Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nake so, abokin mu ne zaiyi aure yau, ina kuma niman izini ba a garin nan za'ayi bikin ba, zamuje mu kwana d'aya gobe zamu dawo." Daddy ya ce "Nawa ne kake bukata?." kai ya d'an sosa sannan ya ce "2 million ne Daddy." Daddy ya d'aga ido ya kalle shi kana ya ce "1 million za'a baka sai ka lallab'a, ka koyi yadda ake maneji." Faisal ya zubawa Zaraddin ido da mamakin karyar da ya sharara yanzu, wanda yana jin sa sanda ya fito zai zo gurin Daddy yazo zai wuce ta kofar bedroom d'in sa yaji yana waya, yana sanarwa wani abokin sa yau da karfe 12 na dare akwai birthday party na girl friend d'in su. "Wato acan zaije ya kwana ke nan." ya girgiza kai Maganar Daddy ne yasashi maida hankali gurin sa "Ku me ke tafe da ku?." Ajeemal yad'an gyara zama sannan ya ce "Daddy muna so ka cika mana kud'i ne mu siyi sabon computer, muna son mu samu babban namu saboda yanayin karatun mu." Daddy ya jinjina kai ya ce "Nawa ne cikon kud'in naku?." Shamsuddin ya ce "2-2 millons ne kud'in computer amma 1 million muke so a cika mana." Faisal ya karb'i batun da cewa "Mun samu irin wanda muke so a Germany zamuyi odar sa can." "To madalla hakan abune me kyau." Daddy ya fad'a yana d'aukar d'aya daga cikin wayoyin sa. Ya yi wa ko wannensu transfer d'in million d'aya da rabi. sannan ya dube su yana fad'in "Miliyan d'aya da rabi-rabi na sa muku sai ku aje 500k ko wata bukatar zata taso muku, kai Zaraddin sai kayi hidimar bikin da zakuyi, amma kai banji kace zaka sayi computer ba, ko kana da ita ne?." Gefen kansa ya sosa ya ce "Am eh.eh..idan na dawo ne zan yi maganar ni ma." "To shike nan sai ku tashi kuje Allah ya yi jagora, amma Shamsuddin Ajeemal Faisal wazai yi muku odar daga can bazakuyi wa d'an'uwanku magana, tun da yana can, ya sako muku a jirgi ba, ko kun yarda da wanda zakuyi harkar da shi ne?." Ajeemal ya ce "Daddy shine ma zamu tura masa, munyi magana da shi ne kan muna son sabon computer shine ya ce, mu turo da rabin kud'i sai ya cika ya siya mana." Daddy ya ce "Inji sa ya ce sai kun bada rabin kud'i kafin ya siya muku abu? to duk ku maido min da kud'i na kuce masa nace ko sisi bazaku bada ba shi zai siya muku da kud'in sa, ya baku sana'ar yi ne da zaku sami kud'i da har zaice ku bada rabin kud'i? a ina zaku sami kud'in kuna 'yan makaranta yabari idan kuka gama karatu kuka kama aiki shine zaiyi wannan maganar, maza-maza kuce dashi na ce ko sisi bazaku bashi ba shi zai saya muku da kud'in sa." Duk suka zaro wayoyin su suna kokarin maida masa kud'in da ya tura musu. ya ce "Ku bar shi ku adana idan kuna da bukatar wani abin sai kuyi da shi, kada ku kuskura ku tura masa ko sisi cikin kud'in nan." suka amsa da to sukayi masa godiya suka mike suka fito. Suna fita Faisal ya dubi Zaraddin da yayi kicin-kicin da fuska, yana harararsu ya ce "Yanzu kayiwa Daddy irin wannan karyar alhalin party zakaje kace zakayi tafiya, ina jin kafa d'azu kana waya zakuje birthday party 12 na dare." baki Shamsuddin ya bud'e ya rike hab'a ya ce "Kasan da wannan Faisal shine kana ji ya yi wa Daddy karya, ya ce zaije bikin abokin sa, ashe party zaije ya kwana a can, to wlh sai na fad'awa Daddy tun da har abun naka yakai ka fara kwana a Club." ya juya zai koma parlour'n Daddy. Ajeemal ya ruko sa yana fad'in "Rabu da shi karma kaje ka barshi yaci gaba tun da hakan ya zab'ar wa kansa." "Munafukan banza, je ka fad'a mana, in banda tsabar bakin ciki za'a bani 2 million, kuka wani kwaso kafa kuka zo wai kuma a baku, kuka sa a ka rage kud'in da za'a bani, munafurcin banza kawai bansan me na tsare muku ba kuka bi kuka samin ido, tun da Dad da Abbieh suna gida zan sami cikon miliyan d'ayan da kuka yi bakin cikin acika min, 'yan sa ido kawai." Ya juya ya wuce. Ajeemal ya ce "Mujen ku kurabu da shi dan Allah Allah ya bashi sa'a." Su Ajeemal suna fita Daddy ya gyara zaman shi bayan ya tura kira a wayarsa. har kiran nashirin yankewa kafin aka d'aga. Daddy ya amsa sallama had'e da gaisuwar da yake masa, sannan ya d'aura da fad'in "Ya aikin dan naga alama aiki na shirin ya fimu a gurin ka, yanzu sai kayi kwana hud'u biyar sati baka neme mu ba, mu in mun neme ka ma sai munyi da gaske muke samin ka, yanzu ma har na cire rai da samin ka, watakila kana gidane yanzun ma yasa na same ka akan lokaci." daga cikin wayar ya ce "Kayi hakuri Daddy yanayin aikin namu ne, kwana biyun nan ina yawan shiga CS ne shiyasa bana samin time d'in d'aukar wayar, ya cikin gidan duk kuna lafiya?." Daddy ya ce "Kowa lafiya, kaifa kana lafiya?." d'an gajeren tsaki ya sake cikin yanayin gajiya da kosawa ya ce "Daddy bana samin bacci kwana biyu, kusan a tsaye nake kwana, majinyatan Israel yawancin nan ake shigowa da su, I'm busy this moment, nagaji kaina yana yawan ciwo, I will go back to Nigeria very soon, in ba haka ba zan iya samin bp." Murmushi Daddy ya yi yasan shi sarai baya son damuwa da yawa, shi yasa ma tun farko yaki aikin likitanci sai da Daddy'n ya matsa masa sosai, dan shi ya taso da burin gadar kakan sa Alhaji Shitu Fiya da kuma shi kansa Daddy'n, wato harkar noma yafi bukata. duk da Daddy'n yahanashi sai da ya sami digiri a harkar noma, bayan ya kammala karatun likitancinsa. Daddy ya ce "Haka kake cewa last year ma haka kace min zaka dawo amma baka dawo ba, ya kamata ka dawo gida Nigeria dan kasarmu ma tana da bukatar ka, duk d'inbin kud'in da suke biyan ka a can, ko da kasarka bata biyaka rabin sa ba, yafi ka zauna a can kana musu aiki kadawo ka ceci al'ummar kasarka." "Daddy ni fa aje aikin zanyi gaba d'aya, nagaji da shi, zan dawo gida na huta." "A'a bazaka aje aiki ba, aikin lada ai ba'a gajiya da shi, yanzu kasan ladan da kake samu na ceton rayukan da kake, ko iya musulman Israel d'in da ka ceta ai lada me yawa ka samu, duk da gwamnatin kasar ce ke biyan ka ai kana samin lada, dan wannan aikin Allah ne kad'ai ke iya biyan bawa bawai kud'in da ake biyan sa ba." "Hmm." kawai ya ce dan shi fa aikin ne baya so, baya son hayani ko kad'an. Daddy ya ce "Dr Omar, High Doctor of General Hospital, ya kirani da kansa ranar, jiya ma yasake kirana yana min tuni, mai girma gwamnan jihar nan Lagos ya tambaye ka da kansa, ana bukatar ka a kasarka a jihar nan, me yasa bazaka dawo ka koma bakin aikin kaba, ga asibitocin ka ma kana ganin ma'aikatan ciki sun wadatar, ka sa rana ka tattaro ka dawo kasar ka." Shiru ya yi batare da yakuma cewa komai ba. Daddy ya ce "D'azu su Ajeemal suka zomin da batun wai ka ce su kawo kud'i ka cika musu ka siya musu computer, to nace kar su tura ma ko sisi, ka siya musu da kud'in ka, suna sana'a ne da zasu sami kud'i." "Daddy ai na ce musu surika zuwa d'aya daga cikin Company duk ranar weekend's, na tambaye su suka ce min suna zuwa suma sun fara karb'ar salari, ina son sanin hazakarsu ne yasa nace su kawo kud'in." Daddy ya ce "Sun ce zasu fara zuwa ni na hanasu zuwa na ce su nutsu da hankalin su da karatu tukun, har su kammala." Kai ya jinjina sannan ya ce "To shike nan Daddy saura 10 minute na shiga CS idan na fito zamuyi waya." "To Allah ya bada sa'a." sukayi salla ya kashe wayar duka ya turashi gefe. ahankali ya maida bayan sa jikin lafiyayyen kujerar office d'in sa, ya lumsahe idanun sa, masu d'auke da gashin ido zara-zara luf-luf kamar an zizara masa. Kyakkyawa ne dogo mai murd'ad'd'in jiki, yana da tsananin kwarjini da cikar haiba mai cika ido. akan kyakkyawar fuskarsa zagaye da saje mai kyau da ya karawa fuskarsa kyau, zuwa gyemunsa da baiwuce kamu d'aya ba. dogon hanci lips mai kyau da taushe, kwantaccen gashin gira mai yelwa da zara-zaran gashin ido. gashin kansa baki sutuf a nannad'e yasha gyara sai sheki yake. yana da faffad'an kirji mai shinfid'e da gashi luf-luf, daya dad'a kawata faffad'an kirjin nasa. sai dai shi sam ba fari bane kuma baza'a kirashi da baki can ba, sai dai mu iya cewa wankan tarwad'a wato chocolate kolo. Dr Abdurrahim Abubakar Shitu Fiya kenan. inkiya (A.A FIYA) A hankali ya bud'e lumsassun idanunsa. ya sauke sa kan tsadaddin agogon diamond d'in da ke d'aure a hannun sa, d'an gajeren tsaki ya ja ganin time d'in shiga CS d'in sa ya yi. da gaske ya ke jin ya gaji da damuwar aikin nan, gaba d'aya sun d'aure shi da jijiyoyin jikin sa. a gida Nigeria ana fitinarsa ya dawo. a nan kasar suma gwamnatin kasar sun ki su barshi ya koma, har cewa suka yi zasu rub'anya masa albashi saboda yacigaba da aiki da su, abinka da arna cewa suke wai shi waliyyi ne aka turoshi gare su, dan shi na musamman ne cikin likitoci, shi kad'an sa yana da baiwar likitoci dudu a kansa. sai dai shi sam baya da bukatar hakan. A sannu ya mike tare da zare rigar jikin sa irinna likitoci, ya rayatayi jikin kujerar daya tashi a kai, ya zura takalman sa. sai da ya mike na nad'a hango asalin kyakkyawar halittar da Allah ya yi awajen nan. batare da ya d'au wayoyin sa ko d'aya ba yafita. Yana fito wa cikin babban parlour'n asibin, wanda shine babban asibitin a kaf fad'in kasar Germany da sauri wasu likitoci da suka kai guda 20 suka rufa masa baya, ya yin da nurse's suma suka mara musu baya. wani office suka shige shigarsu dakamar mituna 10 suka fito, kowa yayi hanyarsa, ya yin da likitoci biyar suka biyo bayan Dr Abdurrahim da wasu nurse's uku suka nufi theater room.........! Zaku iya had'uwa da typing error dan a daddafe na samu nayi rubutun. Ina barar addu'ar ku kwaro ya shiga min kunne duk da an cire amma kunnen bai bar ciwo ba. ba lallai ne kurika samin posting kullum ba. 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* Bismillahirrahmanurrahim 🅿️17 Da sassarfa take d'aura fararen kafafunta kan stairs tup-tup da su gwanin ban sha'awa, masu d'auke da zara-zaran dogayen yatsu wanda fararen farce suka dad'a kawata su. FEERYAL ke nan wan da yanzu ke da shekaru goma sha biyar a duniya. tsagawaran kyau cikar halitta, suke a shinfed'e akuma bayyane a gare ta. mutane sukan gaza tantance kalar ta, wasu suce kamada turawa take wasu kuma suce da larabawa take kama. (Masu karatu ku dai ku d'auki kalar da kuke ganin ta dace da shi cikin ranku) "FEERYAL ki tsaya ki bani wayata ki d'auki wayar ki kuyi wayar da Ammie'n naki." Daga cikin wayar da suke video call da Aunty. Aunty tayi sauren cewa "Ke FEERYAL ki daina gudun nan idan kika same a kan stairs fa, kina gudu kan Upstairs, Allah Maryam idan kika sa ta fad'i zaki gamu da ni." Maryam da ta ruko ta ta baya tana dariya ta ce "Allah Aunty Faty yarinyar nan ta gama rainani ko dun taga tayi tsawon kafa kamar kazar turai, sai girman jiki ba kwari, jiki kamar tumatur ta mai dani sa'arta." Dariya Aunty ta yi ta ce "To ai ke d'in ce sa'arta yanzu, wato zagin da Hajja Umma take mata shine kikai mata yanzu ko, ba Abba ya ce ku dai na ce mata jiki kamar tumatur ba." dariya duk sukayi, suna karasa sauka daga stairs. FEERYAL ta zame gefe ta karaso inda Hajja Umma ke zaune kan kujera, ta zauna gefen ta tare da kwantar da kanta jikin kafad'ar ta. ta d'ago wayar tana cuno pink lips d'in ta gaba da fad'in "Ammie kice mata ta daina ce min kazan turai jiki kamar tumatur." muryar Abba suka jiyo yana cewa "Rabu da ita kishi ke damun ta." murmushi FEERYAL ta sake wanda ya sanya kyakkyawar kumatun ta lotsawa, zagayayyen dimple d'in ta gefe da gefe suka bayyana. fararen jerarrun hakoranta masu d'auke da kyakkyawan hushirya ya bayyana. "Yauwa ga Abba ma ya karb'ar miki baki." cewar Aunty tana musu dariya. Abba ya karaso ya tsaya daga bayan kujerar da suke kai. Aunty ta ce "Barka da warhaka Abba." "Barka dai Fatimah ya gidan?." "Lafiya lau alhmdulillah." Maryam ta zauna d'aya gefen Hajja Umma suka sakata sakiya. Abba ya ce "Amaryata fa this year za'ayi graduation d'in ta, har ta zab'i makaranta ma da zataci gaba da karatunta a Bayelsta ta fad'a miki kuwa?." ido Aunty ta waro ta ce "Bamuyi maganar ba Abba amma naga saurin zuwan lokacin." "Dole lokacin zai yi sauri ga kuma amaryar tawa da kokari, ai kinsan lokacin da ta shiga makaranta a nan primary 5 suka bata, saboda kokarin ta, shiyasa lokacin zaiyi sauri, gakuma rayuwar namu da yake gudu kamar me, Allah dai yasa mu dace." duk suka amsa da amin amin. Hajja Umma ta ce "Ke bakiga bulorans d'in 'yar taki bace, idan aka ganta sai ace wata babbar mace ce, kamar allurar girma ake mata kullum dube ta fa kamar ana mata famfo cikin dare, ai girman ta ne ma abin mamakin, jiki tub'us-tub'us kamar tumatur, ai baki sani ba jiya wani ya wanko kafa wai yazo hira gurin ta." da sauri FEERYAL ta kai hanu ta toshe bakin Hajja Umma tana cewa "Ni dai Allah Hajja Umma ki daina fad'a." dariya Maryam tayi har tana fad'uwa jikin Hajja Umma ta ce "Aunty Faty kin san waye ne? Alhaji Mamman fa na kasan eriyan nan, wanda gidan sa ke da dawakan nan." "Nashige su kice mai gundumar Shira, lallai ya sami damuwa wannan ai jikarsa ce." cikin muryar dariya Maryam ta ce "Wai har da cewa wai zai jirata ta gama karatu, na ce ashe zamu hau dawakai, ranar aure waya ganni a kan doki." Maryam ta fad'a tana kuma tuntsirewa da dariya. Keyarta Abba ya talle yana dariya shima. FEERYAL ko fuska ta b'ata, tana bubbuga kafa a kasa. ya ce "Rabu da su oh amaryas me zakiyi da wani bayan gani nan." Aunty ta kashe wayar tana mamakin lamarin. in banda shi da son zuciya, kamar FEERYAL jikarsa ta biyar wai shine yake so. sai kuma tayi dariya abin yabata dariya kuma. ta mike daga kwancen da take tana kokarin sauka. Daddy ya shigo ya karaso bakin gadon ya zauna yana tambayar ta, dariyar me take haka ita kad'ai. nan ta labarta masa. shima dariya abin ya bashi daya ji ance yakai sa'an Abba. Daddy ya ce "In banda shi ma ina shi ina Feeryal." Aunty ta ce "Ai kuwa dai bakaga manyan jikokin sa ba, yauwa wai this year d'in nan zatayi graduation, kuma wai Bayelsta University ta zab'a can bayalsta state ke nan zata tafi." Daddy yad'anyi shiru kana ya ce "Kai ina hankali na bai kwanta da zuwan nata can ba, ga makarantu da yawa a Abuja, ta zab'i d'aya kawai a can, zanyi magana da Alhajin Abuja anjima." FEERYAL ce zaune cikin bedroom d'in su tana buga game a wayarta, da alama shirin fita suke, dan mayafi ne zagaye a kanta tayi rolling d'inshi. maryam na gaban mirror tana kwalliya. d'an duban in da Maryam ta ke tayi ta ce "Aunty Maryam baki gama ba har yanzu, nifa na fara jin bacci ko na kwanta ne, mu bari sai anjima." Maryam ta ce "Yazu zan gama mu tafi ga Haulat ma nata kira na, nasan tana ta kan jiran mu, bari na d'an yiwa fuskar fenti, saboda ke da kwalliyar ki aka halitto ki, bazaki san illar rashin kwalliya ba." ita dai dariya tayi ta d'an kishin gid'a tana cigaba da buga game d'in ta. dan abin da tafi kauri ke nan a waya bata yin chatting, Maryam tayi ta sa mata ra'ayin har yanzu dai bata d'auka ba. "Taso mu tafi." cewar Maryam tana gyara gyalen ta, ta d'au wayarta da key'n mota, FEERYAL ta mike ta d'au facemask ta sa saka, dan bata ta b'a fita sai da shi a fuskarta, duk da wannan d'an takaitaccen tsaron da take wa fuskarta baya hana a bibiye ta. A parlour suka tadda Hajja Umma ta ce "Tafiyar ke nan, a kwai kud'i a gurin ku ne, ko a baku?." Maryam ta ce "Eh akwai kud'i a account d'ina jiya ma Abba yasamana kud'i a duka account d'in mu." "Ke zaki jaku Maryam naga makullin mota a hannun ki, bazaki bari direba ya kaiku, ya jira ku gama ya maido da ku ba?." Maryam ta ce "Yau ina jin yin tukin ne Hajja Umma na kwana biyu banyi driving ba, kar nazo na mance da driving har FEERYAL tazo ta fini iyawa dan naga yanzu ta dage ta rage tsoro." "Wannan ce ta rage tsoron? ke kazar turai ana magana idanun ki yana kan waya, a haka zaki tafi kina danne-dannen waya, bari kije ki fad'i zaki sani, bawani kwari ne da ke ba, jiki tub'us-tub'us kamar tumatur." dariya FEERYAL ta yi ta ce "Ko zamu gwada tsere ne Hajiya Umma, nafi ki kwari fa, tun yaushe mijin ki ya cika min account d'ina da kud'i, kina nan kina ta surutu da 'yan aiki kuyi nan kuyi can, ni ce zanyi driving d'in mu in zakizo muje gara ki zo ki sha dad'in tukina." "Allah ya kiyaye min, ita dai uwar taki Maryam da ta ga zata iya shiga ki jata a mota, sai taje ta shiga da salati, me zai kaini ina zaman zama ta,nashiga mota wai ke ki jani, haka nan da tsufata nafi ki kwarin jiki, au to bari ya dawo ai gara da kika fad'a min, yazo nima ya bani nawa." "Zanyi tunani ko zan barshi ya baki." FEERYAL ta fad'a tana kashewa Hajja Umma ido tare da kad'a gold eyes d'in ta. "To zamu gani ai." cewar Hajja Umma tana dariya. suka nufi kofar fita, Hajja Umma ta ce kada su dad'e su dawo kan lokaci. Suka nufi parking lot Maryam ta shiga mazaunin direba, FEERYAL ta shiga d'aya gefen. mai gadi ya wangale musu get. Suna fita can suka hango Haulat tsaye bakin get d'in gidan su, suka tsaya ta karaso, ta shiga baya ta zauna tana fad'in "Haba Maryam wlh akwai ki da lezi da duntuni mun tafi, duba time fa ki gani, har yaushe ne za a yi mana gyaran gashi, nifa har da gyaran jiki nake so na jima ba'a turarani an goge ni ba, har wani nauyi jikina yake min, kuma da naso mu biya ta gareji na duba motata, amma mu wuce kawai time ya tafi da yawa." "To uwar 'yan mita yanzu dai gashi mun hau hanya, wai tun shekaran jiyan nan ba'a d'auko miki motar a gareji ba?." "Ina aka d'auko ni na ma fa gaji da ita so nake a canza da ma, jira nake Alhajin mu ya dawo da umurar nan a sake min wata." "Aunty Haulat nima fa za'ayi min gyaran jikin nan, shi yasa tun d'azu nake ta cewa Aunty Maryam ta yi ta gama mu tafi." FEERYAL tayi maganar idanunta a kan waya tana ta aikin buga game. ido Haulat ta waro ta ce "Nashige su, wani jikin za'a goge, jikin naki? fata kamar audugar, ta ina za'a fara goge shi, ai na rantse idan aka gogeki sai kin fitar da jini, ai ke a gogen ki Allah yayiyo ki, mune masu fama da damuwar gyaran jiki." kai ta langwab'e cikin muryarta mai kamada shagwab'a ta ce "Ni kam dai ina so ayi min nima." Maryam ta ce "Haha barta taje a d'aye fatar da dirza, zakiyi bayani, yarinya." bata kuma magana ba idanunta yana kan game. su Maryam kuma suka shiga hirar samarukansu. Har suka isa bata ma san sun iso ba, sai da Maryam ta fisge wayar ta d'ago taga sun iso. kyakkyawar lips d'inta ta turo ta karb'i wayar suka fito, suka nufi shagon. Suna shiga suka tadda ana yi ma wata budurwa gyaran gashi, saurayin ta da ya rako ta yana tsaye a gefen ta, yana ta aikin yaba gyaran da ake mata. FEERYAL ta isa inda kujera yake ta d'an ja rigar abayar jikinta da yake jan kasa sannan ta zauna. tun daga yatsun kafafunta har zuwa sharab'arta masu kama da nunannen gwanda mai taushi, ya kafe shi da ido, gaba d'aya ya mace a kallon ta. wanda ita bata ma san yana yi ba tana ta sana'ar ta wato bugu tame. sosai ya tafi a kallon ta. budurwar tasa ta d'ago jin ya yi shiru da hirar da suke, ganin gabad'aya hankalin sa yayi nisa wani wajen, ta juya da sauri in da hankalin nasa ya tafi. ganin wa mace ya kurawa ido, ta had'e rai. ta mike dama an rigada an gama mata ana gyara mata pakin ne. ta ce "Malam biya kud'in mu tafi." firgigit ya dawo da nutsuwar sa, sai kuma ya shiga kame-kame ya saka hannu a aljuhu ya zaro kud'i bai tsaya kirgawa ba ma ya direwa mai gyaran kan table, ta sakashi gaba sukayi waje. Maryam da Haulat suka had'a ido, suka fashe da dariya suka tafa. "Tana zaune ta had'a fad'a bata ma sani ba." cewar Haulat tana dariya. dariyar su ce ya sa ta d'agowa, suko guri suka samu suka zauna. Aunty Jessica mai shagon itama dariya ta yi cikin hausarta da bai gama nuna ba ta ce "Kefa Feer duk lokacin da kikazo sai kin had'a fad'a, batere da kin san kinyi ba, wai dan ma kin rufe rabin fuskarki ke nan." FEERYAL ta waro ido cikin tsitiriyar muryar ta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce "Ni kuma Aunty Jessica, su wa na had'a su fad'a?." "Saurayi da budurwar da yanzu suka fita, yanzu haka nasan suna kan tirka fad'a a hanya, da ganin ki duk ya rud'e, ke d'in ce ai ba ga na miji ba ko mace ke abin kallo ce a gurin ta, itama d'in dai yanzu kishi ne ya rufe mata ido da sai ta tsaya ta kuma kallon ki, Feer you're very beautiful." "Aunty Jessica Feeryal ba Feer ba." "Oh ni 'yasu your name is so difficult." dariya duk sukayi. FEERYAL taso ayi mata gyaran jiki, Aunty Jessica ta ce bada ita ba bazata tab'a jikin ta jini ya fito ba, fatarta a wanke a kuma goge yake basai an goge shi ba. gyaran gashi kad'ai akayi mata, aka nad'e mata shi kamar gammo. a dawowa FEERYAL ce ta tuko motar dan ta iya yanzu sosai. suna shigowa ta zube kan kujera, Hajja Umma tana ta mata tsiya wai raguwa kamar a kai ta d'auko matar. shafaffen cikin ta ta shafa ta ce "Hajja Umma yunwa." "Sai iya fad'ar yunwa kamar da gaske abincin take ci, d'azu ma na duba naga saura abincin naki kad'an ya kare, nasa a sake miki wani, gashi a kichin da zafin sa ma kuwa, nakuma kara miki wasu yourght d'in a fridge." ai ko da sauri ta mike tayi kichin. jim kad'an ta fito rike da plt da cake 'yan madaidai guda uku cikin plt d'in, sai gorar yourght mai sanyi a d'aya hanun ta. ta karaso ta haye kan kujera ta nad'e kafafun ta da sauri ta d'au cake d'aya ta kai bakin ta ta gutsira, ta wani lumshe ido tana tauna." Hajja Umma ta ce "Ikon Allah mutum bazai ci abin kirki abu mai nauyin da zai rike mishi ciki ba, sai dai ya zauna shiririta." murmushi ta sake idanunta a lumshe, sai da ta kuma gutsira kafin ta bud'e idanunta hankali. tana tauna tana sakin murmushi wa Hajja Umma. Maryam kam ta je ta shako plt da abinci ta zauna tana fad'in "FEERYAL kam ai kamar ba hanji acikin ta, ina cake zai iya rike ni, ai in banci shinkafar nan ba ban ganewa." ita dai tana jin su tana ta cin cake d'in ta tana santi. Baba mai gadi ya yi sallama daga bakin kofar parlour ya gaida Hajja Umma sannan ya ce "Hajiya Maryama wai ana sallama da ku." Maryam ta d'an waro ido ta ce "Mu kuma sai dai FEERYAL ita ke mana janye-janyen mutane duk sanda muka fita, amma wayace maka shi d'in?." "Ya ce ayi masa magana da 'yammatan da suka shigo yanzu a mota." "Mance da shi Baba me gani ka ce baka ganmu ba wata kila mun fita ta d'aya kofar ne." ya juya ya fita domin isar da sakon. Hajja Umma ta ce "Idan Nasiru ne yazo fa." "Umma ba Nasir bane ai da ya kirani, kuma baba mai gadi ai yasan Nasur bazai ce wani ba, na san FEERYAL ma suka gani suka biyo mu." Hajja Umma ta lakaci goshin FEERYAL tana cewa "Ki dai na mana jaye-jaye, in ba haka ba na aurar da ki wa mai gundumar shira." baki ta cuno tana taunar cake, batayi magana ba. dariya Maryam tayi ganin yadda ta cuno lips d'in ta, bata fasa taunar cake d'in ba. murmushi Hajja Umma tayi

Chapter 15 of 20