Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanzu sanar dani alfarmar da kake so nayi maka Hulkas yayi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kas cikin alamun kunya da damuwa kamar ba zai iya magana ba sannan yace yakai abbana ka sani cewa tun da aka haifeni a birnin nan ban taba zuwa ko da wani garin ba daga cikin sauran manyan biranen dake kasar tamu ba, labari ya zo mini cewar hakimin birnin Istanbul ya shirya gagarumar gasa ta jarumtaka kuma an gaiyato manyan jarumai daga bangarori da yawa na duniya lallai ina son na halacci wannan gasa domin a rayuwata babu abinda nake so sama da ganin mutum mai jarumtaka da iya yaki na dade ina rokonka akan ka koya mini yaki a matsayina na jarumin da zai shahara a wannan nahiya tamu amma kaki kuma baka taba gaya mun dalili ba tunda baka son ka sanar dani dalilin nima bana bukatar na sani ni dai yanzu ka amince mini nayi wannan tafiya zuwa birnin istanbul koda yarima hulkas yzo nan a zancensa sai sarki shardas yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun don haka sai ya yunkura da nufin ya juya ya dubi boka barwas domin ya nemi shawararsa amma sai yarima hulkas ya kama hannayansa yace yakai abbana kayi sani cewa bai kamata a sami shamaki ba a tsakanin da da mahaifi muddin wannan da ya kasance jinin mahaifinsa, babu bukatar kayi shawara da wani akan alfarmar da zan nema a wajanka tunda dai nafi karfinta a wajanka koda jin wannan batu sai jikin sarki ya yi sanyi kafin ya bude baki yace wani abu sai boka barwas ya tari numfashinsa ya dubi hulkas yace haba ya kai yarima ai bai kamata kace zaka fita daga cikin birnin nan ba kaje wani wuri ba tunda kasan cewa bincike ya nuna cewa duk ranar da kayi dogon zango kasar nan zata shiga cikin fari da annobar talauci kafin boka barwas ya gama rufe bakinsa tuni shima hulkas ya tari numfashinsa yana mai cewa amma ai cewa kayi sai idan na fita daga cikin yankin kasar nan gaba daya sannan hakan zata faru ya kai barwas kayi sani cewa kana da iyaka a tsakanin da da mahaifi don haka bai kamata ka wuce gona da iri ba yarima hulkas yayi wannan furuci ne fuskarsa a murtuke yana mai hararar boka barwas amma da ya dubi sarki shardas sai fuskarsa ta juye zuwa annuri kawai sai sarki shardas ya maida masa da martanin murmushin yace jeka abinka yakai dana lallai nayi maka izinin ka tafi zuwa birnin istanbul domin idanunka su more da kallon abinda zuciyarka ke so koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima hulkas ya rungume sarki shardas yana mai yi masa godiya nan take yarima hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas ya koma wajen mahaifiyarsa shadila yana riskarta ya rungumeta yana mai yi mata bushatar cewar sarki ya amince masa yayi wannan tafia nan take itama shadila ta cika da farin ciki amma koda ta dago kai tayi arba da fuskokin sarki dana boka barwas tagansu a murtuke babu annuri sai hankalinta ya tashi nan da nan cikin sauri ta kama hannun yarima hulkas taja shi suka juya da baya suka koma cikin gidan sarautar cikin alamun tsananin fishi boka barwas ya dubi sarki shardas yace wannan shine kuskure na uku wanda na gaya maka cewar kada ka aikatashi amma gashi idanunka sun rufe saboda soyayyarsa ka aikatashi ko dajin wannan batu sai sarki shardas ya juyo da sauri ya fuskanci boka barwas cikin tashin hankali yace ban gane abinda kake nufi ba yanzu saboda kawai na bar yarima hulkas yaje yayi kallon gasar jarumtaka a birnin istanbul shine na aikata babban kuskure? Barwas yace kwarai kuwa rashin aiki da shawarata yasa ka aikata babban kuskure na uku wanda nake ta kokarin hanaka ai tunda dai ka fahimci cewar ban son ka bar yaron nan yayi wannan tafiya bai kamata ka barshi yayi ba bincike ya nuna mini cewar yarima hulkas zai sami wata babbar dama ta yakarmu a cikin wannan tafiya da zaiyi amma kuma a dalilin tafiyar ne shima zai sadu da abinda zai zamo sanadin ajalinsa anan gaba Lokacin da sarki shardas yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yaji kamar ya kirawo yarima hulkas yace dashi ya janye izinin da ya bashi nayi wannan tafiya amma kuma sai yaji ba zai iya ba. Kafin ya budi baki yace wani abu sai kawai yaga boka barwas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin alamun tsananin damuwa sarki shardas ya juya ya sauka daga kan matattakalar barandar ya nufi cikin gidan sarautar zuciyarsa cike da sake sake da tunani abinda ya fara fado masa a rai shine wai shin yaya akayi nema har ya bari son yarima ya shiga zuciyarsa alhalin ya san cewa ba jininsa bane asalima ba shi da wani makiyi wanda ya fishi a doron kasa tunda komai dare dadewa sai ya nemi daukar fansar ran mahaifinsa hailur a kansa wata zuciyar kuma sai tace dashi hakika babu abinda yafi soyayya hadari a wannan duniya domin inda tun farko bai kamu da son shadila ba da tun sa adda ya kashe mijinta itama zai kasheta dashi kenan ya huta da fargabar komai don da yanzun bata haife masa alakakai ba kuma kadangaren bakin tulu wato yarima Hulkas maimakon sarki shardas ya wuce zuwa turakarsa sai ya wuce zuwa turakar shadila kai tsaye duk inda ya ratsa sai dai kaga hadimai suna zubewa kasa suna kwasar gaisuwa da isarsa dakin sai ya iske shadila tare da hulkas a zaune cikin nishadi da farin ciki suna cin tuffa a karon farko sai hulkas yaga babu cikakken annuri a fuskar sarki shardas kafin hulkas yace wani abu sai shardas ya dubeshi yace yakai dana ina son ka bamu dan lokaci zan tattauna da mahaifiyarka koda jin haka sai hulkas ya mike tsaye yana mai yin murmushi ya nufi kofar fita daga cikin dakin yace babu matsala fitarsa keda wuya sai sarki ya tura kofar ya rufe ta sannan yazo daf da shadila ya zauna ya sumbaci wuyanta suka rungume juna suna soyayya hm Kunya nakeji Ni uhm daga can sai yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin nata ya hankadata ta fado kasa daga kan kujerar da take zaune ya cafi makoshinta ya shaketa Nan take idanunta suka zazzaro suka kada sukayi jawur ta fara kakarin mutuwa a sannan ne ya saketa ta zube kasa tana numfarfashi kamar ranta zai fita tana mai kurawa shardas idanu A fusace shardas ya dubeta yace wannan jan kunne ne nayimiki gami da tuni bisa alkawarin dake tsakaninmu akan wannan yaro zakuyi tafiya tare kedashi zuwa birnin istanbul domin halattar taron gasar jarumtaka na duniya da aka sabayi idan kikayi amfani da wannan dama kika gayawa danki sirrin dake tsakani na dashi a bakacin ranki ki sani cewa duk abinda zai faru tsakaninki dashi boka barwas zai gani a cikin madubin tsafinsa yanzu zan fita na barki kada ki kuskura ki bari danki ya gane cewar nayi miki wani abu yanzu koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya fice daga cikin turakar yana fita sai shadila ta mike zumbur a lokacin da hawayen bakin ciki da takaici ya zumo mata kawai sai tayi sauri ta dauko wani farin kwalli ta sanya a cikin idanunta nan take idanun nata suka washe sukayi fari kal tamkar bata taba yin kuka ba tana ajiye kwallin saiga yarima ya shigo idanunsa sun ga sa adda ta ajiye kwallin don haka sai ya zargi cewar akwai wani abu da ya faru tsakaninta da sarki shardas doomin baiga dalilin da zaisa tayi amfani da kwalli ba alhalin dama can ta gama yin kwalliya cikin alamun zargi hulkas ya dubi shadila yace yake ummina menene ya faru tsakaninki da abbana?? Shin ya gaya miki wata magana ne wacce ta sosa miki rai? Koda jin wannan tambayoyi guda biyu sai shadila tayi murmushi tace babu wata magana wacce ta sosa mini zuciya farinciki ne kawai yasa kaga alamun sauyin yanayi akan fuskata domin ya shaida mini cewar zamuyi tafiya nida kai zuwa birnin istanbul koda jin haka sai murna ta kama yarima ya rungumeta yana mai cewa burina ya cika yake ummina lallai idanuna zasu ga abinda suka dade suna mafarkin gani A wannan rana gaba daya yarima hulkas bai sami damar hutawa ba ko tsayuwa a waje daya saboda murna sai kai kawo yake yana ta shirye shiryen tafiyar da zasuyi gobe lokacin da dare yayi sai bacci ya kauracewa hulkas da yake akan gado daya suke kwance tare da sarki shardas sai yarima hulkas ya cika da matukar mamaki bisa ganin yadda shima sarki shardas din ya kasa yin barci sai juye juye yake yi kawai akan gado Yarima Hulkas ya dubi sarki cikin alamun mamaki yace yakai abbana wai shin menene ya hanaka barci ne a yau? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi murmushi yace yakai dana kai yarone don haka baka son dacin rabuwa da masoyi ba tunda aka haifeka a cikin wannan gidan sarauta ban taba rabuwa dakai ba tsawon sa a daya jal kullum muna tare dare da rana hatta kwanciyar barci bata rabamu yau gashi an wayi gari zakayi tafiya zamuyi rabuwa ta a kalla tsawon sati biyu a cikin wace irin damuwa da kadaici kake tunanin zan kasance? Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai Jikin yarima Hulkas yayi sanyi nan take idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa bai san sa adda ya rungume sarki ba yana mai cewa....... . A nan zan dakataTSATSUBA Littafi Na Uku (3) Part C. . Lokacin da Hulkas yazo nan a zancensa sai shima sarki shardas jikinsa yayi sanyi ruwan hawaye ya subuto daga cikin idanunsa ya janye jikinsa daga jikin na hulkas suka fuskanci juna yana mai rike kafadunsa yace yakai dana kayi sani cewa ko kadan nima bana son abinda zai sosa maka zuciya kuma babu abin da nake so sama da ganin farin cikinka amma in ba don haka ba da tsawon sa a daya zan kasance a cikin zumudi da dokin dawowarku lafiya kaida mahaifiyarka domin kune ginshikin rayuwata, haka dai sarki shardas da yarima hulkas sukayi ta hira ta bankwana har asubahi ta riskesu basu sani ba a sannan ne hulkas ya fara gyangyadi kafin a jima barci ya daukeshi faruwar hakan keda wuya saiga shadila ta shigo sanye da rigar barci wacce ke baiyana kyakkyawar surar jikinta babban abinda ya daurewa sarki shardas kai shine bai taba ganin murmushin shadila ba a duk sa adda zata shigo turakarsa da daddare sai yau tun a farkon ranar da ya satota daga sansaninsu ya kawota wannan gidan sarauta saboda ya tabbatar da cewar ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta kai tsaye shadila ta fado kan sarki shardas ta fara jan hankalinsa domin ya kwadaitu da ita maimakon ya karbeta hannu biyu sai kawai taga ya bangajeta ta fadi can gefe daya akan gadon ya dubeta a fusace yace menene dalilin da yasa yau kika shigo cikin turakata kina mai murmushi alhalin baki taba yi mun murmushi ba a dukkan dararen da suka shude na barcinmu?? Koda jin wannan tambaya sai shadila ta bushe damahaukaciyar dariya kamar ba zata daina ba karfin dariyar nata baisa yarima hulkas ya faka daga barcin da yake yi ba mai nauyi saboda kasancewar barcin mai nauyi ne daga can sai shadila ta tsuke bakinta ta daina yin dariyar tana mai murtke fuska ta dubeshi tace yakai mijina na dole ka sani cewa ban taba jin kaunarka ba a cikin zuciyata dai dai da darajar kwayar zarra kaine ka rabani da farin cikina kuma kaine ka shayar dani gubar bakin cikin da har abada ba zan iya amayar da ita ba sai dai ajalina ya zame mini saukin ciwon data sa mini Abinda yasa kaga na shigo cikin turakarka ina murmushi a yau ba komai bane face farin ciki bisa sanin cewa gobe zan rabu da ganin wannan fuska taka kuma ba zan sake ganinta ba har sai bayan a kalla sati byu ka sani cewa duk sa adda na kalli fuskarka sai naji kamar bakin kumurci nake kallo haka kuma duk sa adda ka kwanta dani nakanji mugun bakin ciki tamkar na kashe kaina saboda ba masoyina hailu bane yake amfani da wannan kyakkyawan jiki nawa, yanzu na kawo maka kaina ne gareka domin ka more iya son ranka saboda kwanaki goma sha hudu masu zuwa a mafarki jikin nawa zai zama na masoyina wanda ka datse rayuwarsa ka mayar da dansa maraya koda shadila tazo nan a zancenta sai zuciyar sarki shardas ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma ya daga hannu da nufin shararawa shadila mari amma sai ya kasa saboda tsoron kada ya maretan hulkas ya farka daga barci ya gane abinda ya faru tsakaninsu koda shadila taga sarki shardas ya kasa marinta saita sake bushewa da dariya a karo na biyu ba tare da tace dashi uffan ba sai tasa hannayanta biyu ta dauki danta hulkas ta rungumeshi a kirjinta ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuwa sarki shardas sai ya bita da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki fuskarsa nayin gatsine yana jin kamar ya zare takobi yaje ya sareta gari na wayewa sosai sai sarki Shardas ya kirawo mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira sadauki marzanu ya dubeshi yace ina son ka zabo zakwakuran dakaru mutum dubu biyu daga cikin manyan dakarunmu kayi musu jagora a cikin rakiyar matata da dana yarima hulkas izuwa birnin ishtanbul kayi sani cewa zan baku guzuri ishashshe kuma zan baku kudade masu yawan gaske domin ku kawai da dukkan bukatunku amma ku sani cewa idan kuka dawo daga birnin istanbul naga kwarzane guda daya a jikin matata ko dana ko kuma kuka dawo mini dasu babu lafiya ko babu rai a bakacin rayukan iyalanku daku kanku koda jin wannan batu sai sadauki marzanu yarisina yace an gama ya shugaban nan take marzanu ya juya da sauri ya nufi wani bangare daban na gidan sarautar domin ya hado kan dakarun daya dace suyi masa rakiya a cikin wannan gagarumar lafiyamai hadari kafin rana ta take tuni kowa ya gama kimtsawa daga cikin jama ar da zasu yi wannan tafiya shadila da yarima hulkas kuwa sai suka caba ado mai daukar hankali suka shiga cikin keken dokin sarauta sadauki marzanu da sauran dakaru kuwa suka hau dawakai cikin gagarumar shigar yaki suka sa keken dokin a tsakiya sai kuma kuyangi guda uku kacal da aka tanada domin su yiwa shadila da hulkas hidima a cikin wannan tafiya ba tare da bata lokaci ba wannan zuga ta kama hanyar fita daga cikin gidan sarautar, abinda ya daurewa yarima Hulkas kai shine rashin ganin sarki shardas a wannan safiya bare suyi sallama har ya budi baki zai tambayi shadila dalilin da yasa sarki baizo sunyi bankwana ba sai kawai ya hango sarki shardas a can saman bene yana dago masa hannu kuma idanunsa sun ciko da kwalla nan take zuciyar yarima hulkas ta karaya shima ya ji hawaye ya zubo masa take yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya kawai sai hulkas ya daka tsalle ya duro kasa daga kan keken dokin ya ruga da baya izuwa inda sarki yake can saman bene, babu shiri mai jan keken dokin yaja linzami ya tsaidashi itama shadila sai ta duro daga cikin keken dokin a dimauce don a zatonta wani mugun abune ya faru amma sai taga ashe yarima ne ya ruga izuwa inda sarki yake lokacin da sarki shardas yaga yarima hulkas ya rugo izuwa gareshi sai shima ya gangaro da gudu daga saman benen da yake tsaye ya tari yarima a tsakiyar filin gidan sarautar suka rungume juna kuma suka kama kuka a lokaci guda saboda bakin cikin rabuwa yarima hulkas ya dada kankame sarki, yace yakai abbana.menene dalilin da yasa kaki zuwa muyi bankwana tun dazu alhalin kasan cewa ina ciikin kewarka da tunanin rashinka a kusa dani Sa'adda sarki shardas yaji wannan batu sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye sarki shardas ya numfasa yace yakai dana kayi sani cewa ni jarumi ne kuma gwarzon mayaki wanda bai taba zubar da hawaye ba komai wuya da azaba kuma komai farin ciki da bakin ciki tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana amma yau gashi kai ka sani na zubar da hawaye ina mai tabbatar maka da cewa in banda mahaifiyarka babu wani mutum wanda na taba jin ina sonsa dari bisa dari a cikin zuciyata sai kai kuma a halin yanzu soyayyata a gareka ta linka dari bisa dari fiye da komai kuma kai kadai ne mutumin da nake jin cewar ba zan iya cutar da shi ba bisa duk irin laifin da zakayi mini koda kuwa bakin cikin abin dakayi min zai zamo sanadin ajalina koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya sake rungume sarki ya fashe da matsanancin kuka yace yakai abbana tabbas nasan kana kaunata fiye da kima amma ni ina jin kusancinka a raina fiye da kusancin jini da hanta inaji a raina cewar idan babu kai a wannan duniyar ba zan rayu ba kuma ina jin cewar rashinka a kusa dani dai dai yake da jefani cikin kurkukun da babu ci ba sha kuma babu hasken da mutum zai iya ganin ko da tafin hannunsa face matsanancin duhun daba zai misaltu ba koda jin haka sai sarki shardas ya janye jikinsa daga cikin na yarima hulkas kansa na sunkuye yana zubar da hawaye kawai sai ya daga hannu ya yiwa sarkin yaki marzanu inkiya nan take marzanu ya rugo ya dauke yarima hulkas ya ruga da shi izuwa bakin keken dokin ya sashi a ciki itama shadila sai ta koma cikin keken dokin ta zauna nan take aka sakarwa dawakan linzami keken dokin yayi gaba su sadauki marzanu sukabi keken dokin a baya suna maiyi masa kawanya gaba daya gefe da gefe don tabbatar da tsaro nan dai sarki shardas ya bisu da kallo har sai da suka kule ya daina ganinsu sannan ya juya ya koma cikin gidan sarautar cikin tsananin bakin cikin rabuwa da yarima hulkasa bai ankara ba saiji yayi hawaye ya kara zubo masa a wannan lokaci kuma inda yake wucewa akwai dakaru a tsaitsaye kuma ga bayi barori da kuyangi suna ta kai kawo da hidimomi duk wanda yaga hawaye a idanun sarki sai kaga ya firgice domin kowa ya san cewa a tarihin rayuwar sarki shardas babu wanda ya taba ganin hawayansa sai yau da yake an san irin shakuwar dake tsakanin sarki shardas da dan sa yarima hulkas kuma an san cewa yau sun rabu sai kowa ya gane dalilin zubar da hawayan nasa abin da mutane basu sani ba shine wannan hawaye bana soyayyar hulkas bane ba kadai har da takaicin tunanin ainihin alakarsa da hulkas gami da sanin cewa hulkas ba jininsa bane da kuma bakin cikin rashin samun soyayyar shadila a gareshi ta gaskiya kai tsaye su sadauki marzanu suka durfafi cikin daji suka sukayi ta tafiya babu sassauci babu tsoro ko shakkar wani abu saboda sun yarda da kansu tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole a ce da mijin iya baba hakika komai yawan yan fashi da shirinsu idan suka hango wannan runduna ta su sadauki marzanu saikaga sun fasa taresu sun bace daga kan hanyarsu, ba komai bane ya haddasa hakan ba face kwarjininsu kuma ido ba mudu bane ammma yasan kima ma ana kai da ganin dakarun marzanu kasan sun cika zaratan jarumai masu tarwatsa maza domin dukkansu sun kasance manya manya masu kirar mutanen farko, gashi jikinsu a murde yake kuma sun tara kwanji da jijiyoyi kai kace da dutse aka yi gabobin jikin nasu irin shigar yakin da sukayi kuwa mai ban tsoro ce domin kowannansu yana daukeda miyagun makami yaki irin wanda idanu basu saba gani ba kai ba wai yan fashi ba hatta mugayan dabbobin daji da bakaken aljanu wadanda suka kasance azzalumai suna ganin wannan runduna sai kaga sun bace daga wajan saboda boka barwas ya shirya wadannan dakaru tuntuni da karfin sihirin tsafi mai tunkararsu sai cikakken shiryayye abin kwatance a duniya kwana uku kacal wadannan dakaru suka shafe suna tafiya suka iso birnin askandariya suna shigowa suka iske birnin a cike makil da jama a duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan jama a fiye da rabin jama ar da suke gani baki ne wadanda sukazo halattar gasar jarumtaka mafi akasarin bakin kuwa sarakai ne da attajirai da yayansu da kuma fatake da shahararrun bokaye tabbas gaba da gabanta aljani ya taka wut lokacin da keken dokin gimbiya shadila ya kunna kai cikin birnin sadauki marzanu da dakarunsa na biye dashi sai gaba dayan jama ar dake wajan suka dare suka basu hanya kuma kowa ya zuba ido ana kallonsu aka zama kauyawa ba komaine ya haddasa hakan ba face ganin irin dukiyar da aka kashe wajan kera keken dokin da gimbia shadila ke ciki da kuma kayan yakin da dakarunta ke sanye da su domin an sanya jarin wani sarkin ne gaba daya nan fa sarakuna masu ji da kansu ma suka ringa raina kansu basu san sa dda suka rinka leken cikin keken dokin ba domin suga wanda yake ciki amma da yake an saki labulan keken dokin damar hakan bata samu ba a gunsu nan fa aka bi keken dokin a baya duuu har izuwa kofar gidan sarautar birnin ana isa sai akayi cirko cirko kawai sai sadauki marzanu ya zaro wata wasi ka ya baiwa masu gadin gidan sarautar yace su kaiwa sarkinsu, wasikar na isaga sarki hulbasu yana budeta yayi arba da hatimin sarki shardas cikin zumudi ya mike tsaye zumbur ya taho da sauri izuwa kofar gidan sarautar yazo gaban keken dokin yana mai cewa lale marhaban da gimbiya shadila matar sarki shardas na Birnin Romaniya Koda jin wannan batu sai jama a suka zuba idanu domin suga gimbiya shadila saboda labarinta ya gama bazuwa a nahiyar gaba daya ana ta surutun tsananin kyawunta santaleliyar kafarta ta fara zurowa kasa daga cikin keken dokin tun kafin ma jama a suga ragowar jikin nata suka fara gigita da dimauta ai kuwa tana fitowa gaba dayanta aka yi arba da kyakkyawan surar da Allah yayi mata sai mutane suka kama sambatu wasu kuwa basu san sa adda suka kama dalalar da yawu ba tamkar masu hauka sabon shiga a wannan lokaci shadila na sanye da wata shudiyar doguwar riga damammiya wacce ta baiyana dukkan siffofin jikinta a fili wohoho kyawu kyauta ce daga Allah. Mutum ba zai iya baiwa kansa ba, kai ko namijin da bai cika namiji ba idan yayi arba da wannan gimbiya a wannan lokaci sai ya zama namiji domin mace ce doguwa wacce bata kasance siririya ba kuma ba kakkaura ba tana da dara daran idanuwa masu dan karen haske da fari hancinta dogone siriri tamkar fikakken alkalami a kasansa an dasa mata dan kankanin baki kamar yankan wuka cikinta a shamule yake tamkar bata taba cin komai ba kugunta mai fadi ne sosai ga mazaune masu tudu kirjinta a cike yake fal kamar bata taba shayarwa ba gashin ta baki ne sidik kuma dogo ya zuba har kasan marar ta sai haske da kyalli yake kamar madubi TSATSUBA Littafi Na Uku (3) Part.D . Tana gama fitowa daga cikin keken dokin saiga danta yarima hulkas shima ya fito sanye da koren tufafi na alfarma irin nasu na sarakai shima take tsananin kyawunsa ya tafi da hankalin kowa dake wajan domin albasa tayi halin ruwa cikin farin ciki da girmamawa shadila ta risina ta gaida sarki hulbasu har ta budi baki zatace wani abu sai sarki Hulbasu ya tari numfashinta yace yake tauraruwar sarki shardas ai nan ba muhallin yin magana bane kece bakuwa mafi daraja daga cikin dukkan bakin da suka shigo wannan birni nawa ina tsoron dukkan abinda zai bata miki rai koya taba lafiyarki don haka dolene na riritaki tamkar rai guda daya zaifi kyau mu karasa ku sami hutu da nutsuwa keda danki yarima hulkas Koda gama fadin hakan sai sarki Hulbasu ya kira sarkin Yakinsa ya hadashi da sadauki marzanu yace yaje a basu nasu masaukin shi kuwa sarki hulbasu sai ya juya Ya nufi cikin gidan sarautar Gimbiya shadila da kuyanginta su uku tare da yarima hulkas suka bi bayansu basu yi wata doguwar tafiya ba suka iso turakar gimbiya LUZURAINA matar sarki hulbasu inda suka isketa tare da danta yarima Basmar wanda shima yarone dan kimanin shekara tara wato ya girmi yarima hulkas tazarar shekara uku koda yarima hulkas da basmar sukayi arba da juna sai nan take sukaji jininsu ya hadu kafin ma luzuraina ta taso ta taryi gimbiya shadila tuni basmar ya taso da sauri ya tari hulkas yana mai mika masa hannu domin su gaisa ba tare da shakkar komai ba kuwa hulkas ya baiwa basmar hannu suka gaisa basmar ya gabatar da kansa a gareshi a sannan ne sarki hulbasu ya gabatar da gimbiya shadila a wajan matarsa suka rungume juna cikin farin ciki nan take sarki hulbasu ya juya ya fito daga cikin turakar ita kuwa luzuraina ta karbi shadila hannu biyu cikin matukar farin ciki kamar taga yar uwarta ta jini wadda suka dade basu hadu ba nan da nan tasa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka ci tare sama wadannan kuyangi guda uku na gimbiya shadila sai yan uwansu kuyangi suka janyesu suka fice dasu suka taf dasu izuwa nasu bangaren koda aka fara cin abincin sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas ya jashi suka fice daga cikin turakar luzuraina yana mai cewa da umman tasa zamuyi dan tattaki domin na nuna masa gidan nan cikin daga murya luzuraina tace da basmar lallai kada ka fice daga cikin harabata domin sarki ya gargadeni akan na kula da abokinka sosai ko sauraronta basmar baiyi ya yaci gaba da jan hulkas da gudu suka nausa cikin harabar gidan basu tsaya a ko ina ba sai da sukaje wani babban fili wanda aka kawatashi da suke shuke furanni kala kala kuma aka shirya kayan hutu dana wasa a wajan kamar su lilo dawakan katako da wadansu irin gadaje na wasan yara da zuwansu wannan wuri wanda aka kirkireshi musamman saboda yarima basmar sai wajan ya burge yarima hulkas suka hau lilo suna shela kansu suna ta kyalkyala dariyar farinciki daga can sai yarima basmar ya dubi hulkas a lokacin da ya tsaida lilonsa cak yace yakai hulkas kayi sani cewa kaine abokina na farko a duniya kuma na lura cewa kaima nine abokinka na farko koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke

Chapter 6 of 21