a cikin motar in da Sule direba ke zaune yana zaman jiran ta a cikin mota.
wani katon kogo dake gaba da itaciyar ta nufa.
a bakin kogon ta cire takalmarta da mayafin ta,
ta kunce d'ankwalin kanta duk ta had'a ta ajesu a gurin.
ta shige cikin doguwar kogon nan mai zurfi ba d'ankwali ba mayafi ba takalmi.
fad'i ta ke
"Gafara dai boka sannunka dai mai magance matsala ko wacce iri ce."
wani irin kazamin dariya aka kece da shi gaba d'aya cikin kogon yake amsa sautin dariya mara dad'in ji.
ya yin da ake fad'i
"Kinyi dogon nazari mu ke magance matsala, duk bukatar da kika zo da shi kin samu."
"Godiya nake boka godiya nake ubanmu maganin kukan mu,
tun da muka rike ka babu abun da muka rasa."
ta zube a gaban shi ta nad'e kafafuwa kamar mai niman gafara.
yana zaune a kan wata kujerar tsafi wani jan kyalle d'aure a jikinsa, yana rike da sandar tsafin sa.
suffarsa sam babu kyan gani.
ya mike tsaya yana cigaba da wannan kazamar dariyar mara dad'in saurara ya mika hannu ya d'aura a tsakiyar kanta da babu d'ankwali.
yana zazzare manyan idanuwansa munana masu ban tsoro.
zuwa can ya janye hannun nasa yakoma ya zauna kan kujerar sa yana fad'in
"Mun ga bukatar ki me kike so ayi musu?."
Ta gyara zama da sauri tana fad'in
"Yauwa boka Mali shugaban mu mai share mana kukan mu,
so nake a haukata Hajiya Fatima ta bazama duniya hauka na har abada babu warkewa,
da naso a kashe ta ne amma idan aka kasheta ai an mata gata ne a haukata ta kawai kada ta warke har a bada,
taje tayi ta wahala tana bin kwararo-kwararo bola-bola,
daga nan kuma ita yarinyar da take hannunta dole ta bar gidan,
dama zaman Hajiya Fatima a gidan shi ya zaunar da ita daga zaran ta haukace ta bar gidan dole itama ta bar gidan."
sandar da ke hannunsa ya bukashi kan wani kasa da ke tare a gaban sa,
yana jujjiya gwalagwalan idonunsa kan kasar sannan ya ke ce da dariya
"Kin samu bukatarki ta biya,
lallai tabbas Hajiya Fatima zata haukace,
hauka mafi muni,
zamu tura mata bakin aljani daga zaran sunyi ido biyu da ita to zance ya kare hauka tuburan zatayi shi mara warkewa;
sai dai wani hanzari ba gudu ba,
sashinta yana zageye da kariya irin na addu'o'in da take kullum safiya da maraice,
bakin aljani bazai iya tinkarar gurin ba zai iya konewa,
bari dai mu samo wata mafitar."
yakuma buga sandar sa yana juya ido can kuma ya d'ago yana cewa
"Mafita d'aya ce ta in da zaibi ya shige sashin nata,
dole ta sama zaibi bayan munyi masa shirin kariya daga konewa,
ya sauka a gurin najasa dole a band'aki zai sauka,
daga nan bazai iya matsawa ko ina ba, dole a gurin zai zauna yajirata har san da zata shigo bayi, daga nan kuma zance ya kare sai dai watan ta ba dai ita ba,
nan da kwanaki uku zamu tura bakin aljani bayan mun gama masa shiri daga kariyar konewa."
Umma karima ta shiga masa godiya kamar zatayi masa sujjada.
kana ta d'aura da fad'in
"Allah ya ja kwanan boka ina batun kanwata Siyama da d'an mijina Abdurrahim ya kwana,
akwai wata 'yar kawar mamarsa da suke son had'asa da ita Kuraiba 'yar Hajiya Luba, kasan damuwata ai na wancan maganar ta baya,
to ina so a birkita masa lissafi daga zaran ya diro Nigeria yaji duk duniya babu wacce yake so sai Siyama,
tanan ne zamu dad'a samin nasarar wajen cimma burin mu,
sannan game da 'ya'ya na fa har yanzu babu wanda ya fito da niyyar aure,
ita babban 'yata ma Bilkisu da muka samu muka cafke saurayin yace za'ayi aure sutafi
can kasar Japan tare tun da yasa kafa yabar kasar ya dai na kiran ta ma,
babban burina boka ace nima ga d'iyata tayi aure a wata kasa kamar dai Farida 'yar mijin nan nawa,
shekara goma ke nan suna can ba me jin kansu,
boka abinnan na dami na su rai uku babu wani d'an
mai kud'in da yazo yace yana son su da aure,
idan suka zo suka yi hira idan suka tafi sun tafi ke nan,
yanzu maganar da nake maka har karamar su Nabila itama ta zamo budurwa,
boka a taimake ni a karkato da hankali Bilal ya dawo ayi auren nan,
sannan suma sauran a samo musu wasu 'ya'yan manyan suzo su aure su, kamar dai yadda aka karkato mana da hankalin Bilal d'in da dai."
ya ce
"Duk wannan ba matsala bace kin samu."
"Godiya nake boka."
ta bud'e jaka ta rika ciro kud'i tana tara masa a gabansa tana aikin zuba masa godiya da kirari.
har ta mike ta dawo ta zube kasa tana fad'in
"Boka ina ajiyayyen aikin mu?."
"Gashi can cikin tulu a d'ad'd'aure har yanzu kin kasa samo cikiton na karshen, kina kawowa shikenan matsalar ki ta kare."
ta mike tana fad'in
"Na ukun ma bazai gagara ba tun da aka samo biyu, zanje nacigaba da farauta, kannan duk wad'annan matsalolin sun kau."
ta fice cikin kogon tana ta zabga masa godiya.
ta fito ta d'au d'ankwalinta da mayafi da takalmi duk ta saka sannan ta nufi mota ta shige suka juya gida.
Zaraddin ne ya shigo parlour'n Mom d'in su yana magana cikin kunkuni.
"Ai an dad'e ana nuna mana wariya, wlh nayi kud'i babu wan da zan taimaka."
Mom da Shamsuddin suna zaune a parkour.
Shamsuddin ko kallon sa baiyi ba,
Mom ce ta d'ago tana duban sa ta ce
"Kai da waye kuma?."
ya ce "Daddy mana wlh tun ba yau ba yake nuna mana wariya bamu gene bane kawai,
in dai hidimar Ajmaal ne baya bincike zakiga ya bashi ko nawa ne,
wai yanzu naje ya bani wasu 'yan kud'in da basu kai sun kawo ba, amma ya tsaya bincike na wai me zan dasu,
kamar ni d'in nan wai sai an tambaye ni abin da zanyi da kud'i,
abokai na kaga kowa yana abinda yaga dama da kud'i amma wai ni baza'a bani kud'i nayi abin da naga dama da su ba,
in za'a banin ma baza'a bani na kirki ba kuma wai sai an tsaya yi min binciken me zanyi da su,
bawai babu kud'i ba gasunan baza'a bawa mutum ya yi abinda yake so ba,
wai yanzu naje ya bani 5 million zamuyi biki ya tsaya yana ta yi min wasu bincike,
ina gurin Ajmal yazo ya tambaye shi kud'i ya tura masa ba tare da wani bincike ba,
haka wancan karon naje ya bani 2 million ya d'auki million d'aya da rabi ya bani,
ina zauna a gurin ya turawa su Ajmal d'in abin da ya bani bayan ni na fara tambaya,
a fili yake nuna banbanci,
na rantse bazan sake zuwa tambayar sa kud'i bama,
bare a tsaya yimin bincike kamar b'arawo."
Shamsuddin ya harare sa yana fad'in
"Kai wlh baka da godiyan Allah Zaraddin, ai kuwa baka isa kace Daddy yana nuna wariya tsakanimu ba,
aiko kaf cikinmu bawan da yake yawan zuwa neman kudi masu yawa akai-akai ba sai kai,
bini-bini kaje neman kudi agun Daddy kuma ajmal
dakaga yanemi kudi yanzu abu me muhimmanchi zaiyi,
kaikumafa club zakaje dashi ko wancan karon ma daka nemi million biyu
akabamu million daya da rabi rabi mu hidiman karatu zamuyi dashi,
amma kai kumafa naka party kayi dasu."
Mom tace wa Shamsudeen
"Rufa min baki da'alla shikenan mutum bazai fad'i abin da ke damunsa ba,
ya huta sai yabar damuwa a cikin sa ta kasheshi,
ni wlh Shamsudden kana bani mamaki kai da d'an uwanka twins brother naka amma kafi fifita wasu akanshi."
Shamsuddin yagirgiza kai yace
"Mom wlhy Daddy yana iya kokarin shi akanmu,
ko Dad daya haifemu bayamana kokarin da Daddy yakemana,
shifa yadauki nauyin karatunmu harmuka gama yasamamana aiki,
kai kaki nutsuwa ka kammala karatun,
kullum kuma yana damuwa kan ka koma makaranta,
kuma dukda yasama mana aiki muna karb'ar albashi,
amma shi yake bamu kudin man da muke sawa a motocinmu idan zamu fita,
bai ware ba kuma har da kai yake baka."
dogon tsaki
Zaraddin ya yi
ya ce "Wannan duk lissafin ka ne baka san cikin sa ba."
Shamsuddin ya girgiza kai ya mike ya yi ficewarsa. Mom natafad'a shikenan ga gaskiya karara amma ahana mutum fada.
Tun daga dinning Aunty ke kiran Feeryal
"Yanmatan Ammie wai har yanzu ba'a gama wankan bane,
yi sauri ki fito ki karya mana, karfe 12 saura bakiyi breakfast ba?."
ta iso bakin kofarta ta tura d'an jim tayi a bakin kofar jin tana magana had'e da dariya.
tasan Miemie bata zo ba da kawayenta
Chuchu da Chulu take, sai ta janyo mata kofar ta koma da baya.
ta gama shirya breakfast kafin ta dawo
ta turo kofar Feeryal tana fad'in
"Ke Feeryal wai har yanzu baki yi wankan bane?."
Feeryal dake zaune gaban mirror tana murza mai a jikinta, ta langwab'ar da kai cikin siririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ammie nayi fa yanzu zan sa kaya."
"To yi maza ki fito ki yi breakfast."
ta juya ta janyo mata kofa.
ta mike tana duban Chuchu da Chulu ta ce
"Idan nayi breakfast anjima zamuje gyaran gashi da Miemie,
ko zakuje?."
sukace a'a mu zamu tafi in kun dawo zamu dawo.
"Feeryal ki fito mana tun d'azu na zuba miki abincin sai ya yi sanyi ne."
"Nagi zuwa Ammie."
tayi parlour da sauri suma suka kama gabansu.
A saman dinning ta tadda Aunty ta zauna tana fad'in
"Ammie ina cake d'in? shi zan fara ciki."
Aunty da ta kura mata ido har ta zauna ta ce
"Gashi nan cikin plt d'in can, ke Feeryal ya naga kamar babu bra a jikin ki?."
baki ta d'an cuno murya a shagwab'e ta ce
"Ammie zafi-zafi yake min kamar yana mistsina na."
hab'a Aunty ta rike
ta ce
"Au shiyasa kullum bana ganin ki da shi, na d'auka ai ko dun kina zaune a gida ne kawai,
har in zaki fita ma bazakisa bra ba, dubi kirjinki kallo d'aya za'ayi miki asan bakisa bra ba,
kina tafiya nono na motsi cikin riga,
hauka kike Feeryal ko ma me bra'n yake miki bazaki sakaye kirjinki ba,
ko da shike ba laifin ki bane laifin Maryam ce, da take ganin ki kina yawo haka,
idan Hajja Umma bata lura ba ita da kuke kwana tare ku tashi tasan sarai bakya sawa kuma bata nuna miki ki sa ba."
Aunty ta janyo wayarta dake d'aure saman dinning ta na cigaba da fad'in
"Ai ko a can Abuja da babu maza cikin gidan bayan ma'aikata da suke waje, zaki sakaye kirjinki bare kuma nan da muke da manyan kattin maza."
lambar Maryam Aunty ta kira bugu d'aya ana biyu ta d'aga.
daga cikin wayar Maryam ta ce
"Aunty Faty ina kwana ya Feeryal."
"Ba gaisuwa na kira kiyi min ba, dan tsabar rashin hankali kina kallon Feeryal tana yawo haka da kirji a tsastsaye suna motsi cikin kaya baki tab'a ce tasa bra ba,
kina da hankali kuwa Maryam."
"Ayya Aunty Faty ki tsaya kiji, Allah kullum idan zatasa kaya sai na ce ta saka bra,
ita ke kin sawa wai mistsinin ta yake, har Hajja Umma ma nafad'a mata ita tace na rabu da ita tun da yana damin ta."
"Da manyan nonuwa a tsastsaye suna rawa cikin rigar za'a kyale ta tana yawo haka,
nifa banga laifin kowa ba laifin ki kad'ai nagani, kuma zaki gamu da ni."
Aunty ta kashe wayar tana cigaba da fad'in
"Taya za'a bari ki rika yawo haka ai koma me bra yake miki haka zaki daure kirika sawa,
taso maza muje ki saka yanzu, da haka zaki koya har ki saba."
ta janyo hannunta suka nufi d'akin ta.
Aunty tayi mamakin ganin tarin bra cikin kayanta da suka kai kusan guda talatin, da yawa kuma sabbi ne bata tab'a sakasu ba.
ta d'au guda ta mika mata ta ce
"Maza ki saka ki fito yanzu ina jiran ki a parlour."
kamar zatayi kuka tana ta shagwab'ewa har da bubbuga kafa a kasa,
wai iti mistsinin ta yake kuma yana shaketa ya hanata numfashi.
Aunty ta ce
tasa haka maza ta fito yanzu ba da itaba ga kattin maza a gida tana yawo kirji na tsalle a cikin riga.
Ko da ta saka ta fito Aunty ta ce
"Ko ke fa bakiga abubuwan sun kama kansu sun zauna cif sun nutsu a cikin bra ba, ina amfanin kina motsi suna motsi suma."
"Allah Ammie cizona yake."
"Ai saboda baki saba sawa bane kina sabawa zai daina, maza ci abinci."
ta turo mata plt guda biyu gabanta dana cake dana soyayyen kwai da dankali.
tana gamawa kiran Miemie na shigowa wayarta ta d'a Miemie ta ce
"Feeryal fito mu tafi gani a bakin get d'in Aunty."
ta mike tana sanarwa Aunty abinda Miemie ta fad'a mata.
Aunty ta ce
"Ki kula sosai Feeryal kar ku dad'e ana gama muku kada ku tsaya ko ina ku dawo gida."
ta ce tom.
ta gyara rolling d'in gyalen abayar jikin ta, sannan ta nufi waje.
Aunty na ta yimata kashedin kada ta tsaya ko ina suna gama abin da zasuyi su dawo gida.
Atsaye ta tadda Miemie abakin gat d'in Aunty, Miemie ta ce
"Wow kefa kullun kamar kara miki kyau akeyi, muje ko,
mtss hmm ga matar can Umma Karima nafito ina magana wa isa driver ya d'auko mota yakaimu anguwa,
shine ta fito wai yazo yajemata aika kamar batada driver da zaije mata aika ne,
zomuje drivern Ammah yakaimu."
Feeryal ta ce
"Kibari kawai naje na karb'o keyn motan Ammie'na sai nayi deriving namu,
sai dai amma zaki dinga nunamin hanya tunda bansaniba."
Miemie ta ce
"Too lallai ma Feeryal kin iya tuki ne?
ko so kike kije ki zubar damu a hanya."
Feeryal tayi murmushi sannan ta ce
"Na iya mana ni nake janmu na kaimu unguwa da Aunty Maryam."
ta juya tana kokarin komawa ciki,
sukaji horn a bayansu.
Miemie ta waiga tana fad'in
"Lah ya ajmal ne, muyake ma horn zomuje."
tajawo hannunta suka isa wajen motar.
Ajmal ya zuge gilashin motar ya dube su yana cewa "Miemie Feeryal inazuwa haka?."
Miemie tace
"Zamuje gyaran gashine Ya Ajmal."
Ajmal yace
"Kushiga muje na saukeku dama fita zanyi."
kafin yarufe baki Miemie tabude gaba tace
"Feeryal shiga muwuce."
Feeryal ta danyi jim tana dago kanta sai suka hada ido da Ajmal.
da sauri ta kawar da kai a hankali ta shige motar, Miemie kuma tashiga baya suka tafi.
Sunatafe Miemie tanata zuba surutu Feeryal kuwa nashiru dama ba gwanace wajen iya surutu ba.
jifa-jifa Ajmal yake dan satan kallonta,
harsuka isa wurin gyaran gashin,
Feeryal batace kalaba.
suna sauka a motar Ajmal yad'an leko ya ce
"Karfe nawa zaku gama?."
Miemie ta ce
"Bamu sani ba yai, sai yadda ta yiwu "
ya ce "Okay to idan kun gama ku kirani."
yaja motar yatafi.
suma suka wuce shagon gyaran gyashin.
Suna gamawa Miemie takirashi yazo yamayar dasu gida.
suna sauka amotar Feeryal ta dubeshi ta ce
Mungode."
yadan jijjiga kai tareda sakin murmushi yajuya da motansa zuwa site dinsu.
suma su Feeryal kowa tayi shashinsu bayan Miemie ta ce mata zata shigo anjima.
Feeryal nashiga ta tadda Aunty a parkour,
Aunty ta ce
"Har kun dawo."
ta ce Eh.
cikin sauri tawuce d'akin ta dan tana alla-alla taje tacire bra'n dake jikinta domin ba karamin takurata ya yi ba.
tana shiga tacire abayan dake jikinta ta dau towel ta d'aura tawuce bandaki.
tana shiga takunce towel ta ajiye,
tana kokarin zare bra'n,
sai ta d'an tsaya ta kasa kunne tayi shiru.
sai kuma da sauri ta janyo towel dinta ta d'aura, tafice da gudu tayi parlour.
ganin bata ga Aunty a parlour ba shige bedroom d'in ta.
Aunty dake kokarin shi ga bathroom ta ja ta tsaya ta ce
"Ke lafiyar ki meye na gudun har kin gama wankan?."
ta ce
"Ammie kamar kukan mage naji a bayin."
Aunty ta rike hab'a ta ce
"Kamane ina, bakiji ba dan shiririta kika fito."
cikin shagwab'a ta ce
"Ni kam Ammie tsoro nake ji bazan iya wankan a can ba."
Aunty ta dawo da baya tana fad'in
"To zo ki shiga kiyi wankan ki fito sai na shiga."
ta zauna bakin gado ita kuma Feeryal ta tura kofar bayin ta sa kanta ciki.
wani irin burki taja ya yin da tsikar jikinta ya wani irin tashi yarrr,
jikinta gaba d'aya ya d'auki b'ari
kar-kar-kar.........!
To masu karatu a nan na kawo karshen littafi na d'aya wanda tundaga farkonsa har karshensa Free ne.
idan ki-kana bukatar ci gaban labarin ka-ki biya naira 500 kacal domin samun cigaban sa.
tura ta wannan asusun
3170524141 Rashida Salihu first bank.
ko ki tuntub'e ni ta Whatsapp number ta
08034690723.
Idan har kina bibiyan litattafaina irin su
HAMDAH KARSASHI ALFARMA BAZAWARA CE'ITA
da da dai sauransu.
ina mai miki albishir da cewa
labarin FEERYAL ya kwan gabansu.
labari ne mai d'auke da sarkakiya cakwakiya murd'ad'd'iya.
ku dai ku biyo ni na warware muku zare da abawa.
Mommyn Twins ce Rasheedat S Director nake.
har kullum da ko yaushe ina godiya gareku masoyana.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 20