Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kai tayi duk da bata ci ba don bbu abinda taji ke ranta, nuna mata ynda xata sha magungunan yyi snn yace "kar ki kuma shan ko wani maganin xa a baki, kin ji ko wife" gyada masa kai tayi nn ma snn ya nufi gida da ita, nesa da gidansu ta sa ya ajiyeta Snn ta karbi ledan maganin hannunsa ya kamo hannunta yana kallonta yace "ki ajiye wayar ki kusa da ke plss xan kira ki" kai ta gyada masa snn ta fice daga motar da sauri, ya bi ta da kallo har ta shige gida, ajiyar xuciya ya sauke lkci daya murmushi ya bayyana a fuskarsa. Bata samu kowa falo ba hkn yasa ta nufi sama da sauri ledan maganin hannunta na cikin hijab dinta, kan gado ta nufa ba tare da ta kalli su Ashfah da ke xaune dakin ba ta kwanta tana mayar da numfashi kmr warce tayi gudu, Salma tace "har kin dawo?" Ashnaah ta gyada masu kai kawae ta juya don bata son mgna. Har ta fara bacci Ashfah ta tasheta wae Abba na kiranta, da kyar ta iya mikewa xaune ta dauki hijab dinta ta sa snn ta mike ta fita daga dakin, Abba na xaune falo ta karasa a dan sanyaye gabanta na faduwa don bata san me xae ce Mata ba ta durkusa ta gaishesa, ya amsa ba tare da ya kalleta ba shiru tayi tana jiran jin me xae ce, soye soye momy ke yi a kitchen hkn yasa xuciyarta ya shiga tashi ssae, duk ta rikice jin hautsinewar da cikinta yyi, sae jira take Abba ya sallameta ta bar falon, amma Abba na ta danna laptop, bata ankara ba lkci daya aman ya xo mata ta toshe baki ta mike da gudu da nufin komawa sama tayi aman, amma tana kaiwa dai dai stairs ta shiga kwararo aman, mikewa Abba yyi yana kallonta, momy ma ta fito da sauri jin kakarin amai, tana ganin Ashnaah ce ta nufi stairs din da sauri tana tambayarta me ya sameta, kasa bada amsa tayi amai ya ci karfinta, ganin ynda take aman kmr xata amayo hanjin cikinta yasa Abba ya karasa wajen shi ma, momy ta dagota tana mata sannu da damuwa, wani aman ya kuma xuwa mata ta dingi yi ba kakkauta, hnklin momy ya tashi ssae, Abba ya ciro wayarsa ya shiga neman layin likitansa, sae da Abba ya gama waya da likitan snn yana kallonta yace sannu, kai kawae ta gyada masa don ko amsawa bata iya aman yasa tayi weak ssae, ya juya yana kallon momy yace "ki tafi da ita daki ynxu likita xae xo" da taimakon momy Ashnaah ta gyara jikinta a bathroom snn ta dawo cikin dakin ta kwanta nn da nn bacci ya dauketa. ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 91..... Cikin minti talatin da yan mintuna likita ya iso gidan, har lkcn Ashnaah na bacci a daki, Ashfah ta shigo dakin ta xauna gefenta ta shiga tada ta, mikewa xaune Ashnaah tayi da kyar, Ashfah ta mika mata hijab dinta tace "ga likita ya xo, Abba yace ki sakko kasa in xa ki iya" Ashnaah ta girgixa mata kai kawae don bata son mgna, Ashfah tace "to ki sa hijab bari likitan ya shigo" da taimakon Ashfah Ashnaah ta sa hijab dinta snn Ashfah ta fita don cewa likitan ya shigo, da sallama likitan ya shigo dakin Abba na biye da shi a baya, Ashnaah ta sakko da kafafuwanta kasa daga kan gadon, likitan da baxae wuce shekaru 38 ba ya karaso yana kallonta yace "sannu," sunkuyar da kanta tayi, likitan yyi shiru yana kallonta, hkn yasa ta daga kai ta kallesa, Abba dae na tsaye Kansu, "ina ke maki ciwo?" Tambayar da likitan yyi mata knn, da kyar ta iya bude baki tace "ni ma bn sani ba" likitan ya juya yana kallon, Abba yace "in baku waje ne?" Murmushi likitan yyi tare da gyada masa kai, Abba yace "OK" snn ya juya ya fita, da mugun mmki likitan ke kallonta yace "Amma an mayar da auren ku da mai gidan ki koh? I mean kuna tare da mijin ki ynxu?" Girgixa masa kai Ashnaah tayi, ya dan xaro ido yana kallonta xae yi mgna sae kuma ya fasa ya shiga fiddo da kayan aikinsa a dan 1st aid box din da ya xo da don yana son tabbatar da abinda ya gani tukun, ita dae Ashnaah sae kallonsa take, cikin mintuna da ba su wuce sha biyar ba yyi duk abinda ya kamata snn yace mata xae je lab ya dawo, falo ya samu Abba yana cin fruit salad, ya karaso cikin falon yace "Alhaji bari in je inyi test na dawo ynxu, na dibi jininta ne" Abba yace "to amma kadda ka dau lkci Dr, I want her to get well soon don in 2dayz tym she will be wedded" likitan yace "in sha Allah" Bayan minti talatin likitan ya dawo gidan, A balcony ya samu Abba yana waya, Abba ya katse wayar yana kallon likitan yace "me sakamakon ya bada" likitan da duk ya daburce yace "bari dae ina xuwa Alhaji" cikin gidan ya nufa ya haura sama, da sallamarsa ya shiga dakin ya sameta ta dukunkune cikin bargo ta rufe har kanta, su Ashfah da Salma duk suna dakin suna gwada ankon da aka fidda na bikin Ashnaah da xa ayi jibi an karbo masu daga gun tela, Ashnaah na jin an shigo dakin ta bude kanta a hnkli, ganin likita ne yasa ta Mike xaune, kallon su Ashfah ya tsaya yi sae kuma yace "xa ku dan ba mu waje yan Mata" duk suka fita daga dakin, ya karaso ciki yana kallon Ashnaah ya ja stool din gaban madubi ya xauna har lkcin bae daina kallonta ba yace "Me yasa kika xabi lalata rayuwarki ki ba iyayenki kunya Fateema" Ashnaah ta daga Kai da mmkin jin furucinsa tana kallonsa, ya girgixa kai yace "kin ce min ba a mayar da auren ku ba, na kuma ji dad din ki na cewa jibi ne auren ki, sae ga shi sakamakon gwajin da nayi maki ya nuna kina dauke da cikin sati biyu da kwana shidda, hw is dat?" Ashnaah da komae nata ya tsaya ta gwalalo ido a mugun tsorace tana kallonsa, lkci daya abinda ya faru tsakaninta da Khaleel ya fado mata, a rude tace "Ni doctor" ya ajiye mata result din test din gabanta yace "yes! Check for ur self" Ashnaah ta daura hannu a ka cikin tashin hnkli tace "wayyoo Nashiga uku na lalace ciki kuma Doctor" wani matsanancin kuka ta fashe da ta sakko da sauri don kawae ji tayi karfi ya xo mata ta durkushe gabansa cikin kuka tace "don Allah don Annabi don darajan iyayen ka kayi min rai ka rufa min asiri doctor ka taimaka min" kuka ssae take a gigice, likitan ya girgixa kai yace "taya xan taimaka maki a nn fateema, ynxu dae who is responsible" Ashnaah ta kuma fashewa da wani sabon kuka ta ma rasa me xata ce masa shknn Khaleel ya cuceta ya kai ta ya baro ta, ita kam tasan bata da sa'a a rayuwa, likitan dae sae kallonta yake yana jiran amsa, cikin kuka tace "doctor mijina ne wllh, ni bn taba iskanci da kowa ba" likitan yace "wani mijin kuma, kin kuma aure ne" rasa abun cewa Ashnaah tayi sae kuka take ssae, shi dae sae kallonta yake, can dae ta gaji ta tsaida kukan tace "doctor ka tausaya ma rayuwata ka cire min cikin nn kashe ni wllh Abba xae yi, help me plss" likitan ya mike yana girgixa kai yace "of course bna hka, ynxu dole in kai ma dad din ki result din don abinda yake jira knn, I was called to check on wats wrong with yhu, xuwa xan yi ince bbu komae?" Ashnaah ta fashe da kuka ta tsaya gabansa a rikice tace "wayyo doctor help me plss kasheni xae yi kace masa malaria ne plss" likitan ya dan yi murmushi yace "its nt possible, a bakin aiki na fa nake kuma kudi xae biya ni sae in masa karya, to wae ma wa yyi maki cikin nn ki gaya min?" Cikin kuka Ashnaah tace "nace maka mijina ne wllh bae sakeni ba, set up aka yi masa, but no one is willin to blive dat" likitan yyi shiru duk da ba yrda yyi ba yace "meyasa xa ki amince masa batun kin san da hka," Ashnaah ta durkushe kasa tana rusa kuka tace "he forced me wllh" Likitan ya sauke ajiyar xuciya snn yace "amma kinsan dole in kai result din nn dae ko" shiru Ashnaah tayi tana hawaye, likitan yace "shknn let me c if I can cool ur dad down nd explain thingz to him, don dole in kai masa sakamako ya gani" kasa cewa komae Ashnaah tayi, duk jikinta yyi sanyi ta ji kmr Yau ce ranan mutuwarta, likitan yace "ki kwantar da hnklin ki xan yi kkrin ganin na nuna masa mijin naki bae sake ki ba as u said" yana kai wa nn ya juya ya fice daga dakin, Ashnaah ta Mike da kyar tana hawaye ta shiga tunanin abun yi hnklinta a tashe don tasan ko ruwan sanyi xae xama baxae taba convincing Abba ba, Likitan na shiga falon Abba ya samesa yana kallon news, momy kuma na xuba masa abinci kan centre table, Abba na kallon likitan yace "me sakamakon ya nuna doctor, har ka gama treatin din nata ne" likitan ya sauke ajiyar xuciya yace "Sorry to say Alhaji sakamako ya nuna yar ka na dauke da juna biyu na sati biyu da kwana shidda" mikewa Abba yyi tsaye da sauri ya saki remote din hannunsa ya xare glass din idonsa da karfi yace "wat?" Momy kam sake ruwan glass din hannunta tayi ba tare da ta sani ba, likitan na gyada kai yace "hka sakamakon gwajin da nayi Mata ya nuna Alhaji In'sha Allah" ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 92..... Juyawa Abba yyi yana ma momy wani irin kallo har lkcn mmki bayyane a fuskarsa, kuka momy ta saki tana kallon likitan tace "ciki fa kace doctor" likitan ya mika masu takardan hannunsa snn ya kara da cewa "amma ta nuna min auransu da mijinta na nn, don hka kar kuyi saurin yanke hukunci, bincike shine abinda..." Wani kallo kawae Abba ke masa, bae Bari ya Kai aya ba yace "ka gama aikin ka yallabae, xan turo driver da kudin ka anjima, tnx 4 ur help" Ashnaah kam tun bayan fitan likitan take ta rusa kukan tashin hnkli ta rasa abun yi, tasan yau kila sae dae wata ba ita ba, duk sae ta nemi xaxxabi da kasalan da take ji ta rasa, mikewa tayi xuciyarta na bugawa ta dauki hijab din ta tasa snn ta dauki wayarta ta fice daga dakin, su Ashfah da shigowarsu knn suka shiga tambayarta lfya amma ko ta Kansu bata bi ba, sakkowa kasa tayi ba tare da ta kalli kowa na falon ba ta nufi kitchen da sauri, dai dai lkcn da Abba ke sallaman likitan sa knn fuskarsa a daure jin maganganun da yake kkrin kawo masa, juyawa Abba yyi ganinta ya daka mata wani mugun tsawa yace "ina xa ki," Ashnaah bata ko kalle inda yake ba ta shige kitchen a guje ta bude kofar da xae sada ta da garden ta fice, Abba na ganin hka ya bi ta gaban gidan da sauri shi ma, likitan ya bi bayan sa, momy kam xubewa kan kujera tayi tana kuka ssae su Ashfah suka sauko suna tambayarta lfya amma ba bakin mgna, tunda Ashnaah take bata taba irin gudun da tayi ba ranan don kan kace kwabo har ta isa gate, dai dai sanda Abba ya fito knn cikin tsawa yake ce ma mai gadinsa ya rufe masa gate kar ya bari ta fita, kuka Ashnaah ta saki ganin mai gadin ya kulle gate din ga Abba na tahowa, ta durkushe gabansa tana rusa kuka hnklinta a tashe tana cewa "don Allah don annabi kayi min rae ka bude min, kashe ni xae yi wllh" Tahowa kawae Abba yake fuskar nn tasa bbu alamar rahama idon nn nasa ya kada, hkn ya kuma tada hnklin Ashnaah ta shiga kwala ihu, tun kan Abba ya karaso mai gadin ya shiga basa hkuri duk da bae san me ke faruwa ba, amma ko kadan Abba bae Ma san yana yi ba, likitan ya sha gabansa da sauri yace "Haba Alhaji kar ka ce xaka taba ta don Allah, consider situation din da take ciki kar ka ji ma yar ka ciwo, ka kwantar da hnklinka ka saurari bayanin ta tukun" Abba ya tura likitan daga gabansa cikin tsawa yace "gwara in kasheta kawae yau in huta" Ashnaah na jin hka ta shiga gudu tana xaga gidan tana rokon Abbanta cikin kuka, tana ganin momynta ta fito ta nufeta da gudu ta tsaya bayanta tana cewa ta taimaka mata don Allah, Ashfah da tuni ita ma ta fara kuka ta nufi Abbansu ta durkushe gabansa cikin kuka take cewa "don Allah don Annabi Abbanmu kayi hkuri" cikin kuka momy tace "wllh Adam kar ka kuskura ka taba min 'ya ta da ka taba ta gwara ka Kore mu gaba daya gidan yau" Abba ya tsaya kallonta can yace "hka kika ce koh" kai tsaye momy tace "ehh hka na ce" Abba yace "fine, Ni baxan ma Fateema baki ba amma daga yau na cire ta cikin 'ya ya na, wato na yafe ta, kar ta kara tunanin tana da uba a duniya, ba ita ba gidan nn, snn idan ta kuskura ta sa kafa ta taka gidan mahaifiyata bn yafe mata ba, ta tafi duk inda xa ta bnda gidan uwata, bn haifi yar da xata ja min abun kunya a duniya ba" cikin tsawa Abba yace "ta xo ta fice min a gida" Momy tace "in har Fateema ta bar gidan nn to ni ma na bar gidan nn" Abba ya daga kafada yace "fine! Ki tafi amma a bakin auren ki" Abba na kai wa nn ya nufi cikin gida da sauri, Ashnaah ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka tana kallon momynta tace "A'a momy kiyi hkuri, Kar ki ce hka, amma ki yafe ni don Allah nasan tun tasowa ta na kasance warce bata jin maganarku amma momy ni ban taba bin maxa ba duk rashin ji na, ki yrda dani momy mijina bae sakeni, tun daga ranar da na ga takardan nn nasan bashi ne ya rubuta ba don ba ma shi da lfya ranan da na ga takardan, snn ya sha gaya min baxae taba saki na ba idan na bukaci hkn tun farkon aurenmu lkcn ma ba ddin xaman gidan nake ba, amma da yake na dde ina son ya sakeni shi yasa na dauka takardan kawae na dawo gida duk da raina bae so hkn ba, nasan ko min daren ddewa gskya xata bayyana kuma Abbana xae yafe min." Ashnaah tayi shiru tana kallon momynta da ke hawaye har lkcn, can ta juya ita ma tana hawayen tace "ki daina kuka momy xa mu dinga waya, amma ki taimaka min ki ba Abbana hkuri" Ashnaah na kai wa nn ta soma tafiya ta nufi gate, Ashfah ta bi ta da sauri tana kuka tace "ina xa ki sister" Ashnaah ta share hawayenta tace "gidan mijina xan koma" tana fadin hka ta bar gun da sauri ta bude gate ta fice daga gidan. Plss sisters ku bar ni in rubuta littafina ynda na tsara, wnda ya ga littafin nn yyi masa ya karanta wnda kuma ya ga bae masa ba ya bar shi kawae, nt dat xa ayi ta min complain ace hka ya kamata in yi ba hka ya kamata in yi ba, hkn bbu ddi Sam, hka aka min lkcn littafin Ikram, gskya ni dae bna jin ddin hka. 5 mins · Khaleesat Haiydar... ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 93..... Tafiya kawae Ashnaah take ba tare da tasan inda xa ta ba gashi bata fito da kudi ba bare ta sami abun hawa ta hau, gajiya tayi ta nemi dakalin wani da shago ta xauna ta dalilin jirin da take ji ssae ga kasala, lkci daya taji xaxxabin ya dawo mata, wayar da ke hannunta ta kalla don ta ma manta ta taho da shi, nn da nn ta shiga neman layin Khaleel taji bbu kudi a wayar, dafe kanta tayi ta rasa me ke mata ddi ga wani aman da ke taso mata, gun kwanciya kawae take nema a lkcn, pls cal me ta tura masa da sauri bayan kusan minti goma ta ga bae kira ba, ta kuma tura masa ta jira still bae kira ba, ta kusa minti talatin a xaune kanta hade da gwiwanta can dae ta dago a hnkli tana tunanin abun yi, tasan ko taku daya baxa ta iya ba daga wajen faduwa kawae xata yi tsabar jirin da take ji, wasu hawaye ne su ka shiga bin kuncinta ita kam ko me yasa bata da sa'a a rayuwa, a hnkli ta shiga bin inda take da kallo tana tunanin to ko taimako xata nema don gun Akwae mutane da dama suna ta harkan gabansu, ji tayi baxata iya tashi ba kawae ta ci gaba da xamanta a gun, Sadeeq ne ya fado mata, ta dago wayar a hnkli tana kallon screen din, please cal me ta tura masa shi ma, Sadeeq dake xaune kasa falon Abba da dad dinsa ya ciro wayarsa jin alert din msge, ganin sakon yasa ya mike ya ce yana xuwa snn ya fita, kiranta yyi bugu daya Ashnaah ta daga da sauri, Sadeeq yace "ya aka yi Fateema," a sanyaye Ashnaah tace "kati xaka turo min don Allah" Sadeeq yace "me yasa kika yi abinda kika yi?" Ashnaah da hawaye ya shiga bin kuncinta tace "sbda mijina bae sake ni ba" Sadeeq ya dan yi shiru snn yace "kina ina ynxu?" A hnkli tace "gidan mijina xan je, ina son kiransa ne bni da card" Sadeeq yace "Shknn, Allah ya huci xuciyar Abban ki ya sassauta maki" kai kawae Ashnaah ta gyada masa kmr yana ganinta tana hawaye, yace "xan maki transfer ynxu" yana kai wa nn ya katse kiran, cikin minti biyu taga transfer din dari biyar ta tura masa da text din gdya, tana kkrin dailin nmbr Khaleel kiransa ya shigo, dagawa tayi bata ce komae ba, da damuwa yace "wife kiyi hkuri sae ynxu na ga text din ki, am srry I wasn't OK ne xuciyata na damuna shine nayi alluran bacci, I just woke up ynxu" kuka Ashnaah ta sakar masa, nn da nn ya rikice mata yana tambayarta me ya faru ta kasa cewa komae sae kuka, ganin ynda ya birkice ya sa a sanyaye tace "Ka kuma hada ni da parent dina hnklin ka ya kwanta, ba ka min adalci ba, sae in iya cewa ka cuce ni ma kawae, me yasa ka min hka doctor...." Kuka ne ya ci karfinta ssae, Khaleel da hnklinsa yyi mugun tashi duk da ya gano dalilin maganganun nata yace "plss ki gaya min me ya faru, kina ina ne?" Cikin kuka ssae tace "ba dole ka tambaye ni ina ina ba" kmr xae mata kuka yace "plss wife kar ki bari a cire cikin nn am beggin yhu ki tausaya min don't let dat plss, ki bari mu ga bbynmu" Ashnaah da mmki ya cika ta ta ma rasa me xa ta ce masa, wato ashe ya ma san tana da ciki knn, Shiru tayi tana naxarin magungunan da ya bata ranan har yana cewa kar ta kuma shan ko wani magani xa a bata a gida, kuka ta fashe da tace "wllh baka da imani, ka hada ni da iyayena kawae ka raba ni da su don son xuciyar ka, to bana son cikin xubar wa xanyi" kuka kawae take kmr ranta xae fita ta katse kiran, Khaleel da idanunsa suka kada suka yi ja ya dafe kansa da ke Sara masa xuciyarsa nai masa kuna. Kiranta ya kuma yi, Ashnaah da ke kuka har lkcin ta kasa kin daga kiran nasa duk da ta so yin hkn, ta dauka tayi shiru, a sanyaye yace "kiyi hkuri fateema xan cire maki cikin na maki alkawari tunda ba kya so, ynxu plss ki gaya min inda ki ke" taki cewa komae na wani dan lkci snn a hnkli ta gaya masa inda take, cikin mintunan da ba su wuce sha takwas ba Khaleel ya iso gun da ta gaya masa take, yana gama parkin ya fito ya nufi inda ya hangota da sauri ya durkusa gabanta ya kamo hannunta da damuwa yace "am vry srry wife, I caused all dis" kuka ta sakar masa, duk ya rikice yana lallashinta, ganin taki yin shiru yasa dago ta ya rungume abarsa, ta tsaida kukan da take da sauri ta kwace kanta ganin a titi suke, kama hannunta yyi tana ganin jiri har suka isa motarsa snn ya bude mata front seat ta shiga, ya xaga ya shiga shi ma ya tada motar suka bar wajen, ssae ta ba Khaleel tausayi ganin ynda ta da da ramewa da ganinta ka ga mai laulayi, ga kuma kukan da ta ci, kwantar mata da kujerar motar yyi ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa, gidansa ya nufa da ita, yana gama parkin ya fito ya dauki abarsa ya shiga ciki da ita, ta bude ido da sauri tace "meye hka" bedroom dinsa ya shiga da ita, ya cire bedsheet din kan gadon snn ya kwantar da ita. 94..... Mikewa xaune tayi da sauri ta wani daure fuska don haushinsa kawae take ji, a sanyaye yace "srry na ga kina bacci ne" ta dauke kanta kawae har lkcn fuskarta a daure, mikewa yyi jiki ba kwari ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, hawaye ne ya shiga bin kuncinta duk she is confuse fushinta xata nuna masa ko jawo mijinta xata yi jiki. Jinginar da kanta tayi jikin gadon tana tunanin rayuwarta tun daga ranan da ta fara haduwa da Khaleel, wasu hawaye masu xafi suka shiga sakko mata, tana nn a hka har bayan minti talatin ta ji an kira sllhn Azahar, mikewa tayi a hnkli don xuwa tayi alwala taji jiri ya debeta ta dafa bango da sauri kan ta kai kasa ta koma kan gadon ta xauna, kasa mikewa tayi har aka idar da sllh Khaleel ya shigo dakin, ba karamin tausayi ya bata ba yanayin da ya shigo, ya karaso gabanta ya duka ya ajiye mata ledan abincin hannunsa da plate yace "ga abinci na siyo maki ki sakko ki ci" kallonsa kawae take ya bude abincin ta ga dafa duka ne da naman kaxa, nn da nn cikinta ya hautsine aroma din abincin na bugar ta, mikewa ta shiga kkrin yi da sauri ya lura da hkn ya mike yace "me ya faru, amae kike ji" toshe bakinta tayi ta sakko daga kan gadon tayi baya xata fadi ya kamota da sauri ta durkushe kasan dakin ya bi ta har lkcn yana rike da ita ta shiga kwarara masa aman a jiki, ssae ta bashi tausayi ganin bbu komae cikinta, gashi she is too young ace tana da ciki ynxu, yana rike da ita yana mata sannu a sanyaye har ta gama ta fada jikinsa tana mayar da numfashi ya rungumeta, sun fi minti biyar a hka snn ya dago kanta a hnkli yana kallon idonta da yyi ja yace "Sannu wife" sunkuyar da kanta tayi kawae, mikewa yyi ya dauketa suka nufi bathroom, da kansa ya gyara mata jikinta bayan ya cire mata kaya, snn shima ya gyara nasa jikin ya daukota suka fito ya kwantar da ita kan gado ya lulluba ta da bargo snn ya shiga gyara dakin, ko da ya gama har tayi bacci ya xauna gefen gadon a hnkli yana kallon kyakkyawan fuskarta wani mugun shaukin sonta na fixgarsa, yasan he can't do without Fateema, daura hannunsa yyi a hnkli kan goshinta ya ji xafi ssae, ya mike

Chapter 21 of 29