umminsa xata sauko, ya gaisheta snn suka sauko kasa a tare, Ashnaah da ke xaune falo ta gaisheta kan ta a sunkuye ummi ta amsa da fara'arta tana tambayarta ya gida, har kusan magrib Ashnaah sae xuba kunnuwa take taji xancen da ummi xata mata amma shiru, sae hira take da Khaleel, ita kuma sae kallo take, mikewa tayi daga karshe tana kallon ummi tace "momy Rukayya na sama ne" Ummi tace "eh tana sama bata jin ddi ne" Khaleel yace "me ya sameta ummi," ummi tace "xaxxabi ne kawae, ta ma ji dama dama ynxu" Ashnaah tace "bari in Duba ta" snn ta nufi sama da sauri ta bude dakin Rukayya ta shiga, xaune ta sameta tana rubutu, Ashnaah ta dan daure fuska tace "wayar ki xa ki ara min" nuna mata wayar Rukayya tayi ta ci gaba da abinda take, Ashnaah ta nufi gaban madubinta ta dauki wayar tace "kina da nmbr Meenah" Rukayya tace "ehh" Ashnaah tace "da me kika yi savin" ba tare da Rukayya ta kalleta ba tace "Amina sister" Ashnaah ta Duba ta ga nmbr, bbu bata lkci tayi dialing bugu biyu Meenah ta daga, Ashnaah tace "Haba Meenah shine xa ki min wlknci ki ki xuwa ina ta baxa ido koh" Meenah tayi dariya tace "yar gari kin fito yau da mijin naki knn, wllh ke dae in gaya maki momy ce tace bbu inda xa ni kwana biyu bbu abinda nasa gaba sae yawo, amma kar ki damu kila gobe ko jibi in xo ga wayar ki nn na siya tun ranan" Ashnaah ta washe hakora tace yauwa kawalli nagode ina nn ina jiran ki, sallama suka yi Ashnaah ta katse kiran ta ajiye mata wayar nn inda ta dauka snn ta fice daga dakin. Karfe takwas da rabi tana xaune dakin ummi suna kallo bayan ta gama cin abinci Khaleel ya shigo dakin, ya xauna yana kallon umminsa yace "ga ni ummi" ummi tace "dama nace sae a gabanka xan yi magana da fateema" bae ce komae ba ta juya tana kallon Ashnaah tace "fateema wae da amincewar ki xae yi aure" Ashnaah ta daga kai tana kallon Khaleel taga wani irin mugun kallo yake mata, ta sunkuyar da kanta da sauri kmr xata yi kuka tace "ehh toh momy sae daxun nn yake gaya min wae duk xancen da xa ki min in mun xo gida in ce ehh na sani kuma ae na amince idan ba hka ba wae sae yyi min abinda ban yi tunani ba," ta fashe da kuka tace "wllh momy ban san ashe aure xae yi ba, bae gaya min ba"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
49......
Khaleel ya kasa daina kallon Ashnaah da taki kallon
inda yake, duk da bae yi wani mmkin abinda tayi ba
yasan xata iya aikata fiye da hkn dama, da kyar ya
iya maida dubansa ga Ummi ya ga kallonsa kawae
take, ya sunkuyar da kansa, ummi tace "to tashi ka
bar min dakina" bbu musu ya mike yana kallon
Ashnaah ya fice daga dakin, sae a snn Ashnaah ta
dago kanta tana kallon ummi, kmr xata yi kuka tace
"momy dukana fa xae yi in mun koma gida wllh, ki
ce ya bar ni a nn" da mmki ummi tace "duka
kuma?" Ashnaah ta gyada mata kai, ummi ta ma
rasa me xata ce mata can dae ta mike ta fice daga
dakin, Ashnaah ta bi ta da kallo tana murmushi.
Goma saura ummi ta dawo dakin har lkcn Ashnaah
kallo take, ummi tace "tashi ki dauki hijab din ki ku
wuce gida" Ashnaah ta dan xaro ido tace "gida ynxu,
na tsamman a nn xa mu kwana ae" Khaleel ne ya
shigo dakin yana kallon Ashnaah yace "tashi mu
wuce ke nake jira" Ashnaah ta juya da sauri tana
kallon ummi kmr xata yi kuka, ummi tace "gobe xa
da safe xa ku dawo" mikewa Ashnaah tayi ta dauki
hijab dinta ta sa, tuni gabanta ya soma faduwa, tayi
ma ummi sae da safe ta fice daga dakin ya bi
bayanta. Har suka isa gida Khaleel bae ce mata
komae ba, har karkarwan sanyi ta shiga yi don tsoro
amma ko kadan hkn bae nuna a fuskarta ba, sae da
ya jira ta fito snn ya kulle motarsa ya nufi cikin
gida ta shiga jan kafarta da kyar tana bin sa a
baya, oh ko wani irin duka kuma xae mata yau, kin
shiga falon tayi ta tsaya daga bakin kofa tana
kallonsa fuskarta daure, bae ma san tana yi ba din
jira kawae yake ta shigo ya rufe kofar sa, ganin
bata shigo ba ya sa ya daga kai yana kallonta,
dauke kanta tayi da sauri still ta ki shiga falon, ya
juya ya nufi stairs kawae ya haura sama, ta kusa
minti talatin bakin kofar taki shigowa falon ga wani
mugun bacci da take ji, daga karshe dae ta gaji don
kanta tayi shahada ta shiga falon kmr xata yi kuka
ta rufe kofar ta nufi cikin falo ta xauna, har bacci
ya samo dauketa daga xaunen da take taji kmr
motsi kusa da ita ta mike tsaye a tsorace ta gansa
a gabanta ya duka, da sauri ta bar wajen ta ga
remote din dake kan kujerar da take ya dauka snn
ya mike tsaye yana kallonta yace "ni bani da lkcn ki
ynxu, i mean ban gama gather din tym dinki ba"
kashe tv dinsa ta ga yyi snn ya kashe wutan falon
ya nufi sama ta bi sa da kallo snn ta yi murmushi a
xuciyarta tace ko dae momy tace kar ka taba ni ba,
sama ta nufa xuciyarta fal murna ta bude dakinta ta
shige. Washegari da safe Khaleel ya kai ta gida gun
Ummin sa kmr ynda ta umarce shi, bbu yabo bbu
fallasa ta amsa gaisuwarsa ya juya ya fice daga
dakin, ummi na kallon Ashnaah tace "kina ji na
fateema, ki kwantar da hankalin ki, in dae har ina
Raye a doron kasa baxan taba barin Khaleel ya
walakanta ki ba, ki kyalesa yyi auren sa kar ki tada
hankalin ki kin ji" da mmkin ummi sae gani tayi
Ashnaah tayi murmushi ssae tace "to momy dama ni
bn daga hnklina ba" Da rana Khaleel ya xo tafiya da
Ashnaah gida, ko kadan bae ji ddin irin ynda
umminsa ke amsa masa gaisuwa ba, Ashnaah tayi ma
Ummi sallama ta sa hijab dinta ta bi bayan Khaleel,
yana gama parking a gida ya bude motar ya nufi
cikin gida ba tare da ya tsaya kulle wa ba ya bar ta
nn ciki. Washegari lahadi yana kwance dakinsa idonsa
lumshe kmr me bacci ya ji an danna bell, ya mike
xaune yana kallon agogo ya ga goma da kusan rabi
to waye kuma wnn, tashi yyi ya fita daga dakin don
xuwa ganin Wanda ke bakin kofar. Najeeb ne tsaye
yana kkrin kiransa, Najeeb yace "bacci kke ne"
Khaleel yace "aa na tashi tun safe" hanya ya basa
ya shigo falon snn ya shiga tambayarsa daga inda
yake, Najeeb yace "gida mana" Ashnaah ce ta fito
daga kitchen sanye da dogon rigan baccinta har kasa
pink colour me tsantsi, gashin nn nata me kyau na
daure da ribbon baki, hannunta rike da cup din tea,
Khaleel ya juya da sauri da kuma mmki yana kallonta
don bae san tana kasa ba da baxae bude kofar ba,
kallonta kawae Najeeb yake ko kiftawa baya yi, wani
irin tsawa da ya raxanata Khaleel ya daka mata ba
tare da yasan yyi hkn ba yace "me ya sauko dake
nn" tsayawa kallonsa tayi kmr wata sha sha sha don
ita dariya ma ya bata, Khaleel ya juya yana kallon
Najeeb da har lkcn bae kifta ido ba yana kallon
Ashnaah, a fusace Khaleel yyi kanta, ta fasa ihu ta
juya xata koma kitchen da gudu, ya cafkota don
tsabar tsoro hka ta sake cup din hannunta tana
kwala ihu, janyeta yyi daga wajen da sauri ganin cup
din ya tarwatse da ruwan tean ciki, bata ankara ba
taji ya dauketa kmr wata yar bby ya nufi sama da
ita, dakinta ya bude ya jefata ciki yana nuna ta da
dan yatsa yace "wllh wllh kika sauko min falo sae na
kusan fasa maki kai" bae jira me xata ce ba ya fice
daga dakin ya sauka kasa, sae a snn Najeeb ya
sauke ajiyar xuciya ya xauna, Khaleel ya hade rae ya
nufi kitchen ya dauko broom da packer don kwashe
kwalaben da ke kasan falon, sae da ya gama tidy
din wajen snn ya xauna yana kallon Najeeb yace "ya
aka yi guy any prblm" Najeeb ya sauke ajiyar xuciya
yace "wae wnn ita ce yarinyar Khaleel" Khaleel xae
yi magana ya ji muryar Ashnaah a bayan su.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar50....Mikewa Khaleel yyi ya bude baki da mmki yana kallonta, rasa ma me xae ce mata yyi, to wae ita wnn wace irin mutum ce, tambayar da yyi ma kansaknn a xuciyarsa yana ci gaba da kallonta, ta galla masa harara tace "to wae sbda kayi bako sae in ta tsayawa da yunwa baxan nemi abinda xan sa a cikina ba" Najeeb ya fashe da dariya har da kyakyatawa, a fusace Khaleel yyi kanta kan tayi tunanin gudu har ya kamata ya kuma komawa sama da ita ya bude dakinsa ya tura ta ciki da karfi snn ya kulle dakin ya jingina jikin bango ya dafe kansa, yana tunanin shi kam me xae ma yarinyar nnya ji ddi bnda Wanda yyi niyyar mata da, yana ji tanarusa kuka tana bubbuga kofar ya juya ya sauka kasa, Najeeb yace "haba doctor, ka barta tayi harkangabanta mana, me ta tsare maka a nn, ko kuma in ce me ta tsare mana" kallon bnxa kawae Khaleel ke masa, can ya ja tsaki yace "look, idan bbu takamaiman abinda ya kawo ka ka tashi ka bar min gidana in tafi in kwanta pls" Najeeb ya hade rai yace"ka ga fa wlkncin ka ke hadani da kai wllh, is there anything wrong with my coming here? Sae in tashi in bar maka gidan ka malam" Khaleel ya dan yi murmushi yyi kwanciyarsa kan 2sitter din da yake xaune yace "to Allah ya baka hkuri" Najeeb yace "to ynxu dae wnn ita ce yarinyar da ka aura" Khaleel yace "yeah" Najeeb ya dan yi shiru snn yace "kayi ynda nace maka?" mikewa Khaleel yyi da sauri ya xauna yana kallonsa yace "look ni fa bbu abinda xanbari ya shiga tsakaninmu, ni dae nasan I only romance her once or twice, ta min yarinya da yawa nd beside wahalar da kaina kawae xan yi, in ma ka ga nayi sha'awarta to I saw half naked ne amma hka kawae bata bn sha'awa, ka bar big gals irinsu Ameesha da sauransu" Najeeb ya dan shafa gemunsa yace "to ka saketa Khaleel, stop wasting ur tym wllh" Khaleel yace "dats d lst thing I wil do onearth a ynxu dae" Najeeb bae kuma cewa komae basae tsakin da yyi. Karfe sha biyu da rabi Najeeb ya bar gidan, Khaleel ya rakasa har gun motarsa snn ya dawo ya nufi dakinsa ya bude ya tura a hnkli ya shiga, kwance ya sameta kan 3sitter ta juya baya a falo, ya karasa kusa da ita a hnkli ya duka yana lekan fuskarta don duk a tunanin sa bacci take, ido hudu suka yi ya koma baya da sauri ta mike xaune fuskarta a daure tace "meye kke wani lekana" daukekai yyi ya nufi kofar falon ya bude yana nuna mata waje yace "xo ki fita" mikewa tayi ta fice daga dakin kmr xata tashi sama ya bita da kallo har ta sauka kasa snn ya dan yi murmushi ya kulle dakinsa. Washegari Ashnaah na kitchen da rana tana girka shinkafa da miyar da xata ci, sae gunguni take ita daya a kitchen kmr xata yi kuka tana cewa ni dae nagaji da wnn wahalan yaushe rabon mutum da ya ci nama kullum abinci lami to Allah ya Isar min tunda ba hka ake yi a gidan mu ba naga, jin an bude kofar falon yasa tayi shiru tana sauraro taji wnda xae shigo, shirun da taji yasa ta dan leka falo taga Meenah tsaye, da sauri ta fito tana washe baki tace"lahh ashe ke ce Meenah sannu da xuwa" Meenah tace "baya nn dae koh? Don bn yrda da masu gadin nn ba" Ashnaah tayi dariya tace "baya nn wllh" Meenah ta xauna nn tsakiyar falon ta shiga bude Jakarta ta ciro kwalin wata yar karamar waya me kyau techno, da dan envelop fari karami tace "ga wayar da na siyo maki, wnn kuma maganin da kika tambaya ne gashi" Ashnaah ta galla mata harara tace "bayan har na gama period din ma, ae mutuwa kadae ne bnyi ba wllh" Meenah tace "eyya, wllh momy ce ta hanani fita, ki ce daurewa kawae kika ta yi" Ashnaah tayi dariya tace "yayanki ne yyi min allura wllh" Meenah tace "Ahh anyi abun arxiki su Khaleel" Ashnaah tayi dariya ta dauki wayar tana dubawa tace "amma yana da kyau wllh, bari in dauko nmbr mu gwada kira, kin dae sa min kudi koh" Meenah tace "ke Zeenat fa ta koma gidansu tun shekaranjiya" Ashnaah ta dafe kirji tace "ki ce wllh" Meenah tace "wllh kuwa, bn san ynda suka yi ba ni ma, duk bin kwakkwafi na ban gano komae ba wllh" Ashnaah da har jikinta yyi sanyi ta maxa tace"to ae bae baci ba, still sae na kirasa wllh, ae baxae san khaleed din ne ya sace yar sa ba" Meenah ta fashe da dariya tace "ke khaleel sunansa ba khaleed ba" Ashnaah tace "ayyo" bell suka ji an danna duk suka mike a tsorace lkci daya tace"waye?" Murya masu gadi taji, Ashnaah tace "ya aka yi?" Suka ce kaya ne oga yace a shigo da, Meenah tace "ya dawo ne" suka ce "ehh" sama ta nufa da gudu har tana faduwa, Ashnaah ta dauki wayarta da sauri ita ma ta nufi sama don ta boye, sae da ta boye snn ta sauko ta bude masu kofar ta ga akwatuna hudu a bakin kofar, dae dae lkcn da Khaleel ya karaso balconyn yace "ku shiga da su mana" waje ta basu suka shiga da akwatunan tana binsu da kallo, Khaleel ma ya shigo falon yana bin ko ina da kallo yace "me ke konewa hka" da gudu Ashnaah ta nufi kitchen tana cewa "innalillahi wa inna ilai hi raji'un" ya bi ta a baya da sauri, tana shiga kitchen din ta fasa wani ihu bayan ta sauke miyar ta durkushe kasa da sauri tana ci gaba da ihun, ba karamin tsorata shi tayi ba ya durkushe gabanta ya dagota duk a tunanin sa abu ne ya shiga idonta, a rude yake tambayarta "menene?" Kin bari ya daga fuskarta tayi, yace "wait don Allah ki gaya min me ya shiga idon" da kyar ta bari ya daga kanta,yana kallon idonta da ko digon hawaye bbu yace "to me ya shiga idon" kmr xata yi kuka tace "miyar da na sha wahala nayi ya kone"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
51.....
Kallonta kawae Khaleel ya tsaya yi, ta xame jikinta daga rikon da yyi mata ta shiga komawa baya a hankali tana hararansa, mikewa yyi a fusace yyi ball da ita ya fice daga kitchen din, dariya ta saki har da kyakyatawa tana bin sa da kallo snn ta mike, sae kuma ta ja tsaki ita ma ta fice daga kitchen din, falo ta same sa yana kwantar da akwatunan da masu gadin suka ajiye cikin falon, ta karaso cikin falon tana kallon akwatunan, ba tare da ya kalleta ba fuskarsa daure yace "gashi nn kayan fadar kishiya, ba don kin isa na maki ba sae a bisa umarnin mahaifiyata" murmushi kawae Ashnaah take har da washe hakora, ya dago yana kallonta ganin abinda take yasa ya tsaya kallonta, ta dan tabe baki tana daga kafada tace "ni na yafe, ka kara ma warce xaka aura kawae" tsawa ya daka mata yace "to ki xo ki sani nayi hkn" tace "to dolene? Nace bana so ko" ta karashe mgnr tana hararansa, ficewa yyi daga falon don xuwa gun masu gadi ya sa su kwashe akwatunan su mayar masa su cikin mota, takalma ya gani bakin kofar, da mmki yake kallonsu, can dae ya kwashe su yana kallonta yace "takalman waye wnn" da sauri fuskarta daure tace "na wa" wani irin kallo ya shiga mata lkci daya yana bin falon da kallo kmr me son gano abu, dawowa cikin falon taga yyi ya nufi sama, da gudu ta bi bayansa tana cewa "ina xaka" bae ko kalleta ba ya shiga haura stairs din, ta hau saman ita ma da gudu ta sha gabansa tana xaro ido tace "wae ina xaka" hankadeta yyi da karfi tayi baya xata fadi yyi saurin rikota kan ta kai kasa ta fado kansa, ba karamin tsorata tayi ba ta saka kuka, ya matsar da ita gefe xae wuce ta kuma shan gabansa cikin kuka tace "Allah sae ka fada min inda xa ka" a nutse yana kallonta yace "ina ruwanki," bae jira me xata ce ba ya kuma turata daga gabansa ya haura sama, dakinta taga ya bude ta fasa ihu ta kuma bin sa da gudu, da sauri ya shige dakin ya kulle ya shiga bin dakin da kallo a nutse, ido hudu suka yi da Meenah dake bayan kofar dakin kmr munafuka tana kallonsa, juyawa yyi yana kallonta da kyau yace "me ya kawo ki gidana" ta daure fuska tace "momy ce ta aiko ni gun fateema" wayarsa ta ga ya ciro, ko ba a gaya mata ba tasan momyn xae kira gashi bata ma san ta fito ba don bata gidan, da sauri tace "ni fa bbu Wanda ya aiko ni, na xo gaida fateema ne" Ashnaah ta shigo dakin tana hararansa tace "to meye don ta xo gidan nn, xaka wani...." Bata rufe baki ba taji saukan mari lafiyayye, ta dafe kuncin a gigice tana kallonsa, sum sum Meenah ta nufi kofa xata fita da sauri, ya fixgota yana mata mugun kallo snn ya shiga janta tana bin sa a baya har suka sauka downstairs, ita dae binsa kawae take bata ce komae ba don mugun tsoron Khaleel take tun da can, gate ya nufa da ita ya bude ya jefata waje, ya juya yana kallon mai gadi yace "don me xa ku dinga barin mun mutane na shigar min gida" mai gadin da tuni ya mike tsaye da ladabi yace "Ca tayi ita yar uwarka ce oga" cikin tsawa Khaleel yace "ta ina ta xama yar uwata? To daga yau kar ku sake barin ta ta shigo min gida, ban san ta ba" da sauri mai gadin yace "an gama oga" Meenah dake tsaye har lkcn wajen gate tana ma Khaleel wani matsiyacin kallo tace "Da yau ubana bae da gida ne xanyi kuka , amma ynzu kam sae dae inyi shewa, kana talaka da kai har ka isa ka gaya min gida, kasan waye ubana kuwa, u re decievin ur self with dis hel yhu cal home" tsaki ta ja tana masa wani matsiyacin kallo tace "nonsense" tana kai wa nn ta nufi titi abun ta da sauri da sauri, bin ta kawae Khaleel yyi da kallo, lkci daya ya saki murmushi yana gyada kai yace "xan yi maganin ki yarinya, sae kinyi da kin sanin sani na" kashedi ya kuma yi ma masu gadin kan kar su bari ta kuma shigo masa gida snn ya nufi balcony, xaune ya tarda Ashnaah a bakin stairs tana ta aikin rusa kuka har lkcn yana dafe da kuncinta, wani raxanannen tsawa ya daka mata yace "bar min falo na kar in taka ki" ganin bbu wasa tattare da shi yasa ta mike tana ci gaba da kukanta ta hararesa ta haura sama. Da daddare tana kwance daki taji an tura kofa ta juya tana kallon kofar ya shigo dakin rike da leda a hannunsa, kallo daya yyi mata ya ajiye ledan nn bakin kofar ya fice daga dakin, sae da ta ji ya shiga dakinsa snn ta sauko kasan dakin ta bude ledan taga abinci ne.
[10/20, 11:32 PM] +234 803 863 6764: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
52.....
Washegari Ashnaah na jin fitar motar Khaleel da yamma ta fiddo wayar da Meenah ta siyo mata da sauri, tana hamdalan fitarsa a xuciyarta, don tun safe take jiran ya fita amma bata san me ya hanasa fita ba, takardar da ta rubuta nmbr dad din Zeenat da ta adana cikin Jakarta ta dauko ta kwashe a wayar snn tayi dialing, bbu bata lkci ya shiga, ta nufi gadonta tana murmushi ta xauna tana jiran a daga, amma har ya gama ring ba a daga ba, ta kuma kira nn ma ba a daga ba, bata wani damu ba don tasan ae xae ga miscals dole ya kira baya, nmbr mum dinta ta kira, bugu biyu ta daga, Ashnaah na murmushi tace "momyna," Momy ta amsa daga daya bangaren, Ashnaah ta gaisheta cike da jin ddin jin muryar mum dinta, kmr xata yi kuka tace "momy wae har ynxu Ashfah baxa ta xo ba" momy tace "xata xo mana, kar ki damu, da fatan dae kuna lfya" A dan sanyaye tace "lfya lau momy, Abba na fa" Momy tace "yana nn lfya" a hankali tace "momy xan iya kiransa ynxu" momy ta dan yi shiru snn tace "to ki kirasa" Ashnaah tace "to Bari in kirasa" a sanyaye ta katse kiran, snn tayi dialing nmbr dad dinta gabanta na faduwa ta kara a kunne, xuciyarta ya kusa shigewa cikinta jin yana ring, bugu uku ya daga tare da yin sallama, da kyar ta iya bude baki ta amsa sallaman muryarta na rawa, a hankali tace "ina yini Abba" "lfya lau" ya amsa a takaice, a sanyaye tace "Abba ni ce" yace "ke wa?" Kmr xata yi kuka tace "fateema ce Abba" bbu yabo bbu fallasa yace "kina lfya" nn da nn hawaye ya cika idonta ta shiga gyada masa kai kmr yana kallonta da kyar ta bude baki tace "eh Abba" yace "to madalla, ngd da gaisuwar" bae jira me xata ce ba ya katse kiran, Ashnaah ta fashe da kuka duk da taji ddin amsa mata ma da yyi, momynta ta kuma kira ta gaya mata ynda suka yi da Abbanta hawaye na bin kuncin ta, momy tace "to kiyi hkuri watarana Allah xae bayyana gskya, da fatan dae bbu wata matsala" Ashnaah tace "bbu momy amma ina son in xo gida, ki taya ni rokon Abba ya bar ni in xo don Allah" cikin kuka ta karashe mgnr, a sanyaye momyn tace "to xan masa mgna fateema, sae in gaya maki ynda muka yi, wnn layin ki ne" Ashnaah na goge hawayenta tace "ehh nawa ne momy anjima xan kira ki da daddare" a hka suka yi sallama da mum dinta ta shiga rusa kukan takaicin 'bata mata rayuwa da rabata da yan uwanta da Khaleel yyi, ko kadan bata ji shigowarsa gidan ba kawae ji tayi ya bude kofar ta, ta daga kai da sauri tana kallon kofar hawaye na bin kuncinta, kauda kanta tayi da sauri tana ci gaba da kukanta, tsayawa yyi bakin kofar yana kallonta, can ya karaso Cikin dakin ya tsaya gabanta fuskarsa daure yace "me ya faru?" Tsaki tayi ta mike a fusace ta nufi bathroom, ya fixgota ta fado jikinsa, ta fashe da wani matsanancin kukan ta shiga turasa da karfi, amma ya ki sakinta, don kanta ta gaji tayi lamo a jikinsa tana shesshekar kuka, ya dago kanta yana kallon fuskarta ta daga idanuwanta tana kallonsa, kasa cewa komae yyi, ta kauda kanta da sauri, sae a snn yace "kukan me kike" ta fashe da wani Sabon kukan tace "ni gidanmu xan tafi" da kmr baxae ce komae ba yana mata mugun kallo can dae yace "kije kiyi me" ta daga kai ta galla masa harara snn tace "mamata da yan uwana xan je in ga" tsaki ta ji yyi ya turata yace "u are dreamin" snn ya juya ya fice daga dakin. Har dare Ashnaah bata bar kukan da take ba wani mugun tsanar Khaleel kawae take har cikin xuciyarta, don kanta ta gaji da kukan wajajen Karfe goma, snn ta mike ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito, yar rigar baccinta riga da yar karamar Riga tasa bayan ta gama shafe shafenta snn ta dauki wayarta da ke karkashin filo tana mamakin me yasa Baban Zeenat bae kira ba bayan ta masa mis calls, ta kalli agogo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 29