Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yarima hulkas ya dubi basmar yace kai kuwa yaya akayi ka gane haka basmar yayi murmushi yace ai na lura ne da duk irin yanayinka kuma da irin tsananin farin cikin da kake ciki a yau wanda ke nuni da cewar baka taba samun sakewa ba irin na yau sa adda hulkas yaji haka sai yayi ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ai ni nan da kake ganina in ba don albarkacin wannan tafiya da mukayi zuwa wannan gari naku ban taba ma fita daga cikin gidan sarautarmu ba saboda mahaifina baya son naje ko ina dare da rana muna tare babu abinda yake rabamu saboda tsananin shakuwar da ke tsakaninmu. Koda jin wannan batu sai yarima basmar ya cika da tsananin mamaki yace ai kuwa rayuwarka da tawa tazo kusan iri daya domin nima haka mahaifina ya kafa min takunkumin fita baya barina naje ko ina amma sai dana shammaceshi ya zamana cewa ina shiga har cikin gari ba tare da kowa ya sani ba a yanzu hakama akwai wata jarumar yarinya da na hadu da ita wacce tayi matukar burgeni kuma ta bani tsoro domin ban taba ganin karamar yarinya mai jarumtaka kamarta ba don a gabana tayi gumurzu da karti goma duk ta bazar dasu a kasa da karfin damtsenta ba makami ina mai tabbatar maka da cewa shekarunta ba zasu fi namu ba wato ina nufin sa'armu ce koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai hulkas ya bushe da dariya yace haba yakai abokina wannan kuma wace irin tatsuniya ce haka kazo min da ita ai wannan kawai almara ce kazo mini da ita sai dai idan harkar tsafi ce amma ba zahiri ba koda jin haka sai yarima basmar ya kama yin rantse rantse yana cewa lallai al amarin wannan yarinya ba tsafi bane yarima hulkas yace idan har kana son na yadda da wannan labari daka bani sai dai ka kaini naga yarin yar a zahiri da Idanuna yanzu ta yaya kake ganin zamu iya fita daga cikin wannan gidan sarauta taku harmu shiga cikin gari muje ka kaini inda wannan yarinya take? Sa adda yarima basmar yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ai wannan mai sauki ne kamar cire silin gashi daga cikin tandun mai muddin zaka iya yin duk abinda zanyi hulkas yace ai yanzu tuni zuciyata ta kwadaitu da son ganin wannan yarinya da ka bani labari kuma raina ya kagu damu tafi can inda take saboda a rayuwata babu abinda nake so sama da jarumtaka da iya yaki gashi kuma ko sau daya ban taba jarraba yin suba kai in dai wannan labari daka bani gaskiya ne zan iya biyan wannan yarinya dinare dubu domin ta koya mini yaki da jarumtaka ina mai rokonka daka tashi mu hanzarta shiga cikin wannan gari naku koda jin haka sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas suka duro kasa tare daga kan lilon suka ruga izuwa wani bangare daban dake gidan saida sukayi gudu na tsawon yan dakiku masu yawa sannan suka iso karshen gidan sarautar suka shiga cikin wani kwararo wanda ya kaisu inda matattakalar shaddar gidan sarautar take gaba daya da zuwa suka iske wadansu wulakantattun bayi suna ta debo kashi suna lodashi a cikin wani amalanke koda bayin sukaga shigowar yarima basmar tare da hulkas sai bayin suka zube kasa gaba dayansu suka gaida basmar a lokacin da doyin kashin ya ishi hulkas ya kama kau da kai yana toshe hancinsa shi kuwa basmar ko kadan bai damu ba ga dukkan alamu ma ya saba da zuwa wajan basmar ya dubi shugaban bayin yace yau mu biyu ne nida abokina ina son ku fitar damu zuwa cikin gari kamar yadda kuka saba a sirrance koda jin haka sai shugaban yayi dariya yace an gama ya shugabana bamu ladan aikinmu kamar yadda ka saba cikin alamun damuwa yarima basmar ya ce yau na sha afa ban taho da shiri ba ama ai kasan ba zanyi muku wasa ba gobe zan baku ladanku gama fadin hakan keda wuya sai suka jiyo takun sawun dakarun dake kulle dasu cikin hanzari bayin suka boye su yarima hulkas a karkashin amalanken da suke loda kashin faruwar hakan keda wuya sai ga wadansu dakaru biyu sun shigo wajan rike da bulalai da shigowarsu sai suka tsaya a gaban amalanken dai dai inda su yarima basmar suke har daya daga cikinsu ya take danyatsan hulkas guda da katon takalminsa har hulkas zaiyi ihu sai yarima basmar yayi sauri ya toshe masa baki da tafin hannunsa daya daga cikin dakarun ya dubi shugaban bayin ya daka masa tsawa yace a cikinku waye mai murya irin ta yara tabbas daga can nesa na jiyo muryar yaro a nan har shugaban bayi ya budi baki zaice wani abu sai wani daga cikin yaransa ya tari numfashinsa yayi magana da karamar murya iri daya sak da ta yarima basmar al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan koda jin hakan sai dakarun suka kyalkyale da dariya wanda yayi magana da farko ya dubi bawan da yayi muryar yarima basmar yace tabbas kana da hikima watarana zan gabatar dakai gaban sarki domin ka debe mana kewa koda gama fadin hakan sai dakaru biyu suka juya suka fice daga cikin wannan kwararo da ake aikin kashi fitarsu keda wuya sai bayin suka sauko buhuhuna da suka dura kashi a ciki suka zura yarima basmar da hulkas a kansu suka kulle bakin buhuhunan amma sai suka yi dabaara suka farka buhun a dai dai kan fuskokinsu yadda zasu iya shakar numfashi duk da haka sai da yarima hulkas ya kama kakarin amai saboda doyin kashi gashi an labta wadansu buhuhunan a samansu nauyi ya damesu nan take yarima hulkas yaji kwalla ta cika masa idanu yace oh duniya juyi juyi kwado ya fada ruwan zafi wai yau ni yarima hulkas nine a cikin buhun kashi saboda kawai ina son shiga cikin gari naga abin al ajabi tabbas neman duniya ba wasa bane kuma ba a samunta cikin sauki sai ansha wuya yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaji an ja amalamken da suke kai anyi gaba dasu nan fa akayi ta tafiya dasu ana wucewa ta cikin sako sako da lungu lungu na gidan sarautar har sai da aka wuce dasu ta cikin kofofi shida duk kofar da aka zo sai sun tsaya an caje buhuhunan kashin wani lokacin ma sai dakaru sun caccaka tsinin takobi a cikin buhuhhunan saboda zargin ko an sato wani abu a ciki in ba don Allah ya kiyaye ba saura kiris takobin wani badakare ta tsire ido guda na yarima Hulkas shikuwa yarima barmas ma sai da aka dan sokeshi a kafada jini yayi tsartuwa yaji kamar ya kurma ihu amma sai ya daure a haka dai aka samu aka fice dasu ba tare da asirinsu ya tonu ba kafin a isa bakin kogin garinne yarima hulkas yaji nadama ta zo masa bisa wannan ganganci da sukayi na sai da ransu don kawai suna son su shiga cikin gari Ana isowa bakin kogin ne aka sauke buhunhunan dasu yarima hulkas ke ciki ko da aka fito dasu aka ga yarima barmas ya sami rauni a kafadarsa sai hankalin bayin ya dugunzuma ainun suka firgice shi kuwa yarima Hulkas yana ganin rauni a kafadar barmas bai san sa adda ya kama rigarsa ya yagata ya daurewa barmas raunin don tsaida jiniba cikin rudewa hulkas ya dubi barmas ya ce yakai abokina tunda dai ka sami wannan rauni zaifi kyau Mu hakura mu koma cikin gidan sarauta mubar batun ganin wannan jarumar yarinya domin muje ayi maka magani da sauri koda jin wannan batu sai yarima barmas yayi murmushi yace aini idan nayi gaba bana komawa baya kuma idan har muka koma gida bamuga wannan yarinyar ba ai mun sha wahalar banza kenan mun sayar da rayuwarmu a wofi, tunda dai ka tsayar da jinin dake zuba a jikina babu komai zan iya gabatar da abinda muka fito yi lafiya har mu kammala, yanzu sai mu shiga cikin kogin nan mu wanke kashin dake jikinmu don kada muje wajan ta muna wari nan take yarima basmar ya sallami bayin akan cewa idan sun kawo sawun karshe na kashin suyi tafiyar kada suyi shakkar komai don haka suka saba yi shi dasu domin shine ya san dabarar da yake yi yake komawa cikin gidan sarautar ba tare da an ganshi ba ba tare da bata lokaci ba yarima barmas da yarima hulkas suka ruga zuwa cikin kogin suka kwabe kayan jikinsu sukayi tumbur sai da suka wanke kayan nasu tas sannan suka fito suka shanyasu akan wata bishiya suka sake komawa cikin gefen kogin suka kama wanka a wannan lokaci ne yarima hulkas ya tsinci kansa a cikin wani iein nishadi wanda bai taba jinsa ba na farinciki walwala da annashawa abin da yafi burgeshi shine ganin yadda yau ya sami yancin kansa har yake yiwa kansa wanka da wanki alhalin bai taba yiwa kansa wata hidima ba sai dai ayi masa komai sai da kayan da suka shanya suka bushe sannan suka fito daga cikin kogin suka je suka sanya kayan nasu sannan yarima basmar ya wuce gaba hulkas na biye dashi suka nufi wata siririyar hanya wacce zata kaisu cikin gari a wannan lokaci yammaci ne mai dauke da yanayi mai kyau da dadi domin wata irin iska ce mai sanyi ke kadawa kafin su iso cikin garin sai yarima basmar da yarima hulkas suka rude fuskokinsu da rawaninsu ya zamana cewa idanunsu kadai ake gani don kada a shaidasu haka dai suka ci gaba da tafiya suna ratsawa ta cikin unguwanni har suka iso wata unguwa dake can karshen gari kuma suka tunkari gida na karshe a unguwar wanda shi ne mafi muni da kaskanci Da ganin gidan kasan cewa na talakawa ne fitik marasa gata ko kuma bako wanda bai kasance dan gari ba saboda an gina gidanne da katako ko kyakkyawan tsari baiyi ba tun daga nesa su yarima hulkas suka hango wani mutum mai kwarjini zaune a kofar gidan fuskarsa cike da kasumba amma kuma hannunsa guda na hagu a yanke yake sannan kafarsa guda a lankwashe take sai da sanda yake dogarawa mutumin na tsaye a can gefe daya yana kallon wadansu tsuntsaye dake ta wasa akan wata bishiya saiga matarsa wata yar kyakkyawar mace yar kimanin shekaru talatin da doriya wacce ba zatafi sa ar gimbiya shadila ba ta fito daga cikin gidan dauke da kofin shayi ta nufi mijin nata A dai dai wannan lokaci ne mijin matar ya hango su yarima hulkas sun durfafoshi shi da matar tasa sai suka kurawa su yarima hulkas idanu kawai cikin sanyin jiki da mamaki Dama A wannan lokaci su yarima basmar sun cire rawanin da ya rufe fuskokinsu kyawunsu da kwarjininsu irin na yayan sarakai ya baiyana a fili kururu bisa mamaki sai yarima hulkas yaga mijin matar ya kura musu idanu ko giftawar ba yayi koda suka iso daf dasu sai yarima basmar ya risina a cikin biyayya ya gaishe da mutumin da matarsa sannan ya gabatar da kansa yace nine yarima basmar dan sarkin garin nan wanda kuma abokina ne sunansa hulkas munzone wajan yarka siyama domin muga baiwar da take da ita ta jarumtaka da iya yaki saboda abokina bai amince da tana da wannan baiwar ba a sa adda na bashi labarinta.. TSATSUBA Littafi Na Uku (3) Part.E Koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai mutumin da matarsa suka dubi junansu sukayi murmushi sannan mutumin ya dubi basmar yace hakika wannan abokin naka zaisha mamaki kuwa domin a yanzu hakama tuni siyama ta shiga gasar jarumtakar da za ayi a fadar mahaifinka wacce za a fara gabatar da ita gobe kuma ina sa ran cewa itace zata karbi kambun wannan gasa koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya kyalkyale da dariya yace haba ai wannan ma almara ce ya za ayi karamar yarinya wacce aka ce batafi sa a taba zata shiga wannan gasa wacce manyan mutane zasuyi kuma jarumai na daga sassa daban daban na duniya har ace talashe gasar koda jin wannan batu sai ran mahaifin siyama ya baci ya murtuke fuskarsa nan take cikin fushi ya kwalawa siyama kira itakuwa sai gata ta fito daga cikin gidan a cikin shigar yaki siyama ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance duk da cewar yarinya ce yar shekara shida sai mutum yayi zaton takai shekaru goma sha saboda ta kasance doguwar gaske sai mutum ya dubi fuskarta sannan zai gane cewa yarinyace tana da cikakkiyar sura da zati irin na cikakkun mata ababan kwatance koda yarima hulkas yayi arba da siyama sai yaji nan take ya kamu da tsananin kaunarta amma da yaga ta kalleshi tana mai gabza masa harara sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya bai bayeshi yaji kamar ya ruga da gudu saboda kwarjininta siyama ta karaso gaban iyayanta ta risina a garesu tana mai amsa kira kawai sai mahaifin nata ya daga sandar dake hannunsa da hannun nasa lafiyayyan yayi nuni a gareta ko da ganin haka sai siyama ta zare takobinta ta kwala ihu sannan ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta fada kansa suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro ga dukkan mai kallo nan fa duk su biyun suka wanzu suna masu kaiwa junansu mugayan hare hare cikin bakin zafin nama duk sa adda takobin siyama ta hadu da sandar mahaifinta sai dai kaji kal sautin haduwar karafa gami da tartsatsin wuta na tashi tunda yarima basmar da hulkas suke ganin gumurzun mazaje masu tsananin zafin nama da jarumtaka ba kamar siyama da mahaifinta siffanta jarumtakar tasu da kwatantata ba zai yiwu ba sai dai abinda idanu suka gani babu wani jarumi daya fadowa yarima hulkas a rai dayaga jarumtakar siyama da mahaifinta sai mahaifinsa sarki shardas hulkas ya numfasa sannan yace a cikin zuciyarsa babu wani jarumi da zai iya fafatawa da wadannan mutumin ko yarsa siyama ya samu galaba a kansu face mahaifinsa sarki shardas kash ina ma tare da sarki mukayi wannan tafiya da yaga wadannan jarumai masu ban al ajabi da idanunsa yanzu dama she a wannan duniya akwai irin wadannan jarumai sai da siyama da mahaifinta suka shafe sa a daya da rabi suna fafatawa amma dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar jikin dayan ba duk da cewar suna yakinne a fusace da dukkan karfinsu da iyakar kwarewarsu tamkar abokan gaba masu neman hallaka juna koda sukaga sun kasa cutar da junansu da makami sai sukaja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon junansu tamkar zakaru kuma suna murmushi shidai mahaifin siyama murmushin da yake yi bana komai bane face na farin ciki bisa ganin abinda ya koyawa yasa ta kware a a kansa ainun harma ta fishi kwarewar a matsayinta na ya mace ai dama ance kyan da ya gaji ubansa kuma barewa batayin gudu ba danta yayi rarrafe babban abinda ya daurewa su yarima hulkas kai shine ganin yadda mahaifin siyama ya iya yin wannan bkin gumurzu alhalin ya kasance mai hannu daya kuma gurgun da yake dogara sanda kwatsam sai siyama da mahaifinta suka ajiye makamansu a kasa gefe daya wato shi ya ajiye sandar karfen dake hannunsa itakuma ta ajiye takobinta faruwar hakan keda wuya sai sukayi alkafira a kasa suka afkawa juna suka ci gaba da kaiwa juna naushi da bugu hannu da kafa sai gashi siyama tana shanye naushi da bugu kai kace wata katumar namiji ce ba mace ba kuma yarinya karama yar shekara bakwai tabbas horon da siyama ta samu zata iya gumurzu a tsakiyar miliyoyin dakarun yaki ma kuma ta dade tana fafatawa tana mai taka rawar gani a wannan fadan hannu ma sai da siyama da mahaifinta suka shafe kusan sa a biyu gashi dai sun hadawa junansu jini da majina kuma sun gaji likis amma saboda tsananin juriya naci da dakakkiyar zuciya sunki su daina fadan, Koda matar mahaifin siyama taga abin ya wuce gona da iri ta ruga ta shiga tsakiyansu ta tsaida fadan, a sannan ne siyama da mahaifin suka zube kasa suna haki da dariya daga can mahaifin siyama ya dago kai ya dubi yarima hulkas yace shin yanzu ka gamsu kuma ka yarda cewar yata zata iya shiga wannan gasar jarumtaka da za ayi a fadar birnin nan? Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas yayi murmushi yace tabbas na gamsu kuma na yarda dari bisa sari Al amin , zata iya ya kai abul siyama idan ba zaka damu ba ina son na nemi wata alfarma guda a wajanka cikin mamaki mahaifin Siyama yace yaro ina sauraronka fadi tambayarka naji in dai na sani zan baka amsarta, hulkas yayi gyaran murya yace ina son ka bani takaitaccen tarihin rayuwarka sannan ina son na sani shin wannan lalura da na ganka da ita ta rashin hannu da kafa daya ta sameka ne da girmanka ko kuwa a haka aka haifeka kai mutumin wace kasa ne kuma ya akayi kazo nan birnin domin ga dukkaln alamu kai bakone a garin nan bisa lura da yanayin gidanka da na gani wanda ya banbanta da dukkan gidajen birnin nan lokacin da yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jikin mahaifin siyama yayi sanyi yayi sauri ya sunkui da kansa kas don hawaye ne ya subuto masa kawai saiyayi shiru baice komai ba, caraf sai matarsa wato ummul siyama ta dubi yarima hulkas tace ka tambayi mijina tambayoyinda idan ya tuno da amsarsu yake shiga cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa lallai a yanzu ba zaka sami amsar wadannan tambayoyi ba sai dai wani karon koda jin haka sai yarima hulkas da barmas sukaji sun kamu da tausayin mahaifin siyama nan take hulkas ya tako kafafunsa yazo har gaban mahaifin siyama ya dafa kafadarsa ta dama da tafin hannunsa yace ka gafarceni yakai abul siyama inda na san cewa tambayoyina a gareka zasu sosa maka zuciya su tuno maka da wani abin damuwa da ba zan gabatar dasu ba a gareka mun barku lafiya sai gobe a filin fada zamu hadu idan kunzo filin gasar jarumtaka Koda gama fadin haka sai su hulkas suka juya da nufin ya kama hannun barmas su tafi amma sai yaji abul siyama ya dafa kafadarsa cikin mamaki hulkas ya juyo suka fuskanci juna yaga abul siyama yana yi masa wani irin kallo mai nuna alamar kamar ya sanshi kuma akwai alamun dumbin magana a zuciyarsa wacce ya kasa amayar da ita daga bakinsa har abul siyama ya budi baki zaice dashi wani abu sai kuma ya kasa yace yaro mun gode bisa ziyarar da kuka kawo mana amma nima ina rokon alfarma guda daya a wajanku amma bata komai bace face ina son kada ku sake xuwa nan wajanmu domin a duk sa adda na kalli fuskarka ina fama wani mugun rauni dake cikin kahon zuciyata abu na biyu kuma ina rokonku da kada ku bayar da labarina ko na yata ga waninku saboda wani babban sirri na rayuwarmu har sai bayan an kammala gasar jarumtakar da akeyi a garin nan koda gama fadin hakan sai abul siyama ya dafa kafar matarsa da hannunsa lafiyayyan ita kuma siyama sai ta tallafa kugunsa suka taimaka masa suka juya suka nufi cikin wannan gida nasu na katako koda suka isa daf da bakin kofar gida zasu shiga sai ab siyama ya juyo ya yiwa hulkas wani irin kallo idanunsa cike da kwalla take hulkas yaji tsigar jikinsa gaba daya ta tashi kuma kaunar abul siyama ta kara shigarsa tamkar dama can sun kasance yan uwan juna nan fa yarima hulkas ya kasa motsawa daga inda yake kuma yaji kamar yace da yarima basmar ya barshi ya kwana a nan gidansu siyama domin ji yayi babu abinda yake so sama da kasancewa tare dasu kawai sai hulkas ya bisu da kallo har suka kule a cikin gidan koda ganin haka sai yarima basmar ya rugo ya kama hannun yarima hulkas ya jashi da gudu suka bi hanyar da zata mayar dasu can gidan sarautar maimakon su wuce kai tsaye izuwa gidan sarautar sai yarima basmar ya kaisu gidan wani dan kasuwa mai suna abul yamzin wanda kullum sai ya kaiwa sarki hulkasu tulunan ruwan giyar da yake sha gami da ruwan inibi sarki hulbasu ya aminta dari da attajirin abul yamzin don haka ko caje tulunan giyar sa da na inibi ba ayi a duk sa adda ya shige dasu cikin gidan sarautar Tsakanin yarima basmar da attajirin abul yamzin akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna don haka sun san sirrin junansu sosai da zuwan yarima basmar da hulkas gidan attajiri sai aka sanyasu a cikin manyan tuluna guda biyu wadanda babu komai a cikinsu aka hada da wadanda ke dauke da ruwan giya guda goma dana ruwan inibi goma aka zuba su a cikin dana ruwan inibi aka zuba su a cikin wannan amalanke aka tura aka tafi dasu gidan sarki a can gidan sarki kuwa hankalin gimbiya shadila dana luzuraina ya tashi ainun domin ganin cewa tunda su yarima suka fita basu dawo ba har bayan tsawon sa a uku nan da nan aka baza dakaru zuwa kowani sako na gidan ana nemansu koda aka duba ko ina ba a gansu ba sai hankalin su shadila ya sake tashi suna shirin su tura aje a sanar da sarki hulbasu kenan saiga yarima hulkas da basmar sun shigo cikin turakar koda ganinsu sai shadila ta ruga izuwa yarima hulkas cikin matukar farin ciki ta rungumeshi daga nan ta jashi zuwa cikin dakin barcinta da aka bata ta kulle kofa ta dubeshi cikin fishi da matukar damuw atace ina kukaje kuka buya haka har kukayi matukar tayar mana da hankali koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya sunki da kansa kas ya tuna cewa shifa a rayuwarsa bai taba yin karya ba dan haka take ya yanke hukuncin ya sanar da ita gaskiyar duk abinda ya faru tun daga lokacin da sukaje bangaren da ake aikin kashin gidan kawo sa adda aka kaisu bakin kogi sukayi wanka sannan suka wuce gidansu siyama hatta kamannin siyama dana mahaifinta dana babarta sai da ya zaiyana mata har dama irin tsananin jarumtakar baban Siyama a matsayinsa na musaki mai hannu daya da kafa daya sai da ya shaida mata koda shadila taji siffifin baban siyama da yadda yake yakinsa sai nan take zuciyarta ta kama bugawa da karfi, ba komaine ya haddasa hakan ba face tunowa da tsohon masoyinta hailur wato mahaifin hulkas na gaskiya domin shine kadai yake da siffa da sura irin wacce hulkas ya shaida mata yanzu kuma shine kadai mutumin da ta san cewa yana irin salon yakin da aka fada cikin firgici da razana shadila ta mike tsaye zumbur ta kama kafadun hulkas ta girgiza dakarfi tace a ina kaga wannan jarumi mahaifin siyama ya za ayi ka kaini inda yake na ganshi cikin alamun matukar mamaki yarima hulkas ya dubi shadila yace yake ummina shin kinsan wannan mtum ne ko kuwa kun taba jin labarinsa ne a jana wani baniba? Koda jin haka sai shadila ta tuno da gargadin da shardas yayi mata akan cewar idan ta kuskura ta shaidawa hulkas cewar bashi bane mahaifin sa na gaskiya sai ya kasheta ya lalata dukkan rayuwarta nan take shadila ta wayance ta bagazar da maganar ta nunawa hulkas cewar kawai jarumtakar baban siyama ce ta burgeta nan dai ta lallaba hulkas yaje ya kwanta saboda ya mance da komai ita kuma saita juya masa baya a lokacin da hawaye ya zubo mata tace a ranta duk yadda za ayi sai nayi naje na ga mahaifin siyama domin na gani da idanuna ko tsohon mijina ne ya zama nakasashshe kai ba zata yiwu bama ya za ayi ace hailur yana na a raye a duniyar nan amma har ya manta dani yayi wani auren harma ya haifi ya alhalin yana tsananin kaunata fiye da komai a rayuwarsa...... . SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMO SAURAN ABOKAN TAFIYARSU..?? . SHIN SHADILA ZATA SAMI DAMAR ZUWA INDA MAHAIFIN SIYAMA YAKE?? . SHIN ZARGIN DA TAKEYI CEWAR TSOHON MIJINTA NE MAHAIFIN SIYAMA GASKIYA NE??? . TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI FARA MALLAKAR HULAR LAMSARA . Mu hadu A Littafin Tsatsuba Na hudu (4) Don jin Cigaban wannan labari Amma kafin nan Nida na jagoranci rubuta muku shi ba dare ba rana ba ruwa ba iska, komai rintsi da tsanani typing nake ba tsayawa Wato TSATSUBA Abdulaziz s madakin gini Hausaebooks Made:- by shuraih Usman Domin samun wasu kayatattun littatafan hausa amatsayin hausa ebooks sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan wannan adireshin http://shuraih.waphall.com SATSUBA Littafi Na Hudu (4) Part A. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... LOKACIN DA SHADILA TA tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar 'Anya kuwa Hailur yana raye a duniya amma bai nemeta ba? Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan gadonta taci gaba da tunanin jarumi hailur A wannan rana dai shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto a sannan ne barcin ya saceta ba tare da ta sani ba Al'amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye ya farka yaga mahaifiyarsa na ta barci bata ma da niyyar farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi hulkas yaje yayi wanka ya kimtsa gama hakan ke da wuya sai ga yarima barmas ya shigo cikin dakin shima ya caba ado fuskarsa cike da annuri ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika naga alamar cewa ka fini dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da za ayi Yau. Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na zama tsuntsu na ganni a can ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to ai saikayi sauri kazo muje muyi buda baki a can turakar mahaifiyata amma me ya faru naga har yanzu mahaifiyarka tana yin barci bata farka ba? Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar zuciya yace ina kyautata zaton cewa jiya

Chapter 7 of 21