sai kuma kayi buris abib ka,
wancan zuwan naka na ce mu tafi tare kace nabari nadad'a jin sauki tukun,
awani dadilin zaka rabani da kasata; ce maka akai banji sauki ba,
jikoki na suna can ni ina wata duniyar daban, to yau-yau d'in nan ka sa a maidani gida dan ni na warke,
ko kai yanzu baka kaini lafiyar ido ba,
an d'aga ni an rabani da jikoki na an kawo ni wata duniyar da ban san kowa ba, shekara uku ina zaune kamar mara galihu,
to nagaji da zama tun marmaza kasa a mai da ni gida, yau-yau d'in nan."
Daddy ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya bari nasa ayi muku bukin d'in jirgi zuwa ranar Litinin sai ku dawo."
"Da dai yafi dan ni nagaji da zaman shiru, in ba haka ba naje tasha nashiga mota."
"Hajiya daga can zaki shigo mota zuwa Nigeria ai bazai yuwu ba, jirgi ma zaki biyo kiyi hakuri dai."
"Ni dai na fad'a maka idan ranar Litinin tayi baka sa an d'auko mu ba tambaya zanyi a kai ni tashi."
ta katse wayar tana cigaba da bombomi.
Hajiya Bishira dake gefe tayi murmushi rigimar uwar tasu kullum karuwa yake.
Ta ce
"Hajiya wa ya ce miki akwai tashar mota na zuwa Nigeria anan, ai sai dai airport d'in jirji,
dan Allah ki barmu mu zauna anan yafi mana babu hayaniya ba komai, sai dai kaci ka kwanta hankali kwance,
acan fa hayaniyar yara ma kad'ai ya isheka, da wad'an nan masifaffun matan Yaya Abubakar d'in."
"Allah ya sawake min ni da zaman shiru ai sai dai in nashiga kabari, da raina ina numfashi kam baza a hanani walwala ba,
ai dama ku zaman bariki baya damun ku, in da Abubakar zaibi ta nawa ma da gida muka koma can Yelwan Shandam, muje muyi zaman mu hankali kwance, amma kullum kana kulle a gida baka d'an zagawa ina zan iya ciwon kafa ya kamani, ai in baka yawatawa kai da ciwon kafa kun kulla,
ina zan iya wani zama anan, ku da kuka ga zaku iya zama ga guri nan amma ni kam kafata tana takalmi gara na koma in da nafi wayo."
"Wlh kuwa hajjaju da kin bari mudad'a hutawa jiya kuwa Hajiya Bishira take cewa yau direba zai kuma fita da mu mu yawata."
cewar Kulu tana washe baki.
"Amma dai anyi asara Kulu, ina zaki yawatan da kai duk furfura,
an girma ana cin kasa,
sai kuyi ta zama ni kam dai jikoki na nake son gani,
tafiya gida ba fashi, ina zan iya da zaman shiru,
in ban da ma abokin turawa, ya kawo min ziyara wancan satin ai da tun a satin na koma Nigeria abina,
ina zan iya shege da hauka,
tun da kunga gurin zama sai kuyi ta zama."
Kulu ta b'ata rai ita a duniya bata so ace mata tsohuwa, ta buga cinya tana mara baki.
"To Allah ya baki hakuri Hajiya."
Hajiya ta mike tana fad'in
"Bari ma kiga, ni kam naje na fara shiri."
ta shige bedroom..
Ranar Litinin tun da Hajiya tayi sallar asuba bata zauna ba ta rika jidar kayan ta dana tsarabar datayi,
ta tarasu a parlour.
tsabar mitar da take yasa su Hajiya Bishira fito da nasu kayan badun sun shirya ba.
"Ke bishira sake kira min Abubakar idan jirgin ta cika yanzu direba ya kai mu tasha mushiga mota."
"Hajiya ki kara hakuri mana tun da shi jiya ya ce, an shirya mana komawa ai dai zamu koma yau, kuma ma ai har yanzu ba'ayi sallar asuba a Nigeria ba, yanzu haka yana bacci a barshi idan ya tashi sai a kira shi,
karfe 8 ya ce direba ya kaimu airport, jirgi zai tashi karfe 9,
kuma yanzu karfe 6 da rabi ne,
idan muka tafi yanzu zama kawai zamu sha duk mu d'ibi sanyi."
"Yoo bagara a kaimu muna kusa da jirgin har lokacin tafiyar tayi ba, me zamu zauna yi a nan d'in, maza kirawo direba ya kaimu yanzu,
maje mu jira a can,
ke Kulu taso ki je ki kirawo direba,
ko da shike bajin yaren nasu kema kike ba,
ke Bishira da kika iya turancin je ki ce masa yazo ya kwashi kayan mu."
Babu yadda suka iya da Hajiya haka taje ta kirawo direba, ya kwashe su da kayan su suka tafi airport.
sun sha zama ga sanyi sai karfe 9 da 'yan mintina kafin jirgin su ta tashi.
Karfe 2 agogon Nigeria jirginsu ya sauka a babban airport d'in da ke cikin birnin Lagos.
tun saura mintuna 30 kafin saukowar su, mota ta isa airport ana zaman jiran saukowar su.
Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci Aunty lokacin da ta sami labarin dawowar Hajiya Nigeria a bakin Baba Rabi.
dan kuwa Daddy yaki sanar mata dan yasan dole ne hankalin ta ya tashi.
shi kansa bai so dawowan ta yanzu ba amma tun da ta kafe sai ta dawo babu yadda ya iya dole sai ya dawo da ita.
Jiki a sanyaye Aunty ta ja hannun Feeryal da yanzu dawowar ta daga school suka shige d'aki.
Abakin gado ta zauna, ta ja hannunta tana fad'in
"Zauna Feeryal."
zama sosai tayi tana fuskantar Aunty nan da nan yarinyar da wayo sosai ya bayyana gare ta ta fahimci da akwai abin da ke damin Ammie'n tana, gashi nan tana hango damuwa shinfid'e a kan fuskarta.
Cikin yana yin ta maikama da shagwab'a ta karyar da kai gefe kana ta yin rau-rau da ido,
"Ammie mene ne baki da lafiya ne?."
kai Aunty ta girgiza
"Lafiya ta lau Feeryal, yau zamuyi wata bakuwa ce ko ince maman maigidan zata dawo, kibi a hankali kiyi taka tsantsan wajen mu'amala da ita, babu ruwan ki da zuwa side d'in ta ko da kin ga Miemie zata je, ki zauna a in da Allah ya aje ki kiyi hakuri."
ta waro manyan gold eyes d'in ta.
ta bud'e baki cikin yanayin shiga mamaki, wan da yin hakan yaba da gudumawa wajen bayyanar kyakkyawan dimples d'in dake like jikin kyakkyawar kumatunta, wan da suka karawa kyawawan kumatunta kyau da k'awa.
"Ammie bakuwar tana dukan mutane ne?."
tayi maganar tana dafe kumatun ta da hannayen ta biyu.
kai Aunty ta gyad'a ta ce
"Sosai ma, ki kiyaye babu ruwan ki da zuwa gurin ta, duk lokacin da taso kije gurin ta sai kije."
d'an karamin bakin ta cuno ta ce
"Bazan je bama kar ta duke ni."
"Oya to taso muje kiyi wanka."
"Ammie ni zanyi da kaina na iya fa, Miemie ma da kanta take yi."
"To dai muje nayi miki yau gobe sai kiyi."
Motar su Hajiya ce ya faka a parking lot d'in side d'inta.
in da tuni mutanen gidan suka hallaro suna oyoyo.
jikokin ta suka rufu a jikin ta suna yi mata oyoyo.
nan suka d'unguma zuwa parlour'n ta,
dayake a gyare ma'aikata sun gyara shi tsaf, ana ta yi musu barka da dawowa.
an baje anata hira, nan hajiya tasoma kunce jaka.
kowa ta damka masa tsarabar data yi msa.
A b'angaren Aunty tafito daga bedroom d'in Feeryal in da tagama shirya ta.
ta nufi kichin ta d'au basket data shirya kulolin abinci har kala uku ta fito.
Feeryal ta biyo ta har bakin kofar parlour tana fad'in
"Ammie zan biki."
"A'a 'yammatan Ammie zauna ki jirani yanzun nan zan dawo,
zanje side d'in Hajiya ce nayi mata barka da dawowa."
aiko da sauri ta tsaya tana fad'in
"Bakuwa mai duka bazan jeba kije Ammie."
kai ta jijjiga tayi waje.
Acan sashin Hajiya Aunty ta tadda kaf 'yan gidan,
Mommy da Umma Karima na ganinta da basket d'in abinci suka kalli juna suka yamutsa fuska.
ko kallo basu ishe ta ba, ta isa gaban Hajiya ta dire shi,
ta zauna tana yi mata barka da hanya.
Hajiya tashiga amsa gaisuwar ba yabu ba fallasa,
ta damka mata tsarabar ta.
ta amsa tayi godiya sosai.
ta zauna ana d'an tab'a hira da ita, tafi saka baki cikin hirar Hajiya Bishira da kuma Ammah dan su tafi shiri da su sosai a gurin.
Farida dake can gefe tana waya gani abayar da Hajiya ta mikowa Aunty da sauri ta taso tazo gaban Aunty.
ta d'auke shi akan kafarta tana fad'in
"Hajiya amma nace miki ina son wannan shine kika ce min wai aike aka baki,
to ni gaskiya wannan nake so, ga wancan a bata."
tajuya zata bar gurin Aunty tayi saurin riko ta ta baya, ta mike tsaye ta fizge abayar, tare da fad'in.
"Tun da har aka rigada aka bani wannan to yazama nawa, dole kema kirike wan da aka baki amatsayin naki,
da kin nuna kina so ta hanyar daya dace dana baki."
Aunty ta saketa ta koma ta zauna.
Wani banzan kallo Farida ta bita da shi "Mssttss."
taja dogon tsaki.
Hajiya ta ce
"In banda abinki ma Farida ke da zaki tafi kasar da ake kera abaya, banaji Daddy'n ku ya ce idan akayi auren can kasar larabawa ko turawa ne zaku tare da mijin naki ba,
abaya kam ai sai dai ki kawo wa wasu tsaraba."
Farida ta d'aga hanci sama tana yamutsa fuska
"Akan wani abayar da bai wuce 100k ba ake gayawa mutum magana,
ni kaf cikin abayoyi na ma babu mai arha irin wannan, idan na 1million nake so ko 30min bazan yi ba zan saka shi a jikina."
"Uhm masu arzikin ke nan ake fad'a kan wata doguwar riga, ai na d'auka sai dai muji hon d'in tirela na kamfanin abaya."
cewar Umma Karima cikin gatse.
Mommy ta ce "Ai duk abin a baki ne ayi dai mu gani."
Hajiya Bishira ta b'ata rai tana cewa
"Haba Aunty Halima me yasa kuke haka ne, kuda zaku kwab'e Farida sai kuma ku mara mata baya, sam hakan bai dace ba yanzu fa gidan wani zata je,
ke Farida dan baki da hankali Hajiya Fatima sa'arki ce, ki dai iya da bakin ki gidan wani zaki je."
waje Farida tayi tana kunkuni.
Aunty kuwa kamar ma bata san suna yi ba, tana ta amsa wa Ammah hirar da suke.
jim kad'an ta mike ta koma side d'in ta..
Da yamma Miemie ta shigo side d'in Aunty ta ce wa
FEERYAL tazo kuje sashin hajiya ta dawo zata bata tsaraba.
FEERYAL ta waro ido ta ce
"Bakuwa mai duka ni dai bazanje ba ke kije."
duk yadda Miemie taso suje FEERYAL taki firr.
Washegari Aunty ta makara wajen yiwa FEERYAL shirin school, dan har gobe ita ke shiryata,
dan a kullum ganin yarinya kankanuwa take mata.
da sauri FEERYAL tafito tana goye school bag d'in ta,
Aunty ta biyo ta tana fad'in
"Yi sauri nasan yanzu direba yana jiran ki a side d'in su Ameerah."
ai ko da sauri tayi waje had'e da sassarfa tana karanto addu'ar fita daga gida a bayyane.
Ko da ta fito can ta hango motar kofar side d'in Hajiya.
Farida Bilkisu Rahama Saddika Sumayya Nabila Sahla Miemie duk suna tsaye a gurin.
kafa ta d'aga ta kara sauri had'i da sassarfa ta karaso gurin.
Tana isowa Hajiya na fitowa daga side d'in ta rike da Ameerah tanata matsar kwalla,
Hajiya na fad'in
"Ina babanku yake acanza muku wata motar mana tun da bakwa son wannan, yi shiru abin ki maza muje na same shi,
haka kawai dan wa aka tara kud'in ake kuma niman kud'in, ba dun ku bane,
tun da yara sun ce sun gaji da tafi makaranta acikin wannan,
ba sai a canza musu wata ba tun da akwai."
Ajeemal da karasowar sa gurin ke nan ya harari Ameerah.
"Zaki wuce kishiga mota ku tafi ne ko ya, kuna gida har this time, kema Hajiya kin tsaya biye mata suna kara yin latti,
kama hanya ki wuce kishiga mota,
ko su tafi su barki kifita ki nimi taxe."
"Yoo yara sun gaji da abu d'aya sai arika yi musu dole, kai waye yamaka dole, ina sai motar da ka zab'a kaga damar fita dashi a gidan nan kake fita da shi,
ina dawowa gidan nan naga sabuwar mota na tambaya aka ce min naka ne,
je ka kiramin uban naku yazo ya canza musu mota yau d'in nan."
Kai ya kawar yana kokarin barin gurin ta ce
"Kai Ajimi ba dakai nake ba, nace kaje ka kira min baban ku."
"Ni suna na Ajeemal ba Ajimi ba na fad'a miki ki daina ce min wani Ajimi,
Daddy baya nan da safen nan yatafi,
Sahla Nabila Miemie FEERYAL ku wuce ku shiga mota ku tafi abun ku."
Suka matso jikin motar suna kokarin shi.
Hajiya tabi FEERYAL da kallo tana fad'in
"Wannan fa 'yar gidan wa kuka samo, ko har da 'ya'yan turawa ne a makarantar taku?."
Miemie ta ce
"Yarinyar Aunty ce fa Hajiya."
"Wacce Aunty'n?."
cewar Hajiya tana gwalalo ido.
Farida ta yamutsa fuska tare da hararar in da FEERYAL take ta ce
"Aljanar nan ce fa Hajiya wacce Aunty ta tsinto a ruwa, ita ce dai taki mai da ita wa danginsu aljanu, har ta girma mana a gida."
wani irin zabura Hajiya tayi ta bugi kirji tare da ja da baya kamar taga wani mugun abin tsoro.
da karfi ta ce
"Li'eelafiiikuraishin wasayyahuuu, ya tsaya a kanki ke da Fatima,
Fatima bazaki kashe ni ba, mugun nufin ki ya kare a kanki,
kai duk ku taho ku karanto li'eelafi kafa bakwai-bakwai, annoba babba a gida."
Sai kuma tashiga jan hanci tana cigaba da fad'in
"Ni Abubakar zaiyi wa haka, ni ce zai maisar mara amfani mata tafi masa ni, to wlh yau kam sai dai ya zab'i d'aya, ko ni ko Fatima,
je ki kirawo min shi Ameerah, kice wa Sulaiman da Tukur ma duk suzo,
su zamo shaida a gabansu Abubakar ya zab'a, ko ni ko Fatima da Aljanar data kawo,
yanzu fisabilllahi ashe duk tsawon shekarun nan 'yar nan tana cikin gidan nan; tana goganya da jikokina,
shike nan tarigada ta shige jikin su dole na d'auko mai rokiyya ya tare a gidan nan,
amma Fatimah kin cuce ni."
Ameerah ta juya zata tafi kiran Daddy Ajeemal ya ce
"Ameerah wuce ku tafi ni zan kira shi."
Hajiya ta ce
"Wlh ba a mota d'aya zata tafi da jikoki na ba,
ina ma zaki je ai yanzu zaki bar gidan nan ba sai anjima ba, kai Isa direba d'auki su Ameerah ku tafi, ku barta anan yanzu zata tafi in da ta fito."
Ameerah Sahla Babila har da tsallen murna suna wa FEERYAL gwalo, suna fad'in
"A tafi a bar mana gida."
manyan 'yammatan kuwa su Farida Sumayya Bilkisu Rahama Saddika, duk da harara suka bita.
Bilkisu ta ce
"Aje a kare a cikin ruwa, an sami guri an baje a cikin daula sai dai aci a kwanta."
Miemie kuwa kamar zatayi kuka cikin muryar magiya take cewa
"Hajiya dan Allah ki barta mu tafi exam fa mukeyi zata rasa paper."
wani uban salati Hajiya ta sake.
"Laaaa'ilaha'illallahu, ke Miemie dole ta kanki mai rokiyya zai fara dan da gani ba karamar shigar jikinki tayi ta lashe miki kurwa ba,
zaki wuce ku tafi ko sai naci mutuncinki."
Miemie ta juya tana waigen FEERYAL idanunta ya kawo kwalla ta shige mota direba yaja suka tafi.
Hajiya ta juyo gun Ajeemal daya cika har wuya ta ce
"Zaka wuce kaje ka kira min uban naku ne ko ya,
kana wani cika kamar kububuwa, aikin bazan kawai,
da raina ba'a isa a hani magana ba, shegu 'ya'yan hofi ana yaki a kanku bakwa gani,
bazan zuba ido ina gani duk ta lashe ku ba."
"To ai sai kije ki same shi da kanki ni ba in da zani."
"Dun ubanka kar kaje Allah yasa ina da kafa."
ta juya fuu tana fad'in
"Ke mayyar aljana jira ni a nan kada ki sake ki shiga ko ina a gidan nan zaman ki yakawo karshe cikin gidan nan."
Ajeemal na ganin shigewar ta side d'in Daddy ya dubi FEERYAL dake tsaye jikin ta yagama sanyi hawaye ya cika gold eyes d'inta sai walki suke kiris ya rage su zubo.
ya ce
"Zo muje."
ya yi gaba ta tabiyo bayan sa.
Babban parking lot suka je, ya bud'e kofar d'aya daga cikin motocin da suke jere a gurin,
ya dube ta tare da fad'in
"Shiga mutafi kar kiyi latti."
a hankali cikin sanyin jiki ta shiga motar ta zauna.
tana zama ya maida marfin ya rufe ya zaga gefen direba ya shiga yaja motar da gudu security suka bud'e masa get yayi waje.
Hajiya ko tana shiga sashin Daddy ta taras da kofar da zai sadata da ainahin cikin side d'in nasa a kulle.
ta juya ta fito tana sauke buhun masifa
"Duk in da kaje ma zaka dawo, wlh ko ni ko Fatima yau a gidan nan."
Da mamaki ta tsaya tana kallon in da ta bar FEERYAL wayam babu kowa.
sashin Aunty ta nufa tana zuba uban bala'i.
Aunty na ganin ta ta mike tsaye da sauri tana fad'in
"Barka da shigowa Hajiya ina kwana antashi lafiya."
"Rike gaisuwar ki babu ruwanki da na tashi lafiya ko ban tashi lafiya ba,
ni Fatima zaki ha'inta, ki aje min mugun gamasheka a gida tana cud'anya da jiko ki na,
a dire kika sami Abubakar da hakoran sa cur bakin sa,
bayan nagama wahala da shi, yazamo cikakken mutum ya tara dukiya masu yawa,
sai da ya had'a komai da komai kafin ya auro ki, baki san wahalar shi ko na dai-dai da miskala zarratan ba;
ki zab'a ko zaman auren ki ko rayuwa da aljanar da kika tsinto, dan wlh zaman ta a gidan nan yakawo karshe, ko ki fitar da ita a gidan nan kiyi zaman auren ki ko kuma ku tafi tare,
zan nuna miki ni na haifi Abubakar yau."
Hajiya ta juya fuuu tana cigaba da zuba bala'i kamar zatayi aron baki..
Sharaf Aunty ta zube kan kujera tana furta
"Allahumma'ajirnifimusibati."
Dama Hajiya yaya da masifa bare a bin nima ya samu.
sai da Dad da Abbieh suka taru sukayi ta bata hakuri.
Ajeemal kuwa bai bar school d'in su FEERYAL ba sai da aka taso su,
kasan cewar exams suke awa biyu sukayi a aji.
ya d'auko ta ya dawo da ita gida.
Aunty na ganin ta ta rungume ta,
FEERYAL ta saki kuka tana fad'in
"Ammie bakuwa mai duka zata dukine ni dai tsoro nake ji."
"Bazata duke ki ba kinji yi shiru muje ki cire uniform."
da kyar Aunty ta lallab'a ta suka shige d'aki.
Ajeemal kuwa na sauke FEERYAL side d'in Hajiya ya shige.
Hajiya na ganin sa ko zama bata bari ya yi ba.
ta ce
"Kai Ajimi uban naku har yanzu bai dawo?."
"Ke fa Hajiya kin fiye mita da yawa wlh, mutum yana marmarin ki dawo amma daga dawowar ki jiya-jiya kin addabi mutane da masifa,
wai waya ce miki yarimyar can aljana ce kam,
dan kawai tana da kyau da yawa sai ace ita aljana ce,
dan Allah ki kyale ta tayi zaman ta yarinyar nan is so silent babu ruwan ta da shiga rigima irin na yara,
inda mayya ce ko aljana da bata cinye mu tuntuni ba, ko ta shiga jikin namu kamar yadda kike fad'a,
haba dan Allah Hajiya ki bari Daddy ya sami ladar rike ta mana dan Allah,
yanzu idan kika kore ta ina zata je,
bata da iyayen da suka wuce Daddy da Aunty,
tun da bata san kowa nata ba,
dole mune dangin nata."
"Rufamin baki sokon banza, tun da kake ka tab'a ganin mutum kyakkyawa irin ta, ko a kasashen turawan nan d'ai-d'ai ku ne masu kalar ta;
'yar da aka tsinta cikin ruwa, me yakai jariri cikin ruwa in ba d'iyar mutanen cikin ruwan ba,
aljanun ruwa kyawawa ne tun zamanin iyaye da kakanni ake fad'ar irin kyan su,
me ka sani rufa min baki dall,
tashi maza ka je ka kira min uban ka."
Kafad'a ya d'aga ya mike yana fad'in
"Sai dai in zaki bishi in da yaje dan Daddy baya kasar nan ma."
ya yi waje a bin sa ya barta nan tana ta bombomi,
har sai da ta tashi Hajiya Bishira a bacci.
Hajiya Bishira ta fito tana tambayar ta meke faruwa
cikin masifa Hajiya take fad'in
"Maza kira min Abubakar a waya, duk in da yake ya dawo yazo ya fita da aljanar can, ko nasa direba ya d'auke ta ya fidda ita yaje can ya yasheta."
"Yi hakuri Hajiya adai bari ya dawo tukun."
"Bazan bari ba yanzun nan nake so na nunawa Fatima na isa da Abubakar, ba ita kad'ai ta isa ta rika juyashi yadda take so ba."
Hajiya Bishira ta girgiza kai ta d'aga waya ta kira lambar Daddy,
sai da kiran yakusa yankewa kafin ya d'aga.
daga cikin wayar Daddy ya ce
"Bishira yanzun nan na sauka a jirgi ina airport bari na isa masauki tukun."
"To Yaya dama Hajiya ce ta ce na kira ka."
daga in da Hajiya ke tsaye tana juyo sa kasancewar a handsfree ta saka kiran.
Hajiya ta bud'e murya tana fad'en
"In na isa da kai yanzu-yanzun nan kadawo ka d'auki aljanar da ka aje ka fita da ita a gidan nan,
ko nasa direba yaje ya yasheta cikin kwalbati tabi ruwa ta koma gurin dangin ta."
Da sauri Daddy ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya kar ki sa wani ya fidda ita idan na dawo zan d'auketa na maida ita in da muka d'auko ta."
"Na dai gaya maka in ba so kake ka had'u da mummunar b'acin raina ba."
Hajiya Bishira ta kashe wayar tana cewa
"Kibari ya dawo dan Allah Hajiya."
"Yoo in bai dawo kan lokaci bama ni nasan yadda zanyi ai, sai dai ya dawo ya samu na kaita cikin ruwa gun dan gin ta,
ke Kulu zumo min nama mai d'an ruwa-ruwa da kashi mai laushi."
Hajiya ta fad'a tana duban Kulu........!
Mommyn Twinc ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️13
Hajiya na hakimce a kan kujera tana warb'ar ferfesun naman ragon da Kulu ta zubo mata.
Umma Karima ta shigo,
dan labari ya kai mata Hajiya ta ta da bori sai Feeryal tabar gidan.
shine tazo karawa wuta fetur.
karaso cikin parlour'n ta zauna kan kujera tana fad'in
"Ina kwana Hajiya."
Hajiya data kai loman nama baki ta amsa da kai, sai da ta gama taune naman ta had'iye, tabi Umma Karima da kallo.
Umma Karima ta dad'a sake jiki tana marairaice fuska irin yadda marasa lafiya sukeyi.
"Ke karimatu lafiyar ki kuwa, yanaga duk jikin ki ya sake haka?."
Baki ta karkata cikin iya makirci ta ce
"Ina kuwa lafiya Hajiya muna tare da annoba cikin gida,
wlh Hajiya kullum na kwanta bacci da wahalallen mugun ciwo nake tashi,
kullum da kalar razanennen mafarkin da nake akan yarinyar can Feeryal,
yaukam ma abin ya yi muni babu ko da d'in fad'a,
wlh hajiya jikina ya yi mugun sanyi da lamarin."
Hajiya ta waro ido ta ce
"Ai ni tun da ganin yarinyar nan nasan ba karamar gaggaruma bace, wani abu kika gani tana yi ko?.
Umma Karima ta karkata baki
cikin kwarewa a tsalon makirci ta ce
"Wlh Hajiya abun ya munana, har bana son fad'a,
ke nagani cikin mafarki da ita tana binki kina gudu sai da ta turaki cikin wani katon rami kafin ta juyo kai na,
dama jiya sai da Nabila ta ce min ta ganta cikin mafarki tana binta da wuka zata yanka ta,
wlh yarinyar nan barazana ce ga rayuwar mu,
nakasa sukuni ne gara kawai nazo na sanar miki kisan irin zaman da zakiyi da ita."
Hajiya ta gwalalo ido ta buga kirji
"Da wa zan san irin zaman da zanyi da ita,
ai ni da ita hayatan-hayatan, basai ta kuma kwana cikin gidan nan ba kafin ta sami damar bin kurwan mutane cikin dare,
a yau d'in nan zata bar gidan nan bata kuma kwana."
"Ato gara dai dan wannan babbar annoba ce, idan tafi haka a gidan nan ba'a san iya barnar da zatayi ba,
Hajiya
ga wannan hayaki ne na ruko miki,
in zaki kwanta sai kiyi, nima jiya ne nasa aka kawo min, na mance banyi ba na kwanta ai kuwa nasha wuya cikin bacci,
bana kuma kwanci batare da nayi duk da yaran ba."
Hajiya ta amsa tana cewa
"Ai ko nagode zan ajiye maganin wata rana zaiyi amfani,
amma yau kam bata kuma kwanan gidan nan,
bare ma tazo min cikin bacci."
Sai da Umma Karima ta tabbatar da munafurcin ta ya ginu kafin ta tattara ta koma sashin ta.
Hajiya tayi ta zuba ido ganin dawowar Daddy amma shiru har dare.
ta d'agawa Hajiya Bishira hankali sai ta kira mata shi, aka kuwa yi rashin sa'a wayarshi a kashe.
zo kaga masifa gurin hajiya.
tana fa d'in
"Wlh yau sai ta bar gidan nan a daren nan."
Hajiyq Bishira ta ce
"Hajiya bakya jin tsiro idan kuma aljanar ce da gaske ranta ya b'aci tayi miki wani abin fa."
"Ashsha ke kike tsoron aljani, ai idan kika nuna kina jin tsoron su shine ma suke samin garab'asar yi miki tsiya, ai ba'a nuna a na jin tsoron su,
tun kana yara kake gwagwarmaya da su, ni da natab'a kawance ma da aljana tun muna yara,
ai dana gano ta
nayi mata dukan tsiya sai da ta b'ace."
Hajiya Bishira ta girgiza kai.
Hajiya kota d'auki kafa tayi sashin Aunty dan taci alwashin yau fa Feeryal bazata kwana gidan nan ba.
tarika bubbuga jikin get d'in sashin Aunty,
mai ganin get d'in ya bud'e.
jiyo muryar Hajiya ce.
ta shige ciki da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 20