taras da shi na waya, ta zauna gefe tana saurarar abin da yake fad'a
"Ashirya mata duk abin da ya dace zuwa ranar Monday nake so ta fara zuwa makarantar, a kawo mata uniform da sauran abubuwan bukata gida ranar Lahadi,
Monday kuma ta fara zuwa."
yana sauke wayar Mommy ta bishi da kallon tambaya
"Alhaji wa kuma za'a canzawa makaranta, kar dai ace Ameerah sarkin rigima ce ta kuma tada buren sai an sauya mata wani makarantar?."
ta karashe maganar tana washe baki da jin dad'in fitinar d'iyar tata.
Daddy ya ce
"Ai naga alama Ameerah yanzu tana son makarantar nan, tun da najita shiru bata kuma tada borin a canza mata wani ba,
Feeryal ce za a kaita makarantar tasu."
Da mamaki ta ce "Feeryal kuma wacce Feeryal d'in?."
dan ita tagama mancewa da wata Feeryal a gidan ma, dan tun lokutan baya da suka tab'a tafiya saceta sukaga abin da yafi karfin su.
tun da suka gudu basu sake gigin kuma zuwa ba, a sannu kuma suka mance da batuntu, tun da ba ganin ta suke ba, bugu da kari kuma gargad'in da Daddy ya yi musu, kan duk wanda ya fad'awa hajiya abakin auren ta.
Daddy ya ce "Feeryal y'ar wajen Fad'imatu mana."
wani uban ashar Mommy ta mulmulo tare da buga kirji ta gwalalo ido waje
"Kutumar ubancan Alhaji dama aljanar nan tana gidan nan!? muna shakar iskar numfashi d'aya da ita?
wato Fatima b'oye aljanar nan taye,
ta b'oye bakar gamasheka tayi ta raino harta hab'aka tazamo muguwar dafi,
to wlh bata isa ba
dolen ta tabar gidan nan, dan wlh bazamu rayu da aljana ba,
wai kuma har kake batun sakata a makarantar su Ameera, wlh bazai sab'u ba, bazai yuwu a had'a mana ya'ya da aljana ba, taje can ta karaci tsiyarta."
"Ke Halima ina ruwan ki, idan an sakata a makarantar su Ameerar ke zaki biya kud'in ko me? ki cire bakin ki a lamarin yarinyar nan tun ranki bai b'aci ba, idan aljanar ce sai me ni na shirya taimakon ta."
zumbur ta mike tsaye har tana kumfar baki
"Wlh ba a isa a sakata makaranta d'aya da ya'yan mu ba,
Alhaji kafa fitar da mayyar aljanar nan a gidan na, idan kuma ba haka ba to mu zamu kwashe ya'yan mu mubar mata gidan,
dan bazamu zauna da mayyar aljana ba,
Fatima ta gama asirce ka takawo mayya gida ka runguma wane d'iyar cikin ka,
sabo da haka ka hana Hajiya dawowa kasar ma baki d'aya, to wlh asirinsu sai ya tonu,
babu abun da zai hana ni sanarwa hajiya komai,
dan wlh ina ji ina gani kam bazan zauna da mayyar aljanar ruwa ba!."
Daddy ya gyara zaman sa tare da d'aukar gilashin sa ya saka, ya mai da dubansa kan TV sannan ya ce
"Sai dai kubar gidan nan badai Feeryal ba kam, je ki sanar wa Hajiya daga nan kinsan sauran."
Fuuu tayi waje tana cigaba da zazzage buhun masifa
ba'a isa a had'a musu ya'yan su da aljana a makaranta d'aya ba.
Har ta isa side d'in ta bata fasa masifar ba,
ta kirawo Umma Karima ta sanar mata da abin da ke faruwa.
a bujajan Umma Karima ta taho side d'in Mommy
tun daga bakin kofar parlour ta ke fad'in
"Kar ki gayamin wannan zance Hajiya Halima, ya akayi mukayi bacci ne bamu farka da wuri ba,
Eh lallai Fatima tasan me tayi, wato sai da tabi kowa ta toshe masa baki, tasaka kowa baccin ido biyu ta yadda babu wan da zai kuma batu kan aljanar nan,
hahahaa wlh karya kike Fatima bokanki ya yi kad'an."
tawani saki makirin dariya takaraso cikin parlour'n ta hakimce kan kujera.
Da sauri Mommy ta ce
"Meye mafita Hajiya Karima, idan fa bamuyi da gaske ba, Hajiya Fatima zataga bayanmu."
"Akwai mafita amma bazamu sami ganin Mali ba sai nan da karshen wata sabo da sun shiga mitin natsawon wata guda,
sai dai muyi hakuri zuwa lokacin."
kai Mommy ta girgiza tana ciza yatsa.
Farida da Sumayya dake zaune can gefe suna karatu a littafan makarantar su,
Farida ta rike had'a tana wani yamutsa muska cike da iyayi da manyance kamar uwar mata ta ce
"Yanzu dama har yanzu yarinyar nan tana gurin Aunty? sai da Hajiya ta ce wa Daddy su mai da ita
cikin ruwan da suka d'auko ta shine suka ki, ai Hajiyar zata dawo."
ta karasa maganar cike da zallar manyance da rashin kwab'a irin na iyaya.
idan manya suna magana
sai yaro ya tsoma baki, ba a hanashi ahaka duk
suka gina ya'yan su.
babu kwab'a ko kad'an.
"Ai rannan da naje side d'in Aunty na ganta tagirma kamar Ameerah, har ta ce zata bini Aunty
ta ce ta zauna, kun ga in da tayi kamar Miesho
nacikin Film d'in Tigezam, har idon su iri d'aya
da gashinsu."
cewar Sumayya tana waro ido.
Harara Mommy ta banka mata ta ce
"Ai ke kam albasa batayi halin ruwa ba, uban me ya kaiki side d'in nasu,
ai dole tayi kama da Miesho kin tab'a ganin mai
kama da ita ko a kasashen su ne bare a kasar nan mai tsuffar aljanu, idan na sake ganin ki a side d'in
sai na ci ubanki,
me za'ayi da Fatima gayyar tsiya."
Ajeemal da yanzu shigowar sa ya b'ata fuska
"Mommy to ku ina ruwan ku da yarinyar nan, Daddy
shi yaji zai iya riketa imma aljanar ce meye matsalar ku, tun da Aunty ce ke rukon ta ba ku
ba."
"Dalla tafi can ka ba muta ne guri, me ka sani a rayuwar yau."
cewar Umma Karima.
Mommy ko ashar ta auna masa, ya girgiza kai yaja
kafarsa ya yi gaba.
Lanar Lahadi aka kawo wa Feeryal kayan makarantar
ta, ranar ba zama tun da aka gwada mata taki a cire har sai da Aunty ta lallab'a ta tayi bacci kafin a ka cire mata tana bacci bata sani ba.
Washegari ranar Monday da wuri Aunty tagama mata
shiri, tayi matukar kyau sosai cikin shigar uniform.
tagoya school bag d'in ta, sai tsalle take da murnar zata makaranta.
A can side d'in Mommy su Farida sun gama nasu shirin
suna zaune a dinning suna breakfast.
Mommy ta dube autarta Ameerah tashafa kanta tana fad'in
"Daddyn ku ya kafe sai da yasaka munafukar aljanar
nan a makarantar ku, nasan kuma karshe ajin ku
za'a kaita, kar ki kuskura kirika bari tana zama
kusa da ke, bare ta manna miki damuwa;
idan tamiki wargi kici uwarta da duka,
dan aljanu
tsoron duka ne da su, shegiyar yarinya mayyar aljana 'ya'yana sun fi karfin ki,
kuma kar wata ta raga mata acinku ba jinin ku bace
ita, babu abin da ya had'a ku da ita."
Farida da Sumayya suka girgiza kai alamun sunji gargad'in nata.
A b'angaren Umma karima kuwa
Harsu Bilkisu Saddika Rahama Nabila sun gama komai da komai suna shirin fita,
tun tashin su Umma Karima ke musu bitar tsiya har kawo yanzu da zasu fita,
ta dubi Nabila karamar su ta harare ta tana fad'in
"Ba an iya tab'aki ki bud'e baki haa ba, duk san da naji labarin aljanar can tayi miki kallon banza baki cire kwayar idanunta a hanun ki ba,
sai na ci kutumar uban ki da duka,
babu ragawa sakanin ku,
kurika yiwa shegiya dukar tsiya,
yar tsintuwa ce uban ku ba d'aya ba, ko ya mutu bata da gadon sa,
ita uwar kanzagin nata ma haka zata tashi a tutar babu, bata tab'a nishin haihuwa ba sai dai na kashi a shadda,
maza ku kama hanya bance ku ragarwa shegiya ba."
Aunty ta fito rike da Feeryal.
suna daf da fita bakin get d'in side d'in ta, ta ce
"Tsaya-tsaya y'anmatan Ammie, sa kafar ki ta dama kifara fita da shi, sannan kice tawakkaltu'alallah walahaula'wala kuwwata illa billah, sai ki fita da kafar da ma."
baki ta wace har da d'an tsallenta.
sannan ta ce
"To Ammie,tawalkaltu alallah walahaula wala kuwwata illa billaaaah."
murumushi Aunty tayi, batayi mamakin yadda ta iya addu'ar ba, dan ire-iren addu'o'in nan tana koya mata su sosai.
ta shafa kanta tana fad'in
"Yauwa y'anmata Ammie, to ban da kwad'ayi, ban da fad'a, ayi karatu sosai."
kai ta gyad'a tana murmushi itama, suka fito.
Can ta hangi motar dake kaisu Ameerah school bakin get d'in dide d'in
Hajiya Nafisat ya d'auko Sahla ya karaso zai d'auki Mimi.
suna tsaye motar
ta karaso, direba yafito da sauri yad'an risina ya gaida Aunty kana ya bud'e marfin baya in da Meimei da Sahla suke zaune ciki.
baki Miemie ta washe da ganin Feeryal tana fad'in
"Zakije school inmu?."
Aunty ta maso jikin motar ta d'aga ta cak tasaka cikin motar gefen Miemie tana fad'in
"Ita ma ta zama y'ar school d'in ku yanzu."
aiko Meimei ta matsa ta gyara ta zauna tana ta murna.
Sahla ko fuska ta b'ata sai hararar Feeryal take, ga dukkan alamu itama ta sami hud'ubar tsiyai daga gurun uwar ta Hajiya Nafisat.
Aunty tayi musu Allah ya tsare, direba yaja motar zuwa bakin get d'in side in Umma Karima.
ya d'auki Nabila, su Bilkisu suka leko cikin motar suna hararar Feeryal, sai da motar d'aukar su suma tayi musu hon kafin suka bar jikin motar.
Direba ya ja motar zuwa side d'in Mommy.
su Farida suna tsaye agurin ga motar su ta iso yana ta musu hon,
amma suka ki shiga suna zaman jiran isowar motar da Feeryal take ciki.
direba ya sauka da sauri ya bud'ewa Amerrah ya ce
"Shigo da sauri kada mu makara."
ta leko cikin motar sai kuma ta yamusa fuska ta ce
"Ni dai bazan shiga a matse ni ba, ai a gurin zamata ta zauna sai dai ta fita na shiga."
ta nuna Feeryal da yatsa.
direba ya ce "Haba Ameerah dukkan ku yarane ai nan ya ishe ku, to zo ki zauna a gaba ke."
kafa tashiga bubbugawa kasa tana fad'in
"Ni bazan zauna a gaba ba, sai dai ta fita."
Farida ta ce
"Bazata zauna a gaba ba sai dai ita ta fita ta tado gaba, ko kuma tabi wata motar."
Bilkisu da Saddika suka leko daga motar su suna fad'in
"In bazata fita ba, ki fitar da ita da karfi Farida tun da ba motar ubanta bane."
Da sauri Isa direba ya ce
"A'a ku tsaya, fito ke ki dawo gaba."
ya janyo hanun Feeryal yafito da ita yasakata a gaba.
kana yakoma mazaunen sa yaja motar suka nufi babban get d'in fita daga gidan duka.
su Farida suka shige nasu motar suma bayan sun gama aika mata da mugun kallo.
Suna isa makarantar duk suka fito, Miemie ta rike hanun Feeryal Ameerah ta ce
"Sake ta ba 'yar'uwar ki bace."
Miemie ta make kafad'a ta ce
"Ai Ammah ta ce y'ar'uwa ta ce itama."
harran su tayi
"To kar kubi bayana kubi hanyar ku daban."
Ameerah tayi gaba tana hararar su.
duk wan da yazo wucewa in ys hango Feeryal sai ya tsaya ya kalleta, yara 'yan'uwan ta da kuma manya,
kowa sai fad'i ya ke
"La ga baturiya ta shigo school d'in mu."
ta dawo abin kallo har wad'an da ke cikin ajijjuwa leken ta suke.
Ajin su Ameerah kuwa a ka bata, tana shiga aji kuwa yara suka mike suna fad'in
"Laa ga baturiya laa ga baturiya."
Ameerah tayi musu tsawa
"Dalla ku zauna! waya ce muku baturiya ce to aljana ce, mayya bakuga idon ta ba."
hele yaran suka kuma suna leko fuskarta wasu suna fad'in
"Ga aljana ga aljana."
wasu ko daga cikin yaran basu yarda ba.
Miemie ta ruko hannunta ta ce
"Ku bari fa ba aljana bace 'yar'uwa ta ce."
jin hayaniyar su yasa malami shigowa ajin ya yi musu tsawa, nan kowa ya ni mi guri ya zauna.........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️6
Kullum tare direba ke kaisu makaranta ita da Miemie da Ameerah autar Mommy da Nabila 'yar Umma Karima, sai Sahla d'iyar Hajiya Nafisat kuma dukkanninsu ajinsu d'aya.
Bilkisu Saddika Rahama Farida Sumayya duk suna ajin gaba da su, su yanzu suna ajin farko a secondary, su makarantar su daban.
mazan ma haka.
Duk san da suka dawo daga makaranta da kuka Feeryal take dawowa,
wani lokacin kuma da bushasshen hawaye a fuska,
wani bin da toshasshiyar murya, taci kuka har ta gode wa Allah.
idan Aunty ta tambaye ta saita ce mata
Ameerah ce da Nabila da Sahala suka bigeta suka kuma ce mata mayyar aljana.
Kusan kullum da kuka take dawowa.
Aunty ta rarrasheta ta bata hakuri.
Yau da sukaje makaran ta kuwa ana fita break Ameerah da Sahla da Nabila, suka tara yara suka rika jifanta da takalmar su suna fad'in
"Aljana mayya aljana mayya."
idan yaran zasu bari Ameerah ta ce
"Kucigaba da jifanta aljana ce ta b'ace a cikin mu."
Da gudu Miemie ta iso gurin ta tana zube akasa tanata rusar kuka.
ta tattareta ta kare ta da jikinta tana fad'in
"Kurabu da ita ku kyale ta, Allah zan kira Uncle."
daga can wata Anty'n su taga abin da suke ta taho da bulala aiko duk suka dare suka gudu.
Ana tashi direba yazo d'aukarsu, suna ribibin shiga mota, Miemie ta shige motar ta miko wa Feeryal hanu tana fad'in
"Shigo Feeryal ga guri ki zauna a nan."
Ameerah dake bayanta ta fizgo ta ta rure ta gefe, ta fad'i a kasa ta fasa baki.
"Mayyar aljana bazaki zauna min agurin zama ta ba."
Ameerah ta fad'a tana harararta.
Sahla ta sa kafa ta take mata hanu.
ta saki kara me karfi tana yarfe hannun da dafe bakinta in da ya fashe.
Da sauri Isa direba ya zago in da suke yana fad'in
"Kai-kai ku bari mana zaku ji mata ciwo ne,
sannu kinji tashi zo ki shiga gaba."
ya ruko kafad'arta ya mikar da ita ya bud'e gidan gaba ya sakata.
Ko da suka isa gida ganin ta da fasashen baki, cike da damu Aunty ke tambayar ta ya akayi ta ji ciwon.
kwalla ta fara tana jan shasheka.
ta ruko hanun ta suka zauna kan kujera
"Yi shiru Feeryal garin ya kika fad'i kika fasa baki, kirika yi a hankali kinji ko."
ido ta matse sai ga kwalla, d'an karamin bakin ta ta cuno cikin tsiririn muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ba Ameerah ce ta ture ni nafad'i na fasa baki na ba, takuma ce min yayyar aljana,
Sahla kuma ta takamin hannu da kafarta."
ta karashe magamar da matsar kwalla tana yarfe hannun nata.
shiru Aunty tayi idanunta a kanta acikin ranta take fad'in
"Lallai kuwa akwai damuwa in har suma yaran halin iyayen nasu suka d'auko."
kanta ta shafa alamun rarrashi ta ce
"Yi hakuri 'yanmatan Ammie bazasu sake dukanki ba."
"Ammie wai ni mayyar aljana ce?."
ta jefo mata tambayar fuskarta tam da son jin amsar.
"Inji wa? karya suke ke ba aljana bace kuma ba mayya ba."
"Ai Ameerah da Nabila da Sahla sun ce ni mayyar aljana ce sun tara yara suna ta jifa na."
ran Aunty ya b'aci cikin jin zafin abin ta ce
"Zan ja musu kunne bazasu kara ba,
zo muje ki cire uniform kiyi wanka sai kici abinci ko."
ta janyo hanunta suka shige bedroom...
Washegari kamar ko yaushe da wuri ta gama mata shirin tafiya school ta ruko ta suka fito, can ta hangi motar kaisu school a bakin get na side d'in Hajiya Nafisat zai fara d'auko Sahla ita ce side d'in su ke karshe,
kafin yazo ya d'auki Miemie ya gangaro ya d'auki Feeryal d'in sai kuma Nabila sai Ameerah a karshen d'auka.
bata tsaya jiran sai ya karaso ganin Sahla ma bata fito ba,
suka toko da kafa har zuwa kofar get d'in side in Mommy.
anan suka tsaya harya d'au Sahla Miemie yazo ya d'au Nabila
ya karaso.
dai-dai lokacin kuwa su Ameerah suka fito.
Farida da Sumayya duk suka d'auke kai kamar basu gantaba,
bare ta sa ran samun gaisuwa daga gare su.
dan dama basu da wannan tarfiyyar ganin babba su gaishe shi.
Aunty ta ce
"Ameerah Nabila Sahla, me yasa kuke dukan Feeryal kurika yadda ita a kasa tana jin ciwo? 'yar'uwar ku ce fa itama, ku da zakuga wani yana yi mata ku hana amma ku kuke dukanta, kar ku sake dukanta kanwar ku ce kun ji."
maganar Farida tajiyo daga bayan su
"Ah mu ba kanwar mu bace kada ki danganta mu da ita, meye had'in aljana da mutum."
Aunty ta juyo tana kallon yadda Farida take wani yamutsa fuska.
"Kuma mayya ba mai idon mayu."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.
Ganin yaran suna shirin yi mata rashin kunya ta ce
"Kul ingaya muku ni ba sa'arku bace, zan farfasawa yarinya baki, idan tace zatayi min rashin kunya, wata a cikin ku tasake tab'ata ta ga yadda zanyi da ita."
Gajeren tsaki Farida tayi taja hannun Sumayya ta ce "Zo mu tafi kar mu tsaya b'ata lokacin mu anan."
tawani murgud'a baki cike da fitsara, suka shige motarsu da yanzu ya karaso gurin.
Aunty ta ce
"Dukan tsiya zanyi wa yarinya idan tace zata zage ni fitsararrun banza kawai,
kuma wlh wata a cikin ku tasake tab'ata ta gani."
Isa direba yashiga bata hakuri, kana yabud'e wa Feeryal gaba Aunty ta sakata tana musu Allah ya tsare..
kana ta juya ta koma side d'in ta...
Duk da gargad'in da Aunty tayi musu baisa sun ji ba, yau ma sai da suka tara yara sukayi ta jifanta,
ta dawo da jikin ta fusu-fusu.
kullum kuwa haka suke yi mata, su tara yara suyita jifanta suna ce mata aljana mayya.
abun su Ameerah sai gaba ya ke, lura da yadda suka sako ta gaba, ranar malaman su suka tarasu suka zanesu gaba d'ayan su da yaran da suke tarawa.
Kasancewar ranar juma'a ne da wuri a ka taso su a makaranta,
a mota Ameerah nata jan hanci sabo da ba kad'an ba dukan ya shige ta,tarika hararar Feeryal tana kwafa.
suna isa gida, Ameerah aka fara saukewa kofarsu kafin Nabila, sai Feeryal.
Miemie ta leko ta jikin gilashin mota ta ce
"Feeryal gobe weekend zakizo garden muyi wasa?."
ido Feeryal ta d'an waro cike da jin dad'in abun da Miemie ta fad'a, dan tana son wasa sosai.
tabud'e d'an karamin bakinta tana d'an wawware idanunta irin abin yazo mata a bazata.
ta ce
"A Garden d'in Ammah in ki? zan zo da baby na ma, ke ma zaki zo da naki?"
Miemie ta ce
"Ke ba garden in Ammah na ba, a babban garden na bayan sede d'in su Ya Ajeemal, zaki zo?."
kai ta gyad'a mata, duk da bata tab'a sanin da wannan garden d'in da take fad'a a cikin gidan ba,
ya ma za'ayi ta sani ita da ba ko ina take zuwaba a cikin gidan.
daga makaranta sai side d'in su.
ko side d'in su Miemie'n ma baifi a kirgaba zuwanta side d'in,
shima d'in da Ammie'nta suka je.
Miemie ta koma ta zauna kan sit, direba yaja suka nufi side d'insu.
Feeryal ko ta zuba a guje tayi cikin nasu side d'in tana fad'in
"Ammie na dawo Ammie na dawo."
da sauri Aunty dake shirya abinci kan dinning ta bud'e mata hannu ta taho da gudu ta fad'a jikin ta.
Aunty ta rungume ta tana cewa
"Oyoyo 'yammatan Ammie an dawo ya karatu."
sai ta cirota a jikin ta tana kallon fuskanta da mamakin ganin yau babu hawaye kan fuskar nata.
"Yau ba'ayi kuka ba ke nan?."
kai ta gyad'a
"Ai yau su Ameerah basu bigeni ba, Uncle da Aunty sun ce zasu zane su in suka kuma duka na."
"Ah gaskiya Uncle da Aunty sun kyauta, daga yanzu bazasu sake dukan ki ba."
murmushi tayi sai kuma ta ce
"Ammie gobe weekend zamuyi wasa a garden da Miemie."
d'an shiru Aunty ta yi tana kallon ta,
tasan dole su Ameerah suna gurin.
dan duk ran Saturday and Sunday yaran gidan manya da kananun su suna had'uwa a babban garden d'in gidan, ayi ciye-ceye da shaye-shaye da tand'e-tand'e.
Kafa tashiga bugawa kasa tana ce wa
"Ammie zanje Ammie zanje."
"Feeryal su Ameerah fa zasuje suma, kiyi zaman ki kawai a nan."
d'an karamin bakin ta ta turo gaba tana shirin yin kuka, Aunty ta ja kumatun ta ta ce
"To naji zakije shi ke nan, taho muje a cire Uniform."
Washegari da safe Miemie tabiyo wa Feeryal sutafi,
badun Aunty taso ba ta barta suka tafi.
kaf yaran gidan sun hallara, masu wasa suna yi masu ciye-ciye suna ta kai.
tun daga can Sahla ta hango su Miemie da sauri ta matsa in da Ameerah take, ta nuna mata su da hannu.
Ameerah tawani taune baki tuno da bulalar da tasha jiya akan Feeryal.
da sauri ta tafi ta sha gabansu Miemie, ta ware kafafunta ta bud'e hannayenta.
"Baza ta shiga ba ai nan ba gidan su bane gidan mu ne."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.
Miemie ta ce
"Wasa zamuyi kibari Ameerah."
da gudu Sahla da Nabila suka zo in da suke.
Nabila ta ce
"Yauwa Ameerah kin tuna dukanmu da jiya akayi akan."
"Ai rama kayanmu zamuyi."
cewar Sahla tana gyara hannun rigarta.
ai ko kan kace me suka rufu a kanta duka ta ko ta ina suke kai mata.
Miemie tarika jansu tana fad'in
su daina.
ganin bazasu bari ba tayi gudu taje gurin su Farida
"Aunty Farida Aunty Bilkisu ku hana su Ameerah dukan Feeryal, gafa yadda suke dukanta."
Farida ta waigo ta kalli in da suke ta ce
"Suci ubanta dan uwarta wayace tazo nan ko an gayyace ta ne."
Bilkisu ta ce
"Su faffasawa shegiya aljana baki ko zata b'ace mana a gida."
Da gudu Miemie ta juya ganin ba taimakon ta zasuyi ba,
tayi gurin Ajeemal da ta hango yafito daga b'angarensu, zai fita damuwar sa.
"Ya Ajeemal Ya Ajeemal gasu Ameerah can suna dukan Feeryal."
da sauri ya yi in da suke yana fad'in
"Kai bakuda hankali ne."
aiko suna ganin sa suka ruga da gudu suka bar gurin.
ya karaso da sauri ya d'aga Feeryal dake yashe a kasa tana kuka, sun mata lilis sun farfasa mata baki.
karkad'e mata jikinta ya yi ya ce
"Yi hakuri kiyi shiru ki tafi abin ki zan rama miki."
ta tafi tana kuka Miemie na biye da ita tana bata hakuri har side d'in su.
Aunty na ganin Feeryal da kuka ta taso da sauri
"Lafiya Feeryal ke Miemie me ya same ta haka?
ai sai da nace bazaki je ba kika matsa sai kin je."
"Ameerah da Nabila da Sahla ce suka taru suka bigeta."
cewar Miemie kamar zatayi kuka.
rai b'ace Aunty ta ce
"Irin wannan duka haka sai kace jakarsu, ai ni da ma nasan za'ayi haka shiyasa tun farko banso ki je in da suke ba."
ta janyo hannun Feeryal tana dudduba jikinta.
duk a kwakkwarjane sun jijji mata ciwo har yana fidda jini.
Mayafinta ta zara ta janyo hannunta ta ce
"Zo muje idan ba layi na ja wa yarannan ba bazasu barki kisha ruwa ba."
Suna isa garden ta cafko hannayen Ameerah da Nabila da Sahla.
ta ce
"Haba ku kuwa Ameerah Sahla Nabila, me yarinyar nan tayi muku haka,
zakuyi mata irin wannan dukan?
babu kyau cin zali fa, ku duba kuga yadda kuka jijji mata ciwo har jini yake fiddawa
haba ku kuwa,
ai ba ita ta sa a bige ku a makaranta ba jiya,
ku da kuke dukanta kullum ta tab'a ramawa?
kar ku sake mata irin wannan dukan idan kuka kara kuma sai na zazzane ku da bulala,
yanzu ku da girman ku Farida Sumayya Bilkisu Saddiqa,
kuna kallo suyi wa yarinyar nan irin wannan dukan bazaku hana su ba, haba ku kuwa"
Hanci sama duk suka d'aga kowa ta kawar da kanta kamar basa ma jin abin da take fad'a,
Farida kam uwar 'yan rashin kunya sai da ta had'a mata da kallon banza.
bata bi ta kansu ba,
ta jajja kunnuwan su Ameerah tanai musu gargad'in kada su kara.
"Kada ku kara idan kuka kara zan d'auki bulaba, idan tayi muku laifi kuzo ku fad'a min, ni zanyi mata hukunci dan bata isa ta raina ku ba dan kune yayun ta."
Daga bayan su tajuyo muryar Umma Karima tana tafa hannaye da fad'in.
"Iyee da kyau mana bashakka, sakar musu kunne kada ki tsinke dan baki da asara,
akan wannan aljanar ruwan zaki ni mi ki tadawa ya'yan mu hankali, har da wani kabaibaye su kina shirin b'alla musu hannaye da kunnuwa;
to maza sake su,
ke kenan ma da baki san kalar nishin haihuwa da wahalarsa ba kika ji zafin ta, bare mu da muka san wuyar sa,
tsintacciyar cikin ruwa mara galihu aljana-aljana mayya-mayya akan ta ne zaki saka mana yara gaba,
to ko da bakin wasa ki tsaya matsayar ki, dama duk juyar mace sai ka same ta da bakin mugunta kan ya'yan mutane,
dan bata san wuyar d'aukar ciki da haihuwa ba,
shi yasa baki san zafin ya'yan ba, ko wacce kalar mugunta ma zaki iya yi musu, batare da kinji ko d'arrr a zuciyar ki,
kibar 'ya'yan gida su sakata su wala suyi yadda suke so, kada ki sake kice zaki takura musu akan wata agola tsintacciyar cikin ruwa aljana mai idon mayu."
Ta iso fuuu ta fizge hannayen su ta kad'a keyarsu ta ce
"Maza kuje ku sakata ku wala babu wanda ya isa ya takura muku ku da gidan uban ku,
wlh sai yarinyar nan tabar gidan nan, ba'a isa a takurawa 'ya'yan mu a kanta ba."
Murmushin takaici Aunty ta yi sannan ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 20