ta haife ka."
Da sauri Daddy ya mike yana fad'in
"Sannu da zuwa Hajiya yanzu nake shirin zuwa gaishe ki, bismilla ga guri zauna."
hannu ta d'aga masa tana fad'in
"Ba zama ne ya kawo ni ba, na ce yaushe ta haihu ban sani ba!."
kai ya sunkuyar kana ya d'ago ya dubi mahaifiyar tasa kana ya ce..........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
🅿️2
"Da ma Hajiya zanzo muyi magana, amma tun da har kinzo ki zauna kiji yadda akayi zata haihu ne baki sani ba."
"Ba gashi kuwa sai zuwa nayi naga d'a a hannu ba, ai baka d'auke ni da mahimmanci ba, narasa me ke damunka Abubakar akan Fatima duk ka susuce kazama wani iri, tun jiya nake kiran ka a waya sabo da kuna nakudar munafurci kaki d'aga wayar ma, bare har kazo in da nake,
Allah yasa kafin ta haihu dubunta sun haihu,
ko wani munafurcin ne na b'oye cikin da haihuwar oho."
wani irin mummunar fad'uwar gaba Umma Karima ta ji.
yanzu bawai haihuwar ce ke firgitata ba, duk da tabbacin da take da shi kan cewa bazata tab'a haihuwa ba har abada, ga kuma akasin hakan ta gani.
fatan ta d'aya kada a ce namiji ta haifa.
a b'angaren Mommy ma haka abun yake.
mita ta shiga yi tana dad'a ingiza Hajiya
"Yanzu har rashin muhimmancin mu yakai ta haihu a cikin gidan nan bamu saniba, idan an b'oye ciki sai a b'o haihuwa, haba Alhaji me ka mai da mu haka."
Hajiya ta cab'i zancen da fad'in
"Marasa mutunci mana haka ya mai da kowa, to ka zauna da matarka kucigaba da munafurcin ku, kada ka sake kazo in da nake."
Ta juya tana kokarin fita da sauri ya tare ta
"Hajiya kiyi hakuri ki saurare ni,
bafa haihuwa Fatima tayi ba, sai kuma tayi ciki har ta haihu ki gaza sani, abun da ake fatan samu idan aka samu ai kowa sai ya sani,
bana gida ba har da na waje, kowa za'a sanar masa yataya mu farinci,
jiya a hanyarmu ta dawowa muka tsinci jaririyar a cikin ruwa, da alama had'ari iyayen ta sukayi tana bukatar taimako,
shine muka d'auke ta, likita ya shaida mana bazata iya rayuwa ba sai da nonon uwa shiyasa aka samarwa Fad'imatu ruwan nono domin ta ceto rayuwar ta."
Wani irin zabura dukkanin su sukayi.
Hajiya ta bigi kirji ta tuma tsalle ta zube kasa ta saka hannu a ka tana fad'in
"Wayyo Allah Abubakar da Fatima zasu kashe ni, tsintar ta kukayi kuma a cikin ruwa, anya Abubakar
kanka d'aya kuwa ko aljanu sun shafe ka ne,
ku tsinci 'yar kuma acikin ruwa ma har ka lamunci matarka ta shayar da ita,
sabo da karasa 'ya'ya ne ko me?
idan ita juya ce bata haihuwa ai kai da 'ya'yan ka ta ganka tafe da kafafun su,
duk basu ishekaba har sai kanimi kari da 'ya'yan aljanu."
Tamaso ta leka fuskar Feeryal dake rungume a hannun Aunty, data rungume ta tsam kamar za'a kwatar mata ita.
Hajiya takuma zabura tare da mustsuke idonta tana fad'in
"Lahaula maganin baki wasayyahuuuuu ya tsaya a kanki Fatima!
Abubakar d'iyar aljanu kuka d'auko kuka kawo mana gida,
wlh ko shakka babu wannan d'iyar aljanu ce, tun da nake ban tab'a ganin mutum irin wannan ba,
ko a fina-finan masu jajayen kunnuwan da nake gani ana haskosu a TV,
dubi kalarta dubi kalar kwayar idanun ta, sam basuyi kalar na mutane ba,
kwayar ido kamar na magen mayu wlh ba mutum bace;
maza-maza kuyi gaggawar d'aukar 'yar su ku mayar musu in da kuka d'auko musu ita,
tun kafin bala'i ya sauka a gidan nan,
dan bazamu iya da fad'an aljanu ba,
dan babu kaura cikin dangin mu,
wani bala'in kuke son d'auko mana, zaku d'auko aljanar ruwa ku kawo mana ita gida."
Mommy da Umma Karima har suna rige-rigen zuwa leka fuskar yarinyar, bakaramin firgici suka shiga da ganin halittar 'yar ba,
'ya'yansu ma kowa sai da yaje yagano fuskar ta.
Mommy tashiga zabga salati da tafa hannu tana fad'in
"Wlh aljana ce Hajiya dakur'ani bazamu zauna da aljanar ruwa a gidan nan ba, ko a fita da ita ko mu mufita da 'ya'yan mu, dan ambaliyar ruwa bazataci da mu ba ehe."
Umma Karima ta karkata baki cike da rashin mutunci tana aikawa Aunty kallon banza ta ce
"An dai yi asara rashin haihuwa nason bud'a miki kai shine har zaki d'auko aljana ki kawo mana ita cikin gida,
to wlh ba a gidan nan ba, idan haihuwar abin banza ne ki haifa mana,
sai kinje kin d'auko aljanar ruwa kin kawo mana damuwa."
Rumtse ido Aunty tayi tana jin yanda maganganun su ke mata yawo cikin kwakwalwa.
da sauri Daddy yataro Hajiya ganin yadda take shiga bata nan take fita ba.
ya ce
"Hajiya kiyi hakuri amma ba aljana ba ce mutum ce, ina kyautata zaton watakila badaga yankin kasarmu take ba,
shi yasa kamanninta ya bambanta amma mutum ce ita irin mu."
"Inji uban wa tun da kake katab'a gani mutum kyakkyawa irin wannan?
kana kallon aljana kiri-kiri kace mutum,
dama ance aljanun ruwa kyawawa ne gashinan kiri-kiri ina gani kace ba haka ba,
kai Ajimi kirawo min Sulaiman da Tukur yau zan bar gidan nan dan bazan zauna da aljana ba."
Ajeemal ya juya yana jan kwafa, sam baya son fitinar kakar nan tasu.
Hajiya ta cigaba da fad'a har tana kumfar baki, su Mommy na tayata.
batare da b'ata lokaci ba Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suka amsa kiran mahaifiyar tasu.
Hajiya na ganin su takawo kuka ta saka tana sharb'e hanci da fad'in
"Zamata yakare a gidan nan Abubakar ya zab'a ko ni ko aljanar ruwa da matarsa."
da sauri suka karaso in da take sukashiga bata hakuri, Alhaji Sulaiman ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri zo muje sashin ki muyi magana."
da kyar suka janye ta zuwa sashin nata.
Numfashi Daddy ya sauke ganin fitarsu kana ya maida dubansa kan Mommy da Umma Karima ya ce
"Duk wacce bazata iya zamaba ta kama gabanta."
yana kaiwa nan yajuya yabi bayan su Hajiya.
Mugun kallo suka wasawa Aunty Umma Karima ta ce
"Bokanki yafad'a miki karya sai dai ke kibar gidan nan ba dai mu masu 'ya'ya ba."
Mommy kuwa kwafa tayi tare da kuma wasa mata harara tajuya takad'a keyar 'ya'yan ta tana fad'in
"Maza kubar nan kada aljana tashiga jikinku."
Murmushin takaici Aunty tayi tare da bin bayansu da kallo, tana mai dad'a rungume Feeryal ajikinta.
A can sashin Hajiya kuwa sosai ta tubure ita ala dole sai dai Daddy ya zab'i ko ita ko aljanar ruwa,
dan bazata zauna da aljana a gida d'aya ba, bare ta shafe ta ta shafi jikokinta.
da kyar suka shawo kanta da alkawarin za'a mai da yarinyar inda aka d'auko ta.
Ko da suka fito daga sashin nata Alhaji Sulaiman wato Abbieh da Alhaji Tukur Dad suka dubi d'an uwan nasu.
Dad ya ce
"Yaya ina ganin a d'auki yarinyar nan a mayar da ita in da aka sameta ina ganin shine kad'ai samin masalaha,
Hajiya tayi fushi sosai."
Kai Daddy ya girgiza sannan ya ce
"Adai canza mata wani gurin dai-dai ta huce, ta ya za'a ce a maida ta cikin ruwa kisan kai ke nan zamuyi,
yarinyar nan ba aljana ba ce mutum ce, imma aljanar ce iyayen ta suzo su d'auke ta anan ba sai an kaiga cutar da rayuwarta ba,
sannan idan aka rabata da Fad'imatu itama an cutar da rayuwarta,
dan yanzu tamkar mai sabuwar jego take."
"Yaya to kayi wani abu dan Allah dan gujewa fushin hajiya."
cewar Abbieh, kai Daddy ya girgiza kana ya ce
"Insha'allah."
Aunty na zaune tayi jigum Daddy ya shigo, ya zauna gefen ta.
da sauri ta dube shi jiki a sanyaye ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?
dan Allah Daddy kar a rabani da Feeryal wlh ina son ta."
takarashe maganar da damke hannunsa murya a marairaice tamkar zata zubda kwalla.
Hannunta yakuma rikewa cikin nashi kana ya ce
"Insha'allahu baza'a rabaku ba nayi miki alkawari."
wasu hawaye ta share ta ce
"Nagode Daddy." murmushi mai sauti ya yi tare da jan hancinta
"Ammie'n Feeryal a kwantar da hankali haka a daina damuwa da yawa."
kai ta girgiza tana mai da masa murmushin.
A sashin Hajiya bayan fitar su Daddy da d'an jimawa, Hajiya ta cewa Farida taje ta duba mata aljanar tana nan har yanzu ko an tafi da ita.
ko da Farida taje sashin Aunty'n a kulle yake tadawo ta shaidawa Hajiya.
Hajiya tayi kwafa dan a zaton ta sun tafi mai da jaririyar in da suka d'auko ta ne.
ta gyara zama ta soma cin abincin da kulu mai aikin ta takawo mata yanzu,
tana fad'in
"Iya shegen banza da raina da lafiya ta ina gidan wai sai abin da Fatima ke so za'a yi,
rashin haihuwa hauka ce, da zata fara bin teku tana d'iban 'ya'yan aljanu tana kawo mana cikin gida;
wan nan badun daga gidan arziki tafito ba sai na ce wani muguntar take son kitsawa,
takawo aljanu su kwashe mana dukiya su kai mata gidan iyayenta."
"Hajiya wai ashe aljana Hajiya Fatima ta kawo wlh kar kiga yadda na razana aljana kuma a cikin gidan nan, to ita meye gamin ta da aljanu kuma."
cewar Kulu tana zama kan kujera d'an nesa da Hajiya.
Hajiya takai loman katon nama baki tana fad'in
"Niman jaraba mana da niman ganin bayan mutum, to ni nafi karfinta da jikokina,
sai dai taje can ta karata da aljanun, ba dai a gidan nan ba kam, je ki kawo min lemon gorar nan mai d'an sanyi."
Kulu ta tafi tana rike hab'a da mamakin lamarin.
Kwanan Feeryal uku a gidan batare da kowa yasan tana nan ba, dan kowa ya yi zaton da hajiya ta tada bori an mai da ta in da aka d'auko ta.
itama Hajiyar sam batasan tana nan ba.
Umma Karima ce cikin Bedroom in Daddy, shigowarta kenan bayan komawar ta part inta da asuba, data kwana a sashin nasa,
anje anyi wanka an cab'a kwalliya, an shafo wasu turaruka masu tsayawa a kuwa.
ganin baya side d'in gaba d'aya, ta koma side d'in ta,
ta tura babbar 'yarta Saddiqa taje ta duba mata Daddyn su yana part d'in Aunty'n su.
A bakin get in shiga side in Aunty suka had'u da Ajeemal zai wuce side d'in Hajiya.
yana ganin ta ya sai da ta.
"Ina zakije?."
ta ce "Umma ce ta ce naje na duba Daddy a side in Aunty."
ya ce "Wuce ki koma kice baya nan."
baki ta zumb'uro, tana ganin wucewar sa da gudu tayi cikin side d'in.
tana shiga parlour'n Aunty kai tsaye ta wuce cikin bedroom inta babu ko knocking bare sallama.
Aunty na zaune bakin gado tana shirya Feeryal data yi mata wanka,
jin an turo kofa yasata d'agowa tana duban mai shigowar.
ganin Saddiqa ce, ta girgiza kai tana fad'in
"Saddiqa bana ce in zaku shigo kurika yin knocking da sallama ba, ba kyau shigowa d'aki kai tsaye batare da yin sallama ko niman izini ba,
to ya akayi?."
Aunty tayi tambayar tana mai da hankalinta kan shirin da take yiwa Feeryal.
Saddiqa ta juya ta fita bare da ta ce komai ba, kai takuma girgiza wa ta cigaba da abin da ta ke.
Da sauri ta koma side d'in su, tun kan takaraso in da Umma Karima ta ke tashiga fad'in
"Umma Umma Umma wlh Aunty tadawo da aljanar nan, naganta tana sa mata kaya."
huf Umma Karima ta mike ta ce "Ke wai da gaske kinga yarinyar nan a sashinta, eh lallai Fatima anyi bakar munafuka wato boye 'yar tayi,
ko komawa tayi takuma d'auko ta, to wlh sai ta bar gidan nan."
tayi waje fuuu sai sashin Hajiya.
Kirji Hajiya ta buga da jin abun da Umma Karima tazo dashi.
Hajiya ta mikawa Umma Karima waya tana fad'in
"Lalub'o min lambar Abubakar yanzu-yanzun nan, wai ni Abubakar zai maida mutumiyar banza, yazab'i tsintacciyar aljana a kai na."
Daddy na d'aga wayar Hajiya tafashe da kuka tana fad'in
"Ni zakayiwa haka Abubakar wlh yau babu abin da zai zaunar da ni a gidan ka, yanzu-yanzun nan zan bar maka gidan ka,
kacigaba da zama da matarka da bakason b'acin ranta da aljanar da ta tsinto."
Hajiya ta kashe wayar tana sharb'ar hanci, tamike ta nufi bedroom d'in ta tana fad'in
"Ina zan iya zama da annoba a gida d'aya, gara natattara inawa-inawa na koma Yalwa yafi min kwanciyar hankali."
Umma Karima ta saki murmushi akasan ranta tana fad'in
"Fatima ke karamar makira ce."
tamike tafice takoma part d'inta.
Cikin hanzari Daddy yashigo side d'in Hajiya, yana shiga parlour'n ta,
Hajiya nafitowa janye da akwati.
da sauri ya isa inda take yana fad'in
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri kada ki tafi."
"Bani guri da alla! in zauna inmaka me?, ni da bani da mutunci agurin ka,
gara nabaka guri kacigaba da zama da wad'an da kake ganin su da kima,
ina dalili ina mafari zama da aljana guri guda, ina bil adam, kai da kazabi haka sai kayi ta zama da ita,
amma kasani idan jikokina suka sami wata matsala bazan yafe maka ba!."
Da sauri Daddy yarike akwatin ganin tana kokarin tafiyar da gaske ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki gafatarce ni, kada ki tafi, za'a maida ita inda aka d'auko ta dan Allah kiyi zamanki."
"Ni Abubakar ai ka gwada min iyakata aljanar ruwa tafiye maka ni,
ni uwar da na haife ka naci kashinka, ni Abubakar ni."
Hajiya tasaki kuka tana sharb'e hanci da bakim mayafinta.
akwatin ya karb'a a hannunta yana
"Yi hakuri dai Hajiya yanzu za'a fita da ita."
yaja akwatin ya maida shi ciki bedroom, yafito ya isketa zaune a parlour.
hakuri yacigaba da bata sai da yaga ta d'an sauko kafin yafita.
A b'angare Aunty lokacin da Hajiya ta kira Daddy shigowar sa side d'in ta kenan, ko zama baiyi ba yafita zuwa kiran Hajiya.
Kuma jin motsi yasa Aunty fitowa, ganin Daddy ne ta karaso in da yake jiki ba kwari.
murmushi ya yi mata domin karfafa ta, fuska ta dan marairaice ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?."
zama ya yi a bakin gado yana fad'in
"Zanji da ita zaki rayu da Feeryal insha'allah, nayi miki alkawari."
zama tayi gefen sa kana ta ruko hannunsa tana jaddada godiyar ta a gare sa.
tana mai alfaharin kasantuwar sa a matsayin abokin rayuwarta,
dan bai tab'a rageta da wani abu ba, duk abin da ta nima a gurin sa tana samu; hakan kuma baya rasa nasaba da so da kauna da kuma yardar da yake yimata.
Wanda itako take saka masa ta hanyar nuna masa tsantsar kulawa mai had'e da zallar soyayya da nuna damuwa kan abin da ka damu da shi.
Hakan yasa abokan zaman ta suke ganin tagama mallakesa ta hanyar asiri, wan da sam abun ba haka yake ba, Hajiya Fatima babu abin da ta tsana take kyamatar sa sama da bin bokaye da malamam tsubbu.
Hajiya Fatima mata ce mai hakuri da juriya gami da kawaici, tana da matukar hakuri ga ladabi da biyayya; tsafta iya girki iya kwalliya, iya tafiyar da miji yadda ya kamata, uwa uba ruko da addini.
shiyasa tazamo lamba d'aya a gurin maigidan nata wato Alhaji Abubakar Fiya.
Da yamma Daddy yashigo sashin Hajiya, Hajiya na ganin sa ta b'ata fuska, ya isa ya zauna yana yi mata barka da warhaka.
ta katse shi da fad'in
"Har kun dawo daga mai da aljanar in da kuka d'auko ta, ko yaya?
wlh Abubakar ka kiyaye ni in ban da rashin hankali ina kai ina taimakon aljanu,
kai da bakada da wata sari a jikin ka, ko wannan maganin tsari idan nabaka kayi amfani da shi saboda makiya bakayi, bare kayi wa kanka kyakkyawan shiri;
kana nan bakasan da wasu irin mutane kayi huld'a ba, makiya ta ko ta ina sukan iya rab'ar ka, kai har matan da kake aure ba abun yarda bane a wannan zamanin,
amma ka tattara yarda kaf ka d'aurawa Fatima, gashi har ta fara kaika ga halaka,
ai ko matan da suka haifa maka ya'ya Halima da Karima ba zaka tattara yarda duk ka daura a kansu ba,
bare Fatima da bata aje ko d'an hanji agidan nan ba,
shine zaka biye mata ku d'auko aljana har ka lamunce ta shayar da ita,
kaga daga nan sai duk tashige jikin mutanen gidan nan, ayi ta jinya har kud'i ya kare dama abin da takeso kenan,
shi mutum a rayuwarsa baya son ganin wani yaci gaba."
Kai Daddy ya girgiza ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya ai shi kariya yana daga Allah, idan kayi ruko da addu'o'in da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam,
ya koyar babu mutum ko aljanin da zaiyi galaba a kanka,
ko kin mance daga gidan manya Fad'imatu ta fito, wani dukiya ne zai tsole mata ido."
"Eh ai kai a kan Fatima da uban kowa ma zaka ja, tun da ka iya ja da ni,
su sauran da suka fito a tsatson talauci sun fita sau dubu, tun da suka iya haifo min jikoki, tana nan shekara goma da d'ori, ko b'atan wata bata tab'a yi ba."
Kai ya girgiza sannan ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya shifa haihuwa na Allah ne kada muja da ikon Allah."
"To jamin aya tun kan a haifeka nasan wannan."
kai ya kuma girgizawa kana ya ce
"Dama Hajiya nazo ne na sanar miki zaki tafi umura ke da Bishira, daga nan zaku kuwuce Egypt kuga likitan idon ki, gobe da karfe 7 na safe jirkin ku zai tashi,
nasanarwa Bishira zata taho da daddare gobe sai ku wuce."
Hajiya Bishira kanwarsu Daddy ce autar Hajiya ke nan, tana zaune a gidan gadon 'ya'yan ta, mijin ta Allah yamasa rasuwa shekara d'aya daya wuce ya barta da yara biyu,
mace da na miji.
Baki Hajiya ta washe "Kai dama idon nan ya dame ni da kaikayi yanzo ko har ruwa yake idan ya fara kaikayin nan,
ko d'azu sai da nayi ta sosashi kafin naji dad'i."
"Hajiya shifa ido baya son hanu bakiji abin da likita ya fad'a miki ba, idan fa kika matsa da sosashi za'a sami matsala, ana sammanin ya iya rufewa ma."
da sauri ta ce
"A'ah a'ah ai kad'an na sosa ba da yawa ba,
kuma ina sa magani kullum,
ido na bazai makanta ba in Allah yaso, ni dama can ganin likitan muka fara zuwa kafin muje saudin, ai likitocin tacan sunfi kwarewa zasu bani maganin da zai warke da wuri, kai wannan ciwo Allah yaraba bawa da shi."
Gaba d'aya Hajiya ta rud'e, ba karamin razana take a duk sanda taji anyi mata zancen idonta zai iya rufewa ta makanta ta daina gani ba.
tana matukar taoron jin idonta zai iya rufewa bata kaunar makanta a rayuwar ta.
cike da fargaba ta dubi Daddy ta ce
"Amma dai zan warke bazan makanta ba ko!?."
kai Daddy ya gyad'a ya ce
"Insha'allahu zaki warke Hajiya babu abin da zai sami idanunki, amma dai kirika kiyaye wa ki rage sosa idon."
"To-to ai insha'allahu ma na daina da zarar naji kaikayin zan saka masa magani."
Kira ta kwalawa Kulu mai aikin ta
"Ke Kulu d'auko min maganin idon nan nasaka."
"Hajiya a ka'idance ake saka maganin ciwon ido ba ko da wani lokaci ba."
"Ai dai Abubakar yau ma ban saka ba ko sau d'aya, barni kawai nasaka yanzu."
kai ya girgiza ita da ta ce, d'azu ta saka da idon ya dame ta da kaikayi yanzu kuma ta ce bata sakaba, Hajiya ke nan ba'a kaunar abin da zai tab'a lafiyar jiki.
Ya mike yana fad'in
"To Allah ya sauwaka sai ayi miki shiri da wuri, zaku tafi da Kulu dan ku sami mai yi muku d'an wasu aikace-aikacen."
Hajiya kam gaba d'aya hankalin ta ya koma kan maganin da take ta afkawa idon ta, har Daddy ya fita.
Aunty na zaune tana shayar da Feeryal bayan tayi mata wankan yamma, kiran Daddy yashigo wayarta.
da sallama ta d'aga kiran; daga cijin wayar Daddy ya ce
"Ammien Feeryal ba'a bani abincin rana ba har dare ya soma yi."
kai ta dafe tare da fad'in
"Ya subhanallah ayi min afuwa gani nan zuwa insha'allah."
ta sauke wayar ta mike da sauri tare da gyara rukon Feeryal a kafad'ar ta, ta nufi kichin cikin hanzari.
Baba Rabi ta tarar tana ta goge-gogen kichin, Baba Rabi na ganin ta tayi saurin d'an risinawa tana far'in
"Barka da warhaka Hajiya."
"Yauwa barka dai Baba Rabi sannu da aiki, wai me kika dafa ne? gaba d'aya na mance da abincin Alhaji."
"D'aya daga cikin abun da kike so aka dafa Hajiya."
kyakkyawar tukunyar dake kan gas Baba Rabi ta bud'e, wani daddad'an kamshi ya bigi hancinsu.
lafiyayyen jalof d'in shinkafa da macaroni yaji kifi da nama yasha kayan lambu irinsu karas da fis.
Kai Aunty ta girgiza ba laifi girkin ya had'u, Baba Rabi kwararriya ce a fannin girki, tana daga cikin ma'aikatan da suke aikin girki a gidansu. shiyasa da tayi aure ta bukaci mahaifiyarta da ta bata ita su taho tare dan ta yarda da iya girkinta.
amma duk da kwarewar ta a fannin girki, bata lamunce ta girka mata abincin da mijinta zaici ba, ita da kanta take shiga kichin tayi masa girki a duk sanda yake gurinta.
Kai Aunty ta d'an dafe tana tunanin idan fa tace zatayi masa wani girki yanzu lokaci zai kure.
kuma tana da tabbacin baici komai ba tun bayan abincin safe.
da fuskar tausayi Baba Rabi take duban Aunty sanin dalilin da yasata mancewa da lamarin girkin maigidan nata.
sakamakon Hajiya data d'agawa kowa Hankali kan sai an maida Feeryal inda a ka d'auko ta.
cikin muryar tausasawa ta ce
"Kikara hakuri Hajiya."
murmushi Aunty tayi kana ta ce
"D'an rike min ita haka."
ta mika mata Feeryal, ta isa ta d'auki wani kayataccen kula mai matukar kyau da burgewa da ka ganshi kasan ba kirar nan bace, ta zaro wani farin karamin towel da suke a jere a ma'ajin su na musamman.
ta goge kulan ciki da waje, ba wai ko dan ya yi datti ba al'adar ta ce hakan.
sannan ta zuba abincin ta rufe kular.
kana ta d'au plt da cokali da sauran abubuwan da ake bukata wajen cin abinci, tasaka su cikin
Kyakkyawan basket na musamman.
Ta dubi Baba Rabi tana fad'in
"Yauwa bari naje na kai masa, ki kula da ita kafin na dawo."
"To Hajiya." Baba Rabi ta fad'a tana mamakin yau abincin data girka zata kaiwa Alhaji, sai dai taga sauri tattare da ita, wan da shi yahanata tsayuwa girka masa wani abincin.
Sai da Aunty ta koma bedroom ta d'au mayafi kafin ta fita ta nufi sashin Daddy.......!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
🅿️3
Direct bedroom d'in sa ta wuce, a zaune ta taddashi kan wani lafiyayyen dogon kujerar da ke sakiyar katafaren d'akin nasa, mai matukar kyau da tsaruwa.
yana zaune yana duba wasu takardu ya yin da gefe guda yake lasa laptop d'in sa.
gefe da shi ta zauna tana yi masa barka da warhaka, kana ta d'aura da fad'in
"Ayi min afuwa a gafarce ni."
murmushi ya yi sannan ya ce
"Ina Feeryal data kwace min ke?."
itama murmushin ta yi kana ta ce
"Tana gurin Baba Rabi."
kai ya jinjina. ta zubo abincin ta janyo karamin table ta d'aura kai, sannan ta mike ta isa in da fridge ya ke ta bud'e ta ta ciro lemon da yafi so; had'e da kunun ayan da take masa na musamman take aje~ masa cikin fridge in sa, ta dawo ta zuzzuba masa cikin cups.
ta zauna a gefen sa yana ci tana had'a masa kan takardun daya wargaza su.
"Insha'allah ko mai yazo karshe na shiryawa Hajiya tafiya umura gobe, daga nan zasu wuce Egypt taga likitan ido, zasu zauna a gida na dake can nad'an wani lokaci kafin su dawo, insha'allah daga nan komai zai dai-dai ta."
duban sa Aunty ta yi tare da sauke numfashi ta ce
"Allah ya sa."
"Amin amin." Daddy ya fad'a yana kurb'an kunun ayanta mai sashi santi.
yana ci tana d'an janshi da hira cikin sigar jan hankali ta in da zai ci abincin sosai.
Yana kammalawa ta had'a kan kayakin cikin basket.
ya ce taje ta tuba Feeryal kada ta yi kuka, sukayi sallama ta fito, dan yau ce ranar da zai bar d'akinta.
shiyasa ma ya dawo side d'insa.
dan idan itace da kwana sashinta yake tarkasawa ya koma, har sai ya yi mata kwana biyun kafin yadawo side d'in sa da yamma.
sauran
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 20