sauri ta isa jikin kofar parlour tarika bubbugawa.
Aunty ta taso ta bud'e, ga nin Hajiya ce tashiga yi mata sannu.
ko amsata batayi ba ta bangaje ta tayi cikin parlour'n
"Ina kike tsintacciyar mage fito nan tun da ba gidan ubanki bane, zo ki koma in da kika fito."
Aunty ta durkusa gaban Hajiya ta had'a hannaye biyu tashiga magiya da rokon ta
"Dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri, idan ta fita a daren nan ina zata je,
bata san kowa ba sai mu, kiyi hakuri dan Allah Hajiya gari ya waye."
"Bafa zan bari takara ko da kwana d'aya ne a gidan nan ba, bari ma ki gani naje na taso direba yazo ya d'au keta ya fita da ita, can takataci tsiyar ta a can."
ta juya ta yi waje fuuu.
tana fita Aunty ta d'aga waya ta danna lambar Daddy wan da ita kad'ai take da shi a gidan,
idan duk ya kashe sauran wayoyin sa baya tab'a kashe waya mai d'auke da wannan layin, da yanzu take kira.
Feeryal da har tafara bacci tajiyo hayani, ta mike ta fito.
tsayuwa tayi tana kallon Aunty dake tsaye cikin parlour tana hawaye.
da gudu ta karaso inda take ta rungume ta itama ta saki kuka
tana fad'in
"Ammie bakuwa mai duka ne tazo ai naji maganar ta, Ammie tare zamu tafi ni dai bazan tafi na barki ba."
Bubbuga bayanta ta shiga yi tana fad'in
"Yi hakuri yi shiru Feeryal, babu in da zaki je,
kafata kafar ki duk in da zaki shiga ina gun, sai dai mu bar gidan tare tun da ba gidan aljanna ba ce."
"Kada b'acin rai yasa ki fad'in haka,
shin kin mance anan gidan zaki nimi aljannar taki iye Fad'imatu."
maganar Daddy daga cikin wayar dake rike a hannunta wacce ta ma mance da ta kirasa har yama d'aga yana sauraron su,
yayin da yake jin zafi mai gauraye da d'aci a duk fitar sautin kukan su.
Daddy yaci gaba da fad'in
"Hajiya ce ko? kuyi hakuri uwace a gare mu babu yadda muka iya da ita, yazama wajibi muyi mata biyayya amatsayin ta na uwa,
Fad'imatu lallai yau nasan an kure ki har bango, tun da naji fitar kalmar nan daga bakin ki,
kiyi hakuri har na dawo zan yi wa tufkar hanci."
Yana kaiwa nan ya katse kiran.
Ya kunna d'aya daga cikin wayoyinsa.
Lambar Hajiya Bishira ya kira, ya ce ta bawa Hajiya wayar, yakira wayarta bata d'aga ba.
Hajiya Bishira ta shaida masa Hajiya ta fita, taje side d'in Aunty, ya ce
tayi sauri ta kai mata wayar.
Hajiya Bishira na fita can ta hango Hajiya kofar d'akin direbobin gidan, tana bokarin buga musu kofa.
Murya ta d'aga ta dakatar da ita daga bugun kofar nasu.
da sauri ta karaso ta mika mata wayar tana fad'in
"Gashi Yaya na magana."
ta karb'i wayar ta kai kunne tana ce wa
"Ka gama abin da kaje yi tsaf abin ka, bama sai ka dawo ba, yanzu nazo d'aga direba ne ya fita da ita."
"Hajiya kiyi hakuri na dawo tukun ni da kai na zan fita da ita nayi miki alkawari."
Da kyar Daddy ya shawo kan Hajiya akan idan ya dawo zai d'auki Feeryal d'in ya mai da ita in da suka d'auko ta.
Washegari kuwa da zasu tafi makaranta, Hajiya ta fito ta tsare ta ce Feeryal bata isa ta shiga moto d'aya da jikonkin ta ba.
Feeryal ta d'an kalleta a tsorace dan ba karamin tsoron matar take ji ba,
tun da aka ce mata tana duka, Feeryal kuwa ba karamin tsoron duka ta ke ba.
Hajiya ta buga mata wani uban tsawa
"Daina kallo na da wad'annan idanun naki masu kama da na mayu, da jan fuska kamar nunannen gwanda,
anya wannan yarinyar, ta ya za'ayi a ce mutum ce ma, habawa wannan irin kyau haka hankali bazai d'auka ba, wasayyahuuu ya tsaya a kanki li'eeelafi aniya bi aniya, nafi karfin ki da jikoki na."
Feeryal tayi kasa da kai tana kyafkyafta ido zatayi kuka.
ta zuba mata rankwashi a kai
"Munafuka wuce ki bar nan kar ki shafa mana annoba."
ba zato taji saukar rankwashi a ka.
a birkice ta saka hannu tana yamutsa kan, nan da nan idanun ta suka shiga tsiyayar da kwalla.
Hajiya ta kad'a keyar jikokin ta suka shiga mota direba ya ja su suka tafi.
ta juya tana bin Feeryal da harara
"Ai ke da shiga motar nan sai dai ki ganshi da ido mayya mai zubin aljanu, sai ki taka a kafa kije makarantar."
ta wuce ta barta nan tsaye.
tazo daf zata shige side d'in ta kafarta ya hard'e.
ki kake shirimm ta zube kasa kan gwuiwowinta.
Kururuwa mai had'e da salati Hajiya ta sake, tana fad'in
"Wayyo jama'a kuzo kafata, shike nan kafar ta b'alle
yafita, jama'a kuzo jama'a kuzo!."
Feeryal tayi saurin kai hannu ta toshe bakinta da dariya ke son kwace mata, ga kuma tsiraren hawaye a kan kyakkyawar fuskanta.
tana kallon inda Hajiya ke zube, sai kuma ta girgiza kanta.
da alama dai magana take da kai.
A guje security suka taho, Ajeemal Shamsuddin Zaraddin Faisal da suka fito zasu tafi school, suka karaso a guje.
kowa na tambayar yaya me ya faru lafiya?.
Hajiya takuma wage baki tana fad'in
"Ku kirawo mai d'auri na karye wayyo Allah na shike nan nazama gurguwa."
Ciccib'arta sukayi suka shige da ita parlour'n ta.
dan sunga alamun da gaske ko tsayuwa bazata iya ba bare ma tafi.
Dad da Abbieh ne suka shigo hankali tashe.
nan da nan suka kirawo mai d'auri.
Sai a lokacin su Ajeemal suka fito dan in suka dad'a b'ata lokaci zasu makara.
Har lokacin Feeryal tana tsaye a gurin har suka karaso inda take,
tun kan su iso Zaraddin yakafe ta da ido, sai da ya iso daf da ita kafin yawani lumshe ido yaja numfashi kana ya fesar tare da kuma bud'e su a kanta.
murmushi Shamsuddin ya mata yana cewa
"Badai latti kika yi ba Feeryal?."
kai ta girgiza.
Faisal kuwa cewa ya yi
"Shine Miemie bataje ta kira ki ba suka tafi, suka bar ki."
nan ma shiru tayi tana wasa da 'yan yatsunta.
Ajeemal kuwa da ke da tabbacin Hajiya ce zata iya hanata tafiya kamar jiya ya ce
"Zo muje mu sauke ki sai mu wuce."
Suka karasa parking lot, Zaraddin ya yi saurin bud'e gidan baya ya shiga yana fad'in
"Shigo nan ki zauna."
"A'a dawo gaba ku ku zauna a baya."
Ajeemal ya fad'a yana bud'e mata gaban motar, fuska a d'aure, dan tun d'azu ya lura da yanayin sa tun da ya ganta.
tana zama ya rufe ya zaga ya shiga mazaunin direba suma suka shiga yaja motar suka bar gidan.
Sai da suka sauke ta a school d'in su sannan suma suka wuce nasu school d'in.
A gida kuwa maid'auri yazo ya duba kafar Hajiya,
ya ga gwuiwar ta ce ta goce, da kyar aka mayar aka shafa mata magani, Hajiya tayi shame-shame tana sallallami.
mutan gida sai shigowa suke ana gaidata.
dangi na kusa ma tuni sunzazzo.
Satin Hajiya guda ke nan tana zaune tana jinyar kafa,
har kuma yanzu Daddy bai dawo ba yana can kasar China,yana gudanar da wasu harkokin sa.
sai dai kullum suna video call yana ganin yanayin jikin nata.
duk da cuwon dake jikin Hajiya baisa ta saduda ba,
tana daga zaune tana bada umurni da oda.
haka ta kekashe kasa ta hana a rika d'aukar Feeryal a motar kaisu school, takuma sa dole Daddy ya canza musu wata mota yana can kasar bai dawo ba,
a cewar ta wai akwai abu a ciki tun da Feeryal ta shiga.
Ajeemal ne ke kai ta school a motar sa, wani lokacin ya jirata har su tashi idan bashi da abin da zaiyi, wani lokacin kuma ya ajeta yaje ya dawo ya d'auke ta.
baya tab'a bari Zaraddin ya kaita ko ya d'aukota, ko baya da lokaci, yakan iya kashe damuwar sa wajen kaita da d'auko ta,
sau d'aya yatab'a sa Shamsuddin da Faisal suka tab'a d'aukota, ranar d'in ma yana class ne bai fito ba, dan su yana da d'an tabbacin nutsuwa tare da su.
Aunty na kichin tana aiki Feeryal da ta dawo daga school ta shigo.
ta fad'a jikin ta,
Aunty tayi murmushi ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo 'yanmatan Ammie, an dawo ya school?."
d'an karamin bakin ta ta cuno cikin tsiririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ammie wai ba ke kika haife ni ba?."
hannu takai ta toshe bakin ta,
sannan ta waro ido ta ce
"Inji wa? ni na haife ki Feeryal duk wanda ya fad'a miki yafad'a ne kawai, kar ki yadda ki sawa ranki hakan,
to idan ba ni na gaife ki ba to waya haife ki, ko akwai wata mamarki ce a gidan nan?."
kai ta girzaza tana kallon fuskar Aunty.
kumatun ta taja ta ce
"Ko in kaiki gurin wata ce tazamo mamarki tun da kin gaji da ni."
da sauri ta fad'a jikin ta tana cewa
"O'o Ammie ni dai bazanje ba."
dariya Aunty taji ta dad'a rungume ta tana jin kaunarta cikin zuciyar ta.
baki ta kuma cunowa ta ce
"Basu Ameerah bace suke fad'a, wai ke ba ce mamata ba ce kuma Daddy ma ba babana bane, wai ni mayyar aljana ce."
da sauri Aunty ta ce
"Karya suke ni ce nan mamarki Daddy kuma baban ki, kar ki sake biye musu,
oya je ki cire uniform kiyi wanka kizo, ko nazo nayi miki."
kafad'a ta make
"A'a ni zanyi Ammie Miemie tana min dari ta ce wai har yanzu ana min wanka."
"To in banda Miemie ai itace gaba da ke, in ita ta iya ke da sauran ki."
"Ni dai Ammie na iya nima."
"To je jiyi yanzu anjima da daddare da kaina zan miki."
ta juya da sassarfa tayi ta fice a kichin d'in..
Hajiya ce kwance a kan makeken gadon ta tana sharara bacci sai gwarti take saukewa.
daga cikin bacci taji ana kiran sunan ta, ana jajjan kafafunta.
A firgice ta mike tana fad'in
"Wayyooo ni Hanne nayi mugun ji, waye waye anan, Bishira wane ne?."
ta lalub'o makunni wuta dake d'aure a kan bedside ta kunna.
d'akin ya bada haske ba mai yawa ba.
can kuma hasken ya soma karuwa da kansa, yayi wani irin bau ya haske d'akin gaba d'aya lokaci guda.
a take kuma d'akin yasoma amsakuwar magana had'e da tafi tamkar ana gad'a cikin d'akin.
ga wasu irin maganganu barkatai wannan nayi wancan nayi fad'i a ke
"Hajiyaaaa taso muyi gad'a, taso ke ce da shiga fili yanzuuu."
Hajiya da fitsari ke kokarin kwace mata sabar azabebben tsoro tashiga fad'in
"To to laaaha'ilaaaha'illallahu, wasayyahu wasayyahu wasayyahuuu, li'eelafiiiikuraishin,
dan girman Allah kuyihakuri wlh lalurar ido gare ni, ga kwab'ewar gwuiwa, ta ina zan fara,
kuyi min rai."
"Bafa zamu kyale ki ba ke ce da shiga fili taso ki fad'o mu cab'e."
Hajiya ta kwalala uban ihu
"Wayyo Allah jama'a ku kawo min d'auki yaukam nayi gamo,
dan Allah dan ma'aiki Rasulullahi nagama ku da Allah kui hakuri ku kyale ni,
ta ina zan fad'o bana ganin ku, tun zamanin yaranta rabon da nayi gad'a,
wlh babu kafar yin gad'a kuyi hakuri kuje gurin masu kafa."
"Dole ki taso Hajiyaaa ko mu d'aga ki, kuyi sama da ke."
Ba sai ga Hajiya ta mike da kafafunta ba, dama tun sati biyu aka ce ta gwada takawa ta ki ta ce wai da saura tukun guiwar bata gama had'ewa ba.
"Ku taro ta zata gudu."
tuni Hajiya ta saki fitsari, jiki na kakkarwa ta nufi kofa fitsari na zuba,
kafin ta isa kofar ta bud'e tazo daf zata fice kofar yakuma kullewa garamm.
Hajiya tayi dakuwan 'yan bori a kasa, daram da d'uwawu.
ta rufe idanunta gam tana fad'in.
"Yasin kafa dubu, li'eelafi kafa bakwai, lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya,
yasin me manjagara yakwasheku ya zubdaku can kuyi nesa ku tsaya a can, wasayyahuuu wasayyahuuu ku tsaya a can laaaa'ilaaaha'illahu,
aniya bi aniya aniya bi aniya, fatiha da salatin annabi."
Ji kake kuuu cikin Hajiya na bada sauti, tsoro iya tsoro firgici iya firgici a tare da Hajiya.
sai ihu da kwalala take kamar makogoron ta zai fita.
A tare Hajiya Bishira da Kulu suka fito daga d'akunan su, suna rige-rigen shi ga d'akin Hajiya.
a bakin kofa suka ganta tayi zaman dirshem tana kwarara ihu.
duk sukayi kanta suna had'a baki wajen fad'in
"Lafiya Hajiya me yafaru, ciwon kafar ce ta motsa? subhanalillahi!."
Jin moryoyin Hajiya Bishira da kulu yasa Hajiya bud'e idanunta.
ta kankame kafafunsu kad'an yarage ta zubar da su kasa.
Hajiya Bishira ta kara hasken d'akin ta hanyar kunna makunnin koyayen wutan da sukayi wa tsakiyar p.o.p d'akin kawanya,
tamkar kwalliya ta sama.
d'akin yabada haske sosai tamkar tsakiyar rana.
Hajiya tashiga binsu da kallo da alama dai yanzu ne ta dawo cikin hayyacin ta.
Hajiya ki sake mu kar ki yardamu a kanki."
cewar Bishira tana janye kafafun ta daga rukon da tayi musu.
cikin sauke numfashi'n tsoro irin wanda mutum ya kub'uta daga azaba Hajiya ta ce
"Nayi gamo gamo nayi da bakaken aljanu, ku kaini bayan gida ciki na ya rud'e."
"Hajiya wa ya kawo ki nan to ke da ba tafiya kike ba?."
cewar Kulu tana rike hab'a.
"Ban san ya akayi nazo nan ba ina ga su suka kawo ni, ke da'alla kamani ku kaini masai ko sai nayi anan nabar muku aiki."
Suka tallafe ta ta mike Hajiya ta d'aga kafa tana d'ingisawa.
"Hajiya kin warke ashe."
Kulu ta fad'a tana bin kafarta da kallo sai kuma ta waro ido
"Me zan gani Hajiya fitsari kamar kikayi a zaune."
"Har uwar fitsari ma zanyi a nan in ya kama,
da'alla ku kaini bayi na matsu."
Hajiya Bishira ta bi gurin da kallo tambas fitsari ne tun daga bakin gado har zuwa inda suka same ta zaune.
Suna kaita bayi ta sunkuya gudawa daya murd'e ta, zasu fita su bata guri, ta ce babu wan da ya isa ya fita su jirata sai ta gama.
Suna fito da ita takuma cewa su koma tana jin wani.
sai da ta shiga bayi sau biyar a kai a kai.
Tana zaune a bakin gado tana sauke numfashi, su Hajiya Bishira da suka gama tsaftace cikin d'akin da sarkake shi,
suka dawo inda take suna yi mata sannu.
Kulu ta dube ta tana fad'in
"Sannu Hajiya dare d'aya har kin zabge, wai ya akayi mu bamuga bakaken aljanun ba sai ke, ta ina suka shigo ne, ko dai mafarki kika yi,
anya ba mayu ke bibiyar ki ba kuwa?."
"Uhum ke dai bari Kulu ko ta sama ko ta kasa sai Allah, ina bacci narika jin ana kira na, da na amsa kiran da sun tafi da ni, kin san ba'a amsa kiran dare kana amsawa to ka tafi ke nan,
yazama dole a sawa gidan nan kafi, tun ba yau ba nake fad'awa Abubakar ya sa kafi a gidan nan sabo da miyagu yaki ji, to ba ga irin ta ba da babu wani mugun da zai iya shigowa gidan nan, kota sama ko ta kasa ko a b'oye ko a bayyane,
badun nayi ta addu'a ina ja musu yasin ina sauke wa ba da sun tafi da ni."
D'ip Hajiya tayi jin motsi karkashin gado ta kankame su Kulu ta na fad'in
"Yasin kafa dubu li'eelafi kafa bakwai lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya fatiha da salatin annabi wasayyahuuuu."
Hajiyq Bishira ta ce
"Hajiya bafa komai kinga ni kyanwarki ce gata can fa, magen ki ce a kasan gado taga haske ta fito."
"Kin tabbata mage ce."
Hajiya ta fad'a tana zazzare ido.
"Itace ba gata nan ba ta fito, watakila ma ita ce ta razane ki d'azu."
"Um-um ba ita ba ce magana naji bilhakki, kyanwa tana maga ne."
"Hajiya in zaki kwanta kirika addu'a, babu abin da zai same ki insha'allahu."
"Ai ni yau naga karfin addu'a baki ji yanzu ma nayi ba, ai addu'a tana da amfani yana kora miyagu."
"Ai Hajiya wannan da kikayi yanzu ba addu'a ba ce, ki karanta shi a karance ba ki fad'a irin yadda kika fad'i yanzu ba,
ayatul'kursiyu da suratul iklas da falaki da nasi, a duk sanda zaki kwanta ki karantasu sun'ishe ki komai da komai,
zasu karake daga sharrin komai."
Hajiya ta mara baki tana fad'in
"Ahaf wannan addu'ar da kike gani tun muna yawo da jajayen sawu muke ganin amfanin sa, duk shi mukeyi da kawayen mu, muyi fad'a da uban kowa mu kwana lafiya, ai ko munga amfanin sa."
Hajiya Bishira ta girgiza kai tana fad'in
"Allah shi kyauta."
Sun so tafiya d'akunan su Hajiya ta ce sai dai fa su zauna su waye gari anan tun da gari yakusa waye wa.
Washegari Hajiya ta d'agawa Daddy hankali a waya wai sai dai yadawo yanimo kafi a sa a gidan, miyagu nason ganin bayan su.
ya ce mata to yakusa dawowa.
Shirye-shiryen bikin Farida nadad'a matsowa.
uwar amarya Mommy ba zama.
anata kai kawo yadda biki zai gudana baza aji kunyar kawaye ba.
Mommy ce zaune a parlour tana waya da Hajiya'n Dubai wata kanwar su Daddy ce, wacce take da zama a can kasar Dubai.
takan zo Nigeria jifa-jifa dan mijinta yana nan Nigeria ita kuma tana can Dubai da 'ya'yan ta,
zaman ta yafi yawa a can.
Mommy dake rike da d'aya wayarta tana dudduba wasu arnan kayan d'aki da Hajiya'n Dubai ta turo mata,
ta gyara rukon wayar dake kare a kunnen ta tana cewa.
"Gaskiya Hajiya'n Dubai wad'annan set ukun duk sun min, duka za'a bada kud'in su a sako a jirgi a kawo."
daga cikin wayar Hajiya'n Dubai ta ce
"Wai dama Hajiya Halima ba wucewa da su can UK d'in za'ayi ba, Nigeria za'a kawo su?."
"Eh Nigeria za'a kawo su a zuba mata su a gidan ta dake nan, idan sun shigo kasar yazamana da suna da masaukin su mai kyau, a can UK kuma ai shi angon ma yagama shirya gidan sa da ke can yazuba komai babu abinda za'a tafi dashi daga nan,
idan kunje abinda kuka ga babu sai kuyi odan sa acan d'in kawai."
"Ah yayi hajiyar mu, ai harka ta jin kunya baiyi ba,ai ni sam bana son harkar karanta,
me za'ayi da jin kunya kana cikin kawaye karika kunyata, idan fa kikaga gidan da za'a zuba kayan nan ba wani na arziki bane, ba nagani a fad'a bane ,
kawai a basu gida, kada mushiga kunyar kawaye, ace kamar mu aga gidan 'yar mu bai taka kara ya karya ba,
d'iya ga Alhaji Abubakar Fiya guda ace gidan ta zubin na talakawa, haba ina bazamuji wannan kunyar ba, kawaye suzo daga nesa suna yi mana kallon kasa-kasa, kallon raini,
kai ina da wuri ma zan shigo Nigeria naje na duba gidan da kaina,
idan beyi ba gaskiya za'a basu gidan da za'a zuba kayan nan,
dan wlh ban yarda da harka ta jin kunya ba."
Mommy ta sheke da dariya tana fad'in
"Hajiyar Dubai tamu, ai duk in da za'ayi bazan bari aji kunya ba, ko kin mance wane ne mijin Farida ne, Faruoq-Al'Hussain ne fa, kin san naira kuka take a family'n Al'Hussain,
da kanta Farida ta zab'i gidan da take so a cikin gidajen da mahaifinsa, Al-Hussain ya ce ya zab'i wanda za'a d'auko masa amaryarsa a saka ta ciki kafin bayan biki da kwana biyu su bar kasar."
"Yauwa yanzu naji zance ai ni na ma mance da ko d'an gidan wa d'iyar tawa zata aura, ah gaskiya mun baiwa jin kunya baya, Faruoq-Al'Hussain kai ka dace da d'iya ta."
suka sheke da dariya.
A b'angaren amarya Farida ma fa ba zama, duk da ba a kasar nan zasu zauna da mijin nata ba,
a can UK in da yake aiki zasuyi zaman shekaru goma kafin su dawo Nigeria,
sabo da aikin sa da yake yi a can shekaru goma zaiyi ya gama ya dawo gida Nigeria.
ana ta shiga da fita.
Sai ana biki saura sati Daddy ya dawo.
aiko Hajiya ta dira a kansa ko huta gajiya baiyi ba, ta ce ya d'auki Feeryal ya mai da ita tun da ya dawon.
sai da ya yi ta lallab'a ta ya ce tayi hakuri a gama biki tukun zai mai da ita.
da kyar ta yadda.
Tuni gidan Alhaji Abubakar Fiya ya d'auki manya manyan baki na kusa da ma na kasashen ketare.
ciki kuwa harda Hajiya'n Dubai da iyalenta,
da kuma kayan d'akin da Mommy tasa akayi odan sa daga Dubai.
Tun ana saura kwana uku biki aka fara gudanar da shagulgulan biki,
a manya manyan Hall.
Amarya Farida ta amsa sunanta amarya dan kuwa dubbannin d'arurruwan mutane ne suka shaida d'aurin auren, Farida Abubakar Shitu Fiya da angonta Faruoq-Al'Hussain.
Bayan d'aura aure jama'a suka soma taruwa a Hall na musamman dake a cikin gidan ta can baya,
wan da aka tanade shi sabo da tarurruka, na cikin gida idan ya taso.
nan aka tanada domin gudanar da walima bayan d'aurin aure.
Aunty ce ke saukowa daga saman bene ta cab'a kwalli had'i da gwala-gwalai, tayi matukar kyau ta dawo yarinya d'anyiwa sharaf tammar ita ce amaryar,
sai baza kamshi take.
Aunty Hindu d'iyar baffan su Daddy ta saka gud'a tana fad'in
"Kaga Amarya a gidan Alhaji Abubakar Fiya, wlh babu wan da zai ganki ya ce shekarun ki goma da yin aure,
tamkar kece amaryar ai dole ki rika rikita yayan namu, tsaruwa iya tsaruwa."
dariya ta bisu da shi ganin yadda duk parlour'n suka rud'e da zu-zu-ta-ta.
Aunty Hindu ta d'aga wayarta tana cewa
"Tsaya dan Allah na d'auke ki na turawa Yaya nasan tukuicina na daban ne yau."
"A'a huta abin ki ai gani a zahiri yafi gani a hoto, yanzun nan ma gurin sa na dosa."
Duk suka sheke da dariya har suna tafawa.
"Da gaskiyar ki wlh je ki gwada masa ya gani a zahiri wannan irin wanka, ba shigar bane sukayi miki kyau ke ce kikayi wa shigar kyau."
ita dai dariya tayi musu tayi waje...........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
🅿️14
Side d'in Daddy ta nufa ta kofar baya, dan tasan ta ainahin kofar kam cike yake tam da mutane.
ai ko hakan take har cikin babban parlour'n sa ba'i ne maza ciki a ciki.
D'akin kwanan sa direct ta wuce, tana shiga ta kirasa a waya.
ganin mai kiran nasa yasashi mike acikin jama'a ya nufi bedroom d'in sa, domin amsa kiran.
ya tura kofar yana kokarin kuma maida kiran dan ya yanke,
sai ganin ta ya yi tsaye cikin d'akin.
ido ya bud'e da kyau ya kura mata su, itako murmushi take sakar masa.
a hankali ya tako ya iso in da take.
hannu ta mika ta sakalo wuyan sa, tana cigaba da aika masa murmushi.
cikin sanyin muryar ta mai kara masa kaunar ta.
ta ce
"Daddy tun d'azu nake son ganin ka mutane sun min fin karfi."
ta karasa maganar da kashe masa ido.
wani numfashi ya sauke, sai kawai ya rungume ta ya na fad'in
"Godiya ya tabbata ga Ubangijin daya mallakamin wannan kyakkyawar tsuffar."
ya d'ago ya manna mata kiss a goshi.
d'an zame jikin ta tayi tana fad'in
"Daddy ka fara tsufa fa."
"Ina da ke ai ita ma tsufar bata isa ta dumfaro ni ba, sai dai ta tsaya a iya shekaru."
dariya ta yi ta ce
"Yau fa ka aurar da 'ya tsufa ya dad'a bayyana ga furfuran ka sun karu."
ta karashe maganar da muryar dariya.
kumatun ta yaja ya ce
"To kar ki bari tsufar tai mana tasiri, ki san yadda zakiyi ki yake sa tun kafin a fara kiran mijin ki da tsoho, shi ke nan ke ma kin tsufa."
dariya duk sukayi wa junan su.
Ya matsa can jikin bedside drower ya danna ma dannin bud'e sa, gilashin jiki ya zuge, yad'auko d'aya daga cikin makullan motocin da suke ciki.
ya zo ya mika mata.
ta karb'a tana bin key'n da ido sannan ta ce
"Na mene ne wannan?."
ya ce "Naki ne tukuicin wannan kwalliyar."
wani lallausar murmushi ta sake ta rungume shi tana fad'in
"Godiya marar adadi, naji dad'i dad'in da bazai fad'u ba."
murmushi ya bita dashi, yana matukar jin dad'i ya yi mata kyauta yaga tana nuna yabawa da jin dad'in kyautar da ya yi mata.
yana daga cikin abin da yake dad'a kara girman fadarta a cikin birnin zuciyarsa.
Bata jin kanta ita wata ce dan mahaifinta yana da dukiya, ko min kankancin kyauta takan nuna jin dad'in ta mara misaltuwa.
akasin sauran matansa da iyayensu ba koman komai ba sai fad'in ran tsiya.
Da sauri Miemie ta shige side d'in Aunty, ta haura sama da sauri tashige d'akin Feeryal.
tana zaune sunata wasa da kawayen ta, wan da ita take ganin su.
Miemie ta ce
"Feeryal taso muje ayi mana kwalliya ga mai kwalli tana kan yi wa su Ameerah, a side d'in Hajiya,
muje gurin walima ke bazaki je bane?."
"Ni bazan je ba Ammie na ta ce nazauna nayi wasa na a nan kije kawai abinki."
"Dan Allah taso muje gasu Umaima'n Dubai ma sun zo zo muje ki gansu."
ta janyo hannunta suka fita.
tun kafin su karasa sauka daga stairs hankalin 'yan cikin parlour'n ya dawo kansu.
wad'an da dama sunsan Feeryal d'in tun tana jaririya,
suna ta mamakin girman ta da yanayin tsarin zubin halittarta.
wad'an da kuma basu santa ba suna binta da kallon rashin sani, kallon itama daga cikin ba'in da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 20