yayi bala'in sanyi, bata tab'a sammanin abin zaiyi tsamari har haka ba.
Mommy da Umma Karima suka bita da kallon banza, kowa yaja tsaki.
Umma Karima ta ce
"Babbar munafuka, d'a da gidan yayan uban sa ki tsige shi aciki da zallar iya munafurci, zan waiwayo ta kanki bawai na kyale ki bane."
Mom kuwa tsabar bakin ciki da tafasar zuci bata iya bita kanta Aunty ba juya fuuu ta yi side nata.
Ammah ce ta bubbuga kafad'ar Aunty ta ce
"Karki d'aura alhajin komai a kanki, baki da laifi ko kad'an."
kai Aunty girgiza jiki a sanyaye ta ce
"Wlh bansan har haka abun zai kai ba."
Ammah tayi saurin katse ta
"Yi tafiyar ki duk wanda yaji haushin ki ma shi ya sani, hukuncin da akayi masa shine dai-dai da abun da ya aikata, ko a fad'i ko kar a fad'i ma hakan ne,
yunkurin fyad'en da ya yi mata ba abun haushi bane sai hukuncin da aka yanke masa;
wlh ko Faisal ne ya aikata hakan ina goyon baya d'ari bisa d'ari fiye da hukuncin da aka yankewa Zaraddin."
Aunty bata kuma iya cewa komai ba taja Feeryal suka bar gurin.
Acan sashin Mom kuwa kai kawo tarika yi cikin parlour, tana taune baki had'e da jan tsaki ba adadi.
kamar jira take Dad ya shigo ta dira a kansa masifa take babu kakkautawa
"Yanzu ka goyi baya kan abun da akayi wa Zaraddin ke nan, kana kallon dukan da akayi masa kamar an kama d'an fad'in daji;
ya goyi bayan matarsa batare da kwakkwaran bincike ba,
acin bainin jama'a aka wulakanta ta shi, babban d'an naka;
kafin kasan dad'in wani d'a shi ka fara sanin nasa,
kana kallo aka tozarta shi, aka kore shi kakuma bada goyon baya,
to wlh bazan yadda ba d'ana bazai wulakanta ba,
zan bishi muje can muyi rayuwar mu a wani wajen,
kaci gaba da zama agidan sa zuciyar ka a muce,
sai abinda ya yanka ya tsara zaka bi;
kana da kud'in ka dai-dai misali kaje ka gina mana gida mu koma,
kyalkyalin wannan katon gidan ne ya zaunar da kai ko me, bazamu cigaba da zama ana juyamu son rai ba,
akan wani karamin laifin da bai ma aikata ba, za'a wulakanta shi a kore shi, wlh bazan zauna a gidan nan a cigaba da wulakanta min ya'ya na ba!."
Mom in da take shiga bata nan take fita ba Dad ya tare ta yana fad'in
"Ki saurare ni ki bani hankalin ki da kyau Hajiya Nafisat,
ke yau ne kad'ai kika tsinci kanki cikin jin haushin Alhaji Abubakar,
ni tsawon shikaru masu yawa na d'auka da dakon kiyayya da tsanar sa a zuciya ta,
har gobe ina tare da muradin d'aukar fansar abin da mahaifiyar sa tayi wa mahaifiya ta.
ta kasheta tare da kani na dake cikin ta;
domin ta mallaki dukiyar mahaifinmu ita da ya'yan ta su kad'ai,
gashi kuwa burinta ya cika d'an ta ya mallaki dukiyar mahaifin mu baki d'aya,
lokacin da mahaifinmu yake daf da mutuwa ya mallaka masa dukiyoyin sa, akayi rufa-rufa akace wai sayansu ya yi, karshe mu bamu tashi da abin kirki ba,
gashi nan kullum sai dad'a hab'aka yake mu an barmu da yi masa bauta, ko in ce n, tun da Sulaiman cikin su d'aya ne,
bazan yafe duk abin da akayi min ba kullum da burin d'aukar fansa nake kwana nake tashi,
sai dukiyar mahaifina yadawo karkashin iko na,
kada kiyi yunkurin komai ki b'ata min shiri, saura kiris lokaci ya yi,
shi zai tashi ya fita yabar gidan nan ba mu ba, Alhaji Abubakar sai ka nimi matsugunin da zaka zauna kai da iyalinka ka rasa.......!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*Bismillahirrahmanurrahim*
🅿️9
🙋Nace ba dan Allah wad'an da suka turamin kud'i suna son littafin HAMDAH kwanaki uku da suka wuce kuyi hakuri ku sake min magana da wanda suka ce min suna son KARSASHI please ku sake yi min magana wayata ce ta tsundume a ruwa sai yau Allah ya yi dawowa ta online.
wad'an da sukayi min magana sukaji ban amsa su ba duk kuma kuyi hakuri sharrin na'ura ce.
Dad yana gama fad'in haka ya fice a gidan.
a can wajen babban get ya iske Zaraddin yana tafiya,
yasha gabansa a mota ya bud'e masa gefen mai zaman banza ya ce
"Shigo."
fuska Zaraddin ya had'e ya ce
"Kaje kawai abinka gara naje club na kare rayuwa ta a can, nayi ta yiwa mata ciki tun da haka kuka zab'a, banyi abu ba ace nayi."
"Shigo dalla sha-sha-shan banza wanda baisan meye duniya take ciki."
Zaraddin ya shiga motar yana tura baki.
Dad ya ja motor yana fad'in
"D'an iskan yaro kawai, na hanaka shaye-shayen nan ashe bakaji ba,
ka cigaba da sha ne ko,
me kaje ka shawo yau zakayi gigin aikata haka;
meye a jikin 'yar wannan yarinya da zaka nime ta,
kyalkyalin kalar halittar tane ya d'ibe ka ko me?
dan uwarka da kake cewa zakaje club idan kaje kayi wa yaran mutane ciki agidan freezin zaka kare rayuwarka,
bakasan komai ba na dad'e ina tason ganin kunfi haka cikin walwala ku fantama kuyi abun da kukaga dama,
dan haka ka nutsu cip ka dawo da hankalin ka guri guda, ni nasan me nake ciki nan da lokaci kalilan mune zamu rika bada umurni da oda kowa yabi;
yanzu zan kaika gidan abokina ka d'anyi kwana biyu daga nan zan dawo da kai muje ka bashi hakuri,
kada ka sake ka b'ata min shiri,
kuma na fad'a maka ka daina shaye-shayen nan dan kai naga alama zaka iya rusa min shire na ma,
gashi kaine babba amma Shamsuddin yafika hankali da tunani da nutsuwa,
bansan me yake yawo cikin kwakwalwar ka ba."
ya karashe maganar da hararar sa.
shiko Zaraddin sai kumbura yake yana kunkuni ciki-ciki.
a haka dai suka d'auki hanya zuwa gidan abokin Dad kamar yadda ya fad'a.
A b'angaren Aunty
tun bayan faruwar lamarin ta dad'a sakawa Feeryal tsaro sosai, ta dad'a hanata fita nan da can
dama ba fitar take yi ba.
koda zuwa gun Miemie ce sai dai ita Miemie tazo suyi wasa, tun da yanzu hutu suke.
Aunty ce tafe zuwa side d'in Daddy, tana isowa bakin kofar parlour'n sa, Umma Karima na fitowa daga kofar baya dake side d'inta zuwa na Daddy.
hanya ce da dukkanin matansa suke da shi sakanin side d'in su zuwa nashi side d'in, ba sai sun zaga ta ainihin kofar sashin nasa ba, zasubi ta kofofin dake sakanin su kai tsaye.
yau Umma Karima ce da Daddy, ganin Aunty na kokarin shigewa da sauri ta ce
"Ke-ke-ke da kata nan ina zakije a gurin, me zakije d'auka?
kina dai sane yau ni ce da gidan."
kallon shekeke Aunty tabita da shi, abin dariya wai yau itace da gidan ma gaba d'aya.
ta karaso ta tare kofa tana aikawa Aunty banzan kallo
"Baki isa ki shiga gurin Alhaji ba, jarabibbiya sai dai yau ki koma jarabar taki ta kashe ki,
b'arauniya mai satar kwana."
murmushi Aunty ta yi sannan ta ce
"Ke baki kai wacce zan saci kwanar ki ba, bazan b'oye dan ina bukatar miji na ba,
a gaban ki a gaban wacce ta fiki zan yi duk abin da zanyi da shi,
ko ni ce da kwanar ko ba ni bace,
dan babu wacce ta isa ta dakatar dani akan mijina."
"Wlh karya kike baki isa ba, da kuwa sai na nuna miki ni cikakkiyar 'yar barike ce,
munafuka mai raba zumunta kika raba d'a da gidan yayan ubansa, an fad'a miki marin da kika min yatashi a banza ne,
bazan wahalar da hannuna wajen ramawa ba, sai kinyi dana sani mara adadi."
Kai Aunty ta girgiza bata son biye mata amma duk yadda takai ga kawaicin ta sai Umma Karima ta tunzurata ta sata musayar yawu da ita.
kallon marar tunani tayi mata kana ta ce
"Basai kin b'ata yawun bakin ki wajen fad'a min ke 'yar bariki ba ce,
na sani tun da dad'e wa;
sai dai naki barikin mai kunshe da jahilci ne, idan ba dun aure kaddara bace ai Alhaji Abubakar ba sa'an auren ki bane."
mene ne ba'a sani ba, sadakar shinkafarki da ya yi tuski ya tsaya yiwa almajirai, tun da kika kyalla kika ganshi, sai da kika san yadda kika shiga kika fita wajen samun sa,
ke bakikai wacce zan jera kafad'a da ke ba,
dan ko 'yan aikin gidan mu sun fiki sau dubu dan dukkanin su masu ilimi ne ba jahilai ba,
bama d'aukar jahili yazo ya hidimtawa gidan mu,
kingo ko idan badun kaddara ba ke baki kai wacce zan had'a miji da ke ba,
ko ma mene kije kiyi ni da Allah na dogara,
bani hannya na wuce."
tasaka hannu ta ture ta gefe tasa kai tawuce,
ta barta nan tsaye tana ta haushi.
tashiga taje ta aiwatar da abin da ya kaita, ta fito ta koma side d'in ta.
Satin Zaraddin guda da barin gidan, Dad ya dawo da shi ya tasa keyarsa gaba har parlour'n Daddy.
kansa a kasa kamar mutumin kirki.
suka karasa cikin parlour'n bakin Dad d'auke da sallama.
Daddy dake zaune yana kallon labarai a TV ya amsa sallamar, yana duban su.
"Barka da hutawa Yaya, ayi hakuri bamu nimi izini ba muka shigo kai tsaye."
Dad ya fad'a yana zama kan kujerar da ke fuskantar Daddy.
Zaraddin kuma ya zauna tad'an can gefe a kasan carpet, ya nad'e kafa kansa a kasa har lokacin da alama hud'ubar da baban nasa ya yi masa kafin su shigo ya shige sa.
Dad
ya d'an zamo bakin kujerar yana cigaba da fad'in
"An tashi lafiya Yaya ya iyalin?."
Daddy ya gyara zaman sa da kyau da murmushi d'auke akan fuskarsa yake duban d'an uwan nasa, kana ya ce
"Kazama bako kenan da sai anyi ma iso kafin ka shigo, kai da gidan ka Tukur, ai in izinin shiga ne ma sai dai wa wannan korarren dan sati guda ke nan dana fiddashi cikin gidan nan."
Daddy ya karashe maganar yana nuna Zaraddin, yana cigaba da murmushin.
Zaraddin yakuma yin kasa da kai tare da marairaicewa.
"Ina kwana Daddy."
ya fad'a yana d'an duban Daddy da fuskar nadama.
"Rike gaisuwar ka ai bamu shirya ba tukun."
Dad ya aikawa Zaraddin mugun kallo yana jan kwafa tare da cije baki ya girgiza kai, alamun zai gamu da shi.
sannan ya ce
"Ai wlh Yaya badun yazo da magiya gwuiwowinsa a kasa ba, da babu abun da zaisa na saurare shi har na kad'o keyar sa gurin ka ba,
idan ka yafe masa to nima na yafe masa,
idan kuma baka yafe masa to nima na rantse bazan tab'a yafe masa ba;
ya tashi ya tafi ya yi nesa da rayuwar mu!."
Zaraddin ya mike da sauri yazuba gwuiwowinsa a kasa ya had'e hannayen sa cikin karamar murya ya marairaice sosai yana fad'in
"Dan Allah dan girman Allah Daddy Dad kuyi hakuri wlh bazan kara ba, duk abin da kuka haneni bazan kara aikata shi ba, ku yafe min;
idan kuka kore ni ina zan je, bani da wanda suka fiku."
ya fashe da kuka wei-wei kunsan d'an kwaya da ladabin kule.
Daddy mai tausayi nan da nan tausayin sa ya cika shi da sauri ya ce
"Maso nan Zaraddin zo kusa dani."
ya rarrafo yazo gabansa.
Daddy ya sa hannu yana bubbuga kafad'ar sa.
"Ya isa haka Zaraddin, banyi maka hukunci dan bana son ka ba, sai ma dan kaunar da nake maka,
nafi kowa son naga kun gyaru kun zama mutanen kirki, da za'a rika kwatance da ku,
ba kaiba duk wanda ya aikata ba dai-dai ba acikin 'yan'uwan ka irin hukuncin da zan musu ke nan,
yarinyar nan amana ce a gare mu, nauyi ne a kanmu mutsare mata mutuncinta, sai inda karfin mu ya kare idan muka ga wani na shirin ci mata zarafi,
taya kuma za'ayi ace mu da hakkin hakan ke rataye a wuyan mu,
daga tsatson mu ne za'a sami mai son keta mata haddi,
kanwarku ce itama kada ku rika mata kallon wata daban, ku zamo mai bata kariya dan Allah;
wannan gargad'i ne kawai Zaraddin bazan iya nesanta ka gare mu ba wajibin mu ne baka tarbiyya dai-dai gwargwado,
Zaraddin na gamaka da Allah ka natsu ka daina biyewa abokan banza babu inda zasu kaika sai dai su kaika su baro,
nan da lokaci kad'an nake son d'agaku a kasarnan kuje ku karo karatu, kai da Ajeemal da Shamsuddin da Faisal, kai kad'ai nake da shakku a kanka,
dan Allah ka sawa rayuwar ka natsuwa."
Fad'a sosai Daddy ya yi masa Dad na taya shi.
daga bisani Dad yashiga bawa Daddy hakuri yakuma yi masa alkawarin in Allah ya yarda hakan bazata sake faruwa ba.
Daddy ya basu danar su tashi su tafi shi komai ya wuce a gurinsa.
Dad ya mike ya na fad'in
"Allah ya kara girma Yaya bango majinginar al'umma."
sannan ya dubi Zaraddin ya ce
"Sai ka tashi muje ai sha-sha-shan banza mara tunani."
Daddy ya katse shi
"Kul Tukur kar naji kayi masa wani abin."
kai Dad ya girgiza alamun ya d'auki umurnin yayan nasa.
kana ya kad'a keyar Zaraddin suka fita a daga side d'in Daddy, suka nufi side d'in Dad.
Suna shiga parlour da sauri Mom ta mike ta ruko Zaraddin tana dudduba jikin sa.
"Ya naga ka wani dishe, shi da ya ce min gidan masu kud'i ya kaika;
kana samin abinci mai kyau ma kuwa?
a wani irin makwanci kake kwanciya? badai da ruwan rijiya kake wanka ba dai? dubi fatarka duk kawani dishe haka."
Dad ya ce
"Daga zuwa kin tare shi da tambayoyi haka, ki barshi ya zauna mana, karya zan miki gashi ki tambaye shi wani irin gida na kaishi,
ko da bai kai nan ba amma ai gidan mai kud'i ne,
gidan aboki na Alhaji Uba na kaishi."
Baki Mom ta tab'e
"To ai ni banga wani alamun yaje gidan hutu ajikin sa ba, wlh aka sake gwada wa 'ya'yana gadara a gidan nan dole kaje ka siya mana gida mu koma dan bazan juri wulakanci ba,
wuce ka je kayi wanka ka huta,
zansa Ladi ta kai ma abinci yanzu."
Zaraddin ya juya yana wani tafiyar fankama, Dad ya ce
"Ka dai ji gargad'in dana maka idan ka sake
aka kuma samin matsala wlh sai na sab'a maka, bazaku rushe min mafarki na ba,
madadin ki gargad'e shi sabo da ya kiyaye gaba, kin tsaya wasu kananun magana,
gaba ya kamata ki hango da irin rayuwar daulan da zamu kasance ciki."
"Ai dai da b'acin rai bai aikata abu ba ayi masa sharri ace ya aikata."
"Inji wa kinfi kowa sanin halin d'anki yaushe ne naje na ye belunsu a hannun police, sunyi wa yarinya fyad'e."
"Eh ansan wancan amma ai na wannan aljana Feeryal d'in,
ai ba gaskiya ba ne, kage ne kawai."
"Ke dai kiyi shiru kawai ya dai kiyaye dan wlh yasa burina ya rushe ni da kaina zan damkashi hannun 'yan sanda."
Mita Mom ta ciga da yi ta d'au waya ta kira Ladi mai aikinta tana babban kicin su da duk ma'aikatan gidan, suna kokarin d'aura abincin rana.
Ladi na d'agawa Mom ta ce
Ki had'awa Zaraddin abinci mai rai da lafiya ki kai masa side d'in su."
"To hajiya."
cewar Ladi.
ko da Zaraddin ya shigo side d'in su, har ya d'aura hannu kan handle zai bud'e kofar bedroom d'insa,
sai kuma ya tsaya, yakai minti 10 a tsaye yana tunanin anya macijinnan ya fita kuwa, baya cikin d'akin nan?.
A hankali ya tura kofar ya shiga, ta bayan kofar ya sa hanu ya d'au wata doguwar karfe, kana a hankali yashiga takawa cikin d'aki, yana rarraba ido cikin d'akin.
lungu da sako ya dudduba baiga komai ba.
kasancewar ba wani tarkace bane cikin d'akin. daga
makeken bed and bedside sai wardrobe manne a bango guda TV fridge sai doguwar kujera.
har cikin bathroom ya duba babu komai.
ya dawo cikin d'akin gaban gado ya tsaya, a hankali ya kai hannu ya d'auki pant d'in Feeryal, daya gani tsakiyar gadon,
wan daya tub'e mata ranar.
da alama dai tun bayan korar sa da akayi babu wanda ya shigo d'akin,
ko ma'aikata masu gyaran side d'in su ma basu shigo bedroom d'in sa ba.
Ya d'ago pant d'in yana kare masa kallo, sai kuma da sauri ya mannashi a fuskarsa yana wani irin shinshinarsa, yana wani lullumshe ido.
Ajeemal da shigowar sa kenan zai wuce bedroom d'in sa, ya hango kofar Zaraddin a bud'e, ya karaso bakin kofar.
can ya hangosa tsaye da abin da yake yi.
Da mamaki Ajeemal ke kallon sa, har ya karaso cikin d'akin Zaraddin bai san ya shigo ba, ya shagala da abun da yake yi.
"Zaraddin."
Ajeemal yakira sunan sa.
da sauri ya ware idanunsa tare da cire pant d'in a fuskarsa ya yi baya da hanun sa ya b'oye shi ta bayan sa.
"Kace baka cire mata pant ba, ta ya akayi wannan yazo nan?."
Ajeemal ya yi maganar yana kamo hannunsa daya b'oye ta bayansa.
da karfi Zaraddin ya fisge hannusa yana hararar sa
"Sai kuma aka ce maka nata ne wannan d'in, to sayowa nayi."
kai Ajeemal ya girgiza sannan ya ce
"Sabo da ka koma mace shiyasa ka siyo pant dan ka rika sakawa ba, Zaraddin kabi a sannu dai."
"Anki a bi a sannun idan nabi da gudun ma me ya dame ka."
kafad'a Ajeemal ya d'aga
"Babu ruwa na life d'in ka ne, amma abun bakin cikin dole a danganta ka da mu."
"To ku san yadda zakuyi ku goge hakan mana."
"Rabu dashi Ajeemal zo mu tafi ga Faisal can a mota mu yake jira, badai ka mance 9:30 zamu shiga class ba."
cewar Shamsuddin yana karasowa bakin kofar bedroom d'in.
yaci gaba da fad'in
"Duk wanda ya yi na gari ai don kansa duniya ce ai gashi ga ita, ta ishe sa riga da wando,
ba sai ya siyo pant d'in sawa ba, zo mu tafi kar muyi latti."
Shamsuddin ya juya Ajeemal yabi bayansa.
Zaraddin yabi bayansu da harara tare da jan tsaki
"Mttss munafukan banza kawai."
Ya fito parlour ya samo laida ya kulle pant d'in ciki yaje ya jefa sa cikin dosbin.
kana ya koma bedroom d'in sa ya wuce bathroom domin yin wanka.
Tun da Aunty ta sami labarin dawowar Zaraddin takuma tsananta tsaro wa Feeryal.
ko da aka gama hutu suka koma makaranta, duk safiyar Allah idan lokacin tafiya makaranta ya yi ita ke fita ta kaita mota da kanta, sai ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta koma,
lokacin dawowar su nayi kuwa zata fito ta tsaya har sai taga shigowar su ta kama d'iyarta su shige ciki.
Wannan ke nan.
A can cikin fadar sarkin aljanu.
sarki aljani Matip ne hakimce a kan karagarsa,
ya yin da fadawarsa ke zagaye da shi.
wasu kyawawan yara mata ne guda biyu ke zaune a gefe da gefen sa,
kan wasu kujeru masu tsananin walkiya.
waziri Kutup ya d'ago da dubansa daga kan wani makeken madubi dake ta juyayi kamar ruwa.
ya dubi sarki Matip yana fad'in
"Ya shugaba na, ga dukkan alamu tana cikin koshin lafiya, da kulawar daya dace, babu wani abin cutarwar da yake dumfarota a yanzu."
kai sarki aljani Matip ya jijjiga sannan ya ce
"Akwai kalubale a gaba mai tarin yawa cikin rayuwar ta lokaci baiyi ba tukun,
amma sai dai bayan mu akwai wani wanda zai bayyana zata kuma sami kariyar daya dace feye da wanda muke bata."
kasa waziri Kutub ya yi da kansa ya ce
"Ya shugaba na shin akwai wani wanda zai bayyana ya bata kariyar kwatankwacin irin wanda muke bata."
sarki aljani Matip ya jijjiga kai
"Kwaraikuwa akwai shi zai yayyana."
"A jinsinmu ko a jinsin bil'adama?."
yakuma jefo masa tambayar.
sarki aljani Matip ya gyara zaman sa sannan ya ce
"A jinsin bil'adama zai bayyana, shi babban kariya ne a gare ta."
Wasiri Kutub ya jinjina kai yana mai makikin girman isa irin na wannan bil'adama da har zai fisu bata kariya wanda su duk motsinta tamkar a kan idanunsu yake.
ya ce
"Wani hukunci ne za'ayi wa yaron da ya nimi cutar da ita."
sarki aljani Matip ya ce
"Sa'ar sa guda da ya yi amfani da duhu ba a haske ba, da yayi kokarin cimma burinsa a haske ne da mun makantar da shi, a barshi a iya tsoratarwar da akayi masa, gaba idan bai kiyaye ba zamu waiwaye sa,
a kirawo Tarmuzu yanzun nan."
Nan take waziri Kutub ya murza wata kambu, cikin dakika 1 aljani Tarmuzu ya bayyana, a gabansu ya zube bisa gwuiwowinsa yana fad'in
"Na amsa kira ya shugaba na."
sarki aljani Matip ya dube sa tare da cewa
"Daga yau aikin ku ya kare Chuchu da Chulu ne zasu cigaba daga inda kuka tsaya."
rusunar da kai ya yi yana cewa
"Mun d'auki tabbaci ya shugaba."
ya zaro wata kambun dake d'aure a hannunsa ya aje shi gaban shugaban nasu.
sannan ya mike ya koma cikin fadawan nan ya zauna.
sarki Matip ya dubi yara mata biyun nan dake gefen sa sannan ya ce
"Chuchu Chulu, kuje ku bayyana gare ta."
ai ko nan take suka b'ace.
Yau asabar babu makaranta, Feeryal tasha baccinta har wajen karfe goma kafin ta farka.
ta mike zaune tana mussuke idanunta tare da yin hamma.
fuska ta kwab'e zuwa yanzu tana jin yunwa.
cikin tsiririyar muryarta mai kama da na shagwab'a ta ce
"Ammie yunwa."
jin bataji motsin Ammien nata cikin d'akin ba, sai ta kuma ware idanunta sosai tana kokarin zamowa bakin gado.
Da d'an fuskar mamaki take kallon yara guda biyu tsaye cikin d'akin girmansu dai-dai da ita tsawonsu ma d'aya.
suma kuma ita suke kallo suna yi mata murmushi.
itama murmushin tayi musu, tana fad'in
"Laa ku suwaye ne ya sunan ku,
kunzo da Ammie'n ku ne, ina take tana gurin Ammie na, zaku kwana a gidan mu?."
ta joro musu tambayar tana washe baki.
Baki suka had'a wajen fad'in
"Mu kawayen ki ne, sunan mu Chuchu da Chulu,
bamuzo da Ammie'n mu ba mu kad'ai mukazo, idan kina so sai mu kwana a gidan ku idan kuma kince mu tafi zamu tafi, zakiyi wasa da mu?."
kai ta gyad'a tana cewa
"Har da Miemie ma zamuyi wasan, ku jirani Ammie na tayi min wanka nayi breakfast, zakuga Miemie ma tazo.
"Ke Feeryal da wa kike magana ko mafarki kike?."
cewar Aunty data sako kanta cikin d'akin, hab'a ta rike tana kallon Feeryal data rike kugu tana magana tana lankwasa gefe da gefe irin yaro yana jin dad'in abin da yake ko ya gani na burgewa.
"Ke Feeryal wai dama ba mafarki kike ba, da wa kika tsaya kina ta zuba uban zance haka, ko mirror kike wa magana?
ni da nake ta jiranki ki tashi kiyi wanka, taho maza muje kiyi wanka ki samu kiyi breakfast."
ta janyo hannunta suka nufi bayi.
Kafa tashiga bubbugawa tana fad'in
"Kar ku tafi ku jira ni bari Ammie na ta min wanka,
Ammie kiyi min da sauri zamuyi wasa ne."
Cak Aunty taja ta tsaya tare da waigowa tana bin cikin d'akin da kallo, bayan kayan dake cikin sa babu wani halitta mai numfashi ciki sai ita da Feeryal d'in.
"Ammie kiyi sauri ki min kinga sunzo da kayan wasa da yawa."
tayi maganar tana jijjiga hannun Aunty.
cikin yanayin soma shiga fargaba Aunty ta ce
"Feeryal babu kowa fa a nan sai ni da ke, a ina kika ga wasu har da kayan wasan?."
Baki ta cuno tana jan hannun Aunty ba tare da ta bata amsar tambayar ta ba, sai cewar da tayi.
"Ammie yi sauri kuma yunwa nake ji."
Aunty bata kuma kawo komai a ranta ba, sai tunanin shiririta ne kawai irin na yaro.
Tana gama mata wanka ita tariga Aunty fita a bayin, wanda kafin yau idan tayi mata wanka haka zata langwab'e sai ta d'auko ta ta fito da ita,
ta share mata jiki ta shafa mata mai takuma samata kaya.
dube-dube tashiga yi tana niman ta in da sabbin kawayen nata suke amma bata gansu cikin d'akin ba.
tana shirin fita parlour taje ta duba su ko suna can, Aunty ta fito ta ce
tazo ta sa mata kaya.
Aunty na gama shiryata tayi parlour da sauri, ganin basa nan ma sai ta b'ata fuska tare da cuno d'an karamin bakin ta gaba.
Aunty ta karaso in da take tana fad'in
"Zo muje dinning kiyi breakfast."
"Ammie sun tafi gidan su ne yau she zasu kuma zuwa?."
tayi maganar tana d'ago kanta sama tana duban Aunty.
"Wai su waye ne kam Feeryal?
babu fa wanda suka zo gidan nan, Miemie ma bata zo ba tukun, a ta ina kika gansu mebi mafarki kikayi, taho muje kici abinci."
ta janyo ta suka haura dinning.
Tana cikin yin breakfast d'in Miemie ta shigo da babyn wasan ta,
tana gamawa kuwa sukayi d'akin Feeryal d'in dan suyi wasa a can.
wannan d'akin sunan nata ne kawai amma bata kwana ciki da rana ne kad'ai yake da amfani da dare kuma guduwa take gun Ammie'n ta a can bedroom d'in Aunty take kwana.
Suna shiga bedroom d'in Feeryal ta waro ido tana fad'in
"Laaa dama nan kuka zo, shine baku jirani a bedroom d'in Ammie na nayi wanka ba,
ga Miemie tazo muyi wasa."
dariya duk sukayi mata.
d'aya daga cikin su ta ce
"Ai bazamu tafi ba tun da bamu sallame ki ba,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 20