Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne wato kai bama ka damu da lafiyarka ba kawai so kake na kaika kaje kayi kallon gumurzun wasa to ka sani cewa kai rago ne ba jarumi ba kuma baka iya komai ba a yaki Ba zaka iya tsinana abin arziki ba a cikin gagarumar tafiyar dake gabanmu dole sai na baka horo mazaka dauko dan jagoranmu ka rikeshi a hannunka yanzu nan zamu tafi birnin sarki hulbasu kafin a fara wannan gasa ga jagoran namu can a bayanka, koda gama fadin haka sai rulaiya ta bude wata akwatu dake kusa da ita ta debo kayan yaki ta shiga yin damara, shi kuwa yarima hulkas sai ya waiga bayansa da sauri nan take yayi arba da Wannan tsuntsun sihiri wanda aljani Arwasul masdul ya bashi kawai sai ya bude tafin hannunsa shi kuwa tsuntsun sai ya taso a sama yana mai kada fuka fukansa ya dira akan hannunsa yana mai kura masa idanu cikin murna, cikin kankanin lokaci rulaiya ta gama yin gagarumin shigar yaki ta rataya tagwayen masu a gadon bayanta bayan ta sanya wani bakin sulke da bakaken takalmi dogaye iya kwaurinta sannan ta lullube kanta da fuskarta da bakin mayafi ya zamana cewa idanunta kadai ake gani a fili, koda gama wannan kimtsawa sai ta suri yarima hulkas daga kan gadon da yake kwance tamkar ta dauki buhun auduga ta goyashi a bayanta suka fice daga cikin gidan gaba daya, shi kuwa yarima hulkas sai ya damke tsuntsun sihirin a cikin tafin hannunsa guda yana mai matukar farin ciki bisa ganin cewa zasu tafi izuwa birnin sarki hulbasu wajan iyayensa da yar uwarsa, da fitowarsu kofar gidan sai yarima hulkas ya ga wani farin ingarman doki a tsaye shi kadai yana harbin iska tamkar aikoshi akayi garesu ba tare da jiran komai ba kuma ba tare da rulaiya ta dorawa dokin sirdi ba sai ta kama dokin ta haye bayansa tana goye da yarima hulkas din sannan tace dashi maza ka saki wannan tsuntsu dake hannunka shine zai nuna mana hanyar da zamu isa can inda kake so muje, koda jin haka sai yarima hulkas yai sauri ya bude tafin hannunsa nan take wannan farin tsuntsu ya tashi sama ya bi gabas ai kuwa sai rulaiya ta zaburi dokin da gudu suka bi inda tsuntsun ya nufa nan fa yarima yaga dokin nasu yana yin wani irin matsanancin gudu na ban al ajabi tamkar tashi sama yayi domin karfin gudunsa yafi gaban kwatance Al amin Ahmed Misau, abin da yarima hulkas ya ayyana a ransa kawai shine wannan ba doki ba ne irin sauran dawakai kuma tabbas yayi imani shi wannan sihirtaccen dokine domin gani yake kamar dokin zai iya zagaye duniya gaba dayanta a cikin rabin sa a wannan shine abinda ya faru ga yarima hulkas bayan barci ya daukeshi a turakar yarima barmas kuma ya farka ya tsinci kansa a wani wuri daban mai ban Al'ajabi.. '' '' '' AL AMARIN sarki shardas da bokansa labarusa kuwa sai da suka kara shafe kwanaki tara cif a cikin daji suna farautar Aljani Arwasul masadul amma duk tsawon wadannan kwanaki basu sake haduwa da shi ba kuma ko duriyarsa basu gani ba Al amarin da yai matukar fusata sarki shardas kenan ainun bai san sa adda ya cakumi kwalar boka labarusa ba ya daka masa tsawa yace kai labarusa ! Nifa na gaji da wannan farauta ta jaki mai kaho ya zama dole a gareka ka gaggauta yin bincike a cikin hallarar tsafinka ka gano mana wata hanyar daban da zamu bi mu iya zuwa inda hular lamsara take cikin gaggawa Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya fisge kwalar rigarsa daga hannun sarki shardas ya dubeshi yace ka kwantar da hankalinka ya shugabana idan ba don ance tsafi kogi bane da sai ince dakai bamu da wata mafita ko hanya da za a samu wadda zata kaimu ga mallakar hular lamsara cikin sauki da gaggawa to amma ba a koda yaushe kuma a kowanne irin yanayi a ko'ina komai na iya sauyawa lokacin da ba a zata ba, ba zan ki ta taka ba bari na duba mana na gani ko akwai wata mafitar bayan wannan gama fadin hakan keda wuya sai boka labarusa ya zauna a kas dirshan cikin rairayi sannan ya fiddo madubinsa na tsafi ya shiga karanta wadansu dalasimai na tsafi irin wadanda sarki shardas bai ma taba jin su ba, sai da boka labarusa ya dauki lokaci mai tsawo yana shafa madubin tsafin nasa idanunsa a rufe sannan ya tsaya cak, boka labarusa yace ya dodon sarakai ka yi sani cewa a cikin binciken nawa na gano mana wata hanya mafi sauki wacce zata kaimu ga isa kogon da aka ajiye hular lamsara cikin sauki da gaggawa amma sai dai akwai wata matsala babba data bullo a cikin wannan lamari ka sani cewa yanzu a halin da ake ciki Aljanin da muke farauta ruwa a jallo aljani Arwasul masadul sun hadu da yarima hulkas harma ya bashi tsuntsun tsafi wanda zaiyi masa jagora izuwa inda hular lamsara take sannan kuma sai abu na biyu yarima hulkas ya hadu da wata babbar sabuwar abokiyar gabar taka mai suna Rulaiya wadda take da burin daukar fansa akanka kuma a yanzu haka ta goya yarima hulkas akan wani dokin sihirin tsafi da Aljani arwasul masadul ya hadasu dashi sun tafi izuwa birnin sarki hulbasu inda matarka shadila take bisa jagorancin wannan tsuntsun sihiri da Arwasul masadul ya bashi Al amin Ahmed Misau, na gano cewa akwai wani mugun shiri da ake yi maka a can birnin sarki hulbasu don haka lallai ina tabbatar maka da cewa sarki hulbasu yaci amanarka kuma yana son ya rabaka da matarka shadila a yaune za ayi gasar karshe ta jarumtaka a birnin nasa kuma a yau dinne ya shirya kashe gaba dayan dakarunka dake tsaron lafiyar gimbiya shadila, idan bamu je birnin ba akan lokaci zamu iske tuni ya gama dasu kuma yabi su yarima hulkas izuwa dauko hular lamsara koda boka labarusa yazo dai dai nan a jawabinsa sai kan sarki shardas ya daure ya cika da tsananin mamaki da fargaba da kuma takaici, ya dubi boka labarusa cikin damuwa yace akan wanne dalili sarki hulbasu zaici amanata alhalin yana tsananin sona? Shin wacece wannan sabuwar abokiyar gaba tawa wacce naji ka ambashi sunanta rulaiya wacce suke tare da yarima hulkas? Koda jin wadannan tambayoyi sai boka labarusa yace wannan sabuwar abokiyar gaba taka ba wata bace face Yar attajiri Amsar wanda ka kashe shi a cikin gidan darul daulat bayan yaci gasar da kukai ta siyen gida a karshe ka gaje dukiyarsa babban burin wannan yarinya rulaiya a duniya shine ta dauki fansar ran mahaifinta akanka kuma ta mallaki gidan darul daulat tunda mallakin mahaifinta ne Attajiri Amsar, haka shima a yanzu yarima hulkas bashi da wani buri wanda ya wuce ya hallaka ka don daukar fansar abinda ka yiwa ubansa hailur da dukkan zuriarsu ina mai sanar dakai cewa a halin yanzu tuni hailur da matarka gimbiya shadila sun mayar da auransu a cikin birnin sarki hulbasu Al amin Ahmed Misau har sun tare a cikin wani kasaitaccen gida da sarki hulbasu ya basu koda boka labarusa yazo dai dai nan a zancensa sai sarki shardas ya takarkare ya kwarara uban ihu irin wanda ke tarwatsa mazaje a filin fama komai jarumtakarsu da rashin tsoronsu Kai inda ace akwai mace mai ciki a wajen da tuni ta kama nakudar dole saboda firgita da za tayi na jin wannan ihu na sarki shardas kananun jarumai da dakarun yaki kuwa firgicewa zasuyi su dimauta su kama sakin fitsari a wando hehe Al amin Ahmed Misau, shi kansa boka labarusa wannan ihu na sarki shardas ya razanashi yasa zuciyarsa ta buga tsuntsaye da dabbobin dake cikin dajin kuwa gaba dayansu sai da suka kama guje guje da iface iface suna sauya sheka da shigewa cikin ramuka cikin matsanancin fishi sarki shardas ya dubi boka labarusa yace maza ka hanzarta kaini birnin sarki hulbasu kafin su yarima hulkas su isa can, cikin rawar jiki boka labarusa yayi tsafi wani katon Aljani ya bayyana tsulum a gabansa suka haye bayansa ya tashi dasu sama ya luluka izuwa cikin gajimare yana mai tsala azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya, Abinda sarki shardas bai sani ba shine shi kansa boka labarusan bashi da tabbacin zasu iya isa can birnin Na sarki hulbasu akan lokaci kafin komai ya gudana +i ++ ++ ACAN birnin sarki hulbasu kuwa gari na wayewa aka tashi da tsananin tashin hankali a gidan sarautar saboda an nemi yarima hulkas sama da kasa an rasa babu inda ba a duba ba acikin birnin ba har da cikin dazuzzuka amma kamar maye yaci shirwa ga shi kuma a can filin gasa jama a sun taru makil ana ta shewa da ihu ana jiran isowar sarki hulbasu da su jaruma siyama babu wanda yafi kowa tashin hankali sama da shadila domin tunda akace yarima hulkas ya bata take ta faman rusa kuka saboda gani take kamar ya fada hannun sarki shardas ne Da kyar hailu ya shawo kanta ya rarrasheta don kada ta tarwatsa musu dukkan shirinsu na ranar inda ya tabbatar mata da cewa yayi bincike a hallarar tsafinsa ya gano cewa yarima hulkas na nan a raye kuma zai dawo kafin a gama wannan gasa nan dai ya lallabata suka shiga cikin ayarin sarki hulbasu aka tafi filin gasa koda jama a suka jiyo bushin Algaita da bugun tambura alamar cewa sarki ya iso filin gasar sai filin ya sake rudewa da shewa gami da tafi nan fa aka bude kofar filin gasar sarki da mukarrabansa suka shigo bisa dawakai dakaru na take musu baya, amma abin da ya daurewa kowa kai shine sarki hulbasu yayi gagarumar shigar yaki tamkar yana cikin jaruman gasar haka ma dakarunsa na musamman masu tsaron lafiyarsa kuma a cikinsu har da wadansu bakin dakaru wadanda suka rufe fuskokinsu ba wasu bane wadannan bakin dakarun da ke bayan sarki hulbasu ba face su jarumi hailur Lokacin da dakarun sarki shardas masu tsaron lafiyar gimbiya shadila sukaga sarki hulbasu ya fito da wannan shiri sai suka sha jinin jikinsu suka fara zargin cewa lallai akwai wani abu dake shirin yi musu don haka sai suka fara yin kus kus a tsakaninsu Al amin Ahmed Misau, Abinda basu sani ba shine wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi kuma maso abinka yafika dabara, jaruma siyama na daga cikin tsakiyar dakarun sarki tayi gagarumar shigar yaki tare da mahaifiyarta bisa doki guda, koda yan kallo suka ga siyama sai suka rude da ihu aka kama yi mata jinjina, ita dai kawai jaruma siyama tana yin murmushin karfin haline amma hankalinta a wannan rana a tashe yake saboda rashin ganin dan uwanta yarima hulkas Bayan sarki hulbasu da tawagarsa sun gama shigowa filin gasar kuma sun zauna a inda aka tanadar musu sai mai gabatarwa ya fara da kirawo sunan sadauki darkus nan fa magoya bayan darkus suka rude da shewa gami da tafi suka shiga yi masa kirari gami da jinjina koda aka bude wata kofa sadauki darkus ya fito yana tafiya kamar wani toron giwa a cikin gagarumar shigar yaki sai filin gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta saboda kwarjininsu da karar sautin takun sawayensa har sai da sadauki darkus ya iso tsakiyar filin gasar ya tsaya mai gabatarwa ya kirawo sunan jaruma siyama sannan filin gasar ya sake kaurewa da shewa gami da yafi, cikin nutsuwa jaruma siyama ta fito daga cikin tawagar sarki hulbasu ta shiga filin gasar, har sai da ta isa Daf da sadauki darkus sannan ta ja ta tsaya a lokacin da tazarar dake tsakaninta da sadauki darkus bata wuce taku uku ba, ba tare da bata wani lokaci ba alkalan gasar suka bada umarnin a fara gasa nan take, aka buga tambarin fara gumurzu kamar hadin baki sai duk su biyun a lokaci guda kowannansu ya juya da baya yayi taku bakwai sannan suka tsaya suka juyo suna masu zare takubbansu, kawai sai suka ruga da masifaffen gudun tsiya tamkar zasu tashi sama suna masu kwallah ihu mai firgitarwa suna jijjiga makamansu a sararin samaniya kafin su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakaiwa dan uwansa mummunan sara.. Kai nima Al amin Ahmed Misau ganin wannan saran ne yasa na tsaya a nan nake cewa sai Allah ya kaimu gobe kafinnan nidinne dai Al amin Ahmed Misau inkiya Guyson Ko A square daga Kaduna State. TSATSUBA Littafi Na Tara (9) Part C. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Kafin su hadu sai kowannan su ya daka tsalle sama ya kaiwa dan uwansa mummunan sara , duka su biyun a tare suka duro kasa lokacin suna masu juyawa junansu baya, bisa mamaki sai aka ga kowannansu ya tsaya cak a inda yake ba tare da ya juyo ya cigaba da yaki ba, Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan A filin Gasar harni kaina Al amin da nake typing aka sake yin tsit a karo na biyu daga can kuma sai aka ga jaruma siyama da sadauki darkus sun waigo sun fuskanci juna shi yana mai dafe saman kirjinsa jini na zuba ita kuma tana mai dafa hakarkarinta Na hagu jini na zuba A sannan ne yan kallo suka gane cewa ashe kowannansu ya samu nasarar yiwa dan uwansa mugun rauni Cikin matukar juriya da jarumtaka sadauki darkus ya yagi rigarsa ya daure kirjin nasa tamau don tsaida jini itama jaruma siyama sai tayi sauri ta cire mayafin dake zagaye a wuyanta ta daure hakarkarin nata ba tare da jiran komai ba sai suka rugo izuwa kan juna suka kacame da masifaffen yaki mai matukar ban tsoro da ban al ajabi a wannan lokaci mahaifiyar siyama na zaune daf da hailur kuma tuni ta fara kuka bisa ganin yadda aka yiwa yarta rauni tun a farkon fara wannan gasa shikuwa hailur sai ya dubeta yace kwantar da hankalinki yake matata ni na san ko wacece yata ina mai tabbatar miki da cewa ba zata mutu ba kuma ita ce zata lashe wannan gasa sai da aka shafe sa auku cur ana wannan mummunan BAKIN ARTABU tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama ya zamana cewa sun galabaitar da juna domin kowannan ya sami rauni kimanin guda biyu a jikinsa jiri ne ke dibarsu tamkar zasu sake yin RAGAS saboda karfi yazo daya ana cikin haka ne sadauki darkus ya shammaci jaruma siyama ya dankara mata wani karkarfan naushi a ciki saboda karfin naushin sai da jaruma siyama tayi sama da baya bayanta yaje ya gwaru da katangar filin gasar ta fado kasa da rub da ciki a matukar galabaice tana aman jini koda sadauki darkus yaga ya sami wannan nasara sai ya bushe da dariyar mugunta ya daga takobinsa sama ya ruga izuwa inda take ya daka tsalle sama da nufin ya duro kanta ya soke gadon bayanta tuni a wannan lokaci kowa ya gama sallamawa cewa jaruma siyama ta mutu ba zato ba tsammani sai aka ga jaruma siyama ta mirgina can gefe guda takobin sadauki darkus ta lume a cikin kasa kafin sadauki darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki kasa da tafin hannayanta biyu kawai sai gani akayi tayi sama kuma tayi katantanwa sannan ta doki kirjin sadauki darkus da kafafunta biyu, saboda karfin dukan sai da shima sadauki darkus yayi sama yaje ya gwara bayansa a jikin katangar filin gasar ya fado kasa a kan fuskarsa fuskar tasa ta dauje jini ya rufe masa idanu kafin a goge jinin dake kan idanun nasa tuni siyama ta daka sufa a sama izuwa inda takobinsa take ta zarota daga cikin kasa ta luma masa ita a ciki take takobin ta faso gadon bayansa sadauki darkus yayi mutuwar tsaye ya sandare kawai sai jaruma siyama tasa kafarta ta sake dukan kirjinsa sannan gawar tasa ta fadi kasa rikica kamar giwa ta fadi nan fa filin gasar ya rude da shewa gami da tafi ana yiwa jaruma siyama kirari bisa wannan gasa bayan ta kashe sadauki darkus a wannan lokaci ne kuma kwatsam sai aka ga jaruma siyama ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya A guje likitan sarki hulbasu da masu taimaka masa suka ruga zuwa filin gasar kan jaruma siyama don bata taimakon gaggawa a dai dai wannan lokaci ne hailur yazo daf da kunnen sarki hulbasu yayi masa rada yace ya shugabana gada daya fa dakarun sarki shardas da suka rako shadila duk sun sulale sun gudu ga dukkan alamu sun gano shirinmu da jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi murmushi yace ai nima tun dazu na lura da hakan amma ko kadan ban damu ba saboda na san cewa duk shirin da zasu yi a yanzu ba zai kai namu ba maza kaje ka karasa shirin komai ni da dakaru zamu fara yin gaba saika taho da sauran iyalansu gama fadin hakan keda wuya sai aka ga wani karamin tsuntsu ya shigo filin gasar a sama bai dira a ko ina ba sai akan jaruma siyama wacce ke kwance magashiyan likita na yi mata magani tsuntsun na dira akanta sai aka ga ta bude idanunta ta rmike tsaye zumbur tamkar babu abinda ya sameta ta kurawa bakin kofar fita daga filin gasar idanu A dai dai wannan lokaci ne aka jiyo sukuwar doki ya nufo cikin filin gasar tashin kurane ya hana ganin dokin amma kurar na lafawa sai aka ga ashe wani farin ingarman doki ne dauke da mutum biyu na gaban dokin yarima hulkas ne na bayansa kuwa wani jarumi ne a cikin shigar bakake tufafi goye da tagwayen masu koda jaruma siyama ta hango dan uwanta yarima hulkas bisa doki ya tunkarota sai fuskarta ta fadada da murmushi ta ruga gareshi da gudu Nan take shima yarima hulkas ya duro daga kan dokin ya karasa gareta a guje suka rungume juna cikin tsananin farin ciki yana ma tayata murnar lashe wannan gasa a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas yaji an dafa kafadarsa ta baya yana waigawa yaga ashe sarki hulbasu ne shima ya rungumeshi cikin farin ciki sarki hulbasu yayi masa rada a kunne yace bamu da isashshen lokacin Lokacin yin wani bayani ga juna yanzu domin yin hakan zai sa mu bata lokaci yanzu mun gama shirin komai dama kai kadai muke jira maza ka dauko yar uwarka akan wannan doki naku duk da cewa ku uku ne ku sameni a bayan gari mahaifinka ma zai riskemu a can nan take aka kawowa sarki hulbasu dokinsa ya hau dakarunsa suka take masa baya a lokacin da ya zaburi dokin nasa da gudu ya fice daga filin gasar Al amarin da ya daurewa yan kallo kai ke nan suka cika da tsananin mamakin dalilin da ya hana a tsaya a bayar da kyauta ga jarumar da ta lashe wannan jarumtakar da akayi wato jaruma siyama nan dai filin gasar ya waste mutane suka tafi suna hasashe da zargin cewa lallai babu lafiya yau Al amin Ahmed Misau, Al amarin dakarun sarki shardas kuwa ashe gaba dayan suka sulale daga cikin filin gasar suka ruga izuwa cikin daji inda suka sake haduwa suka tattauna akan yadda za su sace gimbiya shadila cikin ruwan sanyi domin su mayar da ita gida kada fishin sarki shardas ya hau kansu nan take shugabansu sadauki Murzanu ya dubesu yace na yarda da jarumtakarku da nacinku gami da iya yakinku saboda haka yanzu zamu koma izuwa cikin wannan birni na askandariyya daya bayan daya kamar yadda muka hadu a nan yanzu kuma sai dare ya raba sannan zamu shiga har cikin gidan sarautar sarki hulbasu mu aiwatar da nufinmu A halin yanzu sarki hulbasu ya gaya mini cewa yanzu zai mana rakiya tare da gimbiya shadila da dakarunsa domin mu isa gida lafiya na nuna masa cewa na amince da hakan amma na san karya yake yi so yake ya shirya mana wani tuggun ya cutar damu shi yasa nace mu rarrabu mu buya a cikin birnin nasa ba tare da ya sani ba tuni na aika da dakarun yan leken asiri domin su kai labarin abinda yake faruwa ga can birninmu saboda a sanar da sarki halin da muke ciki ta hanyar karfin sihiri a duk inda yake koda sadauki murzanu yazo nan a zancensa sai ya sallami gaba dayan dakarun nasa suka rarrabu a cikin shiga ta bad da kama suka bi hanyoyi daban daban shi dai sadauki marzanu tare da wadansu dakarun nasa mutum dari biyu sai suka bi wata barauniyar hanya ta bayan wani katon tsauni sai da suka yi yar doguwar tafiya ta kusan tsawon dakika dari bakwai da arba in sai suka yi kicibis da sadauki Ruhaisu babban yaron hailur shima dakarunsa mutum dari biyu da goma na take masa baya, cikin tsananin kaduwa da mamaki sai sadauki marzanu suka tsaya cak suka dora hannayansu akan kufen takubbansu domin basu taba zaton cewa za a tarfasu ba haka, suma su sadauki ruhaisu sai suka dora hannayansu akan kufen takubban aka fara kallan - kallo Al amin Ahmed Misau, Take sadauki marzanu ya tuno da sadauki ruhaisu sa adda suka fafata kazamin yaki a can shekarun baya sa adda sarki shardas ya kaiwa kabilar su hailur hari suka karkashe su har sarki shardas yaje fa hailur kasan wannan tsauni mai tsawon gaske kuma ya dauke matarsa shadila ya tafi da ita koda shima ruhaisu ya gene sadauki marzanu sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin kiyayyar dake taso masa cikin tsananin fishi ya dubi sadauki marzanu yace yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa jama arku da sarkinku sun dasa mana bakin cikin da har abada ba zamu taba mantawa dashi ba amma na dade ina jiran wannan rana da takobina zata dau fansar jinin kabilata akanku na rantse da darajar shugaba hailur tsakaninmu daku dole ne wasu su zama gawa anan kafin mu rabu koda jin wannan batu sai sadauki marzanu ya bushe da dariyar mugunta yace kai samari hakika tsautsayi ne ya sa kuka yi wannan babban ganganci na tunanin taremu da yaki da kuma kokarin kwacewa sarki matarsa, ina mai tabbatar maka da cewa a wannan karon sai mun karar da ku gaba dayanku ta yadda har abada ba za a kara ganin irin zuri arku ba a doron kasa, koda sadauki marzanu yazo nan a zancensa sai sadauki ruhaisu ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai wawa mara hankali da tunani shin ka manta ne cewa sarkin naku ne ya fara kwatar matar mu ?? Yanzu ne zamu dawo da abarmu garemu kuma mu dauki fansar jinin yan uwanmu da kuka salwantar ka sani cewa ku azzalumai ne masu cin zarafin talakawa sata kwace da danne hakki tsawon shekaru to ku sani cewa shi ramin karya kurarre ne kuma gaskiya dokin karfe ce wanda baya taba mutuwa koda gama fadin hakan sai sadauki ruhaisu ya zare takobinsa ya yiwa dakarunsa nuni da a afkawa abokan gaba, ai kuwa ba su tsawa jiran komai ba sai suka zare takubbansu cikin hanzari suma su sadauki marzanu suka zare nasu takubban aka ruguntsume da azababben yaki nan fa wuri ya hargitse kura ta tashi karar karafa da kururuwar mazaje ta fara cika kunnuwa -- -- -RAGOWAR dakarun murzanu kuwa su dubu daya da dari takwas sun sake rarrabuwa izuwa mutum dari hurhudu wannan shine babban kuskuren da suka tafka domin inda a cure suke gaba daya sai an kai ruwa rana kuma an kai gwauro an kai mari kafin a ci galaba a kansu ++ ++ ++ MUTUM dari hudu da suka nufi gabashin birnin askandariyya sai suka yi kicibis da tawagar sarki hulbasu nan ma sai aka kacame da Yaki amma da yake su sarki hulbasu sun ninkasu sau goma a yawa nan suka karkashesu a cikin kankanin lokaci basu bar daya ya tsira da rayuwarsa ba ++ ++ ++ DAKARUN da suka nufi yammacin birnin kuwa sai sukayi kicibis da yarima hulkas jaruma siyama da jaruma rulaiya bisa doki guda su uku, koda ganinsu sai yarima hulkas da siyama suka zare takubbansu da nufin su afka musu amma sai jaruma rulaiya ta dakatar dasu tana mai daga musu hannu har izuwa wannan lokaci rulaiya bata yarda koda jaruma siyama taga fuskarta ba domin a rufe take cikin bakin kyalle, take jaruma rulaiya ta duro kasa daga kan dokinta ta dubi dakarun nasu sadauki murzanu taga basu fi su dari hudu ba kawai sai tayi tsaki sannan ta juya ta dubi yarima hulkas tace ai abin kunya ne ace mu ukun nan ne zamu yaki wadannan kananan kwari kawai ku barni dasu rabin sa'a tayi min yawa na gama dasu koda gama jin wannan batu sai dakarun sadauki marzanu suka fusata ainun suka zare takubbansu suka afkawa jaruma rulaiya gaba dayansu Wohoho Hakika mai karfi sai Allah ya isa kuma duk wanda ya iya ya huta ana fara wannan yaki sai jaruma siyama ta cika da tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar jaruma rulaiya da kuma tsananin zafin namanta, domin duk yawan dakarun su dari hudu sai ya zama na banza saboda duk inda ta kutsa a cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa domin gididdibasu ta rinka yi sassan jikinsu ya rinka zubewa yana faduwa kasa suna ihu kuma jini na feshi da fantsama Al amin Ahmed Misau Nan fa aka rasa mutum daya daga cikin dakarun wanda ya sami nasarar koda lakutar jikin jaruma rulaiya nan take jaruma siyama ta raina dukkan jarumtakarta ta fara tunanin cewa duk yadda akayi wannan hatsabibiyar bakuwar jaruma wacce yarima hulkas yazo da ita ba mutum bace Aljana ce Koda gama ayyana hakan a cikin zuciyarta sai ta kasa hakuri ta dubi yarima hulkas tace yakai dan uwana wai shin wacece wannan bakuwar jarumar da ka zo da ita kuma a ina ka sameta har yanzu ta fa ka bani labarin inda ka tafi ba muka nemeka muka rasa koda jin wannan tambaya sai jarimi hulkas yayi murmushi yace me yasa baki da hakuri ne yake yar uwata yanzu ina nake da lokacin baki labari a cikin wannan yanayi da muke ciki ki bari sai mun gama da wadannan abokan gaba namu tukunna mun isa can inda hular lamsara take in yaso bayan mun daukota mun kashe sarki shardas sai mu zauna na baku labari keda iyayenmu a cikin nutsuwa da kwanciyar hankali koda jin haka sai jaruma siyama ta bata rai tace yama za ayi nayi ta hakurin jin wannan labari har sai mun kai ga wannan lokaci me ye tabbacinka ma cewa zamu tsira da rayukanmu har mu sami nasarar dauko hular lamsara har yarima hulkas yabudi baki zai ce da ita wani abu sai ya ga jaruma rulaiya ta daka tsalle sama ta kama yin wata irin katantanwa a sama tana fille kawunan dakarun sarki shardas nan da nan ta karar da sauransu gaba daya ya zamana cewa babu dayansu da ya rage a raye saboda tsananin mamakin wannan gagarumar jarumtaka da jaruma rulaiya tayi yarima hulkas da siyama basu sansa adda suka wangame bakunansu ba suna kallonta koda jaruma rulaiya ta dago kanta ta dubesu sa adda take goge jinin takobinta a jikin gawar abokan gabar

Chapter 19 of 21