ta girgiza kai ta wuce babban kichin gurin masu aiki.
Karatu sosai FEERYAL ake yanzu babu zama anata kokarin barin secondary, ba ita ba ga duk wanda yake ajin karshe a secondary School anata shirin ban kwana.
ranar da zasu bar makaranta, kwarya-kwaryar biki akayi na musamman dan makarantar yawancin na 'ya'yan masu hannu da shuni ne.
iyayen d'alibai sun nuna bajinta, a ranar kuwa wad'an da suka bayyana soyayyarsu ga FEERYAL suna da tarin yawa,
ciki kuwa harda malamansu da ba'in da suka zo domin tayasu murna har da ma iyayen wasu d'aliban.
sai dai babu wanda ta saurara cikin su.
ya yin da malamai suka sallami d'alibai cikin karramawa.
bayan anyi ciye-ciye da shaye-shaye dasu d'aukar hotuna.
ko wani d'alibi ya kama gaban sa.
Bayan an dawo gida kuwa liyafar cin abinci Abba ya shirya duk saboda murnar zuwan wannan rana.
aka sallami mutane da kyaututtuka na musamman mai d'auke da hoton FEERYAL ajin ko wace gifts.
Bayan kwana uku
FEERYAL da Maryam suka tafi gidan Aunty Zainab, sai yamma suka baro gidan.
FEERYAL ce ke jan motar, da sauri ta taka burki sakamakon shan gabansu da wata mota tayi.
ta dafe kirji jikin ta na b'ari, dan batayi aune ba taga motar a gaban ta.
cike da jin haushi Maryam ta ce
"Amma wannan anyi mara lissafi so yake ya jaza mana fitina."
ta kalli FEERYAL ganin yadda gaba d'aya jikinta ya d'au b'ari, ta fashe da dariya.
"Ke kam anyi babban matsoraciya anan, sai kace munyi karo, da'alla dawo nan na jamu dan wannan tsoron naki zaki iya jefar damu anjima."
Tun kan ta karasa fad'a da sauri FEERYAL ta b'alle marfin motar ta fito,
dan a yadda ta tsoratan nan bazata iya driving d'in ba ma.
yana ganin fitowarsu ya zoge glass d'in motar sa.
idanunsa a kan FEERYAL.
Maryam ta hararesa tana fad'in
"Wannan wani irin hauka ne sai kace baka gani, zakazo ka sha gabanmu da moto, idan baka son taka rayuwar mu muna son tamu."
FEERYAL kam bata iya cewa komai ta zaga ta shige
gefen da Maryam ta fita.
Gyara zaman gilashin fuskarsa ya yi sannan ya yi sama da gilashin motar,
yaja motar batare da ya ce komai ba.
Maryam tayi tsaki ta shige mazaunin direba, taja suka tafi.
Da misalin karfe 1 da rabi na dare.
Maryam na kwance like da waya a kunnen ta, tana wa da inspector Nasir Bama, expecto na 'yan sanda,
shine mijin da zata aura.
Nasir ya ce
"Wai ni ina FEERYAL ne tun da muka fara wayar nan banji d'uriyar ta ba?."
"Um gata nan ta dukunkune cikin blanket, tana kan sharar bacci,
yau da wuri tayi bacci ma."
"Allah sarki, ki gaishe ta idan ta tashi gobe,
ga aboki na kamar zaiyi hauka a kanta, Maryam bazaki tayamu fadanci ba, wlh Major Sadam yana son ta da gaske kuma ya shirya auren ta,
shikaran jiya dana zo nayi mata magana kansa amma bata ce ko mai ba,
Please Maryam kisa mana baki."
"Nasir wai kuna yi wa FEERYAL kallon wata babba dudu 15 yeah gare ta, in zaka shekara kana mata magana kan wani na son ta bazata ce maka komai ba,
FEERYAL ba irin sauran yaran da ka sani ba ne,
a yanzu yarinya mai shekarun ta tasan ciki da wajen soyayya,
amma ban da FEERYAL har yanzu da sauran ta,
so duk wan da ya biyo ta hannu na kan yana son ta, bana matsa mata kan dole sai ta so shi,
sa boda har yanzu bata da wayon yin soyayya,
bana son kuma na tauye mata hakkin ta,
nafi so da kanta taji tana so, ba tare da an matsalta mata ba,
bare kuma yanzu ne ma zata fara karatu, ai da sauran ta tukun, duk suyi hakuri, su jira."
"To mun aje kokon baranmu a layi kar kuma a zo a wuce kanmu."
Tana shirin bashi amsa taji kamar ana magana sama-sama.
shiru tayi tare da kasa kunne tana jiyo maganar can kasa.
da sauri ta zabura tamike, da sauri ta masa jikin window ta zuge labule ta leka.
kirji ta dafe da karfi ta ce
"Mun shiga uku!."
Nasir da keta magana tun d'azu bata bashi amsa ba ya ce
"Yaya dai lafiya Maryam me ya faru?."
"Nasir kamar b'arayi ne suka shigo mana gida, ga mutane a bakin get da bindigogi kuma ina jin magana a parlour, da muryar su Abba."
da sauri Nasir ya ce
"B'arayi kuma anya kuwa Maryam ko dai ma'aikata kika gansu, kinfa san yanzu dare tayi biyu saura yanzu."
Tass karar harbi yasashi had'iye ragowar maganar sa, Maryam ta saki kara tana toshe bakin ta.
A parlour kuwa Abba da Hajja Umma ne shinfid'e a kasan carpet in da b'ayin suka sasu kwanciya plat hannayen su a bayan ke yarsu.
d'aya daga cikin b'arayin da yake hakimce a kan kujera, ya d'aura kafa d'aya kan d'aya yana busa sigari.
ga dukkan alamu dai shine babban su ya ce
"Ku shiga ku fito da sauran mutanen akwai saura a ciki."
da sauri Abba ya ce
"Ku kyale su dan Allah ko ma meye mu kare da ku anan,
in dai kud'i ne akwai ko nawa kuke so zan baku,
wad'ancan yara ne dan Allah ku rabu da su.
Bakin bindiga ogan nasu ya d'aura masa a kai ya ce
"To ai d'aukar amarya muka zo, idan muka tsaya daga nan me mukayi ke na, ku tsaya a nan ku zaku mana rakiya."
ido Abba ya rumtse da karfi jin yadda yake dannan bakin bindigar a kansa da karfi.
A razane Maryam ta sake wayar ya fad'i kasa jin an banko kofa.
jiki na rawa tashiga ja da baya.
su biyu suka shigo d'akin, dukkanin su rike da manyan bindiga.
d'aya ya yi kan FEERYAL dake bacci ya fisge blanket d'in da take dukunkune ciki, ya fizgota kasa ya dire ta kan kafafun ta.
kara ta sake a gigice san da ta ware idanunta masu d'auke da bacci a kan su,
tuni ta nimi baccin ta rasa, tuni jikin ta ya d'auki kyarma.
gashin kanta ya rike ya turo ta waje, d'ayan ma ya janyo Maryam.
suna zuwa tsakiyar parlour'n ya angiza ta ta zube kasa.
kara ta sake tana rike kafarta data fad'i a kai.
kallo d'aya Maryam tayi masa ta gane shi, shine wan da yasha gaban su d'azu da yamma a hanya har Feeryal ta razana da tukin ita ta dawo da su gida.
Ogan b'arayin ya mike da sauri ya sunkuyo gabanta tare da rike kafar da take rike da shi,
wan da tuni hawaye yashiga zarya kan kyakkyawar fuskarta.
yad'aga kai ya dubi wan da ya wurgotan ya ce
"Kai baka da hankali, idan ka b'alla kafar amaryar da wani kafa zata tafi ke nan,
wannan kyakkyawan furen a hankali zakayi mata karta tsinke."
ya saka yatsarsa a kan fuskar ta ya lakato hawayen ta ya ce
"Wayyo Allah me yasa ka firgitata baka taso ta cikin ruwan sanyi ba,
da nasan bazaku iya ba da da kaina naje, na taso ta,
yi shiru lu'u-lu'u ki dai na kuka."
sai kuma ya yi zaman dirshem
ya nad'e kafafun sa a gabanta yasa annu biyu ya dafe kumatun sa yana kallon fuskarta,
sai kuma da sauri ya........!
Mommyn Twins ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Littafin na kud'i ne 500 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️18
Ya mike tsaye tare da ruko hannunta ya mikar da ita tsaye.
ya dubi 'ya'yan gidan sa ya ce
"Mujen ku maza kada a b'ata lokaci."
da sauri Abba ya mike ganin yaja FEERYAL suna kokarin tafiya da ita.
ya rarrafo fisa gwuiwar sa ya na fad'in
"Ku dakata dan Allah idan ba kud'i kuka zo d'auka ba, garkuwa da wani kukazo yi, to dan Allah ku aje ta ku d'auki wani a cikin mu, ku d'auke ni ni kaina ma,
ko ku tsaya muyi ciniki na fanshi kaina ko nawa ne ma, bama sai kun sha wahalar tafiya da ni ba."
wani ya kai masa naushe da kafa.
"D'aukar amarya mukazo waya fad'a maka kidnapping muka zo yi."
babban nasu ya juyo yana fad'in
"Kai kai kyale shi bishi a sannu kasan mu mukazo nima a gurin shi, na mance ne ban mishi bayani ba."
ya jawo FEERYAL ya dawo da ita ta gab'anshi ya rungume ta ta baya, ya saka hannunsa guda yana shafa tun daga saman kafad'ar ta zuwa yatsun hannunta.
Abba ya rumtse ido da karfi yana jin kuna cikin ransa, da irin cin fuskar da ba'ayin nan suke yi musu.
FEERYAL ko kuka take wui-wui tana mutsu-mutsu cikin hannunsa.
ya ce
"Ku bashi sadaki ku fad'a masa bazan zauna da ita haka kawai ba sai nasa an d'aura mana aure."
yana kaiwa nan ya cirota a jikinsa ya janyo ta ya yi waje da ita.
Abba da hankalin sa ya yi mummunar tashi ya mike a haukace ya na cewa
"Kayi wa Allah da Manzonsa kada ka aikata haka, wlh yarinyar nan amana ce a guri na, dan Allah ka dawo da ita ko nawa kake bukata zan baka, ka taimake ni kaji tausayin marainiya ka dawo da ita, ni ku tafi da ni."
Ko juyo wa baiyi ba ya ciccib'i FEERYAL data keta tirjewa tana mikawa su Abba hannu su taimake ta,
ya rataya ta a kafad'a ya fice da ita.
Abba ya mike zaibi bayansu yana had'asu da girman Allah su dawo da ita shi su d'auke shi.
wanda babban nasu ya ce ya bada sadakin, ya wurgawa Abba jakar kud'i ya ce
"Ka d'auki wannan miliyan goma ne a ciki, sadakin ta kenan,
ka godewa Allah 'yarku tayi goshi da har aka baku sadakin ta, dan oga baya bada sadakin duk wacce yaje d'auka, itace mace ta farko cikin mata sittin da biyar da oga ya d'auko ya bada sadaki a kanta,
kuma ya yi ikirarin zai je a d'aura musu aure da ita, ba zama haka kawai zaiyi da ita ba,
to ai kai ka godewa Allah kun haifo mai kima a gun oga,
rike kud'in nan kai dai zai tare ma wani abun,
mujenku-mujenku."
yad'agawa 'yan'uwansa hannu suka bi bayan ogan nasu da gudu.
Hajja Umma da Maryam suka saka hannu a kai suka kurma kururu, wan da ake kira da kururuwa bayan hari dan ba mai jinsu.
Abba kuwa zaman dirshem ya yi a kasa yana ambaton sunan Allah yakawo musu agaji.
A waje kuwa b'arayin nan suka shige motocin su,
wan da tuni ogan nasu ya shige nashi motar,
suna gidan baya yana rungume da FEERYAL da take ta zabga kuka.
suka ja motocin su da mugun gudu suna harbi, babu kuma wan da ya isa ya yi gigin tinkararsu.
A b'angaren Inspector Nasir kuwa, yana jiyo maganganun b'arayin nan a ta wayar Maryam daya ke yashe a kasa,
kafin su fita daga d'akin.
da sauri ya mike ya sauko a kan gadon da yake kwance.
cikin gaggawa ya kira wayan office d'in su na 'yan sanda.
ya bada umurnin gaggawa mota uku na 'yan sanda suka fito cikin shiri.
nan da nan yakuma kiran Armay barrack ya kira number major Sadam ya sanar masa da abin da yake faruwa.
batare da b'ata lokaci ba major Sadam ya taso da tawagar sa.
FEERYAL a motar b'arayi, tsoro kamar ta haye ranta yakuma rungume ta tsam yana jin sa cikin nishad'i, sai shafa bayan ta yake yana fad'in
"Kar ki sa min kanki ya yi ciwo, ki b'ata mana daren amarcin mu, kiyi shiru da wannan kukan haka,
ke ce mace ta farko dana tab'a lallab'ata duk wacce nad'auka ta kawo min wargi bugun ta nake ko da ina kanta ne kuwa,
kinga ke jikin ki ba irin nasu bane, idan na sa miki hanu bazaki ganu ba,
kiyi shiru kawai mu isa mu more."
Ido FEERYAL ta rumtse tana jin kirjinta na wani irin bugawa, numfashin ta yana wani irin sama-sama, ya yin da kanta ke tsananin sara mata.
tsoro mai tsanani yana dad'a baibaye ta.
Da karfi mator gaban su ya taka burki, kad'an yarage suyi karo da juna.
da sauri ogan b'arayin ya d'ago dan ganin me ke faruwa.
wanda ke jan motar nasu ya ce
"Ogo kalli can ka gani, kamar ba hanyar da muka shigo muka biyo ba."
cikin tsawa ya ce
"Hanyar ce mana dalla ku hanzarta mu tafi ba lokaci."
da sauri direbar d'aya motar gaban nasu ya sauko yazo ya bud'e gefen da ogan nasu ya ke ya leko yana fad'in
"Oga ba hanya fa ta nan, ina ga mun b'ata hanyar ce sai dai mu juya."
"Maza koma mota mu juya da sauri."
"To oga."
ya rufe motar ya juya da sauri yakoma d'aya motar suka juya a d'ari.
sunyi tafiyar 5min a razane suka kuma jan burki sakamakon ganin wani irin haske mai tsananin k'aifin haske daya haske musu ido.
nan take kuma wasu nau'ukan tsuntsaye masu girman gaske suka bayyan ta cikin hasken,
suna shawagi ta cikin haskennan suna karkad'a fukafukan su.
ya yin da kukan su ya karad'e cikin kunnuwan su, tamkar zasu fasa musu dodon kunnuwa.
A kid'ime ya ture FEERYAL daga jikinsa,
ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa, da dodon kunnuwan nasa suke barazanar zazzagowa waje.
yakuma rumtse idanunsa da yake jin tamkar hasken nan zai fasa masa kwayar idanunwa.
ba shiri ya b'alle murfin motar ya fito yana layi da tangad'i cikin tsananin jin azabar da kunnuwansa da idanuwansa suke masa tamkar zasu zazzago su fad'o kasa
A b'angaren 'ya'yan gidan nasa ma, duk kanin su sun fito daga cikin motocin, kowa da ido a rufe kunne a toshe da ala ma dai irin abin da ogan nasu yake ji shi sukeji suma.
FEERYAL na cikin mota a rakub'e sai b'ari da kuka take, bata ma san abinda ke faruwa ba, zaton ta ma sun iso in da zasu kawo ta ne.
Tawagar Major Sadam dana Inspector Nasir a kusan tare suka iso.
jiniyar polisawa da na sojoji ya karad'e cikin unguwar.
san da motocin jami'an ya karyo kwanar layin,
kamar kiftawar ido haske da karar tsuntsayen nan suka b'ace cikin dakika d'aya, b'arayin nan suka nimi abin da suke ji cikin kinnuwansu da idanunsu suka rasa.
hanya ta bud'e samb'al suke hango hanyar ficewa daga unguwar.
da sauri cikin azama ko wannensu ya shige cikin mota, suna kokarin gudu.
jiyo jiniyar hukuma na dumfaro su.
sai dai kafin suyi aune hukuma ta cin musu.
Daga can jami'an tsoro suka soma magana da amsa kuwa.
"Ku dakata a gurin ku aje makaman ku, mun cinmuku muna zagaye da ku."
Da karfi ogan b'arayin ya naushi jikin sit d'in mota yana fad'in
"Oh sheet! maza wuta!."
duk kanin su suka d'auki bindigogin su, suna fita daga motocin suka soma harbi.
tuni jami'an tsaro suka soma musanyar wuta da su.
tuni unguwar ta karad'e da karar harbi kamar za'a tashi unguwar da b'arin wuta tamkar ana diyafara.
mutanen unguwa kuwa kowa ya yi flat a cikin gidan sa yana jiran ta Allah ta kasance.
B'arayin nan basu sakaita wutaba har sai da bulet d'in su ya kare.
inda jami'an tsaro suka sami nasarar harbin mutum biyar a cikin su, ciki kuwa har da ogon nasu da aka harba a kafa,
sauran suna kokarin gudu aka kamasu da hannu.
mutum uku a ka harba acikin jami'an tsaron, biyu police d'aya soja.
Da gudu Major Sadam ya nufi gurin motocin b'arayin yana b'alle makarin bulet d'in dake jikinsa, ya yi wurgi dashi kasa, dai-dai san da yake karasowa jikin motocin, yana haska cikin su da touch d'in wayarsa.
da sauri ya kai hannu ya bud'e marfin motar da ya hango FEERYAL a ciki.
ta tafi gaba d'a zata fad'o kasa,
dan ajikin murfin motar tage rakub'e.
tun lokacin da aka fara harbi na farko ta suma.
cikin hanzari ya tarota ta fad'o jikinsa, ya d'agota cak ya rataya ta a kafad'ar sa.
dai-dai lokacin da inspector Nasir yake karasowa gurin hankali a mugun tashe ya ke fad'in
"Ya dai Sadam badai harbin ta akayi ba?."
"No! harbi bai same ta ba, sai dai she painted, firgici yasa ta suma, muyi sauri mu kaita asibiti dan Allah Nasir, wani asibiti za'a samu yanzu."
cikin hanzari ya nufi d'aya daga cikin motocin su,
inspector Nasir yabi bayansa yana cewa
"Za'a samu general hospital ma, sai dai matsalar ba lallai ne a sami likitocin su ba,
a kwai wani asibiti a d'an gangaren J.Y.P d'in nan.
asibitin wani babban likita ne da yake aiki a kasar waje, yawancin lititocin da suke aiki a asibitin gidajen su yana kusa da asibitin, har da shi kansa me asibitin ma gidan sa na kusa a gurin,
sai dai ba lallai ne mu same shi ba dan bana da tabbacin yana kasar, amma ko sauran muka samu ina da yakinin zasu fito dan suna da kokari sosai kan majinyata."
"Muje can d'in please Nasir yi sauri dan Allah bata numfashi."
ya bud'e mota ya shinfid'a ta a gidan baya.
dukan su suka bada umurni wa tawagar su, su kwashe b'arayin su tafi da su.
Major Sadam yaja motar da kansa batare da ya bukaci wani jami'in sa ba, inspector Nasir na gefen sa suka nufi hospital d'in.
Suna isa kofar katon asibitin ya yi hon, mai gadi ya leko, ganin soja da police a gaban mota,
da sauri ya wangale musu get.
suka shige harabar asibitin, ya gyara parking suka fito.
da sauri Sadam ya bud'e inda take ya ciccib'ota, sukayi cikin asibitin.
Cikin hanzari ma'aikatan asibitin suka nufo inda suke da welcher.
Sadam ya ce "Not ina za'a shiga da ita?."
da sauri wani nurse ya yi gaba ya tura kofar ICU yana fad'in
"A shigo da ita nan."
Sadam ya shinfid'a ta kan bed yana cewa
"Ina likitocin ku suke?."
nurse d'in ya ce
"Tun 6 suka tashi, yanzu nan kuwa bada jimawa ba Dr A.A FIYA ya bar nan ya yi wa wata me ciki C'S ko 30min baiyi da barin nan ba,
amma gaskiya da kyar ya dawo sabo da yau ya shigo kasar, ya shigo asibitin ne kawai ya taras da ita cikin wani hali shiyasa ma ya tsaya har ya mata C'S d'in."
Da sauri Major Sadam ya ce
"Kirashi dan Allah ita ma wannan baka ganta cikin wali hali ba, yazo ya ceci rayuwar ta pls!."
Shiru nurse d'in ya yi yana tunanin ta in da zai fara tuntub'ar Likitan nasu,
ta ina zai fara gashi a gaban soja yakuma umurceshi, wanda aka umurta da ya kira shi d'in ma
a gefe guda shima sojan kansa ne.
bayan keyar sa ya d'an sosa ya ce
"Zaizo kuwa? adai kira wani Dr dai."
tsawa Sadam ya buga masa ya ce
"Kana kallonta a sume ka tsaya kana wani kame-kame,
shi wanda bai jima da barin nan ba shi yakamata ya dawo ya duba ta, sauran da duk yanzu sun jima da yin bacci ta ina zasu iya kulawa da ita yadda ya kamata, ka kirashi yanzun nan!."
Hannu na rawa yashiga lalub'o lambar Dr A.A FIYA. har kiran ya yanke bai d'aga ba.
Sadam yana tsaye yana ji dan wayar a handsfree ya saka, ya ce yakuma kiransa.
sau uku yana kira ba'a d'agawa sai ana hud'u tukun ya d'aga bai yi magana ba.
ganin ya d'aga ya yi shiru da sauri shi nurse d'in ya fara magana.
dan yasan halinsa idan zasu kwana a haka shi ba zai fara yin magana ba,
sai dai ya aje wayar idan ya gaji, kai da ka kirashi kai kasan sauran da kud'in ka,
ko ya kashe watar.
"I'm sorry Sir an kawo patient emergency."
tsaki ya ja tare da kashe wayar ya jefata gefe ya gyara kwanciyar sa, ya mai da kansa pillow.
Major Sadam ya ce "Ka sake kiran sa maza yasan wa yake wa tsaki anan kuwa!."
jiki na b'ari ya mai da kiran shikam yau tashi ta same shi wuta biyu ta gefe da gefe suke kokarin amsawa da shi.
nan ma wayar ta yanke bai d'aga ba, yakuma mai da kiran a karo na biyu har ya kusa yankewa ya d'aga.
da sauri Sadam ya karb'i wayar ganin ya d'aga ya ce
"Kana magana da Major Sadam Wakili, patient tana bukatar taimako kazo ka duba ta."
"I'm Doctor Abdurrahim A.A FIYA, yanzu lokacin bacci na ne."
d'inp ya kashe wayar gaba d'aya ya jefata gafe yakuma gyara kwanciyar sa.
A fusace Sadam yashiga kokarin kuma mai da kiran sai jin sa ya yi a kashe.
"Amma d'an ji da kan nan bai san da wa ma yake magana ba, zan nuna mashi ko wane ne ni!."
Inspector Nasir ya yi murmushi tare da bubbuga kafad'ar sa ya ce
"Yanzu ba wannan ne a gaban mu ba, damuwar mu ta farfad'o ta sami lafiya ne."
ya dubi nurse d'in ya ce
"Gidan sa nan kusa ne ba? taho muje ka raka ni."
Sadam ya ce
"Wai gurin sa zakaje shi zai zo da kafarsa har barrack ya same ni, zan punishment nashi,
mu d'au keta mu tafi wani asibitin."
kai Nasir ya girgiza yana murmushi ya ce
"D'an'sandan ke nan abokin kowa, zanje na d'auko shi, kasan kowa sarki ne a fannin aikin sa,
yanzu idan aka barmu da ita bamusan ya zamuyi da ita ba, saboda ba aikin mu bane,
a wannan fannin dole mu zamu bisa aikin sa ne,
yanzu idan mukace zamu d'agata a nan kafin mu isa wani asibitin ai zamu b'a lokaci, kuma tana bukatan taimakon gaggawa."
da sauri Inspector Nasir ya fita nurse d'in yabi bayan sa.
Babu nisa sakanin gidan nasa da asibiti, titi ne ta rabasu, gidan na kallon asibitin.
suka sallaka suka isa bakin get d'in gidan.
Nasir ya kwankwasa, mai gadi da ke gyangyad'i kan kujera ya zabura da sauri ya mike, ya leko ta mahangarsa dake jikin get d'in.
ya hango police da ma'aikacin asibitin mai gidan sa.
ya bud'e karamar kofa yana rarraba ido da son jin ba'asin abin da ya kawo su tsohon daren nan.
Inspector Nasir ya ce
"Sannun ka da aiki, mun zo gurin mai gidan ne."
ido mai gadi ya gwalalo ya ce
"Yallab'oi Allah dai yasa lafiya, wlh shi kam ma yau ya shigo kasarnan yana can kasan turawa,
yana rayuwar shi babu ruwan shi da kowa."
"Bamu hanya dai yanzu mu wuce."
da sauri mai gadi ya matsa gefe.
suka shigo ciki Nasir ya dubi mai gadin yana fad'in
"Kayi mana sallama da shi yanzu dan Allah."
mai gadi ya isa da sauri jikin garun d'akin sa, in da wayar tafi da gidan ka take sakale a gurin.
ya daddanna ya kara a kunnen sa.
Aci kuwa nan take wayar ta soma kara ta karad'e cikin parlour.
yana kwance idanunsa a lumshe da sauri ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa,
"Ya salam."
ya furta yana mikewa zaune.
kai ya dafe da hannunsa biyu, jin yadda kiran yake kuma shigowa babu kakkautawa.
ya mike a fusace ya fito parlour.
ya fincike wayar ya kai sa kunne cikin tsawa ya ce
"Kai wani irin hauka ne wannan zaka cika min kunne da kira!."
mai gadi ya durkusa kaman yana gaban sa ya ce
"Allah baka hakuri oga hankali na ne a tashe ganin police a tsohon daren nan wai yazo niman ka."
tsaki yaja ya saki wayar Allah ya kare bata isa kasa ba da sai dai wata ba dai ita ba,tana ririto ajikin igiyar ta.
Kugu ya rike tare da furzar da huci mai zafi daga bakin sa.
ya yi da na sanin zuwa kasar shi da ya gudo domin ya huta ashe wata musifar aikin zai kuma gamuwa da shi a nan.
a hankali ya ke takawa yana mammatse idanunsa da bacci yake cike tam a cikin su,
Allah ya sani ba karamin bacci yake ji ba.
ya isa in da takalman takawan cikin parlour'n suke ya zura d'aya a kafarsa ya fito da gajeren wandon jikin sa da singileti.
yana aikin jan tsaki fuskarsa a had'e kamar tun da yake bai tab'a dariya ba.
tun kan ya karaso in da suke Nasir yashiga takowa gare sa shima suka had'e a tsakiya.
I'd d'in sa ya ciro a aljuhu ya nuna masa yana fad'in
"Inspector Nasir B Suleja, barka da dare Dr Abdurrahim A.A FIYA."
Nasir ya mika masa hannu, da kyar ya miko masa nasa hannun suka gaisa.
Nasir ya gyara tsayuwar sa ya ce
"Nasan baka sanni ba, nima dai bana ce nasan ka a ido ba, amma ina jin sunan ka,
akwai kuma kyakkyawar alaka sakanin Alhajin ka da hukumar mu."
fuska ya dad'a had'ewa dan ya kosa da jin bayanan sa, katse Nasir ya yi da fad'in
"I'm okay me ya kawo nan?."
Nasir ya yi murmushi ya ce
"Dole zan sanar maka abin da ya kawo mu ai bayan gabatarwa,
kayi hakuri mun katse maka baccin ka,
dole ne yasa hakan, muma bamu samu mun rumtse ba cikin daren nan,
aikin mu da naka yana kamancece niya so dole bacci zai zamo mana short saboda taimakon al'ummar mu,
muna tafe da patient tana asibitin ka, amatsayin mu na jami'an tsaro mun sami nasarar kwato ta daga hannun 'yan tadaddan da suka saceta suke kokarin guduwa da ita,
mu munyi aikin mu saura naka,
kai kuma a matsayin ka na likita yanzu sauran aikin naka ne, tana bukatar taimako dan Allah
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 20