kaje ka duba ta."
Fuska ya dad'a had'e wa, ina gashi nan kalar aikin da yakin aka matsa masa sai ya yi, shi kullum bashida lokacin kansa sai na mutane.
d'an baccin ma baza'a barshi ya yi ba.
juyawa ya yi yana kokarin barin gurin tare da fad'in
"Ku barta a gurin gobe Doctor's zasu shigo su duba ta."
da sauri Nasir ya sha gaban sa ya ce
"Haba kai kuwa yarinyar da take cikin halin mutuwa ko rayuwa, idan ka taimake ta kaima Allah zai dad'a taimakon ka, bata cikin hayyacin ta gaba d'aya please ka taimaketa dan Allah, daure dai muje ka duba ta,
ai duk irin aikin namu ke nan muna son baccin nan muke hakura da shi."
Gajeren tsaki yaja, kana ya zura hannayen sa cikin aljuhun gajeren wandon jikin sa, ya juya suka nufi kofa.
Nasir yana ta bashi baki har suka fice a gidan suka ketare titi suka shiga asibitin.
Ma'aikatan da suke kwana asibitin suna ganin sa kowa ya mike tsaye da kafafunsa, suna mika masa gaisuwa, ba wanda ya amsa gaisuwar sa ya wuce ICU Nasir na biye dashi.
Har lokacin Major Sadam yana tsaye da kafafunsa yana ta kai kawo cikin room d'in.
yana shiga room d'in ya zare hannayen sa daga aljihu ya nad'e su a kirji yaja ya tsaya.
inspector Nasir ya dube sa, ya yi murmushin gefen baki, a ransa yake fad'in
"Wannan fa d'an zafin kai ne, dube shi kamar wani boss yawani b'ata rai, ya juye tamkar shine sojan."
a fili kuwa cewa ya yi
"Yauwa Dr bari mu baka guri ka gudanar da aikin ka, Major muje ta waje ko."
Sadam ya watsa masa mugun kallo cikin kakkausar murya ya ce
"A kiraka kana wani ji da kai who are you! idan kayi wasa sai Kayi sallen kwad'o a nan,
yarinya tana cikin wani hali kazo ka duba ta,
kana gayawa mutane magana,
mu da muke hana idanun mu bacci domin baku tsaro bamu ce mun gaji ba sai kai ne zaka wani ce wai lokacin baccin ka ne,
kai dole ma na baka wani punishment idan ka gama dubata ka biyo ni office!."
wani kallo ya bisa da shi sannan ya ce
"Go ehead for the punishment in zaka iya,
ku d'auke ta ku fita da ita a nan bazan duba ta ba!."
a fusace Sadam ya bud'i baki zaiyi magana
Nasir ya yi saurin ruko hannunsa.
"Please Major barshi ya yi aikin sa dan Allah babu tima.
ya janyo Sadam dayake nuna Dr A.A Fiya da hannu yana fad'in
"Who are you be careful."
ya jashi suka fito dan yaga Dr nan ba sauki damasan sa sai wani bud'ewa suke babu tsoro ko d'igo a gare shi.
za'a iya yin ba dai-dai ba,
karshe ya nimo masu taya shi rabon fad'a dan bazai iya shi kad'ai da wannan murd'ad'd'en Dr ba.
duk da kuwa kasancewar sa hukuma shi da yake likita yafisu zubin kakkarfan zaratan jaruman maza.
Dogon tsaki yaja a fili ya furta
"See this guy mttss."
yakuma jan tsaki akan wata patient sun d'aga masa hankili sun hanashi bacci, daya sani ma da baizo kasar ba, shi da ya gudo yazo dan ya huta amma daga zuwan sa an wani takurawa rayuwarsa, shifa wannan aikin in da yasan yadda zaiyi ya yakace shi a gareshi daya kakkab'e shi,
domin babu komai cikin aikin sai takura a hana mutum sakewa da hutawa kullum mutum bashi da lokacin kansa sai na mutane,
da Daddy zai duba masa da ya barshi ya jingina aikin nan gefe baya son damuwa.
kwafa ya yi a fili.
tare da sauke idanunsa kan bed in da take kwance flat kamar babu rai a jikin ta, tana sanye da riga da wandon bacci.
a hankali yashiga d'aga kafarsa yana takowa inda take.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️19
Dipp! karar sautin bugun zuciyarsa dai-dai san da idanunsa ya sauka a kanta.
babu zato yaji bugun zuciyar da baisan musabbabin abin da ya haifar da shi ba.
da karfi ya rumtse idanunsa yana sauraran sautin bugun zuciyarsa.
"Why!."
ya furta a file sai kuma ya yi gajeren tsaki.
ya na bud'e idanun nasa,ya janye shi daga gareta ya matsa gefe, yasoma had'a abubuwan da zai yi mata amfani da su wajen bata taimakon gaggawa.
ya taho dasu bakin gadon.
tsayuwar sa ya gyara, a hanlali ya kamo tsinsiyar hannunta, da yatsunsa biyu kamar baya son tab'awa, idanunsa yana kan na'urar da yake ta kokarin saita shi.
2 seconds yana rike da hannun nata, tsaki ya ja sai kuma ya saki hannun,
ya dad'a matsowa yakai hannunsa ta saman wuyan rigar baccin jikinta yad'an jashi kasa,
ya saka yatsarsa a jikin jijiyar gefen wuyanta,
2 seconds nan ma yatsarsa yana gurin, kana ya janye.
ya d'an juyo ya dubi nurse d'in da ke tsaye a gefen sa ya ce
"Je ka kirasu suzo su d'auke ta ta mutu."
da sauri ya juya ya fita yaje ya sanar musu.
a razane duk suka mike suka had'a baki wajen fad'in
"What!."
Major Sadam da ya ji kansa na juyawa ya nufi kofar ICU Nasir na biye da shi.
ya tura kofar da karfi yana fad'in
"No bazai yuwu ace ta mutu ba! ya za'ayi kace ta mutu no bazai yuwu ba!."
gefe Dr A.A Fiya ya matsa yana zura hannayen sa cikin aljuhu, tare da mara baki ganin yadda Major Sadam yawani birkice ya yi kanta yana fad'in
"FEERYAL please ki tashi no bazai yuwu ace kin mutu ba!."
ya jijjiga hannunta yana kiran sunanta.
sai kuma yayi wani irin juyowa yana duban Dr A.A Fiya da jajayen ido
ya ce
"Kar ka sake kabari ta mutu, wlh idan ta mutu da kai da b'arayin can, tare zakuyi freezing sannan na harbe ku da kaina, kayi mata abin da zaisa ta tashi!."
Sadam ya fad'a da karfi yana jijjiga kafad'ar Dr A.A Fiya.
ture hannunsa ya yi daga kafad'arsa ya ce
"Kai ka dawo da ita mana kayi mata abinda zaisa tatashin,
ka d'auke ta ku fita min a asibiti ni na gama nawa sai kaje kayi yadda zata tashin a can waje."
Inspector Nasir ya matso da sauri yana fad'in
"Please let me know Dr da gaske ta mutu!?."
kafad'a ya d'aga kana ya ce
"Ina tunanin hakan."
da sauri Nasir ya rike hannunsa ya ce
"No! tunani kake, bai tabbata ba, ka taimaka ka sake gwadawa insha'allah zata tashi, aikin ka ne mu bamusan yadda zamuyi da ita ba, dan Allah Dr dan Allah ka taimaka dan Allah dan Allah please help."
ya jijjiga hannunsa yana magiya da rokon sa.
hannu ya d'aga musu yana jifan Major Sadam da mugun kallo kana ya ce
"Ku jira a waje."
Nasir yaja Sadam da sauri sukayi waje.
Gajeren tsaki yaja ya matsa bakin gadon,
ya rike kugu yana dad'a jan tsaki.
sannan a hankali ya kai hannunsa kan cikinta ya janye rigar baccin jikinta da yatsu biyu,
ta d'an sama har zuwa saman cibiyarta, yadda yake yi kamar mai tab'a wani abin kyama da baya son hannunsa ya tab'a.
ya d'au defibrillator yana had'asu, kana ya dad'a matsowa ya manna shi kan cikin ta.
da karfi ta zabura ta kuma komawa tana kokarin kuma shiga dogon suman.
yakuma manna mata sau biyu a jere tawani irin zabura da karfi tare da jan numfashi,
mai had'e da ihu a firgice ta yunkura ta fad'a jikinsa ta tsakalo wuyansa ta kankamesa da karfi tare da fasa kuka,
tana b'oye fuskarta cikin kirjinsa.
cikin fizgar munfashi mai nuni da zallar tsoro wanda a yanzu kwakwalwar ta ke tsaye cak baya nanata komai sai kasantuwarta da b'arayin nan.
cikin had'a kalomomi take fad'in
"Dan Allah.. ka..kayi hakuri kar..kar ka tafi da ni, ni bana sonka bazan aure ka ba."
A fusace ya fisgota da karfi ya cirota a kirjinsa ya turata kan bed d'in, ya yi saurin binta da allura ya dannan mata, ta saki wani uban kara jikinta na rawa.
zuwa can kuma a hankali tashiga sauke numfashi, a hankali a hankali nan da nan bacci ya tafi da ita.
Tsayuwarsa ya gyara tare da gyara zaman singilet d'in jikin sa da ta tukuikuye shi,
yawani had'e rai yana kumbura had'e da jan tsaki, kamar wacce take ganin sa,
a ransa yake fad'in
"Yar wannan abin wai take maganar aure msstt."
yaja tsaki had'e da yin kwafa,
duk ta gajiyar da shi ta makalkale masa wuya,
kwafa ya yi a fili.
kana nan da nan ya shiga bata taimakon gaggawa, yana yi yana jan gajeren tsaki da kaga yadda yake dai zakasan bawai da son ransa yake taimakon nata ba.
daga bisani ya d'aura mata drip had'e da ruwan allurai masu karfi da inganci.
yana gamawa kuwa ya juya bai kuma waiwayota ba ya yi gaba abinsa.
nurse yashiga kimsa abubuwan da yayi amfani da su.
Yana fita Major Sadam da Inspector Nasir suka mike suna son jin meke faruwa kuma yanzu.
Nasir ya ce
"Ka sami nasarar cito rayuwarta kuwa?."
"Kushiga ku duba."
yafad'a a takaice.
da sauri sukayi cikin room d'in, shiko yasa kai ya fice a asibitin.
Wani numfashi Major Sadam ya sauke ganinta a kwance tana numfashi, sai dai idanunta a fure da alama dai bacci take.
Nasir ya ce
"Alhamdulillah!."
nurse d'in dake ta kimsa gurin ya yi murmushi yana cewa
"Ai tun da Dr A.A Fiya ne ya fara jinyarta da kansa ai insha'allah zata tashi."
Sai a lokacin suka sami sukuni ganin ta farfad'o har ta sami bacci.
wajen karfe 3 da rabi na dare.
nan suka fita a asibitin bayan sun aje jami'an tsaro kewaye da asibitin.
A b'angaren su Hajja Umma kuwa, ranar sunga tashin hankali.
ga tashin hankalin sace FEERYAL ga karar harb'e-harben da ya birkita cikin unguwar kamr za'a tada unguwar da harbi. bayan lafawar tarzoman,
aka turo jami'an tsaro gidan, yadda sukaga rana haka sukaga dare kowa a zaune ya kwana cikin zullumi da fargaba.
duk da Inspector Nasir ya sanar musu sun kwato FEERYAL a hannun 'yan ta'addan nan sai dai a dame suke da son jin halin da take ciki, dan ya sanar musu tana asibiti.
fatan su dai Allah yasa ba harbinta akayi ko wani abun b'arayin sukayi mata ba.
a cikin daren Nasir yasanar musu ta farfad'o.
Abba ya ce zasuje su ganta, ya ce subari
gari ya waye tukun, tana cikin tsaro sosai a asibitin.
A b'angaren Dr A.A Fiya kuwa, yana komawa gidan sa.
ya fad'a bathroom ya yi wanka tare da d'auro al'waka ya zura jallabi, ya haye kan sallaya yasoma gabatar da sallar nafila,
har sai da aka kira sallar asuba kana ya fita zuwa masallaci.
bayan an idar ya gabatar da azkhar sannan ya nufo gida.
yana shiga bedroom d'in sa ya soma had'a kaya, ya janyo wayarsa ya daddannan kana ya kara a kunnensa.
ringing d'aya ana biyu a ka d'aga.
"Zo ka kaini airport 6:30 airplane zai tashi."
yana fad'in haka ya kashe wayar.
Dr Imran yabi wayar da kallo yana nanata kalmar da ya fad'a.
ya maida kiran nasa yana d'agawa Dr Imran ya ce
"A.A wai ina zakaje ne da asuba d'in nan?."
"Kana b'ata min lokaci kafito kazo ka kai ni ko na aje motar a can airport kazo ka d'auko ta."
ya kashe wayar.
da sauri Dr Imran ya mike yafito daga gidan kwanan likitoci, wan da shima d'aya ne daga cikin gidajen sa da suke cikin unguwar. likitoci ma'aikatan asibitin sa ne suke zaune a ciki.
Dr Imran na shiga gidan nasa ya hangosa a parking lot yana saka jakarsa cikin mota.
ya karaso da sauri ya iso gurin.
key'n motar ya jefawa Dr Imran kana yabud'e gaban motar ya shiga ya zauna yana fad'in
"Yi sauri muje time na tafiya."
Dr Imran yashiga mazaunin direba ya juyo yana duban sa.
"A.A wai ina zakaje ne shekaran jiya-jiyan nan fa ka shigo, ko zaka shiga Lagos ne kabari na shirya mu tafi tare mana."
"Germany zan koma kamar nafi samin bacci da hutu acan, na zo dan na huta amma jiya ko rumtsawa ba'a barni nayi ba, akan wata yarinyar da ma ba lallaine tayi raiba,
haka shikaran jiya ina sauka kuka wani barni da patent, ba gara na koma ba kawai."
baki Dr Imran ya bud'e da mamaki yake kallonsa, sannan ya ce
"Kayi hakuri ka bar tafiyar nan, shima can ai duk aikin ne idan ka koma,
ka dai sani patient zaman jiranka suke, suna sanin komawar ka kuwa zasu taho ganin ka, kuma dole ka duba su, kaga ba hutu ke nan can d'inma."
"Dan Allah muje."
yafad'a yana nuna masa hanya
Dr Imran ya girgiza kai ya yi wa motar key mai gadi ya bud'e suka fice a gidan.
A hanya Dr Imran ya yi ta bashi baki ko zai canza shawari ya hakura da tafiyar, amma sai ce wa ya yi, maganar Imran d'in ma karasa masa gajiya take, yabar cika masa kunne.
sanin halinsa yasa Dr Imran yin shiru, har suka isa airport suna isa kuwa baifi da minti 10 ba jirgi ta d'aga.
Dr Imran ya juyo gida.
tun daga kwanar shiga layin ya hango motar sojoji dana police a kofar asibitin su.
har zai wuce gida kafin ya yi shirin fitowa asibitin. sai kuma ya yi kwana ya shige asibitin dan son sanin me ke faruwa.
Major Sadam da Inspector Nasir da shigowarsu kenan yagani tsaye a parlour'n asibitin, suna tambayar nurse's har yanzu likitan bai zoba suma sauran likitocin basu fito?.
suna kokarin basu amsa Dr Imran ya shigo.
suka nuna shi suna cewa ga Dr d'aya ma ya shigo.
inspector Nasir ya dubi Dr Imran ya mika masa hannu suka gaisa kana ya ce
"Muna da patient a ciki jiya muka kawo ta da daddare, patient in Dr A.A Fiya ne, amma kamar bai shigo asibiti har yanzu ba ko?."
Dr Imran ya ce
"Eh bai shigo ba tukun, amma ta fard'o kuwa Jasin?."
ya karasa maganar yana duban nurse Jasin ya nufi ICU Nurse Jasin ya biyo bayansa yana fad'in
"Sir har yanzu tana bacci, akwai allurar bacci cikin drip d'in da ke shiga jikinta."
kai ya jinjina dai-dai san da suke shigewa cikin room d'in.
Har lokacin FEERYAL tana bacci.
tsayuwa suka yi a bakin gadon Dr Imran ya ware ido sosai a kanta yana kallon ta da yadda ruwan yake shiga a hankali sosai.
yana mai mamakin a ina suka samo ta, ko tana cikin masu kawowa Nigeria ziyara ce ciwo ya kamata.
Dr Imran ya dubi Jasin ya ce
"Ina fayel d'in ta d'uko system mu gani?."
nurse Jasin ya ce
"Ba'a bud'e fayel file ba."
kai ya jinjina a kasan ransa ya ke fad'in
"A.A ke nan 'yar da yake sawa mutuwa gata haryanzu tana numfashi, ai tun da ta fad'o hannunka da ikon Allah da sauran shanruwanta."
nan shima ya d'aura nashi aikin kan na Dr A.A Fiya.
Su Abba sun kasa nutsuwa har sai da suka taho asibitin, sai dai har lokacin da suka ison ma bata farkaba.
Tuni 'yan jaridu da gidajen TV dana radio harma da social media suka fara watsa labarai da rahotanni kan faruwal lamarin.
inda suke sanar da nasarar da jami'an tsaro suka samu kan kama 'yan ta'addan da aka jima ake farautarsu.
NTA ta fito da rahoton faruwar lamarin da yadda komai ya kasance.
ta bakin d'an jaridar da yake karanto labaran kamar haka
"Jami'an tsaron Nigeria sojoji da 'yan sanda sun sami nasarar cafke 'yan tadaddan nan, kungiyar da akeyiwa lakabi da 'yan d'aukar amarya,
ajiya litinin 5 ga wata,
inda suka yi zuga zuwa d'aukar wata yarinya,
a Maitama gidan shahararren d'an kasuwan nan Alhaji Tahir Abbas, dake cikin birnin tarayya Abuja,
in da jami'an tsaro suka sami labari sukayi fitar gaggawa,
inda sukayi bata kashi sakanin su da 'yanta'addan sukayi nasarar cafkesu, suka kuma kwato yarinyar da yanzu haka tana gadon asibiti,
rahoto ya tabbatar mana da cewa jami'ai uku sun sami rauni, sakamakon musayar wutar daya shiga sakanin jami'an da 'yan ta'addan.
a yanzu haka shugaban na 'yan ta'addan Bala kwari da sauran mabiyan tawagarsa na d'aukar amarya suna nan, a hannun hukuma.
Bala Kwari ya jima yana ta'addanci ba a iya birnin taraiya ba harma da sauran jahoyin kasarnan,
duk yarinyar da yaga ta masa ko budurwa ko matar aure to sai ya d'auketa, shekarar data gabata motocin d'aukar amarya yake garkuwa da su bayan ya d'auke amaryar sai ya sake sauran mutanen ya tafi da amaryar.
wakilanmu suna can ofishin hukuma da asibitin da yarinyar take dan son sanin halin da ake ciki,
ku cigaba da biyo mu dan son salin halin da ake ciki."
Labarin da kasa gaba d'ya ta waye gari da shi ke nan, inda jama'a suka ji dad'in nasarar da aka samu na cafke 'yan ta'addan, tawagar d'aukar amarya, da suka addabi al'umma ana kuma yiwa yarinyar fatar samin sauki.
Wani irin mikewa Daddy ya yi yana ware idanunsa kan TV in da ake hasko labaran,
Aunty da ta fito rike da tray daga kichin ta ja ta tsaya jikinta na b'ari.
da sauri Daddy ya d'au rimut ya kashe TV yana kallonta yana fatan Allah yasa bata ji ba dan yasan ta da iya firgicewa, sai dai alamu sun nuna taji ga yadda gaba d'aya yanayin ta ya sauya.
hannu na b'ari murya na rawa tashiga fad'in
"Innalillahi wa innailaihirraji'un me nake ji haka Daddy ka kunna TV mana, Alhaji Tahir Abbas Maitama, Abba ke nan fa, gidan mu meke faruwa a gidan mu wa aka sace!."
gaba d'aya Aunty ta firgice.
da sauri Daddy ya je ya karb'i tray'n da yake kokarin sub'ucewa a hannunta, ya dire shi kasa kana ya ce
"Ki nutsu Fad'imatu, insha'allah komai yazo cikin sauki, ai kinji basukaiga gudu da wacce suka d'aukan ba aka sami nasarar cafke su,
wace ce cikin su Maryam ce ko FEERYAL?
ya Allah ka tsayar haka."
Aunty ta girgiza kai tana fad'in
"FEERYAL ce ma nasan ita ce ita ce kullum ake kawo wa hari."
"Ko wace ce cikin su Allah mun gode maka da ka kawo mana saukin lamarin, bari na kira Alhaji'n Abuja shima wata kila damuwar ce yasa bai sanar mana ba."
Ya dannan number Abba yayi ta ring ba'a d'agaba.
a b'angaren Abba kuwa wayar tasa a gida ya barta suka taho asibiti inda FEERYAL take.
Sau biyar Daddy yana kira ba'a d'agawa, ganin haka yasa hankalin sa ya soma tashi, sai dai bai nuna ta inda Aunty zata gane har ta dad'a birkicewa ba.
ya dube ta yana cewa
"Bari naje na dawo kada ki tada hankalin ki babu komai, ai kinji da akwai da 'yan jaridun sun fad'a."
ita dai shiru tayi amma Allah ne kad'ai yasan ya take ji cikin zuciyarta.
Daddy na fita yasa akayi masa bukin na jirgi, bada jimawa ba kuwa jirgi ta tashi zuwa Abuja.
Ko da ya isa maitama gidan Alhaji Tahir Abbas, ya taras da ba mutan gidan sai ma'aikatan gidan.
nan suke shaida masa suna asibiti, akayi masa jagora zuwa, A.A FIYA Hospital.
Su Abba suka cika da mamakin ganin Daddy dan basuyi sammanin ganin nasa ba, saboda basu sanar musu da me ke faruwa ba.
Abba ya tari Daddy yana fad'in
"Ina da shirin nimanka, amma bayan na tabbatar da farkawarta, dan bansan ta inda zan fara sanar da kai, inda amanar da ka bani ta kasan ce ba."
Daddy ya girgiza kai yana cewa
"Ko a gurin mu idan Allah ya kaddara hakan zata faru sai ta kasance, amma ya jikin nata ta farfad'o kuwa?."
"Har yanzu dai amma ance bacci take."
kai Daddy ya jinjina tare da fad'in
"Allah ya bata lafiya, babu dai abinda suka mata ko?
kuma babu abin da sukayi muku komai lafiya dai ko?."
"Basuyi mata komai ba firgici ne yasa ta shiga dogon suma, amma an sami nasarar cirota a dogon suman yanzu dai tana bacci tun daren jiya amma kikita yanzu ya tabbatar mana idan ruwan da ke jikin ta ya kare zata farka,
babu wanda suka cutar a cikin mu."
"Allah ya bata lafiya, ya tsare na gaba."
cewar Daddy yana sauke numfashi tare da goya hannunsa a baya yana d'an zaga gurin.
Major Sadam da Inspector Nasir ne suka shigo da Dr Imran.
suka shige ICU.
har lokacin FEERYAL na kwance bata ko motsi sai dai numfashin da take saukewa a hankali.
Major Sadam ya dubi Dr Imran jiki ba kwari yana fad'in
"Dr takai 9h tana baccin nan ace har yanzu bata farka ba,
wai ina Dr can yake ne anya ba wani abin yamata ba ace har yanzu tana bacci bata farka ba,
no! ina banma yadda ba kirawo shi, je ka kirashi yazo nan, oya kirashi maza ya zo nan!."
Dr Imran ya ce
"Zata farka daga zaran ruwan nan ya kare mud'an jira zuwa karewar ruwan."
"Kai wai wani irin ruwane ma wannan ace tun cikin dare yana shiga jikinta ace har kuma yanzu bai gama ba,
a cire wannan ruwan tafarka tukun a maida mata."
ya mika hannu yana kokarin zare cannula hannunta.
da sauri Dr Imran ya ce
"Kar ka soma! idan ka maida ita dogon suma ni da kai bazamu iya dawo da ita ba, karshe abinda ake gudun ne zata kasance, ko tantama babu wannan numfashin da kake gani ma, bazaka sake ganin sa ba,
mutuwa zata yi!."
da karfi Sadam ya janye hannunsa ya yi baya da sauri yana fad'in
"What!."
kai Dr Imran ya jinjina tare da cewa
"Tabbas! Dr A.A Fiya baya ma kasar bare ya bata taimakon gaggawa kamar dai yanzu a inda take d'innan,
farkawarta batare da karewar wannan ruwan ba, barazana ce ga rayuwarta,
shi ya saita ruwan a kan dai-dai awannin da yakamata ta farka,
ba ruwa gama gari ne da ka sani ba, ruwa ne mai d'auke da sinadaran magunguna na musamman masu inganci a cikin sa,
dan haka ka jira cikawar awannin koda kuwa wuni zatayi ta kuma kwana a haka."
Inspector Nasir ya ce "Shike nan Major kadai ji a bari kar aje a b'allo wata likin, amma shi Dr yaushe zai dawo?."
murmushi Imran ya yi yana fad'in
"Bana ce ba duk san da ya yi ra'ayi zai juyo."
jinjina kai Nasir ya yi tun a jiya ya fahimci likitan mai tsastsauran bahagon ra'ayi ne,
irin wanda ba'a sasu ba'a hanasun nan,
babu kuma d'igon tsoro a gare shi.
sai kuma ya yi murmushi dan ya burge shi ba kad'an ba.
Fad'a Major Sadam ya soma yana fad'in
"Shine ya bar patient ya tsallaka ya tafi, shi da ya fara ba sai ya karasa ba, idan ya sake aka sami matsala na rantse shima sai ya yi freezing."
hannunsa Nasir ya rike ya jasa sukayi waje.
Dr Imran ya yi karamar dariya yana girgiza kai.
irin dai yafad'i son ransa, baisan da wa yake zancen ba.
shima ya biyo bayan su bayan ya tabbatar da komai dai-dai cikin room d'in.
Dr Imran ya yi mamakin ganin Daddy a asibitin tare da su Abba.
ya karaso ya shiga gaidashi cikin girmamawa,
Daddy ya amsa yana tambayar sa ya mai jikin dai?
ya ce da sauki sosai.
Bayan a wanni uku wanda ya yi dai-dai da awannin 12 kenan FEERYAL ke kwance a asibitin.
sai a lokacin ruwan ya kare bayan mintuna 15 da karewar nasa kuwa ta farka.
Su Daddy Abba Hajja Umma Maryam sunyi matukar farinciki da farkawar nata,
zo kaga Major Sadam yakasa zaune ya kasa ysaye.
Inspector Nasir sai dariya da tsiya yake masa.
A b'angaren Dr Imran ma yaji dad'in farkawar nata ya d'agata a ICU ya canza mata d'aki.
su Daddy suna cikin d'akin suna ta yi mata sannu da murnar ganin lafiya bayyane a gareta.
Dr Imran ya koma office d'insa ya na zama yakira number Dr A.A Fiya.
sai da ya kira sau uku a na hud'u ya d'aga.
Dr Imran ya ce
"A.A ban kira ka naji ko ka isa lafiya ba, tun dawowa na daga kaika airport dana shiga asibiti har yanzu ban fito ba, ko wanka banyi ba,
ashe guduwa kayi ka barmin aiki,
kaifa kasan aikin ka sai kai, kafara ka barwa mutum yarasa ta inda zai kare,
to dai gashi munsha da kyar 'yar da kake sawa mutuwa gata ta farka da bakin ta rau, Allah ya amsa ka mata jinya ta warke."
tsaki yaja ya ce
"To meye na kirana kana fad'a min wannan, sai ka sanarwa 'yan'uwanta ba ni ba."
"To ai kai ne kayi jinyarta shiyasa nake sanar maka nasarar da ka samu, ga Daddy a nan a tare da su nayi mamakin ganinsa a nan."
d'ip yaji ya kashe wayar tun kan ya karasa abinda zai fad'a
Dr Imran ya ciro wayar yana binsa da kallo,
bai damuba dan shi ba bakon sanin halin sa bane...........!
Mommyn Twins ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️20
Aunty ganin shiru-shiru Daddy bai dawo ba,
ta d'aga waya ta shiga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 20