Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shima yarima barmas hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ya kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ya shiga rarrashinsa yana mai rokonsa da ya cire komai daga ransa cikin sanyin jiki yarima hulkas ya mike zaune daga kwancen da yake ya dubi yarima barmas cikin nutsuwa yace yakai abokina ka yi sani cewa ba komai bane ya jefani cikin mugun bakinciki da takaici ba face rashin sanin cewa sarki shardas bashi bane mahaifina na jini Na dauki duk wani SO DA KAUNA ta duniya na bashi a zatona mahaifina ne shi, lallai bani da burin da yafi naga na kasheshi da hannuna domin na huce takaicin iyayena haka dai yarima barmas ya cigaba da rarrashin yarima hulkas amma sai ya zamana cewa shi yarima barmas din ne yayi barci ya bar yarima hulkas da kuma Yarima Al amin Ahmed Misau hm, a zaune zuciyarsa cike da tarin bakin ciki gami da sake sake har gefen asuba idanun yarima hulkas a bushe suke koda yaga barcin ya kauracewa idanunsa sai ya mike ya fito daaga cikin turakar yarima barmas din ya kama kai kawo a cikin harabar turakar, yana cikin wannan hali ne kwatsam yaji wata irin iska mai matukar karfi daga sama ta lullubeshi kafin yarima hulkas yayi wani yunkuri ko ya daga kansa sama yaga abinda ya haifar da iskar sai kawai yaji an sunkuceshi anyi sama dashi nan take yaji kamar an zare masa dukkan lakar jikinsa gaba daya kuma sai idanunsa suka kama lumshewa a take barci mai nauyi ya daukeshi lokacin da yarima hulkas ya farka daga barcin da ya daukeshi mai nauyi sai ya tsinci kansa a wani wuri na ban al ajabi wanda ya kasa tantancewa ko a sama yake ko kasa take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace wai shin anya kuwa a cikin duniya nake Hm Al amin Ahmed Misau, ba komai ne yasa yarima hulkas ya yiwa kansa wannan tambaya ba face ya tsinci kansa ne a cikin wani wuri mai dauke da kayan kawa na gaban kwatance kuma da ya dubi kasansa sai ya ga babu kasa babu shimfida tamkar akan gajimare yake tsaye kuma dayaga kafarsa ya yi tafiya sai yaji kamar akan daben lu'u lu'u yake tafiya shi dai wannan wuri ya kasance babbar fada wadda ta kayatu ainun ga kujeru na zinare ba adadi a kowacce kusurwar na fadar a bangaren gabas a tsakiyar fadar an girke wata kawatacciyar KARAGAR MULKI ta zinare da aka kawatata sai dai babu kowa akan karagar mulkin wani abun da ya kara daure masa kai kuma yayi matukar bashimamaki shine yadda yaga babu wata alamar kofa wacce za a iya fita ko shigowa cikin wannan fada daya tsinci kansa a cikinta kai tsaye yarima hulkas ya tunkari inda babbar karagar mulkin nan take a tsakiyar fadar Al amin Guyson ina biye dashi a baya, yana zuwa daf da karagar mulkin sai ya risina ya sauke guiyoyinsa kasa ya kwashi gaisuwa a gareta tamkar dama ya ga wani akanta yana mai sunkui da kansa kasa cikin yanayi na girmamawa kwatsam sai yaji an bushe da dariya daga kan karagar mulkin A firgice yarima ya dago kansa yayinda Al amin na matsa baya yayi arba da abinda yake yin wannan dariya ba wani bane ya gani face Aljani Arwasul amsabur a cikin siffarsa ta ainihi Aljani Arwasul masabul ya kasance gabjeje kuma katon gaske mai matukar kwarjini da ban tsoro yana da kaho guda biyu akan tsakiyar kansa kunnuwansa biyu ne dogaye ne tamkar na zomo, amma idanunsa da hancinsa tamkar na bil adama suke fuka fukansa manya ne don zai iya lullube gaba dayan jikinsa dasu hannayansa guda hudu ne haka ma kafafunsa, daga cibiyarsa zuwa kirjinsa siffar zaki ce dashi daga cibiyar kuma zuwa kafafunsa siffar dokine dashi Hm Al amin ahmed Misau nake Typing, kaga kenan ya hada karfi biyu na zaki dana doki, tunda yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin halittar data firgitashi ba ainun kamar Aljani Arwasul masadur Duk da cewa siyama ta taba bashi labarin aljanin amma bai kawo a ransa cewa shine wannan ba tunda bata siffanta masa kamanninsa ba cikin kaduwa yarima hulkas ya dubi Aljanin yace yakai wannan halitta wanene kai kuma akan wanne dalili ka daukoni daga can duniyarmu ta mutane ka kawoni wannan duniyar ta daban? Lallai daka san gagarumin aikin dake gabana da baka rabani da iyayena ka kawoni wannan duniya ba koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai aljani Arwasul masadul ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa kuma ya dakawa yarima hulkas Tsawa al amarin da ya kara firgita shi kenan ainun har ma yaji hantar cikinsa ta fara kadawa cikin alamun fishi Aljani Arwasul madadul ya dubi yarima hulkas yace wane irin yaro ne kai haka mara da a da har zaka rinka yiwa manya tambaya ? Kamata yayi ka zuba ido ka ga yadda zamuyi da kai tukunna ka sani cewa mun daukoka ne domin mu taimaka maka bayan munyi maka jarrabawa ta tsawon kwana uku, koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya zube kasa bisa guiwoyinsa cikin alamun tsoro da girmamawa yace kayimin afuwa ya shugabana idan ka rukeni anan har tsawon kwana uku ba karamar asara zanyi ba yanzu dai kaga gobene da safe yar uwata jaruma siyama za tayi wasanta na karshe da SADAUKI DARKUS a GASAR JARUMTAKA lallai ina son naga yadda wannan gumurzu nasu zai kasance Baya ga haka zamuyi wata gagarumar tafiya mai matukar darari nida..... Caraf sai Aljanin ya tari numfashinsa yace na sani cewa kai da mahaifinka sadauki hailur da mahaifiyarka shadila tare dasu sarki hulbasu kuna son ku tafi neman HULAR LAMSARA to ka sani cewa jarrabawar da zanyi maka a cikin wadannan kwanaki uku indai har ka samu nasarar cinye su ina tabbatar maka zaka sami nasara abisa abinda zaku tafi nema ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa kwana uku anan dai dai yake da jini daya na duniyarku kuma ka sani cewa nan kana inda kake kana cikin wata duniya ne daban dake cikin duniyoyin sama amma kuma zan saukar dakai izuwa taku duniyar domin ka fara fuskantar jarrabobinka, kafin yarima hulkas ya budi baki yace wani abu sai kawai yaji jiri ya kwasheshi kuma idanunsa sun lumshe, kawai sai ji yayi ji da ganinsa sun dauke dif ! Nan da nan hankalinsa ya gushe ya kasa gane halin da yake ciki Al amin Ahmed Misau Bayan cikar yan dakiku kadan kuma sai yaji komai ya dawo masa dai dai yana bude idanunsa ya tsinci kansa kwance a kasa bisa ciyawa a cikin wani kungurmin daji bayan ya dubi kowacce kusurwa na cikin wannan daji baiga Aljani Arwasul masadul ba kuma ya duba ko ina a jikinsa yaga ko wuka babu bare ya san cewa yana da wani makami wanda zai iya kare kansa dashi sai kawai ya mike tsaye yai shiru yana nazari da tunani abin da ya fara fado masa a rai shine wai shin wacce irin jarawaba wannan aljani yake son yi masa har da zai kawoshi cikin wannan dokar daji ya ajiyeshi Anya kuwa wannan Aljani ba shi bane Aljani Arwasul masadul wanda yar uwata siyama ta bani labari? Tabbas idan kuwa shine to lallai na yarda cewa taimakona zaiyi ba cutar dani zaiyi ba, koda gama aiyana hakan sai hulkas ya nufi gabas ya kunna kai izuwa cikin dajin kai tsaye ba tare da fargabar komai ba dajine mai dauke da manyan duwatsu dogayen bishiyoyi gami da koramu, tun da hulkas ya fara tafiya cikin wannan daji bai hadu da wani abu ba face kanana dabbobin daji irinsu birrai sai kuma kananun tsuntsaye amma ko dabbar datakai girman barewa bai gani ba haka dai yarima hulkas ya cigaba da tafiya a cikin dajin yana waige waige har tsawon sa a guda kwatsam sai yayi kicibis da wata gada a kwance male male cikin jini tana ta faman nishi tamkar ranta zai fita saboda yawan raunikan dake jikinta sannan kuma kafarta guda a karye take har ta fara kumbura kallo daya yarima hulkas ya yiwa gadar ya kau dakai har ya giftata zai yi tafiyarsa sai yaji tausayinta ya kamashi saboda ya tabbatar da cewa indai wannan jini na jikinta bai daina zuba ba mutuwa zatayi cikin gaggawa yarima hulkas ya dawo da baya ya tsugunna a gaban gadar yasa hannu ya yagi rigar jikinsa ya daure dukkan raunikan dake jikinta ya zamana cewa jinin ya daina zuba sannan sai ya mike tsaye da sauri ya ruga izuwa wata bishiya ya karo kirare yazo ya gyara karayar dake kafar gadar ya daureta A dai dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tsala tsawa da walkiya, koda yarima hulkas ya lura da irin yanayin garin ya gane cewa ruwa ne mai yawa zai sauko kawai sai ya sunkuya ya dauki wannan gada ya sabata a wuyansa ya ruga izuwa cikin dajin yana neman inda zasu fake, har sai da ruwan saman ya fara zuba sannan ya hango wani kogon dutse dan karami mara tsawo da fadi wanda baifi mutum uku ba kacal su iya shiga ciki kawai sai ya kunna kai ciki ya ajiye gadar a gefe daya shima ya zauna dirshan a kasa zaman sa keda wuya sai aka tsuge da ruwan sama mai karfin gaske tamkar da bakin kwarya tun safe aka fara wannan ruwa amma har goshin magariba ba a tsagaita ba nan fa yunwa da sanyi suka addabi hulkas da wannan gada babu shiri yarima hulkas ya mike tsaye ya karyo wadansu busassun itatuwa na wata yar karamar itaciyar sannan ya dauko duwatsu biyu a cikin kogon yayi kyastu dasu dakyar ya kunna wutar, nan da nan kogon yayi dumi amma sai yarima hulkas ya rinka yawan kallon wannan gadar yana kallon wannan dutar da ya kunna zuciyarsa na cewa dashi. Ga nama kuma ga wutar gasa nama me zai hana ka yanka wannan gada ka fedeta ka gashe domin kayi maganin wannan yunwa da ta addabeka wata zuciyar kuma sai tace dashi A a ai tunda har ka ceci rayuwarta da farko bai kamata ka kasheta ba yanzu kawai kayi hakuri ai yunwa bata kisa face kwana ya kare haka dai yarima hulkas ya mike tsaye da nufin ya fice daga cikin wannan kogon dutsen domin ya nemo musu abinda zasu ci shida wannan gadar, Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga wannan gada ta rikide ta zama Aljani Arwasul Masadul yana mai kyalkyala dariya.... Nima kuma Al amin Ahmed Misau, a nan zan daka ta saboda ganin wannan Abin mamaki yasa na kas ci gaba Kafinnan karku manta It's Real Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson Ko A square nake cewa Mu zama lafiya Sai Allah ya kaimu Gobe zakujini da cigaban sa TSATSUBA Littafi Na Takwas (8) Part B. . .Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini AA Misau. Me magana . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga wannan gada ta rikide ta zama Aljani Arwasul masadul yana mai Kyalkyala dariya, al amarin da yai matukar razana yarima hulkas kenan yaja da baya a firgice yana mai tokare jikinsa a jikin dutsen kogon yana mai takure jikinsa gami da zazzare idanu, Koda ganin haka sai Aljani Arwasul Masadul yayi shiru ga barin dariyar yace Yaro kaci jarrabawar farko saura jarrabawa ta biyu kacal ! Sannan na cika Alkawarina na taimakonka a maimakon na cikasa sauran jarrabobi bakwai a gareka, ba don komai ba sai saboda wannan jarabawa ta farko dana yi maka tafi dukkanin sauran muhimmanci gama fadin hakan keda wuya sai aljanin ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajan ba al amarin da yai matukar fusata yarima hulkas kenan bai san sa adda ya takarkace ya kurma ihu ba ya kama naushin kogon dutsen da hannunsa har sai da yaji kamar yatsunsa zasu kakkarye sannan ya daina, ba komai ne ya fusata yarima hulkas ba face ganin irin rainin hankalin da wannan aljani yayi masa wato yazo masa a siffar wannan gada Tabbas inda ya san cewa shine daba zai taba taimakonshi ba kai ko kallonsa ma ba zaiyi ba balle har takai ga ya taimaka masa, haka dai yarima hulkas ya fito daga cikin wannan kogon dutse a jigace yana layi kamar zai fadi kasa saboda yunwa. Al amin Ahmed Misau Guyson nake ko A square nake koda yayi yar gajeriyar tafiya sai yayi kicibis da wani lambu a gabansa cike da yayan itatuwa nunannu, kamarsu tuffa, inibi, ayaba, fasa dabur, baure , ruman da sauransu Ba tare da jin tsoro ba ko shakkar komai sai yarima hulkas ya kunna kai cikin wannan lambun abin ka damai jin yunwa da zuwansa sai kawai ya kama cin yayan itatuwan dake cikin lambun ba sassauci sai kace dabba wani ma idan ya gwawiya sau biya sai ya jefar ya tsinko wani ya kama ci saboda ganin abin a banza haka yarima hulkas yayi ta ci ya yan itatuwan nan har sai da yaci ya koshi kuma yayi barna mai yawa a cikin lambun wato ya zubar da wadansu yayan itatuwan a kasa ya tattakasu bai sani ba faruwar hakan keda wuya kuma sai ya hango wata yar karamar korama a gefen lambun, kai tsaye yaje ya durkusa a gaban koramar wacce ke dauke da ruwa mai kyau garai garai ya sha ya koshi har da yin gyatsa kawai sai yaji motsi a bayansa a lokacin da yake dago kansa daga cikin koramat, kafin ya juyo yaga abin dake bayan nasa sai yaji an gabza masa wani mummunan naushi a wuya saboda karfin naushin sai da yayi sama sannan ya fado cikin wannan koramar ya jike sharkaff cikin tsanani fishi yarima hulkas ya waigo da sauri da nufin ya ga wanda yayi masa wannan naushi ya mayar da martanin dukan da akayi masa amman sai ya kasa sakamakon ganin wanda ke tsaye a gabansa, Al amin Ahmed Misau Guyson nake magana ba wani bane a tsaye a gabansa face wata kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance wacce shekarunta a duniya basu da yawa wato ko yarima hulkas din zai girmeta to da yan shekaru ne kadan ya girmeta ma tun da yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin ya mace mai kyan wannan yarinya ba, a karon farko yana hada idanu da ita yaji ya kamu da tsananin kaunarta fiye da komai dake wannan duniya kuma ya aiyana a cikin ransa cewa lallai idan wannan yarinya ta zama cikakkiyar budurwa sai ta zama sarauniyar kyawawa ta duniya gaba daya domin ba za a taba samun wata mace wadda ta kai ta kyau ba Kai Nifa tawa sarauniyar tafi wannan kyau Ehem Al amin nake Yarinyar na sanye da kaya ne na fatar damisa riga da wando a kuibinta na dama daure a jikin cinyarta wata zabgegiyar siririyar takobi ce a bayanta kuwa kwanson kibiyoyi ne a sakale, hannunta baka ne da ta daga kibiya a jikinsa ta tabe zaren bakan tana mai saita kirjin yarima hulkas da shi , da yi masa alamar yana motsawa zata sakar masa harbi, gashin kanta dogo ne kuma baki sidik wanda ya zuba har kasan mazaunanta sai sheki da walwali yake, idanunta manya ne kuma farare kal kal tamkar ruwan madar hancinta kuwa dogone siriri a saman dan karamin baki tamkar da wuka aka yankashi yarinyar ta dubi yarima hulkas fuskarta a murtuke kuma ta daka masa tsawa tace wanene ya baka izinin ka shigo har cikin lambuna kayi mini irin wannan mummunar barna haka ko kuwa tsautsayin mutuwa ne ya kawoka koda jin wadannan tambayoyi guda biyu daga bakin wannan kyakkyawar yarinya sai yarima hulkas ya tuntsure da dariya sannan yace yakai wannan Aljani ka daina tunanin cewa zaka iya yaudarata a karo na biyu in banda ma toshewar basira irin taku ta aljanu ta yaya za ayi na yarda cewa mutum zai iya rayuwa shi kadai jal a cikin wannan mugun daji bare ma kuma yarinya karama kamar wannan wadda ke tsaye a gabana? Ai wannan aiki sai daiku Aljanu Al amin Ahmed Misau, koda jin wannan batu sai yarinyar ta fusata a karo na biyu ta tari numfashin yarima hulkas tana mai sake daka masa tsawa tace kai shashasha kalleni da kyau ka gani ni mutum ce kamar ka ba Aljan ba anan cikin dajin uwata ta haifeni muka rayu mu biyu kacal har tsawon shekaru shida sannan ta mutu ta barni a haka na cigaba da rayuwa ni kadai Har na kawo i yanzu duk wata dabba ko tsuntsu ko aljan dake cikin wannan daji a karkashin ikona yake amma kaine mutum na farko da na taba ganin yazo har nan inda nake shinka taba haduwa da Wani Aljani wai shi Arwasul Masadul ? Koda jin wannan tambaya sai jikin yarima hulkas yayi sanyi kuma ya kamu da tsananin mamaki ya dubi yarinyar yace ke ya akayi kika sanshi wacece ke kuma menene dalilin zamanku a cikin wannan daji keda mahaifiyar taku har ta haifeki a cikin sa koda jin wadannan tambayoyi sai yarinyar taja bakanta ta kara tabeshi tana mai kara saita kirjin yarima hulkas tace maza ka gaggauta amsa mini tambaya ta ta farko a gareka kafin kibiyata ta huda kirjinka saye ya baka izinin ka shigo har nan cikin lambuna kayi mini barna haka koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya tsugunna kasa bisa guiyoyinsa cikin alamun kaskantar dakai yace kiyi min afuwa yake wannan ma abociyar kyawu da kwarjini kiyi sani cewa yunwace ta galabaitar dani har ta sani nayi miki irin wannan barna gami kuma da rashin sanin cewa akwai mai wannan lambu, koda jin wannan batu sai yarinyar ta sauke kwarinta kasa sannan ta nufo kansa gadan gadan tana zuwa daf dashi sai ta sa kafarta ta doki kirjinsa saboda karfin dukan sai da ya kife kasa yana mai aman jini Al amin Ahmed Misau, kawai sai yarinyar ta durkusa a gabansa ta kamo habarsa da hannu daya ta dago kansa sama ta dubeshi tace wannan shine hukuncin barnar da kayi min yanzu babu bashi a tsakanina dakai, saboda haka yanzu sai ka bani labarinka ta yadda akayi ka sami nasarar zuwa wannan daji idan naji labarinka ya kasance zamu iya taimakon juna nida kai don na san bazaka rasa wani buri ba wanda ya gagareka kamar yadda nima nake da nawa burin sa adda yarinyar tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya mike cikin tsananin takaici ya tuno da cewa wannan shine karo na biyu da mace jaruma kuma yarinya ta nuna masa tafishi karfi da jarumta yar uwarsa jaruma siyama ce ta farko saikuma wannan bakuwar jaruma wacce basan komai a kanta ba yarima hulkas ya goge jini dake kan lebensa sannan kuma ya dan karkade kurar jikinsa ya dubi yarinyar cikin nutsuwa yace ta yaya zan iya baki yardata har na sanar dake koni waye ba tare dake kin fara gabatar min da kanki ba babu mamaki ke wakiliyar abokan gabata ce koda jin wannan batu sai wannan yarinya ta bushe da dariya sannan tace wanda ya ajiyeni anan bashi da abokin gaba ko daya a cikin fadin wannan duniya tunda baka da yarda shikenan ni yanzu zan fara gabatar da labarina amma ba anan ba ka biyoni muje gidana tana gama fadin hakan sai ta juya tabi wani surkuki mai yar duhuwa shi kuwa hulkas sai ya kama binta da sauri yana mai mamakin yadda za a iya samun gida a cikin wannan kasurgumin daji, yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso wani wuri daban mai ban al ajabi, wadansu irin duwatsu ne wadanda kallo daya mutum zai yi musu ya san cewa sassakesu aka yi akayi gida a jikinsu mai dauke da katuwar fada ba wai haka suke ba tun fil azal abinda ya kara daurewa yarima hulkas kai shine shin wane gwanin iya gini ne yayi wannan gida haka, Tabbas wannan aiki yafi gaban aikin bil adama sai dai aljanu aljanun ma sai dai idan sune sarakan gini na duniya shi dai wannan dutse asali kato ne tamkar tsauni amma sai gashi an fafeshi an yanyankashi kuma an fikeshi kai kace kasa ce aka kwaba akayi tubali sannan aka gina, ta kan wata matattakala yarinyar tabi da yarima hulkas suna fara tafiya akan matattakalar wacce ta nufi cikin wata katuwar kasaitacciyar fada mai wadansu manyan dakaru na aljanu ma abota kwarjinin gaske dauke da muggan makamai su da yawa babu adadi suka bayyana suna masu tokare kofar shiga fadar suka raste suka baiwa yarinyar nan hanya ta shige suna masu dukar da kawunansu kasa don gaisheta amma yarima hulkas na isowa daf dasu sai suka tare masa hanya suka zare takubbansu cikin razana da firgici hulkas yaja da baya su kuwa aljanun sai suka yi caa izuwa kansa da nufin su gididdibashi, cikin hanzari suka ja da baya suka koma inda suke tsaitsaye yarinyar nan ta dawo da baya ta dubi dakarun gaba dayansu tace wannan bakona ne na musamman, koda jin haka sai gaba dayan dakarun Aljanun suka risina suka gaishe da hulkas kuma suka dare suka bashi hanya, sannan nima Al amin Ahmed Misau suka dare mun suka bani hanya saboda ganin Kwarjini na ehem suna shiga cikin fadar sai yarima hulkas ya rude kuma ya dimauce domin bai taba ganin fadar da ta kawatu kamar wannan fada ba, sai dai babban abin bakin cikin shine fadar kango ce babu bafade ko guda daya a cikinta bare ma a sami talakawan da za a mulka kai tsaye wannan yarinyar ta nufi kasaitacciyar karagar mulkin dake cikin fadar wacce akayita da zallan Dutsen lu'u lu'u aka kawata shi da adon sarauta Da isarta kan karagar mulkin nan sai ta zauna tana mai harde kafa daya bisa dayar sannan tayiwa yarima hulkas nuni da ya zauna akan wata kujera dake daf da karagar tata ba tare da gardamar komai ba yarima hulkas ya zauna yana mai fuskantarta zamansa keda wuya sai yarinyar ta tafa hannunta sai ga tambulan na zinare tare da Kofuna sun bayyana a gaban su akan iska babu mai rike dasu kawai sai tambulan din ya karkata kansa ya zuba ruwan inibi a cikin kofunan nan biyu kofi na farko ya tafi ga yarima hulkas ya tsay dai dai hannunsa yarima hilkas ya dubi yarinyar cikin alamun tsoro ita kuwa sai tayi masa murmushi tace karbi mana kasha idan so nake na zutar dakai ai tun kafin muzo nan zan cutar dakai din koda jin haka sai yarima hulkas ya saki jikinsa ya karbi kofin ya kurbi ruwan inibin, a dai dai wannan lokaci ne itama yarinyar ta kurbi nata ruwan inibin shima kuma Al amin Ahmed Misau mai typing sai ya kurbi nashi ruwan inibin sannan tayi gyarar murya gami da gyara zama kuma ta dubi yarima hulkas cikin nutsuwa ta ce yakai wannan bako yanzu saika saurareni da kyau domin kaji labarina ... .... ..... ... DA FARKO DAI sunana RULAIYA IBINI AMSAR IBINI WARHAS, Kuma mahaifina ya kasance babban attajiri a birnin kisra, amma tun mahaifiyata na dauke da cikina wata uku aka kasheshi sannan kuma wanda ya kasheshi din yayi yunkurin kashe mahaifiyata sau goma sha daya amma bai samu nasara ba ita kanta mahaifiyar tawa tayi matukar mamakin yadda akayi take tsira da rayuwarta a duk sa adda aka kawo mata hari caraf sai yarima hulkas ya tari numfashin Rulaiya yace wane ne wanda ya kashe mahaifin naki kuma saboda me ya ke son kashe mahaifiyar taki koda jin wannan tambaya sai rulaiya tayi tsaki tace hanzarin me kake yi haka ka bini a sannu mana zakaji komai a cikin wannan labari da nake baka kamar yadda na gaya maka baya a gaba dayan birnin kisra babu attajiri da kai mahaifina tarin dukiya da karfin arziki na fatauci, cinikin bayi da na makaman yaki duk wani isashshen sarki dake nahiyarmu mahaifina yana da kyakkyawar alaka dashi saboda yana yi musu matukar biyayya kuma a duk karshen wata yana aika masa da kyautar bayi da dukiya don haka babu kasar da mahaifina baya zuwa don gabatar da fataucinsa ban da sarakai ma hatta mashahuran bokaye wadanda suka yi shuhura a duniya suna da kyakkyawar mu amala da mahaifina kuma suna taimakonsa da sirrinakan tsafi shi kuma yana yi musu alheri mai yawa, akwai wadansu amintattun rantsatstsun dakaru guda dubu daya wadanda ke baiwa mahaifina kariya ta musamman a duk sa adda zai yi tafiye tafiyensa na fatauci da kai ziyara izuwa ga sarakai ko matsafa na duniya Al amin Ahmed Misau, su dai wadannan dakaru kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu kuma fiye da shekaru goma baya suke yiwa mahaifina aiki ba a taba shiga masifar da suka kasa kareshi ba ko dukiyar sa A duniya babu abinda mahaifina yake so sama da mahaifiyata mahaifiyata ta kasance yaga shugaban yan kasuwar birnin hindu kuma masana da masu bincike sun tabbatar da cewa a zamanin da take budurwa babu wata ya mace mai kyanta kafin mahaifina ya sami nasarar auranta sai da yayi fama da abokan hamayya har ma ya kusan rasa rayuwarsa in ba don ma yana da kyakkyawan tsari ba na bokaye da tuni ya hallaka Al amin Ahmed Misau, A duk sa adda mahaifina ya ziyarci isassun bokayansa suna yi masa gargadi akan cewa ya cigaba da boye amaryarsa kuma kada ya kuskura ya rinka shiga manyan birane tare da ita, bisa wannan dalili ne ya zamana cewa duk sadda mahaifina zaiyi tafiya tare da mahaifiyata koyaushe fuskart da jikinta a lullube suke sosai ta yadda mutum ba zai iya ganin siffarta da kamanninta ba kuma in dai wani babban birni za a shiga to saidai a yada zango a bayan gari in yaso shi da tsirarun dakarunsa tare da hajarsu su shiga cikin garin ya bar mahaifiyata a hannun sauran dakarun nasa, A cikin irin wannan yanayi ne watarana mahaifina ya tunkari birnin wani gawurtaccen sarki wanda ake kira da suna SARKI SHARDAS shi dai wannan sarki anyi ittifakin cewa a duniya kaf babu wani jarumi wanda ya fishi karfin damtse iya yaki da kuma karfin sihirin tsafi, shi kansa mahaifina ba a son ransa zaije garin wannan sarki ba sai don kawai saboda ya amsa gayyatarsa ne domin gaba dayan mashahuran attajiran duniya sarki shardas ya gayyata domin ayi gasar siyen wani gida na musamman wanda aka ginashi a tsakiyar wani kogi a wannan lokaci shi dai wannan gida an ginashi ne da zallan hadin duwatsu uku, wato lu'u lu'u zinare jauhar da zubarjadu shi dai gidan ya sami shekaru goma sha biyu da ginawa amma ba a taba shigarsa ba, a tsawon wadannan shekaru sarki shardas yana tallaka gidan ne ga manyan sarakunan duniya da manyan fatake yana cika baki akan cewa tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu lokacin ba a taba gina gidan da yayi wannan gida nasa kyau, kawatuwa da kuma tsari ba don haka a ranar da za a budeshi an yiwa kowa izinin yaje ya shiga ciki domin ya baiwa idanunsa abinci, kuma wanda duk ya sayi gidan da farashi mafi tsoka shine zai mallakeshi, kuma shi kansa sarki shardas din ya shiga gasar siyen wannan gida nasa kafin sarko ko Attajiri ya shiga wannan gasa sai ya ajiye dinare miliyan daya tukunna a cewarsa wai hakan shine shaidar cewa ya isa ya shiga wannan gasa, an ce a haka ma sarki shardas ya tara miliyoyin dinaren da bai taba

Chapter 16 of 21