Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gari ya waye ayi zagayen karshe na wannan gagarumar gasa domin aga wanda zai yi nasara tsakanin sarki shardas da attajiri Amsar '' '' '' CIKIN farin ciki da kwanciyar hankali attajiri ansar ya je masaukinsa ya kwanta yana mai ayyana wa a ransa cewa lallai idan gari ya waye aka dawo zagayen karshe na wannan gasa shine zai yi nasara, koda ya kwanta akan luntsumemen gadon dakin fuskarsa cike da murmushi sai tunanin mahaifiyata ya fado masa ya tuna cewa yau fa kusan kwanaki biyar ke nan fa rabon da suga fuskokin junansu nan take yaji wani irin bakin ciki yayi katutu a cikin ransa amma daya tuna cewa yana daf da lashe wannan gasa sai zuciyarsa tayi fari fat kuma idanunsa suka fara kekashewa ya Fada cikin sabon kogin tunani inda ya rinka ganin su a cikin wannan gida na darul daulat wato shi da mahaifiyata suna ta kewayawa suna shiga daki daki da ko ina na cikin gidan yana nuna mata irin gagarumar daular da aka shirya a cikin gidan a haka ne barci ya sace shi bai sani ba -- -- -AL AMARIN sarki shardas kuwa tun da aka baro dakin gasa ko zama kasawa yayi bare ya kwanta yayi barcin kawai sai ya kama zarya a cikin dakin yana ta ciza yatsa da lebe yana tsaki gami da mamaki da takaici Zuciyarsa kuwa sai ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki ya fara tunanin cewa lallai a gobe idan gari ya waye watan jin kunyarsa zai tsaya muddin aka yi zagayen karshe na wannan gasa domin tun a daren jiyan ne dawakai da rakuman dake dauke da dukiyarsa suka daina ketaro kogin domin sun kare, amma na attajiri amsar cigaba suke da zuwa tamkar ba zasu kare ba tabbas idan ya ninka dukiyar da attajiri amsar ya sayi wannan gida abu ne ma wuyaci kudin nasa da suka rage sukai adadin hakan koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai ya zura hannu a cikin Aljihun Alkyabbar sa ya fiddo madubin tsafinsa ya shiga sabon bincike Yana cikin wannan bincike ne yaga bokansa ya baiyyana tsulumm a gabansa yana mai kyalkyala dariya Al amin Ahmed Misau, cikin fushi sarki shardas ya dubi bokan ya ce sabo da me tuntuni zaka tafi ka bar ni a cikin wannan zullumi da fargaba ko kuwa so kake daraja ta ta zube a idon duniya kuma arzikina ya karye ?? Koda jin wannan tambayoyi sai bokan ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya matso daf da sarki shardas yayi masa rada a kunne tun kafin gari ya waye gari yayi haske, falon gasa ya cika ya batse da jama akowa ya hallara a wajan babu wanda ake jira face mutum daya jal ba wani bane ba ake jira face sarki shardas da kanshi Al amarin da yabaiwa kowa mamaki kenan aka rasa dalilin da yasa ya makara Ashe sarki shardas kwanciya yayi yana ta shara barci abinsa shi kadai ne ya rama bashin barcinsa na jiya da daddare sai kuma attajiri amsar wanda barcin ya daukeshi yana tsakiyar tunanin mahaifiyata, har sai da hasken rana ya fito sosai sannan aka ji bugun tambura gami da bushin algaita alamar cewa ga sarki Shardas nan zai shigo falon gasar, nan fa dakin gasar ya kaure da shewar jama a gami da ihu da tafi jim kadan sai ga sarki shardas ya shigo cikin falon cikin ado na kwatance kuma fuskarsa cike da annuri dakarun dake bashi tsaro na take masa baya nan fa kowa ya mike tsaye don girmamashi har sai da ya je ya zauna a kusa da attajiri amsar sannan kowa dake falon ya zauna ba tare da bata lokaci ba mai gabatar da gasar ya fara jawabi yana mai cewa yaku jama akamr yadda kuka sani cewa ayau ne za ayi zagayen wannan gasa na karshe don haka yanzu zamu ji daga bakin sarkinmu mai daraja shin zai iya ninka kudin da attajiri amsar ya sayi wannan gida nasa, ance dai waka a bakin mai ita tafi dadi don haka mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade koda gama fadin hakan sai mai gabatar da jawabin ya koma mazauninsa take sarki shardas ya mike tsaye ya dubi gaba dayan taron jamar dake cikin falon cikin murmushi maimakon yace wani abu sai ya juya ya kama hannayen attajiri amsar ya tasheshi tsaye ya dubeshi cikin murmushi a lokacin da falon gasar yayi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa yace yakai abokina ina tayaka farinciki ka lashe wannan gagarumar gasa daga yau wannan gida na darul daulat ya zama naka kuma mallakinka koda jin wannan batu sai falon gasar ya rude da shewa da ihun jama a shi kuwa attajiri amsar sai ya rungume sarki shardas cikin tsananin farinciki mara misaltuwa yana mai yi masa godiya ba zato ba tsammani sai sarki shardas ya yi wuf ya fisge kwagirin dake hannun attajiri amsar sannan ya zato wata wukar tsafi daga cikin alkyabbarsa ya lumawa attajiri Amsar ita a ciki Nan take wukar tsafin ta lume a cikin attajiri amsar jini yai tsartuwa Attajiri Amsar ya kwallah kara tare da sulalewa kasa yana kakarin mutuwa, Al amarin da ya razana kowa ke nan a dakin gasar aka yi tsit ana kyarmar jiki saboda tsabar tsoro shi kuwa sarki shardas sai ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa yace maza ku ruga izuwa can bayan gari tafiyar kwana uku zaku riski matar attajiri amsar tare da dakarun dake tsaronta lallai ku kashe gaba dayan dakarun ita kuma matar tasa kuzo min da ita nan a raye koda jin wannan batu sai dubunnan dakarun suka ruga waje da gudu suka shiga cikin jiragen ruwa suka ketare kogin A wannan lokacin falon gasar yayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi a cikinsa, ba ma attajirai, bokaye da jarumai dake wajen ba hatta sarakunan jikinsu karkarwa yake yi sabo da tsananin tsoron sarki shardas !! Kai Nima Kaina Al amin Ahmed Misau, Saboda tsananin tsoro yasa nakasa ci gaba, SHIN ATTAJIRI AMSAR YANA MUTUWA SAKAMAKON SUKAN DA SARKI SHARDAS YAYI MASA?? . YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI GAMA LASHE JARRABAWAR DA ALJANI ARWASUL MASADUR YAKE MASA HAR YA TAIMAKA MASA YA MALLAKI HULAR LAMSARA ? . TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE YAKE MALLAKAR HULAR LAMSARA?? . SHIN YARIMA HULKAS YANA SAMUN NASARAR KASHE SARKI SHARDAS DA HANNUNSA KAMAR YADDA YA DAUKI ALKAWARI DUK DA CEWAA BAYA SHI YAKE DAUKA A MATSAYIN MAHAIFINSA KUMA AKWAI SOYAYYA DA SHAKUWA A TSAKANINSU ?? . Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Daddadan Labari Author Abdul Aziz sani Madakin Gini Typer Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson Ko A square A karshe nake cewa Ku meye ra ayinku dan gane da TSATSUBA Littafi Na Tara (9) Hausaebooks Made by Shuraih Usman Daga:-http://shuraih.waphall.com Part A . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Me Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . LOKACIN DA DAKARUN SARKI, shardas suka fice daga cikin falon gasar domin cika umarnin da yayi musu na zuwa bayan gari su dauko masa matar attajiri amsar bayan sun kashe dakarun dake tsaron lafiyarta. Kawai sai sarki shardas ya tsugunna a gaban attajiri amsar wanda har a sannan bai daina kakarin mutuwa ba ya tallafo keyarsa da hannu guda ya dubeshi yace ta yaya kake tsammanin cewa zan barka ka rayu alhalin kafi ni kudi kuma kana da kyakkyawar matar da bani da kamarta kuma kana da karfin sihirin tsafi na ban mamaki ta yaya zan barka ka lashe wannan gagarumar gasa ka barni da abin kunya ? To ka sani cewa komai sammakonka wani a tafe ya kwana, tun daga lokacin da akayi shelar wannan gasa nasa bokana ya shiga bincike akan sirrinka, don haka da gayya na gayyaceka izuwa wannan gasa domin naga bayanka sai a jiya ne bokan nawa ya gano cewa gaba daya tasirin sihirinka na tsafi yana jikin kwagirin da kake rikewa a hannunka in ba don na fisgeshi daga hannunka ba da ba zan taba iya kashe ka ba kaga kenan yanzu mutuwa zaka yi na gaje duk dukiyar nan da ka zo da ita kuma na gaji wannan kyakkyawar mata taka, Bani da wani buri a doron kasa wanda ya fi na ajiye tarihin da babu wani sarki ko wani boka ko jarumin da ya ajiyeshi, gama fadin hakan keda wuya sai attajiri amsar ya yunkura cikin karfin hali ya cakumi kwalar rigar sarki shardas ya budi baki da kyar cikin murmushin karfin hali yace tabbas ka sami nasarar hallakani to amma ka sani matata tana da kariyar dani kaina bani da ita don haka ina tabbatar maka da cewar har abada bazaka mallaketa ba sannan kuma matata tana dauke da juna biyu tsawon wata biyar duk abinda ta haifa namiji ko mace sune zasu dauki fansar raina a hannunka bakin azzalumi Koda gama fadin hakan sai idanun Attajiri amsar suka kafe gaba dayan jikinsa ya sandare ya zama gawa koda ganin haka sai sarki shardas ya kurma uban ihu wanda ya razana kowa dake cikin dakin gasar kawai sai ya zare takobinsa ya dubi wazirinsa ya damka masa kubar gidan darul daulat yace kowa ya fita ka kullue mini gidana, yanzu zan tafi izuwa can bayan gari na gani ko dakaruna sun cika aikinsu yana gama fadin hakan ya juya ya cife daga cikin gidan da gudu ya shiga jirgin ruwa aka ketare kogin dashi yana isa bakin gabar kogin ya fito daga cikin jirgin ruwan ya sake hawa doki ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar bayan gari da karfin sihirin tsafi sarki shardas ya shafe tafiyar kwana uku a cikin yini guda kacal amma kuma yana isa inda su matar attajiri amsar suka yada sansani bai iske komai ba sai gawarwakin dakarunsa dana attajiri amsar gaba dayansu babu wanda ya tsira da rayuwarsa, ga keken dokin da matar attajiri amsar ke ciki amma babu ita babu alamarta Al amin Ahmed Misau, nan fa sarki shardas ya dimauce kuma ya haukace yayi ta neman mahaifiyata a cikin daji yana ihu yana kwallah mata kira amma shiru kamar maye yaci shirwa bisa dole ya hakura ya juya ya koma birninsa cikin tsananin bakin ciki da takaici lokacin da yarinya Rulaiya tazo dai dai nan a labarinda take baiwa yarima hulkas sai tayi shiru ga barin zancenta a lokacin da hawaye ya zubo mata, cikin kaduwa da zumudi yarima hulkas ya dubeta yace to daga nan kuma menene ya faru ga mahaifiyarki shin guduwa tayi sa adda dakarun sarki shardas suka kawo musu hari, koda jin wannan tambaya sai yarinya rulaiya tasa hannu ta share hawayanta sannan tace mahaifiyata ba gudu tayi ba ta bani labarin cewa agaban idanunka aka fafata KAZAMIN YAKI tsakanin dakarun sarki shardas dana mijinta masu tsaron lafiyarta kuma gaba dayansu sai suka yi RAGAS Faruwar hakan keda wuya sai taji jiri ya fara dibarta daga can kuma sai ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya lokacin da mahaifiyata ta farfado daga suman da tayi ne sai ta tsinci kanta a cikin wannan gida kwance a kas a gaban wani Aljani ma abocin kwarjini da ko a labari bata taba jin kamarsa ba Ba tare da aljanin ya gabatar da kansa a gareta ba ya dubeta a lokacin da gaba dayan jikinta yake karkarwa saboda firgita da ganinsa yace ki kwantar da hankalinki ya ke matar sarkin attajiran duniya kiyi sani cewa babu mai cutar dake anan iya tsawon rayuwarki, domin na daukarwa mijinki wannan alkawari Anan ne kadai zaki iya tsira daga sharrin abokan gabar mijinki irin sarki shardas Al amin Ahmed Misau, koda jin wannan batu sai zuciyar mahaifiyata ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayanta biyu sannan ta dubi aljanin tace ina labarin masoyina amsar shin an gama wannan ga sa ne ta siyan gidan darul daulat ? Maimakon aljanin ya bata amsar wannan tambaya sai yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton duk abinda ya faru a dakin gasar ya bayyana tun daga ranar farko har izuwa zagaye na karshen gasar koda mahaifiyata taga sarki shardas ya kashe mijinta sai ta kwalla uban ihu ta sake sulalewa kasa sumammiya wannan shine asalin sanadin da ya sa mahaifiyata ta kamu da cutar ciwon zuciya kuma ciwon ne ya zamo sanadin ajalinta bayan haihuwata da shekara shida Bayan mutuwarta ne wannan aljani ya cigaba da kula da Ni kuma ya zamana cewa kullum yana koya mini yaki yana mai cewa nan gaba zan dauki fansa akan makiyina sarki shardas da ya kashe min mahaifina amma ba yanzu ba sai idan lokacin yayi, lokacin da ban sani ba ke nan har kawo i yanzu gashi gaba dayan rayuwata ta kasance a cikin kadaici in ban da uwata da kuma wannan aljani da ya cigaba da kula dani kaine mahaluki na uku da na gani a gaba dayan fadin wannan duniyar, koda yarinya rulaiya tazo nan a labarinta sai ta fashe da matsanancin kuka Al amin Ahmed Misau, Al amarin da ya sa yarima hulkas yaji ya kamu da tsananin tausayinta kenan gami da matukar kaunarta fiye da ko yaushe, don haka bai san sa adda shima idanunsa suka kama zubar da hawaye ba, tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba daga can sai ya dubeta cikin nutsuwa yace yake rulaiya ai labarina da naki duk kusan iri daya ne kuma abokin gabarmu guda ne, nan take yarima hulkas ya zaiyane mata tun daga farko har karshe da yadda akayi ma ya tsinci kansa a wannan gida nata da kuma shirin da suke yi na tafiya neman hular lamsara don daukar fansa akan sarki shardas koda rulaiya taji wannan labari sai ta kamu da tsananin Al'ajabi sannan tayi shiru tana tunani da nazari daga can sai ta dago kai ta dubi yarima hulkas tace duk yadda akayi aljanin da ya ceci rayuwar mahaifiyata ya kawota nan kuma ya koya mini yaki shine ya daukoka ya kawoka nan lallai akwai wata manufa a cikin hadamu da yayi tunda duk burinmu iri guda ne, kash ! Zanso ace nima zanga yadda karshen gasar fadan yar uwarka jaruma siyama zai kasance da sadauki Darkus kuma zanso ace tare dani za ayi wannan gagarumar tafiya ta neman HULAR LAMSARA Kafin Rulaiya ta gama rufe bakinta sai kawai sukaga aljani Arwasul masadul ya bayyana tsuluum ! A gabansu yana mai kyalkyala dariyar farin ciki kawai sai ya dubesu duk su biyun cikin murmushi yace tabbas na gama cika aikina yanzu zan doraku akan tafarki na karshe wanda zaku dauki fansa kamar yadda na yiwa iyayenku alkawari daga nan zaku tafi izuwa can birnin sarki hulbasu tare kuma gobene za ayi wannan gasar ta karshe ke rulaiya ki boye fuskarki ga kowa kuma ki zamo mai taimakon su hulkas bisa duk abinda yazo musu zan baku wani tsuntsu wanda zai yi muku jagora izuwa inda hular lamsara take ku sani cewa yanzu haka makiyanku sarki shardas tare da bokansa basu da burin da yafi su hadu dani domin na sanar dasu inda hular lamsara take amma wannan damar tuni ta wucesu ina mai gargadinku da ku kula sosai da wannan tsuntsu da zan hadaku dashi domin ko yaya ku kayi sakaci ya subuce muku to fa zai koma hannun su sarki shardas ne ya kai su izuwa inda hular Lamsara take idan kuwa sarki shardas ya rigaku taba hular lamsara to dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba bare ma ya dauki fansa akansa koda gama fadin wannan jawabi sai Aljani Arwasul masadul ya bude tafin hannunsa ya lumshe idanunsa yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya ai ga wani farin tsuntsu dan karami wanda baifi girman kanari ba ya baiyana akan tafin hannun nasa gwanin ban sha awa, kawai sai ya mikawa yarima hulkas tsuntsun yace kaine ka cancanci rike wannan tsuntsu saboda kai kadai ne ka haye jarrabawata a duniya kai yakamata ka mallaki hular lamsara amma zanyi maka gargadi guda daya Gargadin kuwa shine duk abinda zaka so to ka soshi SAISA SAISA idan kuwa ka zurma a cikin soyayyarsa tabbas wannan abu shine Ajalinka, Hm Al amin Ahmed Misau Sunana, da wannan furuci nake yi muku bankwana na karshe har abada ba zamu sake haduwa daku ba ina mai yi muku fatan samun nasara akan babban makiyinku amma fa ku sani cewa aikin dake gabanku ya wuce yadda duk kuke zatonsa dole ne ku fuskanci BARAK WUYA da hadarurrukan da ba lallai ba ku kaiga gaci Aljani Arwasul Masadul na gama fadin hakan sai ya bace bat ! Tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin rudewa yarima hulkas ya dubi yarinya Rulaiya yace saboda me wannan aljani zai tafi ya barmu ba tare da ya gaya mana yadda zamu iya kai kanmu can birnin sarki hulbasu ba da kuma yadda yakamata mu tafiyar da komai a cikin wannan gagarumar tafiya dake gabanmu koda jin wannan batu sai rulaiya tayi murmushi sannan tace lallai kai so kake ma ka sami komai kenan a bati ? To ka sani cewa ba a zama wane a banza kuma sai ansha bakar wuya sannan ake shan dadi barina kimtsa sannan mu tafi ka jirani anan kada kayi karambanin zuwa ko ina ko taba wani abu a cikin dakin nan muddin bana kusa Rulaiya na gama fadin haka sai ta juya ta nufi cikin wani daki ta shige cikinsa ta rufe kofa Shi kuwa yarima hulkas sai ya kara kamuwa da tsananin mamaki yace a cikin ransa ' to wai shin menene a cikin wannan gidan mai hadari wanda har rulaiya zata gargadeni da kada in Tabashi ? Ai kuwa matsoraci baya zama gwani don haka bari na yawata a cikin gidan nan na morewa idanuna kallo Gama ayyana hakan keda wuya sai yarima hulkas ya kama yawo a cikin gidan ya nufi wani bangare daban yana kalle kalle yana mamakin irin yadda ginin gidan da kuma kayan alatun da aka zuba acikinsa nan take wani tunani ya fado masa a cikin zuciyarsa yace ni kuwa bayan mun sami nasarar kashe sarki shardas sai na shiga cikin gidan darul daulat na gani tsakaninsa da wannan gida nasu rulaiya wanne yafi girma da kawatuwa a cikinsa koda yarima hulkas yazo nan a zancen zucinsa sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kamashi ya tambayi kansa yace ' saboda me zan bar wa rulaiya wannan gida da dumbin dukiyar dake cikinta data kasance dukiya mai tsananin yawa alhalin yane ranar farko dana fara ganinta a rayuwata shin wannan yana nufin ke nan na kamu da tsananin sonta fiye da yadda ma nake son iyayena da yar uwata siyama tunda gashi zan mallaka mata abinda su ban mallaka musu ba ai kuwa idan hakan ne maganar Aljani Arwasul masadul ce zata tabbata gaskiya, wato zan hallaka a dalilin soyayya kai ! Ba zai yuwu ba dole ne na takawa wannan soyayya birki komai zai faru gareni sai dai ya faru !! Yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaga wata kofar daki ta bakin karfe wacce gaba dayanta a lullube take da yanah a kura tamkar ma ba a taba bude ta ba, kawai sai yarima hulkas ya tunkari wannan kofa da zuwansa daf da ita ya sa hannu ya murda marukinta bisa mamaki sai yaga kofar ta bude ba tare da shakkar komai ba ya kunna kai cikin dakin koda yayi taku uku a cikin dakin sai yaji kofar dakin ta kulle kanta cikin sauri ya koma da baya ya kama kofar da nufin ya bude amma sai kofar taki buduwa sai da yayi iya karfinsa har ya jike sharkaf da gumi amma ya kasa bude kofar koda ganin haka sai ya saduda ya juya ya sake nausawa cikin dakin ba komai a cikin dakin face tarin gumaka na dakarun yaki fululu babu adadi sai dai kowanne badakare yanayin shigarsa daban da dan uwansa kuma makamin yakinsa ma daban, gaba dayan wadannan dakarun yaki suna da siffa ta kwarjini da ban tsoro duk kuwa da cewa gumaka ne komai jarumtakar mutum da dakewar zuciyarsa sai ya firgita da ganinsu saboda gani zaiyi tamkar masu raine ba gumaka ba nan fa uarima hulkas ya cigaba da ratsawa ta tsakiyar gumakan dakarun domin ya isa karshensu, sai da ya yi yar doguwar tafiya sannan ya iso karshen dakim, nan take yayi arba da abinda yai matukar daure masa kai, Al amin Ahmed Misau, ba komai ya gani ba face tarin dukiya mai tsananin yawa tsubi tsubi zube a kasa ta lu u lu u zinare da yakutu wacce inda za a yi aikin kwasheta da magalar rakuma sai an shafe a kalla kwanaki dari ana dibarta bata kare ba koda yarima hulkas ya dubi jikin bangon dake gaban wannan dukiya sai yaga anyi rubutu kamar Haka '- WANNAN DUKIYA HARAMTACCIYACE GA KOWANNE MAHALUKI, BABU WANDA YA ISA YA DAUKO KODA KWAYAR ZARRA A CIKINTA HAR YA FITA DA ITA DAGA CIKIN WANNAN DAKI !! sa adda yarima hulkas ya gama karanta wannan jawabi sai ya bushe da dariya yace ka ji wani zancen banza kuma ya ma za ayi ace wai ba zan iya daukar koda kwayar zinare daya ba alhalin babu mai gadin wannan dukiya a cikin wannan daki face wadannan gumakan banza ?? Gama fadin hakan ke da wuya sai yarima hulkas ya luma hannunsa a cikin tarin lu'u lu'un ya duntso cikin hannunsa ya zuba a cikin Aljihunsa, koda ya juyo da nufin ya koma da baya can inda kofar dakin take sai kawai yaga gaba dayan wadannan gumaka na dakarun yaki sun yi girgiza sun zama rayayyu suna karkade kurar jikinsu gami da zare makaman yakinsu kuma gaba dayansu sai suka durfafo inda yake cikin firgita yarima hulkas ya daka tsalle bay a dai dai lokacin da daya daga cikin su ya kawo masa wawan sara da wani katon barandami, koda yarima hulkas ya goce barandamin ya sari wata dirkar gini mai kaurin gaske sai dirkar ta rabe gida biyu ta fadi kasa saboda karfin saran da kuma kaifin barandamin Al amarin da ya kara razana yarima hulkas kenan babu shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI...... to nima dai Al amin ganin wannan azababben yakin da ake fafatawa yasani dakatawa a wannan waje saboda haka sai kuma Allah ya kaimu gobe zan cigaba daga inda na t TSATSUBA Littafi Na Tara (9) Part B. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . . Al amarin Da ya kara razana yarima hulkas kenan babu shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun aka ruguntsume da azababben yaki, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka nan fa dakarun yakin suka kuntata yarima hulkas suka rinka kai masa SARA DA SUKA ta ko ina ya zamana cewa da kyar yake iya kare kansa idan ba don ma yana da zafin nama ba da tuni sunyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsa, nan take ya raina kansa nadama tazo masa bisa gangancin da yayi ya taba wannan dukiya alhalin an gargadeshi, cikin kankanin lokaci dakarun suka yiwa yarima hulkas rauni har guda biyar a jikinsa ya zamana cewa jini na zubar masa kuma jiri ya fara dibarsa amma saboda jarumtaka da juriya da mugun naci yaki yarda yaje kasa, a haka ya cigaba da maida martanin sara da sukan da suke kawo masa yana kare miyagun hare harensu kokarinsa shine ya kutsa ta tsakiyarsu ya isa can inda kofar dakin take ya sake jarraba budeta amma sai abun ya gagara, Ana cikin wannan bakin gumurzu ne daya daga cikin dakarun ya shammaci yarima hulkas ya gabza masa wawan naushi a kasan habarsa saboda karfin naushin sai da yarima hulkas yayi sama ya gwaru da rufin dakin jini yayi feshi daaga cikin hancinsa da bakinsa ya fado kasa tIm magashiyan, ai kuwa sai dakarun suka yunkura da nufin su gididdibashi, kwatsam ! Sai suka ji an doki kofar dakin ta balle daga jikin garu ta fado kansu sama suna juyowa suka ga ashe Rulaiya ce ta dako tsalle sama izuwa tsakiyarsu tayi wata irin katantanwa ta tarwatsasu da saran takubban hannayanta biyu kafin su sake taso mata ta dira a gaban yarima hulkas wanda ke kwance magashiyan kawai sai ta kama kafarsa da hannu daya ta dagashi sama ta zazzage su, nan take duk lu'u lu un da yarima hulkas ya diba ya zuba a cikin Aljihunsa ya zubo kasa faruwar hakan keda wuya sai gaba dayan dakarun yakin suka kame suka koma gumakansu tamkar basu taba motsawa ba A sannanne Rulaiya ta sunkuya ta dauki yarima hulkas ta sabashi a kafadarta ta fice daga cikin dakin ta kaishi can turakarta ta shiga dinke raunikan dake jikinsa cikin gaggawa don ceto rayuwarsa, jaruma rulaiya na cikin yiwa yarima hulkas dinkine a raunikansa kawai sai taga ya suma, bayan ta gama dinke raunikan sai ta shafa masa magani sannan ta koma gefe daya nesa kadan da kan gadon da ta shimfideshi ta zauna akan wata kujera ta kura masa idanu nan take taga ashe yarima hulkas kyakkyawane na gaske Uhm Al amin Ahmed Misau, abin kwatance kuma yana da kira sosai irin ta manyan sadaukai kawai sai taji zuciyarta tana mai ayyana mata cewa wannan shine irin namijin da yakamata ta aura nan gaba idan ta girma ta cika cikakkiyar ya mace, wata zuciyar kuma sai ta kwabeta ta ce da ita baki da hankaline? Ashe har kin manta da kashedin da Aljani Arwasul masadul yayi miki cewar kada ki kuskura kiyi soyayya da wani da namiji a lokacin yarintarki face kin isa aure? Koda gama aiyana hakan sai rulaiya ta mike tsaye da sauri ta fice daga cikin dakin, domin ta daina kallon fuskar yarima hulkas kada zuciyarta ta kamu da sonsa, yarima hulkas bai farka daga dogon suman da yayi ba sai kashe gari da sassafe A firgice ya farka yana yin arba da rulaiya zaune a gabansa tana kalaci sai ya dubeta cikin tsananin farin ciki yace A wanne lokaci muke a yanzu Dare ne ko Safiya? Shin mun makara wajen zuwa birnin sarki hulbasu domin ganin gasar karshe ta yar uwata Koda jin wannan tambaya sai rulaiya tayi tsaki tace ai idan ma muka makara kaine ka janyo ashe kunnenka na kashi ne ban sani ba me yasaka ka ki bin umarnina alhali na gargadeka akan ka tsaya a inda na barka kuma na gaya maka cewa kada ka taba komai a cikin gidan nan in ba don nayi gaggawar kawo maka dauki ba da tuni yanzu ka zama gawa koda rulaiya tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya Yunkura da kyar cikin matukar karfin hali ya tashi zaune daga kwancen da yake ya zuro kafafunsa daga kan gadon da nufin ya takesu amma sai ya ji ya kasa saboda raunikan dake kan cinyoyinsa nan take takaici ya kamashi har kwallah ta ciko a idanunsa ya dubi rulaiya cikin alamun karayar zuciya yace ina rokonki da ki gafarta mini bisa rashin bin umarninki kuma ina kara rokonki daki daukeni a haka cikin halin da nake ciki ki kaini birnin sarki hulbasu akan lokaci domin naga gasar nan ta karshe tsakanin yar uwata jaruma siyama da sadauki Darkus Koda jin wannan batu sai Rulaiya tayi tsaki tace amma dai kai wawa

Chapter 18 of 21