Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masa caaa kowa na nuna masa cewa abinda yayi bai dace ba. Bala ya mika masa ledar kajin da kayan tea yace ka gani ta kan sauri har zan tafi da cin hancin da xa a bawa amaryar. Mahmud ya amsa ya koma ciki. ME ZAI FARU? Daidai wannan lokacin nfsa tana kwance kan tsalelen gadonta tana sanye da kayan bacci masu santsi da ta kalli kanta a madubi sai taji sha'awa ta sake bijiro mata taja tsaki a fili take cewa ace ranar da aka kawoka mijinka yayi tafiya?danginta yan rakiya da kawayanta suna tafya shima ya shigo yana bata hakuri cewa xai tafi america don Allah tayi hakuri. Ranta ya baci sosai tace suje tare yace babu halin yin hakan kada ta damu sati1 kawai xayai ya dawo amma hashi yau 10 days yadai ce gobe xai dawo shi yasa ma da ta aje kayan matan da take dirka sai yau ta ciro tana sha saboda gobe xaya dawo. Wayarta ta soma ruri ga xaton ta shi ne amma tana kallon fuskar wayar safina ce tace soyayya ta rufe jinki da ganinki kawata ko ki kira mu kiyi man ban gajiya? Nfsa tace yi hakuri safina kina raina ya gajiya na fa gode. Safna tace ba damuwa kin san Allah kawata kin dace duk ckin kawayanmu babu yake,inaga fa kashe auran nan xanyi na rabonan ko xan samu shigen naki don samun irinsu sai sa'a. Nfsa ta saki dariya sannan tace baxan so kiyi ma Alhaji sani haka ba,nfsa tace nafa gaya miki matsolilinsa 2nda ya kai ni gdansa aka gama amarci ke bamu ma gama amarci ba ya watsar dani yaci gaba da bin matansa. Kudinshi kuwa sai dai in nagani na sata,sisin shi ya daina bani in kuma in na satan yaxo yayi ta bala'i rannan har da marina. Mari inji nfsa?safina tace kinji kadan. Nfsa tace lallai to kiyi dai mai yiwuwa safina tace ai shi ne nake son yi yanxun xan dai kiraki. Amma abubuwan da kika sha nasan kin rikita angon ko? Nafisa tace, kuna tfy aka kira shi mitin America, gobe zamu soyewa sai dai kin san wata matsala? Safina tace sai kin fada, tace samun kaina danayi cikin gidan nan in ci, in sha in baje a gado ya dawo min da son mahmud sabo dal. Safina tace, ke dai sakarya ce, dubi motocin daya nuna mana yace naki ne guda 5 duk manyan motoci me zaki tuna wani mahmud? Kin ma san yayi aure ko? Nafisa ta mike tsaye ta ce, "Aure kuma? Ina..." wace ya aura... Santa yake? Na shiga 3! Safina tace nima ina gida lbri yaxo min ynda aka ce min ikilimarku ya aura..." sam bata san lkcin da wayar ta subuce daga hannunta ba, ta dora hannuwanta akai tana zaga dakin, komai ya dagule mata kai wannan mummunan lbri Allah yasa mafarki ne. Tabdi! In ko ya auri iklima ya kasheta domin hakan yana nufin sun rabu tnda sun zama surukai. Hawaye ya shiga sintiri akan fuskarta. Da tayi kukanta ta gaji sai km zcyrta ta shiga saka mata cewa kila karya ne, dn haka taxo inda ta yar da wayarta ta dauka ta kira mamansu cikin kuka tana tambyrta wai haule gaske ne iklima ta auri masoyi na?" Haule don ta kwantar mata da hankali ta ce, ke karyane, ikilimar da naga an nuno ta suna gasar kara2 a saudiya! Nafisa ta sauke ajiyar zucia tace har naji dadi. Haule tace ke da ke gidan wani ina ruwanki da shi? Nafisa tace tab! Har gobe ina son shi, sannan ta kashe wayar. Ta zauna ta zuba tagumi ina ma yana da waya da ta kirashi taji muryar nan tashi mai taushi. Kai ranar dai nafisa b barcin kirki, kwana tayi tana juyi cikin mayen son mahmud tare da begen shi game da tsantsar sha'awar sa. Washegari uku daidai alhaji jamilu ya shigo, tana sanye da riga da wando irin masu rawa din nan dama gashi ta kware wajen juya jiki, bata sa komai ba sai wadannan kayan ta zubo gashi baya. Da gudu taje ta rungume shi, amma ga mamakinta sai ya cire ta daga jikinshi, ya dube ta fuskar shi da murmushi yace na sameki lafia? Tace lfy lau, ya nufi sashenshi ta bishi, biye dasu km yaranshi ne dauke da jakarsa. Kayataccn falon ya bude suka shiga, yau ita ce ranar farko data shigo gefen nashi, gurin kam ya tsaru. Ya zauna kan wata kujera wadda ita kadai ce kalarta daban a cikin falon, tamkar ta zinare. Yaran suka shiga dakin bccnsa suka ajje jakar sannan suka fita tare da cewar mun brka lafia yallabai. Ta dube shi za a kawo ma wani abu ne? Da murmushi yace "je ki huta" ya danna wani guri sai ga makel shugabn kicin kenan. Makel yai gaisuwa, alhajin ya amsa sannan yace hna son abu mara nauyi da mai sanyi. Makel ya fita tare da cewa "To". Dk nafisa na zaune a hannun kujerar dake kusa da alhajin tana kallonsu. Ya dawo a jikin kujerar ya danna wani guri sai ga tebur ya fito na gilash nan ya shiga jera abincin, ya gama ya fita. Tace in in baka? Yace ki huta madam, ke ai yar hu2 ce. Yasa hannunsa ya ciro hakoransa guda 4 na gaba, ashe dk na roba ne ya aje su cikin wani abu. Da ta dube shi sai taga ya bata tsoro, ya cgb da cin abincin sa ya gama ya maida su ya mike tare da cewa bari inyi wanka. Tace "ko nazo muyi ne? Nan ma yace ta huta. Ta zame kan kujera ta zauna tai jugum ta zabga tagumi, ynda ta ganshi ba hakoran gaba din nan dk sai taji ya sure mata. Abinda yafi daure mata kai, da dare takai kanta gurinshi yana zaune yana waya sanye yake da kayan bcci, itama cikin kayan bccn take irin masu mannewa a jiki tare da fidda surar jiki. Dole ne dk lafiyayyen namiji inya ganta hnklinsa ya tashi. Amma shi sai yace bakiyi bcci ba? Tace "Eh" yace ya kamata ki kwnta. Ta xuba mishi idanu tare da cewa jikinka zan kwana, yayi murmushi "au bn sanar dake ba ko? Ya iso kusa da ita, ni ba namiji bane. Ina nufin bazan iya amfana ma mace komai ba Gabanta ya fadi ta dafa kirji shine ka aure ni? Dama dn kawai ka kalle ni ka aure ni? Yace, kwarai ina son zan tsaya takarar dan majalisa to kinga be dace ace bani da iyali ba, ya iso inda tayi mu2war tsaye yace karki damu kudi dai masu suna kudi zan jibge musu ga babban gida da manyan motoci a zatona baki da matsala? Ta girgiza kai, kayi kuskure dk mace mai lfy tana bukatar namiji musamman wadda ta samu hu2 iri na, dn haka kawai ni ka sawwake min". Ya kyalkyale da daria me karfi sannan yace "yaro be san wuta ba sai ya taka" ya ciro wata doguwar takarda a tsakiyar littafi "Ga wannan lissafa, ina zaton in kinbi a hnkli zaki gano lissafin daki-daki, ki maido min da kudina sai na sake ki kawai Total din ta soma kallo, taga an rubuta miliyan dari uku da dubu 6 da dari 7 da hamsin. Nan take ta soma ganin jiri tare da kallon shi yace ki lissafa naira daya bn kara ba, lallai baku da hankli da kike ganin tamkr bn san ciwon kudina ba, ko da nomansu nayi ko hako su nayi dole in san ynda xan kashe su. Amma rannar farko dana fara ganinki anyi miki tayin kudi kika dibi miliyan daya bb dubu dari, yayi yar daria sannan yace tn lkcin nasan ke ba karamar muguwa bace a fagen son kudi" ya cgb da cewa "ynxu ina so kije dakinki ki lissafa ki gani sannan ki zabi daya, zaki zauna ko zaki biyani kudina ki kama gabanki? Ta dafa bngo ta juya shi km cikin murmushi yace "kwadayi mabudin wahala". Ta zube a tsakar daki cikin matsananciyar dmw, zufa tana kwaranya dg jikinta dk da karfin (AC) din dake dakin. Abin al'ajabi alhji jamilu ya soma lissafi ne tn daga kudin daya lika mata har xuwa na man motar da aka maida danginta gida lkcin dasuka yo mata rakiya. Kudin daya bata da gidn daya sai ma mamanta dk suna cikin lissafi, hatta likin dayayi a bikin su, mai hoto da na bidiyo duk kowanne da date da time, da km kudin da aka kashe har da rasitai ma ga sunan. Nafisa ta ajjiye takarda tana ta shiga 3 ni nafisa, ta dau wayarta ta shiga kiran layin haule. Cikin zumudi haule da daga wayar, numfashinta ya nemi daukewa jin nafisa tana rera kuka. Tayi saurin jawo shi sannan tace wace kyauta ya miki mai dadi har ta saki kuka? Nafisa tace "kinji fa haule, ashe alhji mugunta ce tasa ya aure ni, shi ba namiji bane, wlhi baya iya amfana ma mace komai, ya raba ni da masoyina" ga mamakinta sai taji haule tace "To ke ina ruwanki, kin huta ma da damu". Nafisa tace "bazan zauna ba, ya dai ce mu dawo mishi da dk abnda ya kashe mana daidai da ruwan sha da aka siya na bikin ya lissafa kudinsa miliyan dari 3 har da dubunnai". Haule tace "to ke bnda hauka irin naki baga kudi ba? Kwntr da hnklinki kici inya mu2 kin haye. Nafisa tace ni dai ki harhada kudi gurinki ne baxan xauna ba xanxo ne in auri mahmud dina" haule tace "duba nan nafisa, ki samu nutsuwa, mahmud fa ynxu baku da aure don gskiyar magana ya auri ikilima tn kafin a daura naku..... Da karfi tace, "ikilima? Na shiga 3. Ta yar da wayar da takardar, sannan ta zube kan gado tana rera kuka. Alhji jamilu ya shigo yana daria. Madam dama baki san masoyinki ya auri kanwarki ba? Ya xauna kusa da ita, "sakamako kenan na toxarta shi da kikayi. Ko lkcn da kika ce auren dole za a miki dashi naji ki ne kawai don ina da lbrin dawainiyar daya muku. A ynxu lkci ya kure, gara ma ki zauna ki huta yar hutu. Ga babbn gida ga manyan motoci, a sanina burinki be wuce wannan ba. Amma ki bari gobe xan kaiki gidan hajara matar alhji kabiru ta baki shawara". Ya miki tare da cewa sai da safe yar hu2. Ta bishi da kallo har ya fita ta sake fashewa da kuka tare da fadin "Na shga uku!!!"s BOOK MABUDIN WAHALA 2***1 A DAKIN AMARYA Ya shigo da sallama cikin dakin,ya xauna kan kujera sam bata ji ba tana cikin dakin tana ninke hijabinta ta gama ta fito don kwashe plate din da ta kawo ma abokan ango cin cin sai ta ganshi xaune kan kujera shi kam bai ma san ta shigo ba yana duniyar 2nani. Sam baxaya iya fassara yaya yake jin lamarin ba,muryarta ta katse shi da cewa sannu ka dawo?ya daga idanunshi masu cike da damuwa ya xuba su kan fuskar iklima yarinya mai kalar madara in an hada shi da bournvita idanunta farare tar masu kalar tashi daga bacci duk da basu kai girman na nafsa ba amma sun fi nata ban sha'awa daga ganin fuskar xata yi laushi ba irinta nfsa ba da man bilicin yasa mata kuraje,lebunant a yan yala yala hancin ta bashi da tsawo amma ya dace da fuskarta mai dan tsawo. Yace sun tafi tace kaima na xuba maka cin cin din?ya girgixa head tare da kishingida ta koma ciki tayi alwala a bayi taxo ta tada nafila gami da shafa'i da wuturi sannan ta canxa kayanta xuwa doguwar rigar bacci wadda ita kadai aka sako cikin kayan lefen ta saka ta kwanta tana gama addua bacci yayi awon gaba da ita,shi kuwa ya jima idanunshi basu daina ganin hoton fuskar iklima ba duk da ba xaya ce sonta yake ba,ba xai ce bata da kyau ba kyawunta irin sassanyan nan ne matsalarta rashin wayewa,sam bai san lokaci ya tafi ba,sai da ya dubi agogon hannun shi 2 na dare xufa duk ta jika shi saboda yanayin xafin da garin minna ke da shi duk da cewa damina ce. Ya tashi yana son watsa ma jikinshi ruwa sai dai baya son shiga bedroom din nasu dama ya kawo kayan shi ne da ya kunna fanka da yaga bashi da yanda xayayi sai kawai ya danna kai cikin bedroom din. Idanunshi suka sauka kanta,tana baccinta cikin kwanciyar hankali fuskarta tamkar tana murmushi, gashin kanta ne ya fi daukar hankalinsa ya bazu kan filo wasu kuma sun sauka kirjinta. Ya 2no nfsa nata iyakarshi dokin wuya amma birge shi yake yi ita wannan nata har kirji sai dai shi ba ya kyalli irin na nfsa. Ya jima yana kallon kirjinta xuwa hips dinta yana ganin kamar tafi nafsa jki sai dai nfsan tafi ta sarrafa jikin ganin tayi motsi ne yasa shi nufar bandaki don kada ta tashi ta gane tsaye kanta. Lokacin da ya fito tayi juyi ta koma rigingine ya sake xuba idanunshi kanta yana tafiya har yaci karo sannan ya fita,rataye kayanshi yayi ya kwanta daga singileti sai gajeren wando (Boxer) ya kasa runtsawa domin gizon da take mishi. Da ace nfsa ce yau kam yasan baxaya barta ba,ita ce ma xata taimaka burin shi ya cika,ita ko wannan kila ma in yace ga abinda yake so gareta ta raina shii 2nda ba wai son shi takeyi ba, tada sallar da masallacin kusa da su suka yi ne ya tada shi daga baccin mai cike da mafarkin yarinyar wadda ke matsyin matar sa yanzu. Ya dan ja tsaki domin ya xamar masa dole yayi wanka gashi bai kawo suturun shi ko1 gidan ba dole sai dai ya shiga daga shi sai singileti din da boxer in ya fito ya saka kayan shi ya rataya rigar a kafada yayi ciki tashin ta kenan tana xaune a tsakiyar gadon shigowar sa yasa ta rufe jikinta sannan tace mun makara ne? Yace a'a yanxun aka tada sallah ya shige toilet din,ta bishi da kallo. A ranta tace suffar shi ta asalin jarumai maxa masu lafiya da kuxari daga ganin shi kasan ba rago bane. Tayi maza ta canza kayanta kafin ya fito yana fitowa ya saka rigar shi ta shadda yana rike da singletin da boxer din ta amsa tare da cewa kawo,ya bata sannan ya fita falon ya saka wandon sa ya nufi masallaci ita kuma ta shiga don yin alwala tare da saka kayan nashi ckin wani bokiti. Tana kara2n kur'ani mai girma lkcn daya dawo, ya xauna nan falon da ta gama tayi addu'a ta tashi. Shi dayake falon ma ji yake tamkar kar tayi shiru, da dayake jin kara2n nata cikin wayoyin mu2ne da redio yin jama'a ya xaci an goge ne cikin computer an sirance muryar, ashe tata ce. Hakan nan shima mata da maxa suna son kara2n. Ta fito sanye da hijabi itama ta xauna kan kujera tace, "yaya mahmud ina kwana"? Ya amsa ba tare daya kalleta ba sannan fuskar sa ba yabo ba fallasa. Tace mun kwana lfy? Yace "Alhmdlh". Ya miko mata ledar gefenshi ta amsa tare da budewa ta leka, kazar jia ce da kayan tea da bread. Ta dubi fuskar shi "bari na hada rishon, sai dai kalanzir ne matsala. Yace bari na dauko hita a dakina" ya mike tace to ka dawo lfy. Ya sake dubanta sannan yace Allah yasa. Kafin ya dawo ta wanke bayinsu ta gyara gadonta tare da share dakin ta goge. Ta duba cikin akwatinta ta ciro turare ta dinga fesawa a dakin, duk da cewa na jiki ne. Tazo kasan gado tana ciro kayan girkinta. A fili tace, gaskia ina da bukatar kayan aiki. Ta hada risho sannan ta fitar da kofunan roba da jug dinsu, ta fita ta wanke su ta dawo. Sauran matan gidan duk suna cikin dakunansu. Ta bude kicin din shima ta share sannan ja zuba kayan girkinta ciki. Sai gashi ya shigo, ya dube ta, "tsakar gidan ma har da wani uban hijabi? Cikin xuciarsa yayi maganar. Sai dai ta lura da ynda yadan hada rai. Da sauri ta amshi jakar hannunsa tare da cewa "sannu da xuwa" yace "yauwa. Ya juya. Ya sake shigowa da akwatin kayansa ya shiga dasu ciki, tace kazo da hitar ne? Yace "eh, gata can cikin ledar can har da dutsen guga na soma rago kayana ne. Nan ta jona masa ruwan wanka dayayi xafi ta juye cikin buckt ta kai bayin ta sirka masa, sannan tace ga ruwan wanka kafin ka gama wannan yai xafi". Ya dubeta "na gode" kafin ya fito ta shirya kayan tea cikin wani tire da flask din ruwan zafi. Ya fito ya shafa man shi wnda yaxo dasu cikin jaka, ya saka kananan kayansa blue jeans da jar riga, yayi kyau. Yasa turarukansa masu kamshi. Mahmud akwai tsaftar gaske. Ya fito tana ciro takalmansa daga cikin wata leda baka dayazo dasu, ta gama curowa tasa kyalle tana goge su, ta shigar masa dasu ciki byn ya dau wnda zai saka. Ya shinfida darduma ya zauna kasa yace yafi son cin abinci yana zaune kasa. Yace "to zo mu karya. Tace ni ynxu zanyi wanka ne, in na gama zan karya" yace "okey, bari in jira ki. Taxo ta zauna "ra'ayinka za'a bi, bari mu karya din. Tasa karamar wuka tana yanka mishi naman kazar byn ta hada mishi tea din. Ya dauki kofi shima ya hada ga zatonta zaya ce baya son wnda ta hada ne. Ya gama sai taga ya miko mata yana murmushi. Ta karba tare da cewa na gode. Kadan-kadan take kurba don tana jin nauyinsa. Dakin ya tsit don basu saba da juna ba yace "kinki ci bread din, ga naman ma" ta dube shi "nafi son lipton. Ya kalli kofin ashe ko madara baki so, meyasa? Tace na'a- na'a kawai nake sawa. Ya dubeta meye wannan? Ta danyi murmushi, wani ganyen shayi ne muke amfani dashi sbd yana gyara mana murya gurin kara2, bama samun matsala. Ya kurbi shayin "kin san mun taba musu da nafisa nace ina zaton ana goge karatn ki a computer tace min a'a wai muryarki ce" ta dire cup din tare da hamdala sannan tace "dayawa mutane haka suke cewa, amma ba hakan bane" ya dire kofin sa "bari inje xan turo yara da kalanzir din. Zan tattara kayana guri 1 in kawo in bazan takura miki ba sai ki dafa mana wani abu ko? Cikin idanunshi manya masu yalwar gashi ta kalla fuskarta dauke da mamaki tace "umarni kawai ya dace ka bani ba neman taimako ba, me kake son a dafa? Yace duk wanda kika so, sai dai ina zatn su muktar zasu zo. Tace to bb dmw, sai ka dawo" ya fito ta biyoshi har bakin kofar daki tace sai ka dawo yace to Tayi wanke-wanke lkcn matan gidan sun pito bakin pampo suna aiki,ta gayshe su suka amsa cikin sakin puska tayi wanka tare da kwallia ta saka wani yadi riga da wando cikin kayan akwatinta,ta shapa turare. Sallamar yara taji ta pito sukace aunty ina yini? Tace lapia lau sukace yaya ne ya aikomu suka mika mata kalanzir da kayan miya da nama da kipi,ta basu cincin da alkaki tare da tambayan sunayensu,suka gaya mata tare da cewar sun tapi tace to ta goday su gayshe da mutanen gidan. Yaran suka pito suna murna tare da yaba halin auntien nasu. Nan iklima ta para tunanin me xata para dapawa a matsayinta na amarya shirya musu talia tayi ta wadata ta da kipin da naman da kuma kayan lambu wanda ta bada kudinta aka siyo mata ta xuba,gidan ya cika da kamshi 2 dai dai suka shigo lokacin ta gama komai ta xira hijabi ta pita ta shirya musu komai sannan suka gaysa ta koma ciki. Tana jiyosu suna ce mishi,ai wannan tapi ma napisar da kakeso kyau gata kamila. Shi kuma yace ina be yadda ba napisa tana da kyau ga wayewa ga kuma son da yake mata. Dik suna batun ne a hankali amma kuma dik sunaji,sai dai dik da ba sonshi take ba bataji dadin abinda ya pada ba. Tana kwance tana tinanin cewa kenan xai xauna da itane yayarta na xuciarshi alhalin itama tana da wanda takeso kuma ta hakura? Muryarshi ce ta katseta inda yace mun wuce suna ta miki sallama. Tayi ajiyar xucia,sannan tace to sai ka dawo su kuma tace mun gode ku gayda gida. Sukace sune da godia,daganan bai shigo ba sai bayan sallan isha'i ya shigo da kankana da lemo da abarba. Tana xaune a parlour tana karatun Qur'ani, tayi mishi sannu da xuwa sannan tace ko xaiyi wanka? Yace ehh. Dama ta dapa ruwan sai kawai ta sirka kapin ya pito ta hada mishi kayan itatuwan da yaxo dasu cikin plate. Cikin shirin bacci ya pito palon ya xauna tace ga tuwo da aka kawo mana daga gidanku yace xanci kadan dama sun sanni da son tuwo shiyasa suka aikomin. Ta xuba masa yanaci sai yace itapa ? Tace ta koshi. Ya daure puska tare da tsareta da ido kinason ace bana kula dake ko? Dik yau ruwan lipton kawai naga kinsha tace naci abinci daxu yace oyah! Matso kisa hannu mu ci,dama nima yayi min yawa dama shi ba gwanin daria bane,ya tsare gida gashi yana da kwarjini matuka yanda baxa ka iya jan musu dashi ba dan haka sai ta matso ta saka hannu. Ya kalli xara-xaran yatsunta meyasa bakiyi lalle ba? Tayi dan murmushi ban sami lokaci bane saboda shirin tapia da mukayi a lokacin yace hakane, na manta ban miki jinjina ba,sai dai naso ace kece ta parko ina nupin ta 1. Tace ta biyun ma ban saka rai ba dan dik nice karama cikinsu kuma suna da ilimi sosai yace haka, kinyi kokari. Ta tashi da dauko mishi ruwan wanke hannu ta dire a gabansa tace kyauta ya dace ka bani ya dan murmusa ki bini bashi tace ina wasane pa yace nikam da gaske nake xan baki wata rana tace nagode ya sake dubanta cikin idanu tin kapin kiga kyautan kin para godia? Ke kam kina da yawan yin godia. Ta murmusa tare da tattare kayan ta kai kitchen ta kulle itama tayi shirin bacci. Yau ma tamkar jiya falo ya kwanta yana ta sakar zuci shi kam mabuqaci ne amma girman kai yana so ya cutar dashi yanda ya lura da ita sam ba zata yi taurin kai ko wahalar sauraronshi ba. Ita kuwa ta fi tunanin kaninta nafiu da mahaifinta,bata san me girka musu abinci ba,gashi nafiu bai zo gurinta ba bare ta ji labarin baban nasu,Allah ya dai turo mata keyarshi,haka suka kwana. Nafisa zaune tsakiyar gadonta hawayenta sun kasa qafewa.kenan haka zata yi rayuwarta ita daya? Kai da sake! Ita ba zata iya ba domin ubangijinmu bai halicci mace don tayi rayuwa ita daya ba wannan ma wani nau'in azabtarwa ce da Alh jamilun yake son yi mata. Sallamar anty hajara ce ta dawo da ita cikin tunanin. Hajara ta shigo sanye da doguwar rigar atamfa 'yar holland fara mai ratsin ja,gyalenta da takalmin da ta saka ma duk jajaye ne. Ta zauna. Kusa da nafisa tana murmushi ta ce "kanwata kukan ne dai?" Nafisa ta matso ta kwanta jikin hajara tana cewa, anty hajara ki taimake ni na saba ma mahaifina na ci amanar masoyina na haqiqa gashi tun kafin aje ko'ina na soma yin nadama. Hajara tana dan bubbuga bayanta tana cewa "yi shiru ki tashi muyi magana,nima abinda ya kawo ni kenan" ta share hawayenta ta gyara zama ta dubi hajara ta ce "dama alh jamilu ba namiji ba ne?" Hajara ta ce eh,ta ce wlh da ya fada min ba zan aure shi ba. Hajara ta ce duk kin damu kanki,budurwa wadda bata san ya ya namiji yake ba bana zaton zata damu kanta. Nafisa cikin damuwa ta ce "ba zan boye miki ba anti hajara nasan da namiji" Hajara ta ce "to ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki domin ba zai sake ki ba sai kin ba shi kudinshi in ko kin zauna a jikinshi ma sai ki tara ki bashi abinsa ki huta. Kuma yanzun ne ya dace ki saki jikinki ki kwashi kudin in ki ka ci gaba da kunci ba zai sakar maki ba,ni kaina ina da tawa matsalar in kin nutsu za ki fahimci komai ke kusan duk wata mace da ke zaune garin abuja ko bata da matsala to tasan wata ko maqociya me fama da shigen tamu matsalar. Nafisa ta ce "anty fayyace min" ta ce sai kin kwana biyu kin soma gano lamuran yanzun dai ina so ki saki jikinki kada ki fada ma kowa hatta mahaifiyarki. Nafisa ta ce,har kuwa na fada mata. Anty hajara ta ce,kash kinyi gaggawa to me ki ka ce mata? Ita kuma me ta ce? Nafisa ta ce, na fada mata cewa shi din ba namiji bane. To me ta ce? Nafisa ta ce,cewa tayi wannan ba matsala ba ce da zata sani na bar daular da nake ciki har ma tayi ikirarin tsine min in na ce dole sai mijina ya sake ni. A cewarta bata da kudin biyansa,kuma ta soma sabawa da daula ba za ta iya hakura ba,a karshe ma cewa tayi sai na biya ta nononta in har nayi mata asarar zuwa aikin hajjin bana wanda Alh jamilun yayi mata alkwari.Anty hajara tace,to kin ma ji mahaifiyarki,sai dai koda za kii ga ko ki ji wani abun nan gaba wannan sirri ne tsakaninki da mijinki kada ki fada ma wani. Nafisa ta ce,shi kenan. Hajara ta ce "yauwa,ki kwantar da hankalinki,duk abinda ya shige miki duhu ki fada min zan bude maki haske. Nafisa ta ce to.tun daga ranar Nafisa ta hakura,kudi kuwa sai dai ya nuna mata in da zata dauka,in dai karamar bukata ce in kuwa babba ce zai tura mata cikin account. Damuwarta da abinda ke sa ta kuka kullum shine rasa masoyinta.Motoci luwa duk wadda take so zata hau,'yan aikinta ne dai suna ganin wulakanci da iya yi. Kullum dare in ta kwanta kewar kasancewa da masoyinta ke hanata bacci don haka maimakon kyau sai ta shiga rama.Alhaji jamilu kuwa ba shi da lokacinta sai dai ta waya.haka nan ya tsani taje mishi sashe har da maigadin gurin,tun tana jin haushi har ta hakura. Yau gidan anty hajara tayi niyyar zuwa sun gama gaisawa ta dauki ummi tana cewa "kitsonta ya yi kyau,itama kuwa tana son ayi mata kitso" anty hajara ta ce,ummi kira ladi mai aiki in aike ku.Da ta kira ta, ta ce. Suje su ce ma mai kitso in layi ya ragu tazo zata yi ma baquwa kitso. Suna fita ta dubi nafisa ta ce kanwata naga duk kin fige ya ya ne? Nafisa tayi rau-rau da idanunta hawaye suka soma zirara a kan kumatunta ta ce anty hajara ba zan iya zama ba gaskiya ina da bukatar abokin halitta ta,ke mace ce na san kin san cewa duk macen da ta zama cikin hutu lamuranta basa cika sai da da namiji.Ni kuwa ina mamakin ya ya za'a ce ina da miji daga ka ganshi mai kyau da kuzari amma ace ba shi da amfani a gurina. Hajara tace "to ya ki ke so ayi? Shi dai ba za ya iya

Chapter 8 of 20