Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nima nayi amfani da maganar manya da suke cewa idan babba ya rike girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki hanasu kokarin yi mana sata ba dalilin da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko amma yanzu dana gane cewar wata kila kina da mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki ladabi da biyayya larbisa ta bushe da dariya sannan tace ai kowane mutum yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya gaya mini babban burinku na duniya keda mahaifinki wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a kansa? Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down ) zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi zama na musamman mu dake kuma a sannan ne muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace tabbas zancenki dutse ne, haka dai shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan suka kwanta sukayi barci, kamar yadda aka karrama sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki humaisu da dukkan dakarunsa suka ci suka sha sukayi hani'an kuma suka kwanta a masauki mai kyau Al amarin da yayi matukar daure musu kai kenan suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan mafarauta suka tara arziki mai yawa haka ++ Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo musu abincin kalaci ba kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama kimtsawa kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar tattaunawa akan abubuwan da muka sa a gaba koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri cikin murna ta bi shumaira a baya suka fice daga cikin dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da iyayen shumaira suke, sai da sukayi yar tafiya mai dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai dauke da Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda biyar tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike tsaye suna musu girmama sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa nan take larbisa da shumaira suka janyo kujeru daga cikin karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi gyaran murya yace yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya mana abin da ya kawoki garemu kafin muma mu gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi gyaran murya tace ba wani abu bane ya sa na baro kasata ba mulkina da jama ata face don na riski kogon Kitabul sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban burina na duniya na samun damar yin aure gami da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake cikin wannan duniya ba zan iya isa inda kogin yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma wanda ke dauke da mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki wanda zai iya wucewa dani ta cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira daga nan ne zamu wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake kira darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina muna wuce wadannan dazuzzuka sai kuma mu tunkari dajin da kogon Kitabil sihir yake shi kuwa kogon babu mai iya yi mana jagora izuwa cikinsa face jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa A cikin kogon kitabul sihir ne zan iya dauko littafin TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake cikinsa don na sami damar yin aure na sami da ko yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai cikaba Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da ya baiwa larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa.. Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul Shumaira ina dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa abinda kaji na fada??..TSATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part B. . Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala da bata da misali kuma dake da duk abikan tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku. Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a taba samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye ba don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !! Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa iyayena da kakannina domin suma sun bar gida sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda daya wadda ke shafin tsakiya , yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda mu ne kadai mukayi saura kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa ta daukeni shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa zama a cikin gari lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi wannan tafiya dani da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara na kwato mana yancinmu. koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama saita tayasu kukan Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane ya janyo hakan ba face ganin matsalar ta tazo iri daya da tasu Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa daga cikin na shumaira ya dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya ba don haka duk shirinta ya rushe, Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi sai shumaira da sarauniya larbisa suka kasa barci saboda zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen shumaira zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike zaune daga kan gadonta ta dubi larbisa tace ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda zai biyo baya ba zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani abu da ya shiga raina sama da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan mutu nafi son na mutu jaruma akan na mutu raguwa a cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu saboda haka yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji hukuncin da ya yanke koda gama fadin hakan sai shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma zuciyarta na dukan uku uku tana fargabar abinda zaije ya dawo lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye shi kuwa tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar ba zata iya tunkararsu da maganar ba tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki kawai sai shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira , kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar magana koda shumaira ta juyo tana mai amsa kiransa saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi da annuri cikin mamaki shumaira ta tunkari mahaifin nata ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna tsoho Imshal ya dafa kafadar shumaira yace, yake yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya hanaki yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda kiyi wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi tace haba yakai Abbana tayaya zanyi wannan tafiya tare daku alhalin girma ya kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar nine na koya miki yadda ake farauta a cikin daji da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka?? To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata wawa malami har abada malami ne akan dalibansa ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki zamu baku gagarumar gudumawa a cikin wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda haka ki koma dakinki ki gayawa sarauniya larbisa cewar ku fara shirin wannan tafiya tun a daren yau amma ina son ta turo mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas yanzu take kuma ta gaya masa cewa ya taho tare da jakar sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa lokacin da shumaira ta isar da wannan sakon mahaifinta izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin mamakin yadda akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri alhalin bata gabatar dashi ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin abinda ke boye ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan sai huzallatul marwas ya bushe da dariya Al amarin da ya baiwa larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi a fusace tace menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari?? Huzallatul marwas ya numfasa yace hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin ban taba zaton zai gano da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun jakar sihirinsa babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin naji dalilin da yasa ya bukaci ganina, koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas ya yunkura da nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake Tsulum sai suka ga aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai kyalkyala dariya lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana kayi sani cewa zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare da sarauniyarka komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu dalilin da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat, sai jin motsinsa yayi a cikin jakarsa ta sihiri Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene abinyi? Larbisa tayi murmushi tace yadda Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka iskeshi tare da yarsa shumaira da matarsa larisa a zaune koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul marwas sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi larbisa yace ai sai ku bamu wuri don ina son na gana da huzallatul marwasu koda jin haka sai huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace yana daga cikin sharaddan tafiyarmu nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata komai ba koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai sai ya kyalkyale da dariya ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban da babban aboki ma abocin hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu kama hanya dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka juya suka fice daga cikin falon, fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin damuwa tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin da ya kamata mu karanta a cikin littafin tsatsuba domin kawai da wannan matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara? Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka ya fika dabara kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka mallaki littafin tsatsuba a hannunmu munyi mai wuyar da sannu zamu gano duk wani sirri dake cikinsa da jin wannan batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta tuno irin mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi wannan tafiya sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi haka dai ta yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki ta tafi izuwa turakarta kashegari kuwa tun kafin Alfijir ya keto kowa ya gama shirin tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba jaruma shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin dakarun larbisa ma suna gabanta bayan an shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a lokacin da suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu yace ya shugabata kiyi sani cewa ruwa baya tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da rayuwarsu wajen biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske. Yayinda sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a jeba . Kamar yadda sannu sannu ba zata hana ci gaba da rubuta muku wannan littafi ba saidai a jima ba ajeba.. A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe domin jin Yadda zata kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba TSATSUBA Littafi Na Biyu (2) Part C. . YAYINDA SARAUNIYA larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul marwas ya gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne? Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda abinki ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan nake bi damu Amma ai idan baki manta ba zamuje neman jaruma larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar zamu riske ta bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa. Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara cewa komai ba haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango face gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana uku sannan suka iso wani babban birni mai kyau gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu kyau da kawa ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma tana cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za a taba samun birnin da yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi tun kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba haka bane Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka hango tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar manyan mutane ne masu daraja sai suka bude musu kofada sauri har daya daga cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma shumaira ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai shin mu yanzu menene yashigo damu cikin wannan gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma ga yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa ba a cikin gari sai dai a daji? Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace ai da dan gari akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi neman jaruma larifat bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda take wata kilama mu sami karin haske akan yadda zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci wata matsala ba koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba... Fadace kasaitacciya abar kwatance domin lokacin da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar sai gaba dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar yan kauye saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake bangarenta babu wata kasa mai girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai ta fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a taba samun kamarta ba amma a yanzu da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da wannan bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani kyakkyawan saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin wannan fada ya yi babbar shiga ta alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka gawurta ne kadai ke iya yinta domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da kwagirin dake hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma duk na zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin dake kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren zinare a aka dinkasu koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da kwarjininsa ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da tsananin sonsa Hakika babu wata 'ya mace da zata ga wannan sarki bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda baiwar da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska kuma babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya dugunzuma hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu bare kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi cirki cirko caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba wani abu bane ya kawomu birninka ba face neman jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin ujurul majnun domin biyan wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa. Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da annuri ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su sarauniya larbisa ma sai yasa aka basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka kama kimtsa cikinsu suna masu murna da mamakin yadda akayi nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin abindake tafe dasu sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa sosai sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau shekara bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata taba kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau bakwai sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma bata taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi mini magana ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa wannan gidan sarauta Lokacin da na dameta da aika manzanni da kyaututtuka iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini dasu gami da wasika A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina bata lokaci na da tunanina a kanta domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata taba yin aure ba ko soyayya har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani bai taba yi ba a duniya lokacin da naji wannan batu sai na kamu da tsananin bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici domin banga ranar da larifat zata cika wannan buri ba daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a wuri mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji cewar ta sami damar da zata cika burinta A tsawon shekaru bakwai da suka gabata wannan dama bata samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan batun na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba yake sai naji a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a gareni domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har abada ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka babu na san cewa larifat zata karbi wannan tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu wanda zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta cikin dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta burin ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan uwanta da dukkan danginta bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin mutane ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa sauran rayuwarta gaba daya yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat take domin ku gana da ita, ku sanar da ita bukatar dakuka zo da ita a gareta. Amma ina neman wata alfarma guda daya a wajanku? Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi kuka barni fargaba tunani da begen halin da larifatke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa sai kowa ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa da shumaira Kai ni kAina saida na cika da mamakin wannan sarki sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka sani cewa akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da rayuwarka don baiwarka? Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya kamar ba zai daina ba

Chapter 3 of 21