kiran sa.
sai dai har kiran ta yanke bai d'aga ba,
hankali tashe takuma maida kiran a karo na uku, nan ma har ya yanke bai d'aga ba,
abinda Daddy bai tab'a yi ba ta kira sa a waya duk abin da yake zai bari ya d'aga kiran ta,
sai gashi yau ta kirasa har sau hud'u baya d'aga kiran ta.
ba karamin masifar tashin hankali ta shiga ba, lokacin da ta kira wayoyin su Hajja Umma Abba Maryam basu d'aga ba.
sai ga Aunty na hawaye tama rasa me ma zatayi sai kai kawo take sakanin parkour zuwa bedroom.
A b'angaren Daddy kuwa wayarsa ya mance cikin motar kamfanin sa na abuja da akaje d'auko sa a airport, sabar damuwar son sanin halin da FEERYAL take ciki.
su Abba kuwa wayoyin nasu duk a gida suka barosu.
Jin kirar yayi yawa ne direban ya d'auko wayar ya biyo sa da shi cikin asibitin.
Aunty na rike da waya tana zaga guri da ambaton sunan Allah yayin da wasu hawaye ke fita a idon ta batare da tasan suna zubowa ba.
Baba Rabi na ta tausasata tana cewa
"Insha'allah komai zaizo da sauki muyi ta addu'a."
da sauri ta d'ago wayar jin shigowar kira, bata tsaya duba mai kiran nata ba tayi saurin picking call d'in,
ta kai wayar kunnen ta.
jin muryar Daddy yana fad'in
"Hello Fad'imatu."
bata san san da ta fashe da kuka ba tana fad'in
"Daddy kana ina ka bani tsoro ina ta kiranka baka d'agawa, su Abba basa d'aukar waya, dan Allah Daddy kazo, ni zanje Abuja hankali na bazai kwanta ba in banje naga halin da suke ciki ba."
"Ki nutsu Fad'imatu ki saurare ni, ya isa haka kibar kukan nan, bani hankalin ki a nan Fad'imatu, uhm kina jina?."
hawayen ta ta share ta ce
"Eh."
"Yauwa ki kwantar da hankalinki yanzu haka ina abuja gani nan tare dasu Alhajin Abuja,
duk suna cikin koshin lafiya,
d'iyarki ma tasami lafiya tana bacci yanzu haka."
wani numfashi ta sauke ta ce
"Daddy shine ka tafi baka fad'a min ba, baka kuma tafi da ni ba,
to kasa ayi min bukin yanzun nan nima zanzo bari naje na shirya."
"A'a Fad'imatu ki saurare ni, basai kinzo ba kiyi zaman ki,
ba gani a gurin ba."
"Daddy ni dai ina so naga FEERYAL basu mata komai ba ko, me yasa to take asibiti?."
"Babu abin da suka mata razana tayi tashiga dogon suma, kuma ansami nasarar cirota daga dogon suman yanzun nan muna tare muna hira da ita,
bata jima da komawa bacci ba, kar ki damu zan taho miki da d'iyarki."
numfashi mai karfi Aunty ta sauke tanayiwa Allah godiya,
kana ta ce
"Ina su Hajja Umma?."
Daddy ya masa ya mika musu wayar.
jin muryoyin su yasa hankalin Aunty dad'a kwanci.
Bayan Abba sun gama waya da Aunty.
ya dubi Daddy ya na fad'in
"Dama ina fargabar cigaba da zaman FEERYAL a gurin mu a irin wannan lokacin,
munyi magana da kwamishinan 'yansanda yake ce min da da hali da an d'aga yarinyar a nan, sabo da
mai tawagar d'aukar amarya yana da mugun hatsari sosai,
dan yana da mutane da yawa kuma an shaidesa bai tab'a kaho hare ya tashi a banza ba,
zai iya yin komai duk da yana tsare amma akwai idanunsa a waje,
bare kuma ya kai hari an samu nasarar cafkesa zai iya ninka haushin sa,ya yi abinda ba'ayi sammani ba,
ta hanyar waiwayo wa kuma d'aukarta, tun da akwai sauran tawagar sa a waje,
yanzu haka suna ta kan bincike don su sami nasarar cafke sauran tawagar nasa."
Daddy ya jinjina kai sannan ya ce
"Ni ma nayi wannan tunanin, sannan kuma nasan hankalin Fad'imatu bazai tab'a kwanciya ba har in ba ta ganta ba, zan tafi da ita, har zuwa san da komai zai lafa."
Kwanan FEERYAL d'aya a asibiti in aka had'a da daren da aka kawota biyu ke nan.
da yamma Daddy ya bukaci a sallame su ganin jikin nata ya ware sosai, suka tattara sukayi gidan Abba.
'yan'uwa da abokan arziki da makota suka rika tururruwa zuwa gaida FEERYAL da musu jaje.
ancika tam a parlour sai jajanta lamarin ake 'yan cikin unguwar kuwa sai bada labarin yadda suka tsinci kansu lokacin da ake musayar wuta sakanin 'yan ta'addan da jami'an tsaro.
FEERYAL dai na zaune tana bin kowa da ido bata iya ce da kowa komai dama can ita ba mai yawan magana bace,
ga kuma faruwar lamarin da har yanzu yana jikinta tsoro da firgici mai had'e da fargaba, sai ta dad'a zamowa very silent.
Kiran Inspector Nasir ne ya shigo wayar Maryam ta mike tanufi bedroom d'in su.
ta zauna bakin gado tare da d'aga wayar tana jingina bayanta a jikin gado.
"Hello, Nasir ya aikin?."
"Lafiya lau, ya fargaba?."
"Hm har yanzu ban gama dawowa normal ba, fargaba yaki sake ni, har yanzu ina ganin abin a idona."
dariya ya yi yana cewa
"To FEERYAL kuma tace yaya ke nan, ita da ta shiga hanunsu taga yaki a kan idon ta."
"Ai FEERYAL tafini tsoro a mugun razane take har yanzu, kar kaga yadda take ciccire ido a parlour, da zataji karar wani abu yanzu dogon suma zata koma."
dariya duk sukayi.
Nasir ya ce
"Maryam ba kin ga girman irin son da Major Sadam yake yi wa FEERYAL ba,
ki duba kiga irin babban taimakon da ya yi mata,
yabada jikin sa da ransa wajen ceton rayuwarta daga annun 'yanta'addan can,
bai bari sun tafi da ita ba sai da ya tabbar da ya kwato ta a hannunsu,
Sadam yana son FEERYAL wlh bakiga halin da ya shigaba ranar, sai da ta farfad'o kafin hankalin sa ya kwanta,
haka ya wuni ya kwana bai d'and'ana komai a bakin sa ba, har sai da ta farfad'o kafin
ya samu ya sawa cikin sa wani abu."
Zama Maryam ta gyara sannan ta ce
"Nasir FEERYAL ita ta ta baku babban gudumawa wajen cafke 'yanta'addan da kuka jima kuke son kamasu kuka kasa,
bawai ita kuka taimaka ba ita ta taimake ku, ta baku damar cafke su,
Nasir bakasan waye FEERYAL ba,
FEERYAL tana da wani b'oyayyen baiwa da ba kowa ne ya sani ba, sai idan ka zauna da ita zaka san hakan,
ina da tabbacin FEERYAL ita ce silar taimakon ku wajen kama b'arayen nan, bance kun gaza ba ina mika jinjina ga jami'antsaron mu,
kuna kokari kam yadda ya kamata,
amma a wannan fannin kam tambas FEERYAL ita ce Star d'in wasan."
"Hm Maryan ke nan ke dai duk in da aka biyo sai kin toshe, to naji FEERYAL ta bada gudumawa wajen cafke tawagar d'aukar amarya, tun da ita akazo d'auka, har muka samu nasarar kamasu,
amma fa ki sani, Sadam sadaukar da rayuwar sa ya yi yafito gaba da gaba suka gwafza shi da kansa ya harbe Bala Kwari shugaban tawagar d'aukar amarya,
bayan ya harbe mutum uku cikin 'yan tawagar nasa."
"Duk wannan bajintar bayan da ta gama nata aikin ne, mance kawai duk yadda zan gaya maka bazaka fahimta ba,
amma lokacin da zaka fahimtar na zuwa,
san da mukayi aure FEERYAL tazo gidan mu."
"To shike nan Allah ya kaimu lokacin,
bayan ma kina ta jan lokacin please Maryam ki bari
na turo gida a sa mana rana, ban san me kike jira ba,
ko so kike sai kin had'a digiri na biyu ban sani ba."
dariya ta yi ta ce
"Ban ce ba dai ni kam, kai kam to meye matsalar ka bayan sadakinka yana hanu."
"Kin fi kowa sanin matsala ta, dan na bada sadaki iya haka bai wadatar ba, ke d'in nake bukata a kusa da ni,
bari komai ya lafa hakuri na ya kare yanzu kam."
shiru tayi tana saurarar sa.
"Kinyi shiru kina jina ba, kin manna min hauka ina."
"Na'isa yaushe Nasir d'ina ya sami tab'in hankali."
tayi maganar da muryar dariya.
"Saura kad'an ai bakisan rashin aure yana tab'a kwakwalwa ba."
ido ta waro ta ce
"Bana fata ya tab'a maka hankali,
last year insha'Allah zamu kasan ce ma'aurata, shike nan?."
"Yauwa yanzu naji batu, duk da dai har karshen shekara ya min nisa, za'a janyo lokacin."
nan suka cigaba da hira irin dai na masoya.
Daddy ne zaune a parlour'n Abba bayan sunyi sallama da ba'i mazan da suka zo wa Abba jaje.
Daddy ya gyara zama tare da duban agogon hannunsa, kana ya dubi Abba sannan ya ce
"Alhaji mu zamu wuce zamubi jirgin karfe 7, gashi har 6 ta kusa."
"Ah wai yau ne zaku tafin inace sai gobe, ai yanzu dare zatayi, da ka bari zuwa gobe dai."
"Babu ko mai zamu wuce yau har an shirya mana tafiya karfe 7."
"To shike nan bari nayi musu magana zanyi kewar amaryata, amma fa daga zaran komai ya lafa zaka dawo min da ita,
amma wani hanzari ba gudu ba, ya zakayi da Hajiyar ka, kana ganin babu matsala komawar nata can,
ko dai zanyi magana da Aliyu ne a kaita can kasar Lebanon, in yaso zuwa jibi angama shirya mata komai sai ta tafi."
Daddy ya ce
"Babu komai insha'allah zanji da komai baza'a sami wata matsala ba in Allah ya yarda."
"To Allah ya sa, in dai kaga hakan zai janyo wata matsalar to barin kasar natama gaba d'aya zaifi bata tsaro."
Abba ya fad'a yana mikewa ya nufi b'angaren Hajja Umma.
Tun da FEERYAL ta sami labarin zasu tafi da Daddy yanzu, tarika sakin murmushi.
dan dama tun da ta dawo gidan, hankalin ta sam baya kwance, gani take kamar b'arayen nan zasu kuma dawowa cikin daren yau,
bugu da kari kuma dama tana so taga Ammie'n ta, da suka shafi shekaru goma sha, basu zauna sun jima tare ba.
dan ko Aunty tazo Lagos baifi tayi kwana uku biyu ta koma ba.
Hajja Umma da Maryam suka had'a mata kayanta, kasancewar ba komawa duka zatayi ba iya manyan akwatuna biyu suka cika mata.
Duk suka fito musu rakiya jikin motar kamfanin Daddy daya zo d'aukar su.
Hajja Umma tana ta zolayar FEERYAL wai tayi ta tafi dama so take ta tafi ta bar mata mijinta.
a gefe guda kuwa sam basuso ta kauce a cikin su ba, sai dai hakan ce hanyar da ta dace dan su ketarar da ita daga gudun kuma fad'awa wata hatsari, tun da har hukuma da kansu sunce ta kauce a cikin garin.
sannan ita kanta yarinyar zatafi samin nutsuwa ne idan ta kauce na d'an wani lokaci daga inda abin ya faru.
Maryam ta rungume FEERYAL tana hawaye, tambas zatayi kewarta tun da tazo gidan bata tab'a sa kafarta a guri batare da ita ba.
da kyar ta saketa ta shige mota itama tana hawaye.
su Abba suna d'aga musu hannu direba yaja suka nufi airport..
Karfe 9 da mintuna 30 dai-dai jirgin su ya sauka a Lagos.
inda tuntuni direban Daddy ya iso airport yake jiran saukowarsu.
FEERYAL tarika baza ido, tana tuna wai ta tab'a rayuwa a garin duk da bata da wayo sosai lokacin,
sai dai kwakwalwar yaro takan tuna wasu abin tsinta-tsinta ba duka ba kam.
Daddy yad'an zuba mata ido ya lura da tashiga tunani tun sanda suka sauko a jirgi, sai ya yi ta janta da hira yana nuna mata hanyoyi da tambayarta tasan nan ta san can.
kai kawai ta girgiza masa da alama bata fa gane ko ina ba.
suna isa direba ya yi hon security suka bud'e masa get.
direct part d'in Aunty ya nufa kamar yadda Daddy ya umurce sa.
ya yi hon bakin get d'in side d'in mai gadin kofar ya bud'e.
Aunty na tsaye a tsakiyar farfajiya suka karaso, da sauri ta isa ta bud'e gefen da FEERYAL take
ta fito suka rungume juna, cike da farincikin ganin juna.
Daddy yana ta yi musu dariya, ya ce
"Ya yi kyau Fad'imatu ita kad'ai kika sani ko,
ni an share ni."
sai sannan ta sake ta ta rungume shi tana fad'in
"Ayya Daddy na jima ban ganta bane."
"To gashi nan na kawo miki d'iyarki."
"Nagode Daddy."
ta fad'a tana dad'a rungume shi.
Aunty ta ja hannun Daddy dana FEERYAL suka shige ciki, direba ya kwaso kayan ya biyo su da shi.
D'akin FEERYAL na tun da Aunty ta shige da ita,
in da shi kuma Daddy ya wuce bedroom d'in Aunty, domin ya d'an watsa ruwa.
a bakin kofar d'akin direba ya aje akwatin, Aunty ta kwaso ta shigo da su ciki.
FEERYAL tana ta bin d'akin da kallo wanda yake a gyare tsaf sai kamshi yake.
tana ganin d'akin tun da a idon kuruciya,
ga komai na wasanta a ciki har yanzu.
da sauri ta isa inda babyn wasan ta yake ta d'auka ta sunbace ta tana sakin murmushi.
Aunty tana kallonta cike da jindad'i ta ce
"Kin tuna da 'yar tsanan, ki ko."
murmushi tayi tana rungume babyn ta ce
"Na tuna Ammie."
Aunty baki yaki rufuwa taga d'iyarta, a b'angaren FEERYAL ma haka abin yake, farincikinta bazai fad'u ba.
Bayan Aunty tasa FEERYAL tayi wanka dan ta rage gajiya,
suka fito parkour dan sun rigada sun yi sallar su tun a jirgi.
suka yada zangonsu a parlour,
Daddy ya fito ya same su.
abinci Aunty ta kawo musu kala-kala, har da cake da yoghurt dan tasan abincin da tafi so ke nan.
aiko bataci komai sai sai cake da yoghurt d'in.
Aunty ta d'auke plt d'in cake a gabanta ta ce
"Sa hanu kici abinci, har yanzu baki dai na cin wannan abin da bazai koshar da ke d'in nan ba ko."
kai ta langwab'ar gefe.
Daddy ya ce
"Ajiye mata taci kayanta, in da bata koshi ai bazata ci ba."
aiko ta saki murmushin jin dad'i, Aunty ta girgiza kai tana sakar mata hararar wasa.
Sun jima sosai suna hirar yaushe gamo sai da Daddy ya ce FEERYAL taje ta kwanta ganin tana ta sauke hamma..
Washegari da sassafe Daddy ya yi sammakon zuwa gurin Hajiya.
kai tsaye bedroom d'in ta ya wuce, ya tadda ita zaune tana shafa maganin ciwon kafa, a gwuiwarta.
ya sami guri ya zauna kan kujera ya shiga gaisheta ta amsa tana fad'in
"Jiya ban gankaba wannan yaron Ajimi yake ce min wai yanaga tafiya kayi."
"Am..Eh d'an tafiya nayi bamai nisa ba,
amma Hajiya kafar tana damin ki ne da yawa haka?."
"Wlh kwana biyun nan kafar tana d'an tab'ani amma ina shafa wannan maganin sai naji kafar tamin wasai."
"Ai ban sani ba Hajiya da an koma asibiti."
"Ai tun ranar da kafar ta tashi mukayi waya da
abokin turawa, nake fad'a masa yadda yake min ya ce wa Ajimi yaje ya siyo min wannan maganin,
ya ce kullum safiya da maraice narika shafashi,
shike nan na nimi ciwon na rasa,
ni har zan aje maganin ma danaji na warke shi ya ce kar na aje nacigaba da shafawa har sai ya kare."
Daddy ya ce
"To Allah ya sauwaka ya kara lafiya Hajiya."
Ido Hajiya ta zubawa TV dake aiki cikin d'akin tana mara baki,
a b'angaren Daddy shima hankalin sa ya maida kan TV jin labaran da suke watsawa.
Hajiya ta tab'e baki tana fad'in
"Tun jiya labarannan kad'ai akeyi,
ni kamar naji ance gidan Alhaji Tahir Abbas ne b'arayin suka shiga, basu tafi da 'yar da suka sace ba a ka kamasu,
Tahir Abbas d'in nan ba shine surukinka ba?."
Daddy ya ce
"Eh shine mahaifin Fad'imatu ne, Allah ya takaita ma basu tafi da ita ba, mutumin yana da had'ari sosai lalata yara yake daga bisani ya sako su wasu da ciki wasu da goyo."
Hajiya ta ware ido ta dafe kirji
"Kai wannan anyi mugun matsiyaci, wasayyahu ya tsaya masa acan, Allah kare kikokin mu,
amma dai an bincika baiyiwa yarinyar komai ba ko,
dan irin su basa d'aukar asara biyu,
idan yaga alamun fa ya shiga hanu bayada mafaka,
zai iya aiwatar da mugun nufinsa a kan ta kar ya yi biyu babu,
banaji suna fad'in yarinyar tana asibiti ba."
Daddy ya ce
"Amin ya Allah da sauran yara baki d'aya, beyi mata komai ba, ta firgita da lamarin ne shine ta suma aka kaita asibiti,
Hajiya yarinyar nan ce fa FEERYAL wacce ta zauna nan gurin Fad'imatu ita sukayi kokarin sacewar."
Hajiya ta gyara zama da mamaki ta ce
"To..too wacce 'yar kenan ohoo kace aljanar can, dama tana gurin su ashe, yoo ai da sun tafi da ita dama an rage mugun iri,
irin su kam da ma mene ne gaiyan tsiya gayyan fitina a guri,
to ina ga irin ta duk irin abin da nake hangowa ke nan,
ai wannan yarinyar zamanta fitina ce a guri, dama sun bari an tafi da ita da an rage mugun iri,
dan ita ce fitinar da ta janyo b'arayi gidan, wa ya sani ma ko baki suka had'a da ita,
azo ayi sata a gidan,
da yanzu gidan nan zata turo mana su,
ashe haka ta shahara ta zamo gaggaruma."
Daddy ya d'anyi shiru yana tunanin ta ina zai fara bi da Hajiya kana ya ce
"Hajiya ba haka bane su wad'an nan 'yanta'addan suna da tawagarsu na musamman, ba wani ke kawo musu kwangila ba su suke aikinsu da kansu suke b'arna a kasa,
duk wacce suka gani ta musu shike nan sai subi dare ko da rana ma suna shiga su d'auko ta sukuma tafi da ita,
Allah dai ya kare mu daga sharrin su yasa karshensu ke nan da aka kama su."
Hajiya ta mara baki tana fad'in
"Hmm to ai shike nan yadai tsaya musu a can."
Daddy ya girgiza kai kawai sannan yad'an gyara zaman sa kana yaci gaba da fad'in
"Hajiya dama wata alfarma nazo nima a gurin ki,
kinga abin da ya farun nan jami'an tsaro sunci a d'aga yarinyar a garin saboda 'yan ta'addan zasu iya zuwa su sace ta,
shine nake niman alfarma a gurinki tazo ta zauna damu nad'an wani lokaci kafin komai ya lafa, hukuma sugama bincike su kama sauran 'yan ta'addan sai ta koma Abuja,
Hajiya ta ware ido tare da buga kirji
"Nashiga uku! Abubakar kasan me kake fad'a kuwa,
'yarda ta kai fitina can kake so ka kuma dawo mana da ita ta kawo mana fitanar nan,
Abubakar annobar da muka kakkab'eta agidan kake so ka kuma yayub'o mana ita ka dawo mana da ita,
kanka d'aya kuwa Abubakar,
to ka dawo hankalinka ko da wasa kada ka soma ban yarda ba Allah ma bai yadda ba,
kada ka sake ka kuma jajjab'o mana fitina a gida,
barsu su karata a can."
"Hajiya ki fahimce ni ba fa zata dawo gidan nan din-din-din bane zuwa na d'an wani lokaci ne zata koma, daga zaran an gama bincike,
zata zo ne a matsayin bakuwar da zata koma,
ba wani jimawa zatayi ba, daga zaran an kama sauran b'arayin zata koma."
"Oho kace kawai zaka kawo ta sabo da b'arayin su biyo ta nan, sai su had'a da jikokina su kwashe suyi gaba,
Abubakar ina rabaka da kiwon shanu kana ce kyalla ta b'ata, to ban amince ba kada ka soma, na gaya maka ke nan."
Shiru Daddy ya yi bai kuma ce komai ba, kana ya mike ya ce
"To shike nan, duk yadda kika ce hakan za'ayi Hajiya Allah ya huci zuciyar ki, a wuni lafiya."
ya d'aga kafa yana kokarin tafiya da sauri ya kai
hanu ya d'an dafe kirjinsa.
ya shiga d'an kananun tari yana dafe da kirjin nasa.
Hajiya ta mike da sauri tana bubbuga kafad'ar sa
"Kai Abubakar zauna zauna tukun, kana ma shan maganin ka kuwa, ko na kira abokin turawa ne ya rubuto wani maganin da zaka sha yanzu."
kai ya girgiza ya ce
"Kafin na fito ma sai da nasha magani, ba komai zai lafa."
Hajiya ta rud'e gaba d'aya tana jera masa sannu.
Daddy ya ce
"Bari naje na d'an kwanta nasan zai lafa zuwa anjima,
amma hajiya da an duba batun nan wanda ya taimaki wani Allah zai taimake sa, shifa d'a na kowa ne,
idan kaso ya yi kyau ka taimaki al'umma gaba d'aya ne."
Hajiya ta kwantar da murya, duk abinta sam bata so taga 'ya'yan ta cikin halin ciwo
"In ban da kai Abubakar ciwonka na kokarin tashi amma kana magana kan aljanar can,
ina mu ina taimakon aljana ai sai dai danginta aljanu,
duk in da zata zauna sai ta haifar da fitina,
sabo da ba jinsin mu ba ce,
kaje ka nutsu kada ciwo ya kayar da kai,
amma tun da ka matsa sai ta zo ai amma tayi harkarta karta shiga harkar jikokina,
ta zauna can kada ta rab'e su,
ana gama bincike kuma takoma can in da akayi gayyarta."
Daddy ya ce
"Nagode Hajiya."
"Jeka maza kaje ka kwanta ka natsu kirjin zai lafa."
ya ce to.
ya fita ya koma sashin Aunty.
Aunty na ganin sa ta tare sa da sauri tana tambayar sa ya dai dan taga alamar kamar da akwai abin da ke damun sa.
ya ce
Ba ko mai tun shekaran jiya yake jin kirjinsa yana masa zafi, sai da abunnan ya faru ya gane fargabar hakan ne ke bibiyarsa.
nan yake shaida mata Hajiya fa ta amince FEERYAL ta zauna kafin komai ya lafa.
Aunty tayi farinciki matuka sai dai kuma ganin kamar ciwonsa nason tashi sai duk ta shiga damuwa.
bata gusheba sai da ta tabbatar da yasami bacci.
Su Aunty na parlour bayan sunyi breakfast, FEERYAL na kwance jikinta tana ta zuba shagwab'a,
Aunty na taje mata gashi wai dan ta ce zata kira mai kitso tayi mata kitso, take ta birgima a jikinta wai ita bata so yana mata zafi.
Aunty tarike hab'a tana fad'in
"To kawai a aske gashin tunda bakya son kitso,
kinfi so kiye ta nad'e gashi, ai ko tace gashin ma kad'ai ya ishe ki,
in kikayi kitso fa ai zaki huta na kwana biyu,
kafin aje a sake wankewa."
da sauri ta ce
"Allah a aske Ammie damina yake."
dungurin kanta tayi ta.
zatayi magana kiran Ammah ya shigo wayarta
ta d'aga da sallama bayan sun gaisa Ammah ta ce
"Hajiya Fatima ban samu na shigo da safen nan ba,
ya dai kika sami labarin jikin FEERYAL."
Aunty ta yi murmushi ta ce
"Ai gani ga FEERYAL jiya Daddy ya d'auko ta."
"Dan Allah da gaske ikon Allah FEERYAL anzo amma dai jikin nata da sauki ko, bari na gama na shigo."
Miemie dake zaune can gefe tana dane-dannen waya jin Ammah ta ce FEERYAL tazo.
ta jifar da wayar tana fad'in
"Ammah FEERYAL tazo?."
kai Ammah ta gyad'a, aiko da sauri Miemie ta mike da gudu tayi waje........!
Mommyn Twinc ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️21
Da gudu Miemie ta shigo parlour'n Aunty tun daga bakin kofa ta ke fad'in
"Aunty ina FEERYAL wai da gaske tazo, FEERYAL FEERYAL kina ina?."
FEERYAL dake kwance kan kafar Aunty ta mike tsaye da sauri.
Miemie ta karaso ta tsaya suna kallon-kallo.
yayin da dukkanin su kamannin yarantar su yake zuwar musu cikin kwakwalwa,
duk da kamannin su dukansu ya canza a yanzu bai hana amintakarsu tasiri wajen gane junan su lokaci guda ba.
a tare suka nuna junan su da hannu tare da kiran sunan junan su a tare.
"FEERYAL!."
Miemie ta fad'a.
FEERYAL ma ta ce
"Miemie!."
wani irin rungume junan su sukayi cikin mashahuriyar murna da farinciki, suna dariya.
Miemie ta janye jikinta tana duban ta da mamaki take fad'in
"Wai FEERYAL ke ce haka?."
FEERYAL tayi murmushi ta ce
"Miemie kema ke ce haka? ga yadda kika zamo wata katuwa da yawa."
"Kee da ma na girme ki, ko ba haka ba Aunty, amma dubi yadda kika zama har kin fini fa."
cewar Miemie tana zagayata da duba gaba da bayan ta.
Aunty dai dariya take ta binsu da shi, kaunarsu tun na yarinta abin yana ta burgeta.
Miemie ta b'ata rai tare da hararar FEERYAL ta ce
"Ko tuna ni ma bakyayi ni ce kad'ai mai damuwar tunaki, nifa da tunanin ki ma na girma,
ki tambayi Aunty kullum sai na zo part d'innan,
sanda na mallaki hankalin kaina kuwa nakarb'i lambarki wajen Aunty amma ko na kira ki bakya d'agawa,
kusan kullum sai na kiraki bazaki d'aga ba, sai na hakura kawai na daina kiran naki amma ban iya cireki cikin raina ba."
"Miemie nimafa ban cireki a raina ba, kina raina,
bakuwar lamba ce bana d'agawa da kinzo kin kirani da lambar Ammie'na."
"Ai nazo ranar nasa Aunty ta kira min ke aka ce bakya gida kin tafi school,
da yamma kuma nayi ta kiran lambar ki yana shiga baki d'aga ba."
Ganin diramar nasu Aunty tayi dariya ta ce
"Ai wayar FEERYAL kam na buga game ne, na mance ne ma da lamban Hajja Umma ko na Maryam na baki, shine zaki same ta."
Miemie ta ce
"To sannu biloniya wato bakuwar lamba ce bakya d'agawa, gudun kada ace ki kawo kud'ad'e ko."
dariya FEERYAL tayi
cikin tsiririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce.
"Ke ba haka bane ina d'agawa sai ace FEERYAL mun had'u a waje kaza dama wata ce ko wani ne ya bani lambar ki,
to ya yanzu in zo ne,
niko sai in kashe wayar daga nan na daina d'aga bakuwar lamba."
dariya duk suka fashe da shi harda Aunty.
Miemie ta ja hannunta tare da d'aukar d'an karamin gyalen ta dake kan kafar Aunty ta mika mata ta ce
"Zo muje Ammah ta ganki."
Suna tafe Miemie tana ta zuba mata surutu,
FEERYAL ba gwana ce a iya surutu ba, sai dai tayi ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 20