duk ta rasa particular tunanin da take a xuciyarta, tana jin an tada sllh ta mike da sauri ta ciro hijab dinta snn ta dauko handbag dinta ta nufi kofa, a hnkli ta tura kofar ta fita ta sauka downstairs, bbu kowa falon hkn ya bata damar fita da sauri, gate a rufe yake bbu ko wani mai gadi a nn, tasan suna masallaci, ta shiga bude gate din da sauri snn ta fice, sauri sauri gudu gudu ta nufi bakin titi ta sayar da adai daita sahu ta gaya masa inda xata snn ta shiga. Bakwae da kusan rabi Ashnaah ta isa kofar gidansu, ta fiddo kudinsa ta mika masa snn ta nufi gate dinsu, a sanyaye ta karasa cikin gidan tana kallon motar Abbanta da ke Parke, a hnkli ta tura kofar falonsu ta shiga bata samu kowa falon ba ta nufi sama da sauri ta bude dakin mum dinta ta shiga, xaune ta sameta kan darduma caxbi a hannunta, da mmi take kallon Ashnaah, Ashnaah ta sakar mata murmushi tace "sannu momy bari in yi alwala" bathroom ta nufa da sauri tayi alwala ta fito snn ta tada sllh, sae da ta idar snn momy ta juya tana kallonta da mmki tace "daga ina hka" Ashnaah ta kirkiro murmushi tace "ya xo gun wani frnd dinsa ne a nn wajajen shine nace ya bar ni in karaso gida" momy bata ce komae ba, Ashnaah ta gaisheta amsa tana kallon yar tata, ko kadan Ashnaah bata Bari momynta ta lura da komae ba, tace "Abba na nn ko momy" momy tace "yana dakinsa" Ashnaah bata tambayi yar uwarta ba don tasan tana gidan inna, tambayarta momy tayi ko ta ci abinci Ashnaah tace ta ci, don bata jin cin komai, har tara da rabi, momy bata ga Ashnaah na cewa xata tafi ba, momy ta shigo dakinta tana kallonta tace "wae ba yau xaki koma bne, kinsan Abbanku fa bae san kin xo ba" Ashnaah tayi shiru snn tace "sae gobe momy" momy tace "to tun da kwana xa kiyi ki tafi ki gaida Abban ku kar ya gan ki gobe ya xame min abun mgna" Ashnaah ta gyada ma mum dinta kai kawae, momy ta juya ta fita, kuka Ashnaah ta shiga rerawa a hnkli tana tunanin ynda iyayenta xasu dauki xancen da ta kawo masu. Khaleel kam na dawowa daga masallaci ya nufi dakin Ashnaah, bae sameta a ciki ba hkn yasa ya nufi bathroom nn ma bata nn, fitowa yyi ya shiga dakin Ameesha ya sameta xaune kan darduma, yace "fateema fa" Ameesha tace "tun hudu ta hau sama, tana dakinta" juyawa yyi ya fice daga dakin, bbu inda bae duba ba a gidan amma bae ga alamar Ashnaah ba hnklinsa yyi mugun tashi, to ina ta tafi da daren, masu gadi ma suka ce basu ganta ba, sama ya koma ya dauki makullin motarsa ya sauko, rasa inda xa shi nemanta yyi, lkci daya ya shiga tunanin to takardar meye ta gani daxu ta ki ba sa, gidansu ya nufa kawae goma saura qtr ya isa kofar gidansu, ya fito ya nufi gun mai gadi, bayan sun gaisa ya ke tambayarsa ko Ashnaah ta xo, yace masa eh, sae da ya fara sauke ajiyar xuciya snn yace "to ka min mgna da ita don Allah" mai gadi ya nufi cikin gidan, Abba ne ya bude kofar yana kallon mai gadin yace "ya aka yi Musa" mai gadin yace "wae mai gidan fateema ne ke jiranta a waje" Abba yace "wace fateemar" Mai gadin yace "fateema dae" juyawa Abba yyi ya nufi sama ya bude kofar momy fuskarsa a daure yace "me yarinyar nn ta xo yi gidan nn yau ba tare da na sani ba" Momy ta hade rae tace "bn gne me ta xo yi ba" fada ssae Abba ya shiga yi yace "ta xo ta fice masa daga gida mijinta na jiranta a waje" Ashnaah da ke jin duk abinda abbanta ke cewa ta shiga kuka a hnkli tasan dole ta fada masu me ya dawo da ita gida, mikewa tayi tun kan ya shigo inda take ta dauki hijab dinta da takardan sakin da ta gani ta fita a sanyaye don xuwa jin me ke tafe da Khaleel kuma. Yana tsaye jikin motarsa ta fito daga gate dinsu, kallonta kawae yake har ta karaso inda yake snn ta rungume hannayenta fuskarta daure tace "ina jin ka" kallonta kawae yake har lkcn ya ma rasa me xae ce mata, ganin hkn yasa tace "in baka da abin cewa xan koma cikin gida pls" a hnkli taji yace "me nayi maki Fateema" ta daga kai tana kallonsa don bata ma san ya san sunanta ba, sunkuyar da kanta tayi da sauri don kar ya ga hawayen dake kkrin taruwa idonta tace "me kuwa ka min baka min komae ba" shiru taji yyi bae ce komae ba hkn yasa ta fashe da kuka ssae ta mika masa takardan hannunta, karba yyi yana kallon takardan, cikin sakwannin da ba su wuce sha biyar ba ya gama karanta content din, lkci daya komae nasa ya tsaya ya sake takardan hannunsa ya fadi kasa yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ashnaah ta duka ta dauki takardan tana share hawayen fuskarta lkci daya tana murmushi tace "nd am very happy coz I have been lookn fwrd to a day like dis, am vry glad I saw it, dama baka so na bana..." Kasa karashe mgnr tayi sbda kukan da ya ci karfinta, da kyar Khaleel ya iya bude bakinsa da yyi masa nauyi murya can kasa a sanyaye yace "wllh summa tllh bni na rubuta takardan nn ba fateema" da sauri Ashnaah ta juya ta nufi gate dinsu, kiranta ya shiga yi don kasa binta yyi har ta shige gate dinsu, hade kansa yyi da mota yace "No! no, waye yyi min hka" lkci daya hawaye ya cika idonsa. Ashnaah na shiga falon su ta nufi falon Abbanta jiki ba kwari rike da takardan a hannunta, xaune ta same sa da momy, ta durkushe nn tsakiyar falon tana kkrin mayar da hawayen da ke neman xubo mata tana kallon iyayen nata, kasa daurewa tayi ta fashe masu da kuka ssae.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
69.....
Kallonta kawae iyayen nata suka tsaya yi, momy tayi karfin halin tambayarta lfya, shi dae Abba bae ce komae ba sae kallonta kawae yake, kasa cewa komae Ashnaah tayi sae kukan da take kanta a kasa, mikewa momy tayi ta nufi inda take tana kallon takardan hannunta ta karba, momy na gama karanta content din ta juya a sanyaye tana kallon mai gidanta, Abba yyi murmushi yace "har ya sako ta knn koh, dat's gud" Momy ta dauke kanta tana kkrin mayar da hawayen idonta ta dago Ashnaah suka nufi sama, kasa ba momy amsan tambayoyin da take ta ta jero mata Ashnaah tayi, hkn yasa momy bata kuma ce mata komae ba ta mike a sanyaye ta fice daga dakin, ko da ta koma falo bata tarda mai gidan nata ba, hkn yasa ta nufi bedroom dinsa, ta same sa xaune yana Danna laptop, ya dago kai yana kallonta yace "ynxu abinda nake so da ku shine, ku tabbatar ita daya take, don in har tana da juna biyu to wllh wllh baxata xaunar min a gida ba ina ganinta ina ganin takaici." Cikin fushi momy tace "halan tana da wani gidan uban ne bayan wnn, in tana da ka fada min in kai ta" cikin kuka ta karashe masa mgnr Abba yace "ni dae na gaya maku wllh." Ikon Allah kadae ya kai Khaleel gidansu wajen karfe goma da rabi, mai gadi yyi mmkin gninsa da daddare hka da yake suna shiri ssae, khaleel ya nufi cikin gida a birkice ba tare da ya ma san mai gadin na gaishesa ba, bbu kowa falon ya nufi dakin mum dinsa da sauri, ya sameta tana shirin kwanciya, da mmki take kallonsa tana kallon agogo, ganin yanayinsa ya kuma rudar da ita don tafi kowa sanin dan nata, ya xauna gefen gadonta tare da dafe kansa, ta karaso da sauri tana kallonsa tace "me ya faruwa Khaleel" ya dago kai yana kallonta, kasa ce mata komae yyi sae ga hawaye, ummi duk ta rude ta xauna gefensa tace "tok 2 to me son, me ya faru" da kyar khaleel ya iya bude baki ya gaya ma umminsa abinda ya faru, ya karashe mgnr cikin tashin hnkli kmr xae fashe mata da kuka yace "ku taimakeni plss mum, wllh bni ne na rubuta takardan ba ban san da shi ba " still Ummi tayi tana kallonsa da mugun mmki, Khaleel ya sauko kasa ya durkusa nn gabanta a raunane yana rike da kafafuwanta yace "plss Ummi na help me, idan Fateema ta nuna ma iyayenta wnn takardan I knw its over plss ummi" Ummi da duk kanta ya gama daurewa tace "ikon Allah," kwantar masa da hnkli ta shiga yi tace "shknn ka kwantar da hnklinka son Allah na tare da Mae gaskiya, ynxu ka tashi mu tafi gun abbanka muyi masa bayani, gobe sae su tafi can gidan har da kai." Washegari da safe har gida Abba ya kira likita ya gwada Ashnaah ko tana da juna biyu, likitan yyi gwaje gwajensa yace bbu komae, ita dae Ashnaah bbu abinda take sae hawaye duk ta rasa me ke mata ddi a duniyar, bayan likitan ya tafi Abba yasa momy ta kira mashi ita, ta sauko kasa a sanyaye ta durkusa falon Abbanta tana kallonsa tace "Abba gani" Abba ya maida hnklinsa kanta yana kallonta da kyau yace "a ina kika san mutumin nn, kar kuma ki kuskura ki min karya" hawaye ne ya shiga bin kuncinta, ta juya tana kallon momynta da ke kallonta, a sanyaye ta shiga gaya masu abinda ya hadata da Khaleel har ya aureta, bbu abinda ta boye masu har irin xaman da suka yi har ixuwa jiya da ta ga takarda a drawernsa, Abba yyi murmushi yace "wndful! dats gud, yhu c ol dis happen to u as a result of dis obeyin me, but na ji ddin da hkn ya faru, I knw you've learnt a great lesson frm now on, don hka in xa ki mayar da hnkli a karatu ynxu ki maida" kuka ssae Ashnaah take gashi ita dae har lkcn ta rasa gane dalilin kukanta, Abba ya dauki wayarsa ya kira wani abokinsa mai babban motar daukan kaya yace ya ara masa xa a kwaso masa wani kaya ne, da sauri Ashnaah ta daga kai tana kallonsa kukan da take ya karu ssae, Abba yace "ni bance kiyi min kuka ba, ki tashi ki tafi Allah xae saka maki duk da ke ce baki jin mgna, ynxu sae ki mayar da hnklin ki a karatu in kin ga dama, ga yar uwarki nn har tayi nisa" da kyar Ashnaah ta mike jiri na kwasarta ta nufi sama ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kmr ranta xae fita.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
70.....
Karfe sha daya da yan mintina Alhaji Muhd mahaifin Khaleel da wasu daga abokansa da shi kansa Khaleel din suka iso gidansu Ashnaah, hka kawae gaban Khaleel ke faduwa, Abbansa ya fito da sauran abokansa biyu da kaninsa yana kallon Khaleel yace "to ae sae ka fito ka makale cikin mota" Khaleel ya girgixa kansa da kyar yace "bana son shiga Abba" Abokin abbansa yace "ka ji sha shanci to sae mu ce masu me in mun shiga, ka fito mu shiga ayi abinda ya dace my frnd" da kyar Khaleel ya iya fitowa daga motarsa, iyayen nasa suka nufi gun mai gadin dake xaune bakin gate din yana biye da su a baya, kanin Abbansa ne ya tambayesa ko mai gidan na ciki bayan sun gaisa mai gadin ya amsa masa da ehh, snn yace to ayi masu sallama da shi, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo ya ba su ixinin shiga yyi masu iso har falon Abba, Abba dake xaune falon ya mike ganin bakin nasa ya tarbesu ynda ya kamata, tsaf ya gane su barin da ya ga Khaleel, Khaleel kam kasa kallonsa yyi kansa a kasa ya gaishesa, Abba ya amsa bbu yabo bbu fallasa, snn khaleel ya xauna kasa nn gefen Abbansa, bayan an gama gaggaisawa abokin dad din Khaleel Alhaji umar yana kallon Abban Ashnaah yace "to dae ba wani abu ne ya kawo mu nn ba illa mun xo ne mu baka hkuri on behalf of dan mu akan abinda ka gani Alhaji, duk da dae shi wnn yaro yace ba shi yyi sakin ba, xancen dae ga shi nn kmr na wasan yara don ba mu taba jin inda mutum xae ce ba shi ne ya saki matarsa ba bayan ga takarda nn a dakinsa, to ynxu dae muna rokon ka afuwa da ka dubi girman Allah kayi hkuri xa mu mayar da yar ka....." Abba da tun da ya fara xancen yake kallonsa da mmki yyi saurin katse sa yana kai wa nn ta hanyar cewa "dama ashe idan aka yi saki uku mace na komawa dakinta ban sani ba" shiru suka yi duk suna kallonsa, Alhaji umar ya kalli Khaleel da sauri yace "saki uku ne dama" Shiru Khaleel yyi bae ce komae ba, da ka gansa kasan he is nt his self, Abbansa yyi tsaki yace "amma kai fa mutumin bnxa ne, dama kasan saki uku ne xa ka sa mu kwaso jiki mu xo nn kmr wasu kananun yara" da kyar Khaleel ya iya bude baki kmr xae masu kuka yace "wllh Abba bani ne nayi sakin nn ba" daya abokin Abban Khaleel yace "to ae Alhaji in har a lkci daya yyi saki ukun saki daya knn a musulince, ko ba hka ba" Abban Ashnaah yyi murmushi yace "idan ka ce ma mace ka saketa saki daya, biyu, uku, to ta saku knn gaba daya ko ba hka yake ba," kai kawae suke gyada masa, Abban Ashnaah yace "to a hka dan ku ya rubuta sakin" Khaleel ya dafe kansa yana ganin wani jiri daga xaunen da yake lkci daya hawaye ya cika idonsa, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana duban Abban Ashnaah yace "ina takardan yake Alhaji, ko xa mu iya ganinsa" Abba ya mike ya nufi sama, Alhaji umar ya juya yana kallon Khaleel yace "kaga fa kar ka mayar da mu kananan mutane a nn Khaleel, ko kana shaye shaye ne wae" a raunane Khaleel yace "wllh wllh Abba bani ne na rubuta takardan ba, ban saketa ba ku yrda dani, its a set up I think" shiru duk suka yi suna kallonsa kowa na nasa tunanin a xuciya, Abba ya sauko rike da takardan ya mika masu ya koma ya xauna, warware takardan dad din Khaleel yyi lkci daya ya juya yana kallon Khaleel da mmki fuskarsa daure yace "whose writtin is dis" Khaleel ya xaro ido yana kallonsa gabansa na wani mugun faduwa, Abba ya jefa masa takardan ya dauka da sauri don ko kadan shi bae lura ma da rubutun ba ranan da Ashnaah ta basa, sake takardan yyi ya fadi kasa da wani irin shock, Abbansa da tuni ransa yyi mugun baci yace "lallai ka cika mahaukaci khaleel, kar ka raina mana wayo a nn, ka ga mun yi kama da yara ko marasu sanin ciwon kai, be careful fa" mikewa yyi a fusace yana kallon abokansa yace "plss ku tashi mu tafi, Allah ya ba mu alkhairi Alhaji" rikice masu Khaleel yyi ya dinga rantse rantse shi ba shi ya rubuta takarda ba, ya xamar masu kmr wani xautattce, Abban Ashnaah yyi murmushi yace "to ko da saki daya dan ku yyu ma 'ya ta banga dalilin da xan bari ta koma gidansa ba sae dae muje duk inda xa mu, ku dan ban lkcinku ku saurari abinda yasa nayi wnn furucin ba cin fuska ba" komawa Abban Khaleel yyi ya xauna, Abba ya shiga masu bayani a nutse ynda aka yi Khaleel ya auri Ashnaah snn ya kara masu da duk bayanin da Ashnaah tayi masa daxu, Abban Khaleel ya mike yana murmushi yace "ae hkn dai dai ne, kuma Alhmdllh da ta ga takardan, Allah kuma yyi mata sakayya" sallama yyi masa snn suka fice da abokansa da duk suma xancen bae masu ddi ba suka bar Khaleel nn xaune, da kyar ya isa gida a motarsa yana ganin double double, umminsa dake falo ta mike a rude yanayin da ta gan dan nata, ya xube nn gabanta ta duka da sauri tace "ya aka yi kuma? baku je bne?" daura kansa yyi a kafadarta ya shiga hawaye, rungumesa tayi a rude tace "ka gaya min ya ku ka yi son" kasa cewa komae yyi, hkn yasa ta dago sa suka nufi sama ta shiga bedroom dinta da shi ta sa ya kwanta ta xauna gefensa, ba a dau lkci ba bacci ya daukesa tayi shiru tana kallonsa, tasan jiya kwata kwata bae runtsa ba don a dakinta ya kwana, komawa falo tayi a sanyaye ta ci gaba da abinda take, can wajen azahar Khaleel ya tashi, sae da ummi ta tilasta masa ya ci abinci ya sha tea snn yyi sllh. Tana xaune gefensa bayan ya idar tace "ka gaya min ynda aka yi son" a sanyaye murya can kasa yace "mum its a set up, I knw it is, da writtin dina aka yi rubutun no body will blive I wasn't d one dat wrote it...." Kasa ci gaba yyi ta dalilin tokarewa da muryarsa yyi, lkci daya idonsa ya kada ssae, yana girgixa kai yace "I dont think xan iya rayuwa ba ita Ummi na ku taimake ni plss" hawaye ya gangaro idonsa, hawaye ne ya cika idon Ummi a hnkli tace "wa kke tunanin xae maka hka," shiru Khaleel yyi kmr me naxari snn ya mike tsaye da sauri yace "Ameesha! Ita kadae ta iya kalan rubutu na," makullin mota ya dauka da sauri ya fice daga dakin Ummi ta bi sa da sauri har kasa tana kiransa amma tuni ya shige mota ya figi motar yana danna horn aka bude masa gate ya fice a guje.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
71.....
A waje Khaleel yyi parkin bae ko kalli masu gadin da ke gaishesa ba ya nufi cikin gidan da sauri, bae samu kowa a falo ba ya nufi sama fuskar nan tasa bbu alamar rahama ya bude kofar Ameesha, xaune ya sameta gaban madubinta idon nn nata yyi jajir da ganinta kasan ta ci kuka, ya nufeta ya fixgota lkci daya ya watsa mata wasu tagwayen mari masu lfya yana huci yace "ke kika rubuta takardan saki ki ka ajiye dakina don fateema ta gani ko, ki fada min me nayi maki a rayuwa kika min hka, duk halaccin da na maki na aure ki duk da ba son ki nake ba da wnn kaxamin aikin xa ki biya ni is dis my reward? I knw uwar ki ce ta sa ki 3dayz bck da ta xo, confess dat kar in hallakaki" cikin tsawa ys karashe mgnr lkci daya ya kuma watsa mata wani marin ya hade ta da bango yana huci idonsa yyi ja ssae, cikin kuka ssae muryarta baya fitowa ssae take cewa ban gane me kke nufi ba Khaleel, hw dare yhu xaka dinga duka na me nayi maka, bata rufe baki ba ya shaketa, ba karamin wahala ta sha ba ranan don dukan fitan hnkli ya mata, duk ya xama kmr wani mahaukaci, ya fice daga gidan. Ashnaah na xaune dakinsu ta jingina da gado Ashfah ma na xaune sae hiran film din da ake a tv take mata, ko kadan Ashnaah bata san me yar uwartata ke cewa ba, tayi xurfi cikin tunanin da take Ashfah ta dafa kafadarta jin ta kirata ya fi sau uku bata san tana yi, a dan tsorace Ashnaah ta dawo daga tunanin da take ta ce "me kika ce" Ashfah tace "Haba sister, wae tunanin meye hka kike, ain't yhu happy kin dawo cikinmu ynxu, wats ur prblm plss tel me" Ashnaah ta kirkiro murmushi tace "nothin sister just thinkn of my past" Ashfah tace "forget dat plss its nt worth rememberin, ko baki yi farin cikin dawowa cikin mu bne" Ashnaah tayi murmushi tace "am happy sister" Ashfah tace "to bana son in kara ganin kin yi shiru hka pls" Ashnaah ta gyada mata kai kawae, dai dai nn wayar Ashnaah ya shiga vibrate, Ashfah ta miko Mata ta karba a sanyaye tana kallon screen din, usman ta gani ta mika ma Ashfah tace "ki ce ina wanka bana cikin mode din mgna" Ashfah ta karba tayi ynda tace mata snn suka yi sallama suka ajiye wayar, Ashnaah ta dubi Ashfah tace "har an kawo kayan nawa ne?" Ashfah tace "wae masu gadin basu Bari ba wae mai gidan baya nn" Ashnaah bata ce komae ba, Ashfah tace "wae Abba yace mu je ki gaida inna anjima" kai kawae Ashnaah ta gyada mata, aka bude kofar dakin momy ta shigo tana kallonsu tace "abincin waye har ynxu a kitchen," Ashfah tace "na Ashnaah ne wae bata jin yunwa" momy ta hade rae tana kallonta tace "wae wani abu na damun ki ne, ina fa sane da safe baki yi wani kwakwakkwaran kari ba," mikewa Ashnaah tayi tana kirkiran murmushi tace "kallo mu ke ne momy ynxu xan je in dauka" ta gefen momynta ta bi ta fita, momy ta bita da kallo snn ta juya tana kallon Ashfah tace "wae me tace maki ke damunta" Ashfah tace "ynxun nn na gama tambayarta tace wae kawae past take tunawa" momy bata ce komae ba ta juya ta fita. Ashnaah ta sauko downstairs ta nufi kitchen don daukar abincinta da ya kusa awa hudu a ajiye don har an kusa gama na dare, bin ta da kallo Abbanta yyi, ta fito daga kitchen din rike da abincinta xa ta koma sama ys kirata, a sanyaye ta karaso falon ta duka ta amsa tana kallonsa, ya ajiye remote din hannunsa yana kallonta yace "kina da damuwa ne Fateema" ta girgixa masa kai tace "A'a Abba daga bacci na tashi" Abba yace "ok, gobe sae ki shirya driver ya Kai ki sch, kun kusa fara jarabawa ko?" Ta gyada masa kai tace "eh sae next wk xa mu fara wae, amma ynxu sae upper wk" yace "to shknn ki dage da karatu kin ga an wuce ki ssae u have to work hard to meet up" ta gyada masa kai tace "in sha Allah Abba" mikewa tayi ta dauki plate din abincinta ta nufi sama. Khaleel na komawa gida ya shige bedroom dinsa ya saka key ya shiga neman layin Najeeb, bugu daya ya daga, a raunane Khaleel ya shiga cewa "I need yhu plss ka xo ynxu Najeeb" bae jira cewarsa ba ya kashe wayar ya dafe kansa dake juya masa. "Ae ni bbu abinda xan ci gaba da ce maki da ya wuce Allah ubangiji ya kara maki, banxa kawae da bata yo halina ba, me gare Khaleel da har kika nace masa? Ya nemi kashe mana ke, ae sae naga uban da ya tsaya ma Khaleel a garin nn, xae san ya taba min ya ta, sae inda karfin ya kare wllh" cewar mahaifiyar Ameesha ga Ameesha dake kwance bbu abinda take furtawa sae wayyo Allahna, Alhaji mukhtar da ke xaune
Sae girgixa kafa yake shi ma fuskar nn tasa a daure ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. Najeeb yyi shiru yana kallon Khaleel bayan ya gama jin bayaninsa, Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye a sanyaye yace "plss don't b surprise frnd, wllh ni kaina nasan na kamu da son fateema da dde wa, help me plss give me a solution to dis prblm I beg yhu" dafa sa Najeeb yyi a hnkli yace "its OK frnd, ka bani address din su Fateeman, I
will c wat to do"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 29