Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
matan kuwa nan suke zuwa su same sa, sunyi fad'a har sun gaji kan suma sai dai yarika biyo su, ya ce dasu duk wacce bazata iya zuwa ba ta zauna abinta baiyiwa ko wa dole ba. A kofar parlour'n sa suka had'u da Umma Karima tana kokarin shigowa. kallon banza tabi Aunty da shi tare da yamusa fuska cikin gatse ta ce "Uhum iyayen jaraba har ya gudo ya dawo ma ba'a kyalesa ba, me yakawo ki nan a wannan lokacin, bakida hurumin zuwa nan yanzu, sai ayi gaggawar fita a bamu guri, in ba satar kwanan za ayi ba da ma an saba, kada kuma ki sake ki ce zaki rika shigo mana da aljanar nan nan, ya'yan da ya haifa sune kad'ai ke da hurumin shigowa side d'insa, ba agolar aljanar ruwa mayya ba." Murmushi Aunty tayi kana ta ce "Ni da mijina har sai an iyakanta min san da zan zo inda yake? a duk san da na bukaci zuwa in da yake zanzo; ko da kuwa a d'akin barcin ki yake, har a yanzu yana cikin lokaci na daga nan har zuwa fad'uwar rana, ba ke ba ko wacce zai koma gurin ta yau bata da ikon dakatar da ni, zuwa in da mijina yake." Aunty na kaiwa nan ta rab'a gefenta tayi gaba abinta, bata kuma bi ta kanta ba. dan bata fiye biye musu ba idan suna haukansu, manna musu hauka take tabarsu suyita haushin su. Umma Karima tabi bayan ta da harara da basket d'in da ke hannunta, tasan abinci takawo masa yaci. hakan ma bakaramin kona su yake ba, dan ba kasafai yake cin abincin su ba. a kufele ta karasa ciki, tun kan ta karasa cikin bedroom d'in sa tasoma mita "Alhaji abinda kake mana fa baka kyauta mana, mu masu ya'ya mu ne abun wulakantawar ka, mu mukasan zafinka mu yakamata ka daraja mu." hannu yad'aga mata kana ya ce "Yanzu ni kin daraja ni da kika fad'a min d'aki kai tsaye babu ko sallama bare gaisu, babu tausasa lafazi, me nayi muku na rashin kyautatawa?." fuska ta yamusa tana cika tana basewa ta tsaya a tsaye a kansa tana fad'in "Shekara nawa baka cin abincin mu tun da ka auro waccan matar ka ya ye cin abincin mu, a nan duk ran kwanan ta side d'inta kake tarewa, kana gurin mu ma tana biyo ka da abinci." Dakatar da ita yakuma yi ta hanyar kuma d'aga mata hanu ya ce "Ya isa, ai na fad'a muku duk sanda kuka shirya yin girki da hannunku zan ci." "Haba Alhaji me zai sa mu yin girki bayan ga masu aiki har rai nawa, babu kalar girkin da basu iya ba, Allah ya bamu hutu sai kuma mu kasa hutawar, a ce duk wannan daular da muke ciki mukasa hutar da rayuwar mu sai mun bautatu, haba Alhaji ai kai yakamata ma ka ce mu huta, ma'aikata sucigaba da hidimta mana." Kai Daddy ya girgiza kana ya ce "Fad'imatu duk da kaancewar ta d'iyar masu kud'i; bata d'auki girman kai ta sawa ranta ba, da kanta take girki dan naci abinci cikin kwanciyar hankali, da sauran aikace-aikacen da ya kamata, dan haka bakuda bakin da zaku dakatar dani daga cin abincin ta, fad'i abin da yake tafe da ke, in kuma wannan ce ta kawo ki to ki koma sashin ki bana son damuwa." "Eh ai basai kayi mana gori ba, mu y'ay'an talakawan ita 'yar masu kud'i, a haka kuma muka fita ba, idan kud'i na iya yi maka komai taje ta sayi haihuwa tasakawa cikinta tayi nakuda da kanta ta haifa mana, bata soma bin 'ya'yan aljanu tana d'ibowa tana kawo mana su gida ba, kai kuma ka amince mata mu rayu da aljana cikin gida d'aya, daga nan duk ta shige jikin ya'yan mu." "Karima ya ishe ki haka fita kitafi sashin ki nace!." Umma Karima ta juya tana cigaba da mita tafice. tsaki Daddy yaja tare da cigaba da abun da yake cikin computer sa. Washegari da misalin karfe 6, su Hajiya ne zaune a parlour anata fita da kayan su zuwa mota. Mommy Umma Karima Hajiya Safiyya matar Alhaji Sulaiman wato Abbieh da kuma Hajiya Nafisat matar Alhaji Tukur Dad ke nan. da ya'yan su duk suna parlour'n. Hajiya Bishira tun a daren jiya ta iso kamar yadda Daddy ya fad'a. Mommy ta nisa ganin saura kad'an a gama fita da kayan su ta ce "To Hajiya in an tafi kuma sai yaushe? yauwa Hajiya dan Allah ki kumakiyiwa Alhaji magana kafin ki tafi, har yanzu fa baya cin abincin mu sai na wancan matar Fatima, ma'aikata masu tsafta muke da su amma ya ce wai bazaici abincin mu ba, sai dai yarika shiga hakkinmu ran girkin mu ma ita ke masa girki." Hajiya ta d'au gilashin ta ta saka tana fad'in "Kai sai dai fa kuyi hakuri dan abinshin gado ne dan asali ya samo, da ubansa ma baya cin abincin mai aiki, idan ina so yaci kuwa dole sai na girka masa da kaina, shima kuma Abubakar d'in a haka ya taso in har me aikice ta dafa to bazaici ba sai in ni na girka da kaina kafin yaci, bai iya cin abincin masu aiki bane tuntuni, in kun zab'i hutu kawai ku huta ku barta ta cigaba da bauta." Kai Hajiya Safiyya ta girgiza tana mai mamakin hali irin na Mommy da Umma Karima, Hajiya Nafisat kuwa cewa tayi "To me akayi ke nan kana da halin hutu baka hutan ba." Shigowar su Daddy ne yasa Umma Karima da ta budi baki zatai magana yin gum da bakinta. Daddy ya ce "Hajiya taso maza saura awa guda jirgin ku ya tashi." duk suka mike sukayi waje gurin mota. Hajiya na kokari shiga mota Aunty ta karaso gurin, tad'an rusuna tare da fad'in "Ina kwana Hajiya, Allah ya tsare hanya ga wannan ki samu na d'an tab'awa a jirgi." Hajiya ta karb'i laidar da take mika mata ta bud'e, wani roba ne mai d'an girma cikin laidar, ta bud'e robar lafiyayyen dambun naman kaza ce dayaji kayan had'i yana fidda wani irin sihirtaccen kamshi. Hajiya tahad'iye miyau mukutt, ba yabo ba fallasa ta wage baki tana fad'in "Lafiya lau amin amin to angode." "Cusa kai ba kwari niman gindin zama." Aunty tajiyo muryar Mommy dake tsaye a bayanta, bata kula ta ba, yi tayi kamar ma bata jita ba. tamasa in da Hajiya Safiyya take suka shiga gaisawa, Hajiya Nafisat kam 'yar fatin su Mommy ce ko kallo bata isheta ba. Motar su Hajiya na tashi ta juya ta wuce sashin ta... Yau ya kama kwanan Daddy hud'u a side in sa, yau ne zai koma gurin Aunty. lafiyayyun girki kala-kala ta shirya masa, bakajin komai sai tashin daddad'an kamshin turare na musamman ke tashi a side in. Aunty tagama shirya tarb'ar mijinta. Al'adar ta ne a duk san da zai dawo gurin ta, da daddre kafin yatafi side d'in ta sai tazo ta gyara masa sashinsa, dan basa gyarashi haka kowa zata gama zamanta ta tafi, tun da ya ce baya son me'aiki ta gyara masa sashinsa, suka gwammace su barshi haka, dan suma nasu sashin masu aiki ne suke gyara musu. duk da sashinta yake zuwa ya tare idan kwanan ta ya zago, amma sai ta taho ta gyara masa side d'in sa idan yana d'akinta. Tana saka da gyaran part d'in nasa da ya yi datti tamkar ba mata bane sukayi rayuwa a ciki, tsawon kwanaki hud'u. Feeryal na kwance a kan kujerar parlour'n Daddy Aunty na goge-gogen parlour'n. Mommy da Umma Karima suka shigo, kallon banza sukabi ta da shi. ko in da suke ma bata kalla ba in da sabo ta saba. idon Mommy ne ya sauka kan Feeryal da ke kwance kan kujera. ido ta gwalalo ta buga kirji tare da fad'in "Me zan gani haka anan aljana a parlou'n Alhaji!." Umma Karima ta shiga tafa hannu tana fad'in "Dama ashe baki mayar da ita ba sai da kikaga Hajiya ta tafi kika fito da ita, ai kuwa babu abinda zai hana Hajiya bataji labarin nan." "Duk matar da tayi gigin kiran Hajiya a kan maganar nan to a bakin aurenta!." Suka jiyo muryar Daddy dake fitowa daga bedroom d'in sa. "Kasan me kake fad'a kuwa Alhaji? akan wata banza aljana tsintacciyar cikin ruwa kake mana barazana da auren mu." Mommy tayi maganar tana nuna Feeryal. Umma Karima ta karb'i zancen da fad'in "Eh ba laifin ka bane shi dama aljani da makiri babu ta inda baya b'ullowa da salonsa, muje Hajiya Halima amma dole za'a yi zama dan bazamu yarda ba wlh." taja hannu Mommy suka fice sunata surfa bala'i Da sauri Aunty ta dubi Daddy ta ce "Daddy ya zaka ce haka." "Dukkanin su na san halin su idan ba haka nayi musu ba to ko shakka babu sai sun kira Hajiya da zancen, tanan ne kad'ai zai sa su hakura da kiran nata." kai Aunty ta jinjina. Daddy ya isa ya d'auki Feeryal dake ta baccin ta ya sakata a kafad'a, kana ya dubi Aunty ya ce "Muje ko." nan suka fita suka nufi part in Aunty'n. Waiwaye adon tafiya shin wane ne Alhaji Abubakar Fiya? kubiyo ni dan jin wane ne shi. Alhaji Shitu Fiya, mahaifi ga Alhaji Abubakar Fiya haifaffen d'an jahar plateau state ne awani gari da ake kira da Yelwan Shandam, Alhaji Shitu Fiya shahararren manomi ne wanda yake noma gonaki sama da hamsin a ciki da wajen Yelwan Shandam. yana da mata d'aya da ya'ya biyu Abubakar da kuma Sulaiman. yana da manya-manyan gonaki da girman su yakai girma, a kalla sama da guda hamsin, yana noma nau'ikan abubuwan da akafi amfani da su sosai a kasarmu. Auduga, Shinkafa, Masara, Gero, Dawa, Maiwa, Rid'i, Agushi Gyad'a, farar Wake, Waken soya, Doya, Dankali, na hausa da kuma na surawa Rogo. da dai sauran nau'o'in kayan masarufi nayau da kullum. ba a iya noman damina ya tsaya ba har da noman rani. idan amfaninsa tayi bayan ya cire zakka. zai aje wanda gida zai ci na tsawon shekara, kana ya cire wanda zai raba kyauta wa danginsa da y'an garinsa, san nan a kai sauran kasuwa. Cikin kankanin lokaci yazamo shahararren mai kud'in da babu kamarsa a yankin. a lokacin yakara iyali matansa suka zamo biyu, in da aka kuma samin karuwa bayan d'an wani lokaci amarya ta haifo d'anta na miji yaci suna Tukur. Dukiyar Alhaji Shitu Fiya sai dad'a hab'aka take tamkar kullum dare ninka masa ake. ya yi shaharar da kaf fad'in kasar nan ansan da zamansa a wannan gari na Yelwan Shandam. dan yanzu manya-manyan y'an kasuwa ne suke shigowa cikin garin Yelwa suke sayan kayansa suna fita dashi zuwa jahohin kasar nan. Amaryar Alhaji Shitu wato Luba batayi tsawon rayuwa ba, ta koma ga mahaliccin ta , tare da tsohon ciki na biyu a jikin ta, lokacin d'anta Tukur yana da shekaru uku. nan fa mutane masu fama da cutar gulma suka shiga kai kawo suna yad'a jita-jita, aka d'aura alhakin mutuwar ta kan kishiyarta, wai ita ta kasheta dan ta zauna cikin daula ita kad'ai, dama da kyar ta bari akayi auren. nan fa dangin Luba suka rungume zancen a kirjinsu suka yarda kan cewa ita ta kashe musu 'yar'uwar su, dan yanzu taga dukiyarsa ya ninka na da. suka d'auki karar tsana suka sakawa uwargidan Alhaji Shiru, suka masa sai dai a basu Tukar kar shima ta kashe shi. Alhaji Shitu Fiya bai yarda ya basu shi ba, ya ce yana da ransa da rufin asirin da Allah ya yi masa d'ansa bazai je agolanci wani gida ba. Dayaki basu shi sai suka shiga zuwa suna d'aukarsa yana wuni a gurin su. lokacin da yakara wayo kuma yashiga zuwa da kansa, duk san da ya je, haka zasu zaunar da shi suna tambayarsa, me matar ubansa take masa, duk abinda ta bashi idan bai yarda da shi ba kada ya ci dan ita ta kashe masa mahaifiyarsa. da ire-iren wad'annan abubuwan suka rika cusa masa ra'ayi suna dad'a masa hud'uba kan cewa, ita abokiyar gabansa ce dan ita ta kashe mamarsa kada ya yarda da ita, da kuma ya'yan ta. a lokacin Hanne wato uwargidan Alhaji Shitu takuma haihuwan 'ya mace taci suna Bishira. ai kuwa gari yakuma d'aukawa dama ta kasheta ne dan ta tara ya'ya tasami gado. Hannatu ta toshe kunnuwanta da jifan da magauta suke mata, baisa tayi wasi da rukon d'an mijinta ba, bata tab'a nuna masa bambanci sakanin sa da ya'yan da ta haifa ba. Ya'yan Alhaji Shitu Abubakar Sulaiman Tukur da kuma autarsu Bishira. sun fara datawa, in da babban d'ansa Abubakar yafi mai da hankalin kan sana'ar mahaifin nasu, a duk in da Alhaji Shitu ya ke to zakaga Abubakar. Wani aminin Alhaji Shitu ya janyo ra'ayin sa kan sana'ar man fetur da shi ya ke yi, nan yakuma fad'awa tsundum cikin harkar man fetur, bai kuma sake harkar noman sa ba, sai ma abin da ya karu. dan yanzu yasabunta sana'ar ta hanyar amfani da hanyoyin zamani. yanzu shi da kansa yake sarrafa duk abinda ya noma, akasin da da sai masaya sun shigo sun sayi kayansa, su su fita dashi suje su sarrafashi ta hanyoyi daban-daban. Alhaji Shitu Fiya ya kafa manyan kamfanoni a manyan jahohin mu, wan da yasashi dole barin garinsa yakoma Lagos da zama, in da babban kamfanin sa na sarrafa auduga ke gurin. gonakin da yake noman auduga shi ake kaisu kamfanin ake sarrafasu baya sayan auduga daga ko ina shi yake noma kayansa, yaku sarrafa shi ta hanyoyi daban-daban. har wasu ma suzo su siya. duk kayan amfanin da yake nomawa ko wanne sai da ya bud'e masa kamfani na musamman a ko wata jahar dake cikin fad'in kasar nan. Tuni Abubakar ya yi koyi ga mahaifinsa domin kuwa shima harkar noman yarike, baji ba gani, ba karamar karb'arsa noma tayi ba, har mutane suna cewa makoyi zaifi gwani. sosai ya maida hankali kan karatu kan fannin noma daya zab'a. akasin 'yan'uwansa da kowa ke karantar wasu abubuwan daban. lokacin da yakai munzalin aure takanas Alhaji Shitu yaje Yelwan Shandam yanimawa Abubakar auren 'yar d'an'uwan sa, wan da dama maganar had'in take aje dun da jimawa. A Yelwa aka gudanar da duk shagulgulan bikin kana aka d'auko amarya Halima aka kawo ta Lagos. Bayan wani lokaci kwasam Alhaji Shitu yakwanta jinya, daya fahimci rayuwar sa tazo karshe sai ya tarkaso kan takardun kadarorin sa, kana ya tara ya'yan sa da matarsa, ya ce Alhaji Abubakar ya sayi kamfanonin sa da gonakin sa, dan bazai siyarwa wani bare ba. da arziki a garin wani gara a garin ka. ya yi hakan ne badun komai ba sai dun yadad'a karfafawa Alhaji Abubakar gwuiwa kan harkokin noma daya gaje sa. Alhaji Shitu Fiya ya sa hannu cikin takardun mallakawa babban d'ansa Alhaji Abubakar Fiya gonaki da kuma kamfanoni, shikuma ya damka masa kud'ad'ensa. Bayan rasuwar Alhaji Shitu aka rabawa magada makudan kud'i da sauran kadarorin da ya bari, irinsu gidaje da filaye da kuma gidajen man fetur, ban da gonaki da kuma kamfanoni da yanzu suke a matsayin mallakin Alhaji Abubakar Fiya. Sosai Alhaji Abubakar yake gudanar da harkokin noman sa, Allah kuma ya sanya masa albarka, arziki yacigaba da hab'aka. Alhaji Abubakar ya kammala gina wani katafen gida unguwa guda, wan da girmamsa yakai girman wani karamin gari guda a cikin garin Lagos. manya-manyan part-part ne da akalla zasu kai guda goma shabiyar ne a gidan, kuma ko wani side yana d'auke da get da parking lot mai d'aukar motoci uku, had'e da garden na musamman. Katafaren katanga mai matukar girmar tsawo ke zagaye da gidan gaba d'aya, wan da saman ginin aka sanya wayoyin shokin domin tsaro aka zagaye garun gaba d'aya da shi. (A.A FIYA STREET) sunan da unguwar take amsa wa ke nan. Lokacin da zasu tare a gidan Alhaji Abubakar yakara aure ya auro Hajiya Karima, iyayen Umma Karima asalin 'yan Kano ne mazaunan Lagos. lokacin yana da 'ya'yan sa biyu maza da suka haifa da Hajiya Halima, Abdurrahim da Ajeemal. Sai a lokacin Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suma sukayi aure, bai bar su sun tare a gidajen da sukaci gadon sa ba, ya ce duk suzo su zauna a gidan da ya gina, suka d'auko mahaifiyarsu suka koma da ita sabon gida, in da ko wannensu ke zaune da matarsa a side guda guda. Shekara biyar da dawowan su sabon gida Alhaji Abubakar yahad'u da Fatima a gurin taron bud'e kamfanin mahaifinta a birnin tarayya Abuja. mahaifin Fatima abokin kasuwancin Alhaji Abubakar ne, yana siyan kayan kamfanin sa yakai nasa kamfanin. ya gayyaci Alhaji Abubakar ne shagalin bud'e sabon kamfanin sa, a nan yahad'u da y'arsa Fatima ya yaba da nutsuwa da kamalanta, ya nimi yardar mahaifinta atake kuwa ya aminta yakuma yi masa alkawarin aura masa ita. ba'a d'au lokaci ba akayi bikin. Fatima ta fuskanci kalubale da dama a tun ranar da ta sanya kafarta cikin wannan gida. do min kuwa Hajiya Halima da Hajiya Karima sun had'e kansu a tun ranar da suka sami labarin auren da mijin nasu zai kara. wan da a da sam basa zaman dad'i sakaninsu, tun da sukaji zaiyi aure suka had'e kansu. Cikin kankanin lokaci family'n ta soma hab'aka suka fara tara iyali. Hajiya Halima uwargidan Alhaji Abubakar ya'yan ta biyar bayan maza biyun data haifa kafin sudawo sabon gida, takuma haihuwar mata uku, Farida Sumayya Amira. Hajiya Karima ya'yan ta hud'u dukansu mata. Bilkisu Saddika Rahama Nabila. Hajiya Fatima kuwa har yanzu Allah baibata haihuwa ba, wan da hakan yazame mata abin gore a gurin abokan zamanta.. Alhaji Sulaiman shima 'ya'yan sa biyu da matarsa Hajiya Safiyya, Faisal da Miemie Sai kuma Alhaji Tutur y'ay'an sa uku da matarsa Hajiya Nafisat, Shamsuddin Zaraddin Sahla Family ya had'u cas da su🤗. Wannan shine takaitaccen labarin Family'n Alhaji Abubakar Fiya. Mutane na kudai ku biyo ni yanzu wasan yasoma🤸🤗 Mommyn Twins ce 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) *~Free page~* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *Bismillahirrahmanurrahim* 🅿️4 A b'angaren su Mommy tun da suka fita daga side in Daddy suka koma part in Mommy. suke kitsa ta yadda zasuji da lamarin, Umma Karima ta gyara zama ta ce "Hajiya Halima ga wani shawara, muje mu d'auki yarinyar nan mu nimi ruwa nan kusa ko na kwalbati ne mujefa ta ciki, ta koma gurin danginta, kowa ma ya huta, idan fa muka zuba ido muka barta daga karshe mu zata zame mana karfen kafa, tazo ta shafe mana ya'ya ko jinya kad'ai tabarmu da shi ai ta cutar da mu, Fatima bata da asara tun da ba d'a take da shi a gidan nan ba, sai dai tayi farin ciki da hakan, ina tunanin ma wani makircin take son kitsa mana, idan muka zuba ido kuwa mu zata kaimu ta baro mu, kinga ta dad'a mallake Alhaji gaba d'aya ta in da dolen mu mubar gidan nan, bakiji yafara fad'a da bakinsa tun yau ba." Mommy ta jijina kai tare da fad'in "Kwarai kuwa akwai abin da Fatima take son kitsawa wata kila bokanta ne yabata wani sa'ar, dole aljanar nan ta bar gidan nan, to amma yanzu ta ya zamuyi mu d'auke ta daga gidan nan, kinsan fa wannan Fatima mai taurin kan ba bari zatayi ba." "Ai dama ko ta karfin tsiya sai ta bar gidan nan, yanzu dai shammatar ta zamuyi, mu d'ake ta mu fita da ita, idan bamuyi sa'a ba sai mu nimi masu d'auko mana ita." Mommy ta girgiza kai cike da gamtsuwa da maganar Umma Karima. Kusan raba dare sukayi suna kitsa yadda zasuji da lamarin, Umma Karima ta koma side d'in ta, da shirin gobe zasu je su d'auke ta sufita da ita a gidan. Washegari da sassafe Mommy da Umma Karima suka fito da shirinsu na d'auko Feeryal, dan sun san yau talata iwar haka Daddy yana masallaci yana sauraran wa'azi. koda suka iso side d'in Aunty, ganin babu kowa cikin parlour kai tsaye bedroom d'in ta suka wuce. batare da ko d'ard'ar ba dan sun lashi takwabin sai tabar gidan ko ta alin kaka, ko kwana bazata kuma yi a gidan nan ba. Feeryal ce ita kad'ai a d'akin kwance a kan gado Aunty na cikin bathroom. da sauri suka isa bakin gadon cikin kasa da murya Mommy ta ce "Yi sauri mu d'auke ta kafin ta fito." Umma Karima ta mika hanu zata d'auketa, wani irin dirrr taji tamkar jan wutar lantarki, da karfi ta janye hannunta jiki na rawa. a d'an tsorace Mommy ta ce "Mene ne kuma?." batakai ga rufe baki ba sukaga ta wani irin waro ido tana jujjuya shi, ya yin da kwayar idanunta suka fara sauya kaloli daban-daban. kwan wutan cikin d'akin yashiga kawowa yana d'aukewa. tare da sauya kaloli daban-daban kamar yadda kwayar idanunta suke sauyawa, izuwa fari baki ja kore, da sauran kaloli daban-daban. tuni jikinsu yakama b'ari zufa yashiga keto musu, kowa ya shiga neman ceton rayuwar sa. da gudu sukayi bakin kofa tun kan su karaso kofa ta rufe. sai ga Mommy da Umma Karima suna kwalla kururuwan niman taimako. Aunty da ke gyaran cikim bathroom tafito da sauri, nan take wutan nan ya tsaya yadawo dai-dai. da mamaki ta tsaya kallon su Mommy dake cikin bedroom d'in ta sunata kururuwa. kallon kan gado tayi in da Feeryal ke kwance, da sauri taga idon Feeryal ya rufe sai kuma kofar d'akin ya bud'e. aiko da gudu su Mommy suka fice har suna ture juna. shiru Aunty tayi idanunta akan Feeryal sai dai har lokacin bata kuma motsi ba. kirjin ta ne yad'an buga tayi saurin fad'in "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un." acikin zuciyar ta, nan take taji zuciyarta ya yi wasai. numfashi ta sauke a fili ta furta "Lallai Hajiya Halima Hajiya Karima kun d'ebo da zafi amma muzuba mu gani." gaban gadon ta isa tana mai dad'a karfafa zuciyar ta, kan cewa Feeryal mutum ce ba abin da zuciyar ta ke bijiro mata da shi bane ayan da taga yarinyar yanzu. ta gyarawa Feeryal rufuwa kana ta juya ta koma ta cigaba da aikinta. A guje suka karaso parlour'n Mommy suna haki, ganin yadda suka shigo a hargitsi 'ya'yansu duk suka mike suna tambayar su me ke faruwa. "Kada wani a cikinku ya sake yaje side d'in Fatima!." cewar Mommy tana zama kan kujera gaba d'aya a firgice ta ke jikinta sai rawa yake.. Ajeemal ne yakaraso in da take yana fad'in "Mommy wai mene ne kam naga duk kun firgice?." "Ajeemal aljana wlh aljana ce ba mutum ba, mun shiga uku ankawo mana annoba cikin gida, wlh yarinyar can ba mutum ba ce aljana ce, Fatima takawo mana aljana gida, Hajiya Karima kinga abin da nagani kuwa?." "Ni kuwa naga sihiri aljananci maitanci ido da ido, ko shakka babu 'yannan ba mutum ba ce." Umma Karima da tsoro yakusa kasheta taja 'ya'yanta, suka koma side d'in ta, suka rufo kofa a kansu. A b'angaren Mommy kuwa har ta d'aga waya zata sanarwa Hajiya abin da ke faruwa, ta tuna da gargad'in Daddy ta aje wayar jiki a sanyaye tana ciza yatsa. A b'angaren Umma Karima ma taso kiran Hajiyar sai dai tana gudun abin da zaije ya dawo, dan bata kaunar abin da zai gutsire mata igiyar aurenta, takan bi ko wace hanya wajen dakile faruwar hakan. Bayan wata 5 Tun daga wancan ranar su Mommy basu kuma wani yunkuri a kan Feeryal ba, Aunty kuwa ta dage wajen kula da rainon d'iyarta yadda ya kamata. yarinya tana ta murjewa fatarta na dad'a kyau babu alamar maraicin uwa tare da ita, ta sami ruwan nono mai kyau da inganci. tayi wayo sosai tayi mul-mul da ita. har ta fara iya zama. sosai Aunty ke kula da ita Daddy na bata gudumawa yadda ya kamata. bata fita da ita ko ina ko side d'in Daddy zataje ba sosai take zuwa da itaba, takan barta wa Baba Rabi. kaf fad'in gidan kuwa dama babu inda take shiga side d'in Hajiya Safiyyah ce kad'ai take d'an lekawa. kowa na harkar gaban sa a gidan. Yanzu duk wanda yazo gurin ta bata bari yaga Feeryal, b'oyeta take a d'aki har sai ba'in sun tafi kafin tafito da ita. sabo da gujewa maganganun da ake akan ta, dan duk wanda ya ganta sai ya ce wuuu a'ina ta samo wannan mai kalar aljanu sam batayi kama da mutane ba. kyawun ta ya yi yawa. Aunty ce tsaye cikin kichin bayan ta gama shiryawa Daddy abincin sa dan yau zai dawo gurin ta. baba Rabi tana ta goge-gogen in da suka b'ata. Aunty ta dubi Baba Rabi tana fad'in "Bari naje nayi wanka kafin rikicacciyata ta tashi, idan kazarnan ta kara zafi a ciro ta kada ta kone." "To Hajiya." Baba Rabi ta amsa tana maida komai wajen zaman sa. Aunty ta fito daga kichin ta nufi bedroom d'inta, a hankali ta tura kofa cikin kasa da murya take fad'in "Allah yasa bata tashi ba har sai na gama komai." ta maida kofar a hankali ta rufe. idanunta a kan inda bed d'in Feeryal yake, tana fata Allah dai yasa bata tashin ba. da d'an mamaki take

Chapter 3 of 20