Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko kasa na rasa su koda jin haka sai nayi dariya nace ai kin san cewa komai sa a ne da rabo haka dai muka ci gaba da hira har ya rage saura tafiya kadan mu iso gida kwatsam muna cikin tafiya sai zalina tayi tuntube ta fadi a lokacin da zuciyarta ta fara bugawa da karfi, cikin sauri na ajiye mashina mai cake da barewa na tasheta zaune na dubeta cikin kaduwa ina mai dudduba jikinta nace lafiya kuwa menene ya sameki, zalina tayi ajiyar zuciya ta dubeni cikin alanun firgici kawai sai naga hawaye ya zubo mata take ta fashe da kuka tana mai cewa naji a jikina cewa mahaifina yayi kaura, koda jin haka sai nima hankalina ya tashi na dubeta cikin kwarin guiwa nace ke haba ! Tashi mu karasa gida mahaifinki na nan raye kawai dai zuciyarki ce take raya miki hakan nan dai na tasheta muka mike tsaye har zuwa wannan lokacin ina dauke da wannan katon zakin a kafadata ga kuma barewa a jikin mashina haka dai muka cigaba da tafiya harmuka Iso gida tun daga nisa muka hango Abul zalina kishingide a jikin dutsen kogon da muke kwana ya dora kafarsa daya akan daya yana barci, kuma ga sanda a hannunsa in ba don dora kafarsa da yayi ba daya bisa daya da kuma sandar da ya rike a hannunsa da dole ne ace ya mutu Al amarin zalina kuwa lokacin da ta hango mahaifinta a cikin wannan hali tun daga nesa sai jikinta yayi sanyi Al amin Ahmed Misau Nake Guyson Ko A square zuciyarta ta karaya kawai sai ta yarda bakan dake hannunta ta falfala da gudu izuwa gareshi tana isa gabansa sai ta kura masa idanu koda taga idanunsa a kafe suke ko kiftawa basa yi kuma babu inda yake motsi daga cikin gabobin jikinsa sai ta fada kansa ta rungumeshi tana mai tsandara uban ihu sannan kuma ta fashe da kuka koda ganin abin da ya faru sai nima na rugo da gudu ina dogara sandata ina isowa na warbar da wannan zaki na kafadata kuma nayi jifa da sandata da mashin da barewar ke tsire akai kawai sai na tsugunna kasa bisa guiwoyina na fara kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani tsakanina da zalin nikaina Al amin Na tausaya musu gaskiya da wannan gagarumin rashin mahaifin ta da sukayi sai da muka shafe kusan sa a guda muna kuka sannan na mike tsaye naje na kama kafadar zalina na tasheta tsaye na shiga rarrashinat, sai da ta dawo cikin hayyacinta sannan muka fara shirye shiryen binne gawar mahaifin nata, tun daga wannan rana muka bar wannan daji ba tare da fatan komawa cikinsa ba ko don ziyara ga kabarin mahaifin nata wanda ke cikin wannan kogon dutse haka dai mukaci gaba da tafiya a cikin daji mu kwana nan mu tashi can ba tare da sanin inda muka dosa ba muna neman inda yake da ni ima mu zauna muci gaba da rayuwarmu, sai da muka shafe watanni shida cur muna tafiya sannan muka iso wani daji dake cikin nan kasarka ta Askandariyya, A nan ne muka zauna muka ci gaba da rayuwa nida matata zalina inda muka gina wata yar bukka a gefen wani tsauni inda muke kwana har ma muka kafa wani garken dabbobin gida muna kiwo bamu da wata sana a face farauta kuma mu kan kai fatun dabbobi cikin birnika mu siyar mu siyo abin da muke bukata da silallan da muka sayar da fatan dabbobin dajin sannan mu dawo dajin da muke da zama ba tare da mun taba sha awar yin rayuwa ba a cikin gari har muka samu rabon haihuwar Yata SIYAMA tun siyama tana da shekara biyar a duniya na fara bata horon yaki har ta cika shekara tara kuma duk irin horon da za a baiwa babban mutum shi nake bata hakika siyama tasha bakar wahala sosai a wajen horon yaki kamar zata rasa ranta kuma sau tari sai uwarta tayi ta kuka idan taga tana shan wahalar taji kamar ta hanani bata horon amma idan ta tuno da irin kisan gillar da sarki shardas yayiwa kabilarsu da zuri arsu da tawa sai ta hakura, haka dai siyama taci gaba da koyon yaki har ya zamana cewa nima ta fini jarumtaka juriya da naci, a bangaren iya farauta kuwa ni kaina sai da na cika da mamaki bisa ganin irin abubuwan al ajabin da take yi a daji da kuma irin kwarewar da ta samu ta iya harbin kibiya fiye da mahaifiyarta bamuyi shawarar sanya siyama a cikin gasar jarumtaka ba don komai sai saboda mu jarraba karfin damtsenta da kuma iyakar jarumtakarta kuma burinmu shine taci gaba da baiwa kanta horo gami da tanadin daukar fansa akan sarki shardas, ina mai tabbatar maka da cewa yanzu haka ko sunan sarki shardas siyama taji an ambata sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda irin kiyayyar da muka cusa mata kuma a kullum bata da burin da yafi na mu kyaleta ta tafi zuwa birnin shardas ita kadai ta shiga har cikin fadarsa ta kashe shi amma na gaya mata cewa ba zata taba samun nasara ba a kansa a yanzu face idan ta mallaki wata Hula da ake kira HULAR LAMSARA koda Hailur yazo nan a labarinsa sai idanun sarki hulbasu suka zazzari ya kamu da tsananin tsoro gami da mamaki saboda rabonsa da yaji an ambashi sunan wannan hula ta LAMSARA tun yana yaro karami sai kuma yanzu da yaji a bakin hailur, tabbas ya sami labarin hular lamsara a wajan kakansa wato wanda ya haifi ubansa amma bai kara jin labarinta ba kawo i yanzu sai da sarki Hulbasu ya baza fatake jarumai da mayaka izuwa sassan duniya domin su nemo masa wannan hula ta lamsara amma ba a samu wanda ya jiyo labarin inda hular take bama sarki hulbasu yayi gyaran murya sannan ya dubi hailur a natse yace hakika jikina ya bani cewa lallai akwai wani babban sirri a tsakanin shardila matar sarki shardas kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya gano cewa kana nan a raye kuma anan cikin yankin kasata tobama kai ba ko iyalinka hatta nida kaina bz an zauna lafiya ba don zai iya zuwa ya yakeni ya kawai da mulkina koda jin haka sai hailur ya dubi sarki Hulbasu yace yakai wannan sarki mai Karamci me yasa ka taimakeni Alhalin ka san cewa yin hakan hadarine ga rayuwarka da mulkinka koda jin haka sai sarki hulbasu yayi gyaran murya gami da ajiyar zuciya sannan yace A rayuwata babu abinda na tsana sama da zalunci kuma mahaifina kafin ya gushe ya bar mini wasiyya akan cewa idan har ina son nayi nisan kwana akan karagar mulina to dole ne Na guji aikata zalunci ga talakawa na dama duk wadanda suke karkashina ko kasa dani kuma na kwatanta adalci a tsakaninsu gwargwadon iyawata ina so ka sani cewa har yanzu sarki shardas bai san komai ba dangane da wanzuwarka ko baiyanarka a cikin aksata kuma dolene kaci gaba da boye kanka har izuwa lokacin da zaka iya fuskantarsa, duk da cewa yanzu kaga matarka shadila da kuma danka yarima Hulkasa amma dole ne ka hakura da mallakarsu har sai nan da zuwa lokacin da ya dace, idan ba haka ba kuwa zaka rasa su ne gaba daya kuma kai kanka ma zaka rasa kanka ba zan hanaka ka gana da shadila ba amma kada ku kuskura ku bari wannan yaro hulkas ya san cewa kaine mahaifinsa kuma kada ku bari ya san duk abinda ya faru a baya hakan ba zai haifar muku da komai ba face rugujewar dukkanin burikanmu gaba daya da kuma salwantar rayukanmu yayinda sarki Hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe har hawaye ya zubo masa kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda fishi ya dubi sarki hulbasu yace yanzu kana nufin kace dani inaji ina gani zan hakura da matata wadda aka rabani da ita a daren angwancinmu da ita na farko kuma na hakura da dana wanda tun yana ciki bai san cewa nine ubansa ba gashi har ya cika shekara bakwai a duniya, ka sani cewa har kwnaan gobe zuciyata bata bayar da soyayyarta ta gaskiya ba ga kowa face shadila ina son shadila fiye da yadda nake son kaina Al amin ahmed Misau Nake Shin tayaya kake tunanin zan yarda ta sake kubuce min a karo na biyu al halin ban taba zaton cewa zamu sake hadu wa ba a cikin wannan duniya koda hailur ya zo nana a zancensa sai hawaye ya zubowa sarki Hulbasu al amarin da yai matukar girgiza hailur kenan kuma yai matukar bashi mamaki ya dubeshi yace yakai abokina inda dalikin zubar wannan hawaye naka mai tsada koda jin wannan tambaya sai sarki hulbasu yaja dogon numfashi sannan ya sa hannu ya goge hawayansa ya dubi hailur cikin alamun karayar zuciya yace yakai abokina kayi mini tambayar da ta fama min tsohon ciwon dake cikin zuciyata ne kuma shine asalinsanadin da yaja mummunar kiyayya tsakanina da sarki shardas inaso ka sani cewa duk irin kiyayyar dakake yiwa sarki shardas bata kai koda rabin wacce nake yi masa ba domin duk ladabin da nake yi masa a yanzu na dole ne saboda yafi karfina kuma bana son abinda zai taba kasata da jama'ata, ka sani cewa bakincikin sarki shardas ne ya kashe mahaifina kuma sarki shardas ne sanadin dana rasa dana na fari YARIMA HUZEIN Cikin alamun tsananin mamaki da kaduwa hailur ya dubi sarki hulbasu yace tayaya mahaifinka da danka huzein suka gushe koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa sarki hulbasu ya dubi hailur cikin nutsuwa yace yakai abokina ka saurari labarin da zan baka yanzu dukkanin amsar tambayar da kayi min yanzu tana cikinsa...... . JARUMA SIYAMA DA MAHAIFINTA HAILUR SUNA CIKA BURINSU NA DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHARDAS ?. . MAI ZAI FARU IDAN SARKI HULBASU YA GAMA BAIWA HAILUR LABARIN MUTUWAR DANSA DA MAHAIFINSA ? . A WANNE HALI SHADILA TAKE CIKI BAYAN TAYI ARBA DA TSOHON MIJINTA HAILUR ? . YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAN CEWA HAILUR SHINE MAHAIFINSA NA GASKIYA . Marubucin littafin Wato Abdul aziz sani M/ Gini yace mu hadu a Littafin Tsatsuba na (6) Don jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari mai dumbin darasi fadakarwa da nishadantarwa Mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe Al amin Ahmed Misa Inkiya Guyson Ko A A Misau nake TSATSUBA Littafi na shida 6 Na Abdulaziz Sani M gini HausaeBook Made Shuraih Usman Zaku iya dauko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin eBooks ta hanayar ziyartar shafinmu na facebook http://shuraih.waphall.com SATSUBA Littafi Na Shida (6) Part A. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . LOKACIN DA SARKI HULBASU YA ZO NAN A ZANCENSA SAI HAILUR YA jinjina kai gami da yin murmushi sannan ya tattara hankalinsa gaba daya kan sarki hulbasu yace ina saurarenku yakai abokina , koda jin wannan batu sai shima sarki Hulbasu ya mayar masa da martanin murmushin da yayi masa sannan ya fara bashi labarin kamar haka.... ''KIMANIN SHEKARU GOMA SHA DAYA DA SUKA SHUDE, Sa adda satki shardas ke nahiyar nan yana cinsu da yaki sai ya zama dodon maza kuma ki gudu sa gudu domin kuwa duk kasar da ya durfafa sai ya sami nasara akanta, a wannan lokaci mahaifina ne akan karagar mulki ni kuwa nine sarkin yakinsa, kuma nine kadai dansa a duniya kuma nima dana guda daya ne tal a duniya wato YARIMA HUZEIN Lokacin da labari ya riski mahaifina cewar sarki shardas yaci kasashe guda ashirin da daya da yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi da farko yayi shiri ya dauki matakin yin yaki da sarki shardas don har ya bami umarni na tara gaba dayan mayakanmu mu tanadi abinci da kayan yaki da nufin mu yi riga kafi wato muje mu tari sarki shardas da yaki tun gabanin yazo ya yakemu amma sai wani tunani ya zo masa ya dakatar da fita yakin yayi shiri ya tafi izuwa gidan wani mashahurin boka wanda ake kira ZAMARANU IBINI KALBIYA,, boka zamaranu na zaune a cikin wani daji ne dake gabam iyakar wannan birni namu kuma masana tarihi da bincike sun tabbatar da cewar boka zamaranu yafi shekara dari zaune a ciki wannan daji shi kadai, babu wanda yasan abinda yake yi a cikin dajin ko kuma dalilin zamansa amma dai an tabbatar da cewar da shi da bukkar da yake zaune a cikinta kwai rana guda aka gansu sun wanzu ba a san mafarinsu ba, mahaifina Ya durfafi dajin DANYUL shi kadai kai tsaye ba tare da fargabar komai ba alhalin tsawon bayyanar boka zamaranu a dajin babu wani mahaluki daya sake shigarsa walau MUTUM KO ALJAN ba don komai ba kuwa face sai don mugayen bakaken aljanun dake cikinsa, AA Misau Sunana, Komai gawurtar ayari na fatake basa iya ratsa dajin duk tsautsayin da ya sa suka shiga kuwa shi ke nan sun bata har abada ba za a sake jin duriyarsu na a tsawon shekara dari da baiyanar boka zamaranu a cikin dajin Danyul fatake ko yan fashi ba sa sake shigarsa ba, don haka nema ake yiwa dajin lakani da BIRNIN FATALWA, AA Misau Sunana Duk da sanin tsananin hadarin dake cikin wannan dajin haka mahaifina ya kunna kai cikinsa, kai da ganin yanayin fuskar mahaifina a lokacin da yake tafiya bisa dokinsa a cikin dajin ka san cewa babu batun tsoron mutuwa a ransa, in da ma mutuwar zata zo masa to zai marhaban da ita ai kuwa tunda ya shigo cikin dajin ya rinka yin arba da wadansu irin mugayen bakaken aljanu masu tsananin muni da ban tsoro, duk sa adda wadannan mugayen aljanu ska tasamma mahaiina da nufin su dasa masa wawa sai su ga ko gezau baiyi ba alhalin duk bil adaman da yayi arba dasu take yake zaucewa ko sumewa hm AA Misau Sunana, haka dai Aljanin suka yi ta kokarin firgita mahaifina da razanashi amma ko kadan yaki razana wani lokacin ma sai yayi kamar bai gansu ba ko baijisu ba, sai da ya shafe kwana tara yana tafiya kuma baya yarda ya yada zango a ko ina ko barci zaiyi akan dokinsa yake yi, kuma a tsawon kwana taran baiyi bawali ba ko bayan gida, kuma baya tsayawa da tafiya face idan dokin nasa ya gaji ya tsaya don kansa yana hutawa, a ranar kwana na tara ne ya iso kofar bukkar boka zamaranu wacce ke tsakiyar dokar dajin Danyul. ++ ++ ACAN BIRNIN ASKANDARIYYA KUWA, hankalina dana yan majalisar sarki ya dugunzuma ainun, domin mun nemi sarki sama da kasa a cikin birnin nan mun rasa babu wanda ya san cewa ya tafi izuwa dajin Danyul, Ashe cikin tsakiyar dare ya sulale ya fice daga cikin birnin ta hanyar batar da kamanninsa ++ ++ MAHAIFINA NA isa can kofar bukkar boka zamaranu sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak ! Kafin ya sauko daga kan dokin nasa ne yaji an kyalkyale da dariya kuma sai yaji sautin dariyar yana fitowa daga kowanne bangare wato gabas da yamma, kudu da arewa AA misau Sunana sarki ya leka cikin wannan bukka sai yaga wayam babu kowa a ciki kawai sai yaji an dafa kafadarsa ta baya, a firgice ya juya da sauri yayi arba da abinda ya dafa kafadarsa boka zamaranu ne! Boka zamaranu ya kasance dogon mutum kuma siriri mai kwala kwalan idanuwa kunnuwansa wasu iri ne kamar ba na mutum ba domin a tsaye suke tamkar na zomo yana da tarin gashin girar ido mai kauri da tsawo kuma yana da dogon hanci tamkar alkalami, Gaba daya gashin kansa gemunsa da sajensa fari ne saboda tsufa ga masana ilimin karanta shekarun dan adam ta hanyar lura da yanayinsa za su iya bashi shekaru dari biyu da yaya na haihuwarsa, domin gaba daya fatar jikinsa ma ta yankwane ta bushe kai kace ma ba mutum bane Siffofinsa gaba daya sun juye sun zama abin tsoro koda sarki yayi arba da boka zamaranu sai yaja da baya a tsorace a karon farko tunda ya shigo cikin dajin Danyul, koda ganin haka sai boka zamaranu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yace haba yakai sarki mai birnin askandariyya akan wani dalili Zakaji tsorona alhalin ka wuce abubuwan tsoro sama da guda dubu a baya wadanda suka fini firgitarwa? Ka sani cewa kaine kadai mahalukin da ya ratso wannan daji ya iso har nan a raye tsawon shekara dari da suka gabata kuma kaima din bawai jarumtakarka ko sihirinka bane suka kwaceka ba face cire tsoron da kayi a cikin ranka AA Misau Sunana rashin tsoro a cikin zuciyar mutum shine sirrin shigowa cikin wannan daji na Danyul har mutum ya cimma burin da yake dashi dashi acikin dajin ba tare da ya hallaka ba, shin zaka iya gaya mini dalilin da ya saka siyar da ranka ka shigo wannan daji alhalin ga mutanenka can sunyi shirin yin yaki da sarki shardas ? Lokacin da boka zamaranu yazo nan a zancensa sai sarki yayi ajiyar zuciya ya kasa cewa komai domin a sannan ne yaji bawali ya matse shi kuma wata irin azababbiyar yunwa da kishirwa sun kamashi, AA Misau Sunana Kenan kuma Nine Jagoran Wannan typing din Littafin Gaba daya, saboda dama tun a kwana na takwas da tahowarsa dajin danyul guzurinsa ya kare, da yunwa da kishirwa ya kwana Kwatsam! Sai sarki yaji boka zamaranu ya sake bushewa da dariya sannan yayi nuni da cikin bukkar sa yace da sarki sauko daga kan dokinka ka shiga cikin bukkata ka kawar da bukatarka duk abinda kake so zaka samu a ciki koda jin wannan batu sai sarki ya sauko daga kan dokin nasa da sauri ya ruga izuwa cikin bukkar AA Misau Sunana Yana shiga sai kansa ya juye ya firgita ainun domin ba a dakin bukka ya tsinci kansa ba, cikin wata makekiyar fada ya tsinci kansa wacce ta kawatu ainun fice da tasa take kofar wani makewayi ta bayyana tare da bude kanta ba tare da wata fargabar komai ba sarki ya ruga izuwa ciikinta ya kawar da bukatarsa, yana fitowa daga cikin kewayen kuma saiga Abinci da abin sha iri-iri akan wani dogon tebur na alfarma sarki ya karasa kan wannan tebur jikinsa na tsuma zuciyarsa cike da tunani da mamaki domin sa adda ya shigo fadar babu wannan teburi bare abincin dake kansa ba tare da fargabar komai ba mahaifina ya zauna yaci gaba da sha sai da yayi gyatsa mai nuni da alamar Ya koshi Al amin Ahmed Misau Sunana, faruwar hakan keda wuya sai boka zamaranu ya baiyyana tsulum a gabansa yace yauwa tun da yanzu ka sami nutsuwa saika bani amsar tambayata ? Mahaifina yayi gyaran murya yace yakai wannan boka mai daraja kayi sani cewa ba komai ne ya sa na sai da raina na shigo cikin wannan daji ba alhalin na san cewa duk wanda ya shigeshi sai ya mutu face sai domin gudun kada nayi garaje na zuwa yakar sarki shardas saboda masu iya magana sunce mai laya ya kiyaye mai zamani A iya sanina ban taba ganin sarkin da ya yaki kasashe ashirin da daya ba a wannan nahiya tamu har ya sami nasara a kansu face sarki shardas duk da na san cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata kasa mai yawan dakarun yakina, amma duk da hakan sai da zuciyata ta buga kuma tsoro ya darsu a cikin raina bisa al amarin sarki shardas, naji daga bakin bokaye da yawa cewa kaine kadai zaka iya gaya mini wani abu akan sarki shardas bisa wannan daliline yasa nazo gareka domin ka sanar dani shin idan nayi yaki da sarki shardas zan samu nasara a kansa? Baya ga wannan ina so nayi maka wata tambaya guda daya ? Tambayar kuwa itace wai shin menene ya zaunar dakai a cikin wannan daji har tsawon shekaru dari ?? Lokacin da boka zamaranu yaji wadannan tambayoyi sai yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa kamar ba zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi mahaifina cikin nutuwa yace yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wani jarumi ko matsafi daga jinsin MUTUM KO ALJAN wanda zai iya kashe sarki shardas a yanzu domin kuwa yana kan sharafinsa ne kuma zamaninsa ne wow AA Misau Ke magana Babbar Magana Kenan, ina tabbatar maka da cewa idan har ka ce zaka yakeshi sai gaba dayan dakarunka sun kare, kuma sai ya shigo har cikin birninka ya yi maka KISAN GILLA idan kana son ka tsira daga sharrinsa sai dai ka shirya masa kyauta ta dukiya da bayi mai yawa ka aika masa kuma ka tambayeshi duk abinda yake bukata daga gareka domin kai da jama arka ku zauna lafiya, dangane da tambayar dakayi mini kuwa ta karshe amsar tambayar ka itace yau shekarata dubu biyu ina jiran zuwan ranar da wata hula zata bayyana wacce ake kira da suna HULAR LAMSARA Zamana a cikin wannan daji ba na komai bane face na binciken gano inda hular lamsara take da kuma yadda zan iya mallakarta amma har yanzu na kasa gano hakan sa adda boka zamaranu yazo nan a zancensa sai mamaki ya kara kama mahaifina yace, yakai wannan boka mai daraja da abin al ajabi an ce shekaranka dari a cikin wannan daji kuma gashi a yanzu da bakinka ka gaya mini cewa yanzu shekararka dubu biyu kana jiran bayyanar hular lamsara to waishin anya kuwa kai mutum ne ? AA Misau Sunana koa a zamanin baya sosai na kakannin kakanninmu mutane basa yin shekaru dubu biyu a doron kasa, sannan kuma ita wannan hula ta lamsara yaushe ne za ta bayyana kuma me kake so kayi da ita da har ka shafe shekaru dari a cikin wannan daji saboda ita? Koda jin wannan tambayoyi sai boka zamaranu ya bushe da dariya mai karfi har Dariyar ta kama amsa kuwwa ta cika fadar gaba daya, mahaifina yaji kamar kunnuwansa zasu dode ba shiri ya sa hannayansa ya toshe kunnuwan nasa har sai da ya daina dariyar sannan ya dago ya kalleshi, boka zamaranu ya mike tsaye yayi tafiyar taku biyar sannan ya juyo ya fuskanci sarki yace ni mutum ne kamar kai ba aljan ba amma na fito daga cikin mutanen da suka fi kowanne kabila dadewa a duniya domin a yanzu haka da kake ganina shekarun haihuwata sun kai dubu biyu da dari hudu da arba'in, nine kadai mutum da ya rage a duniya daga cikin jinsinmu kuma nine kadai na san sirrin kayan yakin MAZAN JIYA guda hudu makaman yakin da babu kamarsu a duk fadin wannan duniyar gaba daya, idan na mallaki hular lamsara sai na mallaki duniyar nan gaba dayanta, kuma a sannan ne kadai zan iya yin aure har na haifi irina wanda a gaba zaiyi shekara dubu takwas yana mulkin duniya Jikana kuma zai karbi karagar a hannunsa ya ninka shekarunsa haka dai zuri ata zata ci gaba da mulkin duniya har abada ba zan taba cika wannan burin nawa ba face na mallaki hular lamsara yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wanda zai iya hallaka sarki shardas face wanda ya fara mallakar wannan hular ta lamsara A A Misau Sunana Kenan, da wannan furuci nake yi maka bankwana kuma ina mai shawartarka daka gaggauta barin dajin nan ka koma izuwa ga kasarka domin idan ka kara dakika arba in anan zaka iya rasa rayuwarka duk amsar da baka ji ba daga tambayoyinka ba zan iya sanar dakai bane gama fadin hakan keda wuya sai boka zamaranu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, koda ganin haka sai mahaifina ya mike zumbur ya fice da gudu daga cikin fadar sai gashi ya bayyana a gaban wannan bukka a dimauce ya karasa inda dokinsa yake ya daka tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya kama gudu ba sassauci sai da mahaifina ya sake shafe kwana tara yana tafiya sannan ya dawo gida, yana isowa ya bayar da umarnin a janye batun yaki nan take aka sallami kowa mayakan suka koma izuwa ga gidajensu tare da kwance damarar yakin da suka daura suna cike da dumbin mamakin dalilin da ya sa aka fasa zuwa yakin, kashe gari kuwa, da sassafe sarki ya tashi ayari na dakaru dubu uku dauke da bayi dubu ashirin da kuma dukiya mai dumbin yawa ta dinare, lu'u lu'u da murjani cikin akwati dubu suka tafi izuwa ga birnin sarki shardas da kuma wasika, lokacin da wannan ayari suka riski sarki shardas yaga dukiyar da mahaifina ya aiko masa kuma ya karanta wasikarsa wacce ke nuna mubaya a gami da neman zaman lafiya sai ya bushe da dariyar mugunta sannan yace' tabbas na cika zaki uban dawa a wannan nahiya kuma dole ne sarakuna su durkusa a gabana su nemi tsira da jaddada muba ya arsu gareni nan take sarki shardas ya sa aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da ita bayanin dake cikin wasikar shine kamar haka........... Danjin wani bayani ne sarki shardas ya aiko sai ku tarbeni a Post na gobe ehem Dafatan wannan labarin yana kayatar daku Idan hakane kawai ku sauke mun comments dinku gami da likes kafinnan Nidinne Dai Al Amin Ahmed Misau AA Misau Ke Magana Daga Zauran LabaraiSATSUBA Littafi Na Shida (6) Part B. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . NAN TAKE SARKI SHARDAS YA SA AKA RUBUTO AMSAR WASIKAR MAHAIFINA AKA MAIDO MASA DA ITA, BAYANIN DAKE CIKIN WASIKAR SHINE... Yakai mai birnin askandariyya kayi sani cewa sakonka na bayi da dukiya ya riskemu, kuma mun gode da wannan karramawa da kayi mana gami da mubaya'a, amma ka sani cewa ba mu karbi mubaya'arka ba har saika zo da kanka fadata ka zube kasa a gabana ka kwashi gaisuwa sannan zamu aminta da mubaya'arka a garemu, sharadi na biyu kuma shine dole ne duk shekara ka rinka kawo mini irin wannan kyauta daka kawo mini ta bayi dubu ashirin da dukiya akwati dubu sharadi na uku shine dolene ka baiwa wakilina matsayi da mazauni a kasarka domin su dinga kawo mini rahoto duk abin dake gudana a cikin birninka da kauyukan kasarka, sako daga sarki mai cikakken iko kuma sarki dodon maza gallabar sarakuna sarki shardas ** ** Lokacin da wannan wasika ta riski mahaifina aka karanta a tsakiyar fada sai hankalin kowa ya dugunzuma ni kuwa sai raina ya baci jikina ya kama tsuma, cikin tsananin fishi na mike tsaye ina

Chapter 11 of 21