Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka zo daga kasashen turai suke mata. Har sun zo shiga parlour'n Hajiya, Feeryal tayi baya da sauri a matukar tsorace. Miemie ta ce "Hajiya bazata miki komai ba zo muje, kar a gamawa Ameerah a kama yi ma wani." hannu Feeryal ta d'aga baki na rawa ta ce "Ga mage can ni dai bazan je ba." "Baya komai fa ki zo mu shiga." "A'a ni bazan shiga ba!." tayi maganar tana ja da baya a mugun tsorace, tamkar zata shid'e. "Ke Miemie me kike yi a nan ana can anayi wa su Ameerah kwalliya ke kina nan, gashi har an watse an tafi gurin walima, kiyi maza kije a yi miki." cewar Hajiya data fito zata gurin walimar tana gyara zaman mayafin ta. ido ta gwalalo kan Feeryal dake ja da baya da baya. "Me zan gani haka me ya kawo wannan aljanar nan? ke Miemie kifita idona na rufe, ban rabaki da wancan yarinyar mai kamata faran mayu ba, kin d'auko ta zaki kaita cikin jikoki na ta lashe su da maita ko ta shige jikinsu, kar ki sake ki shiga min b'angare mayyar banza mayyar hofi ko na had'a ki da karnuka su yayyaga min namarki anan." Ai da gudu Feeryal ta juya tayi waje. Uwar amarya Mommy ta fito da ka kawayen ta zasu gurin walima, ta cab'a kwalliya cikin wani arnen lashi mai tsadar gaske tasha d'inkin manyan mata, matan masu nera. Umma Karima ita ma da nata kawayen kusan shiga iri d'aya sukayi da Mommy sai dai kalar leshin ta daban ne amma mai tsadar ce ita ma. Motar Hajiya Luba ne ya kunno kansa cikin gidan. bayan ta nunawa security pas d'in gayyatar ta, suka bud'e mata get ta shigo. Mommy suka tsaya suna zaman jiranta su karaso dan ta gane motar ta. a babban parking lot d'in gidan in da motoci ke cike tam nagidan dana jama'ar da suka sami halarta bikin ke tare. direban ta ya dai-dai parking. Hajiya Luba suka fito ita da wata budurwar yarinya. suka karasa in da su Mommy ke tsaye. suka rungumi juna da Mommy, Hajiya Luba ta saki Mommy tana fad'in "Kaga uwar gida a gidan Alhaji Abubakar Fiya, Allah dai yasa bamu makara a walimar ba." "Kun dai kusan makara dan har an fara, na ce gajiyar jiya ce ta hanaki isowa da wuri, to ya gajiyar jiyan." "Wlh ke kam dai ingaya miki bawai gajiya bace ta zaunar da ni, d'iyarki ce gata nan Kuraiba ta b'ata min lokaci, kin san shirin 'yammata sai a hankali, a fenta nan a fenta can, ke Kuraiba ga Mommyn ku nan ki gaida surukan ki." Budurwar da aka kira da Kuraiba ta ce Ina yini." ta fad'a a takaice. Mommy tayi murmushi tana amsawa da "Lafiya lau Kuraiba ya school." ta ce "Alhmdulillah." "Kuraiba fa an girma nakai 1y rabon da na ganta, har tafi Farida a tsaye." cewar Mommy, tana dubanta da murmushi. Hajiya Luba ta ce "Ni da nayi zaton ma lokaci guda za'a had'a bikinsu a wuce gurin." "A'a dai adai bi d'aya bayan d'aya, ayi shi daban-daban ai zaifi dad'i, surukar tawa ko ba laifi." cewar Mommy tana duban Kuraiba. "Da dai mun karasa kar a gama muna tsaye muna wata maganar muyi wacce take gaban mu, abar wannan da ba'a san yuwuwarsa ba tukun." cewar Umma Karima da tun farin maganar ta had'e rai da alama dai akwai wata a kasa,d'ayan biyu ko bata son faruwan lamarin da suke magana a kai ko kuma akasin haka. Hajiya Luba ta ce "Ai Insha'allahu Kuraiba ita ce surukar Alhaji Abubakar Fiya na farko, mudai karasa wanda ake cikin yanzu dai kawai, kafin zuwan nasu lokacin." FEERYAL data fito daga side d'in Hajiya da sauri, sukayi kicib'us da su zasu wuce. Mommy ta bita da harara tana fad'in "Ke kutumar uban ki bakya gani ne zaki bige mutane yarinyar banza kawai." Umma Karima ta kai mata zunguri a goshi tana cewa "Tsintacciyar mage bata mage wuce ki je in da aka gayyace ki." "Wace ce wannan d'in?." cewar Hajiya Kuba tana nuna ta. tsaki Mommy taja ta ce "Yarinyar da Hajiya Fatimah ta tsinto mana." "Wai ita ce haka anya ba sato musu yarinyar mutane tayi ba a asibitin wata kasa ba kuwa? bata shiga US after 2 mon before kawo yarinyar gidan nan ba." Mommy ta ce "Hm zata iya ai dan rashin haihuwa babu abun da bazai iya sata ba, an gama yawon gurin malamai niman maganin haihuwa an rasa ai dole ta b'ullo ta wata hanyar." "Amma dai tayi asara, taraba yarinya da danginta dubi kyakkyawar yarinya fa dan Allah." cewar sauran kawayen nasu. Feeryal bakin get na side d'in Aunty ta tsaya har saida su Mommy suka wuce kafin ta dawo ta d'au hularta da ya fad'i lokacin da Umma Karima ta zungure ta. Ta sunkuya ta d'au hularta tana mikewa, ta saki murmushi ganin wad'an da suke kusa da ita ta ce "Laa Chuchu Chulu baku tafi ba da man?." "Babu tafi ba muma mun tsaya jin wa'azin ne mu je gurin walimar dan anyi nisa da farawa kar a gama babu je ba." "Ni dai bazan je ba, akwai su Mommy a gurin zasu kore ni ko su duke ne." "Baza suyi miki ko mai ba zo muje, bazamu zauna ma a kusa da su ba." yatsa ta saka a hab'arta ta ce "Kun tabbata." "Mun tabbata." suka had'a baki wajen fad'a. Suka sakata a tsakiya suna tafe a hankali suka nufi gurin da ake gudanar da walimar. har suka dumfaro filin gadan-gadan babu wanda ya lura da su. malamar da take gudanar da walimar ita ta fara lura da su. zumbur ta mike tsaye tana fad'in "Yaaaku jama'a ko shin kuna ganin abin da nake gani kuwa!?." Gabakid'aya jama'ar gurin sukabi inda take nunawa da hannu. nan da nan gurin ya kace da hayaniya had'e da kururuwan mata suna fad'in "Wayyo ga zakuna zakuna sun shigo gida." tuni mata suka fara hargitsewa suna niman mafaka domin ceton rayuwar su. zo kaga mata in da suke zubewa kan kujeru suna karya kujeru. Mommy da aka tureta a kan kujera ta zube kasa shirim, ta kasa ko da iya motsawa tsabar tsoro tana baje a kasa jikinta na rawa. idanunta a kan Feeryal da manya-manyan zakunan da suka sakata a tsakiya. suna cigaba da dumfaro gurin gadan-gadan. Hajiya kuwa da rarrafe take tafiya ta tafi bayan wasu kujeru can ta b'oye, ta rufe idanunta gam-gam. tana karanto addu'ar ta da ta saba "Wasayyahu wasayyahu wasayyahuuuuu yasin me manjaga li'eelafi kafa bakwai yasin kafa dubu lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya." Mata sai karo da juna ake ana zubewa kasa, sai ihu da niman agaji. Ganin haka yasa Feeryal taja ta tsaya. tana bin jama'ar da kallo. tsoro taji ganin idon Mommy a kanta sai ta juya da sauri ta gudu, tana gudun kada Mommy'n ta taso ta bige ta, dan a zaton ta, zuwan gurin su da tayi ne yasa ran Mommy b'aci, kuma ta rigada ta san cewa ta hanata zuwa in da suke. Side d'in su ta koma ta haye upstair tana hango yadda mata ke gudu suna fad'uwa suna karya kujeru. Dariya ta tuntsure da shi hango wata katuwar mata ta zube kasa timm , mata sai zubewa a kanta suke sai ihu take kurmawa takasa tashi. tana ta juya katon d'uwawu a kasa. "Ke Feeryal." da sauri ta juyo jin maganar Aunty a bayanta. Aunty ta ruko kunnen ta ta ce "Ke ce ko, ke ce kika sa duk wancan ko?." kai ta girgiza tana kunshe dariya ta ce "Auchii Ammie zafi." "Me yasa kika yi haka Feeryal su d'in sa'annin ki ne, ko abokan wasanki." d'an karamin bakinta ta cuno "Ba ni bace fa Ammie babu ruwana Chuchu da Chulu ne, suke razanin su." fuska Aunty ta had'e ta ce "To ki ce dasu su daina su saida abinda sukeyi haka, ya isa!." Duk da tazaran da ke sakanin su wan da ko ihu mai tsananin karfi tayi daga in da take zuwa gurin walimar nan baza'a jitaba, amma sai gashi ta kira sunan su sun waigo, ta ce "Ammie na ta ce ku dai na razanin su." aiko nan take suka juya su na girgiza gashin jikin su, da suka rikid'a suka koma manyan zakuna masu matukar ban tsoro. suka fice a filin taron. Sai a lokacin hankalin security yakai kan jama'ar da ke ta ihu, suka shigo ciki da sauri. mutane kuwa ganin juyawar zakunan nan yasa wad'anda suka fad'i mikewa tsaye suna kuma niman mafaka. Ganin security yasa wasu dawowa cikin hayyacin su. Hajiya ta fito daga mab'oyar ta tana ciccire ido da fad'in "Kun harbe su kun kashe su ko ya?." security suka ce "Su wa suka shigo Hajiya? babu wanda suka shigo kai tsaye batare da shaidar izinin shiga gidan nan ba." Hajiya ta ce "Injiwa ai wad'annan basa bukatar niman izini, ko ku suka samu loma d'aya zasuyi da ku a bakin get babu wanda ya sani, ku bisu ku harbe su in baku kashe su ba karsu kuma dawo mana nan, zakuna ne suka b'allo suka shigo mana gida." Sai a lokacin Mommy da ta sha tumurmusan mutane ta mike da kyar tana kad'e jikinta. sai matse ido take kafa tayi tsami. Umma Karima kuwa bakin nan mud'uss ya mutu itama ansha birgima gaye ya b'aci. Farida amarya ma ta tumurmusu ba kad'an ba ita da kawayen ta. Su dai jami'an tsaron basuga wani bakon halittar daya shigo gidan ba bayan duk jinsin mutane ne babu na dabbobi. kofar baya ma a kulle take ko mutum bazai iya bud'e shi ba bare kuma dabba, in ta sama ne ma bazasu iya hayewa su shigo ba, babu wata hanyar da zasu iya shigowa sai dai in ta ainihin kofar gidan. suka juya da sauri suka soma bincikar gidan rike da bindigogin su, lungu da sako. amma babu wani halittar da suka gani face mutane wad'an da suka ziyarci bikin. Haka nan taron walima ya watse, da yawan mutane kuwa kowa ya kama gabansa. Da karfe 6 na yamma 'yan d'aukar amarya suka zo, aka d'auki amarya a kaita tsarenren gidan ta na gani na fad'a. Sai da aka nutsu aka fara maida zance. uwar amarya Mommy kam ana zaune ana jinyar kafa dan ko kafa tayi tsami. Hajiya'n Dubai da ita bata je gurin walimar ba tana sashin Hajiya lokacin da abin ya faru, ta ce "Wai kuma kun ganta da idon ku tazo da zaki, a ina ta sami zaki? kai gaskiya da sake wannan 'yar ban yarda da ita ba." Hajiya ta ce "Wlh idona idon ta da jibga-jibgan zakuna, 'yar nan ta girma a maitanci duk jinin mu taso sha kurwar mu ya mata d'aci, shiyasa ta kyale mu, ku kira min Abubakar yau za'ayi ta ta kare, ke Bishira kirawo min matar tasa itama 'yar gol d'in tasa ba, da mayayyar yarinyar duk suzo nan." Batare da b'ata lokaci ba Daddy ya amsa kiran da Hajiya ta masa. Daddy na shiga Aunty da Feeryal suka shigo. da kaga Aunty jikinta a matukar sanyaye yake, dan tasan irin wannan kiran Hajiya'r ba alkhairi ba ne. tun kafin su zauna Hajiya ta dira a kan Daddy masifa take kamar zata ari baki, "Abubakar yau sai ka zab'a ko ni ko mayyar yarinyar can, wlh yau bana kuma kwana gidan ka, ka nuna min iyakata ka gwada min mata ta fini." Hajiya ta kawo kuka ta saka tana fad'in "Fatimah zaki raba ni da d'ana, Abubakar nagama d'awainiya da kai ka nuna min mata ta fini, to ka zauna kai da matarka, kuyi shaida idan na taka kafata na bar gidan nan nabarka har abada ke nan, kada ka kuma min kallon uwa a gare ka, ka rike mata ta zamo uwarka da ubanka, kai har ma da danginka, dan babu wani wan da zai kuma zuwa gidan ka ba kana da kud'i ba, su sayo maka dan gi da iyaye tun da gashi nan ai ka siyo mata da shi." Hajiya ta mike tana sharb'e hawaye. da sauri Daddy ya rike kafafun ta "Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki yafe ni, Feeryal zata bar gidan nan yanzu -yanzu ba sai anjima ba." "Kyale ni na tafi, tsawon sheka nawa tayi a gidan nan kullum haka kake fad'a, tun da kazab'e su a kaina babu ruwanka da ni rabu da ni nayi tafiya ta, ke kuma Fatimah ki zuba ruwa a kasa ki sha yau zan bar muku gidan, ki cigaba da maida Abubakar d'anki dama baki da shi, ita rashin haihuwa ai ba hauka bace da zaki je ki jijjib'o mana annoba ki kawo mana gida, tun da ke juya ce bazaki haihu ba sai aka ce kije kirika kalen 'ya'yan mayu dana aljanu, kice dole sai sun zamu naki, shifa haihuwa wanda kayi nakudar sa da kanka ka ji zafin haifosa duniya shine naka, d'an wani bazai tab'a zamowa naka ba." Aunty ta rumtse idanunta tana jin matsananciyar zafi cikin zuciyarta. tun da take a gidan bata tab'a jin zafin gorin haihuwa irin wanda Hajiya ta mata yanzu ba, duk da ba yau ne karo na farko, da ta fara yi mata gori akan haihuwa ba, amma sai taji zafin na yau yafiye mata na kullum. ko su Mommy da Umma Karima dasunsha yi mata gori a kan haihuwa, amma bata tab'a jin zafin nasu kamar irin na Hajiya na yau ba, dan tasan nasu bakin kishi had'e da jahilci ne ke sasu yin sa. Ta had'iye wani miyau mai d'aci kana ta ce "Kiyi hakuri Hajiya bana fatan ace ta sanadiyya ta uwa ta rabu da d'an ta, idan hakan ta kasance kuwa bazan tab'a yafewa kaina ba." ta mike tsaye ta kamo hannun Feeryal ta na fad'in "Bazaki bar gidan nan ba Hajiya sai dai ita ta barshi." Ta janyo Feeryal sukayi waje. Suna shiga side d'in ta bedroom d'in Feeryal ta shige rike da ita. ta saki hannunta da sauri taje ta d'au katon akwati ta bud'e wardrobe tashiga kwashe kayanta ta na zubawa cikin akwatin da sauri-sauri. Feeryal da hawaye ya cika idon ta tana duban Aunty. Aunty ta kawar da kanta gefe tana maida hawayen da ke shirin zubo mata. akwatin nacikawa ta rufe, bawai dan kayan cikin wardrobe d'in sun kare ba. Ta janyo akwatin zuwa bedroom d'inta. Feeryal ta biyo ta. kayan Feeryal dake cikin d'akin nata ta d'au babban akwati shima ta cika shi, ta rufe tana sauke ajiyar zuciya dan tuni ta kece da kukan zuci. "Ammie ina zamuje tafiya zamuyi?." ta waigo tana duban Feeryal da kyar tayi karfin halin cewa "Ke zaki tafi Feeryal, dole zakiyi nesa da gidan nan, domin samun farincikin masu gidan, ki tafi kiyi nesa da nan." Kuka ta fashe da shi ta taho da gudu ta rungume Aunty, tana wani irin kuka cikin muryar kuka sosai take fad'in "Ni dai bazan tafi ba Ammie kice Hajiya tayi hakuri bani so natafi na barki sai dai mu tafi tare." hawayen da Aunty take ta dannewa ne suka zubo, ta rungume ta tsam tana wani irin gunjin kuka. "Feeryal bazan iya rabuwa da ke ba, abin da suka kasa ganewa ke d'in tamkar jinina na ce, ji nake kamar ni ce nayi nakudar ki, bazan iya rabuwa da ke ba d'iya ta." Jin karar bud'e kofa ya sanya Aunty duban kofar, Daddy ne ya shigo yana dubansu cikin matukar tausayawa. tabbas yasan abune mai matukar wuya rabuwar Aunty da Feeryal, yasan so da kauna da shakuwar da ke sakanin su irin na uwa da d'anta ne. shi kansa rabuwa da yarinyar tamkar rabuwa ne da d'iyar daya haifa. a hankali yataka zuwa inda suke ya dube su cikin raunin murya ya ce..........! Mommyn Twins ce 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* Bismillahirrahmanurrahim 🅿️15 "Kiyi hakuri Fad'imatu bani da zab'in da ya wuce Feeryal tabar gidan nan, in har ina son zaman lafiya da mahaifiya ta." katse shi ta yi da fad'in "Biyayya yazama wajibi akan ko wa ni d'a yayi wa mahaifansa, har in yana son wanyewa da duniya lafiya, Daddy zamu tafi da Feeryal Abuja, bazan maka karya ba zuciya ta bazata jure rashin ta ba." da sauri ya ce "Me kike fad'i haka Fad'imatu, kin san me kike fad'a kuwa!." "Nasani Daddy, zamu koma can duk san da ka sami lokaci, ko da sau d'aya ce a shekara zaka iya ziyarta ta." "Kin sani abin da bazai tab'a yuwuwa ba ne, bazan tab'a jure rashinki ko da na sati guda ne bare na shekaru ba, Fad'imatu ki janye wannan kudirin, kar ki dubi hakan a masayin son kai ko rashin adalci, bazan iya barin ki ki tafi ba koda kuwa komawa zakiyi d'aya daga cikin gidaje na da suke can Abuja bare kuma gidan ku." Ya dad'a matsowa ya janyo hannun Feeryal ya dube ta yana fad'in "Munyi magana da Alhaji'n Abuja zan kaita can ta zauna dai-dai kafin Hajiya ta huce." Aunty ta bud'e baki zatayi magana kiran Alhaji'n Abuja wato Abba'n ta ya shigo wayarta. Bayan sun gaisa Abba'n nata ya d'aura da cewa "Fatimah duk abinda ya yi tsanani watanwata rana sauki na zuwa, ina amaryar tawa an dai gama mata shiri dai ko? na hutar daku dukan ku da ke da mijinki ni nasa a zo a d'auke min ita, ajirgi ma ba'a mota ba za'a taho min da amarya ta, ga mai zuwa d'aukarta yana daf da shigowa tazauna cikin shiri." "Abba tare zamu taho da ita." cewar Aunty tana kokarin maida hawayen ta. ya ce "Kul kar na sake jin wannan maganar Fatima, ki zauna a gidan ki, ko zaki fara yimin musu ne iye Fatima? ni na ce a taho min da jikata." Aunty ta jijjiga kai tana fad'in "To Abba." kiran mahaifinta na yankewa na mahaifiyarta na shigowa. ta d'aga wayar da sallama daga cikin wayar Hajja Umma ta ce "Ina kishiya ban haushi take? duk da kishiya ce ita amma ina farinciki da zuwan ta, kada lamarin ya d'aga miki hankali da zaman ta a gurin ki, da zaman ta anan gurin mu duk d'yane, Alhaji ya ce wai ta jirgi za'a kawo masa amaryar sa, nace aiko bata isa ba dan nima a lokaci na akafa aka kaini, badan yarasa mota ba aka fake da al'ada, dan haka itama a kawota a kafa, ai al'adar tana nan har gobe." Duk da yanayin da Aunty take jin ta aciki sai da ta saki murmushi tana cewa "Haba Hajja Umma ai zamanin ki da nata ba d'aya ba, kuma ai a lokacin gari d'aya kuke da Abba unguwar ku ma ba nisa sakani, itako daga Lagos zuwa Abuja ai sai dai jirgi kam ba'a mota ba, Abba baya so ta wahala da zaman mota ne." Hajja Umma tayi dariya ta ce "To Allah tsare zata taho ta same ni." Daddy dake tsaye har lokacin ya d'aga kiran daya shigo wayarsa yanzu. jim kad'an ya sauke yana duban Aunty data katse wayan da suke da Hajja Umma, har a lokacin tana rungume da Feeryal. ya mika hanu ya ruko na Feeryal, ya ce "Taho muje." Aunty ta dad'a rungume ta tanajin wani irin kaunarta. bata son rabuwa da ita sai dai babu yadda ta iya yazama dole su rabu, karo na farko da ta farajin ciwo game da rashin haihuwa. da ace ita ta haife ta da babu wanda ya isa ya rabata da ita. ta kai hannu ta share hawayen daya zubo mata, kana ta sake masa ita. A b'angaren Daddy shima haka yake jin kansa sai dai kawai dauriya irin na maza. ya janyo Feeryal tana tirjewa da kuka da kiran Ammie'n ta, ya janyo akwatin ta sukayi waje. Aunty ta zube bakin gado ta saki kuka mai ban tausayi. Sai da ya kaita mota yakuma dawowa da kansa ya d'auki d'aya a kwatin kayanta, kafin ya isa parking lot security suka tare shi kamar fitowar sa na farko da akwatin daya fito da shi da FEERYAL. FEERYAL na zaune cikin mota tana kuka, Daddy ya matso yaruko hannunta yana rarrashi. da kyar tayi shiru da dabarun da yayi ta mata. sannan ya umurci direban daya zo d'aukarta su tafi. yana d'aga mata hannu har motar ta fice a gidan. numfashi ya sauke yana jin ba dad'i cikin ransa. Sai kuma ya juya da sauri yana son sanin halin da tauraruwar sa take ciki. A zaune ya same ta bakin gado, hawaye d'aya na bin d'aya. hankali tashe ya zauna gefenta, ya saka tafin hannunsa a rud'e yashiga share mata su yana fad'in "Kiyi hakuri Fad'imatu ki bani kwarin gwuiwar yiwa mahaifiya ta biyayya, bazan iya jure ganin ki cikin damuwa ba, dalilin hakan zai iya kaini ga baud'ewa daga doron biyayya wa iyayen da nake kai, kin san kuwa zan fad'a halaka, muyi hakuri mu sanya hakan cikin kaddarar mu." A hankali ta kai hannu ta rike hannunsa dayake kan fuskarta ta d'aurashi kan cinyarta, tana d'an murzashi. cikin sanyin murya da son gusar da damuwarta dan bata son ace a kanta ya sami matsala da mahaifiyarsa. tasan batayi adalci wa kauna da soyayyar dayake nuna mata ba. "Daddy kewa ce kawai ke damu na tun kan tayi nesa da ni, ka tayani da addu'a na rage jin ta cikin raina." ta kwantar da kanta jikin kafad'ar sa. ya shafo gefen fuskarta "Ai baku rabu ba ko kin mance cikin ahalinki ta tafi yanzu, tamkar kuna tare ne har yanzu." kai ta jinjina tana dad'a kwanciya jikin sa. Sai da ya tabbatar da ya yi nasara wajen rage mata damuwar da take ciki baifi saura taki ba, kafin ya bar sashin nata. Abuja Karfe 5 da mintuna 10 jirgin da su FEERYAL suka bi ya sauka a cikin airport d'in babban birnin tarayya Abuja. wan da suka share mintuna hamsin da uku a sararin samaniya daga Lagos zuwa Abuja. a nan airport suka tadda motar gidan Alhaji Tahir Abbas, yana jiran saukowar su. Tun a cikin jirgi FEERYAL take ta baza ido, har a yanzu da suke tafe cikin mota a hanyar su ta zuwa gidan Alhaji Tahir Abbas da ke maitama, dan bata tab'a tafiya mai nisa ba, daga gida sai school. Aunty bata barin ta ko da Miemie ta bukaci suje wani gurin ko gidajen dangin su, a kan FEERYAL Aunty ta jingine zuwa ko'ina sabo da gudun bakin mutane, dan duk wanda ya ga FEERYAL d'in ya rinka wuu-wuu ke nan, wani ya fad'i alkhairi wani akasin sa. A bakin wani katafaren gida mai girman gaske, direba ya yi hon aka wangale masa get. babban gida ne mai matukar girma da tsaru, duk da girma da tsaruwa irin na gidan Alhaji Abubakar Fiya, sai da FEERYAL ta tsaya kallon tsaruwan gidan Alhaji Tahir Abbas. sabo had'uwan shi shima. Direba na gaba janye da akwatunan ta tana biye da shi. suka shige cikin wani katafaren parlour na alfarma. Tun kafin su karasa cikin parlour'n Wasu dattijai biyu mace da na miji suka fito daga wata kofa. ko ba'a fad'a ba kasan Alhaji Tahir Abbas ne Abba'n Aunty da hamaifiyarta Hajja Umma. suna tozali da FEERYAL a tare suka furta "Tabarakallah masha'allah." ganin ainihin suffarta a zahiri yad'are wacce suke gani a hoto. da gudu Maryar autarsu da ke biye da su, ta wuce gaban su tana fad'in "Wow beautiful oyoyo FEERYAL." ta rungume ta. Hajja Umma tana kokarin tareta, Abba ya yi saurin shangabanta ya ce "Barni ni zan tari amarya ta da kai na." Hajja Umma ta yi murmushi tana cewa "Saboda ni kishiya ko, ai dai gara ni na fara tsare ta na kakkab'e abinda tazo dashi, koma da baya na d'ebo sakin kuka na zuba a hanyar shigowar ki, ya karya abinda kikayiwa Alhaji tsawon shekaru nice amarya nice uwar gida, daga zuwan ki zaki firgita shi." "Taho nan amaryata gimbiya FEERYAL rabu da ita." ya ruko hannunta. suka karasa suka zauna kan kujera. Maryam ta kasa zama tana ta kallon ta, kyawun ta ya mugun tafiya da imanin ta. sai fad'i take "Wayyo Allah kyakkyawa ce wlh kamar ita tayi kanta, kullum tare zamu rika zama ko kamshin kyan ki zai shafani." dariya maganar ya bata ta yi karamar dariya, kyakkyawan kumatun ta ya lob'a. Hajja Umma ta ce "Tabarakallah masha'allah." Direba ya aje akwatunan ta ya fita bayan ya gaishe su. Abba ya ce "Maryam d'auki akwatin ki kaisu d'akin kusa da naki d'akin ta ke nan, amarya ta ko kina son d'akin sama kusa da na Hajja Umma ne?." da sauri Maryam ta ce "Abba a d'aki na zata zauna murika kwana tare." "A'a ki bari dai a bata d'aki na, ni na sauko kasa, ai in bakuyi wasa ba sai dai ka ajeta a kitchen ko store." cewar Hajja Umma tana dariya. Abba ya ce "Ai wannan gold d'in tafi karfin zama a gurin da kika ambata, Maryam kaita taci abinci tayi wanka ta huta, sai tazo muyi hira." Maryam ta janyo akwatunan ta ce "Taho muje." babban d'aki ne mai girman gaske komai na bukata yana ciki kamar d'akin matar aure, bana 'yar matashiya mai tasowa ba. Maryam ta dubi ta tana fad'in "Shiga bayi kiyi wanka ko nazo nayi miki?." kafad'a FEERYAL ta make ta ce "Na iya fa Ammie na ma tana barina nayi ranar da ba school." "To je kiyi kizo ki sauya kaya muje kici abinci." ta shige bayi. ita kuma Maryam ta shiga ciro kayan ta tana sakasu cikin wardrobe. Ko da ta gama ta fito Maryam ta taimaka mata ta shirya tana ta yaba kyawun halittarta, FEERYAL

Chapter 13 of 20