Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya mike xaune da kyar ya rike kansa da ke juya masa. 104..... Mikewa yyi jikinsa a mace ganin har lkcn aman bae tsaya mata ba ya nufi bathroom din, dukawa yyi ya dafata ta turasa da sauri alamar ya kyaleta, komawa gefe yyi yana kallonta har ta gama ta mike ta wanke bakinta da mouth freshner ta fice ta bar masa aman a gurin. Gyara gurin ya shiga yi har ya gama snn ya hada ruwan wanka ko xae ji karfi a jikinsa, bakinsa ya soma wankewa snn yyi wanka ya fito daure da towel a waist dinsa, xaune ya sameta ta jingina jikin gado, suna hada ido ta dauke kanta da sauri don tun da suke bae taba fitowa hka daga wanka gabanta ba, kwanciya tayi ta shige cikin bargo ta rufe har kanta, ya gama sa sleepn robe dinsa yana kallon empty kwalaban da ta ajiye masa gefen fridge, dauke kai yyi da sauri don ko ganinsu bae son yi, agogo ya kalla yaga biyu saura, ya kashe wutan dakin ya kwanta yana kallonta, a hnkli ya birgina inda take ya cire bargon jikinta gaba daya, ta shiga turasa alamar ya rabu da ita, ya rungumeta a hnkli yace "Haba bbyna, am so srry plss" kuka ta sakar masa ya shiga lallashinta ta gaji don kanta tayi shiru, a sanyaye yace "wllh bana kara shan any Alcoholic drink wife, kin ma ga ya fitar min a kai ynxu, da na sha xan yi amae" shiru tayi bata ce masa komae ba, shi ma bae kuma cewa komae ba duk jikinsa yyi sanyi, a hnkli ta xame jikinta daga nashi ta juya masa baya. Washegari karfe goma suka gama shirin komawa gida, falo Ashnaah ta samu dad xaune ta durkusa ta gaishesa snn tace xa su tafi, dad yace "da wuri hka xa ku tafi" tayi murmushi bata ce komae ba, ya mike yace "to ina xuwa" sama ya nufa dae dae stairs suka hadu da Khaleel da ke sakkowa, Khaleel bae bari sun hada ido ba ya basa hanya da sauri, a sanyaye ya karasa sakkowa downstairs yana kallon Ashnaah yace "mu tafi" tace "Abba yace in jira shi" bae ce mata komae ba ya fita falon don yasan ko ya tsaya yi masa sallama ma ba tanka sa xae yi ba tunda bae amsa gaisuwarsa daxu ba, Dad ya sakko rike da kudi ya mika ma Ashnaah yace "to gashi ki siya duk abinda kike so" kasa kin amsa tayi ta karba a kunyace tayi masa gdya ta mike yyi mata Allah ya kiyaye hanya snn ta fita don sun yi sallama da Ummi, xaune ta tarda Khaleel cikin mota yana jiranta, tana shiga motar ya tada mai gadi ya bude masa gate ya fita. Karfe sha daya saura suka isa gida, Khaleel ya juya yana kallon Ashnaah yace "ki shiga ciki wife, xan je siyo maki magunguna kafin su kare daga nn sae in siyo abinci, me kike son ci?" Ashnaah ta girgixa masa kai tace "ba komae, xan sha kunun da Ummi tayi min" kudin hannunta ta mika masa tace "ga shi Abba ya bani" yyi murmushi yace "to kin gode wife" tace "to ka karba mana" ya girgixa kai yace "ae ke ya ba ma wife ki rike kayan ki kawae" bata rae tayi har lkcn tana mika masa, yyi murmushi yace "to ki shiga sae na dawo ki ban" ba musu ta bude motar ta fita ya bi ta da kallo har ta shiga gidan, snn ya juya ya fice da motar, kwanciya Ashnaah tayi kan kujera a falo, wayarta taji yana vibrate ta bude jakar ta ciro da sauri ta ga Ashfah ce ke kiranta, daga kiran tayi Ashfah tace "sister ba ki turo address din ba kuma, ya jikin?" Ashnaah tace "lah gashi ban tambayesa ba kuma baya nn, Bari in tambayi mai gadi," da sauri ta fita ta tambayi mai gadi address din layin ya bata snn ta gaya ma yar uwartata, Ashfah tace to ga ta nn xuwa. Cikin minti ashirin Ashfah ta iso gidan, Ashnaah ta ji ddin ganinta ssae ta rungumeta tana tambayarta momynta fa, Ashfah ta ajiye ledan abincin hannunta tace "ta ce a gaishe ki" a sanyaye Ashnaah tace "Abba ya dawo?" Girgixa kai Ashfah tayi, Ashnaah tace "to inna fa" Ashfah tace "tana nn" shiru Ashnaah tayi bata ce komae ba, can ta mike tana kallon yar uwartata tace "mu tafi sama" mikewa Ashfah tayi ta bi bayanta ta kai ta dakin da take. Hira suka dinga yi har kusan karfe daya suka yi sllh, Ashnaah da kasala da tashin xuciya ya isheta tace ma yar uwarta bari ta dan kwanta don ta gaji, tana kwanciya nn da nn bacci ya dauketa. Ashfah bata xauna ba ta shiga gyara ko ina na gidan, tana kitchen tana wanke dan kwanukan da ta gani Khaleel da Najeeb suka shigo gidan, kin fitowa tayi daga kitchen din har ya suka shigo falon da mmki Khaleel ke kallon ko ina na falon, bbu abinda ke tashi sae kamshi Mae ddi, ya kalli kofar kitchen jin karan ruwa ya nufi kitchen din da sauri, daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta da mmki ganin ynda tayi kwalliya, ko kadan bae lura ba Ashnaah ba ce don mugun kamar da suke, Ashfah taki juyowa jin bae ce komae ba ta ci gaba da wanke wankenta, karasowa cikin kitchen din yyi yana murmushi yace "waww wife duk ke kika yi wnn aikin," da sauri Ashfah ta juya ganin ya nufota xae rungumeta tace "ba ita bace" cak ya tsaya yana kallonta, ta dauke kanta tana ci gaba da dauraye plates din hannunta tace "ina yini" Khaleel ya koma baya da sauri ya fara kame kame "ohh srry sister, lfya lau, sannu da aiki, yaushe kika xo" ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 105..... Ba tare da Ashfah ta juyo ba tace "Yauwa ngd" juyawa Khaleel yyi ya fita daga kitchen din da sauri ya koma falo, xaune ya tarda Najeeb ya kunna Tv yana canxa tasha hnkli kwance uwa falonsa, Najeeb ya daga kai yana kallonsa yace "kace jikin Madam yyi kyau knn tun da har ta fara aiki" kai kawae Khaleel ya gyada masa ya dauki ledan da ya shigo da ya nufi sama, Ashnaah ta fito daga bathroom knn ya shigo dakin, da ganinta kasan amae tayi, bata ko kallesa ba tayi kwanciyarta kan gado ya karaso ya xauna gefenta a hnkli yace "sannu wife" bata tanka sa ba sae ma juya masa baya da tayi, yace "ashe twin sis ta xo, tot ke ce a kitchen sae ta ce min ba ke bace" nn ma dae Ashnaah bata ce masa komae ba, shiru yyi bae kuma cewa komae ba, ta juya ta hade rae tana kallonsa tace "daga ce min ynxun nn xaka dawo shine xa kayi tafiyarka ka barni ni kadae a gida koh" ta karashe mgnr kmr xata yi kuka, Khaleel yace "ohhw am srry bbyna, Najeeb ne ya bata min lkci, but ae twin sis ta xo ta taya min ke xama toh" harara ta galla masa tace "ba ynxun nn ta shigo ba" yyi murmushi ya jawota jikinsa ya lumshe ido a hnkli yace "am so srry wife" lamo tayi bata ce komae ba. Ashfah na gama gyara kitchen din ta fito falo da nufin xuwa ta ce ma yar uwarta xata tafi, kallo daya tayi ma Najeeb da ke xaune falon ta dauke kai lkci daya ta ganesa, yana kallonta yace "ya jikin Fateema" bbu yabo bbu fallasa Ashfah tace "tana sama" bata jira ta kuma jin me xae ce ba ta nufi saman da sauri, Najeeb ya bi ta da kallo da mmki ya mike tsaye da sauri yace "wait! wait" amma tuni ta haura sama, kwankwasa kofar dakin tayi tare da yin sallama, Khaleel ya mike tsaye tare da amsa mata sallaman, Ashnaah tace "ki shigo mana sister" Ashfah ta turo kofan ta shigo tace "sister bbu wani abun da xa ayi maki koh? Xan tafi ne" Ashnaah ta hade rae kmr me shirin kuka tace "xa ki tafi fa kika ce Ashfah, yaushe kika xo" Ashfah tace "kin ga fa ina da lecture xuwa anjima" Ashnaah tace "ashe dama ba kwana xa ki min ba" Ashfah ta xaro ido tace "kwana kuma, ki bari nxt tym sis, ina da class yau" Khaleel yace "Haba sister ki kwana mana sae ki tafi gobe mana" Ashfah ta sunkuyar da kai tace "ka ga fa ba muyi da momy xan kwana ba wllh" Ashnaah tace "dan ara min wayar ka in kirata ni in gaya mata" Khaleel ya mika mata ta karba ta kira momynsu, momy na dagawa ta marairaice kmr xata yi kuka tace "Momy don Allah ki ce Ashfah ta kwana gobe sae ta tafi kin ga wae fa ynxu xata wuce" momy tace "Kinga Abbanku bae san ta fita ba kuma gobe xae dawo ki bari next tym kin ji" Ashnaah ta fashe da kuka tace "momy ba dawowa xata kuma yi ba fa nasani" Momy ta dan yi shiru snn tace "toh shknn amma gobe da sassafe ta taho kar ya dawo ya ga bata nn" Ashnaah tayi murmushin jin ddi tana share hawayenta tace "to momy ngdd" ta katse wayar ta juya tana hararan Ashfah ta ja tsaki ta mike ta fice daga dakin don xuwa ta dauko cup din da xata Debi kunu ta sha a kitchen, Khaleel yyi murmushi yana kallon Ashfah da mood dinta ya canxa lkci daya, yace "kiyi hkuri sister, yau da gobe ae duk daya ne koh" murmushi ta kirkira bata ce komae ba, kasa ci gaba da kallonta yyi don sae yake ganinta kmr Ashnaah don kmrsu tayi yawa, juyawa yyi da sauri kmr wnda ya tuna abu ya dauki hijab din Ashnaah ya bi ta da shi yana kiranta, Ashnaah da har ta kai stairs ta juya tana kallonsa ya mika mata yace "Najeeb na falo" karba tayi ta sa ta fita, tsaye ta tarda Najeeb har lkcn ya kasa xama idonsa a kan stairs, yana ganinta ya nufe ta da sauri yace "pls fateema kice twin sistern ki ta saurareni taki saurarata" Ashnaah tayi dariya tace "wae Ashfah, ae bata kula samari nn da ka ganta" Najeeb ya marairaice mata yace "Haba fateema kar muyi hka da ke mana, help me plss" Ashnaah tace "wllh da gske nake Ashfah bata kula saurayi," da mmki Najeeb yace "to sbda me?" Ashnaah tace "sbda Abbanmu ya hana, karatu ya fi so" Najeeb ya kasa daina mata kallon mmki yace "to ke ya aka yi har kika kula Khaleel ku ka yi aure, ko ita kadae ya sa ma dokar bn da ke?" Ashnaah tayi shiru tana kallonsa lkci daya jikinta yyi sanyi hawaye ya shiga taruwa idonta a xuciyarta tace "sbda bna jin mgnrsa ni" bude baki tayi xata gaya masa abinda ke ranta suka ji muryar Khaleel a bayansu, "enuf of those silly questns Najeeb" juyawa Ashnaah tayi ta nufi kitchen da sauri, Khaleel ya karaso kusa da Najeeb yace "wnn wace irin tambaya ce kke yi Najeeb" Najeeb da ganin Ashfah ya sa ya rude kwata kwata ya mance abubuwan da ke kasa ya fara kame kame, tsaki Khaleel yyi ya juya ya nufi kitchen, kuka ya tarar Ashnaah ke yi, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya rungumeta ta kuma fashewa da wani Sabon kukan, sae da ya tabbatar tayi shiru snn ya barta ta fita daga kitchen din shima ya fito, Najeeb ya nufo sa da sauri yace "am so srry frnd wllh hnklina ya gushe ne, I get I wasn't supposed to bring up dis issue" Khaleel yace "its OK" Najeeb ya dan yi shiru snn yace "which help wil yhu render me in here plss Khaleel, I am blindly in love, wllh tsakanina da Allah nake son yar uwar matarka kuma da aure" Khaleel ya dan yi murmushi don tun da yake da Najeeb bae taba jin yace yana son mace da aure ba, yana shafa kansa yace "ni kuma a su wa a ynxu? Ita yarinyar xan ma mgna ko iyayenta da aka goga min kashin kaxa a gun su xan je in sa ma, ko kuma iyayena da ke fushi da ni har yau akan abinda bn aikata ba xan tura su yi ma iyayenta mgna cewar abokina na son yar uwar matata? Tell me hw dis is goin to be frnd" shiru Najeeb yyi yana kallon Khaleel lkci daya jikinsa yyi sanyi a xuciyarsa yace "but I am d cause of all dis," ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 106..... Juyawa Khaleel yyi ya bar sa wajen a tsaye ya koma kan kujera ya xauna, Najeeb ya runtse ido ya bude yana girgixa kai lkci daya ya share gumin da ke karyo masa ya dawo gefen Khaleel yana kallonsa boldly yace "wat if I claim being the one dat wrote dat divorce content?" Khaleel ya dago ido yana kallonsa, can yyi tsaki ya girgixa kai hade da tabe baki yace "go ahead mana, if yhu think dat will make yhu get her, u will only end up ruining matters, dat is addin salt to injury" Khaleel yyi murmushin da bae yi niyya ba yana kallon abokin nasa, lallai ya yrda Najeeb ya rikice kan Ashfah, Najeeb ya fuxa iska yace "it sound meaningless nd annoying ryt?" Mikewa Khaleel yyi yace "ka ga ka tafi gida ka bar min hauka a nn don Allah, in ka dawo nml koh xuwa anjima da daddare sae ka dawo let get a soln" Khaleel na kai wa nn ya dauki wayarsa ya nufi sama, Najeeb ya bi sa da kallo jikinsa yyi sanyi ssae, ya dafe kansa, yes! yasan no matter wat Khaleel baxae taba yrda shi ya rubuta takardan da ya tarwatse farin cikinsa ba ko jikinsa xae xama kunnuwa ne gaba daya, but hw is he goin to proof dat to him. Karfe takwas da rabi na dare Najeeb ya dawo gidan, Khaleel na kwance falo kan doguwar kujera yana kallon kwallo, yana ganinsa ya mike xaune, Najeeb ya karaso ya xauna yana kallonsa, Khaleel yace "kae da nace ana magrib ka xo malam, to gashi har sun yi bacci har fa nayi mata mgna daxu ta amince xata saurareka" Najeeb kwalalo ido yace "don Allah Khaleel, wllh daga clinic nake shi yasa bn xo da wuri ba, plss ka tashe ta mana" Khaleel yace "A'a ka dae xo gobe da safe xae fi" Najeeb yyi shiru bae ce komae ba, ba don ransa ya so ba ya mike yyi masa sallama ya fice, Khaleel ya bi sa da kallo har ya fita snn yyi dariya. Mikewa Khaleel yyi ya nufi sama yyi sallama ya shiga dakin da su Ashnaah su ke, Ashfah ce xaune kan darduma tana shafa'i da wutr, Ashnaah kuma tana bayi tana wanka, Khaleel ya rasa gane Ashnaah ce xaune kan darduman ko ba ita ba don hijab din Ashnaahr ce, ya dae yi assure din kansa ita ce, tsaye yyi bakin kofa yana jiran ta idar, dae dae nn Ashnaah ta fito daga wanka daure da towel, kallo daya yyi mata ya juya da sauri tare da cewa "oh srry sister" ya fice daga dakin, Ashnaah ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Ashfah na idar da sllh tace "wae ba kin fi ni tsayi ba da haske" Ashnaah dake dariya har lkcn tace "gane min hanya, ko da yake mu ryt frm tym ba a iya banbance mu" Hijab Ashnaah ta sa tace ma yar uwarta tana xuwa snn ta fita, falo ta samesa xaune, ta kuma fashewa da dariya, ya mike yana kallonta da mmki, ta karaso tace "daga ynxu idan kana son sanin wacece fateema tsayin mu kawae xaka kalla," Khaleel ya sauke ajiyar xuciya ya jawota jikinsa yace "OK wife" xaunawa yyi kan kujera ya xaunar da ita kan kafarsa ta shiga kkrin mikewa da sauri ya rungumeta yace "kin ga kin dan fara samun sauki ynxu ko wife, bbyn nn nawa na son ki dayawa baya son wahalar da ke, just a month nd two wk fa yhu re gettin beta," Ashnaah ta galla masa harara tace "ko ba better ba, don kawae ina daurewa koh," kmr xata masa kuka ta karashe mgnr, Khaleel ya shiga kkrin cire hijab din jikinta a hnkli yace "to yi hkuri bbyna yhu re nt gettin beta" ta xaro ido ta rike da sauri tace "tawul kadae ne fa jikina" sake mata hijab din yyi ya shiga dagawa daga kasa a hnkli yana kallon santala santalan kafafuwanta, ya lumshe ido ya daura lips dinsa kan wuyanta murya can kasa kmr me rada yace "wife ki dan tausaya min yau mana, I i need yhu badly" Ashnaah ta hade rae ta fara kkrin tashi daga kafarsa ya rikota da sauri a hnkli yace "to kiyi hkuri wife, I won't again na bari" Karfe sha daya Ashfah ta ishe Ashnaah ta fi gun mijinta ta bar ta ta fara jin bacci, da kyar Ashnaah ta fita daga dakin ba dan ta so ba da sunan xata dawo idan tayi masa sae da safe. Dakin da tasan xata samesa ta shiga, kwance ta samesa yyi rub da ciki kan gado idonsa lumshe kmr me bacci ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 107..... Ashnaah ta karaso gefensa ta xauna tana kallonsa tace "re yhu sleepn" a hnkli ya bude manyan idonsa da suka sauya kala yana kallonta, ta mike tace "came to say gudnt" shiru yyi bae ce komae ba har lkcn idonsa na kanta, hade rae tayi ganin hka ta juya xata bar dakin ya mike xaune ya rikota da sauri ya dawo da ita ya xaunar gefensa, cikin wata kasalalliyar murya yace "am srry wife, me kika ce?" Kmr xata yi kuka tace "ba ka ma ji abinda nace ba koh" lumshe ido yyi ya rungumota a hnkli yace "wllh bn ji ba bby" shiru tayi bata ce komae ba kanta na kirjinsa, sun kusa minti goma a hka can dae ta dago tana kallon agogo ta ga sha daya ya kusa, ta shiga kkrin mikewa tace "xan tafi in kwanta sae da safe" kin saketa yyi, tace "don Allah ka kyaleni in je in kwanta" da kyar ya iya bude baki yace "baki tausayina ko wife?" Ta xaro ido xata yi mgna ya saka bakinsa cikin nata, ssae ta tsorata kmr ranan ya fara kiss dinta, ta fara neman kwace kanta amma ta kasa, hkn yasa ta sakar masa kuka jikinta na bari tana cewa ya bata so, Khaleel bae sarara mata ba duk da ynda ya ga ta rude daren nn har sae da ya kai ga cimma burinsa, bbu abinda take sae aikin kuka tana neman tashi ta bar masa dakin amma ya ki saketa, wani mugun haushinsa kawae take ji a lkcn duk da ta dan sha wahala amma ba kmr na farko ba, bbu irin lallashin da bae mata ba amma kamar 'da da tunxurata yake, ta gaji da kukan wajen Karfe daya bacci ya dauketa, can wajen Karfe uku ta farka ta Mike xaune da kyar ta dalilin xaxxabi da ke jikinta ga wani tashin xuciya da ta ke ji, kkrin sauka daga kan gadon ta shiga yi ya rikota da sauri ta fixge hannunta da karfi ta sauka, gabanta ya shiga faduwa tana tsoron kadda ta kasa tafiya yau ma, amma sae ta ji bata ji xafi ba, ta fice daga dakin da sauri, kasa shiga dakinta tayi ta nufi downstairs don ta ga akwae bayi, nn tayi wankan ta ta fito ta sa hijab xata koma dakinta, xaune ta gansa a falon, ta kauda kai da sauri ta nufi sama ya mike ya bi ta, kuka ta saki ta ki ci gaba da tafiyan, tsayawa yyi inda yake, cikin kuka tace "ni wllh ka kyaleni bana so" shiru yyi yana kallonta, a hnkli yace "kiyi hkuri wife, am srry" juyawa tayi ta haura sama da sauri, tana shiga dakin ta kwanta gefen yar uwarta nn da nn bacci ya dauketa. Washegari da safe Ashfah ta gama shirin tafiya wae tana da lecture, don takaici Ashnaah da ke kwance ga xaxxabin da ya sa ta gaba ga ciwon mara bata ko kalleta ba bare ta tanka mata, Ashfah ta karaso gefen gadon tace "kin ji sister, xan tafi" ba tare da Ashnaah ta kalleta ba tace "Allah ya tsare" Ashfah ta mike tace "Ameen, Allah ya kara lfya sae mun yi waya" Ashnaah bata tanka ta ba har ta fice, Ashfah tayi murmushi kawae ta sauka downstairs abun ta, falo ta samu Khaleel, ta karaso cikin falon tace "sae anjima ni xan tafi" Khaleel ya daga kai yana kallonta yace "da safe hka sister, baki yi breakfast ba ae" Ashfah tace "bana breakfast da safe sae eleven, ina da lecture ne" Khaleel ya mike yace "OK, bari in dauko makulli in ajiye ki" tace "A'a wlh ka bar shi xan samu napep idan na fita" bae saurareta ba ya nufi sama ya dauko makullin motarsa ya shiga bedroom da Ashnaah take, xaune ya sameta tsakiyar gado ta hade kai da gwiwa tana kuka, ya karaso kusa da ita yana kallonta bata jira me xae ce ba ta mike ta shige bayi ta kulle kofar, ya dan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin, a hanya yake ce ma Ashfah ta bar Ashnaah tana ta kuka, Ashfah tayi murmushi tace "wae baxan tafi ba ga shi yau Abbanmu xae dawo, kuma bae san na tafi ko ina ba" Khaleel yace "gskya ne" har kofar gidansu ya ajiye ta ya bata dubu biyar tare da cewa ta gaida masa momy ta karba da kyar snn ta shiga gida yyi reverse ya bar anguwar, a tare suka yi parkin da Najeeb a kofar gida, Khaleel ya rike kai yana dariya har Najeeb ya fito daga motarsa snn shi ma ya fito, Najeeb yace "Allah ya sa sun tashi" Khaleel ya fashe da dariya yace "ynzun nn na mayar da ita gida, ko karyawa ta ki yi wae tana da lecture, lkci daya mood din Najeeb ya canxa yace "ya xa ka min hka Khaleel?" Khaleel yace "its nt my fault frnd" juyawa Najeeb yyi ya shige motarsa ya fixgeta a guje ya bar anguwar Khaleel ya bi sa da kallo yana murmushi. Washegari Asabar ba tare da Najeeb ya Bari Khaleel ya sa ni ba ya lallaba abokanan dad dinsa shi ma ya bisu xuwa can gidansu Ashnaah don ganin Abbanta, Abba na gida a lkcn, as usual da fara'arsa ya tare su snn suka gabatar masa da abinda ya kawo su kan cewa sun xo neman auren Ashfah, Abba ya dan yi shiru snn yana kallon Najeeb yace "ita ta ce ka turo koh?" Najeeb ya girgixa kai da sauri yacec"A'a Dad, hasalima ni bata taba kulani ba wllh shi yasa na ce bari in xo neman ixini a gida" Abokanan dad din nasa suka tsaya kallonsa da mmki don ba hka ya fadi masu ba, Ca yyi yarinyar tace ya turo manyansa in ji babanta, Abba ya dan yi murmushi yace "gskya ne" maida dubansa yyi ga bakin nasa yace "to xancen gskya 'ya ta karatu take ynxu, kuma sae ta gama xan bada aurenta kuyi hkuri dob Allah, kae in kaga kana sonta xaka iya jiran ta gama, saura mata shekara uku idan Allah ya yrda" mikewa abokan dad din Najeeb suka yi kowa ransa a bace, bbu wani kwakkwaran sallama suka fice daga falon, Najeeb kam kasa tashi yyi, ya marairaice ma Abban yace "wllh dad xan bari tayi karatunta baxan hanata ba" Abba yace "to ni bnyi niyar aurar da ita ynxu ba sae nn da shekara uku," mikewa Najeeb yyi jiki ba kwari yyi masa sallama ya fita daga falon. 108...... Dayz went by followed by month, wasa wasa yau cikin Ashnaah ya cika wata shidda da sati biyu cif ynxu kam

Chapter 25 of 29