Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ta kashe taga ririn kallon da suke yi mata na al ajabi sai tayi murmushi ta dubi yarima hulkas tace kuzo mu yi sauri mu karasa gaba tunda bamu san halin da sauran yan uwanmu suke ciki ba ba tare da wani bata lokaci ba sai suka kara hawa kan wannan dokin sihiri na jaruma rulaiya su ukun suka zabureshi da gudu izuwa gaba saboda girman wannan doki da cikarsa duk su ukun sai da suka zamo yan kanana akansa Al amin Ahmed Misau ++ ACAN Inda yaki ya ruguntsume kuwa tsakanin su sadauki ruhaisu da su murzanu abin ya kazanta babu kyan gani saboda karfin yazo daya domin ragargazar kowanne bangare ake yi har ta kai cewa ana ta yin ragas sai da aka shafe sa a daya da rabi ana wannan mugun yaki har ya zamana cewa an karar da gaba dayan dakarun kowanne bangare saura mutum biyu kacal suna fafatawa, wato saura Sadauki Ruhaisu da Murzanu gashi dai kowannansu ya yiwa dan uwansa raunika har guda uku uku jini na zuba a jikinsu juwa na dibarsu amma saboda tsananin nacinsu da mugun buri na son ganin bayan juna kowannansu yaki yarda yaje kasa Lokacin da bala'i yakai bala'i ya zamana cewa sun gaji likis sai suka zube kasa bisa guiwoyinsu suna haki da numfarfashi kamar ransu zai fita bayan dan wani lokaci sai kowannan su ya mike tsaye da kyar sannan suka ja da baya taku bakwai bakwai tamkar sun hakura da yakar juna kwatsam kuma sai suka rugo da gudu izuwa kan juna suna masu kwalla ihu cikin mugun nufi duk wanda yaga lokacin da wadannan manyan jarumai suka tunkari junansu kasan cewa mugun gamo za ayi ko dai a mutu ko kuma ayiwa juna mugun lahani da zai iya zama sanadin Ajali, ai kuwa yana ragewa saura taku uku kacal su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama suka kaiwa junan su suka da takubbansu cikin sa'a kuwa kowannansu ya lumawa abokin fadansa takobi a ciki ta faso ta gadon bayansa lokaci guda suka kurma uban ihu sakamakon Tsananin zafi da zogin da suka ji suka rikito kasa a matukar galabaice suka kurawa juna idanu sa adda suka fara kakarin mutuwa bisa mamaki sai sadauki murzanu yaji sadauki Ruhaisu ya bushe da dariyar farin ciki don haka sai ya dubeshi cikin matukar karfin hali ya budi baki da kyar yace yakai makiyi abokin gaba tayaya aka yi kai da zaka mutu amma kake yin dariyar murna, koda jin wannan batu sai sadauki ruhaisu ya yi kakin jini ya tofar sannan shima ya budi baki da kyar yace ina farin ciki ne zan mutu bayan na cika burina na yiwa takobina wanka da jininku yanzu ne yan uwana da kuka kashe zasuyi barci mai dadi a cikin kabarurrukansu hm Al amin nake typin Dan Misau, kuma idan naje na riskesu zasu yi alfahari dani kai fa da wani farin ciki zaka mutu ? Shin zakayi alfahari ne da cewa ka mutu dan bautar sarki shardas wanda ya maishe daku karnukan farautarsa ko kuwa ? Me kabar wa iyalinka wanda zasu cigaba da rike kansu bayan ka mutu ? Na sani cewa kan yiwa sarki shardas bauta saboda kana tsoronsa amma ba don kuna samun wani abu a hannunsa ba yanzu me ce ribarka a cikin bautar sarki shardas ga shi kayi mutuwar banza idan ma shardas yazo nan yaga gawarka yawu zai tofa maka tunda baka cika aikinsa ba wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin ya gane kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai ya sake dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken Gawa..... TSATSUBA Littafi Na Tara (9) Part D. . TAKUN KARSHE.. Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Koda jin wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin ya gane kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai ya sake dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken Gawa. Shi kuwa sadauki ruhaisu yana cikin wannan hali ne na kakarin mutuwa ya hango hailur bisa doki da a sukwane tare da sauran tsirarun yan kabilarsu Tun daga nesa da hailur ya hango sadauki ruhaisu zaune a kasa dirshan ga takobi a cikinsa sai ya rusa uban ihu cikin kwalla masa kira kuma ya fashe da kuka yana mai karawa dokinsa kaimin gudu Yana isowa daf dashi sai yayi turjiya ya sauko daga kan dokin ya durkushe a gabansa sannan ya kamashi ya rungume a kirjinsa yana mai sake fashewa da sabon kuka cikin Karfin hali sadauki ruhaisu ya daga hannunsa ya kama kumatun hailur suka dubi juna kowannansu na zubar da hawaye amma sai sadauki ruhaisu yayi murmushi a gareshi yace yakai dan uwana bai kamata kayi mini kuka ba tunda na mutu akan tafarkin cika burin kabilar mu alfaharina guda daya ina so ka dauke gawata ka kaita zuwa can asalin birninmu wanda sarki shardas ya baje ka binneta wannan itace kadai wasiyyar da zan bari bayan raina koda gama fadin haka sai idanun sadauki ruhaisu suka kafe suka daina motsi kuma gaba dayan jikinsa ya sandare koda ganin haka sai hailur ya sake kwarara uban ihu a karo na biyu ya rungume gawar sadauki ruhaisu kuma ya sake fashewa da matsanancin kuka nan take ragowar dakarun nasa dasu shadila suka kamu da tsananin tausayi kuma suka kama kuka basu bar wannan waje ba sai da hailur ya sa aka je aka dauko akwatun gawa na katako aka sa sadauki ruhaisu a ciki aka kulle sannan suka kara gaba inda suka iske tawagar sarki hulbasu da su yarima hulkas suna yin wata irin tafiya ta ban Al'ajabi domin da karfin sihirin tsafi suke yinta cikin tsananin gudu na ban al ajabi kuma wannan farar tsuntsuwa ta sihiri ce take yi musu jagora don zuwa inda hular lamsara take.. Al amin Ahmed Misau ACAN BIRNIN askandariyya kuwa sai bayan tafiyar su yarima hulkas da tazarar sa a bakwai sannan aka ga wata irin gagarumar iska tana saukowa kasa daga sama wadda ta dugunzuma hankalin komai da kowa dake birnin saboda karfinta nan fa bishiya suka rinka karyewa suna zubewa kasa rufin gidaje ya rinka kwayewa kasa ya kama girgiza ba komai ne ya haddasa wannan masifa ba face iskar fuka fukan aljanin dake dauke da sarki shardas da bokansa labarusa sai da aljanin ya duro kasa bisa tsakiyar gidan sarautar sarki hulbasu sannan inda ya duro din ya wawake yayi rami mai zurfi sannan iska ta dauke nan fa jama a suka kama guje guje da iface iface aka dimauce sosai kai kace sama da kasa ce zata hade saboda tsananin razanar da jama ar suka yi sakamakon ganin abubuwan uku wato ganin wannan shirgegen Aljani da kuma sarki shardas da bokansa Labarusa har sarki shardas ya zare takobinsa zai nausa cikin gidan sarautar sarki hulbasu sai boka labarusa ya tsaidashi ya dauko madubinsa na tsafi ya nunawa sarki shardas abin da ya faru a birnin kafin su iso koda sarki shardas yaga yadda aka kashe gaba dayan dakarunsa su sadauki murzanu a bayan gari da dukkan shirin da su yarima hulkas sukayi aka gudu da matarsa shadila sai ya kamu da tsananin bakin ciki nan take gaba dayan jikinsa ya kama makyarkyata kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan kankara Al amin Ahmed Misau, zuciyarsa kuwa ta kama tafarfasa kamar zata kone bai san sa adda ya dakawa bokan nasa labarusa tsawa ba yace tsayuwar me muke yi a nan alhalin kana gani makyanmu sun tafi dauko hular lamsara maza muje mu kure musu gudu mu karkashesu cikin alamun tsananin tashin hankali da karayar zuciya boka labarusa yace ai zuwa da wuri yafi zuwa da wurwuri idan muka ce zamu cigaba da wannan tafiya a wannan aljani ba zamu taba iya riskar abokan gabarmu ba kafin su isa inda hular lamsara take, wannan dokin sihiri da yarima hulkas yake bisa yafi wannan aljani namu karfin gudu sau arba in dole ne mu samo wani doki wanda zai iya cin musu, cikin zakuwa sarki shardas ya ce to taya zamu iya samo namu dokin da zai cimma nasu? Koda jin wannan tambaya sai bokan ya zauna a kasa dirshan ya karanta wadansu dalasiman tsafi na musamman guda uku ya tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya doki kasa da tafin hannunsa sau uku faruwar hakan keda wuya sai kasa ta fara girgiza a gabansa nan take ta dare sai ga wani murgujejen jan doki ya faso daga cikinta girman wannan doki ya ninka nasu yarima shardas sau uku koda ganin wannan doki sai boka labarusa ya mike tsaye zumbur cikin matukar farinciki ya shafi dokin sannan ya dubi sarki shardas cikin murmushi yace ya shugabana ina tabbatar maka da cewa a cikin sa a iku kacal wannan doki zai iya cimma su yarima hulkas muna riskarsu sai mu kashesu mu kwace wannan tsuntsu na sihiri tayi mana jagora izuwa inda hular lamsara take koda jin wannan jawabi daga bakin boka labarusa sai sarki shardas ya daka tsalle ya haye bisa kan jan Dokin shi kuwa boka labarusa sai ya bace bat ya sake bayya akan dokin kuma a gaban sarki shardas ya juyo ya dubeshi cikin murmushi yace to sarkin sauri saika sarrafa dokin na gani idan zaka iya sarki shardas ya mai dawa boka labarusa murmushi yace ai kowa a bangarensa sarki ne inda dai batun karfi ne ko jarumtaka nine zan jagoranceka wannan aikinka ne ba nawa ba da jin haka sai boka labarusa ya bushe da dariya Nima Al amin Ahmed Misau na tayasu sannan ya shafi wuyan dokin kawai sai dokin ya zabura da karfi ya falfala da azababben gudu na gaban kwatance da al ajabi saboda karfin gudun dokin har tashi sama yake yana tsallake gidaje koguna da tsaunika kuma a cikin dakika biyar kacal ya ke shafe tafiyar sa a goma, Hakika tsafi gaskiyar maishine in ba tsafin ba babu yadda za a yi a sami doki mai irin wannan karfin gudun ' '' AL'AMARIN su yarima hulkas kuwa bayan sun shafe tafiyar wata guda a cikin sa'a bakwai da karfin sihirin tsafi sai dare ya fara riskesu a cikin wani daji don haka sai sarki hulbasu ya bayar da shawarar a tsaya a yada zango ba tare da wata gardama ba hailur dasu yarima hulkas suka amince, nan da nan aka kafa tantuna sannan kuyangin sarki hulbasu suka shirya abinci hailur ya zauna tare da yayansa yarima hulkas da jaruma siyama da kuma matansa shadila da zalina, shima sarki hulbasu sai ya zauna tare da matarsa luzuraina da kuma dansa yarima barmas suna cin abinci ita kuwa jaruma rulaiya wacce har yanzu babu wanda ya taba ganin fsukarta ko ya san labarinta face yarima hulkas sai ta koma can gefe daya ta nisanta da kowa ta zauna tana cin abincinta ita kadai a kusa da farin dokinta na sihiri a lokacin da dokin ke yin kiwo abinsa yana cin ciyawar kasa koda sarki hulbasu ya hango jaruma rulaiya a can gefe daya ita kadai sai ya dubi yarima hulkas yace me yasa waccan abokiyar tafiyar taka har yanzu taki yarda tabude fuskarta mu gani kuma me yasa take gudun jama a shin ba zaka bamu labarinta yanzu ba ? Sa adda yarima hulkas yaji wadannan tambayoyi sai yayi dan guntun murmushi sannan yace ba don waccen bakuwar ba da tuni na dade da shekewa barzahu ta ceci raina a baya don haka tana bina bashi labarinta yana da yawa gami da ban tausayi da al ajabi kuyi hakuri sai mun sami lokaci isashshe caraf sai hailur ya tari numfashin yarima hulkas yace ai kuwa ni indai haka ne bai kamata ka barta ta rinka kadaita haka ba tashi kaje wurinta ka debe mata kewa saboda na ga alamar cewa kamar tana cikin damuwa da tunani tunda tama kasa cin abincin sosai koda jin haka sai yarima hulkas ya mike tsaye cikin murna ya tafi wajen jaruma rulaiya, da ganin haka sai yarima barmas ya dubi jaruma siyama yace kawata idan bazaki damu ba nima ina son nayi wata magana mai muhimmanci tare dake koda jin haka sai jaruma siyama ta murtuke fuskarta ta daka masa harara amma tana hada idanu da hilairu sai ta mike tsaye ta kama hannun yarima barmas taja shi izuwa gefe daya suka kama hira cikin raha da nishadi lokacin da yarima hulkas ya isa inda jaruma rulaiya ke zaune sai ya isketa cikin tunani mai zurfi don haka sai da ya kira sunanta sannan tasan da zuwansa, yarima hulkas ya dubeta cikin alamun damuwa ya ce yake jarumar mata kuma sarauniyar kyawawa me ya faru naga kinyi tagumi kina tunani mai zurfi haka koda jin haka sai rulaiya tayi doguwar ajiyar zuciya sannan ta dubeshi cikin alamun fargaba ta ce yakai hulkas kayi sani cewa tun da muka yada zango a nan wajen naji zuciyata na bugawa da karfi ina ji a jikina cewar akwai wani mugun abu dake shirin samunmu lallai zamanmu anan yana da matukar hadari kasani cewa dama ina da niyyar baka irin horon yakina a cikin wannan tafiya tamu saboda na san cewa zai amfaneka don haka yanzu saika mike tsaye mu fara, tana gama fadin haka sai ta mike tsaye ta zare takobinta guda biyu shima yarima hulkas sai ya mike tsaye ya zare tasa takobin nan take suka ruguntsume da azababben yaki mai tsanani koda su sarki hulbasu suka ga jaruma rulaiya na kaiwa yarima hulkas mugayen hare hare tana neman hallakardashi har ma ta dan yankeshi kadan a damtsen hannunsa na hagu sai gaba dayansu suka yunkura zasu afkawa jaruma rulaiya amma sai jaruma siyama tayi tafi tasha gabansu tace kada ku shiga wannan yakin domin baso take ta hallaka shi ba yaki take koya masa kuyi tunani mana inda kasheshi take son yi ai ba za ta ceci rayuwarsa ba a baya ba kuma idan a yanzun take son kasheshi gaba dayanmu babu wanda ya isa ya hanata don karfin damtsenta da iya yakinta da kuma karfin sihirinta domin karfin tasirin sihirin tsafinta ya ninka namu sau goma gama fadin haka keda wuya sai suka fara ganin abin al ajabi domin nan take suka ga yarima hulkas ya fara iya duk irin yanayin yakinta sai gashi yana iya kare hare haren ta kuma yana mai da martani sai da suka shafe rabin sa'a suna bakin gumurzu har ma yarima hulkas ya sami nasarar dukan kirjin jaruma rulaiya ta fadi kasa cikin hanzari ya ruga gareta ya bata hannunsa ta kama ya tasheta tsaye sannan ya dubeta cikin damuwa yace Ki gafarceni yake jarumai jarumai koda jin haka Al amin Ahmed Misau, sai jaruma rulaiya tayi murmushi tace aini farinciki na yi da naga yanzu ka sami nasarar kani kas tabbas ka sami horon yaki irin nawa, gama fadin hakan keda wuya sai jaruma rulaiya ta dafe kanta ta kwalla ihu kuma ta sulale kasa sumammiya al amarin da ya razana kowa ke nan a wajen aka rugo izwa kanta sa adda yarima hulkas ya rungumeta a kirjinsa cikin dimauta cikin hanzari aka yayyafa mata ruwa nan da nan kuwa ta farfado cikin tsananin mamaki da kaduwa yarima hulkas ya dubeta yace menene ya sameki kikayi ihu kika fadi kasa sumammiya alhalin kina tsaye cikin koshin lafiya Jaruma rulaiya tace '' A duk sa adda wannan Aljani wanda ya raineni yayi mini wahayi haka nake kasancewa barci ne yake daukata mai nauyi shiyasa kaga kamar na suma aljani Arwasul masadul ya sanar dani cewa abokan gabarmu sarki shardas zasu iso nan ya riskemu a cikin sa a biyu kacal mai zuwa don haka ya gargadeni da mu hanzarta a cigaba da tafiya kuma yayi mini albishir cewa zamu iya isa kogon da hular lamsara take a cikin sa a biyun koda jin wannan batu sai kowa ya mike tsaye zumbur aka shiga shirin gaggawa aka kwashe komai aka hau dawakai aka kama tsala azababben gudu a cikin daren wannan farin tsuntsu na sihiri nayi musu jagora a sama a cikin iska dokin jaruma rulaiya ne akan gaba yana dauke da mutum uku wato ita kanta jaruma rulaiya yarima hulkas da jaruma siyama a cikin sa a biyu cif suka iso bakin wani katon kogon dutse wanda gaba daya bayansa sama da kasansa a shafe yake babu alamar kofar shiga, Al amin Ahmed Misau, kowa dake wajan sai da yayi iya kokarinsa wajan gano inda kofar shiga take amma yarima hulkas na dafa wani wuri a jikin dutsen sai kofa ta bude suka yi arba da cikin kogon wanda yake da tsananin haske yadda ko allura ce ta fadi za a iya ganinta babu komai a cikin kogon dutsen face kayan yaki iri iri masu tsohon tarihi na manyan sarakuna da manyan jaruman da suka shude nan take suka hango hular lamsara a can sama bisa kan wani dutse mai tudu kowai sai jaruma rulaiya ta dubi yarima hulkas ta ce maza kaje ka dauko waccen hula ta lamsara anyi tane domin kai kadai kuma kai kadai ne zaka iya daukota a nan cikinmu Saikuma Jarumi Al amin Ahmed Misau, Amma bari na barshi yauko saboda naci girma hmm, koda gama fadin hakan sai yarima hulkas ya ruga da gudu ya je ya dauko hular lamsara yana daukowa kuwa sai kofar gogon dutsen ta fara rufe kanta, A guje yarima ya fito yana fitowa sai ya daga hular sama da nufin ya sanyata a kansa amma sai yaji an doki kirjinsa saboda karfin dukan bai san sa adda ya saki hular lamsara tayi sama ta fada kan wani tsauni mai tsawon gaske ta kama gangarawa a lokacin da shi kuma yai sama izuwa kan tsaunin ya fado kasa magashiyan yana aman jini yana daga kansa sama sai yaga sarki shardas tsaye a kansa yana yi masa murmushin mugunta boka labarusa na tsaye bisa wani jan doki a gefe guda kawai sai sarki shardas ya yunkura da nufin ya ruga inda hular lamsara take ya dauketa ya sanyata amma sai yaji an daure kafafuwansa da hannayansa da wata tufkekiyar sarkar karfe ta sihiri ba wani ne ya daure hannun sarki shardas ba face bokansa boka labarusa cikin tsananin mamaki da kaduwa sarki shardas ya dubi boka labarusa yace saboda me zaka ci amanata ka hanani daukar hular lamsara? Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa yace dashi tabbas sai yaune na tabbatar da cewa kai wawa ne mara basira kana zaton tsawon shekarun danake yi maka bauta inayi ne saboda kaunarka idan har ka dauki haka to kayi babban kuskure masu iya magana sunce so sone amma san kai yafi kowanne Ai Al amin Ahmed Misau Nake , Aski yazo gaban goshi domin A halin yanzu littafi ya kusan karewa, ina yi maka bauta ne saboda zuwan wannan rana da zan mallaki hular lamsara saboda nasan cewa idan na mallaketa tamkar na mallaki duniyar nan ne gaba dayanta, dukkanin sarakunan duniya sai sun dawo karkashin ikona, duk wata dukiya ta duniya sai ta zama tawa ni kadai a bincike na nagano cewa kaine kadai sarkin da zanjingina dashi na tsorata dukkanin bokaye da sarakunan duniya tunanin mallakar hular lamsara tunda an san kana nemanta kuma kowa yana tsoronka, koda boka labarusa yazo nan a zancensa sai sarki shardas ya kuma wani gagarumin uban ihu cikin bakin ciki ya dubi boka labarusa yace in dai don hular lamsara ka daureni da wannan sarkar sihiri to ina umartar ka da ka gaggauta kwanceni domin na yaki makiyana gasu tsaye a gabana kada su kashe ni a banza na rantse da darajar iyayena nabar maka hular lamsara bana bukatar ta ni dai ka barni na tsare mutuncina da rayuwata, koda jin wannan batu sai boka labarusa ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda ya murtuke fuskarsa yace haba shardas ta yaya kake zaton cewa bera zai taba yarda yayi zumunci da mage ? Kada ka manta cewa sama da shekaru talatin bayanake tare da kai tun kana matashi babu wanda ya san halinka Sama dani yaudara cin amana da rashin imani duk takenka ne shin a rayuwarka ta duniya mata nawa ka mayar gwagware ? Shin a rayuwarka ta duniya yayaye nawa ka mayar marayu ? Al amin Ahmed Misau Nayi imanin cewa baka san adadinsu ba ai dama ance rana da yawa ta barawo rana daya tak ta mai kaya koda gama fadin haka sai boka labarusa ya dubi sarki hulbasu yace ga wanda ya sa ka yanka danka da hannunka kuma yasa bakin ciki ya kashe ubanka sai ka dauki fansa akansa boka labarusa ya sake duban jaruma rulaiya wacce har a sannan fuskarta a rufe take cikin bakin kyalle yace da ita ke kuma ga wanda ya kashe ubanki ya mallake dukiyarsa gaba daya ya janyo kika girma a inda babu mutane sai ki dauki fansa kema ni bani da wata alaka daku burina kwai na mallaki duniya koda gama fadin hakan sai boka labarusa ya tashi sama kamar tsuntsu ya dira a can sama bisa wannan tsauni ya nufi inda hular lamsara take koda ganin haka sai jaruma rulaiya ta dubi yarima hulkas tace idan muka bar wancan bokan ya mallaki hular lamsara zalunci zai shimfida a doron kasa, muma sai mun zama bayinsa ni zanje na yakeshi na kawai dashi kai da jaruma siyama da sarki hulbasu ku yiwa sarki shardas irin kisan gillar da kuke son yi ku daukar mana fansar zaluntarmu da yayi koda gama fadin hakan sai jaruma rulaiya ta cire bakin kyallen dake fuskarta su jaruma siyama sukayi arba da tsananin Kyawunta sai suka cika da tsananin mamaki kawai sai suka ga jaruma rulaiya ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta dira akan wannan tsauni ta nufi inda boka labarusa yake yarima hulkas, jaruma siyama sarki hulbasu suka tunkari inda sarki shardas yake daure a cikin sarkar sihiri koda yaga sun durfafo shi sai ya kama kyalkyala dariya al amarin da yayi matukar basu mamaki kenan sarki hulbasu ya dubeshi yace saboda me kake dariya alhalin ka san cewa KISAN GILLAH zamuyi maka domin mu huce takaicin bakin cikin da ka kunsa mana, al amin Ahmed Misau Sarki shardas yayi murmushi yace ina yin wannan dariya ne saboda dalilai guda biyu rak ! Dalilin farko shine, ba zaku iya kasheni ba inda bana daure cikin wannan sarkar tsafi, kunga kenan ku ba jarumai bane nikuwa na zalunceku ne saboda nafi karfinku, babu yadda zakuyi dani don haka zan mutu ina mai farin ciki da alfaharin na mutu a jarumi abin tsoro, dalili na biyu kuma da yasa nake yi muku dariya shine ko kun kasheni yanzu kamar kun kashe maciji ne baku sare kansa ba saboda wannan bokan nawa boka labarusa idan ya mallaki hular lamsara sai yafini barna da zalunci a doron kasa kun ga kenan a karshe kuma kuma rayuwarku zata kasance a cikin bautarsa da takaicin zaluncinsa wata kila duk ya karkasheku sarki shardas na gama wannan jawabi sai ya cigaba da kyalkyala dariyarsa Yana cikin dariyar ne sarki hulbasu ya zare takobinsa ya kafta masa mummunan sara a kaurin kafarsa ta hagu nan take kafar ta guntule jini yai feshi da tsartuwa sarki shardas ya kwarara uban ihu sakamakontsananin zafi da zugin da ya ratsa sassan jikinsa koda ganin haka sai shima yarima hulkas ya zare tasa takobin ya sare kaurin kafar sarki shardas ta dama wato suka mayar dashi gurgu :) the Al amin Misau A dai dai wannan lokaci ne suka jiyo karafkiyar karafa a can saman wannan tsauni suka gane cewa azababben yaki ne aka kaure dashi tsakanin boka labarusa da jaruma rulaiya, cikin alamun fishi hailur ya dubi yarima hulkas yace yakai dana ka tafi izuwa ga jaruma rulaiya wacce ta ceci rayuwarka kuma kayi mata halarci ka ceci rayuwarta ka bar mu da wannan tsohon azzalumin abokin gabarmu mu dauki fansa a kansa koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya ruga da gudu izuwa jikin tsaunin nan ya kamashi ya fara hawa shi dai wannan tsauni saboda tsananin tsawonsa duk abin dake kansa daga kasa ana hangoshi dan mitsitsi tamkar kuda ne Abinda su yarima hulkas basu sani ba shine ashe can karshen wannan tsauni wutace take dafa dutse yana narkewa saura kadan dutsen yayi bindiga ya fara aman ruwan wutar lokacin da yarima hulkas ya shafe dakiku masu yawa yana hawa kan wannan tsauni yaga ko rabin tsawon tsaunin bai kai ba sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin cewa anya kuwa ma zai iya kaiwa can saman tsaunin har ya taimaka wa jaruma rulaiya ba tare da ya gaji ba ya subuto kasa ya hallaka Al amin Ahmed misau ++ ++ ++ ACAN kasan tsaunin kuwa sai su sarki hulbasu suka taru su uku akan sarki shardas suka rinka yankar naman sassan jikinsa da kadan kadan yana ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da zogi da azabar da yake ji hatta kunnuwan sarki su hulbasau daban -daban suka yankesu sannan suka kwakule idanuwansa daya bayan daya A haka dai suka yi tayi masa azaba kala iri iri har rai yayi halinsa cikin mummunan kisan gilla wato sarki shardas ya zama Gawa ! A dai dai lokacin da su hailur suka kashe sarki shardas ne shi kuma yarima hulkas ya isa can saman wannan dogon tsauni da kyar da sidin goshi bayan duk jikinsa ya kukkuje sau tara yana zamewa a saman kamar zai fado Kasa amma cikin sa a sai ya sake chafe tsaunin hakika yarima hulkas yasha bakar wuya wajen hawa kan wannan dogon tsauni domin kaiwa jaruma rulaiya dauki, yana isa saman tsaunin sai yayi arba da jaruma rulaiya da boka labarusa kwance a kasa jina jina sun yiwa junansu mugayen raunika suna jan ciki sun nufi inda hular lamsara take wacce ke sakale a jikin wata karamar bishiya a can karshen gabar tsaunin A wannan lokaci ne kuma tsaunin ya fara girgiza alamar cewa wutar da ke ci a karkashinsa na yin bindiga a sannan ne kuma hailur da sarki hulbasu da siyama suka hau kan tsaunin da karfin sihirin tsafi kawai sai suka hango boka labarusa da jaruma rulaiya sun durfafi taba hular lamsara da hannayansu shi kuwa yarima hulkas ya ruga garesu da gudu Al amin Misau ai kuwa sai saman tsaunin ya dare gida biyu jaruma rulaiya da boka labarusa suka gangara zasu fada can kasa inda dafaffen dutsen ke ambaliya ga wuta a cikinsa muraran cikin tsananin sa a jaruma rulaiya ta ruko wani dutse bata fada can kasan tsaunin cikin wutar ba amma sai taji caraf shima boka labarusa ya cafko kafarta nan fa nauyin boka labarusa ya fara rinjayar jaruma rulaiya koda ganin haka sai yarima hulkas ya samu da kyar ya daka tsalle sama ya dira a karshen tsaunin shima ya cafo hannun jaruma rulaiya ya zamana cewa nauyinta dana boka labarusa ya dawo hannunsa, hailur da jaruma siyama da sarki hulbasu kuwa sai suka rasa yadda zasu yi su kai wa su yarima hulkas

Chapter 20 of 21