Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TSATSUBA Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator::- Shuraih 99% You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com TSATSUBA Littafi Na Daya (1) Part A. Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini the king of Adventure story Marubucin ya fara da cewa.... SARAUNIYA LARBISA TA KASANCE GAGARUMAR ATTAJIRA kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata kasa babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya girma da yawan jama ah a zamaninta sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA domin duk kasar da suka durfafa da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta babbar matsalar sarauniya larbisa itace bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun tabbatar mata da cewa ba zata taba haihuwa ba sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya idan kuwa tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo mata wani littafi mai suna TSATSUBA wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata A salin wannan littafin mallakin sarkin bokayan Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba'in daya rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa littafin lakabi da suna TSATSUBA Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma makarinsa na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da suka gabata bokayen duniya da yawansu suka bazama neman wannan littafi har suka hallaka bisa wannan tafarki kuma duk wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin lokacin da sarauniya sarauniya larbisa taji wannan batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya bayan tayi dogon tunani da nazari saita watsa shela a ko ina a cikin duniya cewa duk wanda ya samo mata wannan littafin na TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya shidai wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai suka bazama neman littafin TSATSUBA suka rinka mutuwa a kokarin neman nasa. Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa sarauniya larbisa littafin TSATSUBA alhalin yasan cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya mallakarta kuma zai sami kowace irin dukiya da yake so ko matsayi ? Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar gimbiya larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci data bayar da shelar a nemo mata littafin TSATSUBA shekaranta ashirin daidai A duniya kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau kan karagar mulki sarauniya larbisa bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin tsufa ya risketa don kada mulkinta ya tafi hannun wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage a irin zuri ar gidansu wata rana sarauniya larbisa na zaune a fadarta ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba saiga wani almajiri ya shigo yana bara har dakaru sun tareshi zasu koreshi waje sai sarauniya larbisa tayi musu tsawa suka kyaleshi nan take larbisa ta mike tsaye daga kan karagar ta taka taje har wajen almajirin ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace zan baka abinci kaci ka koshi yanzu ya kai wannan tsoho amma ba zaka iya biyana ba da komai domin ni bana bukatar abinci ko dukiya koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta ja tsohon har zuwa cikin gidan sarauta Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta mutanan gari da sauran masu fada aji saboda ita dai sarauniya larbisa bata kasance mai tausayi da jin kan talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar da abin hannunta face akan bukatarta kawai lokacin da sarauniya larbisa takai wannan almajiri cikin babban falo na turakarta wanda girmansa yakai na wani gida guda sai tsohon ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalle domin bai taba tsintar kansa a cikin waje mai ni ima da daula ba irin wannan gaba daya falon a shimfide yake da wata irin dadduma mai tsananin laushi da zarar ka taka daddumar sai kaji kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi kujerun dake zagaye a falon gaba daya anyi sune da zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun dawisu akayi shi da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima ruwa na ta zuba a cikin dawisun yana taruwa akan wani katon faranti na lu'u lu'u abin dai akwai ban sha awa da ban al ajabi. A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya wadanda suma da lu u lu u akayisu sai sheki da walwali suke tayi Baya ga wannan wani irin kamshi na tashi a cikin falon wanda mutum bai san ko daga ina yake fitowa ba duk inda almajirin ya duba a cikin falon sai yaga kuyangi ne tsala tsala sunata hidimar goge goge da gyare gyare tabbas wannan wuri Ya cika aljannar duniya Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini ainun ya ga cewa shidai bai kasance basarake ba ina shi ina zama akan irin wannan kujera kawai sai ya zauna a kasa dirshan bisa wannan darduma mai taushi koda ganin haka sai sarauniya larbisa da kuyanginta suka bushe da dariya domin basu taba ganin wanda yayi wannan kauyancin ba sarauniya larbisa ta dubi shugabar kuyangin wacce ake kira da suna HULAIRA tace da ita aje a kawowa bakona duk irin kalar abincin dake gidan nan hulaira tace an gama ya shugabata nan take hulaira ta juya ta fice daga cikin falon ita kuma sarauniya larbisa saita dubi almajirin tace bayan ka huta zan dawo gareka da yamma domin muyi yar hira kafin na sallameka ka tafi saboda kazo mini da bayani wanda yaje fani a cikin wasi wasi da kace idan na ciyar da kai zaka ciyar dani har abada alhalin ni babu abinda na nema na rasa na gada abinci ko dukiya lallai ba zaka tafi ka barni a cikin duhu ba saika wayar mini da kai koda gama fadin haka sai sarauniya ta wuce izuwa can cikin turakarta sai data jima tana tafiya sannan ta kule almajirin ya daina hangota nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa a ransa wai shin yaya cikin turakar sarauniya zai kasance a kyau da kawatuwa? Lallai dole ne ya ninka nan falon a komai jim kadan da tafiyar sarauniya larbisa saiga wadansu kuyangi daban su goma sha biyu sun shigo cikin turakar kuma kowacce na dauke da katon faranti abinci akan kowanne faranti akwai abinci kala shida nan take kuyangin suka ajiyewa almajirin farantin abincin a gabansa suka juya suka fice Al amarin daya firgita gaba dayan kuyangin dake cikin falon kenan suka fara tunanin anya kuwa wannan almajirin mutunne a iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin mutumin da ya taba cinye koda kwano daya na abincin kasancewar kwanukan manya ne kuma cike suke taf da abinci sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye kwano daya lokacin da almajirin ya gama da abincin farantin dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya gwamutsa abincin kwanon shidan akan farantin duka ya kama ci nan da nan ya karar da abincin ya janyo faranti na uku koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin suka firgice suka ruga wajen falon a dimauce suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin nima kaina ganin wannan hadin nasa yasa na matsa daga kusa dashi. Bari na dakata a nan domin jin ra ayinku game da wannan littafi shin ya kayatar daku mu ci gaba ko kuwa mu chanza wani rince Auwal Auwzab > ‎MAZA GUMBAR DUTSE TSATSUBA Littafi Na Daya (1) Part B. . nan take subauratu yayi sujjada ga sarauniya larbisa yana mai bude fukafukansa ya kwashi gaisuwa sannan yace da ita yake sarauniyar duniya fadi duk irin tambayoyin da kike son ki gabatar dasu a gareni ko kuwa adadin su yakai na yawan gashin dake jikin rago ko tinkiya domin babu wata iska anan wacce zata dami tsufana. Lallai zan baki amsoshin tambayoyinki ko da kuwa zan kwana dubu a zaune ina yi miki jawabinsu koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da da dariya sannan tace aini tambayoyina guda uku ne kacal tambaya ta farko itace naji Huzallatul marwasu yace abokan tafiyarmu izuwa inda zamu samo littafin Tsatsuba su hudu ne kuma ukun cikinsu matane na hudun kuma namijine to wai shin menene amfanin kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya kuma a wane garuruwa zamu riskesu, Tambaya ta ta biyu itace akan wane dalili wadannan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda suyi mana rakiya zuwa wannan tafiya mai tsananin hadari? Tambaya ta ta uku itace ta karshe shin kasan dalasiman tsafin da za a karanta a lalata gaba dayan tsafin dake cikin littafin tsatsuba? Sa adda Aljani saubaratu yaji wadannan tambayoyi guda uku daga bakin sarauniya larbisa sai yayi shiru yana mai kura mata idanu cikin Al ajabi ba wani abu bane ya sa yayi shiru ba kuma ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta da ya dimautashi koda larbisa ta fahimci halin da Aljani saubaratu ya shiga saita daka masa tsawa ta ce shin zaka bani amsar tambayoyina ne ko kuwa zakaci gaba da kallona ne har saika gaji nan take Aljani saubaratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa cikin nutsuwa ya ce ki gafarceni ya shugabata kiyi sani kinyi mini tambayoyi ne masu matukar mahimmanci a cikin wannan tafiyartamu kuma wadanda zasu dauki dogon lokaci ina yi miki bayaninsu da farko dai abokin tafiyarmu wanda zamu fara tafiya nema ba wani bane face JARUMA SHUMAIRA yar mafarauci IMSHAL, a halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki wanda yafi shumaira ibn imshal sanin sirrin daji da iya farauta da kuma juriyar wahala kafin mu isa kogon kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba sai mun keta ta cikin wadansu dazuzzuka guda uku a cikin daji na farko sai mun shafe wata shida muna tafiya sannan zamuje karshensa, A cikin wannan daji wanda aka yiwa lakabi da shajarul shaljuma akwai mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye wadanda kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu hakama tsafi baya aiki a kansu babu abinda zai ceci mutum daga sharrinsu face wanda ya san sirrinsu kuma ya kware a iya farauta gami da jurewa wahala lallai idan babu jagorancin jaruma shumaira bamu isa mu ratsa ta cikin dajin shajarul shaljuma ba a raye Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba kowa bane face jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa gami da jiyo takun sawu komai nisansa Daji na biyu wanda ke gaban dajin Shajarul shaljun ana kiransa da suna Ujurul majnan babu komai a cikin wannan daji face wadansu irin gabza gabzan dodanni masu cin naman mutane da na aljanu da dabbobi suna da kaifin basira wajan dana mugayen tarkuna kuma suna da tsananin gudun tsiya yadda komai tazarar dake tsakaninsu da mutum suna iya cinmmasa jaruma larifat ce kadai zata iya gano duk irin tarkunan da wadannan dodanni suka dana kuma ta iya jiyo sautin sawayen dodannin suke sannan ta iya jiyo sawayensu a duk sa adda suka rugo don kawo farmaki, Daji na uku wanda ke gaban dajin Ujurul majnan ana kiransa da suna Darul Maut Babu komai a cikin darul maut face wadansu mugayen kunamai da macizai bakake wadanda da zarar sun sami nasarar sarar mutum ko harbinsa sau daya take jikinsa ke zagwanyewa ya narke Abokiyar tafiyarmu ta uku itace jaruma Lubaina Yar sadauki Sulzainu Jaruma lubaina ce kadai zata iya yakar wadannan kunamu da macizai ta hanasu cutar damu saboda duk duniya babu wani jarumi mai zafin namanta kuma tana da wata rantsatstsiyar takobi da babu abin da bazata iya tsargeshi ba koda kuwa dutse ne ko karfe, muna fita daga cikin dajin darul maut Bayan tafiyar wata Hudu zamu riski Kogon kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba ya shugabata kiyi sani cewa shiga cikin kogon kitabul sihir dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kudinsa saboda tsananin masiful dake cikinsa da kuma irin gagarumin tsaron da aka yiwa littafin tsatsuba babu wanda zai iya samun nasarar shiga har cikin kogon kitabul sihir ya isa har inda littafin tsatsuba yake a raye kuma cikin kuzari face jarumi Ruhaisu ibn Zaiyanu daga Sarkin Birnin Kufa. A halin yanzu duk duniya babu wani jarumi mai karfin damtsensa sannan kuma yana da tsananin sa a da rabo bisa dukan abinda yasa a gabansa a yanzu haka yana cikin tsananin bakin ciki bisa mutuwar masoyiyarsa wacce yake tsananin kauna fiye da komai a duniya, duk da cewa kama da wane bata wane Ya shugabata ni ina da tabbavin cewar zaki iya yaudarar jarumi ruhaisu da tsananin kyawunki ki nuna masa soyayya da haka ne kadai zaki iya ribatarsa ya amince yayi wannan tafiya har ya shiga cikin kogon kitabul sihir ya dauko mana littafin tsatsuba Lokacin da Aljani subauratu yazo nan a zancensa sai sarauniya larbisa tayi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta fada cikin kogin tunani mai zurfi har izuwa tsawon wani dan lokaci daga can kuma sai ta dago kanta ta dubi Aljani subauratu tana mai ajiyar zuciya tace yakai subauratu kayi sani cewa hakika kazo mini da babban al amari mai wuyar fahimta da gamsuwa wanda dole sai dai mutum yayi kundunbala ya aikata shi ni kam babu gudu kuma babu ja da baya a cikin wannan Al amari amma ina da sauran tambaya guda daya rak a gareka yanzu wacce idan ka gamsar dani da amsarta bani da sauran fargaba tambayar tawa kuwa itace tayaya zamu hada wadannan abokan tafiya tamu su hudu a cikin kankanin lokacin Alhalin kowannansu yana can wani bangaren daban na duniya harmuyi wannan tafiya tare dasu wacce takai ta tsawon shekara guda? Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya , lokaci guda kuma ya hada rai yace ai riskar wadannan jarumai hudu a cikin yini daya jal a wajena dai dai yake da shan ruwa a gareki makurwa daya don haka ki kwantar da hankalinki kawai ki fara shirye shiryen wannan tafiya koda jin wannan batu sai fuskar sarauniya larbisa ta fadada da murmushi bata san sa adda ta kama kyalkyala dariya ba koda ganin haka sai tsoho huzallatu marwasu da Aljani subauratu ma suka tayata kyalkyala dariyar.. A yayinda ni kaina na tayasu kyakyatawa kamar yadda sarauniya larbisa ta fada haka al amarin ya kasance wato a cikin kwanaki uku dai dai suka kammala dukkan tanadi na wannan tafiya ita da tsoho huzallatul marwasu suka hau bisa wadansu ingarmun dawakai guda biyu sannan aka debi dakaru mutum arba in kacal tare da kuyangi goma masu yi mata hidima gami da isashshen guzuri na abinci da dinare mai yawa aka kama hanya aka fice daga cikin birninta bayanta yiwa ta yiwa fadawanta da jama arta sallama akan cewar ba zata dawo ba sai bayan shekara guda sarauniya larbisa tayi shiga ne ta kayan yaki masu matukar kyau da kwarjini kuma ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle idanunta kadai ake gani shi kuwa tsoho huzallatul marwasu kaya na alfarma aka bashi ya sanya irin na sarakai kai kace ma shine da mulkin ba Larbisa ba lokacin da wannan tawaga ta shafe sa a uku ana tafiya a cikin daji ba tare da sanin inda aka dosa ba kuma dama larbisa ce akan gaba saitaja linzamin dokinta ta tsaya cak, Al amarin da ya baiwa huzallatul marwas da sauran abokan tafiyar mamaki kenan kowa ma ya tsaida nasa dokin, huzallatul marwas ya risina a gareta cikin girmamawa yace ya shugabata lafiya kuwa kika tsayar mana da tafiyarmu a nan? Koda jin wannan tambaya sai sarauniya larbisa ta dakawa tsoho huzallatul marwas tsawa tace akan wane dalili zamu ci gaba da tafiyar da bamu san inda muka dosa ba ka yiwa Aljani Sabauratu ibn kimasasa magana ya gaya mana inda zamu fara dosa domin nemo abokin tafiyarmu koda jin wannan batu sai huzallatil marwas ya bugi jakar hannunsa take aljani subauratu yayi magana yace ku nufi kudu zamu gajarce muku tafiyar wata uku izuwa yini biyu da rabi inda zaku riski Dajin Falmaz anan ne inda jaruma shumaira take wacce ita ce kadai zata iya wucewa damu ta cikin dajin shajarul Shaljum a saboda kwarewarta a iya farauta sanin sirrin daji dakuma jurewa wahala lallai kusan yadda zaku lallami jaruma shumaira a kan ta amince da yin wannan tafiya tare damu kada ku nuna mata isa ko iko ko dukiya domin in saboda sune ba zata amince ba koda gama fadin hakan sai aljani subauratu yayi shiru ba kara cewa uffan ba nan take sarauniya larbisa ta bayar da umarni aka sauya akalar tafiya aka durfafi kudu aka ci gaba da tafiya ba sassauci bisa mamaki sai kowa yaga tafiyar tana matukar yin sauri fiye da hasashen mai hasashe kai kace akan isaka suke tafiyar ba bisa doron kasa ba nan da nan suka wuce dazuzzuka da yawa har magariba ta riskesu basu hadu da wani mugun abu ba a sannan ne sarauniya ta bayar da umarnin a tsaya a yada zango domin A ci abinci a huta nan take kuwa akabi wannan umarnin bayan an kafa tantuna an dafa abinci sai sarauniya larbisa ta kirawo tsoho huzallatul marwas izuwa cikin tantinta domin suci abinci tare koda jin wannan tayi sai huzallatul marwas ya risina cikin girmamawa yace ya shugabata ashe har kin manta da ka idata? Ai idan har naci na koshi ba zan sake bukatar abinci ba sai bayan kwanaki ashirin da biyar sai dai kawai nayi ta shan ruwa koda jin wannan batu sai larbisa tayi murmushi tace tabbas haka zancenka yake na sha afat ne amma duk da haka bana son kadaici a yanzu zauna ka debe mini kewa cikin murna tsoho huzallatul marwas ya zauna a gefe guda a lokacin da sarauniya larbisa ta mike tsam ta kwabe kayan yakin dake jikinta ta ajiyesu a gefen shimfidarta ta alfarma ya rage daga ita sai wata riga mai shara shara a jikinta wacce ta baiyana dukkan surar jikinta. Koda tsoho huzallatul marwas yayi arba da wannan kyakkyawar sura ta sarauniya larbisa sai ya rude ya dimauce har kwallar takaici ta ciko a idanunsa A cikin ransa yace kash amma mazan duniya sun yi asara da basu mallaki wannan kyakkyawar mace ba tabbas inda ni saurayi ne kuma jarumi mai jini a jika to ko da zan rasa rayuwata sai nayi iya kokarina wajen ganin na mallaki wannan sarauniya ta kowane hali . Hm to tsoho huzallatul marwas kai tunda ka tsufa bazaka iya mallakar larbisa ba ai saika bawa Auwzab waje domin kuwa na shirya tsaf domin ganin na mallaki wannan sarauniya nikam saboda haka zan dakata a nan saikuma gobe idan Allah ya kaimu TSATSUBA Littafi Na Daya (1) Part C. . SAI NAYI IYA KOKARINA WAJAN GANIN NA MALLAKI WANNAN SARAUNIYA TA KOWANI HALI, haka dai tsoho huzallatul marwas ya ci gaba da zancen zuci gami da sambatu har sarauniya larbisa ta zauna tana mai harde kafafunta a gaban kwanukan abincin dake gabanta ta fuskance shi, koda tasa hannu ta debo loma guda ta bude baki, huzallatul marwas yayi arba da kyawawan hakoranta masu tsananin kyau da haske sai ya sake dimaucewa fiye da ko yaushe bai san sa adda kafafunsa suka kasa daukar nauyin jikinsa ba ya zame kasa kawai sai ji yayi sarauniya larbisa ta kece da dariya, cikin sauri tsoho huzallatul marwas ya mike zaune yana mai zazzaro idanu ya dubeta yace ya shugabata ina dalilin yin wannan dariya taki koda jin wannan tambaya sai larbisa ta hade fuska kamar zatayi kuka sannan ta ce yakai wannan tsoho kayi sani cewa ina sane na baiyana surar jikina a gareka ba don komai ba sai domin na tabbatar da abin da bokaye suka fada mini idan gaskiya ne cewar babu wani da namiji da zai ganni bai rude ba saboda kyawuna kaine namijin farko a duniya da ya taba ganin wannan jiki nawa kuma kaima na yarje maka hakanne saboda ka manyanta a kaina tunda ka isa ka haifi kamata yau shekara goma sha tara kacal a duniya kuma gashi babu abin da ban mallaka ba najin dadin duniya tunda gashi ina sarauta ta birnin da babu kamarsa a duniya sannan ina da dukiya mai tsananin yawan da ni kain ban san iyakarta ba abin da ya rage mini kawai shine na sami abokin rayuwa wato mijin da zan aura domin na sami magaji bokaye sun tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa ba har sai bayan na lalata duk sihirin tsafin da yake cikin littafin tsatsuba bisa wannan dalili ne na ki yarda nayi soyayya da wani da namiji a rayuwata har sai bayan wannan buri nawa ya cika Abinda nake tsoro shine kada soyayya tasa idanuna su rufe har nayi aure ba tare da na lalata sihirin littafin tsatsuba ba kaga kenan ba zan taba samun haihuwa ba, lokacin da sarauniya larbisa tazo nan a jawabinta sai tsoho huzallatul marwas yaji ya kamu da tsananin tausayinta cikin alamun tausayawa da murmai mai sanyi ya dubeta ya ce ya shugabata hakika akwai tausayi a cikin lamarinki kuma samun biyan bukatarki ba abune mai sauki ba sannan ina mai shawartarki daki taka tsantsan da wannan kalma ta soyayya domin abace mai hadarin gaske duk da cewar kin danne zuciyarki kin hanata yin soyayya yanzu nan gaba zata iya tankwaraki domin shi so abune wanda baya sallama kuma baya iso zai iya mamayarki a lokaci guda kamar yadda barci yake sace mutum koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da dariya har ta tafa hannayanta Al amarin da yayi matukar baiwa huzallattul marwas mamaki kenan daga can sai sarauniya larbisa ta nutsu ta daina dariyar ta dubeshi tace ni sarauniya larbisa na cika maka baki babu wani da namiji a wannan doron kasa wanda zai burgeni har na kamu da son sa saboda na tabbatar da cewar duk abinda yake takama dashi na fishi walau kyau, jarumtaka, mulki da dukiya yayin da huzallatul marwas yaji haka sai yayi murmushi yace ya shugabata abin da yasa kika fadi haka akwai kuruciya a tare dake kuma bakisan menene so ba to ki sani cewa shi so na gaskiya babu ruwansa da kyau ko matsayi abu ne kawai na haduwar jini wanda mutum ko aljan baya iya hadashi ko ya rabashi babu wani mai misali ko mai hange wanda zai iya tantance miki karfinsa ko yanayinsa face wanda ya tsinci kansa a cikinsa koda huzallatul marwas yazo nan a zancensa sai ran sarauniya larbisa ya baci bata san sa adda ta daka masa tsawa ba ta umarceshi da ya tashi ya fice daga cikin tantinsa Cikin firgita da biyayya tsoho huzallatul marwas ya risina yace ki gafarceni ya shugabata lallai nayi kuskure. Nan take ya mike tsaye da sauri ya juya ya fice daga cikin tantin amma a cikin zuciyarsa dariya yake yiwa sarauniya larbisa yana mai cewa hakika yaro man kaza ne bai san rana ba sai ta gasashi da sannu zaki san cewa wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi a wannan wuri da aka yada zango aka kwana sai kashe gari da safe bayan anyi kalaci sannan akayi shiri aka ci gaba da tafiya ba sassauci tun da aka fara wannan tafiya sarauniya larbisa bata kara cewa uffan ba kuma fuskarta a murtuke take ko kadan babu annuri alamar cewa tana cikin fishi Al amarin da ya dugunzuma hankalin dakarunta da kuyanginta kenan shi kuwa tsoho huzallatul marwas da yake yasan dalilin fishin nata sai ya kau da kai ga barin

Chapter 1 of 21