Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya sace sarki a wannan lokaci ne ni da huzein muka dawo cikin hayyacinmu na dubi likitan sarki cikin alamun mamaki nace yakai likita wannan wane irin ciwo ne ya sami mahaifina alhalin ina tare dashi tsawon shekaru amma ban taba ganinsa a cikin irin wannan hali ba sai yau koda jin wannan batu sai likitan ya sunkui da kansa kasa yayi shiru kamar ba zaice komai ba har sai da na daka masa tsawa sannan ya dago kai ya dubeni a tsorace bakinsa na rawa yace ka gafarceni ya shugabana ka sani cewa sarki ya haneni da na sanar da kai komai dangane da rashin lafiyarsa, sa add anaji wannan batu sai na sake fusata na zare takobina na dora kaifinta akan wuyan likitan nace na rantse da darajar sarki idan baka sanar dani wannan al amari ba yanzun zan kashe ka koda jin haka sai jikin likitan ya kama tsuma ya budi b baki cikin in ina ya ce tun ranar da wasikar sarki shardas ta iso birninmu na askandariyya fadar mahaifinka yaji sakon da ta kunsa a lokacin ya kamu da ciwon zuciya ina mai sanar dakai cewa wannan ciwo yana da tsananin hadari domin zai iya zama sanadin ajalinsa a ko yaushe cikin kankanin lokaci muddin zai rinka fuskantar abinda zai bata masa rai koda likita yazo nan a zancensa sai na durkusa kasa na fashe da matsanancin kuka al amarin da ya karya zuciyar yarima huzein kenan, shima ya fashe da kuka AA Misau Ke Magana nan take naji na tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma na kudurce a raina cewar in dai wannan ciwo ya zamo sanadin ajalin mahaifina sai na yaki sarki shardas gaba da gaba duk da na san cewa hallaka zanyi muna cikin wannan haline muka ji an kwankwasa mana kofa sai ga wakilin sarki shardas kuma dan uwansa mubairu ya shigo cikin dakin da muke, koda ya ganmu muna kuka kuma ya ga sarki a kwance a gefe daya yana barci ga likita zaune a kusa dashi sai yayi dan guntun murmushi sannan ya dubeni yace yakai yarima hulbasu ka sani cewa nazo ne gareka domin ka sanar dani abubuwan da sarkina ya umarceka daka sanar dani domin na rubutasu nakai masa, koda jin haka sai na dago kai na dubeshi cikin tsananin fishi nace ashe baka da hankali da nutsuwa? Kana ganin halin da mahaifina yake ciki ne zaka zo min da wannan maganar banzar ? Ta yaya kake tsammanin zan iya maka bayani a yanzu bayan ina cikin tashin hankali da damuwa, koda jin haka sai ran mubairu ya baci ya daka min tsawa mai karfi tare da nunani da dan yatsa yace babu ruwana da batun halin da mahaifinka yake ciki domin kuwa umarnin sarkina na gaba dashi maza ka sanar dani abinda nazo sani kafin fishin sarki ya tabbata a kanka yana gama fadin hakan sai ya zauna a kusa da ni ya fiddo littafi, tawada da alkalami domin yin rubutu ni kuwa sai na tattare hannun rigata kamar zan zauna a gabansa amma sai na shammaceshi na gabza masa wawan naushi a fuska sabo da karfin naushin sai da ya wuntsila da baya sau uku a lokacin da jini yai feshi daga cikin bakinsa, ai kuwa sai ya taso da alkafira yai tsalle ya doki tawa fuskar da kafarsa, nima na gwaru da bango na fasa baki kafin na mike tsaye ya danneni kuma ya zaro wata wuka zai caka min a kirjina sainayi wuf na rike hannunsa, a sannan ne likita da sauran hadimanmu suka kurma uban ihu suka ruga waje da gudu suna kiran dakaru domin su kawo dauki, yarima huzein ne kadai tsaye a gabana yana kallon abinda ke faruwa jikinsa na karkarwa sabo da tsananin razana mubairu yaci gaba da kokarin dannan wukarsa a cikin kirjina, ni kuma naci gaba da kokarin hanashi samun nasara, amma sai karfinsa ya rinjayi nawa har wukar tasa ta dan sokeni na kwalla ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da naji, a lokacin da jini ya fara bulbulowa daga cikin kirjina duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance a gefe daya yana shara barci bai sani ba Koda yarima huzein yaga saura kiris mubairu ya sami nasarar hallakani sai yai wuf ya zare wuka a jikinsa ya dako tsalle sama ya sokawa mubairu a wuya take wukar ta lume ta faso makogwaronsa ya sulale kasa matacce huzein ya sunkuya a rikice ya kama Wukar tasa domin ya zareta daga cikin wuyan mubairu A dai dai wannan lokaci ne dakaru sarki shardas suka rugo izuwa cikin dakin su da yawa rike da makamai, koda suka ga yarima huzein yana zare wuka a cikin wuyan muhairu kuma gashi ya zama gawa sai suka yi caraf suka daureshi ni kuwa sai na taso da sauri izuwa kansu na hausu da sara da suka domin na kwaci dana a hannunsu duk da cewa suna da yawa amma sai da na tarwatsa su na kashe sama da mutum arba in Al Amin Ahmed Misau Ke Typing, ina cikin tsakiyar yin yaki dasu ne naji anyi min wani wawan duka a kirji saboda karfin dukan sai da nayi sama na gwaru a jikin katangar dakin na fado kasa a galabaice lokacin dana farfado sai na tsinci kaina a tsakiyar fadar sarki shardas kwance a kasa A gefen damata yarima huzein ne a daure cikin sarka a haguna kuma mahaifina ne tare da dukkan dakarunmu da kuyanginmu suma duk a daure cikin sarka zaune akan karagar mulki sarki shardas ne rungume da gawar dan uwansa muhairu yana ta faman rusa kuka, nan take zuciyata ta buga da karfin gaske na kamu da tsananin tsoro irin wanda ban taba jinsa ba a rayuwata ba komai ne ya sa ni jin wannan tsoro ba face tunanin cewa sarki zai kashe mune gaba dayanmu, idan ya kashemu kuma matata luzuraina ta mutu a wajen haihuwa shike nan fa duk burinmu ya tarwatse kuma lokacin faduwar kasarmu yazo a dai dai wannan lokaci ne yarima huzein ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo masa yace yakai abba na ka gafarceni domin na janyo mana abinda zai kawo karshen mu gaba daya AA Misau Sunana sa adda naji wannan batu sai hawayen takaici ya zubo min na dubeshi nace yakai dana baka bukatar rokona gafara domin baka aikata laifin komai ba tabbas ka kashe muhairu ne domin ka ceci rayuwata babu wani da da zai bari a kashe mahaifinsa a gaban idanunsa muddin zai iya hanawa koda jin wannan batu sai mahaifina ya dubi yarima huzein cikin alamun tsananin tausayi a lokacin da shima hawaye ya zubo masa yace yakai jikana huzein hakika kayi babban kuskure daka ceci rayuwar mahaifinka a hannun muhairu domin hakan zai janyo asarar da babu abin da zai biyata gama fadin hakan ke da wuya sai sarki shardas ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya ajiye gawar muhairu akan karagar sannan ya share hawayansa ya dubi mahaifina fuskarsa a murtuke sannan ya dubeni kuma ya dubi huzein yace yaro ka kashe mini dan uwa wanda shi kadai ne ya rage mini a duniya inda zan kashe gaba dayan mutanen kasarku mazanku da matanku jininku ba zai goge bakincikin abinda na rasa ba zan dasawa mahaifinka bakin cikin da har ya mutu ba zai manta da ni ba domin hakan ne kadai zai sa zuciyata ta lafa daga ruruwar wutar bakinciki koda gama fadin haka sai sarki shardas ya sa aka kwanceni daga cikin sarkoki sannan ya zare wata sharbebiyar wuka ya cillo mini ita na cafe kuma ya zare takobinsa yace nine na doki kirjinka dazu ka suma sa adda kake kashe dakaruna koda ka manta cewa na gaya maka cewa digon jinin daya na wakilaina da zan tura birninku dai dai yake da digon jinin mutanenku saba in to ku sani cewa a yanzu jinin mutum saba in ba zai zamo fansar dan uwana ba abinda nake bukata shine ina son uba ya yanka dansa da hannunsa yanzu a gabana ko kuma na kashe ka da dukkanin jama arsa gaba daya koda jin wannan batu sai mahaifina ya fashe da kuka ya risina ga sarki shardas kuma ya zube kasa gaba daya ya yi masa sujjada sannan ya dago kai ya dubeshi a lokacin da hawaye ke shatata bisa kumatunsa ya kuma dubi gaba dayan fadawan sarki shardas da mutanan gari yace yakai sarkin duniya ka dubi yadda na kaskanta kuma na wulakanta haka a gaban talakawanka a matsayina na sarkin da ya gawurta a wannan nahiya tamu ka dubi darajarr sarauta ka canja wannan nufi naka koda jin haka sai sarki shardas ya girgiza kai yace ai bana yin magana biyu na gama yanke hukunci ko danka ya yanka nasa dan yanzu take ko kuma na kasheka a gaban idansa kuma na kashe gaba dayan dakarunka da kuyanginka da duk hadimanka, mahaifina ya fashe da kuka yace yanzu jinina ni kadai ba zai fanshi jinin dan uwanka ba ? Sarki shardas ya dubi katon badakarensa mai rike da wata katuwar gudumar danko yace dashi yakai KALBAN ka buga gangarka sau goma idan yarima hulbasu bai yanka dansa ba kafin bugu na goma zan kashe mahaifinsa da duk jama arsa koda jin wannan umarni sai kalban ya daga gudumarsa ya doki wata katuwar ganga dake rataye a jikin wani dogon karfe take sautin gangar ya cika birnin gaba daya a dai dai wannan lokaci ne huzein ya kama jan guiwarsa kasancewar a daure yake cikin sarka ya iso gabana ya kwanta kasa ya dubeni yana mai murmushi gami da zubar da hawaye yace yakai abbana ma za ka yankani domin ka kubutar da mahaifinka da jama armu ka sani cewa zan mutu a cikin farin ciki tunda da jinina ya zama fansa ga rayuka masu yawa a wannan lokaci kalban yaci gaba da buga gangarsa har yayi bugu na biyar sa adda naji wannan batu na dana huzein sai hawaye ya zubo mini na dubeshi nace ka gafarceni yakai dana kayi sani cewa zan yanka ka ne ba don na ceci rayuwata ba ko ta ubana ba sai don Rayuwar jama armu ga su can wadanda suka sallama rayuwarsu don biyayya a garemu lallai ina son su koma gida a raye domin su rungumi iyalinsu......... BABBAR MAGANA KENAN SHIN HULBASU ZAI YARDA YA YANKA DANSA YARIMA HUZEIN ? . IDAN YA KASHE SHI IDAN YA KOMA BIRNIN ASKANDARIYYA MAI ZAICE DA MAHAIFIYARSA ? . SHIM MAHAIFIYAR YARIMA HUZEIN TANA HAIHUWA LAFIYA? . INA LABARIN JARUMA SIYAMA DASU YARIMA HULKAS ? . Marubucin Littafin Yace Mu Hadu A Littafin Tsatsuba Na gaba Don Jin Ci Gaban Wannan Kasaitaccen Labari. Marubucin Littafin Wato The King Of Adventure Story Malam Abdul aziz Sani M/Gini Saikuma Ni Al Amin Ahmed Misau wanda nake jagorancin typing din wannan littafi nake cewa Mu zama lafiya saimun hadu a littafi na bakwai.... Dont Forget My Name AA Misau TSATSUBA 7 Littafi na bakwai 7 Hausaebooks Abdulaziz sani M gini Made by:- Shuraih Usman Domin samun wasu littatafanmu sai ku shiga nan kuyi like http://fb.com/hausaebooks SATSUBA Littafi Na Bakwai (7) Part A. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Lokacin da Sarki Hulbasu ya gama fadawa dansa yarima Huzein wannan bayani sai ya rufe idanunsa a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa ya yanga Yarima Huzein tare jini yai tsartuwa daga cikin wuyan huzein a lokacin da Hulbasu ya kurma uban ihu na takaici da bakin cikin ganin cewa ya yanka dansa da hannunsa shi kuwa mahaifin Sarki hulbasu wato Sarki yana ganin sa adda Hulbasu ya yanka yarima huzein da hannunsa sai nan take ya hadiyi zuciya ya sulale ya baje a kasa matacce koda sarki hulbasu yaga mahaifinsa ma ya mutu kuma ga gawar dansa yarima huzein a gabansa sai ya kama sambatu yana kai kawo a tsakanin gawarwakin biyu tamkar mahaukaci sabon shiga shi kuwa sarki Shardas sai ya bude da dariyar farin ciki yayi ta kyalkyala dariyar tamkar ba zai taba dainawa ba lokacin da sarki hulbasu yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa hailur sai yayi shiru sa adda hawaye ya zubo masa yana hada idanu da hailur sai yaga shima hawaye ke sartu akan kumatunsa yana mai kurawa hulbasu idanu cikin tsananin tausayawa hailur yaja dogon numfashi yace tabbas cin zarafin da sarki shardas yayi maka ya ninka nawa saboda kai ya tilastaka ka yanka danka da hannunka kuma ya zamo sanadin mutuwar mahaifinka kuma yanzu gashi ya mai daku bayinsa tunda duk arzikin kasarku wajansa yake komawa, hakika damu daku yanzu bamu da wani makiyi a doron kasa wanda yafi sarki shardas, kuma a halin yanzu yafi karfinmu babu abinda zamu iya yi masa kuma muna cikin mugun hadari na masifarsa domin da zarar ya fahimci cewa ina raye kuma ina tare dakai mu duka har iyalanmu tamu ta kare, koda hulbasu yaji wannan batu sai yai ajiyar zuciya cikin alamun tsananin fargaba da takaici sannan sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, yace to yanzu shike nan haka zamu cigaba da zaman jiran ranar da sarki shardas zai gano sirrinmu sannan yazo ya gama damu hailur ya girgiza kai yace babu wani abu wanda ba zai yiyu ba a cikin wannan duniya face ba a jarraba shiba komai nisan jifa kasa zai fado kuma komai karfin mutun da isar mulkinsa akwai ranar da zai fadi babu wata cuta wacce bata da magani kamar yadda boka zamaranu ya shaida maka cewa zaka iya hallaka sarki shardas amma sai an mallaki hular lamsara to me zai hana mu tafi neman wannan hula tunda ance mai nema yana tare da samu gwara mu rasa rayukanmu a kokarin neman wannan hula da dai mu zauna har makiyinmu yazo ya samu nasarar hallaka mu muna ji muna gani ka sani cewa ba karamin aiki bane a gabanmu idan har muna son mu ga bayan wannan babban makiyi namu dolene sai mutum ya sadaukar da wani abu idan yana son ya sami wani da farko dai dolene ka ajiye sarautarka kuma ka cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarka dolene mu kawai da gaba dayan dakarun sarki shardas da hadiman da suka rako matata domin mu aiwatar da abinda ke gabanmu ka ayyana a ranka cewa zamu fita neman hular lamsara ne ba don komai ba sai domin mu dauki fansa akan sarki shardas shin yanzu zaka iya hakura da karagarka ta mulki da kuma kasarka da jama arka domin cika wannan buri naka koda jin wannan batu sai hawayan takaici ya zubowa sarki hulbasu yace ai bani da wani zabi wanda yafi na hakura da komai din nayi wannan gagarumar tafiya in ba haka ba kuwa zan rasa komai da kowa nawa yanzu akwai abu daya nake tunanin yadda zamu sami nasarar yinsa a cikin nasara wato yadda zamu iya kawai da dakarun da suka rako shadila, koda jin wannan batu sai hailur yayi murmushin yake yace haba ya shugabana a cikin kasarka fa suke wadannan dakaru ai kowa a gida sarkine, ni ina da shawara bisa yadda zamu kawai da su cikin kankanin lokaci a saukake ba tare da mun fuskanci wata matsala ba shawarar kuwa guda biyu ce da farko zamu iya amfani da sanya musu guba a cikin abincinsu duk suci su mutu idan kuma wannan hikima bata yi aiki ba sai mu ritsasu a cikin masaukinsu mu da dakarun masu yawan da ya ninka nasu sau uku mu yakesu, ni ka bar mini jagorancin dakarun da za suyi wannan aiki iana mai tabbatar maka da cewa zan yi iya kokarina na tabbatar da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba don kada yaje ya kai wa sarki shardas labarin abinda muka aikata, lokacin da sarki hulbasu yaji wannan shawara guda biyu na hailur sai yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya kuma ya dubeshi cikin alamun damuwa da fargaba sannan yace da farko dai idan muka yi yunkurin kashesu da guba ba lallai bane ya kasance cewa dukkaninsu zasu ci abincin kaga kenan akwai yiyuwar wani daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa kuma ya sulale daga cikin birnin ya gudu bamu sani ba idan kuwa hakan ta faru asirinmu ya gama tonuwa haka kuma muka ce zamu yakesu anan cikin birnina a masaukinsu jama a zasu jiyo kururuwar yakin koda kuwa cikin dare ne sannan kuma ka san cewa suma fa zakwakuran mayaka ne wadanda suka san TUGGUN YAKI za a iya samun wani daga cikinsu ya sami damar sulalewa ya gudu idan ma hakan bata faru ba babu mamaki a cikin jama ar gari akwai dan leken asirin sarki shardas mai sa ido akan wadannan dakaru Nasa da suka rako gimbiya shadila izuwa kasata don haka ko wani dan motsi ya gani wanda bai yarda dashi ba yana iya garzayawa yakai labari, lallai akwai mummunan hadari a cikin duk wadannan batu sai ya numfasa yace ya kai abokina yakamata ka sani cewa matsoraci bashi zama gwani ko waye don haka dolene mutum ya siyar da ransa wajan neman sa a bisa bukatar dake gabansa ko ka so ko kaki ko ka gudu ko ka tsaya watarana sai sarki shardas yazo ya cika da yaki har gida tinda shi makiyi har abada a cikin kokarin ganin bayan makiyinsa yake lokacin da hailur yazo nan a zancensa sai jikin sarki hulbasu yayi sanyi ya gamsu a ransa cewar bashi da wani zabi wanda yafi ya yi amfani da wannan shawara ta hailur don haka sai yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi yace na amince da duk shawarar da ka bani a daren yau zan hadaka da amintaccen sarkin yakina domin ku shirya duk abinda kuke ganin ya dace akan wannan makiyi namu nidai kawai na baku wuka da nama amma ina son ku gaggauta shirya yin wannan gagarumar tafiya tamu ta neman hular lamsara Al amin Ahmed Misau nake magana koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube hailur yayi godiya sannan ya mike tsaye da nufin ya fice daga cikin dakin sai sarki hulbasu ya ruko hannunsa yace ya zaka tafi baka tsaya kagana da tsohuwar matarka ba babu wanda ya isa ya raba Hanta da jini soyayyarka da matarka shadila tafi gaban wani dan adam ya rubuta saboda tsoron sarki shardas ba zan hanaka ka gana da ita ba tuni na shirya wannan ganawa naku koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya tafi zuwa bakin kofar wannan daki da suke zaune ya kira sunan wani hadimi nasa yace dashi ya ruga izuwa can cikin gidan sarautar bangaren matarsa ya taho da shadila cikin hanzari hadimin yace an gama ya shugabana nan take ya ruga da gudu izuwa cikin gidan sarautar shi kuwa sarki hulbasu sai ya yiwa Hailur sallama ya tafi tafiyarsa keda wuya sai farin ciki mai dumbin yawa ya turnuke hailur yaji kamar duniyar nan gaba daya aka bashi don haka sai ya mike tsaye ya kama kai kawo fuskarsa cike da annuri gami da farin ciki wanda ba zai misaltu ba yana cikin wannan haline yaji an turo kofar dakin an shigo cikin sauri ya waigo kawai sai yayi arba da shadila a tsaye ta kura masa idanu tana zubar da hawaye daki daki nan take shima idanunsa suka ciko da kwallar ya fara zubar da hawaye tsawon yan dakiku sun kurawa junansu idanu suna ta zubar da hawaye kamar ba zasu daina ba daga can kuma sai suka yi murmushi a tare suka ruga suka rungume junansu kuma suka fashe da kukan farin ciki na sake saduwa suna masu kankame juna sosai ba tare da son saki juna ba sai shadila ta ce yakai mijina yanzu ashe kana nan raye a cikin wannan duniya amma ban sani ba koda jin wannan tambaya sai hilairu ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace yake abar begena dare da rana Al amin Ahmed Misau kiyi sani cewa ban taba mancewa dake ba tsawon dakika daya daga sa adda muka rabu kawo i yanzu ban taba zaton cewa zamu sake saduwa ba a cikin wannan duniya tunda ke kanki kin sa a ranki cewa na mutu na sani cewa sarki shardas ya aureki bisa dole to amma abu daya nake so na gani shin kin haife cikin dana dana barshi a tare dake ko kuwa sarki shardas ya kasheshi, koda jin wannan tambaya sai shadila tayi shiru ta kasa bashi amsa cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin na shadila ya girgiza kafadunta ya ce cikin daga murya ki gaya mini gaskiyar ala amari kada ki boye mini komai shin dana yana raye ko ya mutu koda jin haka sai shadila ta fashe da kuka ta kasa bayani saboda tsoron abinda zai biyo baya kwatsam sai sukaji an turo kofar dakin an shigo duk su biyun suka waiga bayansu a firgice da sauri don ganin ko wane ne ya shigo ba wani bane face yarima Hulkas tsaye idanunsa suna zubar da hawaye kuma ya kurawa hailur idanu koda shadila taga hulkas tsaye a gaban hailur kuma taga irin kallon da yake yi masa har yana zubar da hawaye sai ta kamu da tsananin tsoro jikinta ya kama tsuma saboda ta fahimci cewar abinda take tsoron kada ya faru ya gama faruwa cikin sanyin jiki da alamun tsananin takaici hulkas ya nufi inda shadila ke tsaye a lokacin da hailur yabi hulkas da kallo ko kiftawa baya yi domin ya gane cewa lallai wannan yaro hulkas dansa ne domin hatta irin gabobin jikinsa iri daye ne nan take shima hailur yaji idanunsa sun ciko da kwallah lokacin da hulkas ya iso daf da shadila sai ya kama hannayanta ya ruke yace yake ummina menene dalilin da yasa tuntuni baki shaida mini cewa sarki shardas ba shine mahaifina ba, kinsan irin tsananin son da nake yiwa sarki shardas, kuma kinsan yadda na shaku da shi ainun tun ina kankani kawo i yanzu, yanzu da wanne ido zan fuskanceshi Al amin Ahmed Misau Nake magana A matsayin babban makiyina Alhalin shine ya rene ni ya inganta rayuwata ki sani cewa sarki hulbasu ya bani labarinki kaf da asalinki da yadda sarki shardas ya murkushe jama arku kuma ya jefe mahaifina karkashin wannan tsauni mai mugun zurfi sannan ya kamaki da karfin tsiya ya Maisheki matarsa har da dub irin barazanar da yake yi miki akan kada ki sanar dani komai sannan ya sanar dani yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dansa na cikinsa sanadin da ya zamo mutuwar mahaifinsa ya kunsa masa bakin cikin da har abada ba zai gushe ba a doron kasa tabbar sarki shardas ya cika babban azzalumi da babu kamarsa a doron kasa kuma dolene na kasheshi da hannuna, koda yarima Hulkas yazo nan a zancensa sai ya kurma uban ihu kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa biyu ya fashe dda matsanancin kuka koda ganin haka sai itama shadila ta fashe da kuka ta kasa rarrashinsa cikin sanyin jiki hailur ya dingisa ya isa gaban hulkas ya sunkuya ya dafa kafadar hulkas, koda hulkas yaji hannun hailur ya tabashi sai yai shiru tamkar daukewar ruwan sama sannan ya dago kai suka kurawa junansu idanu a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai hulkas ya mike tsaye zumbur ya rungume hailur suka fashe da kuka a tare komai rashin tausayin mutum idan yaga lokacin da wannan da da mahaifinsa suka rungume junansu alhalin basu taba ganin juna ba basu san juna ba sai yau dolene zuciyarsa ta karaya ya tausaya musu Al amin Ahmed Misau Sunana, Koda ganin abinda ya faru sai farin ciki ya lullube shadila sai da hailur da hulkas suka dan jima a kankame da juna sannan hailur ya janye jikinsa daga cikin na hulkas ya dubeshi a cikin nutsuwa yace yakai dana ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani cewa komai yana da lokacinsa ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu in da duniyar nan gaba daya zata taru kaf ba zata iya kawar da sarki shardas ba saboda yana kan sharafinsa babu mai iya ganin bayansa a yanzu face jarumin da ya mallaki HULAR LAMSARA; Kai ni Al amin naji sai wani Zancen Hular Lamsara suke da wahalar Samunta Naga dai Nima jarumine fa Saboda haka nima bari na dauki Takobina Na je neman wannan Hula domin na kawar da Sarki shardas Hahahaha zan iya Kuwa Freinds ? Bisa wannan dalili ne ni da sarki Hulbasu muka yanke shawarar mu rokeku kuma mu kawar da dukkanin dakarun da suka rakoku sannan mu bazama duniya neman Hular lamsara saboda kai kanka yanzu rayuwarka na cikin mugun hadari idan har shardas ya gano ka san cewa shine ya tarwatsa rayuwar mahaifinka na asali ba zai barka da raiba to amma akwai wata matsala guda daya, koda jin wannan batu sai hulkas ya dubi hailur cikin alamun matukar mamaki yace yakai abbana me cece matsara kuma Hailur yace sarki shardas ma ba zai iya hallaka ka ba face ya samo wannan hula ta Lamsara kuma a halin yanzu tuni shida bokansa sun fita farautar wannan hula sun bar garinku a cikin mugun hali domin yanzu haka ana fama da fatara yunwa da fari a kasar tun daga ranar da kuka baro birnin kai da mahaifiyarka ya zamana wajibi mu gaggauta tafiya neman hular lamsara tun gabanin makiyinmu sarki shardas ya rigamu samu Koda jin wannan batu sai hankalin yarima Hulkas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya musamman da yaji cewar mutanan kasarsu na can cikin mugun hali na fatara da yunwa kuma ga batun gagarumar tafiyar dake gabansa ta neman hular lamsara hular da babu wanda ya san inda take.... Kai bari dai na dakata A nan domin nima naje nayi shirin tafiya neman wannan hUla saboda naga Alamar sun tsorata suna tsoron fita nemanta amma akwai wanda zai iya rakani kuwa hahahaha Kafin nan Nine Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square nake cewa sai gObenkuSATSUBA Littafi Na Bakwai (7) Part B. . Marubucin Littafin Abdul azis Sani M/Gini Typing by.. Al amin Ahmed Misau. Inkiya.. Shagala Ko Guyson whtsap No. 08064594218 Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba . Labari ya Zowa Shagala Cewar:..... . Hular da babu wanda ya san ina take Shikuwa yarima barmas tunda suka shigo cikin wannan daki tare da yarima hulkas ya zauna a gefe daya yana ta sauraran bayanin da Hailur ke yiwa hulkas sai takaici da tausayi suka sashi ya kama zubar da hawaye dama da dadewa mahaifin sarki hulbas ya bashi tarihin yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dan uwansa yarima Huzein wato yaya ga yarima barmas sanadin da ya zamo na mutuwar kakansa kenan nan take zuciyar yarima barmas ta kama tafarfasa kamar zata kone babu abinda ya tsana a duniya sama da sarki shardas A cikin wannan haline aka ga

Chapter 13 of 21