Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga bisani kuma sai ya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki ayubul hasnu ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya babu wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan tafarkin mallakar masoyansu ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar da babu masoyi dai dai take da zama a cikin kurkukun daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma shumaira duk kun kasance kyawawan matan da babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye gurbin larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren jarumta kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku biyun nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba samun galaba a kanta ba koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su a ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul hasnu yake fadi shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana da masu bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma larifat wacce ta kasance 'ya mace kamarmu yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai shi kenan inda babu kasa nan ake gardama Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI. Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi sarki Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas mai hular lamsara? Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon numfashi sannan yace labari ne mai tsawon gaske sai dai nayi iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku shi... SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN JARUMAN DUNIYA GUDA UKU wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba kuma ba za ayi ba a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin da ba za a taba mancewa dasu ba sai dai kash duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a tafarkin soyayya Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan labari domin akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar haka...... . Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan gadan a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai Hulkas mai hular lamsara kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya saboda haka sai ku gyara zamanku zuwa anjima zanci gaba da suburbudomuku lbr February 4 at 11:35 AM TSATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part D. . NAN TAKE SARKI AYUBUL HASNU YA SHIGA BASU LABARI KAMAR HAKA. kimanin shekaru Ashirin da hudu da suka shude a birnin Romaniya anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS IBN KAUMIL sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin sadauki mai tarwatsa maza a filin daga yana da tsananin karfin damtse na Allah ya isa don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi kasa kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu komai ba A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake ko izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin arziki cikin bad da kama su kwato bayi da dukiya da mata ba tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan halaiya ne ya addabi gaba dayan kasashen dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa gano mutanen dake yin wannan barna, babu irin matakin da sarakuna basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye basuyi ba don gano rundunar dakarun dake wannan mummunar barna amma abu ya gagara babban abin bakin cikin ma shine sarki shardas ya tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma da tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba amma duk da haka bai daina yin wannan fashi da kwace ba Masana da masu bincike na wannan zamani sun tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki da ya kai sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan sarautar da yakai nashi girma da kawatuwa,duk bayin da ya kamo da mata ana boye sune a gidajen gonarsa da wani bangaren daban na gidan sarautar inda har abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya shaida dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa shine dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun wanda ya taba guduwa ba daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa face sarki shardas yasa anbi bayansa an kasheshi saboda tsananin tsoron da ake yiwa dakarun sarki shardas ne yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin mutum dubu uku sun fito mamayar bazato izuwa wani babban kauye da ke gefen wata makociyar kasa da ake kira salmas sai suka kai hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen kauyen wanda ake kira Malgur. Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu tumaki da raguna masu yawan gaske kuma Allah ya albarkacesu da kyawawan mata ababan kwatance ga kuma tarin zuri'a Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi ne ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa da suna Hailur, a wannan rana ne hailur yayi aurensa na farko a duniya kuma matar da ya aura budurwace yar shekara goma sha takwas a duniya wacce babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin gaba daya A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a cikin bikin auren hailu ana ta kade kade da raye raye saboda murna kowa da kowa ya zage yana ta rawa maza da mata yara da manya gaba daya dakarun ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye makamansu sun shiga cikin taron 'yan rawa suna cashewa kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi dakarun Ajali sun bullo daga kowace kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa dawakai aguje kuma sun zare makamai suna ihu da kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara da tsofaffi suka kama ihu da guje guje suna neman maboya, a dai dai wannan lokaci ango Hailur na tare da amaryarsa shadila a cikin tantinsa suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo iface iface da guje gujen jama arsu a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike tsaye zumbur daga kan shimfidarsu suka suri suturarsu suka sanya hailur yayi waje ya dauko takobinsa da garkuwarsa ya dubi shadila yace komai wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan tanti indai kika kiyaye wannan umarni nawa ni dake duk zamu tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati kada ki kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai jiyoki shadila ta kada kai cikin alamun tsananin damuwa tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka nan take hailur ya sumbaci goshin shadila sannan ya juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta ruko hannunsa ta rungume shi tana mai fashewa da kuka ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a jikinta cewar abune mawuyaci su sake ganin juna, ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face ta dan leka wajan tantin daga tsananin yawan dakarun sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa tabbas an shammaci nasu dakarun ba zasu iya kare kansu ba Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin nata ya sake dubanta cikin yanayi mai nuna yarda dakai yace ki barni kamar yadda kika saba ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da rayuwarki da tawa, shin kin manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa shekaru uku baya sa adda wata rundunar yan fashi suka ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo? Ko dajin wannan batu sai Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin hali tace haba ya masoyina ai ba zan taba mancewa da wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda jin haka sai fuskar hailur ta fadada da murmushi yace to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya ga wannan ina mai yi miki wani babban albishir cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta zaro idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini yanzu? Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a ranar farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don haka yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke da cikin dana kona mutu a wannan yaki bani da nadama ko takaici na san cewa na bar wanda zai kula dake Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin babu abinda na tsana a wannan duniya sama da dana ya taso maraya hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari cewar danki ba zai taso a maraicin rashin uba ba yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice da gudu daga cikin tantin Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar jama arsu ana saransu da sukarsu suna ihu jini na tsartuwa fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa daga cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya hausu da sara da suka ya zame musu guguwar annoba a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan bayi mata da ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a wani bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan take ya hango jarumi Hailur yanata ragargazar dakarunsa duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza na. Zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona Al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan dimin tunda yake fita sumame da yaki bai taba ganin jarumi mai irin zafin naman hailur ba gami da tsagwaron jarumtakarsa duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki shardas sun kashe kaso takwas daga cikin kaso goma na jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya baci ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake cikin dajin aka daina yakin aka tsaya cak tamkar babu abu mai rai a wajen a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin amsa kuwa a dajin gaba daya shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin wannan kururuwa ya kura idanu izuwa sashin da kuwar ta fito da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai da yan dakiku suka shude sannan ya hango sarki shardas ya tunkaroshi daga can nesa kadan take zuciyar jarumi hailur ta buga da karfi ya ji tsoro ya darsu a cikin ransa a karon farko a duk gwagwarmayar da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya haddasa hakan ba face a iya rayuwar jarumi hailur bai taba ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa ba kamar sarki Shardas duk da cewar fuskar sarki shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi hailur ya gane cewa lallai wannan sadaukiba saurayi bane shekarunsa sun kai arba in da 'ya'ya kuma idanunsa ya kalla kawai ya gane hakan, abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma wanda baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da garkuwarsa da kyau koda ganin haka sai sarki shardas yayi murmushin mugunta kawai sai shima ya zare takobinsa daga cikin kufenta wata irin takobi ce mai tsawo da kaifi kuma anyita ne da wani irin karfe na musamman wanda sai kwararren makeri ne zai iya gano hakan take sarki shardas ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu duk sa adda sawun kafafun sa suka taba kasa sai kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya rugo izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai shima ya ruga izuwa gareshi duk su biyun suna ihu da karaji yayin da ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai wawan hari sarki shardas ya kaiwa hailur sara a wuya da nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da garkuwarsa take garkuwar ta rabe gida biyu tamkar an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama hailur ya kaiwa shardas suka da takobinsa a ciki shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma duk da haka sai da takobin ta huda rigarsa ta tsargeta in ba don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai takobin ta huda cikinsa koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da mamaki shi dai sarki shardas bai taba karo da jarumin da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar jikinsa ba amma yau gashi ya hadu da wanda ma ya tsargeta da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge garkuwarsa gida biyu don haka ya tabbatar da cewar duk sa adda takobin shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi masa ba nan fa Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya iya kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun sarki shardas sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin takobinsa sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta sakamakon haduwa da tayi da garkuwar sarki Shardas Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin hailur kenan ya tabbatar da cewar babu wata hanya da zai iya kare kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci garkuwar dake hannunsa yin hakan kuwa yasan cewa ba karamar sa a bace da nasara A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki shardas da tsirarun dakarun su hailur da sukayi saura a wajan sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa matan da aka kama amatsayin bayi aka daddauresu tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan yara wadanda kusan su duka an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu sai da kimanin dakiku dari da arba in suka shede ana kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi hailur kowannansu tunanin dabarar da zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka sake rugawa izuwa kan juna a karo na biyu suna haduwa asama sai sarki shardas ya kawowa hailur sara a cinya shi kuma yakai masa sara a ka kowannansu yayi iya kokarinsa wajan kaucewa harin cikin zafin nama amma sai da takobin sarki shardas ta yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani yayi hailur ya tuje rawanin dake kansa ya fado kasa sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su duro kasa gaba daya tuni hailur ya doki hannun sarki shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta subuto kasa cikin bakin zafin nama hailur ya fada kan garkuwar ya sureta kuma yayi 'yardungure sau uku izuwa can gaba yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin cinyar tasa don tsaida jini shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun dakarun su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun shaida ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa yace su karasasu gaba daya take dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara da suka suka karkashesu a cikin 'yan dakiku kadan koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya kurma uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne ba naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku munyi masa rubdugu ku zuba ido kamar yadda kukayi da farko kuga yadda zamuyi dashi koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari jarumi hailur suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare hare wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin azababben zafin nama na gaban kwatance Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba yayi gaba na baya sai labari duk da irin tsananin juriya da jarumtaka irin ta hailur wannan karon sai da ya raina kansa domin bambancin a baiyane yake kuma sarki shardas ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a lokaci guda ya hada da kai masa naushi da bugu da hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa hailur jini da majina yana bal dashi kamar tamola... . Tab ganin wannan yanayi da hailur yashiga ya sa ni na tsaya a nanSATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part E. . SAI GASHI NAN DA NAN YA HADA MISHI JINI DA MAJINA YANA BAL DASHI KAMAR TAMOLA, ashe duk wannan abu dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take tana ganin abin dake faruwa cikin tsananin fargaba da tashin hankali kwatsam sai sarki shardas ya sami nasarar saran kafadar hailur ta hagu hailur ya kurma ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma sai yayi sauri ya rike takobin ta sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna takobin ta nutse a cikin kafadar koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita kurma ihu bata san sa adda ta fito da gudu daga cikin tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke jiyo ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo yayi arba da ita koda yaga irin tsananin kyawunta sai ya dimauce ya juya da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda karfin dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa kwazazzabo ne da magudanar ruwan wata korama koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya kwarara uban ihu irin na wanda ya saddakar mutuwa zaiyi ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale kasa sumammiya sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya dauketa ya azata akan dokinsa nan take dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba ana tunkarar birnin Romaniya Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da bakin rawani kuma ya shakawa shadila banju barcinta ya sake nauyi don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya da tsakiyar dare lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci kan wani luntsumemen gado na alfarma a cikin wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko daga kan gadon, ta kama kallon kowacce kusurwa koda tagama ganin kayan kawar dake cikin dakin sai tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata ta tuno da duk abinda ya faru a sansaninsu sa adda aka kawo musu sumame na mamayar bazato nan take shadila ta dafe kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar turakar ba wani bane ya shigo cikin turakar face sarki shardas a cikin wata irin kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri ya durfafeta koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin da hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe mini miji kuma ka kashe dukkan mazajen ayarinmu ina sauran yan uwana mata? Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan zuri ata koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace yake wannan ma abociyar kyawu da cikar zati kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama matar sarkin birnin Romaniya a yanzu duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita ki manta da komai da kowa ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci kanki a cikin daular da baki taba ji da gani ba koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka kai kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur ta suri wukar ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni idan ka matso kusa dani zan kasheka. Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar dariya ya durfafeta kai tsaye ai kuwa yana kusantarta sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan dutse ta bugata kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa kan gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya tana ta faman rusa ihu da kukan bakin ciki daga wannan rana shadila ta zama matar sarki shardas da karfin tsiya ya zamana cewa kullum a cikin daula take babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori suyi mata duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri arta lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas akan sai taga inda aka kai sauran +yan uwanta mata wadanda aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora izuwa wani bangare daban na gidan sarautar wannan ranace ta farko wacce shadila ta sami damar fita daga bangaren da turakarta take koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take burinta na son guduwa ya yanke, haka dai sarki shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da sukayi tafiya mai nisa duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna risinawa suna gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata koda shadila tayi arba da yan uwanta mata yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai ta ruga garesu tana mai kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye take suma bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki shardas tace ina neman alfarmar ka yanta wadannan yan uwa nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina. Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila cikin murmushi yace yake matata kiyi sani cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu taba fita ba daga cikin harabar gidanki duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin kisane a kanta koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara rungume shadila sunayi mata godiya ita kuwa shadila sai ta dubi sarki shardas tace na amince da wannan sharadi naka nan take sarki shardas ya sa dakarun dake kula da wadannan bayi suka kwankwance musu sarkokin dake wuyansu da hannayensu sannan aka tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka basu suturu masu kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu tunda aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin romaniya bata taba yin farin ciki ba sai a wannan rana da aka 'yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa sarki Shardas murmushi ba sai a yau din nan Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata haka dai dai da rana daya shadila bata taba mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai tayi mafarkinshi sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta tuno da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya ba babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin da tayi a lokacin da hailur ya gaya mata cewa komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take amma sai ta mance da sharadin ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin da taga sarki shardas ya sareshi da takobi a kafada ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar sarki shardas sai alamun juna biyu suka baiyana a gareta ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo da zazzafi da ciwon kai ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya tura aka kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi likitar ta dubi sarki shardas tayi masa bushara cewar matarsa ta sami juna biyu Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki amma da ya tuno da wani al amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa hannu ya zabgawa shadila mari ba, saboda karfin marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo sarki shardas ya sunkuya ya kamo kafadunta yana mai daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu ba kuma matana na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan bokana ya tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira LAMSARA. Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane maza ki hanzarta sanar dani maishi kona shakeki ki mutu yanzu Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta bushe da dariya al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya mike tsaye yana mai kura mata idanu, shadila ta yunkura ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan daula da nake ciki a wannan gidan sarauta daidai yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya ta fita daga raina tun daga ranar da ka wargaza rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur kuma ka tarwatsa ayarinmu, ka sani cewa wannan hari da kuka kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan dangina a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina hailur wanda har yanzu xuciyata ke wasu wasin cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar maka da cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni mun tafi domin wannan juna biyu da nake dauke dashi nasa Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya sake zabga mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto rayuwarta koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar abinda ya aikata saboda tsananin son da yake yiwa shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo masa A fusace ya

Chapter 4 of 21