mata snn ya fice daga dakin, bbu ynda ta iya hka ta sa hijab din kmr xata fashe da kuka ta fito, har waje Khaleel ya bi ta yana kallon drivern da ke jiran ta jikin mota yace "ba ni makullin motar Ahmad, xaka iya tafiyarka xan kai ta" Ashnaah ta juya da sauri tana kallonsa, ji tayi kmr ta fasa ihu, shi ko ya xagaya ya shiga maxaunin driver, dae dae lkcn da masu gadi suka bude gate sae ga babban mota dauke da lafiyayyun kayan daki na gani na fada, har su biyu suka shigo gidan, Bin motar da kallo Ashnaah tayi, Khaleel ya sauke glass din motar ya daka mata tsawa "wae kina hauka ne xaki bar ni xaune cikin mota"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
57.....
Ashnaah ta bude motar ta shiga har lkcn tana kallon motocin da suka shigo gidan da kaya with much interest, ko kifta ido bata yi, Khaleel ya ja motar bayan ta shiga suka bar gidan, sae a snn ta juya tana kallonsa tana murmushi hade da washe hakoranta, ganin taki daina kallonsa yasa yace "wae lfya kike kallona hka" kmr jira take ta fashe da dariya har da kyakyatawa tana kallonsa tace "na ga ka kusa xama ango ne ina taya ka murna," bae ko kalleta ba ya mayar da hnklinsa kan tukin da yake, tace "kayan amaryar ne aka shigo da ynxu knn?" Ya galla mata harara yace "wnn ba Matsalar ki bace" shiru tayi tana hararansa, can kuma tace "to yaushe ne bikin" nn ma bae tanka ta ba amma fuskarsa a daure yake, tace "to ya naga baka sauya kujerun falo ba da tv ko Akwae sauran tym ne" parkin taga yyi a fusace ya fixgota da shirin xabga mata mari, ta fasa ihu tare da rike hannyensa ta boye fuskarta jikinsa tana basa hkuri, kallonta ya tsaya yi ya kasa dukan nata har lkcn yana rike da ita, ta dago kanta a hnkli tana kallonsa kmr xata yi kuka tace "to don ina taya ka murna, da ina bakin ciki ae baxan dinga tambayarka ba hka, amma tunda baka so na daina" turata yyi ya ja motar suka bar wajen, ba ta kuma cewa komae ba ta hade rae ita ma, ganin tuki kawae yake yasa tace "to wae a ina kasan gidan namu ne da kke ta wani tuki," ba tare da ya kalleta ba yyi murmushi yace "fitsararrki da girman kae ya sa nasan gidan ku" juyawa tayi tana kallonsa bata dae ce komae ba, can dae ta dauke kai hade da tabe baki tace "to ka ji ddi" har kofar gidansu yyi parkin ta bude mota xata fita ya fixgota yana kallonta da kyau yace "kika kuskura kika fita xuwa ko ina ban yafe maki ba don ba da izini na kika yi hkn ba, gidan ku kadae na kawo ki," ya kalli wristwatch din hannunsa yace "dis is after eleven, xuwa Karfe biyu ki shirya xan xo daukar ki" yana kai wa nn ya turata, ta fice daga motar tana masa wani matsiyacin kallo tace "to kai kuma a suwa, ae wllh daga nn sae inda mai na ya kare, kuma ina jiran ka Karfe biyun in ga ko shigowa xaka yi ka jawo ni" tsaki tayi ta shige gate dinsu, ya bi ta da kallo yana murmushi yyi reverse ya bar anguwar, da fara'a Ashnaah ta gaisa da Mai gadinsu snn ta nufi falonsu gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parkn space, murya can ciki tayi sallama ta shiga falon gabanta yyi mugun faduwa ganinsa xaune yana kallon news, kallo daya yyi mata ta dauke kai, Ashnaah ta karasa inda yake jiki ba kwari ta durkushe kasa a sanyaye tana kallonsa tace "ina kwana Abba" ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan tv yace "lfya lau" daga nn bae kuma cewa komae ba, rasa abin cewa tayi, hkn yasa ta sunkuyar da kanta, ta kusa minti biyar a gun, shi dae bae ce Mata komae ba, nn da nn Hawkeye ya cika idonta ta mike a sanyaye ta nufi sama gwiwanta a sace, tana shiga dakin momynta ta xube nn gabanta ta shiga rusa mata kuka, momy ta dago ta a rude tana tambayarta me ya faru, cikin kuka tace "momy Abbana bae kulani ba" a fusace momy tace "to sae me, kada Allah yasa ya kula ki din ae ba gun sa kika xo ba" da kyar Momy ta lallasheta tayi shiru tana ajiyar xuciya, momy tace "daga gida kike?" Ashnaah ta gyada mata kai alamar eh, momy tace "ke daya kika xo" Ashnaah ta share guntun hawayen fuskarta tace "Aa shi ya kawo ni, Momy Ashfah pa?" Momy tace "tana gidan inna" Ashnaah tace "tana xuwa sch har ynxu ko" momy tace "eh tana xuwa" nn da nn wani hawayen ya kuma taruwa idon Ashnaah, a sanyaye momy tace "ke har ynxu baki koma ba ko?" Hawaye ya shiga bin kuncinta tace "ya ki Bari na in koma momy, ranan nayi ma mum dinsa mgna ta taya ni masa mgna ya bar ni in koma makaranta, sae da muka dawo gida yace shi baxae iya biya min kudin makaranta ba sae dae in babana ne xae dinga biya min" momy tayi shiru tana kallonta snn tace " ki fada min gskya fateema, kin san mutumin nn ko baki san shi ba" Ashnaah tayi shiru don tasan in ta gaya ma momynta gskyar abinda yasa Khaleel ya aureta kila ita ma fita harkanta xata yi don sau tari xancen ta baya wuce ta bar walakanta samari don bata san xuciyar wani ba sanin halin Ashnaah knn wlknta mutane," Ashnaah ta girgixa kai a sanyaye tace "Momy ni ban san shi ba" momy tace "to Allah xae saka maki, kuma ki kwantar da hnklinki wataran in Allah ya yrda gskya xata bayyana, kuma duk ran da hkn ya faru ni na tabbata ko Baban ki baxae bari ki ci gaba da xama da mutumin nn ba bare ni" Ashnaah dae bata ce komae ba kanta a kasa, momy tace "to ki tafi gidan inna ku gaisa kar kuma ki Mata xancen komae don tana iya tasowa ynxu ta xo ta sami Abbanku ta kuma ja maki matsala, kawae ki nuna mata lfya kike xaune da mijin ki, Ashnaah ta dan yi shiru duk da tana son xuwa taga kakar tata da yar uwarta Ashfah, can ta dago tana kallon momynta tace " momy bae san xan je can ba ae, kums Ca yyi kar in je ko ina daga nn" sake baki Momy tayi tana kallonta, Ashnaah ta dauki wayar momyn tace "bari kawae in kira Ashfahn ta xo ta sameni."
Like · 7 · Reply · Report · 12 minutes ago
~Dr Khaleel~ by Khaleesat Haiydar
58.....
Karfe uku saura mai gadi ya danna bell, Abban Ashnaah da ke xaune falo har lkcn ya mike da kansa ya bude kofar, mai gadin ya gaishesa da ladabi snn yace "wae fateema ce mai gidanta ke jira a waje" Abba yace "OK bari ayi mata mgna" wayarsa ya dauka ya kira Ashfah da ke sama, nn da nn ta sauko tace "gani Abba" ya bata sakon mai gadin, ta koma sama ta shiga dakin Momynsu tana kallon Ashnaah tace "wae mijin ki na jiran ki a waje" Ashnaah ta hade rae tana hararanta, Momy tace "haduwa ku ka yi da shi ne" da sauri Ashfah tace "aa, Abba ne ya kirani ynxu yake gaya min, ina jin mai gadi aka aiko" momy ta juya tana kallon Ashnaah da tuni yanayinta ya canxa tace "to tashi ki tafi fateema, tun da Abban ku aka ba sakon" bata yi musu da momynta ba ta mike a sanyaye ta sa hijab, Momy ta bude Jakarta ta kirgo dubu ashirin ta mika mata tace "gashi sae ki rike a hannunki kiyi transport xuwa makaranta, kawae nuna masa xa kiyi Abbanki ne ya baki, kiyi ta hkuri wataran sae lbri kin ji" Ashnaah ta share hawayen da ke bin kuncinta, ta karbi kudin a hnkli tace "to ngd Momy, Allah ya saka da alkhairi" turarruka momy ta harhada mata snn suka rakota har Downstairs da Ashfah, Ashnaah ta karasa falon Abbanta a sanyaye ta duka tayi masa sallama, ya amsa tare da cewa "Allah shi kiyaye hanya" mikewa tayi tana kallon momynta da ke ta hararan mai gidan nata, ta dauke kai suka kuma sallama da momynta snn Ashfah ta rakata har bakin mota inda Khaleel ke jiranta a waje, daga inda take tsaye ta gaishesa murmushi dauke fuskarta, kallonta ya tsaya yi da mugun mmki, sae kuma juya yana kallon Ashnaah da ta hade rae har lkcn hawaye na idonta tana kallon Ashfah tace "nagode sister, ki gaida min da inna in kin je" Ashfah tayi murmushi ta daga mata hannu snn ta juya da sauri ta shige gida ganin ynda Khaleel ke kallonta har lkcn mmki bayyane a fuskarsa, juyawa yyi yana kallon Ashnaah a karo na biyu kmr xae yi mgna sae kuma ya fasa, tada motar yyi suka bar anguwar, idonsa na kan titi yace "dama ke twin ce?" Bnxa tayi masa Hkn yasa bae kuma cewa komae ba har suka isa wani babban shoppn mall.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
59.....
Khaleel ya juya yana kallonta bayan ya gama parkn bbu yabo bbu fallasa yace "ki fita ki xabi abubuwan da kike so, sae kuma ki kuma xuwa ki ce ma ummina ban siya maki komae ba," yana kai wa nn ya fita, bbu musu ta fito ta bi bayansa suka shiga tayi shoppn dinta mai yawa, komae taga ni ko bae mata ba jefa shi cikin trolley take tsabar mugunta, shi dae bin ta da kallo kawae yake, har ta gaji don kanta fuskarta daure tana kallonsa tace "na gama." Yyi murmushi yace "tot baki gama muguntan ba ae" Kusan kayan dubu hamsin ta diba don yawancinsu duk turarruka masu tsada ne da takalma, ya biya kudin snn suka fito aka loda masu kayan a bayan mota, sae da ya fara siyan table water a gun da ake sayar da drinks cikin mall din snn ya nufi motarsa, Ashnaah ta juya tana kallon ruwan hannunsa ta hade rae tace "to ni ma Ae xan sha ruwan" juyawa yyi yana kallonta da kmr xae yi mgna sae kuma ya fasa, ya bude ruwan hannunsa ya sha kusan rabi snn ya rufe ba tare da ya kalleta ba ya mika mata, ta xaro ido tace "tab" ajiye ruwan sa yyi ya tada motar ys kama hanyar gida. Biyar saura suka isa gida, bata bi ta kan kayanta dake bayan mota ba ta nufi cikin gidan da sauri don xuwa ta ga gyaran da aka yi ma dakin amarya, mutane ssae ta tarar cikin gidan, duk suka bi ta da kallo, ita ma hka, tabe bak tayii ta nufi sama, dakin da ke kusa da nasa ake jeran, ta karasa bakin kofar dakin tana leken dakin ba karamin hadewa dakin yyi ba, kmr na wata yar shugaban kasa, ta tabe baki hadewa da cewa ikon Allah, kallonta kawae mutanen dake ciki suke da mmki, sae da ta gama kare ma ko ina kallo daga Bakin kofar snn ta juya xata bar wajen dae dae lkcn da Khaleel ya hauro sama, kallonta ya shiga yi yace "me kike yi a nn" a takaice tace "bai ma ido na abinci" bata jira cewarsa ba ta shige dakinta, sae da ta cire kayan jikinta snn ta dauki xani ta daura tayi kwanciyarta xuciyarta fess nn da nn bacci ya dauketa. Can after magrib ta farka tayi sllh, snn ta sauko downstairs sanye da hijab dinta, tsit kke jin gidan alamar duk an watse, falo ta tarar da Khaleel xaune yana cin fruit lkci daya yana waya, kallo daya tayi masa ta nufi kitchen tana tunanin me xata girka ta ci, daga karshe ta ga indomin ma baya ranta ta hada tea mai kauri ta fito, har ta nufi stairs sae kuma ta dawo tana kallon Khaleel fuskarta daure tace "gobe fa xan tafi sch" juyawa yyi yana Mata mugun kallo yace "get out ki ban waje" xaro ido tayi tana kallonsa ta ajiye tean hannunta da sauri ta xa gayo cikin falon tana kallonsa tace "ban gne ba, da xu nayi ma Abbana mgna, har ya ban kudin mota da xan fara xuwa, dama mun kusa fara exams in ji su ummi" yana mata mugun kallo yace "to bbu inda xa ki, bar min falona" kuka ta saki ssae tana cewa "wllh sae na je, tunda kace sae in ubana ne xae dinga biya min, kuma gashi ya bani kudin mota ya ce in tafi" mikewa
yyi ya daka Mata tsawa yace "bar min falona kar in taka ki, Baban ki ke da iko da ke a ynxu ko ni, nace bbu inda xaki, kuma hkn ya xauna" kuka takaici ta kuma fashewa da ta rufe ido ta shiga fesa masa rashin kunya, ya yo kanta ta bar gun da gudu tayi ball da cup din tean da ta ajiye kasa, mug din ya tarwatse ruwan tean ya malale ta fasa ihu ta durkushe wajen, karasowa kusa da ita yyi da sauri ganin jini a kafarta, ya duka gabanta yace "subhanallahi" kuka ta dinga rusa masa tana yarfe hannu, ya Duba kafar ya ga yankewa kawae tayi a tafin kafar, daukar ta yyi ya nufi sama da ita ya bude falonsa ya shiga snn ya nufi bedroom dinsa ya xaunar da ita gefen gadonsa, cire mata hijab din jikinta yyi ganin har kasa yake ja, spirit ya dauko da cotton wool xae wanke mata gurin ta rike sa a tsorace tace "aa ni wllh bna so xafi xae min" ya ce "dan kadan xan sa maki, rufe idonta tayi lkci dayata ta saki ihu ta dafa kafadansa jin wani shegen xafi yana wanke wajen, daga kai yyi yana kallonta har lkcn yana rike da kafarta idonsa ya sauka kan kirjinta da yake hangowa daga durkushen da yake, bude ido tayi a hnkli tana kallonsa, ta xaro ido ganin abinda yake ta kare kirjinta da sauri, mikewa yyi shima da sauri ba tare da ya kalleta ba yace "jinin ya tsaya, nxt wk sae ki fara makarantar kafin nn an kawo min amaryata" mikewa tayi cike da jin ddi ta fice daga dakin. Ran Friday bayan an sauko daga juma'a aka daura auren Ameesha da Khaleel, Ashnaah kam ko a jikinta don ko momynta ma bata gaya ma ba bare wani nata, throughout ranan gidansu Khaleel ta yini da su Meenah don tun da safe ya kai ta, ummi tausayin Ashnaah kawae take don ta ga kmr yarinta yyi Mata yawa ganin ynda take ta harkan gabanta kmr ba kishiya aka mata ba, ita ko ranan dama ta samu dn sun fi awa biyu suna waya da usman dinta, bayan isha Ashnaah na kwance dakin Rukayya tana game da Sabon wayarta Meenah ta shigo rike da Jakarta alamar xata wuce, Meenah tace "wae fateema baki fada min ynda ku ka yi da Baban Zeenat ba ko daxu ta kirani wllh, ko dae har kin fara tausayin mijin naki ne" Ashnaah tace "wani tausayi? Ni wllh na ma manta, ae gwara da kika tuna min bari ma in je in kirasa ynxu wllh" Meenah tace "dare bae yi ba" Ashnaah tace Karfe fa takwas da rabi ynxu" mikewa ashnaah tayi ta fita don xuwa garden ta kira dad dn Zeenat, Meenah na biye da ita a baya. Dai dai bakin kofar fita suka hadu da Khaleel xa su shigo da su Najeeb, Meenah ta koma baya da sauri Khaleel ya shiga Mata wani irin kallo can yyi murmushi yana kallonsu Najeeb yace "nn da wata biyu xa ku kuma xuwa daurin aurena idan Allah ya yrda," Najeeb dae bae tanka sa ba sae kallon Ashnaah yake, juyawa Ashnaah tayi ta koma sama cike da jin haushin kiran da bata yi ba, Meenah ma ta ja tsaki ta bi bayanta. Karfe tara saura Khaleel ya sallami momynsa da ta ki sakar masa fuska tun da ya shigo gidan tafiya da Ashnaah, nasiha ssae ummi tayi ma Ashnaah kmr ynda xata ma yar ta snn tace ta tashi su tafi, Ashnaah ta mike tana kallon Khaleel shi ma ya mike snn yyi ma umminsa sae da safe ya fita.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
60.....
Khaleel ya juya yana kallon Ashnaah bayan ya gama parkin yace "ina son maki wata
tambaya" juyawa tayi tana kallonsa da mmki fuskarta daure tace "tambaya kuma" ya
dan yi shiru snn yace "ki fada min gskya tsakanin ki da Allah, ke kika mare ni ko ba ke
bace" dariya ma ya bata ssae, tana kallonsa da kyau tace "idan bani bace ba fa?" Bbu
yabo bbu fallasa yace "yea sae in sake ki, in dauki revenge Dina kan warce ta marenin, I
mean ur twin sis, don ni bana cuta, nd I wil ask for ur forgiveness of course" shiru
Ashnaah tayi tana kallonsa, ba dan ba dan ba da tace ba ita bace but tana mugun son
yar uwarta baxa ta so wani abu ya sameta ba, can tace "to idan bani ba ce fa?" Ya
shafa sajensa yace "baxan sake ki ba har sae kin duka don kanki bayan na gama koya
maki hnkli kina rokon in yafe maki kin gane kuskuren ki" Ashnaah tayi masa wani
matsiyacin kallo snn ta fashe da dariya tace "dats d last thing da xan yi a rayuwa in
duka ina baka hkuri don ni nasan ban maka komae ba kai ka min, ni da kai xa mu ga
wnda xae gaji yyi surrender. Kuma karka kuskura ka sama yar uwata ido bbu ruwan ta
ni ce nn Fateema na mare ka" Bata jira cewarsa ba ta fice daga motar ta nufi cikin
gida, bin ta yyi da kallo snn yyi murmushi ya fito ya kulle motarsa ya bi bayanta.
Ashnaah ta tsaya corridor din dakuna tana ta kallon dakin Ameesha tana tabe baki,
dakin ta nufa ta tura kofar a hnkli tana kallon cikin dakin, xaune ta ganta kan rug din
tsakar dakin ga kanwarta farida da kawayenta biyu xaune suna ta hira, da mmki
Ashnaah ta ke kallon Ameesha don bata san ita ce amarya ba sae ynxu da take
ganinta, Ameesha dae ta dukar da kanta, Ashnaah tayi murmushi tace "welcm to hell on
earth yar uwa, har na tausaya maki wllh" juyawa tayi ta fice daga dakin, kawayen
Ameesha da ransu ya baci suka ce wacece kuma wnn yar yarinyar ko ita ce uwar
gidan, Ameesha bata ce masu komae ba sae hawayen da ta shiga yi, kanwarta Farida
da baxa ta wuce Ashnaah ba tace "wat? Kuka kike ko me yaya? Wait wae ita kike ma
kuka" a sanyaye Ameesha tace "nace ma Khaleel ya raba mana gida ya ki, ni bana son
tashin hnkli wllh" farida ta fashe da dariya tace "wllh ba ki yo xuciyar mama ba Anty,
ko ni na xage baxan ma yarinyar nn duka ba, dubeta kawae galallawa rai ba gata"
dariya sauran kawayen Ameesha suka yi, Ameesha tace "ni dae bbu ruwana bana son
tashin hnkli ki tashi ki tafi gida" farida tace "wllh bbu inda xa ni, in ta isa ta kuma shigo
mana ta ga ko baxan ballata ba" Ameesha tamike a fusace ta nuna mata kofa tace
"kinga tashi ki bar nn kar in bata maki rai" mikewa farida tayi ta fixgi Jakarta da yar
mayafinta ta fice daga dakin, kawayen nata ma sun yi niyar kwana amma ganin abinda
tayi ma yar uwarta yasa su ma suka mata sallama suka kara gaba, hkn yasa ta shiga
kuka a hnkli ita kadae, a hka Khaleel ya shigo ya sameta, ya xauna gefen gado yana
kallonta yace "wae kuka kike yi Khadija" bata ce masa komae ba hkn yasa ya mike ya
fita ta bi sa da kallo a sanyaye. Bayan kusan minti talatin ya dawo dakin sanye da
jallabiyarsa ya ajiye coffen hannunsa yana kallonta yace "kina ji na" ta dago tana
kallonsa ya dan sakar mata murmushi snn yace "hope xa kiyi amfani da abubuwan da
xan gaya maki" ta gyada masa kai kawae, yace "Kinga ke ce matata a gidan nn, don ita
wancan she is just here for some tym, don hka duk wani responsibility na gidan nn na
kan ki, tun daga kan girki nd every other chores, more importantly bbu ruwan ki da
wancan yarinyar, ke ce matar gidan nn ba ita ba duk da nasan baki da fitina," yyi shiru
snn yace "I think dats ol" ta sunkuyar da kanta tace "in sha Allah, I wil abide" daukan
coffensa yyi ya karasa shanyewa, ita kuma ta mike ta nufi bathroom. Washegari da
safe Ameesha na kitchen tana hada breakfst Ashnaah ta shigo kitchen din, ta tsaya
daga bakin kofa tana kallonta, Ameesha ta dan yi murmushi tace "gud mrnin" Ashnaah
tace "mrnin Amarya, girki kike?" Ba tare da Ameesha ta kalleta ba tace "ehh" Ashnaah
ta karaso kitchen din ta dauki wata yar kula ta ajiye kusa da ita tace "to in kin gama ni
ma ki xuba min nawa" tana kai wa nn ta juya ta fice daga kitchen din. Ameesha ta
gama hada break din ta jera dinnin ta ajiye wnda ta xuba ma Ashnaah, dae dae nn aka
bude kofar falon Farida ta shigo da kulan abinci, da mmki take kallon yayarta tace "wae
girki kika yi" Ameesha tace "eh har na gama," farida ta tabe baki ta ajiye kulan hannun
ta tace "sae anjima." Khaleel ya sauko downstairs yana kallon Ameesha yace "wa ya
shigo ynxu" tace "farida ce ta kawo abinci" yace "OK" snn ya nufi dinnin ya xauna yana
bude girkin da tayi, kulan da ta xuba ma Ashnaah ya bude yace "wnn fa" tace "Ca tayi
in dibar Mata ita ma" wani kallo ya shiga yi mata yace "ita me ya hanata saukowa tayi"
dae dae lkcn da Ashnaah ta sauko falon tana kallon Ameesha tace "har kin gama
amarya" Ameesha tace "ehh ga shi can a dinnin na xuba maki" Ashnaah ta nufi dinnin
din ba tare da ta kalli Khaleel ba xata dauki kulan ya Riga ta daukewa yana mata
mugun kallo yace "ki shiga kitchen kiyi girkin mana" Ameesha ta karaso dinnin din tana
murmushi tace "ae ta shigo taya ni daxu"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
61....
Ashnaah ta gama feshe jikinta da turare snn ta
saka hijab dinta ta dauki yar Jakarta ta rataye a
kafada snn ta dauki dubu biyu cikin kudin da
momynta ta bata ta fito, dakin Ameesha ta nufa
ta sameta xaune gaban madubinta, Ashnaah tace
"na tafi sch" da sauri Ameesha ta juya tana
kallonta tace "da gske, ya bar ki ne" Ashnaah ta
tabe baki tace "kar ma ya bar ni mana, kinsan ne
xa ki girka mana yau" Ameesha tace "aa"
Ashnaah tace "jollof rice" Ameesha tace "OK
Allah ya kiyaye hanya amma ki fara gaya masa
kan ki fita kar kiyi laifi" Ashnaah tayi dariya tace
"ae ni bana laifi" juyawa tayi ta fice ta sauko
kasa, xaune ta same shi falo, ba tare da ta
kallesa ba ta nufi kofa, mikewa yyi da mmki yace
"ina xa ki?" Ashnaah ta hade rae tana kallonsa
tace "ba kace yau Monday Zan yi resuming ba"
tsayawa kallonta yyi ya ma rasa me xae ce mata,
can ya daka mata tsawa yace "to baxa ki ba, yar
rainin wayo" kmr jira take ta fashe masa da kuka
tace "amma kae fa kace min yau" yace "don
nace maki yau shine xa ki xo ki wuce ni ba tare
da kin ce xaki fita ba" ta dan marairaice gudun
kar ya hanata tace "to nayi xaton bacci kke ae"
tsayawa kallonta yyi ta sunkuyar da kai da sauri,
ya kauda kansa yyi murmushi, can ya kuma
kallonta yace "to a hka kike tunanin xa ki fita
fuskarki a waje? Ina nikaf din ki" juyawa tayi ba
musu ta koma ta sako nikaf snn ta sauko, daukar
makullin motarsa da ke kan center table yyi
fuskarsa daure yace "mu je" kmr xata fasa ihu
take kallonsa don bata so ya kai ta ba, amma
bata ce komae ba gudun kar yace bbu inda xata
kuma, ta bi bayansa, har cikin makaranta Khaleel
ya ajiyeta yana kallonta da kyau yace "na hane ki
da yi ma ko wani namiji mgna, Karfe nawa xa ku
gama lecture" tace "shidda" bata jira cewarsa ba
ta bude mota ta fice. Ba karamin farin ciki su
ummi suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 29