An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
1.....
A hankali yake cin fruit Salad din dake gabansa kansa a sunkuye yana murmushin nan nasa mae kyau da ya kai ga har ana iya ganin dimples dinsa, ya girgixa kai snn ya dago yana kallon matashiyar matar dake xaune kan kujerar dake kallon nasa fuskarta a daure ta kafa masa ido tana kallo, murmushi ya kuma yi mai sauti xae yi magana ta rigasa a fusace tace "ohh ga mahaukaciya na magana ko Khaleel, ni ce ma na xama abun dariyarka knn" ya dan marairaice ya ajiye fork din hannunsa yace "ba hka bane Mum, kiyi hkuri," ya dan shafa kansa da damuwa yace "kinsan komai fa lkci ne mum, kawae su Ummi da Abba sun kasa gane hkn ne, sun ki fahimtar abinda nake nufi am just bored of all dis...." shafa kansa ya kuma yi har lkcn fuskarsa na dauke da damuwa yana kallon Small mum din tasa, sallamar da aka yi yasa duk suka maida hankalinsu ga bakin kofa tare da amsa sallamar, mikewa mum tayi ganin baki tayi da fara'arta tana masu sannu da xuwa suka karaso cikin falon aka shiga gaggaisawa, Khaleel ya mike yana kallon Small mum din tasa yace "to mumy sae na kuma dawowa ko xuwa gobe" tace "a'a ka dae dawo xuwa anjima da daddare bamu gama magana ba" yyi murmushi yace "in'sha Allah mum" bowl din fruit Salad din da ya ci ya dauka xae kai kitchen tace "a'a ka bar shi kawae xa a kwashe" yace "No bari in kai mum" ya nufi kitchen da bowl din ya ajiya snn ya fito yyi ma bakin sallama ya fice daga falon yana kallon agogon hannunsa, gun motarsa ya nufa yana tafe yana satan kallon wata bishiya dake dauke da fararen kujerun roba da table a karkashinta ya ga ko wa inda ya gani daxu gurin suna nan ko sun bar wajen, suna xaune ko har lkcn su biyu kmr ynda ya samesu da ya shigo, sae dae wnn karan ba hira suke ba daya na danna wayarta daya kuma na waya ne, hada ido suka yi da warce ke danna waya don ita ma satan kallon nasa take, ya dauke kansa da sauri, ita ko kallon me wayar tayi tana 'yar dariya tace "dubi gantalalle neman gaisuwata yake" da sauri tayi pretend tace "lahh Ya Khaleel yaushe ka xo" juyawa yyi yana kallonta duk da yasan taga shigowarsa daxu bbu yabo bbu fallasa yace "kin ban sako ne" ta dan yatsine fuska tace "No kawae nayi mamakin ganin ka a gidanmu ne yau, coz ba saba xuwa kayi ba, any way ina yini" ya watsa mata wani mugun kallo ya bude motarsa ya shige yyi horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, dariya ta saki tana kallon kawarta da ta kasa ci gaba da wayan da take ta rakasa da kallo har ta daina hango motarsa mai gadi ya rufe gate din, can ta maida kallonta ga kawarta dake ta faman dariya ta sauke ajiyar xuciya tace "gaskiya gayen nn ya hadu Meenah, ni dae hka kawae naji yana burgeni," Meenah tayi ma kawarta ta wani irin kallo tace "shi Khaleel din ke burgeki? Tabdi da kinsan halinsa da baxa ki ce komai ba wllh! wnn mugun dan rainin hankalin, ae ni tun da na taso kallon arziki bae taba hada mu ba kin dae ga dan uwana ne, ki bari xan baki lbrin ko waye shi salma, kin taba ganin wani cousin dina ya shigo gidan nn ban gaishesa ba, kuma kin dae san ni da son xumunci Salma, tunda har ki ka ga Khaleel ya shigo gidanmu ban gaida sa ba na dauke kai kiyi shiru kawae" Salma tace "haba abun ya ban mmki wllh, to Allah shi kyauta, ni dae mu shiga ciki in yi ma Momy sallama in kama hanyar gida kafin Mama ta fara kirana" Meenah tace "haba tun da wuri hka, to ki bari bakinta su tafi mana, nasan ba dde wa xa su yi ba" Salma ta harare ta tace "lallai kam da yake ke a gidan ku kike ba shiyasa xaki ce in jira bakin da ban san ranan tafiyarsu ba su wuce" mikewa salma tayi ta nufi cikin gida, Meenah ta mike tana dariya ta bita suka shiga falon a tare. Barkan Ku da Sallah sisterz.
[10/14, 3:25 PM] +234 806 484 7850: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 2...... Karfe tara da rabi na dare Khaleel ya gama parkin din motarsa a parkin space din dake cikin gidansu dake G.R.A kaduna, ya bude motar ya fito yana kallon motar dad dinsa ko ba a gaya masa ba yasan ya dawo, ya nufi balconyn da xae sada sa da kofar shiga babban falon gidan, can ciki yyi sallama ya shiga falon ya tarda kanwarsa Rukayya kwance tana kallo, ta mike xaune ganinsa tace "sannu da dawowa ya Khaleel" ba tare da ya kalleta ba yace "sannu" snn ya nufi stairs, dad dinsa suka kusan cin karo da ya ja baya da sauri tare da dan ritsinawa ya gaishesa, bbu yabo bbu fallasa mahaifin nasa ya amsa snn yace "ina nemanka a falona" dad dinsa na fadin hka ya juya ya koma xuwa falonsa, Khaleel ya share wata xufa dake keto masa a goshi ya shafa kansa snn ya shiga haurawa saman a sanyaye, dakin mum dinsa ya nufa tana xaune gefen gadonta tana waya, mai aiki na yayyanka mata fruits a faranti, ya nemi gefenta ya xauna har ta gama, tana kallonsa tace "sae ynxu son" ya dan marairaice mata yace "ummi don Allah ki raka ni gun abba wae yana kirana" tayi masa wani irin kallo tace "sae na raka ka? Ashe ko baxa ka je ba" ya ciro handkerchief ya share fuskarsa bae ce komai ba ya mike ya fita daga dakin ya nufi falon Abbansa, xaune ya tarda Abban nasa yana shan coffee, ya xauna kasan carpet din dake tsakiyar falon ba tare da ya kallesa ba yace "Abba gani"Abban nasa ya ajiya kofin hannunsa yace "ka gama play din hide nd seek din dani Khaleel" Khaleel ya dan yi murmushi ba tare da ya shirya ba yace "wllh ba hka bane Abba aiki ne yyi min yawa a clinic" ummi ce ta turo kofan falon ta shigo, Khaleel yaji ddin ganinta ta nemi gefen mai gidan nata ta xauna.
[10/14, 3:26 PM] +234 806 484 7850: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 3..... A hankali Khaleel ya daga kai yana kallon Abbansa ganin shirun yyi yawa, kallonsa ya ga Abba na yi, hkn yasa ya dukar da kansa kuma, Abba ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace "me kke nufi da mu Khaleel?" kasa cewa komai Khaleel yyi har lkcin kansa na kasa, Abba ya maida kallonsa ga TVn dake ta aiki a falon yace "shknn, dat clearly shows dat raina mu kawae kayi, don hka ni na yanke shawarar hada ka da either Meenah ko Maryam, ka je kayi shawara ka xabi daya cikinsu, nd bet me, dat wont take a lng tym, ka tashi ka bamu waje" kasa ko da kwakkwaran Motsi Khaleel yyi daga inda yake a durkushe, komae nasa ya tsaya cak, da kyar ya shiga share xufar dake keto masa a fuska ya daga kai yana kallon Mum dinsa da ko kadan bae ga alaman hkn ya dameta ba, sunayen wa inda Abba ya ambato masa suka shiga yawo a kansa, wae Meenah ko Maryam, ji yyi kmr ya saka ma iyayen nasa kuka, Muryar Abba ya ji a tsakiyar kansa yana cewa "nace ka tashi ka bamu waje" dago kansa yyi da sauri ya marairaice murya yana kallon iyayen nasa yace "don Allah don annabi kayi hkuri Abba wllh ni duk bana son su, na maka alkawarin nn da wata daya kacal xan gabato maku da matar da xan aura plss Abbana consider me, nasan na maku laifi" ya karashe mgnr kmr xae yi kuka, Abba na masa mugun kallo yace "ka raina ma kan ka hankali ba mu ba, common get out my frnd" juyawa yyi da sauri yana kallon Mum dinsa, idonsa ya kada yyi jajur cikin rawan murya ya fara mata mgna "ummi don Allah ki sa baki...." harara ta watsa masa tace "da knn ba ynxu ba" dafe kansa yyi xuciyarsa na tafarfasa, ae shi da ya aure wa in nan yaran da abba ya ambato masa gwara ya mutu ba aure, dat aside ma shi ko kadan bae son auren xumunci kallon arxiki baya hada sa da yaran yan uwan iyayensa gaba daya duk baya sake masu, goge Fuskarsa yyi da handkerchief a nutse yana kallon Abbansa ya fara magana "Abba i knw na maku laifi, plss ku yi hkuri ku yafe min, na kuma maku alkawarin nan da wata daya xan....." tsawa Abba ya daka masa yace "Enough Malam, tashi ka ban waje" Khaleel bae kuma cewa komai ba ya mike da kyar ya juya ya fice daga falon. Karfe sha daya da rabi Ummi ta shigo dakin Khaleel, yana kwance ya kafa ma Ac ido da ganinsa kasan abun duniya ya ishesa, ummi ta karaso ta xauna gefensa tana kallonsa ya mike xaune yace "ummina kin ga abinda Abba ke shirin min ko" Ummi tace "to ae kai ka ja ma kan ka Khaleel, tun yaushe muke bin ka kana kakkaucewa ka maida mu yara" komawa yyi ya kwanta bae kuma cewa komai ba, sarai tasan halin dan nata da abun da ke iya faruwa kafin gobe in ya kwana cikin tashin hankalin nn da yake ciki, hkn yasa tace "ka kwantar da hankalinka son, na shawo mana kan Abba amma fa da kyar, ya kuma baka wata dayan da kace don hka kafin lkcn ka gabato matar, kar ka kuma ban kunya kasan ni bana son abinda xae taba min kai son" mikewa Khaleel yyi ya rungume ummin tasa cike da jin ddi ya shiga mata godiya, ta shafa kansa tana murmushi ta sa masa albarka snn ta mike yyi mata sae da safe ta fita xuwa dakinta. Kasa bacci Khaleel yyi daren ranan duk da hankalinsa ya kwanta, amma damuwarsa daya ta inda xae fara nemo matar da xae gabato ma parent dinsa ynxu, ta ina xae fara wnn jan aikin, tunanin hkn na mugun tada masa hankali.
[10/14, 3:26 PM] +234 806 484 7850: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
4.....
. A hanxarce Khaleel ya gama shirinsa cikin bakar suit da wando da farar T-Shirt sae neck tie ash colour, dakin Umminsa ya nufa ya sameta xaune gaban madubi tana gyara gashinta, yace "ummina xan tafi" Ummi na kallonsa tace "baka yi breakfast ba" ya kalli agogon hannunsa yace "idan naje office xan yi ummi, sae na fara xuwa cikin gari an duba min motata" Ummi tace "ba john ya kai shekaranjiya an gyara ba" ya girgixa mata kai yace "a'a it's still nt ok, xan je da kaina ynxu" Ummi tace "ikon Allah, to shi kadae ne motar ka Khaleel ka dauki wata mana in ya so ko anjima sae john ya maidata" yace "No xan tafi da ita ynxu Ummi na fi son in je da kai na" Ummi tace "to Allah ya tsare" ya nufi kofa xae fita yace "Ameen ummina sae na dawo" tace "to a dawo lfya" a stairs suka hadu da Rukayya tace "yaya baka yi breakfast ba" yace "eh sauri nake sae na je office" tace "to yaya ka ajiye ni ni ma sch xan tafi ynxu" yace "cikin gari na nufa ynxu" yana kai wa nn ya sauka ya nufi kofar fita daga falon, ta bi sa da kallo snn ta dan tabe baki ta nufi dakin ummi. Karfe takwas da kusan rabi Khaleel ya iso cikin gari, ya mika ma engineers din motarsa snn ya nemi kujerah ya xauna tare da fiddo wayarsa yana dannawa to while away time. Tafe take tana bincike jakar dake sakale a kafadarta alaman tana neman abu, cak ta tsaya ta wara ido hade da bude baki ta saki salati tana kallon cikin jakar, hkn ya ja hankalin Khaleel dake xaune har lkcn yana danna waya, juyawa tayi ta bi layin da ta fito daga da kallo, can ta dan tabe baki hade da tsaki ta xuge jakar ta kuma sakala sa a kafadarta da kyau snn ta ci gaba da tafiyarta da takunta mai jan hankali, sanye take da riga da skirt ta atamfa orange colour mae ratsin ash da brown, hijabin jikinta ma orange ne ya wuce gwiwa da kadan, hka ma takalmin kafarta orange ne, jakar hannunta kadae ne brown, da ganinta kasan makaranta xa ta, Khaleel ya bi ta da kallo har ta isa bakin titi snn yyi tsaki ya ci gaba da duba wayarsa, tsaye tayi bakin titin alamar tana jiran abun hawa, ba a Kuma dau lkci ba ta samu ta hau suka bar gurin, kmr ance Khaleel ya juya ya ga wasu fararen takardu a kasa dai dai inda ta tsaya, ya mike ya nufi gurin ya duka ya kwashe takardun har uku yana kallonsu, reciept ya gani da admission letter sae handout na physics, ya girgixa kai hade da tsaki da kmr xae wurgar da su sae kuma ya fasa ya linkesu ya koma ya xauna da xumar ya ba kanikawan idan sun ganta su bata, cikin minti sha biyar aka gama yi ma motarsa abinda ya kamata, ya basu kudi duk da basu bukaci hkn ba snn ya shige motarsa ya kama hanyar office cikin hanxari don ya makara. Tana xaune a class ta sa Chemistry text buk dinta a gaba kmr me karatu taji an rankwasheta, ta juya da sauri kuma a fusace don taga waye, ta wani hade rae tace "bana son irin wasan nn Aisha" Aisha ta xauna tace "Allah ya baki hkuri" sauran kawayen nata ma xaunawa suka yi suna kallonta, Ummi tace "wae me ya faru ne Ashnaah yau duk you re nt ur self" tayi masu wani irin kallo tace "dole ku ce am nt my self tunda ba reciept dinku bane ya fadi" Maryam tace "au wae shi yasa kika xama hka, ba mun ce maki xaki gani ba kila ma a gida kika xubar" tsaki Ashnaah tayi tace "eh naji xan gani a gida ku rabu dani" Bilkisu ta mike ta bar wajen Nafisa ta bi bayanta, Ashnaah ta bi su da harara, snn tace "bari in ta murna na xubar da reciept dina" tana kai wa nn ta mike ita ma ta fice daga class din, Ummi tace "da'alla mu rabu da ita mu muka xubar mata" mikewa su ma suka yi suka bar class din.
[10/14, 3:26 PM] +234 806 484 7850: ~Dr Khaleel By Khaleesat Haiydar
5.....
Khaleel ne xaune office dinsa ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa lumshe, maganganun umminsa ne ke masa yawo a ka, tunanin ta Inda xae fara neman mata kawae yake, ko kadan shi kam matan kaduna ba su masa ba, basa burgesa, bude office dinsa da aka yi ya sa ya gyara xamansa da sauri ya bude ido ya ga wani isasshen ne xae shigo masa office ba knocking, ta rufe kofar bayan ta shigo, ya wani hade rae yana kallonta, da ma yasan baxae wuce ita ba, bae jira jin me xata ce ba a nutse yace "get out" ta dan marairaice masa tace "ka ga fa files na kawo maka Sir" ya kuma hade rae yace "ki bar min office nace" ajiye files din hannunta tayi nn da nn idonta ya kada, ta juya xata fita, murya can kasa yace "Ameesha" ta juya tana kallonsa sae ga hawaye, ya mike tsaye ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta, sae ta sakar masa kuka, dafa kafadarta yyi ya dago kanta yana goge mata hawayen idonta a hankali yace "am sorry" gyada masa kai tayi hawaye na ci gaba da xuba a fuskarta tace "Abbana yace in kawo maka files" tana fadin haka ta juya ta Fita daga office din tare da kullo masa kofarsa, komawa yyi ya xauna ya lumshe idonsa duk abun duniya sun ishesa. Bayan minti goma da fitan Ameesha aka kwankwasa masa kofa, ya tura file din gabansa bayan kmr minti daya yace "come in" wata nurse ta shigo rike da file a hannunta ta gaishesa cike da ladabi snn tace "Dr patient xaka duba, kuma Emergency ne, yace "don me xaki kawo min baki kai ma Dr Umar ba, ni din engine ne?" Tace "No sir suna Theatre ne, Oga ne yace in kawo maka" tsaki yyi ta ajiye masa file din ta Fita, ba a dau lkci ba nurse din ta dawo da patient din ya daga kai yana kallon yarinyar da baxa ta wuce sha takwas ba, bbu abinda take sae kuka tana rike da cikinta, ya dan yi tsaki Mara sauti ya jawo file dinta ya bude yana dubawa, nurse din ta juya ta Fita, yace "ke malama ba kuka xa ki min ba amsa min duk tambayoyina xa ki," shiru tayi tana goge hawayen fuskarta tana kallonsa, jin ynda tayi shiru lkci daya yasa ya daga kai yana kallonta, ta sunkuyar da kanta da sauri, cire farin glass din idonsa yyi ya sake fuska ya dan sassauta murya yace "daurewa xa ki yi Zeenat and tel me wat ur prblm, look at me" ta daga idonta da ya rine don kuka tana kallonsa, ya sakar mata murmushi snn ya shiga yi mata tambayoyi tana basa amsa. Karfe hudu da rabi Ashnaah ta shigo gida ta jefar da Jakarta nan bakin kofa ba tare da ta kalli inna dake tuka tuwo tsakar gidan ba ta Shige falo, inna ta tabe baki tace "aniyar ki ta bi ki yarinya, kuma ba ni kika wurga ma jaka ba, Adamu kika jefa ma" Ashnaah ta fito tace "kin fara ko inna ni dae fa ki dinga kyaleni, kina ganin na batar da takardun makaranta na gaba daya duk ban gani ba" inna ta mike da sauri ta dafe kirjinta tace "takardun makarantar ki?" Ashnaah kmr xata yi kuka tace "eh mana" inna tace "barawo ne ya sace su ko ya aka yi?" Ashnaah tace "eh mana, kuma gashi ni ynxu bn san me xan ce a makaranta ba, ga kuma Abba ma ban san me xan ce masa ba" inna tace "to wa ke ta wani Abba can, ynxu kawae gobe in shirya in rakaki makarantar in yi ma masu makarantar bayani," Ashnaah ta xaro ido ta kwashe da dariya tace "Allah ya tsareni, ance maki makarantar ta yara ce kuma snn ba a bari tsofaffi su shiga, ynxu dae abinda nake so dake kawae ke ce xaki ce ma Abba kina kwalema sae kika bude jakar makaranta ta kiga takardu sun yi yawa sae kika kwashe kika xubar kuma masu kwasan shara suka xo suka xubar kinga ae baxae iya cewa komae ba sae ya tafi makaranta yasa a min sabo," inna tace "ae wnn abu me sauki ne Allah ya kawo sa" Ashnaah tayi murmushi tace "shi yasa nake son ki inna."
[10/14, 3:26 PM] +234 806 484 7850: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
6.....
Khaleel ya ajiye pen din hannunsa yana kallon mahaifin Zeenah dake xaune gabansa yace "ka kwantar da hankalin ka sir, in'sha Allah ur dota will b alryt but nt until yhu give her wat her heart desires" Alhajin yace "nt at all, ni ban tada hankali na ba ae, just dat aure ne dae sae na mata ko ta ki ko ta so, sae dae in mutuwa tayi" Khaleel yyi shiru yana kallonsa, can dae yace "duk da halin da take cikin ynxu Alhaji" Alhajin yace "kwarae kuwa" yana kai wa nn ya mike ya fice yana cewa "to in ta mutun ma uwarta dake xugata tayi asara ba ni ba" Murmushi Khaleel yyi ya daga kafada ya ci gaba da abinda yake. Karfe shidda saura na yamma Khaleel ya rufe office dinsa rike da suit dinsa ya nufi ward din da patient din tasa take, tana xaune tayi jigum, wata matashiyar mata na yanka mata fruit ya karaso cikin dakin yana kallonta yace ya jikin?" Kai kawae ta gyada masa, matar dake yanka mata fruits tace "sae dae fa kirjin nn tace bae daina ba, kan ma ynxu take ce min ya fara mata ciwo," yace "ae dama ba lkci daya ciwon kirjin xae daina ba, anjima xa a shigo mata allura a kuma bata drugs, Allah ya sauwake" yana kai wa nn ya fice daga dakin, last floor ya haura ya nufi wani office, ya kwankwasa kofa aka masa ixinin shigo wa ya bude kofar ya shiga da sallamarsa, yana xaune kan daya daga lafiyayyun kujerun office dinsa rike da jarida a hannu, Ameesha kuma na xaune kan office chair dinsa tana danna laptop, Khaleel ya gaishesa cike da ladabi, ya amsa tare da cewa "yhu re off knn" Khaleel yace "eh dad amma kila in dawo can da daddare," juyawa yyi yana kallon Ameesha yace "baki tafi gida ba dama" Ameesha ta rufe laptop din gabanta tace "dama kai nake jira Dr, drop me" Dakewa Khaleel yyi tare da kirkiro murmushi yace "ni cikin gari na nufa ynxu driver ya kai ki kawae" kmr xatayi kuka tace "plss mana" bata jira me xae ce ba ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 29