Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kofar dakin ta sake budewa saiga Hulbasu tare da matarsa Luzuraina da kuma jaruma siyama tare da mahaifiyarta zalina har da sadauki ruhaisu tsohon yaron hailur koda ruhaisu yayi arba da hailur sai ya kamu da tsananin mamaki kawai sai ya ruga gareshi suka rungume juna cikin farin ciki mara misaltuwa suka kama kyalkyala dariyar murna sannan ruhaisu ya janye jikinsa daga cikin na hailur ya risina a gareshi cikin girmamawa yace ya shugabana ko a mafarki ban taba zaton zan sake ganin wannan fuska taka ba bare har na rungumi jikinka mai daraja ka sani cewa har yanzu akwai sauran jama armu da yawa suna rayuwa a boye cikin dazuzzukan wannan birni da muke ciki, koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake lullube hulkas yace nayi matkar farin ciki da jin wannan albishir naka kuma lallai ina bukatarka tare da sauran wadannan jama a tamu, ka sani cewa ga shadila Allah ya dawo mun da ita don haka akwai gagarumin aiki dake gabanmu wannan yaro da kake gani wato yarima hulkas shine dan da nabar shadila tana dauke da cikinsa koda jin wannan batu sai hawayan farin ciki ya zubowa sadauki ruhaisu ya ruga wajan hulkas ya rungumeshi a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas ya dubi siyama sa adda hawaye ya zubo masa sannan ya bude hannayansa yace da ita ' ashe ke yar uwata ce ban saniba? Taho gareni yake yar uwata rabin jiki cikin matukar murna siyama ta ruga izuwa ga hulkas suka rungume junaa A sannan ne zalina da shadila ma suka durfafi junansu suna murmushin saduwa suna haduwa sai suma suka rungume junansu zalina na kuka tace yake gimbiya hakika kaddara ce ta rabaki da mijin kwarai wanda babu kamarsa a wajena a cikin dukkan mazajen duniya amma tunda gashi yanzu ubangijinmu ya dawo miki dashi inaso mu hadu mu biyu nida ke mu bashi farinciki irin wanda bamu taba bashi ba a rayuwa ki dauka cewa yaune wannan dare na farko na amarcinku ehm keda shi don haka na baki kwanaki goma domin jiya ta dawo yau koda jin wannan batu sai shadila ta sake kankame zalina a kirjinta da kyau cikin matukar farin ciki tana mai yi mata godiya Al amin Ahmed Dan mutan misau wato A square nan take sarki hulbasu ya dubi matarsa luzuraina yace dake da shadila da zalina ku tafi ku bamu wuri zamu yi ganawa ta musamman mu shida dinn nan ba tare da wata gardama ba kuwa sai matan uku suka fice daga cikin dakin suka bar sarki hulbasu, hailur da sadauki ruhaisu , siyama da hulkas da kuma barmas sannan kuma sai Al amin Guyson saboda shine typer ehem nan take dukkaninsu suka zauna tsawon yan dakiku dayansu bai ce uffan ba can sai sarki hulbasu yayi gyaran murya yace abinda yasa na taraku a nan shine kowannanku ya san cewa gimbiya shadila tazo nan birnina tare da tsaro na dakarun sarki shardas su dubu bisa jagorancin SADAUKI MARZANU, yanzu ina son na ajiye mulkina na tafi neman HULAR LAMSARA domin mu kare kanmu gaba daya daga sharrin sarki shardas don haka ina neman shawararku bisa yadda zamu yi dasu sadauki marzanu a mataki na farko da kuma yadda zamu kai ga cimma burinmu lallai ina son kowannanku ya bude kwakwalwarsa yayi tunani mai kyau koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai fara yin magana koda ganin haka sai Hulkas yayi gyaran murya ya dubi sarki hulbasu cikin natsuwa yace ya shugabana ni shawarar da zan bayar itace kada muce zamu kawar da su sadauki murzamu a nan cikin birninka kawai a bari a gama kammala wannan gasa ta jarumtaka sai muyi shiri gaba dayanmu a matsayin zamuyi musu rakiya izuwa can karshen gari muna isa can saimu shammacesu mu afka musu mu kawar dasu gaba dayansu, mu tabbatar da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba amma idan mukace anan cikin wannan gidan sarauta zamu yakesu babu mamaki akwai yan leken asirin sarki shardas anan cikin garin wadanda suka sa ido akan su murzanu wanda da zarar abu ya samesu zasu iya gaggauta sanar da sarki shardas, koda hulkas yazo nan a zancensa sai ruhaisu ya dubi hailur da sarki hulbasu yace a matsayina na wanda ya dade yana jagorantar mayakan hari na sumame na yarda da shawarar yarima hulkas dajin haka sai hulbasu da hailur suka yi murmushi sannan sarki hulbasu ya dubi hailur yace yau nima zan fara shirye shiryen wannan tafiya a sirrance ba tare da kowa ya sani ba sai a ranar da zamu tafi ne zan tara yan majalisata na sanar dasu cewar zan raka gimbiya shadila izuwa ga kasarta don tsoron kada a sami wata matsala Akan hanya na fuskanci fishin mijinta kuma nan take zan bar galadima jiran karagata saboda shine kadai mutumin dana tabbatar da cewar zai iya rike amanata idan kuma akwai wani mai wata shawarar ne a cikinku ya fada koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai jaruma siyama tayi murmushi tace ina so ku sani cewa sai munyi taka tsantsan sosai akan dukkan shirinmu saboda maso abinka yafika dabara, kuma ma su iya magana sunce kifi na ganinka mai jar koma, ina mai tabbatar muku da cewa sadauki marzanu da sauran dakarunsa mutum dubu biyu ba kanwar lasa bane domin sun zuba ido sosai akanmu ko yaya suka ga wani mosti wanda basu yarda dashi ba sai sun dauki mataki, abu na biyu kuma shine sarkin yaki sadauki darkus ma yanzu dolene su sa ido akanmu gaba daya musamman bisa ganin cewa sarki ya bani kariya nida iyayena shin bakwa tunanin cewa zasu iya hada kai dasu sadauki murzanu domin gano sirrinmu koda jin haka sai sarki hulbasu ya girgiza kai yace tabbas hakan zata iya faruwa amma zanyi amfani da damata ta sarki nima nasa amintattuna su zuba ido akansu suyi nazarin dukkan motsinsu da shirye shiryensu Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square abinda nake so daku shine mu dukkannan jarumaine don haka ina son kowa ya jajirce iya yinsa a ranar da zamu gama dasu sadauki marzanu domin mu tabbatar da cewar gaba dayansu ba wanda ya tsira mu bar ganin cewa zan tanaji amintattun dakaruna masu yawa a ranar da zamu fita wannan yaki wadannan mutane suna da matukar hadari da wannan furuci nake sallamarku amma banda abokina hailur koda jin haka sai kowa ya mike tsaye ya nufi kofar fita daga cikin dakin amma banda yarima hulkas domin tsayawa yayi yana ta kallon hailur har saida sarki hulbasu ya dubeshi yace kada ka damu yakai yarima yau tare da mahaifin naka zaka kwana don haka kabi abokinka barmas nan da wani lokaci ma a cikin daren yau zamu sake haduwa gaba dayanmu koda jin wannan jawabi sai yarima hulkas yayi murmushi sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin dakin fitarsa keda wuya sai sarki hulbasu da hailur suka mike tsaye Hulbasu ya kama hannun hailur lafiyayyen ya jashi yana dingisa daya kafar suka fice daga cikin dakin suka durfafi wani bangare daban a cikin gidan sarautar yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wani babban falo wanda aka kawatashi ainun da shimfidu na koren kilishi da kuma korayen kujeru manya na alfarma kai ! Hatta labulayen dakin koraye ne komai a wajen kore abin gwanin ban sha awa Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square sunana babu mutum ko daya a cikin wannan katon falo kuma ga shi tsaf tsaf sannan an zuba kayan Alatu iri iri a cikinsa masu tsananin ban sha awa akwai dakuna guda bakwai a cikin wannan falo gami da kewaye guda biyar kowanne daki an sanya luntsumemen gado a cikinsa mai dauke da shimfidu masu taushin gaske, su kansu kewayen sama da kasansu da jikin bangwayensu dutsen lu'u lu'u ne kuma bahon wankan a cikinsu na zinare ne cike da ruwa mai kamshin turaren miski ga furanni kala a cikinsa sai da sarki Hulbasu ya zagaya da hailur cikin gaba dayan wadannan dakuna da kuma makewayin duka sannan ya dubeshi yace yakai abokina anan nake son kaci amarcinka da matarka ta farko shadila koda jin wannan batu sai mamaki turnuke hailur yace haba ya shugabana ya nida nake talaka ba dan kowa ba zakace na zauna a cikin irin wannan kasaitaccen daki alhalin ni gaba dayan rayuwata ma a daji nayi ta lokacin da sarki hulbasu yaji wannan batu sai nan take yaji ya kamu da tsananin tausayin hailur har lwallah ta cika masa ido amma sai ya dubeshi cikin murmushi yana mai dafa kansa yace yakai abokina shin ka manta ne cewa kai shugaba ne guda na kabila babba kaima sarkine kuma bana fidda ran cewa nan gaba zaka zama sarki don haka komai kyan daki da cikar kawarsa dai dai ne dakai, ni yanzu zan tafi izuwa ga iyalina ka zauna a nan ka jira Uwargidanka shadila ehem Al amin Guyson kenan sunana, zata zo ta riskeka nan ba da dadewa ba amma ka sani akwai walima ta musamman wadda na shirya a tsakanin iyalina da naka iyalin kadai domin tayaka murnar sake saduwa da danka da matarka a cikin daren yau don haka kayi zaton amsa gayyata koyaushe, koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya juyaya fife daga cikin kasaitaccen falon ya bar hailur a tsaye yanata kalle kalle cikin tsananin farin ciki domin ji yake kamar a yau an mallaka masa komai dake cikin wannan duniya '' '' '' A can turakar gimbiya luzuraina kuwa wato matar sarki hulbasu tuni ta zauna tare da gimbiya shadila zalina da siyama an kawo musu gasashshen naman kaji da yayan itatuwa suna ci suna hira cikin nishadi amma kuma hankalin shadila a tashe yake domin ta kasa cin komai ta sunkui da kanta kas tana tunani a lokacinda zuciyarta ke ta bugawa da karfi cikin alamun tsananin tsoro da fargaba koda luzuraina ta lura da halin da shadila ke ciki sai ta kama hannayanta ta rike ta dubeta cikin alamun nutsuwa tace yake kawata wai shin wane irin tunani mai zurfi kike yi ne haka wanda har ya hanaki sukuni ?koda jin wannan tambaya sai shadila tayi doguwar ajiyar zuciya Sannan ta dubi luzuraina dasu siyama tace a cikinku kaf babu wanda yasan sharrin sarki shardas sama dani yaki dashi dai dai yake da mutum daya jal yace zai tari gaba dayan halittun duniya saboda karfinsa da sharrinsa ya wuce tunanin mai tunani, ta yaya kuke zaton cewa gaba dayanmu nan zamu iya tsira daga sharrinsa alhalin ya fimu duk wani abu da muke takama dashi koda jin wannan batu sai luzuraina ta numfasa tana mai dafa kafadar shadila tace yake kawata kiyi sani cewa masu iya magana sunce mai laya ya kiyayi mai zamani ! Ko shkka bana yi cewar komai nisan jifa kasa zai fado a saboda haka dole ne karen bana yayi maganin zomon bana ki sa a ranki cewa wannan yaki ne tsakanin Gaskiya Da Karya da karfin gaskiyar mu ne zamu sami nasara akan wannan babban azzalumi wanda ya dade tsawon shekaru yana cutar da al umma haka dai luzuraina tayi ta kwantar da hankalin shadila tana lallabata har ta shawo kanta taci abinci ta koshi suna kammala wannan cin abincine sarki hulbasu da hailur suka shigo cikin turakar koda ganinsu sai kunya ta kama shadila ta sunkui da kanta kas ta kama murmushi na murna da farinciki ita kuwa zalina sai ta mike da sauri ta tarbi su sarki hulbasu tana mai yi musu barka da zuwa sannan ta dubi hailur cikin raha da zolaya ta ce to ango saboda doki ma ba zaka bari nakai maka amaryar taka ba shine ka biyota ? Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square sunana kenan caraf sai sarki hulbasu ya tari numfashin hailur ya dubi zalina yace ke kuwa waya gaya miki cewa ta zama amaryar tasa ai dole ne da farko mu warware auren dake tsakaninta da sarki shardas sannan a daura mata sabo da hailur a sannan ne ta cika amaryarsa, tuni na gama shirya yadda za a tafiyar da bikin wannan aure a yau din nan cikin dare za a kara gabatar da gagarumar walima koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya kama hailur da shadila har dama yarima dasu siyama sarki hulbasu ya dubi luzuraina yace dama wannan sakon muka zo mu sanar da ku kawai don haka idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa can inda za a gabatar da ita, Al amin nake cewa haka kuma idan lokacin cigaba da wannan littafi yayi zakujini wato dai Gobe kenan kafinnan kuma Nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square Dan garin Kaduna nake cewa Mu zama lafiya...TŠÅTеßÄ Littafi Na Bakwai (7) Part C. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . . Idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa inda za a gabatar da ita, koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya kama hannun hailur suka juya suka fice daga cikin turakar, fitarsu keda wuya sai shadila ta rungume zalina tana mai cewa godiya a gareki mara adadi yake abokiyar zamana domin na san cewa duk wannan shiri naki ne tabbas kin dawo mini da farin cikin rayuwata wanda ya fiye mini komai a cikin wannan duniya kiyi sani cewa koda zan sami dare daya ne jal na wannan farin ciki na mutu ya fiye mini shekaru dubu da zanyi nan gaba na zauna tare da babban makiyi shardas koda zalina taji wannan batu sai tausayin shadila ya turnuketa har hawaye ya zubo mata ta sake kankameta a jikinta tace yake abokiyar zamana kiyi sani cewa dole ne nasoki kuma na kaunaceki dari bisa dari kuma na san martabarki a cikin zuciyarsa kece masoyiyarsa ta farko a rayuwa kece kika sha wahalarsa duk da cewa nima nayi wahala dashi amma ai kin kunshi bakincikin dako rabinsa ni ban kunsa ba sa adda shadila taji wannan batu na zalina sai taji itama ta kamu da sonta fiye da ko yaushe don haka sai ta kara kankameta a jikinta suka kama kukan murna Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson ko A square yayinda yarima hulkas da jaruma siyama suka ga haka si suma suka kamu da tsananin tausayin iyayen nasu har hawaye ya zubo musu a tare, kawai sai siyama ta kama hannun hulkas ta ja shi suka fice daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban a cikin harabar gidan sarautar sai da suka iso wani fili mai fadi inda babu jama a wanda ya kasance mai shirun gaske sannan suka zauna tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan siyama tayi gyarar murya tace yakai dan uwana kayi sani cewa nayi matukar farinciki dana san cewa ashe ina da dan uwa a cikin wannan duniya wanda muke uba daya A farkon haduwata dakai naji ina sonka So irin wanda mace ke yiwa namijin da take fatan zama abokin rayuwarta amma yanzu da na gane cewa kai muharramina ne sai naji nafi kaunarka fiye da ko yaushe a matsayinka na jinina don haka kukanka kukana ne kuma farincikinka nawa ne mahaifin nan namu ya dade yana bani horon yaki saboda kawai na dauki fansa akan ubanka na karya wato sarki shardas ko a bayan ransa, shin yanzu zaka bani hadin kai mu hada karfi da karfe domin cika wannan bavvan buri na mahaifin mu? Ka sani cewa raina ba a bakin komai yake ba akan wannan al amari shin zaka iya cire soyayyar sarki shardas dake cikin ranka ka kasheshi da hannunka koda siyama tazo nan a zancenta sai idanun yarima hulkas suka ciko da kwallah nan da nan hawaye ya kama sartu akan kumatunsa, Al amarin da ya karya zuciyar siyama ke nan ta rungumeshi kuma itama ta fara kukan cikin sanyin jiki hulkas ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye Al amin Ahmed sunana hulkas yace yake yar uwata kiyi sani cewa bazan iya cire son sarki shardas daga cikin zuciyata ba amma zan iya kasheshi da hannuna ba don komai ba sai domin a halin yanzu babu mutumin da na tsana sama dashi a doron kasa na tsaneshi ne saboda zaluncin da yayiwa iyayena da kuma munafurtata da yayi ya rinka wahalar da mahaifiyata tsawon shekaru da shekaru amma yana nuna mini cewa shi masoyinta ne na kwarai, ban taba sanin cewa har dukanta yake yi ba a boye a bayan idanuna, shin yanzu ke a cikin zuciyarki kina da yakinin cewa zamu iya gano inda Hular Lamsara take har mu mallaketa mu sami damar da zamu dauki fansa akan sarki shardas alhalin bamu san a inda take ba kuma bamu san wanda ya san inda take ba koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jaruma siyama taja dogon numfashi sannan ta kama hannayansa biyu ta rike suka kurawa juna ido sannan tace yakai dan uwana kayi sani cewa a cikin wannan duniya babu abinda ba zai yiyu ba face wanda ba a jarraba yinsa ba shin baka da labarin yadda akayi JARUMI HANTARU ya sami nasarar dauko Takobin SAIFUL LUJARA ? yasha bakar wahala kuma yasha gwagwarmaya da manyan sadaukai irinsu RABBASU wadanda suka fishi karfi amma saboda sa a da naci gami da rabo sai da yakai ga gaci. Al amin Kenan Mai shararo muku Typing, shin baka da labarin jarumin nan mai mashin GALILUL HARAS ? wato SADAUKI SHADDADU shima yasha bakar wuya gami da gwagwarmaya kafin ya mallaki wannan mashi to a yanzu ma ina ji a jikina cewa kaine jarumin da zai mallaki HULAR LAMSARA sai dai kuma ...... Koda siyama tazo nana a bayaninta sai muryarta ta shake da kakarin kuka ta kasa karasa abinda take son fada ta fashe da kuka sosai al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin yarima hulkas kenan ya sake rungumeta a kirjinsa yana mai cewa haba yake yar uwata menene na kuka me zaki boye mini alhalin ni dan uwanki ne na jini to ki sani cewa na san abinda kike boye mini wannan abu ba komai bane face duk wanda ya mallaki wannan hula ta lamsara sai ya rasa rayuwarsa kuma a tafarkin SOYAYYA zai hallaka kamar yadda ragowar JARUMAN DUNIYA biyu suka hallaka Tuni na dade da jin tarihin wannan manyan makaman yaki guda uku kuma na sani cewa nine na ukun Nasu nasan cewa mutuwa zanyi to amma ki sani cewa ni yanzu nayi matukar farin ciki da ya kasance bake bace masoyiyar da zan mutu a tafarkin soyayyarta ba ke yanzu yar uwata ce ta jini wadda na tabbata da cewar ko bayan raina zata iya kula da mahaifiyata lokacin da yarima hulkas yazo nan a jawabinsa sai jaruma siyama taji kaunasa ta kara linkuwa a cikin ranta don haka sai ta sake rungumeshi suka fashe da kuka gaba dayansu sai da suka dan jima kankame da junansu sannan jaruma siyama ta janye jikinta daga cikin na yarima hulkas ta mike tsaye kawai sai ta juya masa baya tace wane shiri ka fara yi domin ka kai ga wannan matsayi na zama JARUMIN DUNIYA na uku mai hular lamsara ? Yakai dan uwana kayi sani cewa ba a zama wane a banza dole sai an sha bakar wuya da tarin gwagwarmaya, koda jin haka sai yarima hulkas ya mike tsaye yasha gaban siyama yace yanzu wane irin shiri kike nufi zanyi ? Jaruma siyama tayi murmushi tace dole ne ka cigaba da baiwa kanka HORON YAKI har ka sami wanda zaka iya zuwa inda hular lamsara take ka daukota Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square sunana a halin yanzu bincike ya nuna cewa kai da sarki shardas kuna bukatar wannan hula ta lamsara kafin dayanku ya sami nasarar hallaka daya shi dai sarki shardas a halin yanzu yana da karfin da zai iya zuwa wannan wuri da hular lamsara take bisa taimakon bokansa to amma inda matsalar take shine dashi da bokan nasa basu san a inda hular lamsara take ba sai dai kuma akwai wanda suka nema wanda shine kadai zai iya yi musu jagora izuwa wajen ba wani bane ba wannan jagora nasu face wani hatsabibin Tsohon Aljani wanda a halin yanzu duk fadin duniya babu Aljanin da yafishi yawan shekaru babbar magana Al amin nake typing yafi kowa sanin sirrin wadannan manyan makaman yaki guda uku wato takobin saiful lujara, mashin galilul haras da kuma hular lamsara shidai wannan tsohon aljani ana kiransa da suna ARWASUL MASADUL Aljani Arwasul masadul yana da tsananin karfin gudu a cikin sararin samaniya domin daga birnin hindu yana iya zuwa birnin sin a cikin abin da bai wuce sa a biyu da rabi ba don tafiyar da bata wuce ta kwana talatin ba kuwa a cikin abinda bai wuce wasu yan dakiku ba yake kammalata ya kasance bashi da takamaiman wajan zama kuma yana iya zagaye duniya kaf a cikin yini daya kuma kullum sai ya zagayetan ma ana dai baya zama waje daya tamkar shanshani komai karfin sihirin tsafin boka bai isa ya iya ganin a inda aljani arwasul masadul yake ba kuma bai isa ya kirashi ya amsa kiransa ba haduwa da aljani arwasul masadul sai babban rabo da sa a kawai neman Aljani arwasul masadul dai dai yake da neman jaki mai kaho idan kuma har mutum yayi dace haduwa dashi tofa duk abinda ya bukata daga gareshi indai akwai shi a cikin wannan duniya to zai kaishi inda abin yake a cikin kankanin lokaci Inda matsalar take shine aljani Arwasul masadul baya yawo a cikin siffarsa Al amin sunana wato Guyson, gaskiya Littafin nan nikaina da nake typing dinshi duk da na jima da karantashi yana sake kayatar dani uhm kufa ? Yakan rikida ne izuwa siffar bil adama sau tari ko ta dabba ko ta kwaro don haka sai mutum yaci jarrabawarsa sannan yake taimakonsa babbar illar aljani arwasul masadul itace ba a rudarsa da dukiya ko mace ko mulki, kuma bashi da tausayi ko jin kai shi kawai yana da wadansu ka'idoji ne wadanda sai ka cikasu sannan zai taimakeka kuma dole sai ya zauna tare dakai tsawon kwana uku yaga ka cika ka'idojin babu wanda yasan wadannan ka'idoji na aljani arwasul masadul, baya ga haka aljani arwasul masadul yana da karfin damtse na rikakkun zakuna guda dubu dari da tamanin kuma duk duniya babu mai karfin sihirinsa na tsafi amma wani abin al ajabi a tare dashi shine babu abinda ya tsana sama da kudi ko mulki kuma babu abinda yake so sama da jarumi mara tsoro kuma mai sa a ya kai dan uwana kai mutum ne mai tsananin sa a bisa duk abinda kasa a gabanka sannan kuma na fuskanci cewa ko kadan baka da tsoro bisa wannan dalili ne nake da yakinin cewa zaka mallaki hular lamsara kafin sarki shardas ya fita nemanta, ka sani cewa sammako anema ba shine samu ba kai dai kawai ka nemi sa a da dace, lokacin da jaruma siyama tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya kamu da tsananin mamaki ya dubeta yace yaya akayi kika san duk wadannan al amura koda jin wannan tambaya sai siyama tayi murmushi tace na taba haduwa da Aljani Arwasul masadul kuma na cinye jarrabawarsa a lokacinda nake yawon farauta a cikin daji kuma nayi mu amala da shi ta tsawon kwana uku ba tare da na san ko shi waye ba lokacin da yagabatar da kansa a gareni kuma ya fito mini a siffarsa ta ainihi sai ya tambayeni abinda nake bukata a cikin wannan duniya ya kaini inda abin yake domin na mallakeshi, Al amin Ahmed Misau koda naji wannan tambaya daga gareshi sai nayi murmushi nace abinda nake bukata ba zaka iya bani shi ba cikin mamaki aljani arwasul masadul ya dubeni yace ke yarinya kin yi babban kuskure da kika fadi haka ki sani cewa komai yawan dukiyar da kike bukata zan kaiki inda take kuma na kwasheta nakai ta inda Kikeso a cikin dakiku kadan idan mulki kike so na kowacce kasa a cikin wannan duniya zan iya baki shi koda karfin tsiya a cikin dakiku kadan ke idan ma duniyar gaba daya kike sonki mulka zan iya yi miki sanadin hakan to menene kuma abinda kike ganin cewa zai iya gagarata sa adda naji wannan batu na aljani arwasul masadul sai nayi murmushi a karo na biyu nace yakai wannan aljani ka sani cewa duk abinda ka ambata bana bukata ko daya daga cikinsu face ina son ka hana aikata zalunci a doron kasa a tsakanin al ummar mutane da aljanu da kuma tsakanin dabbobi da kwari sannan ka hana zubar da jini a ko ina na duniya ya kasance duk duniya kowa na son kowa ana zaman lafiya babu batun sata ko kwace babu fyade kuma babu bambanci tsakanin attajiri da talaka da kuma tsakananin bawa da sarki wadannan abubuwa sune kadai cikar burina na duniya idan har ka har ba zan gansu da idanuna ba bana fatar nayi doguwar rayuwa a cikin wannan duniya domin takaicin rashinsu ne zai zama babban bakin cikina koda nazo nan a zancena sai naga hawaye ya zubowa Aljani Arwasul masadul yasa hannayansa biyu ya dafa kafaduna ya ce kece bil adama ta farko a duniya data taba burgeni a cikin jinsin mata kuma ban taba haduwa da mai irin wannan ra ayi naki ba ba wani abu bane yasa kika ga na zubar da wannan hawaye baface takaicin kin tambayeni abinda har na mutu ba zan iya samarwa da wani shi ba Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana ina mai tabbatar miki da cewa aduniya ba za a taba zama lafiya ba domin a hakan ta fara kuma a hakan zata kare wannan shine tarihin da na riska a wajan kakana na dari da ashirin kuma nayi imani da wannan tarihi, yake wannan jarumar mata hakika ba zan taba mancewa dake ba a rayuwata domin ni a wajena kece jarumar jarumai wadda bata damu da komai na duniya ba yaune ranar karshe ta saduwata dake kuma ba zaki sake ganina ba har izuwa ranar da zan mutu ko ke ki mutu amma ina fatan nayi miki taimako a sirrance ba tare da kin sani ba kafin karshen rayuwata ina mai yi miki fatan nasara da sa a a rayuwarki bisa wannan buri naki da naji kin ambata daga yau nayi alkawarin cewar ba zan sake zaluntar wani bil adama ba a doron kasa kuma ba zan taba taimakon wani azzalumi ba amma lallai ki bar wannan al amari sirri karki gayawa kowa face jarumin da kika tabbatar da cewa shine zai kawo karshen zalunci , shugaban azzalumai na wannan zami a cikin jinsinku na bil adama da wannan furuci nake yi miki bankwana na karshe koda aljani Arwasul masadul yazo nan a jawabinsa sai hawaye ya zubo mini na rungumeshi ai kuwa sai naji shima ya fashe da kuka daga can kuma sai haji babu shi a jikina ina bude idanuna na nemeshi sama da kasa na rasa yau shekara uku kenan da faruwar wannan al amari kuma ban taba baiwa kowa labarin

Chapter 14 of 21