sa miki hannu cikin wando Feeryal!."
bin ko wannensu tayi da ido idanunta yatsaya kan Uncle Samir, ta d'aga hannu ta nuna shi.
ai kuwa kowa idanunsa ya koma kansa ana sallallami.
Daddy ya saki hannunta ya tako gabansa, Uncle Samir kansa a sunkuye, bawai ko dun jin kunyar abin da ya aikata ba.
sabar azamar da yake ji ne shi ya hana shi ko da iya kyakkyawar motsi,
a yanzu zafin azabar ta fiye masa jin kunyar.
"Kai d'angidan uban waye ne a kasar nan da kake shirin lalata min d'iya ta."
ba'a ankara ba sai ganin Daddy akayi yana aika masa da maruka ta ko ta ina a fuskarsa.
yakuma cewa security su tafi da shi.
Hakuri malaman suka shiga bashi, bai saurare su ba ya ce
suma bincike zata zo ta kansu, kuma zai cire yayan sa duka a makarantar dan sai ya yi Shari'a da mai makarantar gaba d'aya.
ya ja Feeryal ya ce da su Ameerah suzo su tafi ya kwashi yayansa duk ya yi gaba da su.
Aunty na zaune a parlour har lokacin har su Daddy suka dawo.
tana ganin su ta mike tana tambayar
"An same shi ko ya b'oye yaki bayyana kansa?."
Daddy ya ce
"Zauna Fad'imatu."
ya nuna mata in da ta tashi ta zauna jiki ba kwari idanunta akan sa.
kai ya girgiza mata ya ce
"An same shi da kanta ta nuna shi kuma nasa an tafi da shi, kuma da bakinsa ya amsa laifinsa ya ce bai yi mata fyad'e ba hannu kawai ya sa mata."
numfashi ta sauke tana fad'in
"Alhmdulillah, d'an iska zai iya sawa 'yar cikin sa ma, Allah ya kare ki Feeryal."
Daddy ya d'aga kiran da akayi masa yanzu a waya ya yi waje.
Aunty ta mike ta ruko hannunta suka shige bedroom bayi ta kaita sai da ta kuma duddubata ta dad'a tabbatar da babu ko mai dai, iya d'an karcewar nan ne dai ta gani, da ya yi mata da yatsunsa.
kana tagasa mata gurin da ruwan zafi.
tana yi tana godewa Allah da yasa a iya haka ya tsaya bai kara gaba ba.
Kan kace me gaba d'aya gidan ya d'auki zancen anyiwa Feeryal fyad'e.
dan 'yan kaho rahoton su Ameerah Sahla Nabila fyade suka ce Uncle nasu ya yi mata.
Mommy da Ameerah ta gama shirya mata zance wan da rabin sa karya ne.
ta rike hab'a ta na fad'in
"Tabd'i jam da ma ashe dukan kun da yake idan kun tab'ata yasan me yake samu a jikinta, 'yar kwal uba tun tana 'yar karamar ta tasan iskanci, ai da ganin da ma ta jima tana yi yanzu ne asirin su ya tonu,
to shi Alhaji da yasa atafi da shi beyi tunanin idan b'era da sata daddawa ma da wari ba."
A b'angaren Umma Karima kuwa tsistsinewa Feeryal d'in tayi,
ta ce "Dama tambad'ad'd'iya ce tun can nagode Allah ya kara na gobe, naso naji ance an garzaya da ita gadon asibiti, yamata kaca-kaca ya wargaza ta gaba d'aya,
shegiya tambad'ad'd'iyar yarinya,
mai zuben mayun aljanu, ko da shike aljanar ce da ma."
Hajiya Nafisat wato Mom ta d'unguma tayi side d'in Mommy a can suka had'e duka Mommy da Umma Karima da ita Mom d'in.
suka cigaba da tofin ala tsine wa Aunty da kuma Feeryal.
Hankali tashe Hajiya Safiyyah mahaifiyar Miemie Ammah kenan ta tafi sashin Aunty
suka shiga jajanta lamarin
Ammah ta ce
"Allah Ubangiji ya dad'a bawa 'ya'yan mu kariya, badun Allah ba kam da bamusan meyau zata haifar
ba, su kuma masu aikata hakan Allah ya cigaba da tona musu asiri, su kunyata a idon nuniya wata
kila ta sanadin hakan su shiryu,
idan kuma ba masu shiryuwa bane Allah kayi gaggawar kawar mana da su a ban kasa."
Aunty ta ce
"Amin ya Allah wlh Ammah'n Miemie kar kiga yadda na
shiga tashin hankali Allah kar ka kawo mana abin da bazai wuce."
haka sukayi ta jajantawa Ammah tajima
sosai a sashin kafin ta koma nata sashin.
Da daddare Mommy na side d'in Daddy dan yau ita ce da shi.
tun shigowar ta take ta sako maganar Feeryal d'in yaki kula ta ne, dan ya fuskanci kamar murna suke
da faruwar abun.
dan d'azu Umma Karima ta gama kalar nata.
d'an muskutawa Mommy ta yi ta ce
"Alhaji wai kuma fisabilllahi an kama yaron nan
anje an rufe shi, ba'ayi tunanin in b'era da sata daddawa da ri ba, karfe fa bata kara ita kad'ai dole
sai da abokin had'i, itama yarinyar ai tana da laifi, idan bata biye masa ba ai bazai sami kofa ba."
a fusace Daddy ya ce
"Haba Hajiya Halima 'yar wannan yarinyar me ta sani da zata beye wa wani na miji,
ku dai ji tsoron Allah kuma kuna da ya'ya matan nan,
musamman ita Karimatu ya'ya mata rai hud'u gare ta, babu wacce ta wuce kaddara,
ke ma kina da ya'ya mata uku,
ina tayi muku gargad'i ku fita a hurumin Allah babu ruwanku;
Feeryal ba fyad'e akayi mata ba, ya dai so ya keta mata haddin Allah kuma ya kare ta."
Baki Mommy ta tab'e ta ce
"Namu a wanne ana ta wani b'oye mana, fyad'e kam anyisa yana nan a zane baya gogewa watarana zai bayyana, mu ai 'yan kallo ne,
akan wata tsintacciya kake yi wa ya'yan cikin ka mugun fata,
to in Allah ya yarda bazamu gani a kan ya'yan mu ba, ehe."
kai Daddy ya girgizar ya mike ya shige bayi yabarta nan zaune.
Kwana biyu da faruwar lamarin mai makarantar da kansa ya yi tattaki zuwa gurin Daddy.
ya yi ta bashi hakuri da ban baki, yakuma ce zasu saka tsastsauran tsaro a makarantar insha'allah hakan bazata sake faruwa ba anyi na farko anyi na karshe.
sannan kuma ya kori uncle Samir a makarantar, ya aika masa da takardar kora a can ofishin 'yan sanda da ya ke a tsare a can.
Daddy ya ce ya hakura amma bazai mai da ya'yan sa makarantar ba.
da kyar dai ya hakura a bisa roko da ban hakurin da ya cigaba da yi masa.
washegari kuwa yasa direba ya kaisu makaranta.
Satin Samir guda a tsare a hanun 'yan sanda, sai da iyayen sa sukayi ta sintiri suna niman afuwan hukuma da kuma na Daddy,
da kyar Daddyn ya hakura dan dama yasha alwashin sai ya yi zaman gidan yari.
duba da iyayen nasa bamasu karfi bane,
sanadin hakan yasa a sake shi,
daga nan kuma a ka garzaya da shi gurin magani, dan abin cikin wandon sa ya daina aiki ya koma kamar lagwani.........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️8
Yau kimanin watanni biyu ke nan da faruwar haka, amma kullum 'yan gidan sai sun raya maganar ya dawo sabo.
duk wan da yazo gidan kuwa sai an sanar masa anyi wa Feeryal fyad'e.
wasu 'yan gulma basa iya hakuri harsai sun dangana da sashin Aunty wai sun je mata jaje.
Aunty da ta fahimci gulma ke kawo su ba jaje ba, takan ce musu, ita bata ma san wannan zancen ba ga dai d'iyarta nan, tana cikin koshin lafiya.
in dai kamar Feeryal za'ayi wa fyad'e da kuwa har yanzu bata sami lafiya ba,
ga shi kuma suna ganin ta kem kamar kullum lafiya ake karamata.
haka kowa zata koma da guntun gulmarta.
wasu kuwa cewa suke ai dan sabo da ita ba cikakkiyar mutum bace shiyasa baza a ga alamu ba hakan zai b'uya a jikinta.
Feeryal sunyi jarabawa sun sami hutu yanzu kullum suna gida,
yanzu malamin da ke zuwa koya musu karatun Alkur'ani da sauran littatafan addini, tun goma yake zuwa baya barin gidan sai karfe shida na yamma.
Yau Alhamis wannan ranar baya da cikin jadawalin ranakun zuwa koya musu karatu,
dan haka yau yaran duk a sake suke.
suna free kowa na sha'anin sa.
Tun da safe Miemie da Feeryal suke tare a sashin Aunty har kawo yanzu da ake kiran sallar azahar.
kafin ta koma side nasu ta ce wa Feeryal zata dawo anjima.
ganin shiru Miemie bata dawo ba, Feeryal ta nufi kofa zata bita.
can Aunty ta hangota bakin kofa tana kokarin fita.
"Ke Feeryal ina zaki?."
juyowa tayi ta marairaice fuska tana d'an mui-mui da bakinta
"Zanje gurin Miemie ce."
"Zo ki jira ta zata dawo bata ce miki zataje ta dawo bane."
kafad'a ta make ta ce
"Ni dai zan bita."
d'an shiru Aunty tayi kana ta ce
"Zaki iya tafiya da kafa har side d'in su?."
kai ta gyad'a da sauri ta ce
"Eh."
"Karfa ku had'u da mage da kare kuma a hanya."
baki ta b'are zatai kuka ta ce
"Maza jeki Allah ya tsare karnuka suna d'aure ma abinsu."
da sauri kuwa tayi waje.
Tana tafe tana d'an wasan ta da hannu a baki.
daga can saman bene Zaraddin ya hangota, ido ya kura mata babu ko kiftawa a fili ya furta
"Kai kayan marmari a cikin gida."
da sauri ya nufi starais, ya sauko yafito daga side d'in matasan gidan ya iso inda take ya sha gabanta.
sai yanzu ma ya gane ko wace ce daga sama daya hango ta ya d'auka wata bakuwa ce, ashe yarinyar da Aunty ke ta b'oyewa ne.
yawani lumshe ido
"Shiyasa mana ake ta b'oye ki irin wannan halitta haka, wayyo Allah , ai dole ace aljana."
hannunta ya ruko ya ce
"Ina zaki je yama sunan ki?."
yatsarta ta curo a baki sannan ta ce
"Zanje gurin Miemie ce."
"Okay to zo muje na kaiki gurin ta yanzu naga tayi ta can."
ya nuna kofar side d'in su na matasan gidan.
kai ta gyad'a ya ja hannunta suka nufi gurin.
suna tafe rike da ita ya ce
"Ya sunan ki ma?."
ta ce "Feeryal." "Oh nice name."
Sai da ya kalli gefe da gefen sa ya tabbatar da ba wanda ya gansa sannan yawuce cikin side d'in da ita.
kasancewar babu kowa cikin side d'in duk matasan kowa ya tafi sabgar gabansa, kai tsaye d'akin sa ya wuce da ita,
dan duk kanin su kowa da d'akin sa da ban.
suna shiga ya tura kofar ya murza masa key
kana ya dube ta ya ce
"Zo ki gani Miemie tana can cikin bathroom zo ki jirata ta fito."
ya janyo ta zuwa bakin goda ya d'aurata a kai shima ya haura.
ya mika hannu ya kashe wutar d'akin, gaba d'aya d'akin tayi duhu tamkar dare.
da sauri yashiga tub'e kayan sa ya yi zigidirr.
ya janyo ta yashiga kokarin tub'e mata kaya, duk a cikin duhun yake yin komai.
ganin kamar zai b'ata lokaci,
dan yasan duk yadda akayi Ajeemal da Shamsuddin da Faisal bazasu d'au wani lokacin kirki ba zasu dawo,
gara yayi-yayi abin da zaiyi kafin su dawo sai yabar cire kayan.
ya shinfid'a ta yashiga lalub'e cikin duku ya zare pant d'in jikinta.
Fuska ta kwab'e tare da sakin kuka da sauri ya ce
"Yi shiru ko na yankaki, kina kuma kuka sai na yankaki a nan."
aiko tayi d'ip tana rarraba ido cikin duhu cike da tsoro.
da sauri ya durkusa a kanta ya saita 'yar abarsa da bata gama kwari ba, yashiga niman hanyar wucewa.
Cak ya saida a bin da yake shirin aikatawa.
ganin wani irin haske na bayyana ta jikin windo.
a iya jikin windo hasken ya bayyana.
a hankali wani murd'ed'd'en maciji yasako kansa ta cikin window yana bayyana ta cikin hasken nan.
wani irin b'ari jikinsa ya d'auka har sai da ya saki fitsari suuu a kanta.
a hargitse ya mike yadoro a gadon da gudu ya yi bakin kofa ya bud'e ya yi waje ad'ari har yana kifewa a kasa, bai tsaya ko ina ba sai a sashin uwarsa Mom.
yana fita a take hasken nan da macijin suka b'ace wutan d'akin ya kawo da kansa, tamkar wani ne ya kunnan sa dan harda karar sautin kunnan wutan ya bayyana.
Tuni Feeryal ta saki kuka ta duro a gadon tayi waje tana cigaba da kukan.
har ta fice gaba d'aya daga side d'in ta nufi nasu part d'in.
da kuka.
jiyo kukan ta yasa Aunty fitowa da dauri ta tare ta.
"Ke Feeryal mene ne me ya same ki?."
cikin muryar kuka ta ce
"Ba yayan Sahla ne ba ya tub'e min pant d'ina."
kirji Aunty ta buga ta ce
"Nashiga uku wani yayan nata d'aya, Shamsuddin ko Zaraddin!?
sai kuma me ya mika bayan cire miki pant, be yi miki wani abun ba ko."
gaba ki d'a Aunty ta birkice tana dudduba jikinta ai ko ba pant a jikinta,
kirji ta buga, ta d'agata da sauri ta kwantar kan kujera ta ware ta tana leka kasanta.
nannauyan numfashi ta sauke ganin babu komai a gurin.
da sauri ta d'ago ta
ta janyo ta da sauri tana fad'in
"Taho muje wlh basu isa su saka min hawan jini ba, zan iya jure komai a kaina amma bazan jure ganin tozarci a kanki ba,
iyayen su su sako ni gaba, sannan ya'yan su mata su saka ki gaba da duka,
mazan kuma su nimi su maidake dokin hawansu,
to wlh karya suke basu isa ba."
ta jata sukayi waje da sauri.
Suna fita kuwa ta hango Shamsuddin da Ajemal.
suna kokarin shiga side d'i su.
ta dakatar da su ta hanyar fad'in
"Shamsuddin Ajeemal ku dakata a gurin."
takaraso inda suke ranta a matukar b'ace.
rai b'ace Aunty ta ce
"Shamsuddin! ka bud'e kunnuwar ka da kyau ka jini, wlh shine Allah ko da wasa ka sake kuskuren ko da rike hannunta ne kawai,
bare har ka kai ga cire mata pant; wlh sai kayi nadamar da har abada bazaka dai na yin sa ba!
ina dalili ina mafari ita ce kad'ai d'iya mace a cikin gidan nan, babu sauran mata ne gasunan yara irin ta da wanda suka fara zamowa 'yanmata in banda tsabar jarabar tsiya,
meye a jikin Feeryal d'in da har zaka nimi kwakularta?
to wlh na farko na karshe idan kuma bakaji ba, bazan sa ayi ma hukuncin a sakar nan ba kurkukun Tailan zan sa a kaika!."
Kirji Shamsuddin ya dafe ya ce
"Ni kuma Aunty? wlh bansan komai ba! yanzun nan shigowarmu gidan nan tun d'azu bama nan, Ajeemal ka fad'a mata mana tun d'azu muna tare da kai yanzun nan muka dawo."
"Eh Aunty yanzun nan shigowar mu tun d'azu muna tare da shi, a babban parking lot muka aje mota bamu shigo da shi nan bane sabo da zamu kuma fita,
amma bama nan wlh munkai 3h da fita."
Aunty ta biso da kallon son gano gaskiyar su, sai kuma da sauri ta ce
"Ina Zaraddin shima d'in tare da shi kuka fita?."
da sauri ta yi tambayar tuno da ko waye Zaraddin d'in, yana da mugun rawan kai gabin abokan banza.
kai Ajeemal ya girgiza ya ce
"A gida muka barshi bamu fita da shi tare ba."
Da karfi ta ce "Shine ke nan shi ne, ina yake ku kirawo min shi."
Shamsuddin ya d'aga kafa da sauri yanufi sade d'in Mom.
tun daga kofa yake kira
"Zaraddin Zaraddin, kai Zaraddin ina kake to ka fito nan ka girbe abin da ka shuka."
"Kai wani irin iskancin kira kake wa mutane haka daga waje."
cewar Mom tana fitowa Zaraddin na biye da ita.
ta bankawa Shamsuddin harara tana fad'in
"Bazaka iya shigowa ciki ka same shi ba, sai ka tsaya daga waje kana masa kiran rashin mutunci sai kace sa'anka,
uban me ya shuka a wajen da zai girbe?."
kai Shamsuddin ya girgiza yasani sarai Mom d'in su bata son laifin Zaraddin ko kad'an.
yana harka da abokan banza yasha zuwa ya fad'a mata amma bata d'auki wani mataki ba.
tun yana shaye-shaye a b'aye da abokansa har ya zamana yanzu kowa ya sani.
an tab'a kamasu aka kaisu police station sunyi wa wata yarinya fyade shi da abokinsa, uwar tasu ta sa Dad d'in su zuwa ya je ya yi belinsa.
kai yakuma girgiza wa ya ce
"Mom Aunty ce ta ke niman sa gata can a kofar side d'in mu."
"Me yaci mata me ya tare mata take niman sa, gida gidan wan ubansa ne, bata isa ta hanashi yin abin da yaga dama a cikin gidan nan ba, zonan muje naji me take nima da kai, iyalen sharri iyalen k'azafi."
ta yi gaba fuuu.
Shamsuddin na cewa
"Mom kibi komai a hankali kinsan dai Aunty bata shiga tsabgar da bai shefeta ba."
bata ko saurare shi ba tayi gaba.
suka biyo ta a baya shi da Zaraddin d'in.
Tunkan takaraso inda Aunty take tasoma d'aga murya wadda hakan ya soma janyo hankalin 'yan gidan garesu aka soma taruwa.
cikin d'aga murya sosai Maom take fad'in
"Meya shuka miki da zai girbe Hajiya Fatima? bazan yarda da sharri ko k'azafi ba, shi ke nan ko wani cin maita a gidan nan akan Zaraddin zai kare,
ko da shike kai ka janyo shiyasa ko wani dattin bola a kan ka yake karewa."
ta harari d'an nata dai-dai lokacin da suka karaso in da Aunty suke.
"Hajiya Fatima nace me ya shuka miki da zai gurba?."
Aunty bata ko kalli ta ba ta dubi Zaraddin da kyau kana ta mai da duban ta ga Feeryal sannan ta ce
"Wannan shi ya cire miki pant?."
kai Feeryal ta gyad'a tana yi masa kallon tsoro.
Wani uban kururuwa mai had'a da manya-manyan ashariya Mom ta kurma.
"Kutumar uban can, kaga kulu uwar sharri, yau tanan kika b'ullo, Hajiya Fatima,
a ina ya ganta da har zai cire mata pant,
sharrin fyad'e zaki masa, ina abin kwakula ajikin wannan figigiya tatsitsiyar!?
na rantse da Allah bazan yarda ba sai kin wanke zargin da kike masa a gaban kotu,
yihuhu jama'a kufito kuji wlh Hajiya Fatima ba ki isa ba, baki isa ki bakanta min d'ana ba,
sharrinki a kanki zai kare,
aljanar 'yar da kike b'oye ta ina zai ganta har ya yi yunkurin yi mata sharrin da kike kokarin kulla masa!
bazan yarda ba yau Fatima zaki san da ni Nafisatu kike zance, idan kin saba yi wa wasu ki share to ni wlh karyan ki ba ayi ruwan isarki ba wlh!
kije can kije ki nimi wanda yakuma yiwa mata fyad'e,
badai Zaraddin ba wlh."
Ta bigi kirji baki na kumfa cike da bala'i da masifa had'e da rashin mutunci.
kan kace me mutan gidan kaf sun taru a gurin,
har hankalin security yafara karkata wurinsu.
Mommy da Umma Karima suka shiga tambayar Mom abin da ke faruwa, ta ce
"Sharri zatayi wa Zaraddin wai ya cirewa wannan mayyar aljanar pant, idan ba sharri ba a ina Zaraddin ya ganta ita da ake b'oyewa a kunshe a d'aki kamar daddawa a kwano, a ina zai ganta."
hab'a Mommy ta rike ta ce
"Tabd'i jam lallai akwai aiki, yau d'in ma fyade za'a ce akayi mata ke nan,
lallai wannan lamari akwai lauje cikin nad'i."
ta wasawa Aunty kallon banza.
Umma Karima kam cewa ta yi
"To ai ba farau bane, yau aka fara sharri wa mutane akan ta irin haka, har makaranta akaje aka tozarta malami, da ganin yarinyar nan ba karamar hatsabibiya za ayi ba, tun tana kankanuwa tasan yadda ake makalewa maza, ita kad'ai ce a makarantar ba sauran yara ne, me yasa hakan bai tab'a faruwa da wataba sai ita, shine abun yanzu ya dawo har cikin gida ko, to wlh bazamu yarda ba."
"Haba Hajiya Karima wani irin magana ne wannan yanzu fisabilllahi wannan yarinyar har ta san yadda ake bin maza haba ku kuwa, kuyi adalci a maganar ku."
cewar Ammah tana binsu da kallon takaici.
Fuska Umma Karima ta yamutsa
"Wani irin adalci kuma daya wuce wannan, ko aki ko aso wannan ita ce dai gaskiyar,
sharri ya tashi daga waje ya dawo cikin gida,
kada a aje mana gamasheka a cikin gida, ta tashi ta koyawa yaranmu iskanci da bin maza, dan da gani karuwa za ayi anan."
Idan ran Aunty ya yi dubu to ya b'aci, bata san san da ta d'auke Umma Karima da marima ba.
cikin tafasar zuciya tashiga nuna ta da yatsa sannan ta ce
"Kada ki kara danganta min 'ya da karuwa, gargad'i na karshe, idan kuma bakijiba zakiyi nadamar kuma fad'in haka!."
Umma Karima ta dafe gefen fuskantar ta tana fad'in
"Bura'uban can ni kika mara Fatima, ni zaki ki mara?."
"An mare ki, ko yanzu kika kuma jefinta da kalmar karuwa sai na kuma d'auke ki da mari!."
Umma Karima tayi wani kukan kura zarayi kan Aunty da sauri Ajeemal ya shiga sakaninsu.
Umma Karima sai wani tsalle take ita a dole a barta ta shake Aunty.
baki na kumfa take fad'in
"Wlh yau sai na nuna miki ni cikakkiyar 'yar tasha ce, ni zaki mara Fatima, ko sa'a ta bata tab'a kai hannu jikina ta share ba, ba re ke!
kud'in ubanki bazai bani tsoron naci uban ki anan ba,
wlh yau sai na nuna miki ainihin ko wace ce ni."
Ammah data ruko hannun Aunty tana janta gefe ta ce
"Dan Allah Hajiya Fatima kada ki kulata ba girman ki bane, irin wad'an nan, abun kunya gaba suka bashi ba baya ba."
"Rabu da ni Hajiya Safiyyah matar nan ta ishe ni,
ai ba yau nasan cewa ke 'yar tasha ba ce, mai sai da shinkafa akan titi ba, ke in banda ma kaddara ai ko in da nasa kafa ba ki isa ki sakaba bare nayi zaman kishi da ke,
kurabu da ita tazo zan nuna mata kalar tawa barikin."
Hon d'in motar Daddy da yanzu ya shigo ne ya mai da hankalin su wajen sa.
da sauri Ajeemal ya nufi gurin motar ya bud'e marfin gefen da yake, yana ya yi masa sannu da dawowa.
Jim kad'an Daddy ya fito daga cikin motar ransa a b'ace, ga dukkan alamu dai Ajeemal ya shaida masa abun da ke faruwa.
ya nufo inda suke rai b'ace.
a kusan tare motar Alhaji Tukur wato Dad mahaifin su Zaraddin da na Alhaji Sulaiman Abbieh mahaifin su Miemie suka shigo.
Ganin yadda yayan nasu yake nufar inda mutan gidan ke tara da alama ransa a b'ace yake.
yasa su fitowa cikin motocin su da sauri suka rufa masa baya.
Daddy na isa baiyi wata-wata ba ya janyo kwalar rigar Zaraddin.
ya tura shi wa
security kattin maza guda biyu dake biye da shi cikin murya mai nuna zallar b'acin rai ya ce
"Ku tub'e shi ku zane shi!."
Nan da nan suka shiga aiwatar da umurnin da aka basu.
suka tub'e masa riga da wando suka barshi da iya gajeren wando.
Zaraddin daya gama tsurewa yashiga bada hakuri yana fad'in
"Dan Allah Daddy kayi hakuri wlh ba abun da na mata, bammata komai ba, ni ko ganin ta ma banyi ba yau."
tuni security
suka zare bel d'in jikinsu suka shiga shinfid'a masa ta ko ina, yana ihu.
Ido Dad ya rumtse, yana jin zuciyarsa na tafasa.
da kyar ya iya dai-dai ta kansa ya yi kokarin b'oye fushin sa.
yana fad'in
"Ku kara masa sha-sha-shan banza, mu zaka b'atawa sunan family."
Mom gaba d'aya ta birkice ji take kamar ta je ta tsare ta ce kada wani ya sake dukar mata d'a, amma ina babu hali Daddy ne da kansa ya bada umurnin hakan.
ba Zaraddin ba ko Dad akasa a zane babu wanda ya isa ya dakatar da faruwar haka.
jikin Zaraddin yayi taya-taya ya daku sai birgima yake a kasa.
Daddy ya d'aga wa security hannu tare da fad'in
"Ku barshi haka."
aiko cak suka d'auki umurni kowa janye belt d'inshi a kansa.
Daddy ya sunkuya ya kwashi kayansa ya wasa masa a jikinsa.
ya nuna sa da hannu
sannan ya ce "Tashi kabar gidan nan yanzun nan kayi nesa da nan! kar ka sake nakara ganin ka a eriyar unguwar nan!."
Abbie ya yi saurin masowa in da Daddy ya ke ya ce
"Allah yahuci zuciyar ka Yaya, dan Allah ayi hakuri a barshi, ya yi laifi kam, zai gyara kuskuren sa gaba."
"Sulaiman yaron nan bansan me ke damun sa ba, yana ta kokarin dole sai ya b'ata mana sunan family,
ni da shi na kirasa na zaunar dashi,
kan ya natsu ya dai na biyewa abokan banza,
suna sha-shan ci,
suna gama makarantar da suke waje zan turasu shi da 'yan uwansa, akasar nan ma ke nan a gaban mu, yake irin wannan hali bare kuma da yaga baya kasar ma baki d'aya,
babu idon kowa a kansa, bazai dai na ba ya tafi kawai idan ya gyara ya dawo!."
Dad ya taune lab'b'ansa ya yi saurin yiwa Mom ido dayaga tana shirin magana.
ya dubi d'an nasa cikin b'acin rai ya ce
"Ta shi aka ce ka tafi! wannan shine hukuncin da ya dace da kai."
ya shure shi da kafa yana cigaba da fad'in
"Kai d'ayan ka baka isa kasa mana ciwon kai ba,
ba kai kad'ai muka haifa ba,
kuna da yawa, tashi ka b'ace mana da gani, ku d'auke shi ku fita da shi!."
security suka janye shi sukayi waje da shi.
Dad ya dubi Daddy cikin kwantar da murya ya ce
"Allah ya baka hakuri Yaya,
wlh ina iya bakin kokari na akan ganin ya natsu kamar sauran 'yan'uwansa."
kai Daddy ya girgiza ya ce
"Banga gazawarka akan tarbiyarsa ba, d'an yau shiriyar Allah ce kad'ai mafita a gare sa, Allah ya shirya mana zuriya baki d'aya."
duk suka amsa da amin.
Daddy ya juya ya nufi side d'in sa bayan ya ce, kowa ya koma nashi matsugunin.
Jikin Aunty
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 20