Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan kika ce mutafi sai mu tafi, mun jiraki a nan ne kizo muyi wasa." Murmushi tayi tana jin dad'i tayi sabbin kawaye 'yan wasa. ta dubi Miemie ta ce "Miemie zauna muyi wasa da su a gwada girma da babyn mu da nasu wanne yafi girma." Zama Miemie tayi bawai dan ta fahimci inda batun nata ya dosa ba, suka cigaba da wasa Feeryal tana yi tana magana da bada amsa ita kad'ai. Miemie kam data gaji ta mike ta d'au babynta ta kama hanyar fita daga d'akin tana fad'in "Feeryal ni kam zanje garden nayi wasa ta a can ki zo mu je." da sauri Feeryal ta mike tabi bayanta tana cewa "Zo ki basu babyn shine zaki kwace a hannunsu, suna mata kitso." Miemie kam tuni tayi waje daga d'akin dan bata fahimci abin da Feeryal d'in take nufi ba. "Miemie ki tsaya ki basu aro ai idan suka gama wasan zasu baki." tayi maganar tana rike babyn Miemie. Aunty da ke zaune cikin parlour ta ce " 'yan'matan Ammie rigima ko, ina naki babyn je ki d'auko mana, gobe zansa diraiba yakai Baba Rabi taje tayi miki shopping ta siyo miki wata tun da bakya son wancan d'in, babbama wanda tafi wannan; zo abinki 'yammatan Ammie, zo mu zauna a nan." Kafad'a ta make tare da cuno baki gaba ta ce "Ammie kawaye na ne fa suke wasa da babyn ta shine ta kwace." Ido Aunty ta zuba mata Miemie kam tayi waje abinta. Gwuiwa a d'an sanyaye Aunty ta ce "Wasu kawayen naki Feeryal?." "Ba gasu can a d'aki ba shine Miemie ta hanasu abin wasa." tayi narai-narai na ido zatayi kuka. Aunty ta mike ta na fad'in "Yaushe suka zo suna ta ina ko tare da Miemie suka zo." kai ta girgiza tayi gaba Aunty ta bita a baya. Daga bakin kofa Aunty ta tsaya tana raba ido cikin d'akin babu kowa, numfashi ta sauke ta ce "Ina kawayen naki Feeryal ni banga kowa cikin d'akin nan ba." "Ammie gasu nan baki gansu bane." jiki a sanyaye Aunty ta girgiza kai tana fad'in "Ban gansu ba Feeryal, ni banga kowa ba." Juyowa tayi in da kayan wasan ta suke ta ce "Ammie na wai bata ganku ba, ai bazata sa Baba Rabi ta siyo muku babban baby ba, Ammie ki ware idonki da yawa zaki gansu gasu nan." ta yi nuni da hannunta. sai kuma ta waro ido tana fad'in "Ammie wai ke bakya ganin su inji wannan?." takuma yin nuni da hannunta. Zuwa yanzu jikin Aunty ya fara yin la'asar kai ta gyad'a "Eh ni banga kowa ba, Feeryal ki dai na wasa babu kowa a nan taho mu tafi." Aunty tayi waje da sauri zuciyar ta na d'an harbawa. Daga inda take tsaye cikin parlour tana jiyo sautin maganar Feeryal, wanda yake nuni da tabbas akwai wanda ita take gani harkuma suke magana sakaninsu, wanda ita Aunty bata iya ji ko ganin su.........! Mommyn Twince ce 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* 🅿️10 Kamar wasa Feeryal ta b'ata tsawon lokaci cikin d'aki, Aunty na zaune a parlour tana jiyo ta tana ta surutu can anjima kuma ta kwashe da dariya. shiru Aunty tayi da tunani fal cikin ranta. "Anya Feeryal bata sami matsala ba kuwa?." tayi wa kanta da kanta tambayar. me yake kuma shirin faruwa ne bayan lokaci mai tsayo da aka d'auka bata kara ganin wani sauyi tare da ita ba sai yanzu?. wani b'ari na zuciyar ta ya shiga karanto mata. "Kar dai ace sai da ta barki kika sakankance da ita kafin ta ke son nuna miki asalinta." Da sauri tayi kokarin kawar da wad'annan tunanin ta mike ta nufi kichin, tana sawa ranta kawai wasa ce da shiririta irin na yaro. ta sami Baba Rabi suka cigaba da aiki. Wasa gaske Feeryal ta share awanni uku tana wasa. lokaci zuwa lokaci Aunty take zuwa ta leka ko zataga 'yan wasan nata, amma wayam bata ganin kowa. yoghurt da cake kad'ai ta fitowa ta d'auka ta ce wa Aunty zasuje suci su sha da kawayenta. ita dai Aunty to kawai ta bita da shi. ganin batada niyyar barin abin da takeyi bare ma harta fito ta ni mi abinci, Aunty ta tako bakin kofar ta leko tana fad'in "Feeryal ya isa haka wasan taso kizo kiyi wanka ki ci abinci lokacin wanka ya yi." Fuska ta b'ata ta cuno baki gaba "Ammie wasa fa mukeyi." kai Aunty ta dafe "Oh Allah ki ce da kawayen naki suma suje suyi wanka, kuma kar su dawo, sai gobe, maza taso kizo muje." Feeryal ta juya tana kallon wani gefe sannan ta ce "Kuma kuje ayi muku wanka nima Ammie na zatayi min." murmushi ta sake sai kuma ta d'aga hannu tana bye-bye. sai da ta daina ganin su kafin ta sauke hannunta. Aunty na tsaye tana kallon ikon Allah. "To taso muje." ta fad'a ganin ta sauke hannun nata, ta ruko ta sukayi waje. Washegari da safe Aunty na kichin tabar Feeryal tana bacci. tana gama abinda take ta dawo d'aki taga bata nan. bathroom ta shige tana kiran sunan ta, tsayuwa tayi ganin bata ciki, sai ta juya tanufi kofa tana cigaba da kiran ta. bata parlour bata kuma cikin bedroom d'inta in da take wasa ciki. Daddy dake zaune cikin parlourn ya dube ta yana fad'in "Ko tana toilet ne kin duba can." "Babu in da ban duba ba Daddy." batare daya d'ago daga kallon labaren safe da ake a TV ba ya ce "Zata fito ai tashige wani gurin ne." Bata kuma magana ba dan ita kam lungu da sako duk ta duba bata nan. da d'an mamaki ta tsaya cikin parlour da tunanin to ina taje. "To ina taje? kar dai ace taje gurin Miemie ce." tayi maganar tana nufar kofar fita daga parlour'n, da sauri. Tana fita farfajiyar waje, cikin hanzari ta nufi bakin get d'in side d'in ta. har tarike karamar kofa zata bud'e, taji yo dariyar ta ta can baya ta cikin garden. da sauri ta waigo tare da soma nufar gurin da take jin sautin dariyar nata. da mamaki take kallon ta kan lilo ita kad'ai, lilon na lilata sai b'arkewa da dariya ta ke tana kuma fad'in "Ku kara yi min sau biyar ni ma zan muku." Hannu Aunty ta d'aura a kirjinta tana son dai-dai nutsuwarta, cikin karfin hali daga in da take takira sunan ta. "Feeryal." da sauri ta kalli gurin da Aunty take sai kuma ta ce "Kutsai da ni ga Ammie na zanje gurin ta, zan dawo na rama muku." ta diro a kan lilon da gudu ta taho in da Aunty take, ta ruko hannunta tana d'an bubbuga kafa cike da shagwab'a take fad'in. "Ammie yunwa nake ji." Aunty ta had'iye tsoro mai had'e da fargaban da yake taso mata ta dube ta a hankali ta ce "Shine kika tsaya anan kina kuma jin yunwa iye Feeryal? to muje kiyi wanka sai kici." sun kusa isa bakin kofar parlour Feeryal ta juyo tana fad'in "Kuma zakuje Ammie na tayi muku wankan kuci abinci ne?." da sauri Aunty ta waigo, bataga kowa ba sai ji da ta kuma tana fad'in "Ammie suma zakiyi musu wankan ko?." Bata iya yin magana ba har suka shige cikin parlour. Daddy na ganin su ya ce "A'ina kika samo ta, Feeryal ina kkje da safiyar nan?." Zamewa tayi a hannun Aunty ta koma jikin sa tana fad'in "Daddy wasa muke yi da kawaye na." "Wasa kuma Feeryal da safen nan, baki ji ana sanyi ba, ko kayan sanyi fa babu a jikin ki, sanyi zai kamaki je maza Ammie'n ki ta sa miki rigar sanyi." ta ce to. ta mike ta dawo gurin Aunty da ke tsaye. Aunty ta kad'a keyarta ta ce "Je maza ki jira ni a bathroom ina zuwa, kice da kawayen naki kar su biyo ki." kai ta gyad'a da gudu tayi cikin bedroom. Fuska Aunty ta kwab'e tana kallon gefen da Daddy ya ke. murmushi mai sauti ya yi, kana ya miko mata hannu ya na fad'in "Taho muji ya akayi ne, kefa wani lokacin rikicin ki yafi na d'iyarki Feeryal." Hannu tamika masa ya janyo ta tazauna gefen sa. sosai ya maida hankalin sa gare ta, "Mene ne ko angaji da zaman gida ne, nayi mana bukin zuwa London." kai ta girgisa sannan ta ce "Yanzu ina fad'a sai kace gizo ne, kai bakaji Feeryal ta ce maka taje wasa ne da kawayenta ba, sai tayi ta magana ita kad'ai fa tun jiya, kamar da wasu take magana, kuma har nuni tayi min ta ce ga wad'an da take maganar da su, nikuma banga kowa ba." murmushi ya yi, ya ce "Gimbiyata ban isa in fad'i ba yanzu kam, dan naji da kunnena ta fad'a, magana kuma a gun yaro shi kad'ai, ba yana nufin da wani agun bane, yaro shi komai nashi na wasa ne." baki ta tsuke bata kuma cewa komai ba, dan tasan duk yadda tayi da shi bazai tab'a fahimta ba. ta zame jiki tayi d'aki. Tana shiga bathroom ta isketa tana ta wasa da tsalle cikin ruwa tana fad'in "Ku zubo mana ruwan gidan ku muyi wankan yafi dad'i." "Anya Feeryal bata sami matsalar kwakwalwa ba kuwa?." tayi maganar a kasan ranta. "Idan har ba matsala ta samu a kwakwalwa ba to kuwa akwai wani abin akasa." Haka ta daure tayi mata wanka, tana mata tana fad'in "Ammie kiyi wa kawaye na suma." Bayan ta gama mata wankan tafice da gudu, tana fad'in "Ayi rige-rige." Aunty ta tsaya ta gyara in da suka b'ata, koda ta fito d'akin. can saman wardrobe ta hango ta d'ororo a tsaye da kafafunta, tana ta kyakyata dariya. tsoro ne ya ziyarci Aunty, ko ita tsawonta baya kai saman wardrobe d'in nan. ko abu zata d'auko a saman sa sai ta samo abin hawa takara tsawo kafin hannunta ya iya kai wa saman sa, sai ga Feeryal d'ororo a saman wardrobe. Hannu ta mika tana fad'in "Ammie ki saukar da ni sun gudu sun barni." da sauri Aunty ta yi waje, jikinta na b'ari. ganin yadda ta fito yasa Daddy fad'in "Lafiya Fad'imatu?." Kofa tashiga nunawa tana fad'in "Feeryal a saman wardrobe." Daddy ya mike yana cewa "Me kuma ya kaita saman sa, kin d'aura ta ne kika kasa sauke ta?." kai ta girgiza da sauri ta ce "Bani na d'aurata ba a kai na ganta." da d'an sauri Daddy ya nufi bedroom yana fa d'in "Shine zaki fito ki barta idan kuma ta fad'o taji ciwo fa?." Yana shiga ya ganta tsaye a cikin d'aki. Aunty da ke biye da shi ta tsaya cike da mashahuriyar mamakin ganin ta a tsaye cikin d'akin. Daddy ya dubi Aunty yana cewa "Bansan me yasa kike kin amfani da magani da hayakin can ba, bari nayi waya a karb'o miki wani." "Daddy ka maida ni mai tab'in hankali ce ko?." tun kafin yakuma cewa wani abu, ta b'ata fuska ta koma parlour tayi zamanta. Yakama hannun Feeryal da kansa ya saka mata kaya ya shiryata tsaf yaruko hannunta suka fito. Aunty na ganin sa takuma had'e fuska. murmushi ya yi ganin yadda ta cika tam. ya kad'a keyar Feeryal ya ce "Je kichin maza Baba Rabi ta had'a miki breakfast." tace tom. da gudu tayi hanyar kichin. Ya karaso ya zauna gefen Aunty yaruko hannunta tare da kiran sunan ta "Fad'imatu." da sauri ta tari numfashin sa. "Daddy gizo ne yanzun d'in ma kada ka ce komai, amma ni bana da wata matsala a kwakwalwa ta, wlh ina son Feeryal ban tab'a jinta a wata daban ba, ina jinta ne tamkar jinin jikina, wacce ta fito daga tsatsona; abubuwan danake gani tare da ita ne kawai yake sani shiga fargaba a kanta, ina tsoron kada wataran na rasata, bayan nayi sabo da ita." Hannuta ya dad'a rike wa cikin nasa ya ce "Insha'allah bazaki rasata ba, sai kin kaita har d'akin aurenta, kin ga jikokin ki." ido ta d'an lumshe ta bud'e tana jinjina kai. Kullum abin Feeryal karuwa yake salon yau daban na gobe da ban ita da Kawayen nata da babu mai ganin su sai ita. zuwa yanzu Aunty tafara tunanin kodai mayu ne ke bibiyar ta, tana tsoron kada su bata maita ko su cinye ta. kullum a cikin addu'a take ba dare ba rana, Allah ya kare mata ita daga sharrin miyagon da ido baya iya ganinsu. Kimanin wata biyu ke nan ana cikin wannan halin kuma kullum abin gaba ya ke ba baya ba.. Aunty ce zaune cikin bedroom tajiyo hayaniya cikin parlour. jin muryar Mommy tana fad'in "Wlh sai kin bar gidan nan tun da bana ubanki bane, baki isa kice zaki takurawa 'yan gida ke kina agola ba, wacce ta tsaya mikin ma bata isa ba bare kuma ke." Da sauri Aunty ta fito parlour'n. Mommy Ameerah Feeryal Miemie Sahla Nabila. tagani cikin parlour'n. Mommy na damke da hannun Feeryal, kamar wacce ta kamata tayi mata sata. Ameerah tsaye baki na fidda jini gefen goshin ta ma haka. Mommy na ganinta takuma d'aga murya tana cigaba da fad'in "Wannan annobar 'yar da kika kawo mana gida take kokarin kashe mana 'ya'ya wlh in akan buzu kike kwana karshen tsafi, sai nayi duk yadda zanyi naga tabar gidan nan, kina sane da cewa dai nafiki fawa a gidan nan, da uban Alhaji Abubakar da ubana uwarsu d'aya ubansu d'aya, kinsan dai na d'are miki nesa ba kusa ba, d'an'uwa na jini kuma mijina nice nan kuma uwar manyan 'ya'yansa, kinsan ina da hanyoyin da zanbi cikin sauki na fidda wannan aljanar mayyar a cikin gidan nan, ba ita ba hatta ke wlh ina da yadda zan bi kibar gidan nan tacikin ruwan sanyi, kibi a sannu na gaya miki ke nan; ina dalili ina mafari da zata sako mana 'ya'ya gaba, jiya ta fasawa Nabila baki an kyaleta shine yau bari ta komo ta kan autata, to wlh bata isa ta ci bulus ba, baki isa ki takurwa 'yan gida kina tsintacciyar agola zubin mayun aljanu ba, a gaban uwar tsintuwar taki zan ci uban ki." Ta tsulawa Feeryal bulalar da ke rike a hannunta, har sau uku. Feeryal tasaki kara tana tsalle da yarfe hannu. A guje Aunty ta karaso inda suke ta kwace ta a hannunta tana fad'in. "Haba Hajiya Halima kiyi hakuri dan Allah, kin san sha'anin yaro, sai a hankali, Allah dai ya shiryar mana da su kawai, ke Feeryal me yasa zakiyi mata haka, ku dai na fad'a sakanin ku mana, kuda 'yan'uwan ku kurika fad'a kaman masu ganin hanjin juna, duk yaron da nasake ganin ya sake fad'a da d'an uwan sa sai na zane shi." "Dalla rufamin baki munafukar banza munafukar hofi, idan da mai ganin hanjin wani ai wannan mayyar aljanar da kika kwaso mana ita gida ne, idan maita kuke ke da ita sai dai kuci kanku, munafuka al'gunguma, ke kuma Feeryal kike ko ferfela sai na ci ubaki idan kika kara dukar min 'ya shegiya mayya kawai, sai kin bar gidan nan." ta kuma kai mata bugu da hannu a kan baki, aiko bakin ta ya fashe sai jini. "Ya ishe ki haka Hajiya Halima, ita sau nawa suke dukanta suji mata ciwo, natab'a zuwa na sameku kan batun, sai dai nayi musu fad'a, sabo da nasan d'a na kowa ne, ina abin duka a jikin wannan yarinyar in banda rashin imani, ai ba'a ki kimata hukunci ba amma ba irin wannan ba, tun da kuma bakwa yadda a kan naku nima bazan zuba ido ina gani a cutar min da ita ba, Feeryal zama daram a gidan nan kije kiyi duk abin da zakiyi." "Ai haka kika ce ko? ai kuwa zaki ga abinda zanyi." ta janyo hannun Ameerah ta ce wa sauran yaran "Ku zo mu tafi, zan nuna miki kasawar ki kuwa, sai na nuna miki karfin dangantakar datake sakanin mu da Alhaji, yafi wacce yake sakanin ku." Baki Aunty ta tab'e dan tajima tana jin wannan kalmar daga bakin ta, kulllum Mommy gorin ta da kowa ke nan tana da dangantaka mai karfi sakanin ta da Daddy, shiyasa take tsiyarta son ranta babu mai iya takata. ta ce "An dad'e ana ruwa kasa tana shanyewa, in banda bazan iya jurar rike wad'annan sangartattun 'ya'yan naku da kuka gama baud'ar da su kuka sangartasu, basusan girman nagaba da su ba, kuka kasa basu tarbiyya mai kyau ba, da kuk nasa an sallame ku kuje ku koyo darasin rayuwa, kusan yadda ake daraja mutane kafin ku dawo, kucigaba da rainon su." "Sai dai ke ki bar gidan nan ba dai mu ba, juyar banza juyar hofi kawai, in banda Alhaji ma da niman kalen jan raini wa mutane, har ke kin isa ki tsaya a gabana ina fad'a kina fad'a, wacce a haihuwar akuya nakai na haife ki." "Sai dai in a haihuwar akuyar kam, amma ke baki isa ki haife ni ba, ai girma batayi rana ba tun da har yanzu hankali bata ishe ku ba." Mommy tayi bakin kofa fuuu tana zazzaga buhun masifa. tana isa bakin kofa zata d'aga kafa ta wuce kafa taki gaba taki baya, tayi-tayi ta d'aga kafar ta kasa, nan da nan zufa yashiga ke to mata, sai ga Mommy tana salati da sallallami. Aunty ta tab'e baki ta juya tana kokarin komawa bedroom rike da Feeryal. takuma jiyo salatin Mommy "La'ilaha'illahu, wayyo Allah kafata nashiga uku, ke Sahla Nabila kuje ku kira min Ajeemal da Daddyn ku." Aunty na tsaye tana kallon ta, ganin dai da gaske kasa d'aga kafar tayi, tana ta faman jansa yaki gaba. zuciya irin na Aunty nan da nan jikin ta ya d'anyi sanyi, ta tako in da take tana fad'in "Me ya sami kafar taki, subhanallah sannu mugani ko kin taka wani abun ne." ta sunkuya tana kokarin dubawa, da sauri Mommy ta ce "Kada ki sake ki tab'a min kafa, bakar munafuka, waya sani ma ko takan sihirin ki na bi na taka." "Ashsha me yasa kuke son mu'amala da shirka ne, laifin da Allah baya yafewa bawa har idan yamutu yana aikatawa bai tuba ba, kawai daga kafarki ya kama ciwo sai ki d'aura alhakin hakan a kan wani, komai ya faru da bawa da sanin Ubangiji." "Dalla gafara can bance ki tsaya kawo min aya da hadisi ba, narigaki sanin Allah, matsa daga nan kada ki sake ki tab'a min kafa ki shafa min wani abin." Kai Aunty ta girgiza ta mike daga durkushen da take. da sauri duk suka jiyo jin Feeryal ta fashe da dariya. san da Mommy ta kuma yunkurin d'aga kafarta tana cewa "Wayyooo Allah jama'a kuzo ku kawo min d'auki Fatima zata kashe ni." Feeryal dariya har tana fad'uwa da rike ciki, idan ta nuna Mommy da hanu sai ta kuma tuntsirewa da dariya. Aunty tayi saurin karasowa in da take ta finciko ta tana fad'in "Kinci kaniyar ki sa'arki ce da zaki rika yi mata dariya, kar na sake ganin kina yiwa babba haka." baki ta kunshe da dariya ciki, aiko dariyar ta tsub'uce, cikin muryar dariyar ta ke kuma nuna Mommy dake kurma kururuwa ta ce "Ammie Chulu zata rike d'ayan ma." Da sauri Aunty ta kalli inda take nuna mata gurin Mommy kana ta maida dubanta gareta ta ce "D'ayan me zata rike Feeryal? ki dai na wannan dariyar." "D'ayan kafar Mommy wanda Chuchu bata rike ba." ido Aunty ta waro ta ce "Waya rike kafar nata da?." "Chuchu ce ba gata can ba tana caccaka mata kaya akan kafar, laaa Ammie kin gani Chulu ma ta rike d'ayar." takuma fashewa da dariya. Aiko nan Mommy ta saki wani uban kururuwa ta zube kasa warwas, tana birgima da rike kafa kamar zata fice a hayyacin ta. Tsawa Aunty ta bugawa Feeryal "Ke Feeryal kice su sake mata kafa yanzun nan." cikin muryar dariya ta ce "Chuchu Chulu ku sakar mata kafa Ammie na ta ce ku barta." ai ko nan take Mommy ta saida kururuwar da take, jin tamkar an zare gashi cikin fura, cikin dakika d'aya ta nimi cuwon ta rasa. a bujajan ta mike tayi waje bata ko bi takan autar tata ba Ameerah da take tsaye a kanta tana tayata ihu. ganin uwar nata tayi waje itama ta bita a guje. Ido Aunty ta zubawa Feeryal cikin sanyin jiki da sanyin murya ta ce "Feeryal ki dai na hakan ba kyau." ita kam Feeryal gaba tayi abin ta taje ta sunkuya wasan ta. Aunty ta shige bedroom ta zauna bakin gado tare da d'aukar wayarta ta lalub'o lambar, Hajiya Fara wato mahaifiyar ta, wacce suke kira da Hajja Umma. Jin mahaifiyar tata ta d'aga tayi saurin fad'in "Assalamualaikum ina wuni Hajja Umma ya gida." "Lafiya lau alhmdulillah Fatimah ya kuke, ya mutan gidan?." ta ce "Duk suna lafiya, ina Maryam yau ba school ana gida, ta ce min zata zo tayi ta shafamin romo a baki shine taki zuwa ko." "D'azun nan taje gidan kawun ku Idris, sai da ta isa ta bugo min waya wai a can zata kwana." Aunty ta ce "Lallai kuwa a gaida Maryam shine ni taki zuwa min shekaru nawa rabon da ta kawo min ziyara, Hajja Umma ki ce mata ta zo ni zan biya kud'in jirgi ni ban ce ta taho a mota ba, basai ma Abba ya biya mata ba." "A'a ba yanzu ba dai kubar min autata kusa da ni, Zainab ma tana ta masawa sai ta je mata, na ce ba yanzu ba." "Kai Hajja Umma shine kike hanata zuwa mana." "Zata je muku amma dai ku bari sai an yi hutu mai tsawo tukun, wai ni kam ina kawata ce banji d'uriyar ta kusa ba, Alhaji kullum sai maganar ta yake, na ce ban gane ba daga ganin farar fuska sai ka rud'e, tun tale-tale muna zaune baka tab'a batun wata ba sai akanta, ki bani ita na fad'a mata mu bibbiyu da ni da ita ta rabu min da miji." Dariya Aunty ta yi ta ce "Amaryar Abba ai shekaran jiyan nan ma ya kira ya ce a bata, ke kam dai Hajja Umma an barki a gefe baki sani ba, kullum Abba sai ya kira sunyi hira da ita." "Ai ko zamu gamu da ita, tazo ina jiran ta duk sai na kora ma'aikatan gida na, nakafa sabon murhun itace a waje ita zata rika min girki sai fatar nan nata ya canza kala. amma Fatimah lafiya dai ko ya naji kamar bakya yanayin nutsuwa, ba na ce kiyi ta hakuri nasan ki da ita, ki kara kirika mai da komai ba komai ba, kada ki yada addu'a makarin mumini ne, me zai dame ki mijinki na son ki, da har da ke cikin jerin wad'an da Abban ku zai biyawa kud'in hajjin bana, mai gidan ki ya ce, shima a barshi ya sami lada, sau biyu kad'ai shi yatab'a kaiki hajji, Abba'n ku kuma sau hud'u, shima yana da bukatar samin karin lada, me zai d'aga miki hankali mijin ki na biye da ke, kada damuwar wasu ya tada miki hankali kin san dai Abba'n ku bazai jure jin ki cikin matsala ba, idan ni na jure shi bazai jure ba." Numfashi Aunty ta sauke ta ce "Umma ni damuwar mutanen gidan mu baya gabana yanzu, dan nagama gane cewa jahilci ke damun su, ina da ilimi na bazan zauna biyewa jahilai wad'an da basu san abin da suke yi ba, Hajja umma matsala ta yanzu d'aya Feeryal, natab'a fad'a miki tun tana jaririya abubuwan da narika gani a tare da ita, sai gashi a 'yan kwanakin nan ina kuma ganin wasu sauye-sauye a gurin ta, Hajja Umma ita kad'ai zakiji tana magana kuma bil'hakki da wani take, yanzun nan kamma tayi wani abinda ya shanye min ruwan kai, wlh Hajja Umma ta dad'a jefani cikin kokonto daban-daban, anya yarinyar nan ba miyagu suke son kulla alaka da ita ba, d'ayan biyu ko hakan ko kuma da gaske ita d'in ba mutum bace........! Mommyn Twins ce 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* 🅿️11 Shiru Hajja Umma tayi tana sauraran bayanan da Aunty take kora mata, na duk abinda ya faru a baya da kuma abin da ya faru da Mommy yanzu ba da jimawa ba. Aunty tad'aura da fad'in "Nakanji tsoro wani lokacin na tsinci kaina cikin fargaba, wlh Hajja Umma ina son Feeryal bana son rabuwa da ita, ni ko aljana ce ma ita ina son ta zan rayu da ita a haka, abin da nake tsoro d'aya kada ta cutar da ni ko wad'an da nake tare da su, bana so na rabu da Feeryal, wlh ina son ta a haka." Aunty ta karasa maganar cikin sanyin murya. Hajja Umma ta jinjina kai sannan ta ce "Yanzu ina Feeryal d'in?." "Tana parlour tana ta kan wasa wai da kawayen ta, da ni bana ganin su, ni tsoro na ma d'aya kar ta faje da wasu tarika cutar da mutane." d'an shiru Hajja Umma ta yi kana ta

Chapter 9 of 20