Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *Bismillahirrahmanurrahim* 🅿️1 Sassanyan iskar damina ne ke kad'awa ya yin da hadarin damina yayiwa sararin samaniya kawanya. yadda hadarin ya yi bak'i ana sammanin ikon Allah ta kasance, a'iya yin ruwa mai tarin yawa. katon teku da girman sa yawuci misali yacika ya tumbatsa. ruwa na gudu na k'ugi ga dukkan alamu tuni ruwa ya sauka daga can nesa da in da kogin yake. wani irin k'ara ne mai matukar firgitarwa tamkar saukar aradu, yakarad'e ilahirin sararin samaniya. ya yin da wasu irin halittu suka bayyana sukayiwa koginnan kawanya daga sama. daga can tsakiyar halittun manyan aljanun da sukayiwa kogin nan kawanya, wani irin haske ne tamkar gilmawar walkiya ya bayyana a tsakiyarsu, wani aljani mai d'auke da fuffuke yana rike da wani kwando, a hanunsa yasaki kwandon cikin tsakiyar ruwan yafad'o cikin katuwar tekun nan, ji kake banjammmm!. kwandon ya lume cikin tekun can karkashin tekon, mai matukar zurfi. dawasu abubuwan ban tsoro masu tsananin firgitarwa. Akan wani katon babban kejin karfe kwandon nan ya fad'i akai. nan da nan jaririyar da ke rufe cikin kwandon ta calla kara, dai-dai lokacin da kwandon ta bud'e tayi gefe jaririyar tafice ciki tafad'a kan kejin karfen nan, mai tabaibaya da wasu sarkokin karfe masu matukar karfi, wanda ko da injin yanka karafu ne sai ya yi da gaske kafin ya iya fasa sarkokin da ke tabaibaye da jikin kejin karfen, ba mutum ba ko aljani sai ya shirya. Kara jaririyar takuma callawa tana wutsil-wutsil da kafafunta, d'isss! haka hawayen idanunta ya d'iga akan kejin karfen nan. nan take kejin ya yi wani irin kara tare da tarwatsewa tamkar narkakkiyar dalma, wacce taji wutan ziga ta cikin karkashin kasa ta dawo tamkar roba, ba karfe mai tsananin karfi ba. Nan wani dattijon Aljani ya bayyana d'aure da saurkoki a jikinsa dai-dai lokacin da hawayenta na biyu yakuma d'iga ajikin sarkokin dake tabaibaye ajikinsa, sarkokin suka tarwatse gaba d'aya daga jikin dattijon aljanin nan. da sauri cikin azama yatari jaririyar datake kokarin dad'a lumewa cikin karkashen tekun, da gaba d'aya tekun ya yi wani irin hargitsewa da abubuwa masu matukar ban tsoro da firgitarwa. Wani irin tafarfasa koginnan yake tamkar ana tafasa narkakkiyar dalma. tuni sassanyar iskar dake kad'awa agun yakoma zazzafa. tashin hankali ba'a sa masa rana, a wannan lokacin ba iya yankin kogin ba duniya gaba d'aya ta girgiza. tuni halittun dake cikin tekun nan suka fara mutuwa, dabbobin dajin da suke yanki da kewayen gurin. wasu sun hallaka wasu kuma sun zube ƙasa suna birgimar mutuwa. 'yan bori matsafa bokaye malaman tsubbu mushirkai dake fad'in duniya gaba d'aya, wannan rana tazame musu bakar rana mafi tashin hankali a gare su. Wani irin zabura boka Mali ya yi lokacin da tukwanan tsafin sa suka fashe, suna fitta wani irin hayaki mai razanarwa had'e da sauti mai firgitarwa. tsabar tashin hankali a take agun yafad'i sumamme. hakan ne ta kasance ga ko wani mushirikin dake fad'in duniya. Da sauri dattijon aljani Matip ya gyara rikon jaririyar nan, kana yayi saurin durkusawa kasan tekun ya burma hanunsa cikin karkashin kasa da karfi irin na jinnu. nan take jikinsa yashiga kakkarwa ilahirin jikinsa yashiga fidda hayaki tamkar ana zuba masa garwashi na wuta. ya yi wani irin kara tare da zaro hanunsa, ya dunkule abunda ya ciro daga karkashin tekun na, da karfi cikin hannunsa. jikinsa nawani irin jijjiga, cikin karaji da amon sauti irin na jinnu yake fad'in "Ni kad'ai zaku cutar kada ku zalinci wad'anda basujiba basu gani ba, meye laifin bil'adama salihai da dabbobi? meye laifin aljanun da basu taka mukuba, har idan ina numfashi bazan tab'a bari kucutar da kowa ba, ku da kanku zaku zalunci kanku da bil'adaman da suke biye muku kuna b'arna a doron kasa, babu wanda zan kyale shi cikin ku!!." Ya matse tulun daya ciro daga karkashin kasan tekun wanda cikinsa sai tafasa yake yana fidda bakin hayaki har sai da ya fasashi da hannunsa, ya tarwatse wan da hakan yayi sananiyyar haifar da ambaliya nan take. Aljani Matip ya zube kasa jaririyar dake rike a d'aya hanunsa tasub'uce tafad'a karkashin kasan tekun. yana kallonta sai dai ina baya da ikon iya ceton ta dan ba karamin galabaita ya yi ba, duk jikinsa sunyi rad'a-rad'a ya kokkone da wutar tsafi dake ruruwa cikin tulun tsafin daya fasa. ido ya rumtse a wahalce yana kallon yanda wacce tasanadiyyarta yasami tsira da kub'uta daga zalincin da akayi masa tsowon shekaru masu yawa, yake d'aure a karkashin tekunnan. tazo ta ceceshi sai gashi yana ji yana gani zata halaka bashida ikon iya taimakon ta. muryoyin yaran biyu Aljani Matip yaji a kunnen sa suna fad'in "Shugaba yakub'uta shugaba ya kub'ata." dakyar ya iya furta "Ku ceceta kada ku bari ta halaka." Cikin kankanin lokaci tekunnan yafara dai-daita, dabbobi da halittun da suka suma kowa yadawo cikin hayyacinsa. duniya ta dai-daita daga firgici da ban tsoron da tashiga cikin kankanin lokaci, iska mai sanyin dad'i daya juye yakoma zafi yadawo sassanya mai dad'in gaske komai ya dai-daita tamkar komai bai faruba. Gudu motor take ga dukkan alamu wad'anda suke cikin motar sauri suke su isa gida, gudun kada ruwa ta tare su. wani kamilallen dattijo ne mai cikar haiba da cikar kamala, ke zaune a mazaunin direba, ya yin da gefen sa wata farar mata kyakkyawa wanda a kalla shekarunta zasu iya kaiwa 30. ke zaune cikin nutsuwa da kamala. Alhaji Abubakar Fiya kenan shahararren d'an kasuwa ne mai tarin dukiya, wanda ya ke d'aya daga cikin nagaba-gaba a masu kud'in kasarmu. shi da kansa yake jan motar, al'adar sa ne har idan da abar kaunarsa Hajiya Fatima zaifita. idan har ba tafiya mai nisa zasuyi ba to da kansa yake jansu a mota, baya bukatar direba a sakanin su. duk da kuwa yau tafiyar tasu mai nisa ne bai sashi sanyo diteba cikin tafiyar tasu ba. Yankin tekun Matip yamma da kogin hanyar tsako gajeren hanya, sakanin yankin da babbar tekunnan Matip tafiyar kimanin kilomita dubu ne. daga cikin dajin tekun Matip da hanyar mota da akayi ta saman kogin daya shigo har ta gefen gari yasami hanyar wucewa, inda akayi masa gada motoci suke wucewa idan hanya tabiyo dakai ta gurin. ko yanzu ma hanya ce tabiyo da Alhaji Abubakar Fiya da matarsa Hajiya Fatima. Ido Hajiya Fatima ta zubawa katuwar kogin nan dasuka zo daf dashi zasu wuce tasaman gada, yana wani irin haniniya, yana ƙugi yana wani irin tsalle tamkar zai haura saman gadar. daga can gefen gab'a, wani irin haske ne ya bayyana a gurin, daga bisani hasken ya disashe. da sauri ta dubi mai gidan nata tare da fad'in "Daddy kalli can ka gani." tayi masa nuni da hanu ta bakin gab'a. ido ya zubawa gurin sosai jaririya acikin kwando tanata zabga kuka ga ruwa yana d'an tafiya da ita, sai shure kafafu take. da sauri Hajiya Fatima ta ce "Daddy ruwa zai tafi da ita tsaya dan Allah mu taimaka mata kada ta mutu acikin ruwan nan, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me yakawo jariri cikin wannan ruwa kuma, kai duni ina zaki da mu." da sauri ya gyara parking a gefen titi har suna rigi-rigen fitowa. da gudu hajiya Fatima tayi bakin ruwan ganin kwandon yana cigaba da tafiya cikin ruwan tana fad'in "Daddy duba kaga ruwa zai tafi da shi." "Dakata Hajiya kibi a sannu wannan ruwa yana da had'ari bai kyale 'yan gari bama bare ba'i." suka jiyo muryar wani matsinci a bayan su. da sauri ta waigo tana fad'in "Dan Allah ku riketa kada ruwa ya tafi da ita." Alhaji Abubakar ya ce "Ki nutsu Fad'imatu kin ji ance ruwannan yana da had'ari kibari y'an gari su shiga, bawan Allah taimaka dan Allah kaciro sa yana bukatar taimako." yakarasa maganar yana duban matsincin nan. kai matsincin ya gyad'a kana ya aje abubuwan kamun kifinsa ya fad'a ruwan ya d'auko kwandon yafito. dasauri har suna rige-rige wajen karb'ar kwandon. dukkaninsu ido suka kafawa jaririyar dake cikin kwandon tana ta mutsu-mutsu da y'an kananun kuka, da mamaki dukkanin su suka kalli junansu har da matsincin nan, ganin halittar dake cikin kwandon. kyakkyawar jaririya wacce kyanta bazai tab'a misaltuwa ba kyawun da duk wanda yagani sai ya firgita shi. murya na rawa dasauri Hajiya Fatima ta dubi mai gidan nata ta ce "Mutum ce kuwa?." Alhaji Abubakar da shima yashi tantama sosai ya ce "Ni ma dai tunanin da nake ke nan, kawai mu maidata cikin ruwa tayi tafiyar ta, wata kila ma tana tare da iyayenta ne." yad'aga murya da karfi yana kallon cikin ruwan tare da cigaba da fad'in "Kuna dai gani ba da niyyar cutar da d'iyarku muka d'auko taba sai dan tunanin ko jinsin mune ita, gudun kada rayuwarta ya salwanta, yanzun nan zamu maida muku abunku ku gafarce mu." Alhaji Abubakar ya dubi matsincin nan ya ce "Taimaka ka maida musu da ita ka kuma basu hakuri bada niyya mukayi ba." Kai mutumin ya girgiza sannan ya ce "Alhaji bana tunanin aljana ce wannan dan kuwa da lokacin dana shiga d'auko ta danaga wasu alamu, a nan wurin ansha samin yara irin haka suna tafiya a kan ruwa sai dai yawanci ba a samin su da rai, wad'anda ake samu da ran basufi a kirgaba, nafi tunanin wannan mutum ce, Allah ne ya ketar da ita dai kawai, ko had'arin jirgi ko masu raba iyaye da y'ay'ansu." Alhaji Abubakar ya girgiza kai cike da tausayawa ya ce "Allah ya saka miki idan har makiya ne suka rabaki da mahaifanki, idan kuma rabuwar ta Allah ce sanadin had'ari Allah yajikan mahaifanki, idan kuma suna raye to Allah ya bayyana su cikin gaggawa." Tuni idanun Hajiya Fatima suka kawo kwalla, tamasa kusa da mai gidan nata. ta saka hannu cikin kwandon da jaririyar take ciki ta d'agota tana kare mata kallo kana ta rungumeta tana fad'in "Daddy ina kaunar yarinyar nan ina sonta mutafi da ita." a hankali Alhaji Abubakar yakai hanu cikin kwandon dake rike a hannunsa kasan inda aka d'aga jaririyar wata takarda ce ta bayyana mai d'auke da hoto da rubutu karkashin hoton jaririyar, (FEERYAL) sunan dake rubuce a karkashin hoton jaririyar kenan. a karkashin hoton kuwa wasu abun hanun gold ne masu kyau guda uku manya uku kanana da sarka da y'ankunne acikin gidan su. ajikin kyakkyawan kwantenar gold d'in nan d'auke da tambarin kasar Russia. Alhaji Abubakar ya d'ago hoton nan da kyakkyawan mazubin gwala-gwalai d'in nan yana fad'in "Da alama dai wannan badaga kasar nan take ba, watakila hanya ce ta biyo dasu tagefen yankin nan suka samu had'arin ita Allah ya ketar da ita, zai iya yiwuwa kuma y'ar kasar nan ce, tambarin wata kasa baya nufin y'ar kasar ce, tun da kayakin kasashe da dama suna shigowa kasarmu." Hajiya Fatima ta karb'a a hannunsa tana fad'in "Ikon Allah ta ina za'a fara cigiyar dangin ta bama y'ar kasa bace ashe, Allah sarki Daddy mutafi da ita kawai." Masincin nan yadube su tare da fad'in "Alhj ku tafi da ita Ubangiji ne ya turo ku ta fad'a a hannunku, idan kuka barta anan karshe asamu masu maidata cikin ruwan nan dan bakowa ne zai yarda ita d'in mutum bace, duk da tabbacin da ya nuna ba y'ar kasar nan ba ce, ba lallai ayarda da hakan ba, dan aljanu babu abin da bazasu iya yi ba, kowa da wannan fuskar zai rika kallon ta, idan har kunyi niyyar taimakon ta to kutafi da ita kawai." kai Alhaji Abubakar ya jinjina kana ya zaro kud'i masu yawa ya mika masa yana fad'in "Mun goge da taimako." mutumin ya karb'a yana yi masa godiya. nan suka nufi inda matarsu ya ke, Hajiya Fatima na rungume da jaririyar. ko da suka hau hanya Alhj Abubakar ya juyo yana duban Hajiya Fatima dake rungume da jaririyar tana ta aikin jijjigata. murmushi ya yi tare da fad'in "Raino ya yi miki kyau." itama murmushin tayi ta ce "Kamar nawa ko ina fatan hakan ta kasance amma da kamar wuya." da sauri ya ce "Gashi kuwa ta kasance kin sami kyauta daga Allah, ki gode masa ta hanyar rukonta tamkar mu muka haife ta." kai ta jinjina ta ce "Wlh ina jin sonta acikin zuciyata lokaci guda naji hakan ya kasance da ni, sai nake ji kamar y'ar danayi nakudan ta, Allah nagode maka." takarasa maganar da d'ago yarinyar ta sumbaci goshinta. Alhaji Abubakar ya maida idanunsa titi yana cigaba da fad'in "Kyakkyawar yarinya ban tab'a ganin kyau irin nata ba, ni dai har yanzu ina kokonto a kanta, idan ba jinsin mu bace Allah kagani mu taimako mukayi niyya, kutaho ku d'auki d'iyar ku cikin salama batare da cutar da mu ba, dan muma ba da niyyar cutarwa muka d'auke ta ba." Hajiya Fatima ta girgiza kai tana fad'in "Wlh har cikin raina ina jin cewa ita mutum ce irin mu, nafi gamsuwa da cewa watakila ba daga yankin kasarnan take ba, dan zubin halittar ta ya banbanta da namu, sai dai Allah babu abin da bazai iyaba, zai iya halitto ta cikin kasar mu takuma bambanta a cikin mu, dan ikonsa ya wuce yadda ake zato." kai ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman ta, dan ita d'in ta musamman ce a garesa.. Lagos (A'A FIYA STREET) A katafaren tamfatsetsen wani get Alhj Abubakar ya yi hon aka wangale masa get, ya kusa hancin motarsa ciki. da sauri wasu sojoji biyu masu sanye da kaki suka rufawa motar baya da gudu, daga bakin get zuwa sashin Hajiya Fatima dake side 5 zuwa parking lot d'in dake side d'in, tafiya ne daya kai na mintuna 10 a mota. a parking lot ya gyara parking, sojojin nan suka karaso da gudu d'aya ya tsaya a gefen Alhaji Abubakar d'aya a gefen Hajiya Fatima. suka bud'e musu kofa cikin hanzari suka kuma sara musu tare da kamewa. Alhaji Abubakar da Hajiya Fatima suka fito, kana sojojin nan suka maida murfin motan suka rufe tare da kuma sara wa suna fad'in "Welcome sir welcome Madam." hannu ya d'aga musu kana ya ce "Sannun ku da aiki." Hajiya Fatima ma barka da aikin tayi musu kana suka nufi cikin side d'in kai tsaye. mai kamada aljannar duniya. Suna shiga direct d'akinta Hajiya Fatima ta wuce, in da Alhaji Abubakar yawuce nashi d'akin dake nan cikin sashin nata, dan ya watsa ruwa ya rage gajiya. wan da a kaf girman gidan iya sashin ta ne kad'ai yake da d'aki bayan nashi side d'in. Bakin rantsattsen gadonta ta isa ta shinfid'a jaririyar da tun a hanya tayi bacci. ta janyo katon blanket d'inta mai kyau da laushi ta rufe ta da shi kasancewar sassanyar AC daya karad'e ilahirin bedroom d'in. ta wuce katafaren bathroom d'inta mai kyau da kawa tamkar d'akin kwana. tsaf-tsaf da shi ko ina a goge kwalkwal sai sheki da tashin kamshi yake. kyakkyawan pampo na alfarma ta matsa ta tari ruwa mai d'umi dai-dai in da jikin jariri zai d'auka, ta tari ruwa cikin bawun mai kyau da tsafta, ta zuba tureren wanka mai sanyin kamshi cin ruwan sannan. ta d'auko tafito da shi cikin d'akin. ta kashe AC. dai-dai lokacin da jaririyar take farkawa, ta isa da sauri ta d'auketa ta tub'e mata kayan kijinta. kana ta sakata cikin ruwan tayi mata wanka da sabulu mai tsada. ta dunkuleta cikin towel mai taushi ta kwantar da ita kan gado, kana ta tattare gurin ta tsaftace shi. sannan ta isa gaban ramb'asheshen wardrobe d'inta taciro wani kayataccen akwati mai kyau da kaganshi kasan na musamman ne sannan kuma badaga kasarnan yafito ba. bud'e akwatin tayi tana bin kayan ciki da kallo, kai ta girgiza tare da sakin murmushi. kayan yara ne masu kyau da tsada, wan da ta jima tana adanarsu. duk sanda suka fita wata kasar sai ta shiga kasuwarsu tayi siyayyan kayan jarirai. dukda kuwa bata da tabbacin samin cikin dan har tafara cire rai da samin haihuwa. Tana cikin shirya ta aka turo kofa da sallama. ta tad'ago da murmushi tana amsa sallamar. shima murmushin yake aika mata ya karo bakin gadon ya zauna yana fad'in "Ammie'n FEERYAL tun yau anfara nuna min anyi baby anshare ni, an barni nayi komai da kaina, da ma ance idan mace ta haihu tofa daga ranar soyayyar ka tadawo rabi rabin kuwa za'a maida kan d'anka, to nagode tun da iya rabi ne ba duka Feeryal zata kwace min ba, zan samu a bani abinci kuwa?." yakarashe maganar yana d'aukar FEERYAL data sha mata kwalliya cikin wani dogon rigar jarirai mai matukar kyau da d'aukar ido. ido ya zuba wa yarinyar tare da fad'in "Sarki ya tabbata ga Ubangijin halittu daya halicci wannan kyakkyawar halittar, tabarakallah masha'allah." murmushi Hajiya Fatima data amshi sunan Ammie tayi ta ce "Ayi min afuwa yanzu ma kuwa zan baka abinci, bari nashiga kichin yanzu na samar maka abincin da zakaci." Hannunta ya rike ganin tana kokarin mikewa ya ce "Dakata mufara samar mata da nata abincin kafin, muje asibiti musami shawarwari gurin likitocin yara, ta in da zamu inganta mata lafiyarta da kuma abincin da zata rika ci." kai Hajiya Fatima ta girgiza kana ta ce "Kuma yunwa takeji da gani, tun d'azu take ta kananun kuka." mayafinta ta d'auka yana gaba rike da FEERYAL tana biye da shi suka fita, direba yakaisu asibiti. Kasancewar likitan sananne ne agurinsu, Alhj Abubakar ya yi masa bayanin komai kan tsintarta sukayi. bayan likitan ya bincika lafiyar ta da nazari kan abincin da zai karb'i jikinta. ya shaida musu madara bazai d'auki jikinta ba, idan har akace za'a masa kan sai tasha madara, karshe ta iya rasa ranta dole nono ne kad'ai zai iya d'aukar ta. Alhaji Abubakar ya ce Za'a nimi mai shatar da ita, Hajiya Fatima ta ce ina ita zara shayar da ita. Da amincewar maigidan nata atake agun aka sakamata sinadaran da zasu kawo mata ruwan nono bayan wasu y'an awanni suka juyo gida. Kan kace me ruwan nono ya kawo tamkar mai sabon haihuwa kuma na fari, haka ruwan nono yaciko. nan da nan kuwa yarinya ta karb'i nono takama sha. Washegari da safe. Hajiya Fatima ta shirya jaririyarta cikin wasu kaya masu kyan gaske, suna zaune a parlour, Alhaji Abubakar nazaune a gefen ta yana kallon yanda take yashar da jaririyar, gwanin ban sha'awa. murmushi ya yi tare da shafo gefen fuskarta. "Yamiki kyau sosai shayarwa, Allah ya baki iko da lafiyar cigaba da shayar da ita." da ido ta amsashi tana aika masa murmushi. Knocking akayi tare da turo kofar parlour'n. burki taja daga bakin kofar tarike hab'a tana kallon Hajiya Fatima da jaririyar da take shayarwa, cike da matukar mamaki. murmushi Hajiya Fatima ta yi ta ce "Ki karaso mana Farida, ya kika tsaya daga bakin kofa." Fuska ta yamutsa gulma na cinta har kafarta na rawa tana alla-alla ta yuya ta ce "Daddy wai kazo inji Hajiya." tana gama fad'i ta juya da sauri. gudu ta saka bata tsaya ko ina ba sai side d'in Hajiya Halima mahaifiyarta kuma uwargida ga Alhaji Abubakar Fiya. a parlour ta tadda uwar tata, da kuma Hajiya Karima mata ta biyu ga Alhaji Abubakar, da y'ay'an su duka. kamar zata zube kasa cikin haki take fad'in "Mommy Aunty ta haihu." cikin rashin fahimta Hajiya Halima wato Mommy ta ce "Ke wata Aunty? kin shigo a razane duk kin razana mutane." murya na rawa cike da tsugudidi ta ce "Aunty Fatima wlh yanzu nan naganta tana baiwa jariri nono, Daddy na zaune a gurin." Ido Hajiya Karima ta gwalalo tare dare da fad'in "Zancen banza kai yaushe akayi cikin da za'a yi haihuwar har kowa ya kasa sani, ai wannan sai dai taga haihuwa a tsuliyar wani badai a nata ba." "Wlh Umma Karima naganta da idona tana bawa yaro nono." kirji Hajiya Karima ta buga har suna had'a baki da Mommy wajen fad'in "Yaushe tayi ciki har ta haihu bamu sani ba." "Wlh ni dai na ganta dama Hajiya ce ta aike ni kiran Daddy tun jiya take ta kiransa a waya baya d'auka, shine tace naje na kirawo mata shi dan tasan yana can makale wajen kinibabbiyar matar nan tasa, bari ma naje na sanar mata sabon labari." tafice da gudu tanufi sashin Hajiya wato kakar su. Tun daga bakin kofa take fad'in "Hajiya Hajiya Hajiya." wata dattijuwar mata dake zaune a wani kayataccen parlour tana sanye da gilashi a idanunta, hutu da kwanciyar hankali sun bayyana a kijinta, wanda ya b'oye tsufarta, zaka iya mata kallon daya gaza shekarunta sabar hutu. "Ke wani irin shashancin kira ne wannan, sai naci mutuncinki Farida, ina tun d'azu na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa ko." cikin rad'a da iya gulma ta ce "Hajiya wlh Aunty ta haihu Daddy yana can." baki Hajiya ta karkace ta ce "Ke Farida Fatima ce ta haihu cewa akayi miki haihuwar wasa ce, shekara nawa tana zaune sai dai taci taje ta juye a shadda, ko b'atan wata bata tab'a yi ba, wannan da ita yafara aura nasan bazata tab'a barinsa ya kara aure ba, da ni da ganin jikokina ta gefen sa kuwa har abada, sai dai in cikin abinci tayi ta haifa a shadda, bari naje na ganewa idona." "Wlh Hajiya kije kigani da gaske ne." Hajiya ta mike tanufi kofa tana fad'in "Yanzu ma kuwa, dan rashin daraja Fatima tafi masa ni, tun jiya baizo ya gaishe ni ba yana makale a gurin ta." A b'angaren su Mommy kuwa bakaramin girgiza sukayi da jin lamarin ba, dukkanin su suka nufi sashin Aunty dan gane wa idon su abin da ke faruwa. a kusan tare suka iso da Hajiya dan ita direban ta tasa ya kaita side d'in Aunty'n dan tafiyar tafi yi mata sauki. suna shiga parlour'n kowa yatsaya cike da d'in bin mamakin ganin jaririya a hannun Aunty tana shayar da ita. hankali tashe Mommy da Umma Karima suke kallon-kallo, kowa da irin abun da yake sakawa a ransa. hajiya ta rafka wani uban salati tare da tafa hanu tana fad'in "Ikon Allah Abubakar ina cikin gidan ayi haihuwa ban sani ba, kamar yadda bansan da cikin ba, Eh lallai ta wanke ta baka kasha, ka mance da uwar da

Chapter 1 of 20