nan Khaleel ya basa Address dinsu Ashnaah, Najeeb ya kwafe a wayarsa snn yace "amma me yasa xaka xarga Ameesha har ka doketa, idan ba ita bace ba fa" Khaleel yace "don't tell me dat, ita kadae ta iya rubutu kmr nawa, snn bayan ita bbu mai shigar min daki, to wae ma mu nawa ne a gidan da xaka ce kar in xargeta, ko kwana biyar fa ba ayi da xuwan uwarta gidan ba abun nn ya faru, to wa ya sa ta idan ba ita ba" Najeeb ya mike yana kallon abokin nasa yace "kar ka damu frnd ka kwantar da hnklinka, gobe xan tafi can gidansu fateeman."
~Dr khaleel~ By khaleesat Haiydar 72..... Nan Najeeb yyi masa sallama ya fita, Khaleel ya fada kan gadonsa ya runtse ido, duk ji yyi duniyar tae masa xafi, Ashnaah da komae nata kadae ke masa yawo a ka, nn da nn ya ji kmr xaxxabi xae rufesa. Karfe shidda saura na yamma Abban Khaleel ya shigo gida ya nufi dakin Ummi fuskarsa a daure yana kallonta yace "ina ibraheem" da kmr baxa ta ce komae ba sae dae tace "me ya faru kuma" cikin tsawa yace "nace yana ina" bae rufe baki ba Khaleel ya shigo dakin kmr wani mara lfya a sanyaye yace "gani Abba" kallonsa Ummi ta tsaya yi ganin ynda ya wani rame lkci daya, Abba ya juya yana kallonsa a fusace yace "don uwar ka wae halan kana shan giya ne" shiru Khaleel yyi bae ce masa komai ba, Abba ya daka masa tsawa yace "ka fada min me yarinyar mutane tayi maka ka ne mi kasheta yau" fada ssae Abba ke yi kmr xae maresa shi dae Khaleel bae ce komae ba hka ma Ummi, Abba ya gaji don kansa ya juya ya fice a fusace, Khaleel ya daga kai ya kalli mum dinsa snn ya juya ya fice daga dakin. Yana shiga dakinsa da minti goma kiran dad din Ameesha ya shigo wayarsa, da kmr baxae daga ba sae kuma ya daga yyi masa sallama, ba tare da ya amsa ba yace "ka xo gida ka same ni" bae jira cewar Khaleel ba ya katse wayar, sae da aka yi sllhr magrib Khaleel ya samu umminsa yace xae fita snn ya kama hanyar gidansu Ameesha, xaune ya tadda iyayen nata a falo da yayyinta maxa, Abbanta kadae ne ya amsa gaisuwarsa, ya xauna kasa yana kallon Abban nata bae dae ce komae ba, Alhaji mukhtar yace "wato da abin da xa ka biya mu knn ko Khaleel, dats great" takarda da pen ya dauka ya jefa gaban Khaleel yace "bani takardan ta ynxu" daukar takardan Khaleel yyi da pen cikin minti daya ya gama rubutun da yake ya dauka ya risina ya mika masa, karba yyi yana duba content din takardan kmr hka, "Ni Muhd Khaleel na saki khadija saki daya" Alhaji mukhtar yyi murmushi ya dauki wani takardan yyi rubutu yyi sign snn ya mika ma Khaleel, khaleel ya karba ya shiga duba rubutun, sack letter ya gani, mikewa yyi ya cukuikuye takardan ya jefar nn tsakiyar falon yace "sae da safen ku" snn ya juya ya fice daga gidan, mum din Ameesha tace "duk inda xaka neman aiki baxa ka samu matsayin da ka rasa ynxu ba sha sha sha kawae mahaukaci me gare ka xaka walakanta yar mi" Khaleel na shiga motarsa ya hade kae da steering xuciyarsa na masa wani irin xugi, yes tunda ya rasa Ashnaah komae ma ya rasa, wasu hawaye ne suka shiga sakko masa, duk duniyar yaji tayi masa xafi ya rasa me xae yi ya ji ddi, y him?" Da kyar ya iya jan motar ya bar layin, har ya kama hnyar gida yyi tunanin xuwa layinsu Ashnaah ko Allah xae sa su hadu, yana shiga layinsu cikin ikon Allah ya gansu ita da Ashfah sun dawo daga gidan inna knn.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 73..... Parking Khaleel yyi daga gefe ya fito da sauri ya nufo su, kamshin turarensa kawae Ashnaah ta shaka ta juya da sauri tana ganinsa ta ruga a guje ta nufi gate dinsu da sauri, Da mugun mmki Ashfah ke bin Ashnaah da kallo har ta shige gate din kawae gani tayi ta kwasa a guje ba dalili, juyawa tayi da sauri don ganin me take ma gudu, suka yi ido hudu da Khaleel ita ma ba sae ta ruga a guje ba, bin ta yyi da sauri ya shiga kiranta yace "don Allah don Annabi ki tsaya sister," kasa ci gaba da gudun ta yi ta ja burki ta tsaya ba tare da ta juyo ba, karasowa yyi inda take da sauri ya marairaice mata yace "Plss kanwata, kice da fateema tayi hkuri ta saurareni ko na minti daya ne plss help me beg her" Ashfah ta rasa abun cewa can dae tace "to bari in je in mata mgna" da sauri yace "yauwa kanwata ngd ssae ina jira plss" ta gyada masa kai ta nufi cikin gidansu, dakinsu ta samu Ashnaah kwance tana ta rusa kuka, ta karaso da mmki tana kallonta tace "meye abun kuka kuma sister, Kinga fa ni bana son hka, don me xa ki dinga daga min hnkli ne" Kmr ta kara tunxurata ta kuma fashewa da wani matsanancin kukan, Ashfah ta nemi gu ta xauna fuskarta dauke da damuwa tace "don Allah Ashnaah ki daina kukan nn wllh bana so yana damuna" da kyar ta lallasheta tayi shiru sae a snn ta tambayeta a sanyaye ko Khaleel ya tafi, Ashfah ta dan yi shiru snn tace "ehh ya tafi" komawa Ashnaah tayi ta kwanta tare da lumshe idonta kmr mai shirin bacci, Ashfah ta lulluba mata bargo tace "kiyi baccin ki kawae" Washegari da safe driver ya wuce da Ashnaah makaranta kmr ynda Abba yace, ko kadan Ashnaah bata gaya ma kawayenta abinda ke damunta ba kmr ynda suka bukaci sani, through out lectures din ranan shiru kke jin Ashnaah, lectures din ma ba fahimtarsu take ba kwata kwata, Karfe uku da rabi suka ga lectures Ashnaah ta dauki Jakarta ba tare da ta jira kawayen nata ba ta fito don jiran drivernta don tasan at anytime xae xo tunda ta fada masa lkcn tashin su, motar usman ta hango ta dauke kai da sauri amma har ya ganta, ya karaso inda take snn ya fito daga motar da damuwa yace "y ain't yhu pickn my cal Ashnaah" Ashnaah tace "to ina lecture din xan yi pick din cal dinka," shiru yyi yana kallonta, hkn yasa ta dan saki ranta tace "lecture muke ne wllh ka ga fitowa ta knn" yace "bbu damuwa, ya kike ya gida" tace "Alhmdllh" yace "ynxu xa a xo daukarki ko" ba tare da ta kallesa ba tace "ehh" ya dan yi shiru snn yace "kin ko gaya min lkcn da mijin ki ke fita da safe Ashnaah, koh kina ga...." Da sauri ta katse sa tace "ka ga ni fa we re no longer togeda, ya bani takardata tun shekaran jiya ina gidanmu" da mugun mmki Usman ke kallonta yace "waow re yhu serious dear shine baki gaya min ba, waww am so..." Da sauri Ashnaah tace "ka ga, sae mun yi waya ga driver can ya xo" bata jira cewarsa ba ta nufi gun motar gidansu da sauri don ba karamin farin cikin xuwan drivernsu tayi don ko kadan bata son jin mai usman ke shirin cewa. Karfe hudu da kusan rabi Ashfah ta sauka daga a dai daita sahun da ya ajiyeta dai dai bakin gate dinsu, da ganinta kasan daga makaranta take, Najeeb da ke jingine jikin motarsa can nesa da gidansu ya karaso da sauri ganinta, sallama yyi mata ta juya tana kallonsa, wani irin kallo tayi masa xata shiga gida ya sha gabanta da sauri yace "ki saurara pls fateema" Ashfah tayi tsaki tace "ni ba fateema bace malam ka bani hanya" xae yi mgna sae ga Ashnaah ta fito daga cikin motar da yyi parkin gefensu don drivern yace baxae shiga ciki ba momy ta aikesa kasuwa, juyawa Najeeb yyi yana kallon Ashnaah snn ya kuma juyawa ya kalli Ashfah da mugun mmki, kallo daya Ashnaah tayi masa ta dauke kai ta karasa xata shiga gida, Ashfah kam tuni har ta shige gida. Najeeb yace "wait plss fateema" juyawa tayi tana kallonsa, sae kuma ta tsaya don jin me xae ce, ya karaso inda take da sauri yace "dama ku yan biyu ne" juyawa Ashnaah tayi xata shige gida ganin tambayar bae da ma'ana, yyi saurin cewa "ki saurareni plss fateema" Ashnaah ta kuma juyawa tana kallonsa tace "ka ga idan ba ka da abun cewa ka rabu dani don bana son Abbana ya gani tsaye a nn" Najeeb yace "OK but mgnr na da tsayi, ko in bari da nyt" ta daga kafa tace "Allah ya kai mu" snn ta shige gida. Ana sllhn magrib Ashnaah ta sauko kasa ta samu mai gadinsu tace "don Allah baba xan yi bako kuma bana son abbana ya sa ni, anjima kadan xae xo idan ya xo ba sae ka shigo ba kawae ga nmbrta ka min flashn sae in san ynda xan fito" Mai gadin yace "to shkkn" snn ta ba shi nmbrta ta koma cikin gida. Khaleel na kwance dakinsa idonsa lumshe kmr mai bacci aka bude kofa Najeeb ya shigo, bude ido Khaleel yyi a hnkli duk a tunaninsa umminsa ce, najeeb ya karaso ya xauna gefensa yace "y Khaleel Ummi tace tun safe ka ki cin komae" Khaleel bae ce masa komae ba ya dauke kai kawae, Najeeb yyi shiru yana kallon abokin nasa, lkci daya wani tausayinsa ya shigesa, Najeeb ya dafe kansa
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 74...... Bayan kusan minti goma Najeeb ya dago kai yana kallon Khaleel yace "ka kwantar da hnklin ka plss Khaleel, ynxu ma daga gidansu fateema nake" da sauri Khaleel ya mike xaune yana kallonsa abun tausayi yace "pls re yhu serious frnd, ka samu ganinta" Najeeb yace "yes mun hadu but tace baxata iya tsayawa ba kar dad dinta ya dawo ya same mu, ynxu anjima da daddare xan koma" Khaleel ya kamo hannayensa lkci daya hawaye ya cika idonsa yace "pls frnd help me convince her dat I wasn't d one dat wrote dat divorce letter, plss I beg yhu" Rungumesa Najeeb yyi yace "its OK, I will try my vry best frnd nayi maka wnn alkawarin, but nt until u stop does tearz" Khaleel ya dafe kansa bae ce masa komae ba xuciyarsa na masa kuna, mikewa Najeeb yyi ya fita ya karbo abincinsa gun Ummi snn ya dawo ya ajiye masa yace "ga abinci kaci kar ka sa ma kanka wani ciwon Khaleel" Sae da Najeeb yyi da gske snn Khaleel ya ci spoon uku a abincin ya ki cin sauran, Najeeb na kallonsa yace "ko xuwa gobe da nyt sae mu je ka ba Alhaji mukhtar hkuri na tabbatar xae hkura don bn ji ddin xancen da nake ji ba" Khaleel ya mike da kyar yana kallonsa yace "am going no where" yana kai wa nn ya shige bathroom. Karfe takwas da kusan rabi Najeeb ya isa gidansu Ashnaah, mai gadin yyi ynda ta ce masa, ba a dau lkci ba ta fito ts nufi gun Najeeb dake jingine jikin motarsa, ya kafa mata ido har ta karaso ta rungume hannayenta tace "ina jin ka" Najeeb ya dan sauke ajiyar xuciya yace "ki fada min gskya fateema, re yhu happy ynxu da Khaleel ya sake ki" daga kai tayi tana masa mugun kallo tace "wani irin tambaya ce wnn" Najeeb ya dan yi shiru Snn yace "kafin ki ji abinda ke tafe da ni sae kin ban amsa gskya, re yhu happy now dat d both of u re nt togeda" Ashnaah tace "yes am happy, y won't I b happy, I'm vry vry happy coz I've..." Kuka ta fashe da ssae, Najeeb yyi shiru yana kallonta, ta hade kanta da mota ta dinga rusa kuka kmr an aikota, a hnkli Najeeb yace "karya kike fateema, yhu re nt happy, nevertheless I came on behalf of my frnd" dago kai tayi tana kallonsa har lkcn tana hawaye, Najeeb ya dan yi shiru snn yace "ba Khaleel ne ya rubuta maki takardan saki ba," Ashnaah ta tabe baki tace "kwa dae raina ma kanku hnkli ba ni ba" Najeeb yyi murmushi yace "wllh kuwa its a set up, kinsan Wanda yyi rubutun ya sa a drawernsa" Ashnaah tayi shiru tana kallonsa yace "Ameesha, can yhu still remember d day her mum came to c her" Ashnaah sae kallon Najeeb take a dan rikice, ta shiga gyada masa kai tace "ehh na tuna" Najeeb yace "to ita ta sa Ameesha tayi hka don a tunaninta Khaleel ya fi son ki kan Ameesha, ae tuni ya ma saketa ita ma" hawaye kawae Ashnaah take a sanyaye tana kallon Najeeb, ya gyada mata kai a hnkli yace "yes, wllh wllh ba Khaleel ne yyi rubutun nn ba kin ji na rantse maki fateema, ynxu hka yana can bae da lfya, tok to ur parent plss" kuka ssae Ashnaah ke yi ta ma rasa me xata ce masa, yace "shknn ni xan koma, gobe da daddare xan kuma dawowa sae ki fada min ynda kuka yi ae kin gane ko" kae kawae ta gyada masa ya xaga ya shiga motarsa ita kuma ta nufi cikin gida jikinta a sanyaye, to wae ma meyasa ta damu kanta hka bayan tasan ba son shi take ba shi ma ba sonta yake ba.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
75.....
Washegari da safe Khaleel na kwance dakin umminsa Rukayya ta
shigo wae mai gadi yace wani bako na sallama da shi a waje, ya
mike xaune yana kallonta yace "waye?" Tace "ni ma ban sani ba"
Khaleel ya dan yi shiru snn yace "Abba ya fita ne" Rukayya tace
"ehh tun safe ya fita," ko kadan Khaleel bae son haduwa da dad
din nasa, ganin wani irin shasharesa da yake yi tun bayan abinda
yyi ma Ameesha, mikewa yyi ya fita don xuwa ganin bakon nasa.
Da mmki yake kallon Al-ameen yace "kai ne bako kuma?" Al-ameen
yyi murmushi yace "yes ina jin kunyan Ummi ne, na dde ban xo
gaisheta ba" Khaleel yace "ae tasan ba garin nn kke aiki ba" Al-
ameen yace "na ta kiran nmbrka no answer, shi yasa nace mai gadi
yace kayi bako" Khaleel yace "wayar na bedroom dina, ni kuma
dakin Ummi nake, mu shiga daga ciki mana" bbu musu Al-ameen
ya bi sa har cikin gidan ya gaida Ummi snn suka nufi dakin
Khaleel, Al-ameen sae kallon abokin nasa yake ganin ynda ya
rame, Khaleel na dan kirkiran murmushi yace "let me get yhu
drink" Al-ameen yace "No No am OK wllh" Khaleel ya koma ya
xauna yana tambayarsa iyalinsa, Al-ameen yace "they're ol fyn,
wai in tambayeka Khaleel" Khaleel yace "OK ina jin ka" Al-ameen
yace "na taba maka wani laifi ne duk xaman mu tare?" Khaleel ya
wara idonsa yace "laifi kuma na me?" Al-ameen ya girgixa kai yace
"na ga ni na damu da kai, kai kam bbu alamar hkn, wae ynxu ace
ga abinda ya faru sae a bakin Umar nake ji, shi ma Najeeb ne wae
ya gaya masa, wae meyasa ka fi ba ma Najeeb din nn Value ne,
ynxu me gayen nn ya tsinana maka throughout life din ka bnda
tsiya, I c no reason to b frndin a guy like him, he is worst, wen I
say worst I mean worst kai ne baka gane ba har ynxu, dat a side
ka gaya min me ya faru, hw manage" Khaleel ya sauke ajiyar
xuciya cike da damuwa yace "wllh don't really no where to start
frnd, OK kaga ni dae nasan we went to party nd of course without
being told I knw I got drunk a can kuma ni bn ce xan sha giya ba
Najeeb ne ya kawo min, so at d end dae I found my self at home at
early dawn, nd of course I started vommittn coz idan na sha giya
over hka yake min, so ina bacci sae Najeeb ya kawo min
magunguna ya fada mata ynda xata ban idan na tashi shknn ya
tafi, ina tashi kuwa ta shigo xa ta ban maganin to a nn ta ga
takardan, kasan Allah Al-ameen ba ni ne na rubuta ba kuma
writtin dina ne jikin takardan" a sanyaye ya karashe mgnr,
kallonsa kawae Al-ameen yake da mmki, can ya sauke ajiyar
xuciya yana murmushi yace "kun taba mgnin saki da wani, misali
ko da wasa kace ae xaka saketa ko kuma makamancin hka" Khaleel
yace "not at all, nasan Ameesha ce ma, coz ita kadae ta iya
rubutuna" Al-ameen yyi murmushi yace "to kafin ka bar gida
ranan kae baka lura sa takarda cikin drawern ka ba?" Khaleel yace
"a ciki fa na dauki wristwatch dina, I saw nothin inside ae bana
barin komae ciki, sae bayan fita na aka sa ka" Al-ameen yace
"uhmm meyasa baka xargi Najeeb ba coz ka ce ya shigo ya bada
drugs a ajiye maka" Khaleel yace "Najeeb kuma, Haba Haba dats d
lst person I will suspect a duniya I knw he can never do dat 2 me"
murmushi kawae Al-ameen yake yana kallonsa yana girgixa kai,
hkn yasa Khaleel ya dan hade rae. A sanyaye Ashnaah ta karaso
falon Abbanta ta durkusa tana kallonsa, Abba ya kalleta yace "ba
kiyi bacci ba" tace "uhn ynxu xan yi" Abba yace "to ya aka yi" ta
dan yi shiru snn a hnkli ta soma mgna kanta a kasa, "Abba dama
wae ashe ba shi ya rubuta wnn takardan ba da na gani abokiyar
xama ta ce ta rubuta ta ajiye a dakin don in gani wae, Abba ba shi
ya rubuta ba wllh" kmr xata yi kuka ta karashe mgnr, da mugun
mmki Abba ke kallonta lkci daya yana murmushi yace "Haba? Ke
wa ya gaya maki?" Da sauri ta dago tace "abokinsa ne ya xo ya
gaya min, wllh Abba ba shi ne ya rubuta ba" ko kadan bata san
lkcn da Abbanta ya mike ba kawae jin saukan wani mari da ya
kusan kai ta kasa tayi, ya kuma kai mata wani marin ta mike a
gigice tana kwala ihu, da gudu momy ta fito, ita kuma tayi ta
kanta, cikin fushi momy tace "meye hka Alhaji me ta maka" Abba
yace "wllh wllh in har wancan dabbar yarinyar bata yi hnkli ba a
gidan nn sae nayi mugun ba ku mmki dama na lura da take
takenta, kuma ko bayan rae na ban yadda ki da ta sake aure ta
koma gun matsiyacin nn ba, Neva" cikin tsawa ya karashe mgnr.
Yana kai wa nn ya nufi dakinsa. Momy ta juya ta nufi dakinsu
Ashnaah ta sameta sae aikin rusa kuka take Ashfah na lallashinta,
momy ta hade rae tace "wani xancen kika xo ma da Abbanki?"
Cikin kuka tace "momy kin ga fa wae yace ba shi ne ya rubuta
takarda...." Tsawan da ya gigita ta momy ta daka Mata tana nuna
ta da dan yatsa tace "wllh idan baki kama kan ki kin shiga hnklin
ki a gidan nn ba xa ki sha mmki na, don uban ki me kike nufi, ko
kin fara hauka ne, to ki kama kan ki, kuma duk me Abban ki xae
maki wllh ko a gyalena don ba ke kadae na Haifa ba da xa ki sa
min ciwon xuciya, sha sha sha kawae" momy na kai wa nn ta juya
ta fice daga dakin.
76.....
Washegari da kyar Ashnaah ta iya tashi da asuba don yin sllh,
duk jikinta yyi mata nauyi, tana idar da sllh tayi duk abinda
tasan take yi snn ta shiga shirin makaranta, a tare suka gama
shiryawa da Ashfah snn suka sauko downstairs don yin break, ita
dae Ashnaah ko ruwan tea bata sa a bakinta ba tana dae xaune ba,
Ashfah da ta fita harkar ta ta mike ta nufi sama don dauko jakar
makarantar ta, a sanyaye Ashnaah ta bi bayanta ita ma ta dauko
Jakarta, bata bi ta kan babban wayar da Abba ya bata tun
shejaranjiya ba nn ta bar sa gaban madubi ta tafi da karamar
wayarta kawae. Falo suka nufa don gaida Abbansu da ya fito a
lkcn ba tare da ya kallesu ba ya amsa snn ya mika ma Ashfah dubu
daya da Dari biyar yace "ki dauki dubu daya ki bata Dari biyar
tunda ke ba driver xae kai ki ba" mikewa suka yi suka bar falon
bayan sun sallami momy, Ashnaah ta shiga mota a sanyaye suka
bar gidan da driver. Karfe biyu saura Ashnaah ta fito daga lecture
ta xa ta samu usman da ke jiranta tun bayan sllhr azahar a waje
ta hade rae tace "ga ni" ya dan yi shiru snn yace "har kun gama
lecture din ne" tace "kmr ya mun ga ba nace maka sae shidda ba
yau, kaga usman kawae kana son ja min mgna ne gun Abbana,
ynxu idan aka ganmu aka je aka fada masa wani mataki kke
tunanin xae dauka a kaina wnn karan, kaga idan har ka san kana
so na ni dae ka fita harkata har in gama karatu indae har so na
kke, tun da burin Abbanmu knn muyi karatu ni da yar uwata"
tana kai wa nn ta daure fuska ta rungume hannayenta, shiru yyi
kawae yana kallonta, can bayan kusan minti biyar ya sauke ajiyar
xuciya yace "to shknn Fateema, I've heard, Allah sa hkn ne mafi
alkhairi i will do as u said, I will wait" sallama yyi mata ya nufi
motarsa ta bi sa sa harara tare sa jan tsaki ta bar wajen. Da
daddare Ashnaah tayi sneakin ta fito ta samu Najeeb dake jiranta a
waje kmr ynda mai gadi ya kirata ya sanar da ita, yana ganinta
yyi murmushi yace "welcm, any good news," girgixa masa kai tayi
tana kkrin danne kukan da ke neman kubce mata tace "nobody is
willing to blive dat, they ol tot it's a lie" kasa daurewa tayi ta
fashe da kukan, Najeeb yyi shiru yana kallonta snn a hnkli yace
"dama kina son Khaleel ashe Fateema, shine kike kuma neman
hanyar da xae sake ki...." Da sauri ta goge hawayenta ta katse sa
fuskarta a daure tace "hka nace maka, har shi yana da abun da xa
a so shi, kai na kawae nake ji ma da aka mayar dani baxawara at
my early age" tana kai wa nn ta juya da sauri ta bar wajen, ya
shiga kiranta da sauri amma tuni ta shige gate yace "shit", gidansu
Khaleel ya nufa, Khaleel ya mike da sauri ganinsa yace "ya kuka
yi" Najeeb yace "no gud news, tsohonta bae saurareta ba hka ma
mum din, she was so depressed, cryn cryn" a hnkli Khaleel yace "re
yhu serious" Najeeb yace "wllh kuwa, wae ku da kunsan kuna son
junanku ku ke ta wani ja ma juna aji aka ki xaman lfya kullum
cikin fada ku ke, to ynxu da kuka rasa juna ae kun ga value din
junan ku," A sanyaye Khaleel yace "ni ne na kamu da sonta da
ddewa but ita nasan bata so na, bna ma gabanta u knw" Najeeb ya
xaro ido yace "in ji wa bata sonka, kullum naje bata da aiki sae na
kuka, is she just cryn for cryn sake or wat, kuma da bata son ka da
wllh baxata saurareni ba bare har ta yi ma iyayenta magana, duk
kun kamu da son juna kuna can kuna hauka baku sani ba, nafi
ma tausaya mata wllh, don ita yarinya ce ssae gashi xuciyarta xae
wahala" dariya Najeeb ke yi har da dafe kai yace "amma so bae ma
Khaleel da Fateema adalci ba, ya kai su ya Baro ba tare da sun
lura ba" kallonsa kawae Khaleel ke yi har ya gaji don kansa ya
daina dariyan, a hnkli Khaleel yace "it seems funny ryt" Najeeb
yace "not at all, ynxu ya kke ganin xa ayi kuma, am alwayz dia 2
help yhu frnd" Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace "ganinta kawae
nake son yi" Najeeb yace "dats vry simple kawae ka je gidan nasu
kayi ma mai gadi mgna nn da nn xae kirata ta fito hka muke yi" a
hnkli Khaleel yace "baxa ta fito ba idan ta san nine" Najeeb yace
"says hu? Ynda take nemanka ido rufen nn me xae hanata fitowa
kawae kai dae ka je, kuma ai ba cewa xaka yi kai bne, kawae Ca
xaka yi ayi maka sallama da ita nn take xae kirata kuma xata yi
tunanin ni ne ta fito " Khaleel yyi shiru snn ya dafe kansa yace "to
Allah yasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 29