Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baro turakar shadila ya aika aje a kirawo masa babban bokan birnin wanda ake kira da Barwas ibn Mus ab Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta masa duk abinda yake faruwa nan take bokan yake shaida masa abubuwan matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan wannan juna biyu data samu ya kasance mai nuna mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba ka zamo mai tarairayarta kada ka bari koda kuda ya taba lafiyarta kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa adda zata haihu lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci kun shaku ainun da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a cikinta kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar mallakar hular lamsara ina mai tabbatar maka da cewar da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne dukanta a tafin hannunka komai da kowa sai ya dawo karkashin ikonka kuma babu wani makiyinka da zai iya samun nasara a kanka . Anan zan dakata hakaTSATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part F. . Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin damuwa yace ya shugabana yaya batun alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya yace ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi face rashin biyan bukatata, daga wannan rana sarki shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga ashe zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da kulawa Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba a ranta ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya kamata ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a cikinta kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta watarana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai a wannan lokaci tana sanye da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi cikinta taga ya dan fara girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take ciki koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki shardas ya jiyo a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu izuwa cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa a cikin turakar face shadila ita kadai a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan kumatunta cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune ya kama hannayanta biyu ya rike suka kurawa juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai taushi da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan na rabaki da duk zuri'arki na kawoki kasata da karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake matata ta dole har abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare harna sami gafararki ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika daya ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na yiwa mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba zan taba haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar yadda na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon shekaru bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki sani cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar nan don tafiya neman hular lamsara bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a sannan ne nake son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa domin daga wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da cewar sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu gano inda hular Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san kamannin danki ba shima bai san nawa ba don haka ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan gaba idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan hailur kuma nan take zan kasheshi Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a wajanki kuma ki tuna cewar kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki tun da kinsa na 'yanta matan zuri arku daga matsayin bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya. A lokacin da Nikuma Zankoma Inda nafi Wayau wato Neman na Aure,,, .. Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO KARSHE marubucin Littafin yace. . SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A WAJANTA? . SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU? . WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA . DAGA KARSHE SHIN AUWZAB ZAN SAMU DAMAR GAMA RUBUTO MUKU WANNAN LITTAFI DUKA ??? . marubucin yace mu hadu a Littafin TSATSUBA na Uku (3) Don jin cigaban wannan labar TSATSUBA Littafi na uku Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator::- Shuraih 99% You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com TSATSUBA Littafi Na Uku (3) Part A. . Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin hankali kamar yadda sarki shardas ya bukata haka al amarin ya kasance, wato daga wannan rana suka ci gaba da renon juna biyun nata tare, ya zamana cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata lokacinsa tare da shadila, yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na damunta take zai tura a kirawo likitoci su dubata sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba kwana a tashi sai cikin shadila ya tsufa ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai dai ayi mata A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara ne nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai kawai akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara tsawa da walkiya ; al amarin da ya razana jama'a kenan aka kama guje guje A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta watse jama'a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu suna rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin a sanar da sarki abindake faruwa don ana zaton ko allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi zasu hallakar da mutanen kasar Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai fuskarsa a murtuke yana muzurai koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a gabansa aka yi tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka marwas yace ya kai dirkar birnin Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo mana? Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya suke faruwa a sararin samaniya alhalin babu ko alamar hadari? Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya bushe da dariya Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan boka barwas ya turbune fsuka yace matar sarkice zata haihu yu zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai shahara a ko ina cikin wannan duniya daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni namu mai albarka za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da wannan yaro zaiyi wata tafiya manufa ya fita daga cikin wannan gari namu koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda zasuyi tsakanin murna da bakinciki domin ta leko ne ta koma, babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane a cikin bayanin boka barwas sunji cewar da zarar wannan yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai yaye don haka sai wasu suka fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da dai a shiga farinciki da farko a karshe kuma a shiga tasku Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa Ana cikin wannan haline aka yi wata irin tsawa mafi karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har gidajen birnin gaba daya saida yayi rawa, kasa tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta dabbobi suka kama guje guje suna shigewa maboya, mutane kuwa suka rude suka dimauce kamar zasu haukace, A dai dai wannan lokaci ne kukan jaririn Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa kuwwa izuwa cikin dazuzzuka Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan sama kamar da bakin kwarya wata irin iska mai dadin sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya addabi mutane faruwar wannan sabon yanayi keda wuya sai murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa jama a suka ci gaba da cincirindo a kofar gidan sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba da wannan sabon jariri da aka haifa ko ya sami tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa wannan jariri dan baiwa ne tunda gashi ni'ima ta sauka a birnin a irin lokacin da ba ataba samunta ba shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa bane daga Allah, ruwane daga shaidanu domin kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin hanyar bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun a matsayin ababan bautarsu, bayan kofar fada ta cika makin da mutane ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan mutane sanyin iskar dake kadawa har ya fara addabar jama'a amma saboda naci sunki su tarwatse sai tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan sarautar dauke da jaririn da shadila akan tafin hannayensa jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba ga sabon yankan cibi a jikinsa ruwan saman nata dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake kyakyatawa yana ta wutsil wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama'a sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka har sau uku sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas jaririn ya karba, ya fuskanci jama a yace yaku jama ar wannan birni na Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi kukana sun bani da alhalin na shafe shekara da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina mai tabbatar muku da cewar wannan da dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai jama'a suka amsa masa da cewar sunyi Alkawari zasu so wannan da tamkar dan cikinsu. Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi boka barwas ya mika masa hannu domin ya karbi jaririn kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya sallami jama'a kowa ya watse aka tafi ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe bayan jama a sun watse sai sarki shardas da boka barwas suka juya suka nufi cikin gidan sarautar suna masu jera kafada tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice uffan ba sai sarki shardas ya dubi boka barwas yace yakai abin dogaro na yakai shamakin dake tsakanina da allolinmu ina son ka gaya mini dukkan dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da na umarci jama a dasu so wannan jariri na shadila koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai wannan abu da kayi shine babban kuskurenka na farko a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne cewa a duniya kaf baka da wani makiyi wanda yafi wannan yaro? Shin ka manta ne cewa a halin yanzu yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda suke son ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a lokacin da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular lamsara shine zai hau karagarka ta mulki kuma idan muka je muka samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga kan karagarka ba abu bane mai sauki duk da cewar zamu iya hallakashi farat daya a wannan lokaci saboda zamu fuskanci fishin jama a domin a sannan suna kaunarsa fiye da kai kuma suna matukar jin dadin mulkinsa, dolene sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu wanda zai gane cewar dasa hannunmu, ni abinda nake so dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka kuskura wannan yaro ya san cewa ba kai bane uban sa ba har izuwa tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi akwai ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin idan ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara saimun sha bakar wahala kafin mu sami nasarar hallaka wannan yaro Auwzab nake Typing, kuskuren kuwa shine kada ka kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga ranka domin hakan zata iya faruwa don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga rai Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha bayan kowane kwana talatin, indai kana shan wannan akan lokaci babu yadda za ayi son wannan yaro ya shiga ranka shi kuwa kuskuren da zaka yi na uku ba yanzu zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka sani yayi Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye, jarumai da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya boka barwas ne ya radawa jaririn suna yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna sai da aka kwana ashirin da daya kullum ana gabatar da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa saida akayi ta almubazzaranci tamkar a bola ake tsunto su hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya walima tsawon wadannan kwanaki sarki shardas a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima Hulkas dansa ne na cikinsa wato jininsa ne hm daga wannan rana wani abin mamaki ya fara wanzuwa a cikin birnin romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa a cikin birnin suna tahowa daga manyan kasashe na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu a birnin Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da bai taba yi ba a nahiyar gaba daya nan da nan talauci da fatara suka yaye, arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki iri iri akayi ta shigowa da su birnin da hajoji kala kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a nahiyar fiye da shekaru daruruwa da suka wuce sai da akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba dasu al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata taba tsintar kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato Hailur saita kefe kanta a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda sarki yasan halin da take ciki duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan magani wanda boka barwas ya bashi don kada soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana wani ba a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa da cewa nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin bai rigashi mallakar Hular Lamsara ba a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki shardas baya kusantar shadila don kada ma yayi arba da Jarumi Hulkas hmm Domin zai iya hallakashi nan take saboda zuciyarsa tana tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa na tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar, A kwana a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure duk irin abinda zuciyarsa ke raya masa akan wannan yaro Hulkas har dai aka sami tsawon shekara Uku A sannan ne ya tsinci kansa a cikin tsananin so da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar ba zai iya yin rayuwa ba idan babu shi wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya shaku da sarki Shardas ya zamana cewa yama shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa Shadila har takai cewa ko abinci baya yarda yaci sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai dai ya kwana da yunwa shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana Hulkas yake dinka musu kullum sai dai kaga sunyi anko sunzo fada tare sun zauna akan karagar mulki duk da rana babu abinda yake rabasu kullum .. sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki shardas sannan shadila ke daukeshi tayi masa shimfida a kusa da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka baiga sarki ba sai dai ya fashe da kuka kuma babu mai iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din ita kanta shadila lokacin da taga shakuwar sarki da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk tunanin mai tunani sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta kuskura ta sanar da yarima hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba idan hulkas ya girma A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka na rufe wannan sirri dakuma gargadin da sarki shardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki........ Uhm Allah sarki Shadila Komai Lokacine A nan ne Kuma Ni nake cewa Sai mun Hadu a part Na gaba TSATSUBA Littafi Na Uku (3) Part B. . Idan ta tuna gargadin da sarki Hsardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrinsa sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki haka dai aka ci gaba da wannan rayuwa har yarima hulkas ya cika shekara shida ya zamana cewa gaba daya mutanen kasar Romaniya suna matukar kaunarsa kai ba ma yan kasar ba hatta baki sonsa suke saboda kyawunsa da farin jininsa da kuma kyawawan halayansa da irin hankalin da Allah ya bashi tamkar bai kasance yaro karami ba sannan ga shi Allah ya bashi jin kai da tausayin talakawa sabanin sarki shardas wanda ya kasance Kasurgumin Azzalumin bawa. Gaba daya zaluncin da sarki shardas ke yiwa talakawa sai da yarima hulkas ya hanashi kamar matsa musu wajan karbar haraji mai yawa kai sumame na mamayar bazato a kamo bayi a kwashe dukiyar talakawa sai dai takai cewa duk inda yarima Hulkas ya gifta a cikin nahiyar kasar sai dai kaga jama a suna yi masa kirari da sarkin Gobe Yadda ake yi masa ladabi, biyayya, da girmamawa kuwa ko sarki shardas ba a yi masa haka duk da cewa kuwa ana tsananin tsoronsa hatta a cikin gidan sarautar kwau Bayi, barori, kuyangi da dakari ma suna bin umarnin yarima hulkas tamkar sarki shardas ne yake basu umarnin, kai sai da takai cewa yarima hulkas yana zartar da abubuwa da yawa ba tare da yayi shawara da sarki ba ko da kuwa shi sarki shardas baya son wannan abu ba zaice uffan ba bare ya hanashi Ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin sarki shardas da yarima hulkas boka barwas na lura da shi amma sai yayi shiru baice kala ba wata rana da yammaci sarki shardas na tsaye a can saman ginin wata baranda yake cikin harabar gidan sarautar sai ya hango yarima hulkas tare da mahaifiyarsa shadila sun fito rangadi suna kewaye a cikin gidan sarautar sunta rabawa bay dakaru barori da kuyangi kyaututtuka na suturori kala kala koda ganin wannan al amari sai ran sarki ya baci zuciyarsa tayi bakikirin ya tuna cewa tunda fa aka haifi wannan yaro hulkas rayuwar kasar gaba daya ta sauya duk wani iko nasa kwarjininsa da tsarin mulkinsa ya dakushe ya zama kamar mutum mutumi sai abinda hulkas ya zartar a fada shi ake bi su kansu fadawan sarki shardas basa karbar umarnin sa sai abinda yarima Hulkas ya zartar domin a gaba daya sarakai, attajirai da talakawa sun dauki hulkas fiye da kima wasu ma gani sukeyi kamar ya cancanci a bauta masa kamar yadda ake bautawa sauran alloli na kasar saboda ganin irin abubuwan al ajabin da suka faru daga sa adda aka haifeshi kawo iyanzu duk da cewar yarima hulkas ya sami wannan dama da daukaka bai dauki wani girman kai ba ya dorawa kansa kuma hakan ba ta sa ya raina mahaifinsa ba sarki shardas face ma tsananin sonsa da yake karuwa a cikin ransa, duk abubuwan da yarima hulkas yayi a fada ko yasa aka zartar a kasar sai yaje ya sanar da sarki a yayin da suka kebe kuma ya tambayeshi idan akwai gyara a cikin abubuwan da ya aikata domin yaje ya gyara ko sau daya sarki shardas bai taba nuna cewar akwai abinda hulkas yayi ba dai dai ba bare ma ya nuna masa fishinsa a zahiri ko a badini, haka kuma duk abubuwan da yarima hulkas keyi basu sa shakuwarsa da sarki ta sami rauni ba face ma karuwa da takeyi a kullum su kansu fadawan sarki shardas da duk masu fada aji a kasar suna matukar mamakin yadda wannan al amari ya kasance domin ko a mafarki babu wanda ya taba zaton cewa akwai wani mahaluki wanda zai zo ya iya sauya halayan sarki shardas haka sarki shardas na tsaye a can saman barandar gidan sarautar yana hango yarima hulkas da mahaifiyarsa shadila suna ta raba kyautar suturori ga hadiman gidan sarautar sai tsulum yaga boka barwas ya baiyana a gabansa take boka barwas ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya juyo ya leka kasan barandar ya dubi yarima hulkas da mahaifiyarsa, barwas ya dago kai ya dubi sarki shardas yana mai ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ya shugabana hakika in ba don ina kusa da kai da tuni ka tafka babban kuskuren da zamu hallaka gaba daya duk da cewa kana shan wannan magani dana baka a karshen kowane wata, kaunar wannan yaro a cikin ranka ta gama yin katutu idan baka yi da gaske ba makiyinka zai samu nasara a kanka koda jin wannan batu sai idanun sarki shardas suka zazzaro zuciyarsa ta kufulo har fuskarsa ta kama yatsine saboda fishi ya dubi boka barwas yace yakai dirkar birnin romaniya kayi sani cewa har gobe ban manta da asalin yarima hulkas ba na sani cewa bani da wani makiyi a doron kasa wanda ya fishi don haka duk wannan soyayya da nake yi masa ta banza ce tunda lokaci kawai nake jira wanda zamu tafi neman hular lamsara da ita ne kadai zan sami nasarar hallaka wannan yaro kamar yadda ka fada lokacin da sarki shardas yazo nan a zancensa sai boka barwas ya tuntsire da dariyar farinciki sautin dariyar tasa ne ya janyo hankalin yarima Hulkas da shadila suka Hangosu cikin tsananin farin ciki yarima hulkas ya baro shadila a inda take tsaye ya ruga da gudu izuwa kan matattakalar bene da zata kai shi inda su sarki shardas suke koda sarki shardas ya hango yarima ya taho gareshi sai shima ya tareshi suka rungume juna hulkas na hada idanu da boka barwas sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi wani irin tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa dama duk sa adda yarima yayi arba da boka barwas sai yaji haka Hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas yace yakai abbana kayi sani cewa yanzu nake shirin na tafi zuwa turakarka bayan mun gama raba kyaututtuka ga hadiman gidan nan na nemi wata alfarma guda daya a wajanka Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi murmushi yace haba ya kai dana shin ka taba neman wata alfarma ne a wajena na hanaka? Ai duk abinda kaji zuciyarka tana da muradi kayi nayi maka izini muddin wannan abu ba zai zubar mana da kimarmu da mutuncinmu ba,

Chapter 5 of 21