soma magana.
"Akwai wani malami a can jahar Bauchi awani gari da ake kira Duguri,
Allah ya basa baiwar fahimtar irin wad'an nan matsalolin,
ki kaita can koma mene ne zakiji, in har ba mutum bace bama kafin ku isa zaki nime ta ki rasa, dan bazan mance ba, lokacin jinyar Yayan ku da muka gama karad'e kasashe da dama bamu dace ba, a can gurun sa muka dace,
lokacin da mukaje wata mata tazo da kwatankwacin irin wannan matsalar sai dai ita haifar d'iyar tayi aka canza mata,
ya ce taje ta zo da yarinyar, 'yar tana goye a bayan ta a hanya ta b'ace, bata sani bama har sai da tazo zata kunceta ta shafa taji wayam babu komai a bayan ta,
ganin yadda hankalin ta ya tashi malamin yace ai dama ba 'yarta bace nasu ne ta koma gurin iyayenta,
shi da kansa yaje ya karb'o mata asalin d'iyarta a gurin su,
idan zaku tafi ki sanar mata da in da zakuje, in har Feeryal ba mutum bace baza ta soma dumfarar gabansa ba zata gudu, tun kafin ku isa,
zan bincika ko yana nan har yanzu dan shekarun da dama tun Yayan ku na d'an shekara uku."
Aunty ta ce "Amma Hajja Umma ba dai irin mushrikai d'in nan ba ko? yanzu sai susa ka kauce hanya."
"Haba Fatima ni da kaina bazan kaiki in da zaki halaka ki rasa imanin ki ba,
kin san ba irin wannan tarbiyyar na baku ba, haka nima ba irin wacce iyayena suka bani shi ba ke nan,
idan da yana shirka da tun zuwata ta farko bazan kara zuwa ba,
bare kuma har na tuna da shi a yanzu har nayi miki sha'awar zuwa gurin sa,
malami ne mai aiki da ilimin addini, ba irin masu fad'e-fad'e da karyace-karyacen nan ba,
zan bincika ayau d'in nan idan yana nan sai kubi jirgi kuje."
Aunty ta ce to. nan sukayi sallam.
A b'angaren Mommy kuwa, tana fita ta had'u da Ajeemal dasu Sahla suka kira sa.
da sauri ya tare ta yana fad'in
"Mommy lafiya? su Nabila sun ce min wai kin fad'i kina ihu."
"Biyo ni kawai Ajeemal kar ka tsaya anan da alama kaf yankin side d'in ta ta zagaye shi da kafin asiri."
kai ya girgiza shi sam baya son irin wad'an nan abubuwan da Mommy da Umma Karima suke yi,
baisan me ya kaita sashin Aunty'n ba da take maganar wani asiri.
su komai sai sun dangantashi da asiri.
sam baya jin dad'in yadda iyayen nasa suke zama da abokiyar zamar tasu.
yabi bayanta.
Suna shiga parlour'n ta Mommy ta zube a kan carpet tana dudduba kafafunta, da d'azu take jin sa tamkar za'a finceke su sufice daga ganganr jikinta.
"Kai Fatimah bakar munafuka ce, wannan zata iya kashe mutum da bakin asiri take aiki."
Fuska Ajeemal ya b'ata ya ce
"Mommy to me ya kaiki side d'in Aunty Mommy ku dai na yin haka fa."
wani uban harara ta buga masa.
"Rufa min baki dan ubanka me kasani a rayuwar duniyar, abin da yafi asiri ma in akwai Fatima zata iya, an tab'o uwar ka ai dole ka nuna b'acin rai, ai nasan ba banza ta barku ba,
dole ma na tashi tsaye,
kafin a fini karfi a kan 'ya'yana."
Bai kuma yin magana ba yaja bakin sa ya yi shiru yana girgiza kai kawai.
a sawace ta ce
"Wuce kabani guri ai najima da sanin 'ya'yana mata ne kad'ai masu tausayi na, dama ciwon 'ya mace na d'iya mace ce, da kazo ka same ni cikin halin da nake ciki ma d'azu da asirinta ya rike ni, da babu abin da zaka iya yi min ma acan sashin nata, sai dai in zanmutu ad'au gawata."
"Allah ya baki hakuri Mommy."
yafad'a yana nufar kofa ya fice abinsa.
Kamar yadda Hajja Umma ta fad'a, a ranar tasa a binciko mata labarin malamin da yake garin Duguri dake jahar Bauchi.
ta turowa Aunty cikakken adireshin sa har da lambar waya.
kana ta biyo bayan sakon da kira.
Aunty tana rike da waya tana saurarar karin bayanin da Hajja Umma take mata.
Hajja Umma ta d'aura da fad'in
"Idan kun d'au hanya ki ambata mata inda zakuje da sunan wanda zakuje gurin sa,
sunan sa malam Buba Mani,
na sami labarin tun a wancan lokacin bayan jinyar da mukayi a gurin sa bada jimawa ba,
ya daina jinya da shigan irin wad'annan kasadar daya shafi junnu,
ko an je masa baya saurara, amma kuje ku gwada Allah zai wuce gaba"
"Har jikina ya yi sanyi kuma Hajja Umma, anya zai saurare mu?."
"Insha'allah mu dai gwada mu gani, ni ma nafi kyautata zaton 'yar nan mutum ce, sai dai su jinnu basu da kama,
sukan iya sajewa a cikin mu tamkar mu d'in, surika yin komai irin namu, ku dai je muji,
in kuma ta koma gurin danginta a hanya to ai shike nan sauki ma ke nan."
jiki a sanyaye Aunty ta ce to.
Ko da Aunty ta sanarwa Daddy, da fari kamar bazai amince ba, amma dayaji ta ce Hajja Umma tabada yakinin mutumin baya shirka sai ya aminta.
ya ce zaiyi musu bukin zuwa jibi sai subi jirgi su tafi, har da shi za'a tafi.
da kuma Baba Rabi ko bukatar wani hidima zai taso a can suna da mai yi musu.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan kuwa suka biyo jirgi daga Lagos zuwa Bauchi.
bayan Daddy ya sanar wa aminin sa gwamnan jihar Bauchi, zai shigo garin sa.
suna sauka a airport, suka taras da motar zuwa d'aukarsu a cikin airport d'in.
motar da gwamnan jihar Bauchi aminin Daddy ya turo a d'auke su a kaisu masauki.
direct government house aka wuce da su.
a kyakkyawar masauki na alfarma aka sauke su,
bayan sun gaisa da mai girma gwannan jihar Bauchi, sukaci suka sha.
gwamna yaso su kwana kafin su wuce Duguri, Daddy ya ce kawai zasu wuce yau baya so su b'ata lokaci.
nan da nan aka shirya musu jagora zuwa garin Duguri, da motoci uku, biyu nasu d'aya na jami'an tsaro.
tun a mota a kan hanyarsu na zuwa Duguri Aunty tarika sanarwa Feeryal inda zasuje.
suna zaune a bayan mota su biyu Baba Rabi tana gaba a gefen mai zaman banza.
sai direba a mazaunin sa.
Daddy na d'ayan motar shi da deputy governor.
sai direbar dake jan su.
Aunty da tun d'azu hankalin ta ke kan Feeryal d'in tana ta son gano wani sauyi tattare da ita,
ta ce
"Feeryal kinsan ina zamuje?."
Feeryal dake tsaye kan sit tana leka titi ta jikin window mota tana kallon wuraren da suke giftawa ta girgiza kai alamar a'a.
D'an numfashi Aunty ta sauke cikin yin kasa da murya ta in da direba ko Baba Rabi baza sujiba ta ce
"Zamuje gurin Malam Buba Mani ne, malami kuma mai magani."
Feeryal ta b'ata fuska ta dawo jikin Aunty ta kwanta tana fad'in
"Ammie kice kar ya min allura, yabani magani kawai, zan sha bazanyi kuka ba, kar ya min allura."
tawani cuno baki tana dad'a shigewa jikin Aunty tana niman yin kuka.
Aunty dai shiru tayi tana binta da kallo ya yin da kaunarta ke dad'a shigarta bata fata ace ta tafi ta barta,
ita dai fatan ta arabata da gane-ganen da take, taji ta gani zata iya zama da ita ko ba mutum d'in bace.
Jin mota ta tsaya yasa Aunty d'agowa sai gani tayi ashe dai har sun iso, gasu a kofar wani d'an madai-daicin gida ginin laka.
Duk suka firfito daga cikin motocin,
inda Daddy da dipiti gwamna suka fito daga tasu motar.
cikin azama jami'an tsaron dake tare da su suka zagaye su sukayi wa gurin kawanya.
dattijan dake zaune a gindin bishiyar kofar gidan.
duk suka mike cike da girmamawa suka shiga mika musu gaisuwa,
duk da basu san ko su d'in su waye bane, amma sun fahimci su d'in ba kananun mutane bane.
Daddy ya mimmika musu hannu duk suka gaisa,
suna mai mamakin ganin sanyin hali irin nasa.
da gani ba sai an fad'a musu ba sun san cewa shi d'in bana wasa bane.
Dipiti gwamna da tun saukar su waya yake sai sannan ya sauke wayar, yad'aga musu hannu alamun gaisuwa yana fad'in
"Sannunku dai barkanku da war haka."
da sauri
duk suka amsa da "Barka dai ranka shidad'e, sannunku da zuwa."
shi kam sun gane shi mataimakin gwamnan jahar su, suna ganin sa a jikin posta.
"Yauwa godiya muke, am nan ne gidan malam Bubu Mani ko?."
cewar dipiti Gwamna yana nuna kofar gidan da suke.
suka ce "Kwarai kuwa nan ne gidan ai yanzun nan ma yashiga ciki duk muna tare da shi a nan."
D'aya daga cikin mutanen cike da girmamawa ya ce da su Aunty
"Hajiya bismilla ku karasa ciki mutan gidan suna ciki."
kana yayi saurin d'auko d'aya daga cikin taburman da suke zaune a kai mai hasken ciki ya shinfid'a wa su Daddy yana fad'in
"Bismilla ranku shidad'e ga gurin zama bari a kirawo sa."
Aunty na rike da hannun Feeryal Baba Rabi kuwa na rike mata da handbag d'in ta suka shiga gidan da sallama.
Inna Delu matar malam Buba Mani, dake aiki a sakar gida ta amsa musu sallamar tana fad'in
"Lale barkanku da zuwa."
tayi saurin mikewa ta isa ta d'auko tabarmar kaba ta shinfid'a musu tana cigaba da fad'in
"Ku iso ga gurin zama maraban ku dai."
Wani irin mikewa malam Buba Mani dake zaune cikin wata 'yar rumfar kara ya yi.
"Ta bayyana ke nan!."
ya yi maganar a zabure.
kafin su Aunty su karasa gurin zaman da aka musu shi ya rigasu fito wa, daga cikin rumfar karar da yake ciki.
da sauri tamkar mai tafiya kan iska tsohon dattijon ya iso gaban su kamar kiftawar ido.
Beyi wata-wata ba ya kai askar dake rike a hannunsa kan goshin Feeryal, ji kake kyasss ya tsaga shi dai-dai tsawon gab'ar yatsa d'aya.
nan da nan wani bakin jini yashiga tsartuwa.
Jikin Aunty ya d'auki b'ari ba ita kad'ai ba har da Baba Rabi da ita kanta mai d'akinsa Inna Delu.
abin mamaki Feeryal na tsaye babu wani alamar da ya danuna jin zafin yankan da aka mata bare d'igon hawaye a idon ta.
Malam Buba Mani.
ya kamo hannun Feeryal ya janyo ta cikin 'yar rumfar karar nan, da sauri ya zaunar da ita kan wata kututturen itaciya.
ya mike da sauri ya shiga wani d'aki dake cikin rumfar,
da sallama mai karfi d'auke a bakin sa.
da gani dad'ad'd'en d'aki ne,
yana duk ya baiyaye ko ina.
ya saka hannu ya yaye yanar da ke gabansa kana ya mika hannu ya d'au wani d'an karamin tukunyar kasa,
ya yaye yanar da ya rufe jikin tukunyar kana ya juya yafito da sauri.
A gaban ta ya aje tukunya yasaka hannu da sauri cikin sa, ya d'auko wani magani ya mannashi a goshin ta dai-dai gurin da ya tsaga.
da sauri ya danne gurin da yatsarsa ta tsakiya.
yashiga goga maganin a gurin yana zagaye da shi kamar zagayen mantega.
sai da ya d'anyi fad'i da shi kana ya d'aga hannunsa ya d'au wani, maganin yakuma shafe gurin da shi.
nan take gurin ya shafe tamkar ba gurin bane a ka yankata kafin yanzu, ya dawo normal kamar inda ainihin fatarta yake.
Aunty suna tsaye suna kallon ikon Allah.
Numfashi Malam Buba Mani ya sauke, ya mike tsaye yana dafe jikin karar rumfar sa, yana kuma sauke numfashi, kamar wanda ya yi aikin gayya.
kan kace me suka fara jin kukan tsuntsaye da wasu nau'ikan dabbobi.
kamar kiftawar ido tsuntsaye suka cika gidan ta sama suna ta shawagi da kuka iri daban-daban.
Dajin Malie.
A can cikin kasurgumin dajin boka Malie a karkashin kogon tsafin sa.
A firgice boka Malie ya mike yana zazzare jajayen manyan idanuwansa, masu matukar tsoratarwa had'i da firgidar ga duk wanda ya yi arba da shi.
ya damke tsandar tsafin sa, cikin hargitsatsen murya mai fidda amon sauti maraddad'i mai cike da razanarwa ya furta
"Ma somar faruwar wata husuma!."
Ya buga sandar tsafin sa a kasa, yana gwalalo manyan munanan idanunsa, yana son ganin me ke faruwa.
sai dai daya buga kasa madadin ya sami amsar tambayar sa,
sai dai yaga bakin hayaki mai duhu ya kasa ganin komai.
Nan da nan ya tura aike izuwa fadar sarkin bokaye.
Sarkin bokaye Lazzi shima a gurinsa yaji alamun faruwar wata husuma, sai dai duk iya binciken sa ya kasa gane mene ne, ya wanzu yanzu-yanzu.
Dole shima sai da ya dangana ga sarkin bakaken aljanu.
Sako ne ya dawo wa sarkin bokaye Lazzi daga gurin sarkin bak'aken Aljanu,
wacce suke nima ce ta bayyana sai dai babu haske a gareta basa iya ganin komai sai duhu.
Nan da nan sarkin bokaye Lazzi ya sanarwa boka Malie abin da ke faruwa.
tsabar firgita sai da ya fad'i ya suma.
Duguri
Malam Buba Mani yafito daga rumfar karar sa, in da Feeryal ke zaune ko a jikin ta tasa yatsar ta cikin baki tana wasa da shi.
har lokacin su Aunty suna tsastsaye da kafafun su, sai dai yanzu duk kawunan su a sama yake suna kallon tsuntsayen da suke ta shawagi saman gidan. kasa-kasa kamar zasu sauko kansu.
ya yin da tsoron su ya karu ganin wasu irin halittun tsuntsaye daban-daban, wasu masu yanayin ban tsoro.
lokaci kankani suka cike saman gidan sai kuka iri daban-daban suke.
sunayi kamar zasu sauko kasa.
Malam Buba Mani ya d'aga hannu sama yana fad'in
"Maza kuyi tafiyar ku babu abin da ke faruwa anan, tana cikin koshin lafiya."
ai ko nan take tsuntsayen nan suka soma watsewa, har suka watse duka.
sai guda biyu suka rage akan rufin d'aki.
Baki Feeryal ta washe daga in da take zaune tana hango tsuntsaye guda biyun nan, wan da a zahiri ita ba tsuntsu take gani ba mutane ne.
da saure ta mike tafito daga cikin rumfar tana nuna su da yatsa
"Laa Chuchu Chulu yaushe kuka zo kuma a jirgi kuka zo, ya ban ganku ba,
shine kuka hau sama kuma?
ai naga mutane da yawa a sama, nima ku hau da ni."
ta d'aga hannu sama tana tsalle, wai itama zata haura sama.
Aunty ta zubawa tsuntsaye biyun nan ido da Feeryal ta kira su da sunan da take kiran kawayen ta da su, abin ya matukar d'aure mata kai.
Maganar Malam Buba Mani yasa Aunty dawowa daga tunanin da ta tafi jin yana cewa
"Ku gusa a gareta kar ku shagaltar da ita."
yana rufa baki suka fire.
Fuska ta bata tana cuno baki
"Ba kun tafi ba, ko kunzo gidan mu bazan baku baby na kuyi wasa da ita ba, ai Ammie na ta siya min babban baby kuma."
Malam Buba Mani ya dubi Aunty da ke tsaye tsoro ya bayyana gare ta.
ya ce
"Bismillah Hajiya ku isa ku zauna."
da kyar ta iya jan kafarta, Baba Rabi ma da tsoro ya gama da ita ta biyo bayan ta suka karasa kan tabarmar da aka shinfid'a musu suka zauna.
D'aya daga cikin mutanen da suke tare da su Daddy a waje, ya kwad'a sallama cikin zauren gidan.
Malam Buba Mani ya amsa tare da nufar zaure ya fita.
Aunty na zama Feeryal ta dawo jikinta ta zauna, tana ta zuba mata shagwab'ar ta data saba.
Aunty dai bata iya ko kyakkyawar motsi ba dan tsoro yagama cinye kanta,
sai satar kallon goshin ta take inda d'azu ke fidda jini yanzu kuma yadawo tamkar inda da yake.
Jim kad'an Mamal Buba Mani ya dawo gidan, ya karasa 'yar rumfarsa ya zauna.
da hannu ya kira Aunty ya ce
"Kuzo ku da d'iyar ta ki."
jiki a sanyaye Aunty ta mike rike da Feeryal suka karasa cikin rumfar ya nuna musu gurin zama suka zauna.
Dattijon ya dube Aunty da kyau kana ya soma magana cikin nutsuwa,
"Duk wani wanda Allah ya hukunta zamanta a gurin sa dole yaji fargaba da tsoron abubuwan da zai rika gani da ji a gare ta,
shin ke ce mahaifiyarta?."
Aunty ta girgiza ta ce "A'a."
"To wace ce ke a gareta?."
Aunty ta gyara zama tare da duban Feeryal sannan ta ce
"Tsintar ta mukayi, ni da megida na acikin ruwa, ruwa yana shirin gudu da ita,
shine muka riketa har izuwa wannan lokacin."
kai ya jinjina kana ya ce
"Angaishe ku da kokari, sannunku da ceton farar aniya."
ya shafa kan Feeryal da ke ta wasa da igiyar tabarma,
ya ce
"Karni bayan karni shekaru masu tsawo fidda rai ga samin 'yanci bayyanar ki ya dawo da komai sabo,
an jinjina miki 'yar baiwa,
shekaru arba'in rabon da na shiga wancan d'akin amma yau ganin ki ya bani tabbacin zan iya shigarsa batare da wata tsaiko ba,
zan kuma cigaba da taimakawa mutane da baiwar da Allah ya yi min,
wan da nakasa kuma taimakawa wani tun bayan shekaru arba'in."
ya gyara zaman sa kana yaci gaba da fad'in.
"Nasan abinda ya kawo ku nan bai wuce kokon to a kan ta ba,
ita mutum ce kamar ki kamar ni kamar kowani mutum, sai dai ita ta bambanta, tana da wasu irin tarin baiwa da ba kowa yake da irin sa ba,
ita kanta a wannan shekarun nata sam bazata fahimci komai cikin rayuwar ta ba,
har izuwa wasu shekaru masu dama,
kada ku damu da yana yin ta ko wani d'abi'arta,
idanunta da kanta a bud'e suke tana iya ganin abin da ku bazaku iya ganinsa ba,
baiwa ce daga Allah, kada hakan yabaki tsoro,
zata iya yin mu'amala da su kamar yadda zatayi da ku, kada ganin hakan yatada muku hankali babu komai da yardar Allah,
naji dad'i da Allah ya nufeku da tunanin zuwa nan, bakuyi tunanin zuwa gurin wani ba,
bamu sani ba wanin ko shi wane ne, wala'alla ko shi na d'aya daga ciki 'yan kwangilan da aka baza domin niman ta,
a wannan lokacin da sukasan da bayyanar ta, suke fafutukar niman inda take,
shi yasa nayi gaggawar goge shaidar da zai sa suyi saurin gane ta, a duk inda zasu had'u bazasu tab'a gane abin farautarsu ba,
haka zasuyi ta nima su rasa, na goge tabon da ke goshinta da zai bayyana ta a gurin su cikin ruwan sanyi."
Kai Aunty ta jinjina cikin ranta cike yake fal da tambayoyi.
kamar yadda nasan kuma kan ku masu karatu kuke d'auke da shi cikin zuciyar ku.
"Wace ce ita meye had'inta da aljanu bayan ita mutum ce ba aljanar ba,
me yasa wasu ke niman ta, to ko shi yasa aka jefata cikin ruwa ya tabbata ba had'arin jirgin ruwa sukayi da iyayen ta ba?."
ya akayi ya santa bayan bai tab'a ganin ta ba."
ire-iren waɗannan tambayoyin ke yawo cikin zuciyar Aunty.
Malam Buba Mani ya yi murmushi ya na fad'in
"Nasan akwai tarin tambayayo cikin ranki amma lokacin sanin hakan yana zuwa, naji dad'in jin a hannunku ta ke, nasan zata sami tsaro da kulawar daya da ce,
kutashi ku koma gida d'iyarku mutum ce mai daraja ma kuwa."
Kai Aunty ta jinjina tana fad'in
"Mungode Malam Allah ya saka da alheri."
"Amin amin Allah ya tsare muku hanya nasan bazasu bari ku d'au hanya ku kad'ai ba, zaku sami 'yan rakiya, dan ita d'in mai girma ce agare su, tana tare da tsaron su a ko yaushe, gudun faruwar wani abu."
kai Aunty ta jinjina ta mike tana cigaba da masa godiya ta ruko hannun Feeryal, sukayi masa sallama har bakin zaure Inna Delu ta rako su.
Malam Buba Mani kuwa har jikin mota sai da yaga tashin su kafin ya koma gurin zaman su da mutanen sa.
Cikin garin Bauchi suka dawo a government House suka kwana washegari suka bi jirgi suka koma Lagos.
zuciyar Aunty wasai da jin Feeryal d'in ta mutum ce, sai dai wani b'arin zuciyar ta na kunshe da tambayoyi da son sanin dalilin daya sa wasu ke niman ta.
A b'angaren Daddy ma sai da suka dawo gida kafin yasa mi sukunin tambayar ta me Malam Buba Mani ya fad'a a kanta.
Aunty ta shaida masa komai, ya jinjina lamarin ba kad'an ba ya ce
"Ita d'in ikon Allah ce, Allah ya taya mu rukonta ya kauda idon makiya a kanta,
zamu bada iya karfin mu wajen bata kariya idan har idanunmu zai iya ganin abin cutarwa a gare ta."
Aunty ta amsa da amin amin.
Daddy ya mike yanufi kofa domin zuwa side d'insa, dan dama Umma Karima ce da shi, tafiyar daya taso ne ya tsallaka ya tafi.
har ya d'aura hanu kan handle ya jiyo muryar Feeryal
"Daddy kar ka kwanta a kan gadon ka akwai jiji."
cak yaja ya tsaya tare da juyo wa.
Aunty ta yi saurin cewa
"Ke Feeryal a ina kika ga jijin?."
"Na gani yana cikin pillow Daddy."
Daddy ya tako in da take yarage tsawon sa dai-dai nata ya ruko fad'unta sannan ya ce
"Zai min wani abu ko?."
ido ta wawwaro ta ce
"Eh jiji ne fa Daddy, yana cikin pillow'n ka."
kai ya jinjina ya ja kumatun ta yana murmushi.
Ya juya har ya kai kofa Aunty ta ce
"Jira ni Daddy, Feeryal je gurin Baba Rabi tayi miki wanka."
da gudu tayi kichin gun Baba Rabi ita kuma tabi bayan Daddy.
Tare suka tafi side d'in sa.
suna shiga bedroom d'in sa suka soma binciken cikin pilullukan da suke jere a kan makeken bed d'in sa na alfarma.
kaf suka cire rigunan filon basuga komai ba, suna cikin mai da pillowcases d'in ne idon Aunty ya sauka kan na hannunta da alamun kamar anyi d'inki ta tsakiyar sa, wan da duk pillows d'in na kamfani ne babu alamun d'in ki a jikin sa.
hannu ta saka tana shafa gurin,
ganin hankalin ta ya koma kan sa Daddy shima ya maida hankalin sa kan gurin.
ya mika hannu ya janyo durowar gifen gado ya d'au almakashi ya tsaga gurin, ya zazzage audugar pillow'n a sakiyar gadon sai ga wani d'aurin laya ya fad'o.
Aunty tayi saurin d'auka da mamaki suke kallon sa.
Daddy ya karb'a yana kokarin warware shi Aunty takuma amshewa tana fad'in
"Babu amfanin bud'e wa aga me ya kunsa a kona kawai."
kai ya jinjina.
Tayi saurin tattara audugar ta mai da shi cikin pillon kana ta maida komai in da yake, taje ta d'auko wani sabon pillow ta saka masa pillow cases d'in da ta citewa wancan, ta d'au wanda aka saka layar ciki ta tafi da shi side d'in ta.
a tabaya ta can gefen garden taje ta kona duka da layar da pillow'n.
Aunty da Daddy kad'ai suka san da wannan labarin na Feeryal ko Baba Rabi da kusan komai ya faru a kan idon ta bata fahimci komai ba, sai dai itama da tarin tambayoyin cikin zuciyar ta,
bata kuma da mai bata amsa dan bata da ikon tinkarar uwar gijiyar tata, haka tabar abin a ranta.
Yau Monday Aunty ta gama wa Feeryal shirin makaranta tsaf, suna zaune kan carpet tana breakfast, Aunty ta dube ta cikin hikima ta ce
"Yammatan Ammie, kina ji na ko, kada ki fad'awa wani kina ganin wasu, ko Miemie ce kada ki fad'a mata,
in ba hakaba zasuce ke mayya ce, ko kina so su Ameerah su rika ce miki mayya suna dukanki?."
kai ta girgiza tana yin rau-rau da ido hawaye nason taruwa.
"To ko kin ga kawayen ki kiyi shiru kada ki fad'awa kowa, idan ke da sune babu kowa a gurin sai kuyi wasan ku, kinji ko."
ta ce "Tom."
"Yauwa good girl, to yi sauri ki cinye ku tafi karkuyi latti."
Kamar kullum da ko yaushe har cikin mota ta kaita kafin ta dawo......!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️12
(Bayan shekaru uku)
Wanda hakan yayi dai-dai da shekarun Feeryal 7 ke nan ta kara girma da wayo sosai.
ya yin da kyara da tsangwamar dake sakanin ta da su Ameerah Sahla Nabila, da kuma iyayen su mata ke dad'a ninkuwa.
kawancen ta da shakuwar ta da Miemie kuwa ke kara karfi.
Egypt
Hajiya ce zaune a wani kayattaccen parlour a can ka'sar Egypt.
Kulu na zaune a kasa a gefen ta, tana mammasa mata kafafu.
tun safiyar yau Hajiya ta tashi da masifa, ita fa bata kuma kwanar kasar nan k'asar ta zata koma ita dai gida zata koma taga jikokin ta.
waya ta mika wa Kulu ta na fad'in
"Kulu kirawo min Abubakar, yau bani kuma kwanan k'asar nan, aikin banza kawai yakawo ni ya aje cikin masu jajayen kunnuwa ina rayuwa ni kad'ai kamar mayya,
duk sanyi yabi ya addabe ni, jekoki na suna can ni ina wani gurin,
to yau bazan kuma kwana garin nan ba maza yasa jirgi ya d'auke ni ya mai da ni in da nafi wayo."
Kulu ta mika mata wayar tana cewa
"Gashi Hajiya ya d'aga."
"Yauwa bani ni shi nan."
daga cikin wayar Daddy ya yi sallama yana kokari gaisheta ta katsashi da fad'in
"Kai Abubakar ka kawo ni ka aje nan ni kad'ai kamar mayya, shekaru uku ina zaune kamar wata mara galihu,
kullum nace kasa a maido ni gida sai ka ce to zaka sa,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 20