Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kallon cikin d'akin, ganin babu gadon nata gaba d'aya a cikin bedroom d'in. "Ta ina tayi ko ta tashi garin rarrafe ta fad'o a gado ne, to ina ma ganon yake?." ta had'a tambayoyi wa kanta tana rarraba ido. da sauri ta d'aga kafa tana kokarin karasawa cikin d'akin. wani irin tsinkewa gaban kirjinta ya yi tayi baya da sauri, jikinta na wani irin cirawa tsoro da firgici suka dirar mata lokaci guda. gaba d'aya jikinta ya d'auki b'ari. Hango gadon Feeryal ya tashi sama tamkar ana lilata gadon yana juyawa shi kad'ai sai kyakyata dariya take. kamar yadda take mata wasa take b'allewa da dariya haka nan take yi, har tana mika hanu alamun a d'auke ta. Cikin kad'uwa da firgici Aunty takuma yin baya da karfi ta furta "Innalillahi'wa inna'ilaiihirraji'un!." ai ko kamar jira ake tayi magana. a hankali godon yashiga saukowa har ya diro kasa tamkar an dai-dai ta zamansa a gurin zaman sa. Karaf Feeryal ya saukakan Aunty, ganin Aunty tafara mika hanu ta d'auke ta, Aunty kuwa cikin hanzari ta bud'e kofa jiki na b'ari tayi waje cike da d'inbin tsoro. Tana jiyo kukanta bata ko waiga ba, a parlour ta tsaya tana maida numfashi, tare da dafe kirjinta dake dukan tara-tara!. addu'a tafarayi wanda duk yazo bakinta yi take tana saukewa. a matukar tsorace tashiga kwad'awa Baba Rabi kira. "Baba Rabi Baba Rabi!." da sauri Baba rabi ta fito tana amsa kiran, ganin yadda gaba d'aya ta rasa nutsuwarta Baba Rabi tashiga tambayar ta ba'asi. bata iya magana ba sai nuna kofar bedroom d'inta take da hannu. da sauri Baba Rabi ta nufi kofar bedroom d'in jiyo kukan Feeryal daga ciki. dan tagama tsinkewa wani abun ne ya sameta, ganin yadda gaba d'aya Aunty ta firgice. Tana shiga d'akin ta hangoto zaune a kan gadon ta tana kela kuka da mika hanu tana niman mai d'aukarta. da sauri ta karaso gareta ta sa hanu ta d'auke tana fad'in "Me ya same ki Feeryal Ammie'n ki ta shiga firgici? kuma dai gaki lafiya lau nagan ki, to ko wani abun tagani cikin bayi?." Tayi waje da ita tana jijjigata. ta taho in da Aunty take tsaye zuwa yanzu nutsuwa yafara shigarta da taimakon addu'o'in da take ta yi. ta mika mata ita tana fad'in "Hajiya wani abin kika gani ne cikin band'aki akirawo security suzo su cire? dama da an fara zafi wad'an nan muggan igiyoyin kasan zasu fara niman gurin sanyi su rika fitowa daga mab'uyarsu suna shigewa ramuka ta baya suna shigowa mutane ta cikin toilet." Ido Aunty ta kurwa Feeryal da tsoron ta ya kamata batare da ta karb'e ta ba, itako sai zillo take tana mika hanu tana so ta taje gurinta. "Rike ta naje na kirawo su suzo su kashe kada ya shige wani gurin a rasa shi." Baba Rabi ta kuma fad'i tana dad'a mika mata ita. Ja da baya tayi idon ta a kan ta tana kallon cikin kwayar idanunta farare soll masu sananin farin haske, kwayar idanunta madadin fari da d'igon ash, shi fari ne tas da d'igon green da d'igo-d'igon gold and ash a had'e. yanzu kuwa yadda'a sauyawa har wani kore'kore yake ga duk wan da yaga yanayin sai ya bashi tsoro. Ido Aunty ta rumtse tana kuma bud'e su a kanta, sai taga kalar ya ragu ya koma irin kalar idanunta. "Baba Rabi bakiga komai cikin d'akin ba?." "Babu komai cikin d'akin nan hajiya, sai dai naje na kirasun suzo su bincika kin san igiyar kasa basa tsoron mata." kai Aunty ta girgiza ta ce "Kar ki kirasu babu komai kawai na tsorata ne." Baba Rabi zata kuma magana Daddy ya shigo. Da sauri ta d'an rusna tana miko gaisuwa. ai ko Feeryal na ganin sa tafara miko masa hanu tana wage baki. ya karb'e ta yana amsa gaisuwar. da sauri Baba Rabi ta wuce kichin domin kammala aikin ta. Daddy ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour'n yana yi wa Feeryal wasa sai b'arkewa da dariya ta ke. har lokacin Aunty na tsaye jikinta a sanyaye. "Ya dai Ammie'n Feeryal wani abin ne?." cewar Daddy yana duban ta. kai ta girgiza jiki a sanyaye ta ce "A'a." ya jinjina kai yaci gaba da yiwa yarinyar wasa. A hankali Aunty ta ja kafafunta d'aya daga cikin bedrooms d'in parlour'n ta shiga, ba bedroom d'in kwanan ta ba, a nan tayi wanka. ta fito tana shirin yin sallar magriba da aka soma kira. Daddy ya shigo da Feeryal a kafad'ar sa tana bacci. "Yau an sauya mana gurin kwana ne dama an jima ba'a sauya ba." murmushi ta yi "Ba yau ba wanka kawai nayi a nan d'in zan koma can." "Feeryal tayi bacci tayi ta mita da alama yunwa take ji ko za'a tasheta tasha mama ta koma." "A'a abarta tayi bacci sai ta tashi, Daddy ka shinfid'a ta a can zanje nayi salla a bedroom ina." ta nuna kan bed d'in d'akin. Da sauri tayi waje yana kwantar da ita yabi bayan ta. "Fad'imatu." yakira sunan ta tana daf da shigewa d'aki. taja ta tsaya tare da waigowa gare shi. yakaraso in da take, idon sa a kanta ya ce "Wai me ke faruwa ne me ke da min ki? akwai abin da ke damun ki nafi kowa sanin ki." ido ta d'an lumshe ta bud'e su a kansa sannan ta ce "Daddy nafara shiga kokonto akan Feeryal, acikin kwanakin nan ina ganin wasu sauye-sauye tare da ita, idan na aje ta naje nayi aiki na sha zuwa nasame ta tana wasa ita d'aya tayi ta dariya kamar wanda take kallon wani da ni bana ganin sa; da fari ban d'auki hakan akomai ba nasan yaro yakan yi haka, amma yau Feeryal ta bani tsoro!." da sauri ta waiga jin kamar an wulga ta bayanta. ido Daddy ya kura mata ganin yadda taja numfashin tsoro. hannunsa ta rike gam sannan ta ce "Bakaji kamar an wuce ba?." kai ya girgiza ya ce "Banji ba." sai kuma ya janyo hannunta suka shige cikin bedroom. a bakin gado ya zaunar da ita yana tsaye a kanta ya dafa kafad'arta, ya dube ta da kyau sannan ya ce "Fad'imatu, kar dai ace maganar mutane yafara tasiri a kanki? kada ki bari kururuwan jama'a yayi galaba a kanki, ya akayi kika mance da addu'o'in ki, kefa kk tunasar da ni wani lokacin, duk in da bawa yake shed'an yana nan a gurin, haka aljanu duk in da muka sa kafarmu suma suna gurin, imma shed'anunsu imma na kirkinsu, sai dai mu bama ganin su, akwai hanyoyin da ake bi dan nisanta kai daga sharrin shaid'an ibilis da kuma shaid'anun aljanu, ina sammanin sai dai ki fad'awa wani dan kinsan hanyoyin, babu abun da shaid'an bazai iya ba ko kin mance wa'azin malam Aminu Daurawa ya ce shaid'an yakan zuba kasa akan gado, mata tayi shinfid'a tayi komai dan ya had'ata fad'a da mijinta?." ya karashe maganar da murmushi. kai ta jinjina ta ce "Amma Daddy kasan ya na shigo na tadda Feeryal kuwa, gadon ta yana lilo a sama fa tana ta dariya, ina tsaye ina gani kuma gadon ya sauko." d'an shiru ya yi alamun nazari sai kuma ya d'an dara ya ce "Da alama dai yau bakiyi Azkhar d'in yammaci ba, idan kikayi salla kiyi, kisa a ranki babu komai gizo ne kawai, sa rai akan abu yakansa kaga abun kamar ya faru, yau she kika fara yarda da maganganun mutane iye Fad'imatu? kada ki bari maganganun su ya yi tasiri a zuciyar ki, har yayi nasarar hanaki taimakon rai da kika d'au himma." "Ban tab'a yarda da maganar mutane ba, ban tab'a jin Feeryal amatsayin aljana ba, kawai abin da nagani ne yasani shiga shakku." Nurmushi Daddy ya yi dan son share mata shakkunta yakuma karfafa mata guiwa ya ce "Gizo ne kawai kinsan wani lokacin haka d'an adam yake musamman wad'an da damuwa tayi musu yawa a kwakwalwa, yau dai da alama kin shiga sahun su, bari na tafi masallaci kada na rasa salla babu komai Ammie'n Feeryal kiyi addu'a kinji." Kai ta girgiza tare da sauke numfashi, yafita zuwa masallaci ita kuma tamike domin gabatar da sallah. Tajima tana addu'o'i har sallar ishe yasame ta kan sallaya. bayan ta gabatar ta mike ta shirya ta fito, tana jin zuciyarta wasai nutsuwa na shigarta. D'akin da Feeryal ke bacci ta shiga, ta isketa tana ta baccinta. ta d'auko ta, ta mai da ita bedroom d'in ta. Washegari da safe bayan Aunty tagama kimsa side d'inta da taimakon Baba Rabi, kamar yadda suka saba idan Daddy yana gurin ta, tun kan Daddy ya fito parlour Baba Rabi take shigowa side d'in. ta gyara parlour zuwa kichin, ta tanadar mata da duk abin da tasan zatayi amfani da shi na breakfast a kusa, sannan ta koma b'angaren su na ma'aikatan gidan. dan a iya nan aikin ta ya tsaya dan ko gyaran bedrooms d'in cikin side d'in Aunty ke yi da kanta, idan kaga Babaa Rabi tayi girki; to Daddy baya side d'in. bayan Aunty ta fito ta wuce kichin ta tadda Baba Rabi ta tanadar mata da duk abin da zata bukata kusa, nan ta soma had'a breakfast d'in da tasan Daddy ya fi so. Bayan ta gama ta kwaso hadaddun breakfast data shirya wajen kala uku ta kawo su kan dinning. ko da ta koma bedroom ta tadda Daddy ya farka, ta wuce bathroom ta had'a masa ruwan wanka. bayan yafito ya shirya yafito parlour. a tare suka yi breakfast cikin plt d'aya kamar yadda suka saba. Bayan sun kammala Daddy ya dawo parlour yana kallon labarai. Aunty ko na kichin tana wanke kwanukan da suka b'ata. kukan Feeryal da tajiyo ne yasa ta fita da sauri tana fad'in "An tashi ke nan." Daddy da ya mike zuwa d'auko ta ganin fitowar Aunty yasashi komawa ya zauna. Da sauri ta kara cikin d'akin ta d'auke ta tana jijjigata. "Ya isa ayi shiru antashi ne yunwa ake ji ne?." tana fad'i tana bubbuga bayanta. ta zauna bakin gado sai da ta rarrasheta tayi shiru, sannan ta mike ta aje ta a kasa tana fad'in "Nasan hali zauna a kasa bazan aje ki a kan gado ki fad'o ba, ba'a iya rarrafe ba sai rawar kai, zauna muzo muyi wanka, yau muyi anan ba sai munje bayi ba." ta shige bayi ta had'o ruwan wankan a bawo mai d'an girma ta fito. Feeryal na zaune a gefe tana ta wasa da abin wasan da ta saka mata shi a gabanta. d'an gajeren tsaki Aunty taja, tuno da bata d'auko sabulu ba ta mike ta koma bayin. Ta fito d'auke da sabulu turus taja ta tsaya bakin kofar bayin tana kallon Feeryal da ta ganta cikin bawon wanka, ga kuma kayanta a gefe an cire mata, tana zaune cikin ruwa sai wasa take tana dariya. tana mika hanu kuma alamun a d'auketa tana kuma kallon gabanta tana cigaba da dariyar da kuma mika hanun ma wanda ita bata ganinsa. Bin cikin d'akin tayi da kallo tana tunanin ko wani ne ya shigo ya tub'e mata kayan ya sata cikin bawun d'in. babu kowa cikin d'akin babu wani alamar da ya nuna wani ya shigo daga d'an shigarta bayi d'aukar sabulu zuwa fitowarta, da bai wuce second 40 zuwa minti 1 ba. ta kuma san ba Daddy bane dan shi bazai barta a cikin ruwa mai yawa haka yafita ba. Numfashi taja sai kuma ta d'an saki murmushi ya yin da take karanto wasu addu'o'i cikin ranta, tana fata idan abin da take tunani hakan ne to surabu da ita lafiya dan ita bada niyyar cutarwa ta d'au ko ta ba. ta karaso in da take tana fad'in "Nab'ata lokaci wajen d'auko sabulu ko? bari nayi miki wankan ki ko Baby'n Ammie'n ta." kamar wacce ta fahimci abin da take fad'a tashiga bubbuga hanunta cikin ruwan tana yin irin yadda yara suke idan suna cikin ruwan wanka suna wasa da shi. da karfin addu'ar da take taga ma yi mata wanka, kana ta shirya ta cikin kaya masu kyau da tsada. sannan ta d'auko ta suka fito parlour bayan ta gyara in da suka b'ata. Daddy na ganin su ya mika hanu itama ta wage baki ya karb'eta yana cillata sama, tana kyakyata dariya. Aunty ta bisu da murmushi. har Daddy ya fita batayi masa hirar abin da tagani ba, dan tasan yanzun ma ce mata zai yi gizo ne... Da yamma Aunty na kichin tana aiki, Feeryal kuma na parlour tana wasa a zaune da kayan wasanta. lokaci zuwa lokaci take fitowa duba ta. ta kwaso kulolin abinci kan babban tray tanufi dinning da shi. tun kan ta karaso dinning d'in take kallon ikon Allah. Feeryal ce zaune a tsakiyar dinning hannunta biyu cikin bama tana sha tana kwab'awa, ta kwab'a bakinta da fuskanta gaba d'aya, sai ta kwamulo shi ta mika hanu alamun tana mikawa wani sai a karb'a sai dai bata ganin mai karb'ar sai dai taga babu komai a hannunta. A hankali Aunty ta juya ta dawo parlour ta dire tray'n kan table d'in parlour, sannan ta koma kichin da sauri bata bari ta ganta ba. suka cigaba da gyara kichin d'in tare da Baba Rabi. bata fitoba sai da suka gama komai suka fito tare da Baba Rabi. Abin mamaki a zaune a tsakiyar parlour in da ta aje ta da fari tana wasa, agurin yanzu ta tarar da ita, zaune tana wasa, jikin ta tsaf babu d'in komai. kallon saman dinning tayi shima a kimtse komai na zaune a gurin zamansa. Baba Rabi tayi wa Aunty sai da safe tayi waje bayan ta gama yi wa Feeryal d'in wasa, har Aunty ta juya zata wuce bedroom sai kuma ta juyo ta dawo inda take ta mika hannun zata d'auke ta ba shiri ta cire hannunta a cikin ta tayi wani irin mikewa ta ja da baya da sauri jiki na rawa.........! Mommyn Twins ce 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *Bismillahirrahmanurrahim* 🅿️5 Wani zabgegen maciji tagani sakankanin kafafuwanta, a kanannad'e acure guri guda ya fasa kai. takuma yin baya a muguwar razane, da karfi ta furta "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!." cikin tsananin kad'uwa. tana furta kalmar innalillahi da sauri macijin ya shiga ware jikinsa yana bi ta kan kafafun Feeryal da ke zaune tana wasa da shi, yanufi kofa yana isa dai-dai bakin kofa ta nime shi ko sama ko kasa ya b'ace mata bat bata kuma ganinsa ba, bata kuma san ta in da ya bi ba dan kofar a rufe take. Rasashi ke da wuya tasoma jin wani kara mai cike da amon sauti na dukar can cikin kunnuwanta. da karfi ta rumtse ido tare da kai hannu cikin kunnenta da take ji kamar dodon kunnuwan nata zasu zazzago su fito waje. ji tayi ana fad'in "Ke kad'ai bazaki iya bata kariya ba dole sai da taimakon muuuu!." kuma toshe kunnuwanta tayi da karfi tana juyi had'e da tangad'i har sai da ta zube kasa. a dai-dai lokacin da taji kamar an fisge mata dodon kunne, nan da nan wani uban zufa ya shiga keto mata. a hankali kuma taji yanayin ya d'auke cak cikin second 1 tadawo dai-dai. Da sauri ta mike zaune tashi ja da baya tana bin Feeryal da kallon tsaro. ita ko yarinyar baki ta b'are tana mika mata hanu alamun ta d'auke ta. Cikin rawar murya Aunty tashiga fad'in "Ban tab'a cutar da ke ba, ban d'auko ki dan na cutar da ke ba, sai dan na taimake ki, ki dubi girman Allah kada ki cutar da ni, zan mai da ke in da na d'auko ki, nayi zaton ke d'in jinsin mu ne shiyasa na d'auko ki, ban d'auko ki dan na cutar da ke ba!." Gaba d'aya Aunty ta birkice ta ko ta ina a jikinta b'ari yake, tsoro mai tsanani ya baibaye ta. ta kasa iya mikewa kan jafafunta sai ja da baya take a zaune. Jin karar bud'e kofa ta waigo da sauri a bala'in razane, dan tagama zaton macijin ne ya dawo. ganin Daddy ne ya shigo da sauri ta mike a guje tayi gurin shi, ta fad'a jikin shi ta kankameshi da karfi tana fad'in "Daddy maciji na ganshi da ido na! dan Allah ka d'auke ta ka mai da ita in da muka d'auko ta, wlh nahakura zanci cigaba da zama a haka gara na tabbata a matsayin juya, na hakura bana son d'a zanyi rayuwa ta ni kad'ai a haka!." Da sauri yadad'a rukota sosai ganin yadda gaba d'aya ta fita hayyacin ta. ya janyo ta suka karaso cikin parlour, ya zauna kan kujera tare da zaunar da ita a gefen sa. "Fad'imatu." ya kira sunan ta yana kallon fuskarta. ido ta zuba masa sai kuma ta girgiza kanta kamar wacce ke son dawowa hayyacin ta. ta yunkura zata mike da sauri ya ruko ta yakuma duban ta da kyau ya ce "Ki dawo hayyacin ki." wani nannauyan numfashi ta sauke da sauri ta waiga gefe da gefen ta sai kuma ta maida duban ta gareshi. "Fad'imatu." yakuma kiran sunan ta murya a raunace. kai ta girgiza ta ce "Daddy." "Numfashi ya fesar sannan yakuma rukota da kyau ya ce "A ina kika ga macijin Fad'imatu? akaf fad'in gidan nan da kewayen sa, ba macijiba ko kwaro in har mai cutar wa ne bai isa ya matso yankin gidan nan ba, ta ko wane kusurwa; tazarar taku dubu ne ta ko wata kusurwa sakanin mu da duk wani nau'in kwaro mai cutar wa, ko ta sama ko ta kasa, sam maciji bazai iya shigowa gidan nan ba, a zagaye gidan nan yake da maganin su, idan kuwa sukayi gigin shiga to kuwa zasu mutu tun kan su karaso, koda ta cikin karkashin k'asa ne kuwa." "Daddy na ganshi da ido na fa babba ne sosai agaban Feeryal tana wasa da shi, kuma naji ana magana da karfi kamar za'a fasa min kunne, ni dai a maida ita kawai wlh na hakura." shiru ya yi yana kallonta a kasan ransa yake fad'in "Anya ba aljanu ne ke son shafarta ba?." kwana biyu gaba d'aya yaga yanayin ta ya sauya, abin da bazai faruba tarika cewa ya faru. kai ya jinjina sannan ya ce "Gizo ne kawai." da sauri ta ce "A'a Daddy wannan kam ba gizo bane nagani da ido na da gaske ne." "D'azu bakya hayyacin ki Fad'imatu akwai abin da ke shirin faruwa da ke, yakamata a dakile faruwar hakan, ina zuwa." Yafad'a yana mikewa ya nufi bedroom yafito d'auke da Alkur'ani mai girma ya dawo in da take, ya bud'e ya mika mata. ya ce "Kirika karantawa ina zuwa, bari naje na dawo, dan shi yafi komai kariya." Ya isa ya d'auki Feeryal data fara kuka ya ajeta a gefenta. yana cewa "Ta gaji da zamane ko tana jin yunwa." ido ta bita da shi harga Allah tsoro take bata yanzu. Cikin hanzari yafita, Daddy yakai awa d'aya zuwa d'aya da rabi kafin ya dawo. a bedroom ya same su dan ta sami kwarin gwuiwa da taimakon karanta Alkur'anin da tayi, har ta ji karfin zuciya ta d'auke ta ta je tamata wanka, tana gama shiryata kuwa tayi bacci. Daddy ya mika mata kullin laidar daya shigo da shi. ta karb'i laidar tana d'an jujjuyashi a hannunta sai kuma ta kunce laidar. da mamaki take kallon kulli-kullin magunguna. da fuskar tambaya ta dube shi, sai kuma taga ya d'au abin saka kuraren wuta ya jona shi gijin wuta, yana fad'in "Hayaki ne da wanka na karb'o miki, zo maza kiyi hayakin anjima in zaki kwanta kiyi wankan maganin sai ki kara yin hayakin." "Hayaki da wanka kuma? asabo da me ni fa lafiya ta kalau." kai ya girgiza ganin ba tasowar zatayi ba ya janyo hanunta. "Aljanu na son shafarki kice lafiyan ki lau, ina kuwa batun lafiya anan." "Daddy kada ka rika yarda da wad'annan masu magungunan karyar fa." "Zauna dan Allah." ya yi maganar yana zaunar da ita. da kansa ya bud'e yahakin ya saka yakuma rufeta da hijabinta kamar yadda aka ce masa. sai da ya tabbatar hayakin ya ratsata sosai tana ta sauke tari da atishawa kafin ya bud'e ta. yana fad'in "Sai dai su kare a haka amma bazasu tab'a samin damar shigar jikin ki ba." ita dai ido ta bisa da shi. Da daddare kafin ta kwanta sai da ya tabbatar da tayi wankan maganin da hayaki. duk da bataso ba. Washegari da safe Aunty ta fito zata nufi kichin, tana bud'e kofar bedroom taga wani katon zomo fari soll, idanunsa manya masu matukar razanarwa. yana zaune a dai-dai tsakiyar bakin kofa, ya d'aga kunnuwansa sama yana juya idanun nasa da sam basuyi kama da idanun zomo ba. wani irin juyi ta yi da farfe ta maida kofar ta rufe. Tana waigowa kirjin ta ne yawani irin tsinkewa hango sa da tayi kan gadon Feeryal, wacce ke bacci yanzu kafin ta fita sai da ta gyara mata kwanci, sai ga shi ta ganta zaune suna wasa da zomon da ta gani a bakin kofa, yanzu-yanzu da ko second 1 baiyi ba wani uban kara ta sake sakanakon had'a ido da shi da idanunsa masu matukar ban tsoro. ta yanke jiki ta zube kasa. Da sauri had'e da gudu Daddy dake cikin bathroom yafito, ya yi kanta cikin hanzari yana jijjigata da kiran sunan ta. gani bata ko motsi da sauri yaje ya d'au gorar ruwa yazo ya yayyafa mata. numfashi mai karfi ta sauke ta zabura zata mike, da sauri ya ruko ta. "Fad'imatu mene ne ki natsu." hannu ta shiga nunawa in da Feeryal ta ke "Yana can yana can akwai wani abakin kofa." ya waiga in da take nuna masa baiga komai ba, sai Feeryal da ke zaune. ya ce "Babu komai fa ni ban ga komai ba, bakiyi hayakin nan ba yau, muje maza kiyi." ya d'agota suka karasa cikin d'akin. Ranar haka Aunty ta wuni sukuku lamarin nason fin karfinta★★ Tekun Matip acan cikin fadar sarkin aljanu Matip, dake karkashin teku cikin wani katon kasurgumin kogo mai matukar girma. duniya ce guda a gurin. matakan tsaro ne jiga-jigai masu matukar had'ari. kifaffen masarautar da aka kifeshi tun tsawon shekaru d'ari biyu da hamsin da suka shud'e. shine yakuma dawowa daram. shugaba sarkin aljanu Matip yake cigaba da mulkarsa. bayan tsawon shekarun da ya yi a tsare a kuma garkame sakamakon faruwar wani lamari. Manya-manyan jiga-jigan dodanni aljanu majiya karfi masu tsuffar ban tsoro ne ke tsaron kofar masarautar, tasama da kasa. Acikin fada sarki aljani Matip ne zaune a kan karagarsa na alfarma da aka yi sa da gundarin zinari. ya yin da fadawa ke zagaye da shi. Sarki aljani Matip ya dubi wazirinsa Kutub sannan ya yi gyaran murya, ya ce "Akirawo Tarmuzu yanzun nan." waziri Kutub ya dukar da kai ya ce "Angama ya shugaba na." wani kambu dake rike da shi ya murza cikin second 1 wani aljani ya bayyana a gaban sarki Matip. yazube gaban sa yana fad'in "Na amsa kira ya shugaba na." Sarki Matip ya dubesa sannan ya ce "Tarmuzu Kudakata haka ku dai na bayyana ta ko wata tsuffa kuna razanin uwar gijiyarta, zata rasa samin kula yadda ya kamata idan hakan ta faru kuma bazan yafe muku ba!." "Tuba muke ya shugaba na a gafarce mu." aljani Matip ya girgiza kai sannan ya d'aga masa hanu, nan take yab'ace.. Kimanin sati biyu kenan Aunty bata cikin walwalar ta, sai baya-baya take da Feeryal burin ta dai surabu lafiya. kullum dai Daddy na karfafata da bata kwarin gwuiwa, yana ta so yaga ta cire kokonto kan Feeryal d'in, duk da shima yanzu lamarin yafara jefashi cikin nazari. sun shefe tsawon sati gudannan bata kuma ganin wani abin tare da Feeryal ba. sai dai wani lokacin idan ta barta ita kad'ai takanzo ta same ta tana ta wasa kamar tana yi da wani, haka nan zata d'auke ta, dan tayi alkawarin cigaba da kulawa da ita, amma cikin takasantsan burin ta dai surabu lafiya..★★ Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Feeryal nata dad'a kara wayo, ya yin da suffarta dake saka kokonto cikin zukatan duk wanda ya ganta ke dad'a karuwa. zuwa yanzu Aunty ta saki zuciyar ta da Feeryal. har ta yarda abaya wancan lokacin da take gane-ganen Feeryal tana wasu abubuwan da gaske gizo ne, da kuma sharrin shed'anun aljanu da suke son shafarta kamar yadda Daddy ya fad'a mata. sosai ta dawo kula da d'iyarta. tuni Feeryal ta kai na yaye aka yaye ta.. Kamar wasa rayuwa mai tafiya da sauri shekarun Feeryal hud'u ke nan, amma a zahiri idan ka ganta zaka iya kira mata shekaru biyar har da d'ori. Aunty bata barinta fita ko nan da can, iyakacin ta cikin side d'in da farfajiyar sa zuwa garden d'in cikin side d'in. bata zuwa side d'in kowa a gidan, kamar yadda kowa ma baya zuwa nasu side d'in. in banda Hajiya Safiyyah da kuma 'yarta Meimei sa'ar Feeryal ce, sai dai ta d'an girme mata ita shekarunta shida ke nan, amma kusan tsawon su d'aya, sosai Feeryal ta saba da Meimei, Hajiya Safiyyah tana kawota suyi wasa da ita. Ganin bakinta ya bud'e sosai da magana, Daddy yace za'a sata a makarantar su Ameerah. Ranar wata juma'a Daddy na zaune a parlour'n sa yana waya. Mommy ta shigo parlour'n ta

Chapter 4 of 20