Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinda ya faru ba sai yanzu da nake sanar dakai saboda zuciyata ta yarda kuma ta aminta cewa kaine jarumin da zai kawo karshen zaluncin shugaban azzalumai na bil adama wato sarki shardas koda siyama tazo nan a zancenta sai yarima hulkas yaji gaba daya tsigar jikinsa ta tashi kuma yaji cewa a zuciyarsa ta aminta da duk abinda siyama ta fada dari bisa dari saboda haka sai ya sake kamo hannayanta ya rike yace yake yar uwata kiyi mini Alkawarin cewar zaki kasance a tare dani a cikin wannan doguwar tafiya da zamuyi ta neman hular lamsara kuma zaki taimakeni da ranki da dukkan karfinki kuma babu abinda zai rabamu face mutuwa domin a yanzu ne na tabbatar da cewa kece rabin jikina idan babuke babu abinda zan iya aiwatarwa na dangane da babban burin dake gabana saboda ra ayina ya kasance iri daya da naki kinga kenan burinmu duk iri daya ne ni dake koda jin wannan batu sai siyama ta rungume yarima hulkas ta fashe da matsanancin kuka Al amarin daya karya zuciyar sa ke nan shima ya fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu Lokacin da dare ya soma yi ne wata kuyanga ta taho turakar gimbiya luzuraina ta risina ta kwashi gaisuwa gareta sannan tace ya shugabata sarkine ya aikoni nayi muku jagora zuwa dakin walima ke da amarya shadila koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube luzuraina da shadila dama tunda aka watse aka barsu su biyu suna ta hira ko gyangyadi basuyi ba tuntuni duk su biyun sun caba ado don haka sai suka mike tsaye zumbur da nufin su fita amma sai shadila ta rike hannun luzuraina suka tsaya ta dubeta tace ba zan iya zuwa wannan dakin walima ba face bisa jagorancin abokiyar zamana zalina don haka sai dai mu biya ta dakinta mu tafi tare, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi tace ai rashin hakuri kikayi ai dole ne mu nemi sa hannun uwar gida a cikin wannan al amari don haka muje gareta yanzu Nima kuma bari naje ga neman kudina yanzu Kafinnan Nidinne dai Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson Ko Asquare nake cewa mu zama lafiya it's Real Al amin Ahmed Misau TSATSUBA Littafi Na Bakwai (7) Part D. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai luzuraina ta kama hannun shadila tajata suka fice daga cikin dakin itama wannan kuyanga da tazo domin tayi musu jagora izuwa dakin walimar sai ta koma bayansu sukayi ta ratsawa ta gaban dakarun dake tsaron gidan sarautar suna wucewa ta cikin kofofi Abinda ya daure musu kai shine a wannan dare gaba daya hadiman gidan sarautar babu su wadanda komai dare a cikin kai kawo suke suna gabatar da ayyukansu su kansu dakarun tsaron a yau sun kasance kalilan basu da yawa kuma sune amintattu wadanda koyaushe suna tare da sarki basa rabewa koda ganin wannan sauyin yanayi sai mamaki ya turnuke shadila ta dubi luzuraina a cikin dan alamun tsoro tace yake kawata menene dalilin daya sa naga komai na gidan nan ya sauya a wannan dare ba haka na saba ganin abubuwa suna gudana ba, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi tace ba komai ne ya kawo haka ba face tabbatar da sirrin daurin wannan aure da zai gudana daga sanin makiyanmu. Koda jin haka sai farinciki ya lullube shadila ta kama murmushi tayi shiru bata ce komai ba, haka dai suka cigaba da tafiya suka iso kofar dakin da zalina take, da isowarsu sai luzuraina ta kwankwasa mata kofar tace yake uwargidan hailur ki fito ki raka amaryarki izuwa ga angonta kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni an bude kofar dakin kawai sai suka ga zalina tsaye a gabansu ta caba ado na gaban kwatance tamkar itace amaryar kuma fuskarta cike da annuri gami da murmushi kana kallonta ka san cewa tana cikin matukar farin ciki tana ganin shadila sai ta rungumeta tamkar wacce taga yar uwarta ta jini sannan ta kama hannunta tajata suka yi gaba tana mai cewa muje na damkaki a hannun masoyinki na kwarai koda jin wannan batu sai shadila da luzuraina suka cika da mura nan take wannan kuyanga ta shige gaba tayi musu jagora izuwa dakin walimar, falo ne babba mai matukar tsawo da fadi wanda sarki hulbasu ke yin babban taro a cikinsa musamman a lokacin da ya gaiyato manyan baki daga kasashen duniya babu kowa a cikin wannan babban falo face sarki hulbasu hailur da yarima hulkas dakuma jaruma barmas sai kuma amintattun hadiman sarki hulbasu da amintattun kuyanginsa gaba daya teburan dake xikin wannan falo an cika samansu da kayan alatu na abinci dana shaye shaye kala kala na alfarma babu irin kalar da babu, a gefe daya kuma wadansu makadane da mawaka na sarki suma amintattunsa ne wadanda babu yadda za ayi su bayyana sirrinsa domin tun zamanin kakansa suke yin wannan aiki A can wani bangare na daban kuma wadansu kyawawan yan mata ne su takwas sanye cikin fafaren tufafi wadanda suka kasance yan rawa sun kama tamkar gumaka da babu ruhi a jikinsu koda shigowar amarya shadila da su zalina cikin wannan babban falo sai makada suka fara wani irin kida mai taushi da dadin gaske su kuma wadannan yan mata yan rawar dake kame suka fara yin rawar Mawakan kuwa sai suka kama rera wata irin waka mai dadi suna ambaton sunan shadila suna kodata gami dayi mata kirari nan take wannan al amari yayi matukar burge kowa a wajan Abdul Aziz sani Madakin gini yace' Hatta ni da nake baku wannan labari ban san sa adda na kama yin rangaji ba ina jin wani irin nishadi da farinciki a zuciyata' sannan kuma Ni Al amin Ahmed Misau wanda nake typing din littafin nan nima na dan tsaya da typing din na fara takawa oyah uhm gaskiya ne..... Bayan mawakan sun gama koda amarya shadila saikuma suka kama wasa ango hailur shima suna yi masa kirari bisa irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa tamkar a gabansu komai ya wanzu dolene abin ya burge mutum saboda irin hikimar da aka yi amfani da ita kuma dole ne mutum yaji ya kamu da tsananin tausayin wannan ango da amarya domin kuwa a takaice aka bayar da tarihin soyayyarsu da yadda aka rabasu da karfin tsiya hatta sarki hulbasu dasu yarima hulkas basu san sa adda suka kama zubar da hawaye ba nima Al amin Ahmed Guyson Saida na zubar marubucin littafin ma yace Nikaina a yanzu naji idanu na sun ciko da kwallah ana cikin yin wannan waka ne falon yayi tsit tamkar babu wani mahaluki daya mai numfashi a cikinsa sakamakon tsayuwar masu kida da wakar suma yan matan nan yan rawa suka kame kam yayinda ni kaina Al amin Na kame kam, A dai dai wannan lokaci ne kofar falon ta bude sai ga sadauki ruhaisu ya shigo tare da wani dattijo wanda shima asalinsa dan kabilar su hailur ne kai tsaye suka nufi inda hailur da shadila suke suka kamo hannayansu suka taho dasu izuwa tsakiyar falon suka daura musu sabon aure bisa al ada irin tasu faruwar hakan keda wuya sai yanayin sararin samaniya ya sauya nan take ya zama tamkar na damina hadari ya gangamo aka fara wata irin TSAWA DA WALKIYA mai tsananin ban tsoro A dai dai lokacinne da wannan abu ya faru sarki shardas na cikin wani kurgurmin daji tare da bokansa abin dogaronsa sun yada zango a cikin wani kogon dutse suna barci amma ana tafka wannan tsawa sai sarki shardas ya farka firgigit A firgice zuciyarsa na daka da karfi, babu abinda ya fado masa a Rai face matarsa shadila, take yaji a jikinsa cewa lallai wani abune ya faru ga shadila domin wannan tsawa da walkiya da aka tafka ba na zahiri bane ishara ce, Aljanunsu na tsafi suka yi masa bisa abinda ya faru cikin gigita sarki shardas ya tashi bokansa daga barci ya dubeshi yace yakai abin dogarona kayi sani cewa lallai akwai wani abu ya sami matata shadila maza ka duba mini abinda ke faruwa koda jin wannan batu sai bokan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi sarki shardas cikin nutsuwa yace ya shugabana ai dama tun kafin mu baro gida idan baka manta ba na gaya maka cewa a cikin wannan tafiya da yarima hulkas zaiyi ne zai sami damar da zai iya cutar da kai to ka sani cewa duba maka wannan al amari ba zai haifar da komai ba face dakushe maka zuciya gami da karyar da ita akan babban aikin dake gabamu na nemo inda hular lamsara take ka sani cewa baka da wata mafita wacce tafi ka hanzarta mallakar wannan hula ta lamsara kafin makiyanka su rigaka lallai kana da babbar dama ta samun haka tunda ka rigasu fitowa neman nata amma ko yaya ka darsa batun soyayyarka akan shadila a cikin ranka to lallai zaka rasa nasara koda bokan yazo nan a zancensa sai hankalin sarki shardas ya dugunzum ainun fiye da ko yaushe ya dubeshi a fusace sa adda zuciyarsa ke tafarfasa yace ka gaya mini cewa mun fito ne neman wani Aljani wai shi arwasul masadul kuma tunda muka baro gida muke ta keta dazuzzuka birane da kauyuka barkatai amma ko alamun wannan aljani bamu gani ba bamu san yaushe zamu hadu da shi ba, kuma bamu san a inda zamu ganshi ba anya kuwa baka ganin cewa wahalar banza muke yi ? Koda sarki shardas yazo nana a zancensa sai bokan ransa ya baci yace Al amin ahmed Misau ; guyson Sunana Ko A square ashe akwai ranar da zaka yi kokwanto akan abinda zan gaya maka shin ka manta ne cewa nine na tsareka na baka dukkan kariya daga sharrin dukkan makiyanka tun kafin ka hau karagar mulki shin ka manta cewa zuri ar gidanmu sun shafe sama da shekaru dari suna bauta a gidanku cikin amince da kauna ?? Babu yadda za ayi na bata yaudararka ko na gaya maka karya dolene ka kasance mai hakuri gami da juriya komai dadewar shekarun da zamu yi muna yin wannan tafiya kafin mu hadu da aljanu Arwasul masadul koda kuwa sai mun tsofe tukuf fatanmu dai shine nasara da sa'a koda gama fadin hakan sai bokan ya koma ya kwanta yaja bargonsa ya lullube jikinsa gaba daya saboda hunturun sanyin dake kadawa a cikin dajin yaci gaba da barci abinsa tamkar a cikin dakin matarsa yake a lokacinn da kuune baya jin sautin komai face na manyan dabbobin daji ababan tsoro shi kuwa sarki shardas saboda zuciyarsa na suya don tsananin fushi idanunsa sun bushe babu alamar jin barci kuma ko kadan baya jin uban sanyin da ke kadawa haka dai ya zauna yana ta tunanin zuci gami da wasu wasi a ransa bisa yin abinda yake ganin cewa shine zai fishsheshi wata zuciyar tace dashi : wai shin yama za ayi ace duk irin wannan masifaffen karfin damtsen nawa da kuma karfin sihirin tsafi ace ba zan iya kashe wannan yaro hulkas ba ? Wai shin ma menene dalilin da yasa duk abin da wannan bokan yazo mini dashi sai na amince shin bokaye basa yin karya ko kuskure ne a bincikensu da furucinsu,? Aljanu ne fa suke sanar dasu komai kuma su kansu aljanun suna shirya karya kuma suna yin son zuciyarsu kamata yayi na yi watsi da shawarar wannan boka akan batun neman wannan hula ta lamsara kawai na juya da baya na tafi izuwa birnin hulbasu naje na kama yarima hulkas a gaban mahaifiyar tasa shadila nayi masa yankan rago duk da cewa ina kaunarsa !! Al amin Ahmed Misau, koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa kuma wata zuciyar tasa ta daka masa tsawa tace shin baka da hankali ne yanzu kana nufin kace zaka yanka yaron da ka raina da hannunka wanda ka kaunaceshi tamkar dan cikinka, idan har zaka iya aikata hakan to tabbas dan da ka haifa da kanka ma zaka iya kasheshi !! Koda gama aiyana hakan sai hawaye ya zubo wa sarki shardas a karo na biyu ya kishingida akan shimfidarsa ya lumshe idanunsa domin yayi barci amma sai barcin ya gagara A takaice dai yadda yaga rana haka yaga dare da asubar fari boka nata faman shara barci abinsa sai sarki shardas yaji yana sha awar ya shiga daji yayi farauta ko ya harbo wani tsuntsu ko kuma ya samo musu dabbar da zasu yi kalaci da ita saboda ya gaji da cin irin abincinsu na guzuri wanda suka tanada, ba tare dasarki shardas ya tashi bokansa daga barcinsa ba sai ya mike tsaye ya dauki damararsa ya daura ya gyara zaman takobinsa a cikin kufenta sannan ya dauko kuttun kibiyoyinsa ya sakashi a kafadarsa ya rike sandar bakan a hannunsa yana gama wannan shiri sai ya fice daga cikin wannan kogon dutse da suka kwana yana sanda don kada ma boka labarusa ya farka daga barcin ya hanashi fita wannan farauta, nan da nan sarki shardas ya kutsa cikin dajin yayi nisa cikinsa yana ta dube dube leke leke da neme neme sama da kasa gabas da yamma kudu da arewa a cikin kowanne sako kwari da tudu har cikin ramuka sarkakiya da duhuwoyi amma ko gafiya bai Gani ba bare ya sami abin farauta har tsawon sa'a guda Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan nan har tsoro ya dan darsu a cikin zuciyarsa yace ya za ayi ace duk girman wannan daji da kuma tarin ni'imar dake cikinsa amma ace babu dabbobi dake rayuwa a cikinsa? Ko dai wata annoba ce ta kashesu gaba dayansu a lokaci guda ? Idan hakane kuwa ai yakamata ace annobar ta bar gawar koda daya ne daga cikinsu, koda sarki shardas ya gama aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai yaji wata irin iska mai karfin gaske ta giftashi ta samansa, cikin hanzari ya daga kansa sama domin yaga ko menene ya gifta din kawai sai yaga ashe wata jibgegiyar halitta ce mai manyan fuka fuki amma saboda tsananin karfin gudunta ya kasa gane ko dabba ce ko aljan ko kuma tsuntsu domin kafin giftawar ido halittar ta bace a cikin sararin samaniya cikin matukar karfin hali sarki shardas ya yunkura da nufin ya tashi sama da karfin sihirinsa na tsafi amma sai yaji ya kasa tashi saman al amarin da yai matukar razanashi kenan kuma yai matukar bashi mamaki saboda wannan shine karo na farko a rayuwarsa da ya taba jarraba amfani da karfin sihirinsa na tsafi yaki yayi tasiri amma da yake shi sarki shardas mutun ne wanda bai san tsoro ba kuma yana da dakakkiyar zuciya sai kawai ya falfala da masifaffen gudu yabi bangaren da wannan jibgegiyar halitta tabi, sai da ya shafe sa a guda yana gudu yana daga kansa sama ko zai hango halittar kuma yana duba kasa ko zai ga alamun sawunta idan ta sauko kasan amma bai gani ba, kwatsam yana cikin falfala wannan azababben gudu da dube duben halittar nan ko sawunta kawai sai ganin wani katon kogi yayi a gabansa saura kiris ma ya fada cikinsa yayi turjiyar bazata ba a bakin gabarsa cikin tsananin sauri da zafin nama, tsayuwarsa a gaban kogin keda wuya sai yaga tsakiyar kogin ya kumburo sama wani abu mai girman gaske na shirin fitowa daga karkashinsa aikuwa kafin yayi wani yunkuri sai ga wannan jibgegiyar halittar ta taso izuwa saman kogin ta dora kafafunta guda hudu a samansa tamkar kasa ta taka ita dai wannan halitta mutum bai isa yace ga abin da take kama dashi ba ita ba tsuntsuwa ba, ita ba dabba ba, kuma ba aljana ba tana da tsananin muni gami da matukar kwarjini da ban tsoro kawai sai halittar ta juyo da kanta ta kurawa sarki shardas idanu ba tare da tayi wani yunkuri ba koda ganin hakan sai sarki shardas ya durfafi halittar har sai da yaje dab da ita sannan ya dubeta ba tare da nuna alamun wani tsoro ba yace yake wannan halitta waye kai kuma menene dalilin da yasa kaine kadai halittar dake rayuwa a cikin wannan daji mai tarin ni'imomi haka ? Al amin Ahmed misau Guyson koda jin wannan tambaya sai halittar ta bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da saukar kwarankwatsa tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba lokaci guda kuma sai ta turbune fuskarta ta dubi sarki shardas cikin nutsuwa tace yakai wannan hatsabibin bil adama kayi sani cewa babu wata dabba ko wani kwaro ko mutum ko aljan da ya isa ya shigo cikin wannan daji har ya rayu na tsawon dakiku dari face ya kasance mashahurin matsafi abin kwatance don haka nayi maka jinjina kai da bokanka labarusa kafin halittar ya gama rufe bakinsa tuni sarki shardas ya tari numfashinsa yana mai cewa wane ne kai kuma menene dalilin da yasa wannan daji ya zama daban da kowanne daji dake nahiyar nan koda jin wannan tambayoyi sai halittar ta sake bushewa da dariya akaro na biyu sannan tace ni kaina bansan kaina ba tunda ban san asalina ba amma dai na san na kawo i yanzu babu uwa babu uba don haka ko suna bani dashi, koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata, sannan nima Al amin Guyson na fusata ya dubi halittar cikin fishi tare da daka mata tsawa yace kada ka raina mini hankali mana ai ko a ina ka rayu zaka iya sakawa kanka suna ko kuma a saka maka tunda ba zai taba yiwuwa ba ace ka ray a inda babu aljan ko mutum koda jin haka sai halittar tayi murmushi tace yakai wannan sarki kayi sani cewa hakuri na daya daga cikin tafarkin dake kai mutum izuwa ga nasara bisa abinda yasa a gabansa kai kuwa baka da hakurin sarki shardas najin haka sai ya kara fusata da fishi mai tsanani ya zare takobinsa ya dubi halittar cikin fushi yace tabbas bani da hakuri kuma babu wani mahaluki wanda ya taba gaya mini magana haka cikin gadara kamarka haka kuma babu wani abu da na taba sashi a gabana ba tare da nayi nasara ba saboda haka kaima sai na jarraba sa a ta akanka domin na san ko kai waye ne koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daka tsalle sama tamkar an harboshi daga cikin baka yayi sama izuwa kan halittar yakai mata wawan sara a wuya cikin bakin zafin nama halittar ta sunkuya takobin sarki shardas ta sari iska kafin sarki shardas yayi wani yunkuri tuni halittar ta maka masa jelarta akan kirjinsa saboda karfin dukan sai da sarki shardas yayi baya a sama tamkar an janyeshi da majajjawa yaje ya gwara bayansa a jikin wata katuwar bishiya sannan ya fado kasa tim a cikin matukar galabaice yana kumallon jini ta baki da Hanci kuma ya kasa mikewa tsaye koda halittar taga ta sami wannan nasara sai ta bushe da dariya tare da bude fuka fukanta tayi sama tana mai cewa ya kai wannan sarki hakika ka cika wahalalle kuma asararre domin girman kanka da rashin kunyar ba zasu taba kaika ga samun nasara akan abinda ka sa a gabanka ba ina yi maka bushara da cewa kayi babbar asarar damar da ba zaka kara samun kamarta ba kafin sarki shardas ya daga kansa sama domin yaga bangaren da halittar tayi a sama tuni halittar ta bace bat a cikin gajimare tamkar bata taba wanzuwa ba....... . SHIN WANNAN WACCE IRIN HALITTA CE . SHIN WACCE IRIN DAMA SARKI SHARDAS YAYI ASARA WADDA BA ZAI SAKE SAMUN KAMARTABA? . YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA HAR YA GA BAYAN MAKIYINSA DA YA DAUKA A MATSAYIN MASOYINSA WATO SARKI SHARDAS ? . INA LABARIN SU SARKI HULBASU DA HAILUR DA SABUWAR AMARYARSA SHADILA DA AKA SAKE DAURA MUSU AURE A BIRNIN SARKI HULBASU ? . SHIN SU SARKI HULBASU SUNA SAMUN NASARAR HALLAKAR DA DAKARUN DA SUKA YOWA SHADILA RAKIYA BA TARE DA SUN BAR KODA DAYANSU YA TSIRA BA BALLE YAJE YA SANAR DA SARKI SHARDAS ? . WANNE IRIN AZABABBEN YAKI ZA AYI A GABA ? . SHIN YARIMA HULKAS YANA FADAWA TARKON SOYAYYA WADDA HAR ZATA ZAMO SANADIN RASA RAYUWARSA ? . TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA ? . SHIN AL AMIN AHMED GUYSON ZAI SAMU DAMAR KAMMALA MUKU WANNAN TYPING DIN ? . Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Wato Littafi Na 8 Don Jin Cigaban Wannan Kayataccen Kasaitaccen Labari wanda ni Al amin Ahmed Misau Nake Jagorantar Typing Dinshi kuma mai son ganin Farin cikinku nake cewa sai Allah Ya kaimu Gobe A littafi na TSATSUBA Littafi na takwas 8 Abdulaziz sani m gini Made by Shuraih Usman @http://fb.com/hausaebooks TSATSUBA Littafi Na Takwas (8) Part A. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau (Guyson) Ke Magana. . Kuyi hakuri jiya kunjini shiru wasu matsaloli ne suka sha kaina . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . LOKACIN DA WANNAN SIHIRTACCIYAR halittar ta make sarki shardas ta luluka sararin samaniya ta bace, a dai dai wannan lokaci ne boka labarusa ya karaso bakin kogin a guje ya isa inda sarki shardas ke kwance yana kumallon jinin koda yaga halin da sarki shardas yake ciki sai ya dimauce hankalinsa yayi matukar dugunzuma nan da nan cikin hanzari ya bude jakarsa ta guzuri ya dauko wani garin magani ya hambadawa shardas a bakinsa ya hadiye sannan ya dauko wani farin mai ya shafe kirjinsa dashi faruwar hakan ke da wuya sai sarki shardas ya daina kumallon jinin da yake yi idanuwansa da suka wurkile suka zama jajaye sai suka dawo dai dai kuma ya dawo cikin hayyacinsa alhalin da yana . Numfashi sama sama A sannan ne boka labarusa ya dubeshi cikin girmamawa yace ya shugabana menene dalilin da yasa ka baro can kogon dutse inda muke kwance kazo nan kuma menene yayi maka wannan mugun naushi a kirji haka wanda in ba don kana da nisan kwana ba da tuni ka dade da shekawa barzahu ? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya kawo gwauron numfashi ya ajiye cikin tsananin mamaki gami da takaici sannan ya dubi boka labarusa yace yakai dirkar birnina kayi sani cewa ba komai ne yasa na baroka ba a can kogon dutse sai saboda ina sha awar na shiga daji nayi farauta na samo mana naman da zamu yi kalaci dashi saboda na gaji da irin abincinmu na guzuri, nan dai sarki shardas ya baiwa boka labarin duk abinda ya faru gareshi har izuwa sa adda ya hadu da wannan shirgegiyar halitta da yadda aka sami sabani a tsakaninsu har yayi yunkurin hallakata a karshe kuma sai tayi masa duka daya wanda yai matukar galabaitar dashi, koda boka labarusa yaji wannan labari sai ya kurma uban ihu cikin tsananin takaici ya dubi sarki shardas a fusace yace, saboda me zaka zubar mana da wannan gagarumar dama da muka samu ?? To ka sani cewa wannan halitta ba komai bace face Aljani Arwasul masadul wanda muke nema ruwa a jallo shin ka manta ne na fada maka cewa duk mutumin da ya hadu dashi sai yayi masa jarrabawa tukunna sannan zai amince ya yarda dashi har ya taimakeshi ? A cikin jarrabawarsa guda goma guda daya jal yayi maka yanzu kuma gashi ka fadi, haduwa da aljani arwasul masadul sai babbar sa a bare mu sami damar haye ragowar jarrabawar tasa guda tara yana yin Adalci guda daya idan mutum yaci jarrabawa biyar daga cikin goman yana iya taimakonsa kaga kenan yanzu ka fadi jarrabawar farko, Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square koda boka labarusa yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki shardas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda yake masa dadi a duniya kuma ya kamu da tsananin takaici gami da bakin ciki mara misaltuwa saboda haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba wanda amsa kuwwarsa ta cika dajin gaba daya har kwallar nadama ta cika masa idanu, koda ganin halin da sarki shardas ya shiga sai boka labarusa yaji ya kamu da tausayinsa don haka sai yazo daf dashi ya zauna ya tallafo kafadarsa izuwa kan kirjinsa yace ya shugabana kayi sani cewa mai dukkan rai baya cire tsammani da samun rabo don haka muna da sauran dama wacce indai muka yi amfani da ita zamu iya kaiwa gaci, tashi mu ci gaba da tafiya tunda dai himma bata ga rago kuma mai nema yana tare da samu, koda jin wannan batu sai sarki shardas yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi don haka sai ya mike tsaye da sauri cikin matukar kuzari ya dafa kafadar boka labarusa ya dubeshi cikin murmushi yace kayi gaskiya yakai amintaccena kawai mu kara himma nan take suka juya suka koma izuwa wannan kogon dutse inda suka yada zango Wannan shine abinda ya faru ga su sarki shardas da bokansa boka labarusa a cikin tafiyarsu ta neman hular lamsara '' '' '' LOKACIN da aka tafka wannan tsawa da walkiya bayan sake daurin auren shadila da hailur sai kowa dake cikin dakin walimar yaji zuciyarsa ta buga da karfi kuma tsoro ya baibayeshi amma sai aka basar aka cigaba da shagali har sai da aka kammala komai ango ya tafi da amaryarsa izuwa masaukinsa dake cikin gidan sarautar taron ya watse kowa ya kama gabansa lokacin da ango hailur ya kadaita da amaryarsa shadila a cikin daki tana zaune akan gado ta sha lullubi kanta na sunkuye tana wasa da yan yatsun hannunta koda hailur ya kamo hannunta da lafiyayyan hannunsa sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta dago kai ta dubeshi cikin murmushi da tsananin farin ciki a lokacin da hawaye ya subuto mata, koda ganin wannan hawaye sai tsoro ya kama hailur ya dubeta a firgice yace yake masoyiyata ina dalilin zubar wannan tsadadden hawaye nakai mai tsada? Shadila ta sake yin murmushi a gareshi a karo na biyu sannan tace yakai abin begena dare da rana ka sani cewa ba komai ne ya sakani wannan zubar hawayen ba face tsananin farin ciki na tunowa da daren farko na auranmu ni dakai ka tuna cewa daga wannan dare ban sake jin dumin jikinka ba a jikina, kuma ban sake ganinka ba sai a yau bayan shudewar wadansu shekaru dana jima da fidda rai da sake ganinka a wannan duniyar har abada na rantse da darajar iyayena daga yau ba zan sake yarda wani abu ya Rabamu ba face mutuwa domin a yanzu daka dawo gareni ka zama rabin ruhina idan babu kai ba zan iya cigaba da rayuwa ba a doron wannan kasa koda shadila tazo nan a zancenta sai farin ciki ya sake lullube hailur ya rungumeta kuma ya kai hannu izuwa fitilar dakin ya kashe ta, Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana Kenana, wannan shine abinda ya faru ga sababbin ma aurata wato hailur da matarsa shadila bayan an sake daura aure a karo na biyu '' '' '' ACAN dakin yarima barmas kuwa sai da suka kusan raba dare suna hira shi da yarima hulkas akan masifar da suke ciki ta sharrin sarki shardas idan har ya gano halin da suke ciki, suna fara yin wannan hira sai yarima barmas yaga yarima hulkas yayi shiru yana tunani daga can kuma sai idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye koda ganin haka sai

Chapter 15 of 21