Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kallonta yama kara gaba yaki yarda su jera tare yaci gaba da sha aninsa kawai HAKAN NE YASA ITAMA jikinta yayi sanyi kuma taji a zuciyarta cewar abinda ta yiwa tsohon bata kyauta ba don ya fadi gaskiyaamma saboda girman kai irin na masu sarauta sai ta basar taki yarda tayi masa magana har suka shafe yini na biyu aka yada zango na biyu A cikin wani daji mai yawan bishiyoyi da duhuwoyi tabbas wannan daji yana da kwarjini gami da ban tsoro domin komai jarumtakar mutum idan ya tsinci kansa a cikinsa dole ne ya san cewa ya shigo wuri ma hadari sunana kenan daga zauran labarai bayan an kafa tantuna sai sarauniya larbisa ta tara gabadayan dakarunta ta shaida musu dacewa kada dayansu ya kuskura yayi barci domin akwai alamun mugayen abubuwa a cikin wannan daji saboda haka wani abun zai iya kawo harin sumame a yayin da dare yayi koda jin wannan batu sai shugaban dakarun nata wanda ake kira da sadauki muhairu ya risina ya ce ya shugabata kiyi mini izini mu kewaye sansaninmu da dogayen manyan itatuwa domin samar da cikakken tsaro kinga indai wani abune mai rai zai kawo mana harin ba zai samu damar afko mana ba kai tsaye koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace hakika kazo da shawara mai kyau amma idan ta nine ban damu da sai an kewaye sansanin ba sai dai saboda ku da kuyangina koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta tafi izuwa cikin tantina nan take sadauki muhairu ya umarci wadansu daga cikin dakarunsa dasu je su saro manyan bishiyoyin da za a kewaye su haka ramukan da za a sanya itatuwan Nan take kuwa dakaru suka kama aiki ba lalaci a lokacin dasu kuma kuyangi suka kama aikin dafa abinci ai kuwa kafin magariba tayi an kammala dukkan aikin ya zamana cewa an kewaye gaba dayan sansanin da manyan bishiyoyi yadda koda giwaye ne suka zo sai sun sha wahalar gaske kafin su sami damar ture bishiyoyin da aka kewaye sansanin bayan anci abinci sai dakaru suka ki su kwanta sukayi lambo suna masu dana kwari da bakansu masu takubba ma suka zauna a cikin shiri kuma aka kashe dukkanin fitilun iccen dake ci a sansanin ko ina yayi duhu dundum sarauniya larbisa kuwa kayan yakinta ta sanya ta zare takubba guda biyu tayi lambo a gaban dakarun nata saboda ita a jikinta ta san cewa lallai ba za a rasa wani mugun abu ba a cikin wannan daji kuma lallai abin zai iya kawo hari a koda yaushe har dare ya raba ba a ji wani bakon motsi ba a cikin dajin Al amarin da ya karya zuciyar dakarun sarauniya larbisa kenan suka fara tunanin cewar babu wani mugun abu da zai kawo hari dama a wannan lokaci da yawa daga cikinsu sun fara hamma saboda jin barci koda sarauniya larbisa ta lura da halin da dakarunta ke ciki sai ta dubi sadauki muhairu wanda yayi kwanciyar lambo kusa da ita tace maza ka gayawa sauran yaranka cewar duk wanda ya kuskura yayi gyangyadi na dakika daya ni zan sareshi da hannuna Nan take muhairu ya radawa daya daga cikin wannan batu shima sai ya radawa na kusa dashi a haka sauran gaba dayan dakarun suka sami wannan sako bayan faruwar hakan da kamar nisan dakika dari uku sai kawai kawai su sarauniya larbisa suka fara jiyo wani irin gurnani mai yawan gaske daga can nesa gurnani ne na wadansu irin halittu masu yawan gaske kamar na dodanni ko manyan birirrika inka dauke sarauniya larbisa da sadauki muhairu babu wanda hantar cikinsa bata kada ba a sansanin shikuwa tsoho huzallatul marwas kuwa fitowa yayi daga cikin tantinsa ya tsaya a tsaye yana mai rike kugunsa yana kallon can bakin kofar sansanin don yaga abinda zai faru alhalin kowa ya sami wuri ya buya a wannan lokaci kwatsam sai yaji jakarsa ta sihiri ta bude aljani subauratu ya baiyana a sama dai dai fuskarsa yana mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai karfi dake kadawa yace yakai mai gidana me kake takama dashi har da zaka fito ka tsaya a cikin wannan sansani alhalin kana gani cewar jaruman ma da suka yarda da kansu kwanciya sukayi a kasa sukayi lambo ko kuwa kunnenka baya jiyo sautin gurnani halittun dake shirin kawo farmaki izuwa wannan sansanin? Lokacin da tsoho huzallatul marwas ya ji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace haba yakai subauratu in banda abinka akan wane dalili tsoho zaiji tsoron mutuwa musamman ma kamata wanda bashi da kowa kuma bashi da komai ka tuna fa cewa ni yanzu na rasa babban masoyina wato mahaifina kuma na rasa uwata tun ma ina jariri na rabu da yan uwana na jini wadanda a halin yanzu ma bani da tabbacin suna raye ko sun mutu idan ma suna raye basu da wani amfani a gareni tunda sun kasance manyan makiyana a doron kasa lokacin da tsoho huzallatul marwas yazo nan a zancensa sai Aljani subauratu ya dubeshi yayi murmushi yace ai yan uwanka suna nan a raye duk su hudun amma a halin yanzu duk duniyar nan babu matsafan da suka fisu karfin sihirin tsafi amma hadin kansu ya watse sun zama abokan gabar juna ba don komai ba sai saboda kowannansu yana son ya mallaki littafin tsatsuba shi kadai saboda ya mulki komai da kowa na cikin wannan duniya koda jin wannan batu sai mamaki ya kama huzallatul marwas kuma hankalinsa ya tashi ya dubi Aljani subauratu cikin alamun tsananin damuwa yace kai kuwa menene dalilin da yasa tuntuni baka labarta mini wannan labari ba tun ina da sauran kuruciyata da karfin jikina ba yanzu ba da shekaruna suka haura hamsin? Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya sannan yace ai gaya makan bashine wani amfani tunda ba zaka iya yin komai ba akan lamarin dolene ka jira har zuwa lokacin da zaka sami daukakar da tafi tasu kafin huzallatul marwas ya budi baki ya kara cewa wani abu sai kawai sukaji kasa ta kama girgiza tamkar zata tsatstsage su rufta cikinta kuma sai gurnanin da suke jiyowa a can nesa ya kara kusantosu sosai bayan kamar dakika hamsin sai sukaji gurnanin ya cigaba da wanzuwa a lokacin da yake kara kusantosu suna nan a tsaye sai kawai suka ga dandazon cincirindon tarin birirrika sun durfafo inda suke kai tsaye yayinda huzallatul marwas yaga haka sai yayi maza ya mayar da Aljani Subauratu cikin jakar sa a lokacin da sarauniya larbisa ta fito daga cikin tantinta suma sauran dakaru haka suna fitowa ne sukayi Arba da tahowar wadannan birirrika nanfa hantar cikin kowa ta kada Amma banda na sarauniya larbisa saboda ita tasan cewa Jarumar gaske ce amma kuma matsalar itace basu da zafin nama da jarumtakar da zasu iya yakar wadannan birirrika nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa bitowar da tayi neman wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta.... Wow nima A nan zan dakata sbd ganin wadannan birirrikan kuma nake cewa sai Allah ya kaimu gobe zan ci gaba TSATSUBA Littafi Na Daya (1) Part D. . Nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa fitowar da tayi neman wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta, gama aiyana hakan keda wuya sai wani daga cikin birirrikan ya shammaceta ya gabza mata naushi a haba saboda karfin dukan sai da tayi sama tamkar an janyeta da majajjawa koda shugaban dakarun nata sadauki Humairu ya hango shugabarsu a can sama kuma ya tabbatar da cewa idan ta fado kasa cikin wadannan birirrika ta zama gawa sai ya falfala da gudu izuwa kan birirrikan yana mai kwalla ihu Ai kuwa sai birirrikan suka raba hankulansu biyu ya zamana cewa wasunsu sun daga kawunansu sama suna jiran sarauniya larbisa ta fado cikinsu su dasa mata wawa wasunsu kuma sai suka ruga izuwa kan sadauki Humaisu yayinda ya rage saura yan dakiku kadan larbisa ta fado kan birirrikan shi kuma humaisu yayi karo dasu sai kawai humaisu da larbisa sukaji an suresu anyi sama dasu cikin tsananin gudu na ban al ajabi tamkar za a taba hadari dasu kawai sai gani sukayi an diresu a tsakiyar sansaninsu nan take Aljani subauratu ya baiyana tsulum a gabansu yana mai kyalkyala dariya ya risina ga tsoho huzallatul marwas yace yanzu na cecesu ya shugabana amma kayi sani cewa anan ne kawai zan iya taimakonku amma da zararr mun kara gaba sai dai ku ceci kanku kafin larbisa ko tsoho huzallatul marwas dayansu yace wani abu tuni Aljani subauratu ya rikide ya zama guguwa guguwar ta tafi da tsananin gudu irin na tauraruwa mai wutsiya ta fada cikin dandazon birirrikan kawai sai gani akayi kawunan birirrikan suna guntulewa suna faduwa kasa gangar jiki na bingirewa sai dai kaga jini na tsiri da feshi daga cikin wuyansu koda birirrikan suka ga suna ta mutuwa kuma sun rasa wanda yake yi musu wannan barna sai suka haukace suka rinka ruri da kururuwa suna kaiwa iska duka amma duk a banza domin dada ragargazarsu ake yi suna zama gawa tabbas wuya ba dadi kuma idan kaji ana cewa ga ki gudu to tabbas sa gudu ne baizo ba lokacin da wadannan birirrika sukaga sun kasa kare kansu daga sharrin guguwar da ta addabesu sai suka fara juyawa da baya a guje suna kokarin komawa inda suka fito amma sai guguwar ta rinka kure musu gudu tana ci gaba da cire musu kawuna har saida ya zamana cewa babu sauran daya daga cikinsu wanda ya tsira da rayuwarsa A wannan lokacine dakarun sarauniya larbisa suka fara firfitowa daga cikin wuraren da suka buya cikin alamun kunya suna masu sunkui da kai kas cikin fushi sadauki Humaisu ya rufesu da fada yana kokarin hukuntasu kawai sai sarauniya ta tari numfashinsa tana mai kallonsa cikin murmushi tace kada ka hukunta su domin banga laifinsu ba bisa guduwar da sukayi suka buya kai kanka ai kasa tarar birirrikan kayi sai da kaga zan hallaka sannan kayi kundunbala ka rugo domin ka kawo mini dauki hakika kayi gagarumar gwaninta wacce ta burgeni don haka idan mun koma gida zan yi maka wata gagarumar kyauta wacce ban taba yiwa wani mahaluki ba koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Humaisu ya zube kasa bisa guowoyinsa a gaban larbisa yana godiya nan dai larbisa ta bayar da umarnin aje a kwanta ba tare da wani bata lokaci ba kuwa kowa yaje ya kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba. Kashe gari kuwa da sassafe aka kimtsa bayan an yi kalaci sai sarauniya larbisa tsoho huzallatul marwas tace Ljaninka ya gaya mana cewar tafiyar yini biyu da rabi zamuyi mu riski dajin da jaruma shumaira take tabbas yanzu mun shafe tafiyar yini daya kunga kenan saura ta yini daya jal a gabanmu shin akwai sauran wani mugun abune da zamu hadu dashi kafin mu isa dajin da jaruma shumaira take? Koda jin wannan tambaya sai tsoho huzallatul marwas da sadauki Humaisu suka dubi juna sukayi shiru larbisa ta dubi huzallatul marwas cikin fishi tace ai kai ne ya kamata ka bani amsar wannan tambaya huzallatul marwas yayi ajiyar numfashi sannan yace ya shugabana aini a ganina yanzu bai kamata kiyi shakkar wani abu ba tunda dai gashi mun ga bayan wadannan mugayen birrirrika saboda nasan cewa abu ne mawuyaci mu sake haduwa da wani mugun abu wanda ya fisu hadari koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta yi murmushi tace tabbas kazo da magana mai ma ana yanzu kawai saimuci gaba da tafiya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka hau kan dawakai bayan an debe komai aka ci gaba da tafiya ba sassauci tsoho huzallatul marwas ne akan gaba yana jagorantar rundunar, sarauniya larbisa, da sadauki Humaisu na biye da shi sannan sauran dakarun, Kamar yadda Aljani subauratu ya fada haka Al amarin ya kasance wato sai da suka shafe tafiyar rabin yini guda sannan suka iso wani katon daji mai yalwar Bishiyoyi, koramai da fadamomi, kai da ganin wannan daji kasan cewar dajine mai ni'ima irin wanda mafarauta ke so domin dole ne a samu dabobin daji da tsuntsaye masu yawa a cikinsa da shigarsu sai suka hango wani katon garke na ragon dawa cike da raguna da tinkiyoyi abin mamaki shine an kewaye garken ne da siraran itatuwan bishiya marasa kwari wadanda dabbobin zasu iya kakkaryasu su watsu amma kuma dabbobin basu ture itatuwan ba sun gudu koda dakarun sarauniya larbisa suka hango garken wannan dabbobi sai suka cika da farin ciki suka ruga izuwa cikin garken suka dasawa dabbobin wawa da nufin kowa ya kama iya rabonsa kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji ana naushinsu ta sama suna zubewa kasa duk wanda akayi wa naushi daya sai dai kaga yayi sama ya fado kasa a matukar galabaice wanda ke naushin nasu kuwa a samansu yake shawagi kamar tsuntsu har sai da ya gama bazar dasu kasa sannan ya duro kasa bisa kafafunsa aka fara kallon kallo tsakaninsa da sarauniya larbisa ba wani bane yayi wannan gagarumar jarumtakar ba face jaruma shumaira kai da ganin irin kallon da sarauniya larbisa ke yiwa jaruma shumaira kai kasan cewa tana cikin tsananin mamaki ba wani abu bane yasata wannan mamaki ba face a rayuwarta bata taba zaton cewa zata ga wata ya mace ba mai kyau kamarta ba amma a yanzu da tayi arba da shumaira saita raina kanta kuma ta tabbatar da cewar babu abinda zata fi shumaira dashi face mulki da dukiya cikin tsananin fishi shumaira ta dubi su larbisa tace dame kukazo wannan daji shin yan fashine ku ko kuwa matafiyane wadanda basu san ya kamata ba duk mai hankali idan ya dubi wadancan dabbobi ya lura da yadda aka kebancesu yasan akwai mai su duk da cewa kuwa a cikin daji suke kuyi sani cewa wannan daji nawa ne don haka komai na cikinsa mallakina ne babu wanda yake da ikon yin farauta a cikinsa face ni A cikin wannan daji kakana na bakwai yayi rayuwarsa kuma tun daga zamaninsa kawo i yanzu babu wanda ya isa ya taba komai a nan sai da izininmu da yardarmu ku gaya mini abinda ya shigo daku cikin dajin nan in ba haka ba kuwa sai dai na yakeku koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai larbisa ta matso gaba kusa da ita ta sauko daga kan dokinta ta dubi shumaira cikin murmushi tace yake shumaira yaga mafarauci Imshal ki yi sani cewa nice Sarauniya Larbisa mai mulkin birnin darul kaizul kuma musamman nazo wannan daji naki domin na gana dake bisa wata muhimmiyar bukata tawa koda jin wannan batu sai jaruma shumaira ta gyada kai cikin alamun fishi da rashin yadda tace mu bama mu amala da masu mulki kuma baki da wani abu wanda zaki iya biyana dashi na taimakeki saboda haka ina mai shawartarku daku gaggauta fita daga cikin wannan daji nawa idan ba so kuke muyi yaki ba koda gama fadin hakan sai jaruma shumaira ta juya da baya ta nufi wannan garke na dabbobin ta ta shiga gyara turakan dake ciki tana daure dabbobin koda ganin haka sai sarauniya larbisa ta dubi gaba dayan dakarunta tace duk abinda zai faru tsakanina da jaruma shumaira kada ku saka baki ko hannu nan take larbisa tabi shumaira izuwa cikin wannan garken dabbobi ta kama tayata aikin daure dabbobin Al amarin da ya fusata jaruma shumaira kenan ta kaiwa larbisa wawan duka da kafa a wuya, cikin bakin zafin nama larbisa ta kaucewa dukan nan fa suka kaceme da azababben fada suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tun da su jarumi Humaisu suke ganin gumurzu na fadan hannu tsakanin jarumai basu taba ganin fada mai tsananin ban tsoro ba kamar wannan domin gwanintar ta hadu da gwaninta kuma sadaukantaka tayi kada da kishiyarta Sai da wadannan jarumai biyu suka shafe rabin sa a suna naushi da bugun juna hannu da kafa ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina kuma sun fara galabaita amma saboda bakar zuciya sunki su daina fadan amma kuma jaruma shumaira tafi sarauniya larbisa jure duka domin ita tana iya shanye duka uku na larbisa amma data naushi larbisa sau daya sai kaga ta fadi kasa sai dai tayi hanzari ta mike taci gaba da fadan Al amarin da ya dugunzuma hankalin su sadauki Humaisu kenan domin sun tabbatar da cewa idan aka ci gaba da wannan fada a haka har zuwa wani dan dogon lokaci shumaira zata iya sumar da larbisa ko kuma tayi mata wawan rauni Gashi kuma larbisa ta gargadesu akan kada su kuskura su shiga cikin wannan fadan Ana cikin wannan bakin gumurzune shumaira ta shammaci larbisa ta daka tsalle sama ta doki fuskarta sau uku da kafa take larbisa ta dimauce kuma ta gigice ko da taji zafin dukan saita zare takobinta ta kaiwa shumaira sara cikin sa a kuwa ta yanki shumaira a damtsen hannunta na hagu har wajan ya dan dare kadan jini ya fito shumaira tayi tsalle gefe daya tana mai yin yar kara bisa jin zafi da zugin da taji koda ta dubi hannun nata taga raunin da larbisa tayi mata sai ta fusata ainun itama ta zaare rantsatstsiyar takobinta ta ruga izuwa kan larbisa itama larbisa saita rugo izuwa kanta koda ya rage saura baifi taku uku su hadu ba sai kowacce ta daka tsalle sama suna masu kai mugun sara Takubbansu na haduwa saita larbisa ta rabe gida biyu, A saman shumaira ta doki kirjin larbisa ta fado kasa a dimauce kafin larbisa ta mike tsaye shumaira ta duro kanta da nufin ta soka mata takobinta a gefen jikinta...... . Wow lallai Yakamata nima nakaiwa Larbisa Dauki Amma bari naje na dauko Rantsatstsiyar takobina sannan na dawo . Anan ne kuma littafin Tsatsuba Na daya yazo Karshe marubucin yace... SHIN SHUMAIRA ZATA SAMU DAMAR SOKAWA SARAUNIYA LARBISA TAKOBINTA KUWA? . SHINSU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU? . WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? . SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA? . Mu Hadu A Tsatsuba Littafi Na Biyu Domin Jin Ci Gaban Wannan Labari Daga Mai debe muku kewa a Kullum kuma a ko Yaushe TSATSUBA Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator::- Shuraih 99% You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com SATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part A. LOKACIN DA TAKOBIN SHUMAIRA TA ISA kirjin sarauniya larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin danna takobin a cikin kirjin nata kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa daga baya bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa, ta mike tsaye daga kanta ta waigo tayi arba da wanda yayi mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci imshal. Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya kamashi sosai domin shekarunsa zasu kai kusan arba in gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk farin gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka a bayansa rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi sune da fatar damisa Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana mai nuna girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya larbisa ta mike tsaye tana mai dafe gefen kirjinta inda shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya cikin biyayya ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar yana mai kare mata kallo sama da kasa sannan ya karewa dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike yaki da wannan mace mai daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani cewa haka kawai wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na umarcesu da su fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu amma saboda naci sai wannan sarauniya ta biyoni har cikin garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na gama da ita yanzu domin da ita da yaran nata su gane cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da dariya sannan ya hade fuska ya dubi shumaira yace ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki bata gaya miki cewar tana da wata bukata ba a wajanki? Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar tana da wata bukata a wajena amma saina gaya mata cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi mata koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci shin bakya tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila a sanadinta ne muma zamu fita bakin cikin da ya addabemu tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne cewar na gaya miki zamu iya nasarar samun abinda muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu bakin jarumai guda uku? Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai daga can kuma sai ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan sarauniya ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi mini bayani imshal yace hakane amma dai ki tsaya muji abinda ya kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa cikin nutsuwa tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan sarauniya ma abociya kyawu da karjini wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo har wannan daji namu? Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta yace amma kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya bude wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin magani me maiko da kauri kamar daskararren nonon shanu ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki kuma ki shafawa bakuwar tamu cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta sannan taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata fuskarta a daure babu annuri, su kuwa su sadauki Humaisu sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda tsoho Imshal ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani a rauninta sai tsoho Imshal ya dubi larbisa yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku keda jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso bayan kun nutsu saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya taimakon juna zamu iya yarda da buqatarki, idan kuma ke kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan samun nasara ki kara gaba, koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarauniya larbisa , Tare dani mai Rubutu, ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace nayi farin ciki da wannan tayi da ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta bani cewa nima zan iya baku taimako bisa taku bukatar Tsoho Imshal yayi murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai yana gama fadin hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon dutse yana mai yafito su larbisaa Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau tabi su. Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan sadauki Humaisu da sauran Dakaru. Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa ya cika da mamaki bisa ganin wani dankareren gida wanda aka ginashi da duwatsun wuta Gidan katone kuma anyi masa fasali na gidan sarauta dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine babu bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida kuma ba wani bane face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya baibayeta domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin wannan daji da ta ga sun zo mata da mutane har gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo har sai da suka matso kusa taga cewar babu wata alamar damuwa akan fuskar mijinta da 'yarta Ita kanta larisa shekarunta sun kai hamsin da biyu koda uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya bata mutum ba zai taba zaton ta kai hakan ba Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya Larbisa a gareta sannan ya gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci cikin farin ciki larisa ta karbi sarauniya larbisa tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu sadauki Humaisu izuwa wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma shumaira izuwa dakinta Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka kafin larbisa ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai itama shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan suka zauna tare bisa wasu kujeru dake karkashin wani tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffab ba Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin ba abinci ne mai dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci musamman mazauna daji cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa tace yake wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan abinci namu na talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai irin naki abincin da kika taho dashi? Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta itace yin koyi da irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina matukar jin dadin wannan abinci naku amma fa babu abinda ya bani mamaki a yanzu sama dake koda jin haka sai shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace ke kuma me nayi wanda ya baki mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci gami da yin ajiyar numfashi sannan tace gani nayi da farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi kikauda batun matsayina na sarauta yanzu kuma sai gashi kina yin biyayya da hidima a gareni Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai

Chapter 2 of 21