Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaton zai Samu ba, A tunanin sarki shardas zai yi amfani da wannan gasa ne ya talauta gaba dayan sarakunan nahiyar da attajirai domin ya kasance duk karfin arzikinsu ya dawo hannunsa, shi kuwa wannan gida da aka gina akan tsakiyar kogi sai da aka shafe shekaru goma sha shida ana gininsa ba wai mutane ba hatta aljanu tsegumin gidan suke suna ta yadashi a duniya, lokacin da aikin ginin yayi nisa sai da sarki shardas ya sare, domin gani yayi tattalin arzikinsa na neman karyea, bisa dole ya kara ninka harajin da mutane ke biya a kasarsa kuma ya tsananta farautar bayi da kai harin sumame ana kwace dukiyoyin jama a wata nahiyar ana maishe su bayi A haka dai aka samu aka kammala wannan kasaitaccen gida na gaban kwatance, bayan an kammala ginin gidan ne sarki shardas yasa rana ta wannan gasa wacce a ranar za 'a bude wannan gida wohoho tun kafin ranar tayi da tsawon sati hudu birnin nasa ya cika ya tumbatsa da baki daga ko'ina na duniya, yazamana cewa ko ruwan sha mutum ke siyarwa a garin yana samun kudade masu yawa a wannan lokaci kudin shiga birnin ma da aka samu ba'a taba samun kamarsu ba Al amarin mahaifina kuwa wato Attajiri Amsar............ Wow Domin jin yadda zata kasance mu hadu a part na gaba amma kafinnan nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square nake cewa mu zama lafiyaTSATSUBA Littafi Na Takwas (8) Part C. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . AL'AMARIN MAHAIFINA KUWA WATO ATTAJIRI AMSAR, a cikin daji ya yada sansani da tazarar kwana uku a sannan ne ya debi dakaru dari biyu kacal ya bar ragowar dari takwas domin suyi gadin mahaifiyata koda yazo zai yi sallama da mahaifiyata sai ta fashe da kuka tace yakai mijina ban taba rabuwa dakai ba tsawon yini guda amma yanzu gashi zaka tafi halartar wannan gasa har tsawon kwanaki bakwai lallai zan kasance a cikin kewarka da begenka, ka sani cewa na sami labari cewa wannan gida da sarki shardas ya gina a duk fadin duniya a yanzu babu kamarsa a kyau da kawatuwa lallai ina yi maka fata da addu ar ka mallakeshi, kuma lallai ina son naga wannan gida da idanuna koda kuwa ba zan sami damar shiga cikin sa ba sa adda mahaifyata tazo nan a jawabinta sai nan take idanun mahaifina suka ciko da kwallah ya dubeta cikin alamun tsananin takaici yace ki gafarceni ya masoyiyata kiyi sani cewa wannan ne karo na farko da kika tambayeni abinda ba zan iya baki shiba a cikin wannan duniya ki sani cewa idan na kuskura na shigar da ke cikin wannan birnin karshen zamana dake yazo bare ma har na kaiki kiga wannan kasaitaccen gida wanda za ayi gasa a kansa, wannan shine kashedin da bokayena suke yi mini idan kuma kina son mu rabu ne to shikenan sai na kaiki kiga wannan gida koda jin wannan batu sai mahaifiyata ta rungume attajiri amsar ta fashe da matsanancin kuka tana mai kankameshi a kirjinta tace ai ko duniyar nan kaf za a bani in dai za a rabani dakai bana bukatarta, koda jin haka sai farin ciki ya lullube mahaifina Al amin Ahmed Misau, sai da sukadan jima a kankame da juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata sukayi sallama ya hau kan dokinsa, kafin ya tafi sai da ya dada jan kunnen dakarun nasa su dari takwasa da zasu yi gadinta da kuma kuyangi uku da zasu yi mata hidima yace lallai su tabbatar da cewar wani abu bai kusanceta ba bare ya cutar da ita nan dai mahaifina attajiri amsar tare da dakaru dari biyu suka nufi cikin birnin sarki shardas , mahaifiyata da sauran jama arsa suka bisu da kallo har sai da suka ga sun kule '' '' '' BIRNIN ya ciki ya tumbatsa da al uma duk inda ka duba babu abinda zaka gani face kawunan bil adama rututu babu masakar tsinke, sai da ta kai cewa an rasa gidaje na haya inda ake saukar baki, dole jama a suka rinka kwana a kasuwa wasu ma a gefen gari suka rinka kafa tantuna sai dai siye da siyarwa ya shigo dasu cikin birnin gidan sarautar sarki shardas kuwa ya cika da manyan sarakuna manyan attajirai manyan bokaye da manyan yarumai kuma kowannansu an bashi masauki mai daraja kuma an girmamashi A rayuwar sarki shardas yana son zama tare da wadannan mutane guda hudu wato sarakai, attajirai bokaye da jarumai wato Mu ke nan ehm Al amin nake, har izuwa safiyar ranar da za ayi wannan gasa hankalin sarki shardas bai gama kwanciya ba duk da cewa shi ya tara dukkanin sarakunan nahiyar da kuma amsu gayyata Al amarin daya sa wazirin sarki shardas ya fahimci cewar sarkin nasu yana cikin wata damuwa don, haka sai ya dubeshi cikin girmamawa yace wai shin menene yake damunka ? Naga sai kallon kofar fada kake yi shin akwai wanda kake son ganin zuwansa ne, sarki shardas yayi ajiyar zuciya sannan yace ai banga sarkin attajiran ba attajiri Amsar ibn Warhas, anya kuwa zai amsa wannan gayyata tawa, koda jin wannan batu sai waziri ya dafe kirjinsa kuma ya zazzaro idanu yace, haba ya sarkin sarakuna , kaine fa zaki uban dawa kuma kaine dodon maza sa gudu maganin ki gudu yanzu kai a tunaninka akwai wani daya isa a wannan duniya da zai ki amsa gayyatarka, kome mutm yake takama dashi kafishi, kuma duk wanda yaja dakai sai yakai kasa sarakuna nawa ne suka mutu a dalilin bakincikin da ka kunsa musu bokaye nawa ne suka jarraba karfin tsafinsu akanka suka mutu Attajirai masu tarin dukiya nawa ne ka talautar dasu ai ina tabbatar maka da cewar ajali ne kadai zai hana attajiri amsar halartar wannan gayyata taka kuma ko don ma ya nuna matsayinsa akan sauran attajirai dolene ya amsa gayyatar ka amma abin tambayar shine wai shin menene dalilin da yasa ka damu da zuwan attajiri Amsar ibini warhas ? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi dan guntun murmushi sannan yace lallai ina son attajiri amsar yazo wannan gasa saboda sai yafi kowa siyan wannan gida nawa da daraja, to amma fa ina tsoron abu guda daya shin baka ganin cewa yana da kudin da zai iya siyen wannan gida nawa har ni kuma ya hanani mallakarsa ? Waziri ya gyada kai yace haba ya shugabana yanzu ashe akwai attajirin da zai fika kudi a wannan nahiya tamu ai a ganina ko nawa attajiri amsar ya siyi wannan gida kai kuma sai ka kara kudinka ko ka ninka akan nasa sau talatin tunka ka san cewa babu asara a cikin aikata hakan ka tuna fa cewa daga cikin dokar wannan gasa shine duk kudin da mutum ya taya wannan gidan ba za a dawo masa dasu ba Al amin Ahmed Misau, kaga kenan komai yawan kudaden da aka tara naka ne kai kadai, koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki shardas ya kama yin murmushin murna yana mai cigaba da kallon bakin kofar fada sannan ya dubi wazirinsa yace gaba dayan manyan sarakuna da attajiran da na gayyata sun iso tare da iyalansu tun tsawon yan kwanaki kafin zuwan wannan rana ta yau me ya sa shi attajiri amsar baizo da wuri ba bare da iyalansa alhalin na dade ina son naga matarsa saboda naji ance agaba dayan birnin hindu babu mai kyanta, abinda yake bani mamaki shine duk karfin shirin nan nawa na tsafi na kasa ganin hoton siffar matar tasa a cikin madubin tsafina kuma a iya bincikena nakasa ganin ranar da zan ganta bisa wannan daliline yasa na ke dan shakkar al amarin attajiri amsar ibn warhas, domin lokacin dana fara zurfafa a cikin binciken sirrinsa sai na gano cewa yana samun kariya ne daga wani takadarin aljani wanda ni kaina ban sanshi ba kuma na kasa gano ko waye shi hatta bokana abin dogarona ya kasa gano min aljanin da yake baiwa attajiri amsar kariya, sarki shardas na zuwa dai dai nan a jawabinsa kwatsam sai ga attajiri amsar ibn warhas ya shigo cikin fadar dakaru dari biyu kacal nakewaye dashi Da shigowar attajiri amsar cikin fadar sai gaba dayam jama ar dake wajan suka mimmike tsaye suka rinka dukawa suna gaishe da attajiri amsar saboda kwarjininsa tamkar ya kasance wani babban sarki, tufafin dake jikinsa ma babu wani basarake a wajan daya sanya mai kyansa da tsadarsu saini Al amin Ahmed Misau hatta shi kansa sarki shardas din kuwa kai ko mutum bai san attajiri amsar ibn warhas ba yana ganinsa dole ne ya girmama shi saboda tsabar kamalarsa da kwarjininsa ko shi kansa sarki shardas wanda kowa ke tsoronsa da yi masa biyayyar dole ba shi da irin wannan kwarjini da kamala na attajiri amsar don hatta manyan fadawan sarki shardas basu san sa adda suka rinka rugawa izuwa ga attajiri amsar suna kama hannunsa suna sumbata ba haka ma sauran sarakunan da ke cikin fadar domin kowa gani yake kamar idan har ya sami nasarar sumbatar hannun attajiri amsar ya sami tabarrakin da shima zai zamo gagarumin attajiri kamar attajiri amsar din, koda sarki shardas yaga yadda ake girmama attajiri amsar sai ya kamu da tsananin kishi gami da matukar baki ciki ya fara tunanin cewa babu abinda yafi attajiri amsar dashi face jarumtaka, tunda yana da mace mai kyan da bashi da kamarta kuma yana da dukiyar da wata kila tafi tasa yawa bayan attajiri amsar ya gama gaisawa da manyan mutane wadanda suka yi ta shan gabansa suna hanashi zuwa wajan sarki shardas sai ya kukuta da kyar ya isa inda sarki shardas ke zaune bisa karagar mulki yana zuwa daf dashi sai ya zube kasa wanwar ya kwashi gaisuwa tamkar zaiyi masa sujjada don girmamawa al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan shi kuwa sarki shardas sai farin ciki ya lullubeshi yaji kansa yayi nauyi don haka sai ya mike tsaye daga kan karagar sa ya taka matattakalar ya sauko har kasa har gaban attajiri amsar ya kama kafadun sa ya tasheshi tsaye ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini sannan kuma sai ya kama hannun sa ya jashi zuwa kan karagar mulki suka zauna tare akan karagar, Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarki shardas ya girmama wani mutum ba kamar haka yadda ya yiwa attajiri amsar nan take sarki shardas ya bada umarni kuyangi suka shigo cikin fadar dauke da abinci da abin sha irir iri na musamman irin wanda ba a taba kawowa ba tun daga ranar da aka fara saukar baki, sai da aka gama ciye ciye da shaye shaye ya zamana cewa kowa ya sami nustuwa sannan sarki shardas ya mike tsaye a lokacin da fadar tayi tsir tamkar mutuwa ta gifta yayi gyaran murya yace yaku manyan baki kuyi sani cewa yanzu taro ya cika tunda sarkin Attajirai amsar ibn warhas ya iso saboda haka yanzu ba tare da bata lokaci ba zamu dunguma gaba daya mu tafi izuwa inda wannan gida yake wanda nayiwa lakabi da suna DARUL DAULAT ! Duk wanda ya san zai shiga wannan gasa to ya tafi da dukkan shirinsa amma yanzu za a fadi dokoki uku na shiga wannan gasa, doka ta farko itace dole ne kowanne sarko ko kowanne attajiri ko boka ko jarumin da ya amsa gayyata ya shiga wannan gasa kuma duk kudin da ya zuba a gasar ba za a dawo masa dasu ba walau yayi nasara ko bai yi ba doka ta biyu itace idan aka shiga cikin wannan gidan gasa babu wanda zai fito har sai an kammala kuma kowa ya kwantar da hankalinsa domin an tanaji masauki da isashshen abincin da kowa zaici har a kammala Al amin Ahmed Misau, doka ta uku wacce itace ta karshe itace duk wanda ya lashe wannan gasa dole ne ya baro kasarsa ya dawo wannan gida da zama tare da iyalansa har izuwa karshen rayuwarsa, koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai hankalin gaba dayan masu gasar ya dugunzuma ainun musamman attajiri Amsar domin wannan doka ta karshe ba karamar tayar masa da hankali tayi ba Nan take ba tare da bata lokaci ba aka fito daga cikin fada aka debo jakunkunan dinare aka loada akan dawakai da rakuma da alfadarai sarki shardas ne da kansa ya jagoranci gaba dayan yan gasar kowa dakarunsa Na bashi tsaro da kariya aka nufi bakin kogi inda gidan Darul Daulat yake sauran jama ar gari kuwa sai da wannan zuga tayi gaba da tsawon rabin sa'a sannan aka sa dakaru suka yi musu rakiya tafiyar kusan rabin sa a akayi aka iso bakin katon kogin dake bayan gari tun daga nesa hasken gidan darul daulat ya fara dallare idanun mutane kuma tsananin girman gidan da kyawunsa ya dimauta kowa hatta su attajiri amsar kuwa duk da cewa gidan a can nesa yake a tsakiyar kogi amma kowa ya firgita da ganin irin gini da akayi masa a bakin tekun an ajiye manyan jiragen ruwa sama da guda dari wadanda za a shiga a ketare kogin a isa gidan na sarakai , attajirai da wadanda suka isa sannan kuma akwai kwale kwale kimanin guda dubu na talakawa da zuwan su sarki shardas bakin tekun sai kowa ya sauka daga kan dokinsa suka rinka shiga cikin jirgin ruwan jirgin sarakai daban haka mana na attajirai da sauran bokaye da jarumai ko kyakkyawan motsi sarki shardas baya barin attajiri amsar yayi ma ana baya yarda yayi nesa dashi don gudun kada wani tsautsayi ya rabasu lokacin da jiragen ruwan suka yi nisa a cikin kogin suka kusanci tsibirin da aka gina gidan darul daulat sai kowa ya sake cika da tsakanin mamaki ba komai ba sai domin ganin tsananin girman nasa ya kai rabin birnin gaba daya na sarki shardas abin da yafi daurewa mutane kai shine' wai shin ta yaya aka iya gina wannan gagarumin gida ? Tabbas aikin ginin wannan gida yafi karfin ace mutane ne sukayi shi dai sai aljanu aljanun ma sai dai idan wadanda suka gina birnin farisa ne suka yi ginin wannan gida nan fa kowa ya zama cikakken dan kauye aka rinka wangame baki ana kallo wasu ma basu san sa adda suka fara dalalar da yawu ba sai da gaba dayan jiragen suka iso bakin gabar kogin daf da kofar gidan sannan kowa ya fito daga cikin jirgin aka bi sarki shardas a baya, ita kanta kofar wannan gida inda za a cireta a baiwa mutum ta isheshi gudanar da sauran rayuwarsa ta duniya kai Madaki Al amin Ahmed Misau Sunana domin jarine babba saboda anyi tane da zallan dutsen lu u lu u mai tsawo da kaurin gaske gami da fadi inda karti dubu zasu taru ba zasu iya daga kofar sama ba saboda nauyinta su kansu aljanun da suka kerata sai da aka zabo majiya karfi arba in sannan suka iya dagata sama suka kafata a jikin ginin, nan take sarki shardas ya zaro wata kuba ta zinare ya mitsitsiya kuma siririya ya zurata a cikin kofar mukulli, shigar kubar keda wuya sai aka ji sakata na zare kansu, wani zagayayyen mukulli mai kauri da tudu ya rinka zagaya kansa a tsakiyar kofar har sai da ya kewaya sau goma sha biyu sannan sakatun suka gama zarewa duka, take kofar ta bude wanwar da kanta, a dai dai wannan lokaci ne sarki shardas ya waigo cikin murmushi ya dubi gaba dayan yan gasar yace duk wanda ya lashe wannan gasa shizan damkawa kubar wannan gida, yana gama fadin haka sai ya zura hannunsa cikin kofar mukullin ya zare kubar ya zurata a cikin Aljihun wandonsa sannan ya kama hannun attajiri Amsar ibn warhas yaja shi suka kunna kai izuwa cikin wannan gida na darul daulat, take suma sauran, sarakai Attajirai da jaruman gasar suka rufa musu baya Wohoho !! An dade ana bautawa kasa anyi mata ado da dukiya ! Duk wanda ya sanya kafarsa ya taka lu'u lu'un da aka shinfida a kasan gidan ya ga yadda ko ina ya kasance fes fes ! Babu ko kura ko guda daya bare yanah, sai ya cika da al'ajabi kai kace kullum akwai hadimai sama da miliyan goma masu share ko ina da gogewa alhalin babu wata halitta guda daya mai rai a ciki ba tare da wani bata lokaci ba sarki shardas ya wuce kai tsaye izuwa cikin wani babban falo na gidan wanda ya ninka fadarsa sau goma a girma da kawatuwa... Nima kuma sai nabishi a bayaaaa. Al amin Ahmed Misau zan dakata Anan saikuma Allah ya kaimu Gobe zamu cigaba Nidinne dai Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson Ko A square Dan garin KadunaTSATSUBA Littafi Na Takwas (8) Part D. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . BA TARE DA WANI BATA LOKACI BA SARKI SHARDAS YA WUCE KAI TSAYE IZUWA CIKIN WANI BABBAN FALO NA GIDAN WANDA YA NINKA FADARSA SAU GOMA A GIRMA DA KAWATUWA hatta kujerun da shimfidar dake cikinsa babu wanda ya taba ganin makamantansu, duk yawan jama ar da suka halarci wannan gasa suna shiga cikin wannan falo sai suka zama yan kadan tamkar an sanya kwayar gero guda daya jal akan faranti, har izuwa wannan lokaci sarki shardas na rike da hannun attajiri amsar ibn warhas, shi kuma attajiri Amsar yana dogara wani dan karamin kwagiri na zinare dake hannunsa, kwagiri ne na zinare wanda aka kawatashi da adon sarauta, irin sane kwagirin da manyan sarakai ke dogarawa yayin da suke tafiya don kawata kwalliyarsu, kai tsaye sarki shardas yaja attajiri amsar suka je suka zauna akan wata luntsumemiyar doguwar kujera mai daraja, shi kuwa wazirin sarki shardas tare da sauran fadawansa sai suka rinka kai sauran manyan baki izuwa mazaunin da ya dace dasu Kafin kowa ya zauna sauran talakawa sun iso a cikin kwale kwale dakaru na shigowa dasu suma ana zaunar dasu a inda ya dace duk a cikin wannan babban falo sai da kowa ya gama zama sannan sarki shardas ya mike tsaye yayi jawabin farinciki na ganin wannan rana gami da godiya ga dukkanin manyan baki da suka amsa gayyata sannan yace yaku jama ata ina mai sanar daku cewa inda zan jagoranceku mu zagaya cikin wannan gida domin muga ko ina da ina kuma muga duk irin daular da aka shirya a cikinsa da sai mun shafe a kalla tsawon kwaanaki bakwai bamu gama shiga kowanne daki da kowacce fada ba A cikin wannan gida na darul daulat akawai dakuna guda casa'in da tara sannan akwai fadoji guda arba in kowacce fada guda ta ninka fadata sau talatin a girma, akwai kasuwa da asibiti a cikin wannan gida kuma akwai gidajen gona guda arba in da bakwai Sannan lambu na shakatawa kala tamanin da bakwai Al amin Ahmed Misau , duk wanda ya lashe wannan gasa ya mallaki wannan gida to a ranar da ya tare a cikinsa ne hadiman Aljanu dubu dari tara da casa in da tara zasu fara kular masa da gidan, sauran hadimai na aljanu kuwa ya nemo iya adadin da yake bukata Yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zamu fara wannan gasa kuma ta kaina za a fara don haka ni na bude wannan ciniki da dinare miliyan uku ga kudina lakadan yanzu zan dankasu a hannun alkalan Kasa !!? Sarki shardas na gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa nan take hadimai sukaje can wajen kofar gidan suka fara dauko buhunhunan dinare daga kan dawakai da rakuma na sarki shardas suna shigowa dasu suna zubesu a tsakiyar wannan babban falo har sai da suka ajiye jaka talatin wato kowacce jaka na daure da dinare dubu dari koda ganin wannan al amari sai sarakai da attajirai suka kama yin murmushi saboda sun raina kudin da sarki shardas ya fara bude wannan gasa dasu duk kuwa da cewa kudade ne masu yawan gaske sun ishi talaka iya rayuwarsa koda sarki shardas yaga yadda sarakai da attajirai keyin murmushin murna don ganin suna da ninkin kudin da aka fara gasar dasu sau da yawa sai yayi dariyar mugunta a cikin ransa yace a zuciyarsa Uhm ! Ai sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo muje zuwa wai mahaukaci yahau kura, tsawon yan dakiku sai falon yayi tsit ba a sami wanda ya sake taya gidan ba har sai da sarki shardas ya sake budar baki yace, wai shin babu yan kasuwa ne a wannan waje ? Koda jin wannan tambaya sai sarkin birnin misra yace ya ninka wannan kudin da sarki shardas ya siyi gidan sun koma dinare miliyn dubu shida take aka kawo kudin aka zube a gaban jama a daga nan ne fa kowa ya sami bakin magana sai da sarakai da attajirai dari uku suka ninka kudin kuma aka kawo kudaden aka zube a tsakiyar fadar ya zamana cewa yan gasar mutum dubu uku da doriya gaba dayansu kowa ya zuba kudinsa saura mutum daya ne jal bai sa ba ba wani bane fwannan mutum guda da ya rage ba face ATTAJIRI AMSAR IBN WARHAS wanda har izuwa wannan lokaci ba a daina kawo rakuma da dawakan dake dauke da dukiyarsa izuwa bakin kofar wannan gida na darul daulat ba Kaji Manya Hm dama ance ta safe ta yara ce Ai Al amin amma kowa an gama kawo tasa dukiyar sai ta sarki shardas take ta bayan tasa, kafin a gama shigo da dukiyar wacce ta ninka duk ta sauran attajiran gasar dare ya raba a sannan ne fa gaba dayan sarakunan da attajiran suka tsorata ainun da al amarin Attajiri amsar suka fara tunanin cewa Aljanu ne ke sato dukiya daga bangarorin duniya suna kawo masa, haka kuma a sannan ne suka tsinke da al amarin sarki shardas ma domin har a sannan shima ba a gama shigowa da dukiyar daya tana da ba don wannan gasa koda sarki shardas ya fahimci cewa dare ya raba kuma kowa ya gaji ana jin yunwa da barci sai ya mike tsaye yace to a halin yanzu dai babu wanda yafi attajiri amsar farashi na wannan gasa, kuma tunda jama asun gaji kuma gashi dare ya raba to za a tsayar da wannan gasa domin akai kowa masaukinsa yaci abinci ya kwanta yayi barci sai gobe da safe a cigaba da wannan gasa A zagaye na biyu Koda gama fadin hakan sai fadawan sarki shardas suka yiwa manyan baki jagora aka kai kowa masaukinsa duk wanda ya shiga falonsa sai dai ya iske abinci da abin sha a shirye yana jiransa na kasaita kuma kala kala wani kalar abincin ma mutum bai taba ganin irinsa ba da idanunsa Al amarin daya bai wa kowa mamaki kenan kuma ko ya kwayar abinci daya ta dira a kasa sai dai aga ta bace bat Don kada a sawa wajen datti kai da gani ka san cewa wannan aiki ne na mutanen boye, bayan sarakuna da attajirai sun ci sun sha sai kowa ya zauna tare da jama arsa aka shiga tsegumi ana tattaunawa akan gasar inda kowacce jama a ke baiwa shugabanta shawara akan cewa kada ya kara zuba kudinsa a cikin wannan kasa tunda Al amarin ya shallake tunanin mutum Duk sarkin da ya ce zai fara zuba kudi ko attajiri to lallai karayar arzikinsa tazo, nan take kowanne sarki ya gama yanke hukunci a ransa cewa sai dai ya zama dan kallo a wannan gasa yabar wa manyan giwaye biyu dama kuma kudin da ya zuba a yanzu ya bar su a matsayin asara da kaddara Al amin Ahmed Misau, Kashi gari kuwa da sassafe aka sake haduwa a wannan babban falo na cikin wannan gidan darul daulat sauran jama ar gari ma yan kallo duk a wajen kofar gidan suka kafa tantuna suka kwana don kada wannan gagarumar gasa ta wuce su bayan dakin gasar ya gama cika ga tarin jakunkunan dinare jibge a tsakiya sai gaba dayan sarakunan da attajiran gasar suka sanar da alkalan gasar cewa su sun janye sun barwa sarki shardas da attajiri amsar sun sallama cewar ba zasu iya ba koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe da dariyar mugunta gami da farinciki saboda ganin cewa gaba dayan wadannan makudan kudaden da yan gasar suka zuba sun yi asararsu kuma shine zai mallake su a banza. Sannan kuma har a can karkashin zuciyarsa yana ganin cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya yarda da dukkan shirin da yai akan gasar da kuma tanadin da yayi na tsawon shekaru goma sha, ba tare da wata fargaba ba sai sarki shardas ya dubi Alkalan gasar cikin takama da jin izza yace na linka kudin da attajiri amsar ya siyi wannan gida a yau koda jin wannan batu sai falon ya rude da shewar jama a aka shiga yiwa sarki shardas kirari ana kodashi, saboda ana ganin cewa ya gama lashe wannan gasa domin attajiri Amsar ba zai iya linka wannan kudin ba nan take aka fara shigo da kudin da sarki shardas ya siyi wannan gida adadin ninkin wadanda ke zube a wajen saboda yawan wadannan kudade sai da aka yini ana shigo dasu sannan aka kammala duk yawan dabbobin da suka dauko kudaden na sarki shardas sai da kaso daya da rabin dukiyar cikin uku ya kare Shi kansa attajiri amsar yayi mamakin yadda akayi sarki shardas yayi wannan kundunbala shi kuwa sarki shardas sai ya kamu da tsananin farinciki ya rinka washe baki saboda gani yake kamar attajiri amsar ba zai iya sake ninka wadannan kudade ba sai dai ya hakura da gasar tsawon dakiku alkalan gasa suna tambayar attajiri amsar shin zai iya ninka wadannan kudade ko kuwa ya sallama amma sai yai shiru ya kasa cewa komai saboda jinjina wautar sarki shardas yake yi a cikin ransa har alkalan gasar sun mike tsaye zasu fadi jawabin cewa gida ya zama na sarki shardas sai attajiri amsar ya tari numfashinsu yace na sake ninka wannan kudi wanda sarki shardas ya siyi wannan gida Koda jin haka sai gaba dayan jama ar da ke wajan suka kame kAm ! Inji Gwanja Haha Al amin Ahmed Misau Nake Kamar Gumaka kowa ya wangame baki tamkar matattun kadoji a wajen saboda tsananin mamakin kasassabar da attajiri amsar yayi, nan take kuwa aka fara shigowa da jakunkunan kudin har sai da aka gaji , lissafi ya kwace musu a lokacin da zakara ya fara carah sakamakon wanzuwar asubahi Duk da haka a kofar wannan gida na darul daulat dawakai da rakuman dake dauke da jakunkunan dukiyar Attajiri Amsar sai ketaro kogin ake yi dasu bisa dole alkalan gasar suka dakatar da gasar domin kowa yaje ya kwanta yayi barci nan fa jama a suka watse kowa ya tafi yana fadin albarkacin bakinsa wasu suka rinka cewa ' duk yadda akayi wannan dukiya ta attajiri amsar dukiya ce ta iska kawai wato aljanu ne ke kawo kudin Wasu kuma suka rinka cewa ' to ai shima sarki shardas din ai tasa dukiyar ta iska ce tunda ba a gama kureshi ba nan fa jama a suka yi ta dokin ganin

Chapter 17 of 21