Meenah tace "to mu tafi tare mana" Ashnaah ta
xaro ido tace "ae ya gaya ma masu gadin kar su bar ni in fita, da
ana bari na in fita da tuni na gudu na kara gaba ae" Meenah ta
fashe da dariya, Ashnaah tace "bari in dauko kudin" meenat tace
"to amma ba ynxu xae dawo ba dae ko, kar ya xo ya sameni in
shiga uku" Ashnaah tayi dariya tace "ae sae dare yake dawowa
gantalallen"
~Dr Khaleel ~ By Khaleesat Haiydar
40.....
Ashnaah ta sauko rike da dubu takwas din da ya rage cikin kudin da aka bata ta mika ma Meenah, Meenah ta kirga snn ta xuge jaka ta xuba su ciki ta kulle, tana kallon abincin gaban Ashnaah tace "to ina kika samo tuwon nn" Ashnaah ta dan tabe baki tace "wae fa kansa ya siyo ma xae ci to da ya gan ni da baki sae kunya ta kamasa kmr xae nutse shine fa ya ajiye min, kinsan dae ba sata kadae bne abun kunya" dariya kawae Meenah ke yi, ita kam komae na Ashnaah dariya yake bata, gata dae yarinya amma in ta xaro maka mgna sae kace babba yyi ta, Ashnaah na kallonta da mamaki tace "ae gskya ne, ko ruwan fa da xan sha gidan nn bbu sae dae in je in sha na famfo duk tsutsa, ko me aikin gidan mu wllh ruwan gora take sha, to ina dalili" Meenah tayi dariyarta me isarta tace "to shi wani ruwa yake sha tunda bbu ruwa a gidan" Ashnaah tayi murmushi ta mike tace "ina xuwa in nuna maki" sama ta nufa ta bude falonsa ta shiga snn ta nufi fridge dinsa, a rufe ta tarda fridge din ta cije dan yatsa a xuciyarta tace "ae sae na nema wllh" bbu rabon xata wahala ta hango keyn kan fridge din ta bude da sauri tana kallon ciki, wines din basu fi biyar ciki ba, biyu iri daya, uku iri daya, kinkimansu tayi gaba daya ta nufi gun Meenah ta dire su gabanta ta nemi guri ta xauna tace "kin gansu nn" da mmki Meenah ke kallon kwalaban ta daga tana kallon Ashnaah tace "wnn ae giya ce fateema" Ashnaah ta tabe baki tace "to su ne ruwansa a gidan nn, in ya kafa kai baya ajiyewa sae ya kwankwade gaba daya" Meenah da kanta yyi mugun daurewa tace "dama Khaleel na shan giya" Ashnaah tace "gashi ko kin gani, suna can da yawa a fridge dinsa kala kala" Meenah tace "haba shi yasa ko da yaushe xan ji fridge dinsa a rufe idan naje can gidan su" Ashnaah tace "to ynxun ma an gaya maki a bude na samu, da kyar na samo makullin," Meenah tace "dole ko da yaushe xaka gansa cikin rashin fara'a, kin san Allah tunda nake kallon arxiki bae taba hada mu ba" Ashnaah tace "ga tuwo ki ci bari in je inyi sllh, ko azahar bn yi ba" Meenah tace "to je ki dawo in baki wata shawara" Ashnaah tace "to" snn ta nufi sama don yin alwala tayi sllh. Khaleel na xaune office bayan ya fito daga theatre ya jinginar da kansa jikin office chair dinsa idonsa lumshe kmr me bacci aka bude office dinsa, ya bude ido da sauri don ganin wanda xae shigo, Ameesha ce ta shigo office din da sallamarta, ya mayar da kansa ya lumshe idonsa, ta dan tsaya nesa da shi tace "ka gaji koh" ya bude ido yana kallonta yace "yep, bacci ma nake ji" tace "to abinci fa, ina tuwon da na kawo maka daxu" ta fadi hka tana dudduba abincin a office din, da kmr baxae ce komae ba sae kuma yace "sorry na bayar da shi" shiru tayi tana kallonsa, ya mike xaune da kyau yace "kin yi fushi ne" girgixa masa kai da sauri tayi, yyi murmushi yace "amma ae na ci kadan, vegetable din yyi ddi, kin yi kokari, u re a gud cook" murmushi tayi da ya kara fito da ainahin kyanta, a hankali tace "thank yhu" ya gyada mata kai yana murmushi snn yace "gida xa ki ynxu ne" ta gyada masa kai alamar eh, ya mike ya dauki makullin motarsa yace "mu je gidana ki min girki sae in kai ki gida" shiru tayi tana kallonsa, yace "ko baxa ki bne" a hnkli tace matarka fa, ya galla mata harara yace "waye hka" kasa cewa komae tayi sae kallonsa take, yyi tsaki ya kwashi wayoyinsa yana kallon agogo ya ga Karfe biyar saura, Yace "mu je in xa ki" ba musu ta bi bayansa suka fita ya kulle office dinsa, sae da ta fara xuwa office din dad dinta ta dauki handbag dinta snn ta sauko tayi ma sauran nurse din sallama ta nufi gun motar Khaleel don yana ciki yana jiranta. Ashnaah da Meenah na xaune har lkcn a falo, Ashnaah na digestin duk abinda Meenah tace mata, bbu irin abinda Meenah bata kintsa mata ba, gate suka ji an bude, Meenah ta mike tsaye da sauri tace "waye hka xae shigo" Ashnaah ta wara ido tana kallon agogo, jin karar motar Khaleel yasa ta kalli kwalaban wine din dake xube gabansu har lkcn bata mayar ba, mikewa tayi a tsorace tace "wayyo na shiga uku shine ya dawo, me ya dawo da shi ynxu" Meenah ta xaro ido ita ma a tsorace tace "kin shiga uku ko na shiga uku," kwashe kwalaben Ashnaah tayi ta nufi kitchen da su da gudu jikinta na rawa sae kuma ta fito da su duk a rude, sae ca take na shiga uku ina xan Kai su xae iya shiga kitchen ya gansu, kitchen ta kuma komawa da sauri ta boye su cikin store, ko da ta fito bata ga Meenah a falon ba, xata bar falon ita ma aka bude kofa, ta juya da sauri tana kallonsa nn da nn ta hade rae, ya kwaso takalman da ya gani bakin kofa da mamaki yana kallon Ashnaar yace "takalman waye wnn"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
41
Shiru Ashnaah tayi tana kallon Ameesha da ke bayan Khaleel ta ki shigowa, ya daka mata tsawa yace "ba kya ji na ne, nace takalmin waye wnn" Ashnaah tace "wacece wnn a bayan ka" bude baki yyi da mmki yana kallonta yace "ina maki tambaya kina min tambaya" dauke kanta tayi fuskarta a daure taki cewa komae, ya kuma daka mata tsawa yace "nace takalmin waye wnn" ta juya tana kallonsa tace "sae ka fara gaya min wacece wancan a bayan ka" ta karashe mgnr tana hararansa, ihu ta fasa ganin ya yo kanta ta nufi bayan kujera da sauri tana cewa "wayyo wllh xan gaya maka ka tsaya" ganin kamata yake son yi yasa tace "don Allah kayi hkuri na wa ne ina son in fita in siyo abu ne sae mai gadi ya hanani, sae na manta ban shigo da shi ba" tsayawa kallonta yy, yyi kwafa yace "bace min a falo" hararan Ameesha tayi snn ta haura sama. Bayan kofarta ta tarda Meenah a labe, ta fada kan gado ta dinga kyalkyala dariya, Meenah ta fito da sauri ta mata alamar tayi shiru, Ashnaah tace "ae ba shigo wa xae yi ba," a hankali Meenah tace "to ya xa ayi in bar gidan nn yau, ga shi nace ma momy ba ddewa xan yi ba" Ashnaah tace "ae xae shi ga dakinsa sae ki fita da gudu, muyi hirar mu don Allah," Meenah ta galla mata harara tace "da wani bakin xan yi hira, kin san ynda ciki na ke kara kuwa, ba mutun ci gare mijin nn naki ba sae ya iya wurga ni waje wllh" Ashnaah tayi dariya tace "to sae kiyi ta tsayuwan, nace maki baya shigo min daki sae in nayi laifi" dakinsa suka ji ya bude, Meenah ta koma bayan kofa da sauri har tana bugewa, Ashnaah ta toshe bakinta kar ta Tona masu asiri da dariya, fitowa Meenah tayi tace "to ya shiga dakin, ta ina xan bi" Ashnaah ta mike tace "ina xuwa" snn ta fice, ba a jima ba ta dawo rike da takalman Meenah tace "oya xo ki gudu yarinyar da ya kawo ma na kitchen, amma yaushe xa ki kuma dawowa don Allah" Meenah tace "gskya ba ynxu ba" Ashnaah ta marairaice tace "haba don Allah to wayata fa gashi fa kinsan abinda yasa nake son siyan wayar" Meenah tace "to xan yi kokari gobe in na siya in kawo maki amma fa baxan dde ba" Ashnaah tace "yauwa don Allah kar ki manta ki siyo min maganin ciwon ciki in xaki xo, wllh tsoro nake ji period dina ya kusa xuwa kuma wahala nake sha wllh, ynxu ma ya fara damuna" Meenah tace "to Allah sa kar in manta" Ashnaah ta riko hannunta tace "Aa don Allah kar ki manta ki siyo min, ina jin jiki in ina yi" Meenah tace "to naji, amma kuma ba ga ki da likita a gida ba" Ashnaah ta bude baki tace "au likita ne, ki ce wllh" Meenah tayi dariya tace "ohh da baki sani ba, wllh likita ne kuma babba ma" Ashnaah ta tabe baki tace "oho ni ina na sani" Meenah ta saka takalminta tace "kin ga sae na xo" a hnkli ta bude kofar ta shiga sauka daga stairs da sauri, da gudu gudu sauri sauri kmr munafuka ta fice daga gidan gaba daya, Ashnaah da ke lekenta ta window sae dariya take har da kyakyatawa tana rike ciki, bude kofar ta taji an yi ta juya da sauri taga Khaleel ne, da mmki yace "ke kina da hnkli kuwa, wa kike ma dariya a window" Ashnaah ta kuma kwashewa da dariya har da durkushewa inda take tana rike ciki tana kallonsa, dariyar shima ta basa, ya kauda kansa yyi murmushi ya juya ya fice daga dakin, sae da ya sauka kasa snn shima ya shiga dariyan, anya yarinyar nn ita kadae take kuwa tambayar da yyi ma kansa knn bayan ya shigo falo. Har Ameesha ta gama girkin da Khaleel ya sa ta Ashnaah bata fito ba, tasan kila adduarta Allah ya amsa, don tun da ta shigo kitchen din take adduar Allah yasa kar Ashnaah ta sauko, don ita hka kawae take tsoron ta, kan dinnin ta jera masa abincin ta karaso falon tana kallonsa tace "na gama," ya mike xaune yana kallonta yace "thnk yhu dear, kawo nn mu ci" ta girgixa masa kai tace "ni na koshi gida xan tafi" ya harareta yace "ae kya bari in ci abinci ko" murmushi tayi ta gyada masa kai, yace "to kawo min abincin nn falo" juyawa tayi ta je ta dauko abincin ta shigo falon ta ajiye masa gabansa, bin ta kawae yake da kallo, ssae take basa sha'awa, kujera ta xauna tace "bari in jira ka a nn" ya gyada mata kai snn ya shiga xuba shinkafar gabansa a plate. Shidda saura ya mike yana kallon Ameesha yace "tashi in kai ki gida dare na yi" ta mike tana gyara mayafin kanta, shi kuma ya nufi sama, dakin Ashnaah ya bude a hankali ya sameta kwance tayi dai dai tana bacci, no wonder yyi mmkin rashin saukowarta, har xae rufo mata kofa sae kuma ya fasa, yana kallonta yace "ke" a firgice ta farka, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, ya galla mata harara yace "hka aka koya maki a gidan ku ki dinga bacci da yamma" hamma tayi tana hararansa, snn ta mike tsaye tayi mika ta nufi bathroom abunta ta bar sa nn tsaye, binta yyi da kallo har ta shiga bayin snn ya kulle mata kofar dakin ya sauka kasa, bakin mota ya tadda Ameesha tana jiransa, ya bude motar suka shiga suka bar gidan. Bakwae saura ya ajiye ta a kofar gidan su yace xa su yi waya anjima, tayi murmushinta Mae kyau ta daga masa hannu snn ta nufi gate dinsu, bin ta yyi da kallo har ta shiga snn ya sauke ajiyar xuciya yyi reverse ya bar anguwar ya kama hanyar gidansu, a masallacin da ke kofar gidansu yyi sllh snn ya shiga gida, sama ya nufa ganin bbu kowa a falo ya shiga dakin umminsa, ya sameta xaune kan darduma, sae da ya jira ta gama addu'o'inta snn ya sauka kasa ya gaida ta, ta amsa tana murmushi tace "sae yau Abbana, ina Fateema" yyi murmushi yace "tana gida ummi, rukayya fa" ummi tace "ina jin tana dakinta, daga ina kke hka," yace "daga gidan su Ameesha" Ummi tace "Ameesha kuma, lfya dae ko" yace "lfya ummi ajiyeta nayi ne" ummi bata ce komae ba, can dae tace "to ina fateemar," yace "tana gida nace ummi" "to ya baka taho da ita ba xaka var ta ita daya da magariban nn" shiru yyi bae ce mata komae ba, can yace "Abba na nn" ummi tace "ina ga ya dawo daga masallaci ynxu ka Duba dakinsa" mikewa Khaleel yyi yace "ina xuwa mum" snn ya fita xuwa dakin Abbansa, Abba na canxa channel xaune falonsa da remote a hannu Khaleel ya shigo, wuri ya nema ya xauna nn kasan carpet snn ya gaida dad din nasa, ya amsa yana cewa "kayi wuyar gani son" Khaleel yyi murmushi yace "wllh kam Abba aiki ne ya rike ni" Abba yace "to Allah ya taimaka, ya iyalin ka" Khaleel yace "alhmdllh Abba" hira ssae suka yi da dad din nasa daga bisanni yace "Abba dama wata magana na xo maka da, Allah yasa xaka ban goyon baya" Abba ya tattara hankalinsa gaba daya kansa yace "to ina jin ka son, wace mgnar ka xo da"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
42....
Khaleel ya dan shafa kansa ba tare da ya kalli Abban nasa ba yace "Dama ba wata magana bace Abba aure nake son kara yi" yana fadin hka ya dago kansa don ganin reaction din dad din nasa, kallonsa kawae Abban nasa ke yi, Khaleel ya sunkuyar da kansa, Abba ya numfasa yace "aure kuma?" Khaleel ya dago kansa a hankali yace "in'sha Allah Abba" Abba yace "lfya dae koh" Khaleel yyi murmushi yace "lfya lau Abba" Abban yyi murmushi yace "to Allah ya bada sa'a, amma ina ka samo matar" Khaleel ya kuma sunkuyar da kansa yace "Ameen Abba, Khadija ce," Abba yace "wace Khadijar" Khaleel xae yi magana Abba yace "au! ko dae yar wajen Alhaji Mukhtar" Khaleel ba tare da ya dago kai ba yace "ita Abba" Abba yyi murmushi yace "ahh ae hkn da kyau Masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi, amma matar ta ka ta amince dae ko?" Khaleel yace "eh ta sani abba" Abba yace "gud! Allah ya xaba abinda ya fi alkhairi son" Khaleel yyi murmushi yace "Ameen Abba, but plss Abba kae xaka ma ummi magana don bn san ynda xata dauki xancen ba" Abba yace "sam bata da ikon hanaka aure don ko uku kace kana so ynxu in dae xaka yi adalci aura maka xa ayi" Khaleel bae dae ce komae ba yyi murmushi kawae, bae bar falon Abbansa ba sae kusan Karfe tara, don tare ma suka fita masallaci don yin sllhn isha suka dawo suka ci gaba da hirarsu, ummi ce ta shigo falon tana kallon Khaleel tace "kai kasan xa ka jima hka don me xaka bar yar mutane ita daya a gida da daren nn fisabillahi" Khaleel yace "ynxu xan tafi ummi ni ban san ma lkci ya wuce hka ba" tana hararansa tace "ina ko xaka sani" juyawa tayi ta fice daga dakin, Abba yyi murmushi yana girgixa kai, Khaleel ya mike shima yana murmushin yace "Abba bari in je sae da safe" Abba yace "to Allah ya tashe mu lfya" dakin mum dinsa ya shiga yace "to ummi na tafi sae da safe" tace "Allah ya tashemu lfya" murmushi yyi ya juya ya fita ya rufe mata kofar ta, dakin Rukayya ya bude ya sameta kwance tana danna waya, ta mike xaune da sauri tace "lah yaushe ka xo yaya" hararanta yyi yace "me yasa baki xuwa gidana" ta dan turo baki tace "ae ya Khaleel matar nn taka ce bata da mutun ci shi yasa bana son xuwa" yace "gidanta ne ko nawa" tace "to yi hkuri yaya xan xo kila Sunday" yace "Allah ya kai mu," snn tayi Masa sae da safe ya rufo mata kofar ta ya sauka kasa. Karfe goma saura Khaleel ya isa gida, yana shiga falo ya kashe wutan, snn ya nufi sama, har xae bude dakinsa ya shiga sae kuma ya nufi kofar Ashnaah ya bude, xaune ya sameta kasan dakin ta hade kai da gwiwa, ta dago da sauri tana kallon kofar, hawayen dake makale idonta ne ya sauko a hankali bisa kuncinta, ta mayar da kanta bisa gwiwanta, tsayawa yyi yana kallonta, can dae ya karaso Cikin dakin
Har lkcb yana kallonta, ya durkusa gabanta bbu yabo bbu fallasa yace "kina da matsala ne" dago kanta tayi da sauri can ta mike tana huci, ta shiga masa wani matsiyacin kallo tace "ikon Allah, halan dae meye gami na da kae da har xaka wani shigo min daki kana neman sanin matsalata???" kallonta ya tsaya yi, can yyi huci me xafi ya kai mata wani wawan mari, bata gama recover ba ya kuma Kai mata wani snn ya turata da karfi ta fadi ta buga kai da gado ya juya ya fice daga dakin, kuka ta dinga rusawa tana rike da kanta tana masa Allah ya isa, tayi mai isarta snn ta mike a hnkli ta hau kan gadonta tana sauke ajiyar xuciya, ranan kwata kwata bata runtsa ba, ga ciwon cikin da ya addabeta tun daxu ga kuma ciwon kan da Khaleel ya daura mata. Da safe tana kwance ta ji fitar motarsa, ta mike xaune da sauri tana tunanin inda xata samu kudi ta ba mai gadi ya je chemist ya siyo mata maganinta don tasan in ba maganin nn ta shiga uku, mikewa tayi da kyar, ta fita daga dakin ta nufi dakin Khaleel, a kulle ta ji shi, ta ja dogon tsaki wato kila jiya ya gane ta shigar masa daki knn, komawa dakinta tayi ta fada kan gado ta shiga rusa kukan takaicin jin mgnr mahaifinta da bata yi ba tun farko, da yasan tana jin mgnr sa da bbu abinda xae sa yyi Mata irin wnn auren masifar, ta ci kukanta ssae daga karshe baccin da bata yi ba jiya ya dauketa, ko da ta farka da rana ko kadan bata da appetite sae taji kmr xaxxabi ke neman rufeta, ta dae samu da kyar ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh snn ta koma ta kwanta, wajajen Karfe hudu ta farka ta dalilin wani axababben ciwon mara, ko ba a gaya mata ba tasan period dinta ne ya xo mata, ta sauko daga kan gadon da kyar ta xauna kasa jin xuciyarta na tashi kmr xata yi amae, kasa daurewa tayi ta fashe da kuka ssae tana yarfe hannu ga shi Meenah bata xo ba, ynxu da gidan su take da tuni an tanadar mata magungunanta tunda an san irin axabar da take sha, ko pad din ma bata da, to wa xata gaya ma, tunanin hkn yasa ta kuka ssae, ta dinga mutsu mutsu a daki ita daya kmr me nakuda, har aka yi isha tana nn xaune ta ci kukanta har ta gode Allah, Karfe tara da kusan rabi Khaleel ya shigo gidan, ya kashe wutan falonsa as usual ya nufi sama xae shiga dakinsa, shesshekar kukanta ya ji, ya juya yana kallon kofar dakinta, ya dde tsaye inda yake daga bisanni ya nufi dakin ya tura kofar, da sauri ta dago tana kallon kofar har lkcn tana xaune inda take, ssae idonta ya kumbura lebbanta suka yi ja sbda kukan da ta ci, kauda kanta tayi, ya karaso cikin dakin ya durkusa gabanta yana kallonta yace "idan kika min mgnr bnxa xan baki mamaki, Meye matsalarki?" bbu yabo bbu fallasa yyi tambayar, tayi shiru ta ki cewa komae fuskarta a daure, tsawan da ya tsoratata ya daka mata yace "ba mgna nake maki ba" ta fashe da wani Sabon kukan tana komawa baya daga xaunen da take tace "ni ka rabu dani bbu ruwan ka" fincikota yyi ta fasa ihu a tsorace tace "wayyo kayi hkuri wllh cikina ke min ciwo" cikin kuka ta karashe mgnr, kasan tiles din dakin taga yana kallo ta sunkuyar da kanta da sauri ita ma don ganin abinda yake kallo, jini ta ga dae dae inda ta bari, juya masa baya tayi da sauri ta kuma saka kuka.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
43.....
Kallonta kawae Khaleel ya tsaya yi, ta shiga kkrin mikewa tsaye amma kunya yasa ta kasa, komawa tayi ta xauna ta shiga rusa wani Sabon kukan, ya mike ya xagayo gabanta yana mata wani irin kallo yace "wa kika gaya ma cikin ki na ciwo" kauda kanta tayi bata ce komae ba har lkcn tana kuka, ya hade rae yace "ohh don cikin ki na ciwo shine xaki dinga bata ma mutane waje da kazantar ki, kina hauka ne" cikin kuka tace "to ni nasan inda xan samu abinda xan sa" ya galla mata harara yace "baki gansu cikin kayan akwatin ki ba" ita ma ta galla masa harara tace "to na taba Budewa ne" murmushi yyi ya nufi gun akwatunan lefenta ya shiga bubbude su, ta juya tana kallonsa don tun da ta shigo gidan bata taba bude ko da akwati daya ba a cikin akwatuna shiddan da yyi mata, tana kallo ya ciro pad daya cikin akwatunan da aka xuba kayan shafe shafe da kayan make up, yana rufe jakar ta dauke kanta da sauri, ya jefa mata kan gado ya juya xae fita, da sauri ba tare da ta shirya ba tace "toh cikina ciwo yake min kuma bbu maganin da xan sha" ta karashe maganar cikin kuka tana yarfe hannu, juyowa yyi yana kallonta sae kuma yyi tsaki ya fice daga dakin, kuka ta kuma fashewa da ssae, ta mike da kyar ta nufi bathroom, mop ta dauko da ruwa xata gyara dakinta amma ta kasa don wani axaban ciwo da mararta ke mata ta durkushe wajen ta dinga rusa kuka kmr an aikota, ta kusa minti goma tana abu daya, Khaleel ya bude kofar dakin ya shigo, tsawa ya daka mata yace "wae kina da hnkli kuwa, baxa ki tashi ki gyara jikin ki ba" cikin kuka tace "ni baxan iya ba cikina ciwo yake min" karaso wa kan gadonta yyi ya dauki pad din da ya ajiye mata ya karasa kusa da ita ya mika mata yace "tashi ki bace min a nn" mikewa xata yi amma ta kasa, hkn yasa ya dago ta ya mika mata pad din snn ta nufi bathroom dinta tana ci gaba da kukanta, ko kafin ta fito har ya gyara gun da ta bata, yana xaune gefen gadonta yana hada allura, kallo daya tayi masa ta dauke kanta tayi kwanciyarta kan gadon tare da juya masa baya, yana gama abinda yake ya juya yana kallonta yace "have u eaten" fuskarsa a daure yyi mata tambayar, ba tare da ta jiyo ba ta girgixa masa kai, mikewa yyi ya fita daga dakin, sae gashi ya dawo da ruwan xafi cikin cup, ya xauna inda yake da, ya shiga bude kayan tean da ta jera kan bedside drawernta, ya gama hada tean snn ya bude sugar xae xuba yaji bbu komae ciki, juyawa yyi da sauri yana kallonta don yasan bae ci ace sugarn ya kare ba yace "ina sugarn dake kwalin nn" ta juya ita ma tana kallonsa tace "ya kare mana, sugarn ma da ba xaki" yace "yyi kyau, shine xaki ce min cikin ki na ciwo ko" kin cewa komae tayi yace "rokon ki xan yi ki tashi ki sha tean" mikewa tayi fuskarta a daure ta karaso gabansa ta durkusa ta dauki tean ta shiga sha a hnkli, kallonta kawae yake, ta cire bakinta a cup din ta dago tana kallonsa ya dauke kansa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 29