zaka sameshi mai rike amana da kare masoyinsa da sallama rayuwarsa a gareshi a koda yaushe komai RINTSI DA TSANANI, na rantse maka da girman iyayena da kakannina ba zan taba cin amanarka bakona juya maka baya musamman idan kayi la akari da irin taimakon da kayi mini a cikin daji wanda har na mutu ba zan manta dashiba, ina son ka saki jikinka da zuciyarka ka sanar dani duk abin dake faruwa shin menene tsakaninka da shadila matar sarki shardas? Na lura da duk abin da ya faru dazu a tsakanin kai da ita a filin GASAR JARUMTAKA, naga hawaye na zuba a cikin idanunta sa adda rawanin fuskarka ya kwaye tayi arba dakai, shin kun san juna ne dama ? Ka sani cewa ko ka sanar dani wannan sirri ko ka ki tuni yanzu rayuwarka da ta iyalanka tana hannuna domin inda ban shigo daku nan ba cikin gidan sarautata tuni kun dade da zama gawa, lokacin da sarki yazo nan a jawabinsa sai hailur yaja dogon numfashi ya ajiye sannan ya dubeshi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai wannan sarki mai Adalci kayi sani cewa gimbiya shadila matatace a baya kafin sarki shardas ya mallaketa, koda jin wannan batu sai idanun sarki hulbasu suka zazzaro tsoro ya kamashi kuma jikinsa ya kama kyarma shi kuwa hailur sai yaci gaba da bayani yana mai cewa a ranar angwancina da ita ne sarki shardas da dakarunsa suka kawo ma kabilarmu harin Mamayar bazato sukayi ta ragargazar dakarunmu kuma suka kame matayanmu da yawa a matsayin bayi ni ne kadai jarumin da na gagaresu har ma nayi gumurzu da sarki shardas amma a karshe ya jefani kasa daga saman wani tsauni mai tsananin tsawon tsiya sanadiyar da na rasa hannuna guda daya na hagu kenan kuma kafata guda daya itama ta sami wannan nakasa ta shagidewa, nidai kawai farkawa nayi na tsinci kaina a cikin wata bukka a tsakiyar daji koda na yunkura domin na mike zaune sai naji na kasa domin gaba daya jikina babu kuzari, yayin da na sake yunkurawa domin na yaye mayafin da aka lullube ni dashi akan shimfidar da nake kwance sai naji babu hannuna guda daya na dama, nan take na kwarara wani uban firgitaccen ihu cikin tsananin bakin ciki da razana faruwar hakan keda wuya sai ga wani dattijo tare da wata kyakkyawar budurwa sun shigo izuwa cikin bukkar da shigowarsu sai suka durkusa a gabana dattijon ya dubeni a dimauce yace yaro me ya faru gareka ka tsandara wannan uban ihu haka shin wani mugun mafarki kayi ko kuwa wani mugun abune ka gani sa adda naji wannan tambaya sai hawaye ya zube mini na dubi dattijon cikin nutsuwa nace me yasa kuka ceci rayuwata baku barni na mutu ba yanzu menene amfanin rayuwata a doron kasa tunda na rasa komai da kowa nawa kuma na rasa lafiyata ina mai rokonku daku gaggauta kasheni yanzu domin na huta da bakin cikin dake nukurkusar zuciyata yayin da na zo nana zancena sai dattijon da wannan kyakkyawar budurwa suka kamu da tsananin tausayina. Dattijon ya kalleni yace samari hakika kana da nisan kwana a duniya domin a tarihin wannan tsauni wanda ka fado daga kansa fiye da shekaru dari bakwai baya ba a taba samun mahalukin daya fado daga kansa ba ya rayu sai kai muma nan da ka ganmu muna zaune a cikin wannan daji mun fitone daga cikin wata babbar kabila da ake kira BANU IKHLAS. kamar yadda sarki shardas ya karar da kabilarka haka muma ya karar da tamu kabilar ni da wannan ya tawa ce zalina kadai muka tsira da rayuwarmu alokacin sa adda ya kawo farmaki zuwa kauyanmu nida ita bama nan muna cikin daji muna yin farauta bayan mun dawo mun iske iyayanmu da yan uwanmu da duk danginmu sun zama gawa sai muka kama kuka mutum daya kacal muka samu da sauran numfashi a jikinsa shine ya gaya mana cewa sarki shardas ne da kansa shida dakarunsa suka zo sukayi mana wannan mummunar barna da dai muka ga cewa ba zamu iya daukar fansa a kan sarki shardas ba sai muka hada kayanmu muka sake komawa cikin daji muka ci gaba da farauta, amma bamu zauna a waje daya ba sai muka ci gaba da tafiya muna ketawa ta gefen garuruwa da kauyuka amma bama zama a inda babu cibiyar ruwa Tabbas ruwan dake kasan wannan tsauni da ka fado ne ya kawoka nan domin daga can zuwa nan tafiya ce ta kwana saba in da hudu, sa dda mahaifin zalina yazo nan a zancensa sai na cika da tsananin mamaki kuma na sake kamuwa da bakin ciki mara misaltuwa don haka ban san sa adda na fashe da kuka ba ina mai cewa ina ma na mutu ban rayu ba sakamakon fadowa daga kan wannan tsauni tun da yanzu bani da kowa kuma bani da komai a wannan daji, koda jin wannan batu sai tausayina ya kama zalina da mahaifinta zalina ta dubeni tace yakai wannan jarumi ma aboci kwarjini da jarumtaka ka yi sani cewa yadda baka da komai da kowa a wannan duniya haka muma muka kasance ni da mahaifina amma tunda yanzu kaddara ta hadamu mun sameka ka samemu, zaifi kyau mu rungumi kaddara bisa yadda ta samemu mu ci gaba da rayuwa ko don nan gaba mu ga yadda karshen mulkin sarki shardas zai kasance koda kuwa mu bazamu iya ganin karshen nasa ba, ka sani cewa babu wani abu madawwami kuma komai nisan jifa kasa za fado, don haka duk abinda sarki shardas ke takama dashi watarana sai ya fado kasa tunda idan ba mutuwa akwai tsufa akwai lokacin da yanaji yana gani ba zai iya yin zaluncin da yake yi ba yanzu koda mu bamu ga wannan lokaci ba ina son ire irenmu sugani Al amin Ahmed Misau, Guyson Ko A Square nake magana lokacin da zalina tazo nan a zancenta sai jikina dana mahaifinta yayi sanyi saboda mun san cewa duk abinda ta fada gaskiya ne, tun daga wannan rana zalina da mahaifinta sukaci gaba da jinyata har na sami lafiya ya zamana cewa ina iya mikewa tsaye na dogara sanda na bisu izuwa daji don yin farauta amma fa duk sa adda na dubi hannuna na hagu naga babu shi kuma naga kafata ta dama ta shagude sai na fashe da matsanancin kuka na bakinciki domin gani nake kamar rayuwata bata da wani sauran amfani duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo cikin hayyacina.... Nima kuma a yanzu sai Anyi da gaske za a rarrasheni naci gaba hahaha wasa nake fa sai Allah ya kaimu Gobe Cigaba amma kafinan dai zanso ku san cewa nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square nake magana daga zauran labarai page sai gobe SATSUBA Littafi Na Biyar (5) Part C. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo cikin hayyacina wani abin mamaki wanda ya daure min kai shine duk da cewar na rasa hannu daya da kafa daya ko kadan ban rasa karfin damtse na ba da kuma iya yakina don haka duk sa adda muka shiga daji farauta duk muguwar dabbar da ta zo gabanmu take nake gamawa da ita, komai yawan gungun yan fashi kuwa idan mukayi gamo dasu ni kadai nake tarwatsa su, amma zalina da mahaifinta suna taimaka mini saboda sun kware ainun a iya harba kibiya A lokaci guda kowannansu na iya harba kibiyoyi bakwai sai dai kaga maza na zubewa kasa yayinda tsinin kibiyoyinsu suke ratsa kirazansu, A kwana a tashi sai na sami wata bakwai tare da su zalina ya zamana cewa na shaku dasu ainun musamman zalina wacce komai tare muke yi shimfidar barci kawai muke rabawa A hakane na fuskanci cewa soyayya ta shiga tsakaninmu amma dana tuna cewa ni fa yanzu masaki ne bani da hannu daya da kafa daya sai na ga cewa idan na nemi soyayyar zalina na cutar da ita Haka kuma idan na tuna cewa na rasa masoyiyata shadila sai naga cewa ai na gama soyayya a duniya don ba zan taba samun wacce zan sota ta soni ba kamarta bisa wannan daliline na rinka danne soyayyar zalina a cikin zuciyata kuma duk sa adda naga zata nuna mini soyayyar tata saina bagarar, hm Ni abinda yake bani mamaki ma shine me zata yi da masaki muna cikin wannan hali ne mahaifin zalina ya kamu da cuta mai tsanani wacce takai shi ga kwanciya, abu dai kamar wasa kullum sai ciwo ya rinka gaba ya zamana cewa ba a samun sauki Al amarin da ya dugunzuma hankalinmu kenan muka rasa sukuni da kwanciyar hankali ita kuwa zalina kullum bata da aikinyi sai kuka da bakin ciki da kyar nake iya rarrashinta, ba komai ne yake sata wannan yawan kuka ba sai ganin cewa babu alamar samun lafiya ga mahaifinta kuma ga dukkan alamu ciwon nasa bana tashi bane, wata rana na tashi da sassafe ina shirin tafiya daji domin naje nayi farauta naman da zamu ci da rana a lokacin zalina na can wajan kogon da muke kwana ta dora tukunya akan wuta tana dafa mana abincin kalaci sai mahaifin zalina ya kira sunana a lokacin da nake daf da fita daga cikin kogon Cikin tsananin mamaki na juyo na dubeshi saboda rabonsa da ya budi baki yayi magana tun daga ranar da ya kwanta wannan cuta, cikin matukar sanyin jiki na karasa daf dashi na tsugunna a gabansa inamai kura mas aidanuna ya shi kuma sai ya kamo hannuna ya dora akan kirjinsa ya dafe hannun nawa da dukkan hannayansa biyu sannan ya budi baki da kyar yace yakai hailur kayi sani cewa wannan ciwo nawa bana tashi bane mutuwa zanyi kuma a koyaushe wa adina zai iya cika ina neman Alfarma guda daya jal a wajanka alfarmar kuwa itace ina son ka auri zalina, koda jin wannan batu sai zuciyata ta buga da karfi na dubeshi cikin mamaki nace yakai abul zalina ai idan kace na auri zalina bakayi mata adalci ba domin kana sone ta auri nakasashshe koda jin haka sai tsohon yayi murmushin karfin hali ya dubeni cikin nutsuwa yace yakai hailur kayi sani cewa a zahiri kake nakasashshe amma a zuciyarka kafi ta lafiya sannan kuma har yanzu sadaukantakarka da jarumtakarka suna nan basu ragu ba dai dai da matsayin kwayar zarra ina son ka sani cewa yata ta kamu da tsananin sanka a cikin wannan hali da kake ciki na nakasa kaga kenan ashe soyayyarta itace soyayyar gaskiya ka auri yata zalina ko don saboda ka samu zuri ar da zasu ga bayan babban makiyinmu sarki shardas ka sani cewa kowacce mace tana son ta auri namijin da zai iya kare mutuncin ta da rayuwarta koda kuwa shine yafi kowa nakasa a doron kasa lallai ku cika mini burina na ganin bayan sarki shardas wannan itace kadai wasiyyata a gareku, ashe duk wannan bayani da mahaifinta yake yimini zalina dake can kofar kogo tana sauraro don haka sai ta kasa cigaba da aikin da takeyi ta koma gefe daya ta zauna tana ta faman kuka, koda na fito daga cikin kogon dutsen rataye da takobina da nufin na shiga daji don gabatar da farautar sai naga zalina tana ta kukanta Al amarin da yasa na gane cewa lallai duk taji abinda muka tattauna kenan dani da mahaifinta cikin sanyin jiki na karasa gareta na zauna daf da ita kanta na sunkuye sai na tallabo habarta da lafiyayyen hannun nawa kuma na share mata hawaye muka kurawa junanmu idanu sannan na dubeta nace shin kin amince na zama abokin rayuwarki koda jin wannan tambaya sai zalina ta murtuke fuska daga can kuma sai ta rungumeni ta kama kyalkyala dariyar farinciki muna rungume da juna mukaji motsi a bayanmu a firgice muka juya da sauri sai mukaga she mahaifin zalina ne ya fito daga cikin kogon dutsen yana dogara sanda da kyar yana numfashi sama sama A guje na janye jikina daga cikin na zalina na karasa gareshi na rukoshi na zo dashi wajan zalina itama ta kamashi muka zauna gaba daya sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace haba ya kai Abbana yaya kai da kake cikin wannan hali zaka taso kayi tafiya sa adda abul zalina yaji wannan tambaya daga bakin yarsa zalina sai ya dubeta yayi murmushin karfin hali yace yake yata ai dole ne na taso ko don naga abin farinciki na karshe wanda idanuna zasu gani wanda shine amincewar junanku akan aure lallai ina so naga wannan aure naku da idanuna kafin rai yayi halinsa, nan take tsohon ya yiwa hailur bayanin yadda zasu daura auren bisa al adar su kabilar wato kowannansu ya yanki dan yatsansa ya diga jininsa a cikin ruwa bayan jinin biyu ya gauraye sai kowannan su ya sha ruwan nan take kuwa muka aiwatar da hakan, muka rinka shan ruwan muna kallon juna cikin murmushi har sai da ruwan ya kare kaf A dai dai wannan lokacine farinciki ya lullube abul zalina ya dubi hailur yace yakai babban gwaro kayi sani cewa yanzu ka zama na zalina kuma zalina itama ta zama taka babu abinda zai rabaka face kaddara ko mutuwa, wannan dama shine manufar shan jinin juna da kukayi, bisa al adar kabilarmu a ranar da miji ya mallaki matarsa babu abinda zasu fara face zuwa daji farauta tare, don haka yanzu saiku tafi sannan da ku ka samo shi zaku kawo a gasa muci muyi walima da farin cikin aurenku, koda jin wannan batu sai na dubi abul zalina cikin alamun damuwa nace haba yakai abul zalina yaya za ayi mu tafi daji mu barka kai kadai a nan alhalin kana cikin wannan halina rashin lafiya, koda jin haka sai abul zalina ya dubeni cikin murmushi yace kada ka damu dani lallai zakuje ku dawo kuma ku sameni cikin koshin lafiya da sauki fiye da ko yaushe wannan shine abinda na gani a mafarkina na daren jiya bisa wannan dalili ne ma a yau din nan na sami saukin da har na iya mikewa tsaye na taka kafafuna na fito daga cikin wannan kogo haka dai abul zalina yaci gaba da rarrashinmu har ya samu ya shawo kanmu muka amince da barinsa a wajen amma kafin mu tafi sai da ya rungumemu yana ta dariyar farinciki bayan ya janye jikinsa daga cikin namune mun juya zamu tafi izuwa cikin daji sai zalina ta waigo ta dubeshi take ta hango kwalla a cikin idanunsa al amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan ta dubeni tace yakai mijina nifa zuciyata bugawa take da karfi ji nake kamar idan muka dawo ba zamu riskeshi a raye ba ni kaina naga alamun hakan a tare da mahaifin nata kuma duk kalaman da yake yi na bankwana ne amma don kada hankalin zalina ya tashi sai naki sanar da ita haka dai muka nausa cikin daji muna waigen Abul siyama shi kuma ya bimu da kallo yana yi mana murmushi har muka kule muka daina hangoshi A sannan ne kuma muka falfala da azababbn gudu izuwa cikin daji mukayi ta tsala gudu ba sassauci muna neman dabbar dajin da zamu samu babu abinda zai baka mamaki face yadda nake iya gudu ina dogara sanda alhalin kafata guda daya bata da kyau kuma har tserewa zalina nake yi a gudun ni ina rike da takobi ne kuma karshen sandar da nake dogarawa mashi neita kuwa zalina a hannunta kwari ne kuma ta rataya kwanson kibiyoyin kwarin a bayanta don haka ita bata rike wani makami sai kwari da baka koda muka nausa cikin daji sai muka rabu ni kuma nayi gaba ita kuma tayi yamma sannan kuma muka baiwa junanmu tsawon rabin sa a akan mu hadu a bakin wani dutse dake can tsakiyar dajin kowannanmu na rataye da kaho a bayansa wanda duk sa adda ya shiga wani hadari wanda ba zai iya kubutar da kansa ba sai ya busashi komai nisan inda yake dan uwansa zai iya jiyowa har yakai mas dauki shidai wannan kaho na sihirine kuma gadon gado ne a kabilar tasu zalina kuma mutum ba zai iya mallakarshi ba face ya kasance dan kabilarsu ko kuma ya auri jinin Kabilar bayan mun rabu a cikin daji nida matata zalina sai muka wanzu muna masu neman abin farauta baji ba gani, lokacin da naga na shafe dan dogon lokaci ina neman abin farautar ban samu ba sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda ina ganin cewa ai abin kunyane ace a ranar daurin aurena na kasa farauto abincin da zamu ci nida amaryata Ehm Al amin Ahmed Misau, Guyson ko A square Ina cikin wannan haline naga wata barewa ta nufo inda nake cikin azababben gudu gashi dai barewar ta hangoni a gabanta rike da makami amma ko shakkar tunkaro ni batayi ba dada durfafo ni takeyi al amarin da yasa na fahimci cewar lallai masifar da ta korota ta nufoni don tsira da rayuwarta ta wuce tawa hadari, ai kuwa ban ankara ba sai naga ashe wani murjejen zaki ne ya tasota a gaba tun daga nesa dana hango zakin ya falfalo da azababben gudu har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa kuma harshensa na zazzagowa waje daga cikin bakins ana gane cewa lallai wannan zaki a cikin muguwar yunwa yake koda naga cewa barewar nan so take ta wuce ta gabana domin ta tsira da rayuwarta sai na yunkura cikin zafin nama na daka tsalle sama a lokacin da itama barewar ta daka tsalle da nufin ta shallakeni muna haduwa a saman na soketa da mashina ta zama gawa na duro kasa bisa kafafuna barewar na sakale a jikin mashin nawa, ai kuwa sai wannan zaki yayi tirjiya a lokacin da tazarar dake tsakaninmu bata wuce taku goma ba nan fa muka fara kallon kallo tsakaninmu da murjejen zakin nazarin da zakin yake yi shine ni zai farwa sannan ya dauke barewar ko kuwa barewar zai karba ni kuwa nazarin da nakeyi shine ta yaya zan iya .Ya kasance shi ba karamin tashin hankali bane duk da na san cewa na sha yin gumurzu da manyan dabbobin daji ina samun nasara a kansu sai da zuciyata ta karaya akan wannan zaki domin ban taba yin gamo da tsohon zakimai girma da kwarjinin wannan ba nikam tuni na gama aiyanawa a raina cewa duk rintsi ba zan iya sallama barewar ba ga wannan zaki koda hakan na nufin zan rasa rayuwata kawai sai na cake mashin nawa a cikin kasa wanda ke dauke da barewar sannan na buda hannuna mai rike da takobi ina mai gyara tsayuwata kuma na koma gefe daya na tsaya ina mai baw azakin zabi tsakanin barewar da ni kaina ya zabi wanda zai fara afkawa take zakin yayi wani irin gurnani mai ban tsoro wanda yasa hantar cikinsa ta kada amma da na tuna cewa amaryata zalina na can fa tana farauta a cikin wannan daji wata kilama yanzu ita ta dade da samo nata abin farautar taje inda mukayi zamu hadu ta zauna tana jirana sai naji zuciyata ta kekeashe ga barin dukkan tsoro..... . . Tofa ba zan gane hakan ba sainaga ai an fara wannan gumurzu kufa ya kukace abokai nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe SATSUBA Littafi Na Biyar (5) Part D. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Kamar hadin baki sai nida zakin muka falfalo da gudun tsiya izuwa kan juna muka dako tsalle sama a tare kafin nayi wani yunkuri na saran zakin ko sukarsa da takobina tuni shi ya sa kirjinsa ya bangajeni ai kuwa sainaji kamar aksusuwan kirjina sun kakkarye nayi can baya da karfi bayana ya gwaru da jikin wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice ina aman jini ta hanci da baki, koda zakin yaga halin da na shiga sa adda shima ya duro kasa sai ya wangame baki ya kwalla wani uban ruri anda ya fi wanda yayi a baya mai nuna kuranta kansa da dai yaga na kasa tashi ina ta numfashi sai ya wuce ta gabana ya daka tsalle da nufin ya suro wannan barewa dake sakale a jikin mashina ni kaina ban san yadda akayi ba na sami gagarumin karfi da kuzari kawai gani nayi na mike tsaye zumbur na daka tsalle daga inda nake na rungumo zakin kafin bakinsa ya cafi barewar mun fado kasa tim ! Nan fa muka kama kokawa a kasa muna ta birgima idan zakin ya danneni yana kokarin kafa min hakoransa sai na juye dashi nima ina kokarin turmushe shi da karfin tsiya domin na hallakashi sai da muka shafe kusan sa a daya muna ta bakin artabu ya zamana cewa zakin ya karkarce jikina da kaifin faratan hannayansa yai mini raunika masu yawa jini na zuba a jikina amma kuma ya kasa kafa min hakoransa a jikina lokacin da jiri ya fara dibana na tabbatar da cewar ina daf da halaka sai zuciyata ta kufulo cikin tsananin zafin nama na suri zakin na dokashi akan wani katon dutse nan take kan zakin ya dagwargwaje ya zama gawa A sannan ne na yanke jiki na fadi kasa cikin mugun yanayi da kyar na iya bude jakar guzurina na fiddo magani na shafa akan raunikan jikin nawa da hannu daya wadansu raunikan ma dake gadon baya na in da hannuna ba zai kai ba ban sami damar sa musu maganin ba a sannan ne na dauko battar ruwana na bude nash Sai da na dan huta naji karfin jikina sannan na mike tsaye na dauki gawar zakin na saba a kafadata amatsayin abincinmu na rana itama barewara sai na barta a jikin mashin nawa naci gaba da tafiya na nufi inda zamu hadu da matata zalina hakika SADAUKANTAKA tana da rana tabbas in ba don na kasance sadauki ba da babu yadda za ayi na iya daukar wannan katon zaki har na sabashi a kafadata da hannu daya kuma naci gaba da tafiya alhalin ina rike da barewa bisa mashina, haka dai naci gaba da tafiya har na iso inda zan hadu da zalina matata tun daga nesa kuwa na hango zalina zaune akan wannan dutse tana hange hange da waige waige ko zata gano ni, har ma ta zaku tana mikewa tsaye akan dutsen ai kuwa tana hangoni dauke da zakin da kuma barewa sai ta cika da tsananin mamaki, cikin tsananin murna ta duro kasa daga kan wannan dutse ta farfalo da gudu izuwa gareni ta rungumeni koda taji raunika a jikina sai ta janye jikinta daga cikin nawa da sauri ta dubi sauran raunikan na jikina, take hawaye ya kwararo daga cikin idanuwanta ta dubeni cikin alamun tausayi tace yakai mijina me yasa ka sai da rayuwarka don kawai ka cika wannan ka ida ta al adarmu Sa adda naji wannan tambaya sai na bushe da dariya nace yake matata kiyi sani cewa ko a tamu al adar namiji baya samun matar aure a cikin sauki har sai ya sha bakar gwagwarmaya ta hanyar gasa a neman auren, kuma gasa ce mai hadarin gaske wacce mutum ma zai iya rasa rayuwarsa gaba daya, nan dai muka juya da baya muka nufi hanyar gida, muna cikin tafiya ne na dubi zalina na bushe da dariya, Al amarin da yai matukar bata mamakikenan ta dubeni tace yakai mijina kai kuwa menene dalilin yin wannan dariya taka, kawai sai nayi ajiyar numfashi nace gani nayi nidake mun shafe sama da sa a biyu a cikin nan muna farauta amma ke ko fiffiken dan tsako baki samo ba, dajin wannan batu sai itama ta kyalkyale da dariya tace ni kaina na yi matukar mamakin yadda ko tsuntsu guda ban iya harbowa ba daga sama alhalin ga su nan birjik suna ta kaiwa da komowa a sararin samaniya sai dana yi asarar kibiyoyina sama da guda talatin, kai bama tsuntsaye ba hatta kananan dabbobin daji sai dana kasa tsere da wajan guda bakwai amma da zarar sun shiga cikin duhuwa saina nemesu sama

Chapter 10 of 21