Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai zare takobina na dubi sarki nace yakai abbana kayi sani cewa idan muka bi wannan sharadi na sarki tamkar mun zamo bayin sane domin zamu rike masa saniyar tatsa ne ya rinka tatsar nononta AA Misau Sunana zamu zamo bamu da wani sirri na kanmu a cikin kasarmu kuma tattalin arzikin mu zai raunana mutanenmu zasu iya fuskantar fatara da talauci kafin na gama rufe bakina tuni sarki ya daka min tsawa yana mai tarar numfashina ya ce, idan muka ki bin umarnin sarki shardas sai ya kashe kowa a kasar nan ya mallake komai namu idan mukace zamu yakeshi komai yawan nan namu sai ya karar damu saboda yana kan sharafinsa abin da boka zamaranu ya gaya mini kenan A matsayinka na dana kuma yarima mai jiran gado ya kamata ka zamo mai kishin kasarka da jama arka, abinda sarki shardas ke bukata kawai shine na kaskanta kaina a gareshi kuma mu bashi dukiya kada ka dubi matsayina da kimata a wannan nahiya, zan iya sallama rayuwata ma gaba daya don kare jama ata da kasata dukiya kuwa shirme ce idan ka rasata zaka iya samun wata, ina mai dada ja maka kunne babu batun yaki tsakaninmu da sarki shardas kuma kada ka kuskura ka yi wani abu wanda zai jefa kasarmu ko jama armu cikin hadari ina mai umartarka da ma za kaje kasa a shirya mana tafiya gobe gobe zamu durfafi birnin sarki shardas don amsa kiransa, kuma dakarun da zasu yi mana rakiya kada su wuce su dari biyu don samun kariyar hanya daga sharrin yan fashi da dabbobin daji, koda gama fadin hakan sai sarki ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin gidan sarautarsa, ni kuwa sai bakin ciki ya lullube ni na sunkui da kaina kasa a lokacin da idanuna suka ciko da kwallar takaici a wannan lokaci ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa aka barni ni kadai a zaune babban abin da ya kona zuciyata shine idan na tuna cewa mahaifina zaije gaban sarki shardas ya durkusa masa alhali a nahiyar mu gaba daya babu wata masarauta mai tsohon tarihi da daukaka sama da tamu AA Misau Ke Magana, idan har sarki ya durkusawa sarki shardas shikenan darajarsa da kwarjininsa a idanun jama a sun zube har abada kuma ba za su kara dawowa ba ina zaune cikin wannan halina bakin ciki dana yarima huzein ya zo gareni ya dafa kafadata koda na dago kai nayi arba dashi sai naga shima yana zubar da hawaye, cikin sanyin murya huzein ya dubeni yace yakai abbana ka zamo mai hakuri da juriya bisa wannan kaddara data same mu ina so ka sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado don haka komai dadewa akwai ranar da sarki shardas zai fadi duk wulakancin da zamu fuskanta daga gareshi yanzu yana da iyaka wataran sai labari, ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya kuntata mana a yanzu da zamaninka to nan gaba namu zamanin sai komai ya sauya sa adda huzein yazo nan a zancensa sai na cika da mamaki bisa dalilin yin wannan jawabi tamkar wanda ya jiyo wani abu daga wajen bokaye nan take na rungume huzein iana kuka nace yakai dana zan kasance mai fatan ganin ranar da sarki shardas zai fadi kafin mutuwata koda jin wannan batu sai huzein ya janye jikinsa daga cikin nawa ya dubeni cikin murna da murmushi yace yakai abbana ina neman alfarma guda daya a wajenka cikin mamaki na dubeshi nace yakai dana kai kuwa wacce irin alfarma kake nema a wajena ? Huzein yace ina son kuyi wannan tafiya tare dani gobe zuwa birnin sarki shardas koda jin haka sai idanuna suka zazzaro na dubeshi cikin alamun damuwa nace haba yakai dana ka tuna cewa idan sarki baya nan nima bana nan kuma babu kai babu wanda zai gajemu kenan koda tsautsayi yasa mun hallaka wannan tafiya da zamuyi mai hadari ce komai zai iya faruwa a garemu ko akan hanya ko kuma a can birnin sarki shardas, bugu da kari a halin yanzu mahaifiyarka na dauke da tsohon juna biyu haihuwarta yau ko gobe idan babu ni babu kai a kusa da ita wa zata kalla taji dadi? AA Misau Ke Magana sa adda yarima huzin yaji wannan batu nawa sai jikinsa yayi sanyi amma duk da haka sai yaci gaba da rokona akan na Rarrashi sarki ya amince ayi wannan tafiya tare dashi, muna cikin wannan hali ne muka ji takun sawu a bayanmu cikin sauri muka waiga mukayi arba dashi, ba wani bane face mahaifina fuskarsa cike da annuri kawai sai ya karaso garemu ya zauna a tsakiyarmu sarki ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yayi murmushi yace naji duk abinda kuka tattauna, kuma na amince zamu tafi tare dakai gobe koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima huzein ya rungume sarki yana mai sumbatar goshinsa kawai sai sarki ya janye jikinsa daga cikin na huzein ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace yakai jikana kayi sani cewa na amince muyi wannan tafiya tare dakai ne saboda dalili daya rak dalilin kuwa shine nima sa adda na taso a wannan gidan sarauta daga san da aka haifeni zuwa lokacin dana kai shekarunka wato shekaru bakwai a duniya sau daya rak aka taba barina na fita wajen birnin na, bai kamata ace yarima guda wanda zai mulki al umma da yawa ba ya kasance kifin rijiya yana da kyau ka shiga duniya kaga yadda talakawa ke rayuwa kuma kayi gwagwarmaya kasha wahala sosai domin ka san menene rayuwa amma ka sani cewa akwai sharadi guda uku a kanka daga ranar da muka fita daga cikin garin nan, sharadina farko shine ba ka da ikon zuwa ko ina walau a cikin daji ko a cikin gari face da izinina ko na mahaifina sharadi na biyu shine duk abinda zakayi saika shawarcemu sharadi na uku kuwa shine ba zaka ci ko ka sha wani abu ba face wanda muka baka da hannunmu, shin ka amince da wannan sharadai guda uku dajin wannan tambaya sai yarima huzein yayi murmushi kuma ya zube kasa a gaban sarki ya kama godiya cikin farin ciki tare da tabbatar da amincewarsa ga wadannan sharudda Kashe gari kuwa da sassafe aka yi shirin tafiya dakaru dari biyu ne suka yi mana rakiya dauke da isashshen guzuri sai kuma kuyangi goma wadanda za su rinka yi mana hidima tsakanin yan fashi da mugayen dabbobin daji sai da mukayi karo da rukuni rukuni har guda bakwai kafin mu isa birnin sarki shardas amma sai da muka tarwatsa su muka kashe na kashewa masu gudu suka tsere dakaru guda arba in kacal muka rasa a cikin wannan gumurzu AA Misau Ke Magana, da la asar sakaliya muka iso birnin sarki shardas koda muka tsaya a bakin kofar gidan sarautar akaje akayi mana iso sai sarki shardas yaki fitowa saboda jin izzarsa da takamarsa kawai sai ya turo wani hadiminsa aka kaimu masauki bayan mun zauna munci abinci muna hutawa sai tunanin gida ya fado min inda na tuno lokacin da muke yin bankwana da matata luzuraina wacce ke dauke da tsohon juna biyu hm Kunya AA Misau, sa dda ta rungumeni mu biyu ni da yarima huzein ta fashe da kuka tana mai cewa yakai mijina kayi sani cewa bana son wannan tafiya da zakuyi domin ina bukatarku a kusa dani a yanzu fiye da ko yaushe ba don komai ba sai don saboda ita haihuwa bata da tabbas zan iya rasa rayuwata a wannan tafarki ko kuma na rasa abinda na ke dauke dashi haka zan iya rasaku tunda kuma tafiya zakuyi mai hadari tun a jiya da sarki ya shirya wannan tafiya sai naji zuciyata ta kama bugawa yadda naga rana haka naga dare ina mai tabbatar muku da cewa ba zan taba samun sukuni da kwanciyar hankali ba face naga dawowarku lafiya, koda luzuraina ta zo nan a zancenta sai ni da huzein muka kamu da tsananin tausayinta muka kara kankameta a jikinmu mukaci gaba da kuka kamar ba zamu daina ba, daga can sai na janye jikina daga cikin nasu na dubi luzuraina cikin nutsuwa da murmushin karfin hali nace yake matata kiyi sani cewa bana son nayi wannan tafiya saboda rashin sanin halin da zaki iya shiga amma kuma idan har na bar sarki yayi wannan tafiya shi kadai zan shiga cikin tashin hankali da wasi wasi akan halin da shima zai iya shiga don haka dole ne na bishi ko don na bashi kariya ina son ki kwantar da hankalinki ki sani cewa nayi miki alkawari duk wuya duk tsananin sai na dawo gareki a raye kuma na dawo miki da yarima huzein cikin koshin lafiya gama fadin hakan keda wuya sai ga babban hadimina ya shigo cikin falon nawa ya risina gareni yace ya shugabana sarki ya fto ku kadai ake jira koda jin haka sai ni da yarima huzein muka mike tsaye da sauri muka nufi kofar fita, a guje luzuraina ta sha gabanmu tana kuka ta sake rungumemu sannan ta janye jikinta ta dubeni tace idan na haihu baka nan wanne suna za a sakawa abinda na haifa ka sani cewa yarima huzein zai samu kani koda jin wannan batu sai mamaki ya kamani na dubeta nace yaya aka yi kika san cewa da namiji zaki haifa luzuraina ta ce sau uku ina yin mafarkin na haifi da namiji don haka ina ji a jikina cewar lallai da namiji zan haifa sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi sannan na dubi yarima huzein na ce na baka dama ka zabi sunan da za a sawa kaninka yayin da yazo duniya cikin murna yarima huzein ya daga kansa sama yayi dan tunani sannan ya dubi mahaifiyata yace ki sawa kanina suna YARIMA BASMAR, kuma kiyi masa bushara da cewa ya jira yayansa yazo suyi was Lallai nine zan koya masa yadda ake sarrafa doki da takobi koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa luzuraina ta sake rungume yarima huzein tana mai sake fashewa da wani sabon kukan A dai dai wannan lokaci ne muka jiyo muryar sarki yana mai kwala mana kira cikin hanzari na fisge yarima huzein daga cikin luzuraina na ja shi da gudu muka fice daga cikin falon huzein na waigen mahaifiyasa yana hawaye itama tana kuka lokacin da na zo dai dai nan a tunanina sai yarima huzein ya dafa kafadata na dawo cikin hayyacina yarima huzein ya dubeni cikin alamun damuwa yace yakai abbana anya kuwa babu wani mugun nufi a zuciyar sarki shardas a kanmu ? Yakamata ace ya fito ya tarbemu a bisa irin matsayin mahaifinka da daukakarsa a wannan nahiya amma kuma sai kawai ya aiko da hadimi aka taho damu nan masauki sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace kada ka damu ya kai dana duk wannan ba komai bane, babu wani mugun abu da sarki shardas zai yi mana, kawai dai wulakanci ne irin nasa da son nuna isa, A A Misau Ke Magana, koma menene ai da zarar mun isa gabansa za a yita ta kare yaz sallame mu mu koma izuwa kasarmu burina kawai shine mu koma gida mu iske mahaifiyarka ta haihu lafiya kafin na rufe bakina saiga sarki ya shigo cikin dakin namu kuyanginsa guda hudu na biye dashi dauke da abinci cikin hanzari muka zube kasa muka kwashi gaisuwa su kuwa wadannan kuyangi sai suka ajiye wannan abincin da abinshan a gabanmu suka juya da baya suka fice sarki ya zauna a gabanmu ya dubemu cikin annashuwa yace na kasa cin abincina shi yasa na yanke shawarar na zo har nan dominku muci tare koda jin wannan batu sai mamaki ya kamamu na dubi sarki nace yakai abbana kai kuwa menene dalilin daya hanaka cin abinci ? Sarki ya yi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kasa sannan yace tun da muka shigo cikin garin na naji zuciyata tana bugawa abu ne mawuyaci mu bar garin nan lafiya cikin farin ciki musamman idan muka yi duba da irin karbar da sarki shardas mana ta wulakanci da rashin nuna muhimmancina a gareshi ya yinda sarki yazo nan a zancensa sai nayi dariya nace haba yakai abbana akan wane dalili zakayi irin wannan tunanin alhali mun kasance masu biyayya ga sarki shardas gami da bin umarninsa, ni na san cewa babu wani tsautsayi da zai same mu lafiya kalau zamu koma gida kawai mu jira muga yadda zata kasance tsakaninmu da sarki shardas koda jin wannan batu sai sarki ya saki ransa hankalinsa ya kwanta nan take muka kama cin abinci cikin raha da nishadi muna ta hira da ban dariya har sai da muka koshi...... Wow littafi fa yanzu ya fara tafiya domin yanzu ne zaku san an fara karanta TSATSUBA zakuji yadda zata kaya tsakaninsu da yadda Ake tsantsan yaudara da cin amana gami da rashin imani Kafinnan dai Nidinne Al amin Ahmed Misau AA Misau Ke Magana Admin Na Zauran Labarai Page. Ke cewa Ku huta Lafiya...SATSUBA Littafi Na Shida (6) Part C. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . NAN TAKE MUKA KAMA CIN ABINCI CIKIN RAHA DA NISHADI MUNA TA HIRA DA BAN DARIYA HAR SAI DA MUKA KOSHI, A wannan rana sarki bai koma dakinsa ba anan dakinmu ya kwana saboda ko kadan baya son nisanta damu sai da muka kwana uku a cikin gidan sarautar sarki shardas amma wai har tsawon wadannan kwanaki sarki shardas bai kirawo mu ba duk da cewa kullum yana zama a fada, duk sa adda ya bukaci ya gana da shi sai yace a gaya masa cewa ya kara sauraro KAJI MANYA MASU JI DA KAI SARKI SHARDAS KENAN HM a ranar kwana na ukun ne da safe bayan mun gama kalaci sai ga hadimin sarki shardas yazo mana take hadimin ya shaidawa mahaifina cewar sarki yace muje mu riskeshi a fada cikin farinciki muka mike tsaye muka yi shiri sarki ya taramu gaba dayanmu dakarunsa da kuyanginsa sannan aka debo wadannan bayi guda dubu ashirin gami da akwatunan dukiya guda dubu muka wuce izuwa fadar sarki shardas fadar ta cika makil ta batse da mutane ko ina ka duba saikaga fadawa dakaru da manyan attajirai da sauran masu fada aji a kasar A gefe daya kuma mutanen gari ne maza da mata a durkushe a kas babu wani mutum guda daya a tsaye ko akan kujera face sarki shardas wanda ke kan karagarsa ta mulki, koda muka shigo cikin fadar mahaifina na kan gaba muna biye dashi gaba dayanmu sai naga an zubawa mahaifina idanu kawai mutane so suke su gani shin zai iya durkusawa a gaban sarki shardas ya kaskantar da kansa? Babu abin takaici sama da ganin yadda mahaifina yayi gagarumar shiga ta alfarma mai tsananin tsada wacce ta ninka ta jikin sarki shardas sau uku amma kuma gashi zai kaskanta a gaban dubunnan talakawa a wannan lokaci ina rike da hannun yarima huzein muma munci ado na kwatance domin ko a cikin fadawan sarki shardas da duk jama arsa babu wanda ya sa suturar data kai tamu daraja ni da huzein ke bin bayan sarki sai kuma kuyangi da sauran dakarun da muka taho dasu daga birninmu don yi mana rakiya lokacin da ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin mahaifina da karagar mulkin da sarki shardas ke zaune a kai sai yaja da baya cak muma da muke bayansa sai dukkanmu muka ja muka tsaya cak a bayansa nan take mahaifina da sarki shardas suka fara kallon kallo fuskar sarki shardas a murtuke take ko kadan babu annuri kuma jikinsa ya kama tsuma har fuskar tasa na yin gatsine saboda fishi bisa tunanin cewa ko mahaifina ba zai durkusa masa ba kawai sai akaga mahaifina ya durkushe kasa bisa guiwarsa guda ya risina yana mai dukar da kansa ga sarki shardas cikin murya mai dauke da ladabi yace gaisuwa gareka ya shubana a madadina da al umar kasata nazo domin mu jaddaja mubaya armu a gareka ya sarkin duniya kuma na amsa kiranka, gani nazo da duk abinda ka bukata koda mahaifina yazo nan a zancensa sai fuskar sarki shardas ta fadada da murmushi ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar murna sannan ya tako yazo har inda mahaifina ke durkushe ya kama kafaduna ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna yace lale marhaban da sarki mai birnin Askandariyya lallai ka tsira daga dukkan fishinmu kuma daga yau ka zama amintaccenmu nan take fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki shardas jinjina da kirari bisa ganin yadda sarki mai daraja da cikakken iko kamar mahaifina ya mika wuya a gareshi a wannan lokaci takaicida bakinciki suka lullubeni har idanuna suka ciko da kwallah ban sani ba A A Misau Sunana , sarki shardas ya daga hannu sama sai fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta , A sannan ne sarki shardas ya bushe da dariyar farinciki ya kirawo wani hadimi nasa mai dauke da tambulan na ruwan giya gami da kofi guda biyu da zuwan hadimin sai sarki shardas ya dauki kofi guda hadimin ya tsiyaya masa ruwan giyar sannan ya dubi mahaifina yayi masa tayi, batare da fargabar komai ba mahaifina ya dauki daya kofin shima aka tsiyaya masa ruwan giyar amma sai yaki yasha koda ganin haka sai sarki shardas ya bushe da dariya sannan ya kurbi ruwan giyar har sau biyu ya dubi mahaifina yace kwantar da hankalinka abokina ai ba zan shayar dakai guba ba, saboda me kake tsoron shan wannan giya mai albarka wacce nasa aka yi ta musamma don tarbarka? Koda jin wannan batu sai mahaifina yayi murmushi yace ai ba komai bane yasa naki sha ba sai don yin ladabi a gareka kada na rigaka dandana dadinta dajin haka sai sarki shardas ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya kamo kafadar mahaifina ya juyo dashi suka fuskancemu sarki shardas ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yace wannan danka ne yarima hulbasu mai jiran gado tare da dansa yarima huzein ko ? Mahaifina ya gyada kai yace kwarai kuwa sune sannan ya dubemu yace kuyi gaisuwa ga sarkin duniya AA Misau Sunana, da farko sai na dan noke a lokacin da huzein tuni ya duka kasa ai kuwa sai nan da nan fuskar sarki shardas ta juye izuwa fishi har sai da nima na durkusa na gaisheshi sannan yayi murmushi yazo ya dafani ta yadda har muna iya jin numfashin juna ya budi baki cikin karamar murya yadda babu mai iya jinmu ba sannan yace, Samari nasan abinda kake ji a ranka bisa kaskantar da kan da mahaifinka yayi a gareni domin jaddada min mubaya arsa amma ina mai shawartarka da ka zamo mai biyayya idan har baka son daular birnin Askandariyya ta fadi, yana gama fadin hakan sai ya wuce gabana ya shiga duba bayin da aka kawo masa guda dubu ashirin har sai da ya tabbatar da cewa gaba dayansu lafiyayyune sannan yaje kan akwatunan dukiya guda dubu sai da aka bude gaba dayan akwatunan yaga dukiyar dake cikinta nan take sarki shardas ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dawo wajen mahaifina ya kama hannunsa ya jashi har zuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare a wannan lokaci fadar tayi tsit ko tsinke ne ya fadi kasa sai an ji kararsa sarki shardas ya dubi mahaifina cikin nutsuwa ya ce ya batun sharadin da muka gindaya maka a cikin wasikarmu? Shin ka amince zaka yi abinda muke so ko kuwa ba zaka bi ba ? Sa adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya risina cikin biyayya yace ya sarkin duniya na amince da duk bukatarka amma ina neman wata alfarma guda daya, alfarmar kuwa itace ina son ka rage yawan bayin da zan rinka kawo maka duk shekara da kuma yawan akwatunan dukiya su koma rabin wadanda na kawo maka yanzu ba don komai ba sai saboda hakan zai iya kawo karyewar tattalin arzikin kasata domin a halin yanzu bayi sunyi karanci a kasata kuma bayin nan sune suke yi mana aikin noma a gonakinmu noman kuma shine yake kawo mana dukiyar da zamu tara mu kawo maka koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata ya dakawa mahaifina tsawa yace babu ruwanmu da wannan matsala domin kai ta shafa bamu ba don haka sai ka san hanyar da zaka bi ka nemi bayi koda kuwa sai kayi farautarsu ne a sauran kasashen da ke kusa daku ka sani cewa gobe goben nan zan hadaka da wakilina mutum uku wadanda zaka tafi dasu izuwa fadarka a dinga gabatar da harkokin mulki tare da su domin su rinka kawo mini rahoton duk abubuwan dake gudana, a karshe ina mai gargadinka da cewa digon jini daya na wadannan wakilai nawa dai dai yake da digon jinin saba in na jama arka don haka a kula da su da kyau kuma a basu duk abinda suke bukata sa adda sarki shardas yazo nan a zancensa sai nayi wuf na matso gaba kusa da karagar mulkin sa na dubeshi nace yakai wannan sarki ka yi sani cewa idan ka hadamu da wadannan wakilai naka tamkar ka rushe karfin mulkin mahaifina ne gaba daya tunda ba shi da ikon yin wani sirri a cikin harkokinsa na mulki kuma ba shi da ikon zartar da komai sai da saninka da amincewarka ni ina ganin A A Misau Ke magana, wannan ba adalci bane zalunci ne da kaskantarwa....... Kafin na gama wannan jawabi tuni jikin sarki shardas ya kama tsuma saboda fishi har gumi ya fara tsatstsafowa daga fuskarsa shi kuwa mahaifina a wannan lokaci ya firhita ainun so yake ya hanani ci gaba da magana amma ya kasa, kawai sai sarki shardas ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya zo daf dani ya zare takobinsa ya dora kaifinta akan wuyana yana mai ci gaba da tsuma ni kuwa ko gezau ban yi ba A lokacin gaba dayan mutanen dake fadar sun firgita ainun kowa ka kalla sai kaga jikinsa na bari don gudun kada laifin wani ya shafeshi, sarki shardas ya daka min tsawa ya ce kai dan samari kaine mahaluki na farko wanda ya taba shigowa har cikin fadata yayi mini bakar, don haka yanzu zan kasheka domin na gusar da kishirwar karya wannan lago nawa da kayi, koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daga takobinsa sama da nufin ya sareni amma sai mahaifina yayi wuf ya janyeni daga gabansa sannan yayi sujjada a gareshi ya dago kai yace ya sarkin duniya ina nemawa dana afuwa ka san cewa har yanzu akwai kuriciya a tare da shi koda jin wannan batu sai sarki shardas ya sake bushewa da dariyar mugunta sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dafa kafadata yace samari ka tsira daga kaifin takobina yau, amma ka sani cewa idan ka sake aikata kuskure irin wannan ba zaka taba tsira ba yana gama fadin hakan sai ya juya ya fuskanci fadawansa ya kirawo wadansu mutane uku daga cikin dan uwansa wanda ake kira MUHAIRU wanda ya kasance dan yayarsa sarki shardas ya dubi muhairu ya ce yakai dan uwana daga yau na cireka daga matsayin gwamnan birnin DAILUFA a yanzu kaine shugaban wakilaina na birnin Askandariyya saboda haka kaje ka fara shirin binsu gobe amma kafin goben ina so ka zauna da yarima hulbasu ya sanar dakai iya adadin biranensu da kauyukansu da kuma duk harajin da suke tarawa a kowacce shekara ka rubuta komai ka kawo min muhairu ya risina yace an gama ya shugabana kawai sai sarki shardas ya juya ya fice daga fadar ya wuce izuwa cikin gidan sarautarsa, shi kuwa muhairu sai ya zo gabana ya tsaya yana mana wani irin murmushi na mugunta da raini ya dubeni yace ka saurari zuwana nan da lokaci kankani yana gama fadin hakan sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya wuce abunsa sauran wakilai guda biyu na take masa baya suma suna kyalkyala mana dariya Nan take dakarun sarki shardas suka ingiza keyar bayin da muka kawo guda dubu ashirin aka wuce dasu izuwa can wani bangare na gidan sarautar sarki shardas, kuma aka kwashe Wadannan akwatunan dukiyar da muka kawo , A sannan ne fadar ta watse ya zamana cewa daga mu sai jama armu kacal a tsaye cikin tsananin bakin ciki da takaici A dai dai wannan lokaci ne zuciyata ta kama tafarfasa kamar zata kone ban san sa adda na kurma uban ihu ba mai tsananin firgitarwa na durkushe kasa ina mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki Al amarin daya janyo hankalin dakarun sarki shardas kenan suka zare takubba suka rugo izuwa kanmu, koda suka ganni durkushe a kasa ina kuka sai suka kama dariya suka tafi suka barni a wannan lokaci ne mahaifina da yarima huzein suka durkusa a gabana sa adda suma suka fara zubar da hawayen bakinciki kawai sai sarki ya rungumeni tare da fashewa da kuka sosai mu duka sai muka kama kukan, sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan muka mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu....... . Wow Zan dakata A wannan guri saikuma Allah ya kaimu Gobe zan cigaba daga nan Amma kafinnan Nidinne Dai Al amin Ahmed Misau AA Misau Ke Magana Admin Na zauran labarai page. April 1SATSUBA Littafi Na Shida (6) Part D. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . SAI DA MUKA DAN JIMA ZAUNE A CIKIN FADAR MUNA KUKA SANNAN MUKA MIKE TSAYE MUKA TAFI IZUWA MASAUKINMU.... Bayan mun isa masaukinmu mun zauna cikin bakinciki muna tunanin wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki na takaici da wulakanci, sai sarki ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo masa yace yakai dana ka yi sani cewa wadannan sharadai da sarki ya gindaya mana sai sun janyo fari da talauci a kasarmu kuma wannan shine lokacin da na dade ina tsoron gani a rayuwata fadin hakan keda wuya sai sarki ya fara wani irin tari mai karfi kafin a jima kuwa sai ya kama aman jini cikin rudewa na kwallah ihu ina mai kiran likitan sarkiwanda muka taho tare dashi tun daga birninmu domin duba lafiyarmu, nan da nan wata kuyanga ta ruga taje ta kirawo likitan yazo ya shiga duba mahaifina dan ceto rayuwarsa da kyar likitan ya samu ya shawo kan cutar sarki ya tsayar da jinin dake zuba a bakinsa sannan kuma ya bashi magani ya sha faruwar hakan keda wuya cikin dakika kadan nannauyan barci mai karfi

Chapter 12 of 21