Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ya nuna baya so me yasa ta amso? In ma Baban ta ya ji wannan batun ranta zai matukar baci. Nafsa suka yi sallama suka shigo,ta dubi dakin ko ta ina sannan ta zauna a kujera. Iklima ta nata yi musu sannu da zuwa,Nafsa sai ya mutsa fuska take yi tare da toshe toshen hanci,wai warin me take ji? Iklma tace "ba komai,kin ji wari ne? Tace "naji ki shiru ban ganku ba shi ne na biyo. Ita kuwa nafisa jinsu shiru basuzo ba sai tasa aminu ya kawo ta gidan byan magariba. Ikilima ta idarda sallah kenan ta zabga tagumi tana tunanin yadda zata shawo kan mijin nata. Sai yanzu taga wautarta, tun acan daya nuna bayaso meyasa ta amso? Inma babanta yaji wannan batun ranta zai matukar baci Nafisa sukayi sallama suka shigo, ta dubi dakin koina sannan ta zauna a kujera. Ikilima tanata yi musu sannu da zuwa, nafisa sai yamutsa fuska take yi tareda toshe toshen hanci, wai warin me takeji? Ikilima tace bakomai, kinji warin ne? Tce najiki shiru ban anku ba shine na biyo. Iklma ta tashi taje gurin Maman Ummi tace yauwa bani kudin nan dama na Mamana ne ta bani ajiya,ga shi nan ta aiko. Ta zi ta danka ma Nafsa tare da cewa "gashi yaya,nayi2 amma ya ki karba".Nafsa ta amsa tasa a jaka "shi kenan yayi ma kansa. Kice masa duk lkacin da ya canza ra'ayi ina jira. Iklima tace "to zan fada mishi Allah Allah take yi su tafi kafin ya shigo. Haka yayi mata yajin kwana3, kai gsky fada da miji babu dadi hardai irinsu mhmud, don cikin kwanakin ikilima tayi baki ta kuma rame. Hakuri kam ta bashi hartagaji amma bai saurareta ba, damuwaa da rashin cin abinci su suka haifar matada ciwoncikin tamkr mai nakuda cikin dare yana falo inda yayi mata yaji, yajiyo nishinta da sauri ya shigo ya riketa an mata sannu sai 4 saura cikin yadan lafa matada ciwo. Shine barci ya kwshesu har suka makaara. Toh dukda bai saki duka ba ana kulada ita, nan tasamu dama ta bashi hkr sosai yace ya hkra amm kadata sake I mashi makamancin wanan tace insha Allahu bazata kumaba. Sun dawo zamansu daidai saidai rashi domin na cefane babu sai dai yan daabaaru. Ita kuwa nafisa ta koma da takaicin ama tasha alwashin cimma burinta. Taana mamakin wacca irin tsanace wannan harya ki karban kudin hannunta? Dubu goma ta biya aka sa mashi wuta a shago don tayi amfani da wanan damar ta jawoshi da kudi. Sunansa kawai zata kaiwa boka, hakan kuwa tayi lokacin data ama zayyanama boka komai. Saiyace bari yayi bincike, daya gama yace maganin dazan baki sai ya had shimfida dake zaiyi tasiri, zai bar kow nashi bama matarsa ba in har kikayi amfani da maganin saiya zama kina korarsa ma. Wa'iyazubillah! Tace toh abu mai wuyar shine yadda zamu hada shimfida dashi don ba mazinaci bane. Boka yace wanan kuma aikinkine, koki kawo mana hotansa mu turo maki shi har gida, tace to zanga me zanyi. Suka barshi akan zata kawo hoton. Shikuwa mahmud ya maida lamuransa ga Allah kamar yadda ikilima kulum take tausar sa. Yanxun sun rage barci kowane dare suna rabasa wajen kai kukansu wajen Allah, duk da irin sonda mahmud keyima kayan wutansu musaman fridge dole ya fitar dasu suka sayar don babu abinci. Cikinta ya shiga watan haihuwa amma ko pant basu saya ba tunda ba kudi. Asibiti ma xuwanta 1 haryau bata koma ba don sun bata scaning ko nuna masa takardan batayi ba sbd zai damu. Makaranta ma ta daina xuwa tunda ba kudin biya, towa keta batun makaranta? Omo na wanki ma ya gagara, Allah kayi mana da sauki. Duk da wanan halinda suke ciki baisa ikilima daga hankalin mijinta ba. Su maman ummi da matan gidansu hakan yayi masu dadi. Bansan meyasa mata kowane lokaci suke da irin wanan dabi'ar ba wasu matan ko yaushe burinsu suganki kina shan wahala gurin miji ko suga kuna fada ko kuma suga bakuda cin yau balle na gobe. Nan zasu nuna suna son taimakwa idn anyi kwantan abinci a baki dakin juya ayita zundenki inkin fita unguwa a kasa gulmar ki, in ko anga mijinki na sonki yana maki komai shi kenan sai a dauki gaba dake ace kin cika iyayi sai inga wanan ba halin kwarai bane domin malamai suna aya mana; MABUDIN WAHALA 2**7 Manzon Allah (S.A.W) yace; mu sowa yanuwan mu abinda muka sowa kanmu, duk kuma wanda ya rufama dan uwansa asiri Allah zai rufa masa. Ikilima dai ko sun bata abinci bata karba kuma bata taba nuna masu gazawar mijinta ba. Yau sun wayi gari ba suda komai sai shinkafa gwangwani 5, gashi basu dakomai sai gishiri. A hita ta jona ta dafa masu ta ajiye dan shi bai taso bama. Ta zuba cikin kula ta zauna tasa ta gaba tana kallo Wani ciwo take ji can kasan mararta amma ta danne. Ta sameshi zaune akan gado tace ruwan wankanka ya huce. Ya dubeta cikin tausayawa dama baki dafaba yau da zafi sai nayi a shower. Ya shiga yayo basuda sabulu ma da guntun omo ta aijiye mashi turare sannan tace ga abincin sai dai yau abincin namu shine asalin garau garau. Ya bude kular, da miya ne? Tayi murmushi batace komaiba ya gane. Don haka ya rufe bari in fita in samo ko mai ne a saya. Ta rike masa hannu kada ka ciyo bashi fa muyi hkr da wanda ya samu Allah yana sane damu. Yayi shiru sanan yace wanan baxai ciwuba ikilima tace zauna ka dandana zai ciwu mana. Wlh na neman kamar wanan bai samuba zauna ina zuwa, ta nufi kicin ta daga galan din man gyadan ta dina zazzagowa cikin roba ta gama ya dan taru tasan ya isheshi taxo ta xuba masa shinkafar cikin plte ta juye masa man yace kefa? Tace da wani a kicin din yaci harya koshi tanayi masa yar hira cikin dauriya don mararta tana dan ciwo. Tana kai kawon aikin gyaran dakinta ciwon na karuwa daga karshe saita koma daki har bayan laasar sai wani ruwa ke zuban mata. Tana cikin haka ya shigo. Ta zauna cikin dariya yace bakijin dadi ko? Ta kirkiro murmushi meka gani? Yace kinyi wani iri ne tace na gajine. Ya miko mata ledar hannunsa tareda cewa fura da nono aka bani shine nace barina kawo maki nasan kina so. Ta yatsina fuskarta sbd ciwon dayake taso mata tace baxan shaba kasha yanxun ina shan fura kwanarfi take sakani Ameena Baba Suleiman Ta yunkura barina dauko maka kofi ka juye. Yace yi zamanki ya tashi ya fita. Yana shan furar suna yar hira daga baya ya fahimci cewa batajin dadi yace ikeelee baki da lfy? Tace ni nace maka lfy lau ya tashi kona nemo kudi muje asibiti ne? Tace aa ina da kudina in haihuwa ce ai zan fada maka ciwon kaine, yace ba wani kudin dakike dashi don dai kada na ciwo bashine. Tace zauna ni dai muci gaba da lbr kacemin zaka fara binsu hamza aiki? Yace eh, nayiwa su hamzan magana zan dinga binsu aikin gini in sun samu su fada min Cikin tausayawa tace zaka iya yayana? Yace mezai hana? Namijine fani zama bazai minba wlh, yanda nake ji ko dako ne zanyi. Injin nauyi ace ni da zan ba mahifana abu saisune zasu bani. Nine babba agidanmu ya dace ace zuwa yanzun na ragewa babana nauyin wasu daga cikin kannena duk cikin yayansa nine na samu gatan makaranta Tace Allah yasa ka koma cikin saa yace amin. Har bashir dake buga tayals nace musu zan bisu aiki. Cikin dare fa haihuwa gadan gadan ta kuma hanashi kiran kowa wai ya bari saida safe itadai ya riketa. Lokacin haihuwar yaxo gadan gadan kankame shi tayi tana nishi gamida salati iyaka firgicewa mahamud ya firgice ga zatonsa mutuwa zatayi itama hakan ta zata sai fadi take ka yafemin kace dasu baba su yafemin Hawaye sharkaf idanunsa baima san suna zuwa ba. Wani yunkuri guda 1 tayi saiko ga da ya fado ya canyare da kuka take uwa ma ta fado sai taji tamkar an zare mata ciwon. Suka shiga yiwa Allah godiya sai kuma ya tuna ba kaya yace innalillahi wa ina ilaihir rajiun gashi ba kayan baby, tce ka kira minsu hajiya kosu maman ummi yace toh. Ya fada tareda mikewa tace k aya masu saika wuce idansu hajiyan. Maman ummi dukka suka dauki sankacecen yaron mai kamada ubansa sak suka nade shi cikin zani bayan sun yanke cibi sai sannu suke mata. Sai gashi su hajiya uwa da haj rabi nan aka jona ruwaa aka wanke yaro itama tayo sunata cewa tanada juriya, sunyi kokari su kadai basu kira kowaba saida akace ina kaya? Yana jinta daga falo tana cewa basusan lokacin haihuwar yayiba harya bata kudin tace ya bari sai watan gobe Haj uwa taace ina kikaga ana haka? Wanan ai kuruciya ce, to ashi kin haihu babu ko wandon da za'a sama yaron. Nan suka nade yaro cikin zani suka gyara gurin suki nufi gida don yin sallah. Bayan su mahmud sun dawo daga masallaci yazo ya zauna kusada ita ya dauki yaron yana kallonshi Tausayin yaron ya kamashi hawaye suka zubo masa dan shine babu kayan sawa. Ya share hawayen ya kwantar dashi ya fita waje sukaci karo da babansa ya dawo ya fito masada yaron daga aljihu ya bashi ga wann nasan bakada kudi kuma su haj sunce ka bata kudin siyayyar bata yo ba bata zaci haihuwa ba, ai wanan shirmene. Mahmud ya dubi babansa yace baba wlh ta fadi hakane donta rufan asiri amma wlh ban taba bata ko sisi ba. Alhajin yace Allah sarki matar rufin asiri kenan. To ayi kokari a nemo mashi tufafi. Yace to Allah ya saka. Ya shigo ya samu ta farka yace baba na gaisheki ya nuna mata kudindaya kawo tace to kadan siyo mana kayan tea daga nan dan Allah kada kaci bashi. Yayi murmushi ya fita Ya tsinto masa kaya yan masu sauki, ya kuma ciyo bashin kaan shayi gurin da yake sari da. Yaje gidansu ya fada kuma babansu ya shaida ma haule. Shima baban yaxo dubata sanan ya kawo dubu 1 yace ta rike don kowa yasan halinda suke ciki Su hamxa sun sami aiki kuma yabisu harya somo dubu1 ya dan sayo shinkafa. Killum haj uwa na zuwa mata wanka tayima yaro , kannensa na gidan aure suzo suyi mata girki. Ranar kauri duk ya damu don sun saba kan akuyoyin nan kowa yasan ana dafawa da kunu Ita kuwa tace ta yafe kada ya damu. Makwabta da dangi kowa yazo cewa take ita batason bidi'a taron suna ma dasu maman ummi sukazo sukace ta kawo cingam za'a raba tace ba za'ayi taroba nan suka koma daki suna ta dariya dama tunda akayi haihuwar suke cewa zasuci dariya zasuga yanda zaayi hidima bata daure masa gindi ba ita mai tausayin miji sai su wuni a daki ai gashinan. Mhm mutane kenan Allah yasa mufi karfin zuciyarmu Allah ya tsaremu daga sharrin masu sharri da mahaassada Ko daya zo mata da shawarar cewa yana son yasa sunan mahaifinsa ibrahim, tace Allah ya albrkace shi. Ana gobe suna yace ya za'ayi? Tace ba fa za ayi wani taro ba, dama wannan dk ba sunna bane bazamu ci bashi ba. Tnda Allah yasa lfyta lau mun gode ma Allah. Ido ya zura mata bai san me zai ce mata ba. Ya rungumeta tare da cewa, na gode ikilima ynda kike rufa min asiri Allah ya rufa miki kema. Mahaifiyar shi taxo ana gobe suna, acan gidan taji wai ba taron suna, sai dare taxo gidan mejego. Sukayi hira, tace yan nan naji ance baza ayi taron suna ba? Tace mama dk wannan bidi'a ce, ku dai in zakuyi kuyi a can gidn alhji. Tace shikenan, amma kina samun dan nama kina ci ko? Tace yana siyo min. Alhalin tnda ta haihu ko kifi bata gani ba. Byn tfyrta da yan mintuna ne sai ga haule da nafi'u, murna gurin ikilima, haule ta kalli ko ina, sannan tace dubi dakin yarinyar nan sai kace dakin tsohuwa. Ikilima Batayi magana ba, ta tashi ta miko mata yaron ta amshe shi tana kallanshi tana tabe baki, baku da tawul din daukan jariri? Tace muna dasu, an wanke ne basu bushe ba. Ta kalli ko ina, ina kayan jariri fa, ina nufin durowar yaro? Tace, muna da akwati shiyasa nace ya brshi. Haule tace wancan mitsiyaciyar akwatin guda 1 jal, kai Allah ya raba mu da tsiya, dubi dk ynda kika kare kika dashe sai kace wnda kika kwnta ciwo. To me zaku girka goben? Ikilima tace, mama nace bana son taron suna, kin san dk bidi'a ne. Haule tace, matsiyaciya, nasan dama ke ai ba wnda ke kan tafarki madaidaici se ke. To kin hutar damu, dama nafisa tace ita baxata zo ba, dn hk muma masha zamanmu. Ita dai bata ce komai ba, ta bada yaro ta mike tare da cewa, kudin mu ya huta dn wlhy tnda kince bb taron suna sile biyar bazan kashe miki ba. Ikilima tace ba komai mama, haka ma na gode Allah. Tace oho miki dai. A masallaci aka sa suna. Mejego tai kyau cikin atamfar akwatinta daya data rage, ta bada aka dinko mata ta saka abinta. Yaro ma cikin kayanshi sabo. Ibrahim amma khalil zasu dinga kiranshi. Ya sameta zaune tana shayar da yaron shima dk ya rame ya dube su da kyau yai murmushi. Maman khalil kunyi kyau dayawa. Tace mun gode baban khalil. Ya ciro dubu goma sha uku da dari 5 ya miko mata tare da cewa kirga ta kirga ta bashi yace su mama ne dasu hajia wai suka bani gudunmawa dubu takwas dari 5, dubu 5 km bb ya bani wai in cika in sai rago. Ta zuba mishi ido ynxun ragon zaka siya? Yace Eh, tace ni ko nawa ganin da an hkra da rage ka sai mana kayan abinci mu dan kwana 2 muna ci. Yai shiru yana tuna matan gidan su wato su maman ummi, jia ya shigo da dare gulma tayi dadi ko sallamar shi basuji ba, suna cewa kai wannan mata da son mijin tsiya take, dn kar ya wahala ne tace kada ayi taron suna da ta bude wuta ko rance ne ba dolen shi yai ba, to bari mu gani za ayi hakika ko shima zata ce ta yafe? Maman ummi tace tnda fa ta haihu ko kifi bata taba ci ba, kina ganin abincin ma da kyar ake samu, wake ta wani kifi? Dk yana jinsu. Ikilima ta dube shi tana cewa, shawara ce, in km kana ganin gara ragon to bb matsala. Ya sauke ajiyar zucia ikilima ynda kika ce din yafi sai dai surutun mutane ne yan sa ido, kai baka damu da mu2m ba shi ya damu da kai. Tace ina ruwanmu da mutane? Mu dai muyi harkar gabanmu. Bama cire rai dg rahamar Allah, yace shi knan haka za ayi, Allah ya kara mana kauna da son juna tace amin. Itama matar baban su ikilima ta dako yaji, su manja, gishiri, magi, daddawa har da albasa. Shi km baban karamin buhun shinkafa da turmin zani da rigar yaro suka kawo. Danlami da haule tace kada su mata komai ya sai mata turmin zani a boye ya ba nafi'u ya kai mata. Kannan mahmud da mamanshi dasu hajia sun hada ma mejego kaya da zannuwa 3 da riguna sun kai mata. Albrkacin haihuwa sun sami alkairi. Haka nan bayan suna makota wasu sun aiko mata, me sabulu, me dari, me hamsin. Su maman ummi kam dk inda aka zauna sai ance matar gidan mu danta ba a mishi hakika ba, itama aisha haka, dk inda taje sai ta tsegunta. Ita kuwa mejego ko a jikinta, abinci ya wadata shima ya samu nutsuwa ganin suna da abinci. Sannan abokanshi masu aikin hannu dk wnda ya samu aiki yana bin su dan samun na batarwa. Itama tuni ta nemi koyarwa a islamiyyar da take xuwa, km sun dauke ta amma sai tayi arba'in. Shi da kanshi mahmud din ne ya shawarce ta yin koyarwar. Sunyi arba'in khalil yai bul-bul gwanin sha'awa lkcin mahmud ya saba da aikin gini. Sun zaga dangi har kwantagora suka je suka kwan 2, da zasu dawo cikin tsarba har da tsumi da sauran tarkace lkcin ne ta gane ko maganin me mama ke bata, domin har gjy take da message din baban khalil. Zamansu gwanin sha'awa ta soma koyarwa ta hkra da boko, da safe taje islamiyarta da yamma taje koyarwa. Nafisa na xaune gaban boka tace boka ina mamaki ace duk aikin dkkeyi yanci mma wann ya gagara. Yace ban taba tura tsafi ya dawo b si wnan karon, ban san dame suka dogara ba. Tayi shiru tna tunanin cewa duk yaanda akayi ikilimace ke bata mata aiki da yawan adduo'I tasanta ko lokacin da suke gida duk dare saita tofe jikinta da aduo'I sanan itama ta tofa mata. Wata rana har fada sukeyi da nafisa in tana shafa mata tace kada ki kara shafan yawunki kazamar banxa Nafisa ta sauke ajiyaar zuciya tace ikilima ce ta kalli bokan tacigaba; matarsa tanada yawan adua kodai itace ke bata aikin? Boka yace yanxu naji maana, na tura tsafi da safe ya dawo, na tura da yamma ya dawo, na turda dare ma ya dawo, toh bnsan yanda zanyiba. Saidai ki binciko lokacin da basa yin aduar Nafisa tace to zan kokarta. Way ta dinga yiwa haule wai in ikilima tayi 40 tazo mata yawo. Lokacin da ikilimar taje idan haulen sai take ce mata nafisa tace kije bari na kirata kuyi magana. Nan kuwa suka gaisa tayi mata barka tareda cewa kiyi hkr banzoba banajin dadi ne. Ikilima tace bakomai Allh ya sawwake tace amin, zakizo min din insa direba yaxo dauko ku? Ikilima tace zanxo amma zan fada masa idan ya yarda zamuxo nafisa tace idaan bai yarda bafa? Kindai san halinsa tsaf, saiya ki yarda. Ikilima tace zai iya kam. To in yaki shikenan kin raba zumunci dani? Kindaiyi kratu kune dai malam kinsan makomr mai ynke zumunci Tace na sani zan lallaba shi. Nafis tace in ma yaki kice masa jalingo zaki. Ikilima tace insha Allahu ma zai yarda. Tunda ta dawo take tufka tana warwarewa, ta rasa ta ina zata soma tambayar. Dadare ta gama yiwa khalil shirin bacci ta kwantar dashi ta juye ma babansa ruwn wanka yaana zaune yana cin abinci yace ki sirka min shi da dan dumi jikinaa da ajiya ina anin ma wankan ke zakiyi min. Tace toh. Tana cudashi suka fito da alwala sunyi shafa'I da wutiri sanan suka kwanta tana matsa masa jiki tace yauwa baban khalil! Ya dan bude ido naam maman khalil! Tace inason ziyarar ya nafisa. Ya mike zumburda cewa; wace? Taji shaakkar mimaitawa don tasan yaji. Yace kinyi shiru? Tace cewa nayi zan ziyarci ya nafisa, yayi tsaki ya kwaanta tareda cewa sai kin dawo amm in zaki tafi ki tabbata kin aje min yarona a gida...... Tayi sororo tana kallon shi, ranta ya baci tace shi kenan, ynxun zaka yanke mana zumunci don Allah? Yace na isa? In dai zaki tafi ynxun ma ga hanyar nan, yaro nane nace bana so aje min wani guri dashi. Ke yaruwarki ce, shi fa me suka hada? Ranta ya sake baci, ai ko shima uwarshi ce domin in aka tsaga jinina za aga na yaya nafisa, to haka za aga nashi. Dn hk ni sai naje dashi. Ya tashi zaune yana kallonta, ta daure fuska irin ynda bai taba gani ba shima ya daure tashi fuskar, to sai kije dashi din in gani, ina me tbbtar miki zaki sha mamaki in har kika je dashi. Ya juya yayi kwanciyar shi tace ai wannan raba zumunci ne wlhy manzon Allah S.A.W yace mai yanke zumunta be zai shiga aljanna ba. Allah ya sani naso zuwa, shi kenan ace mutum abu ba zai wuce a gurinshi ba? Ya dai yi bnza da ita. Haushi ya sake cikata, tace ni dai bb mai raba ni da yaruwata tnda tare aka ganmu, km in mutum yace in tafi dole gurin su zani, namiji bashi da tbbs! Jin zantukan sunyi yawa gashi masu kona rai sai ya dauki filo ya fita falo. Ya cika da mamaki, ikilima yarinya me hnkli ita ce ke gaggaya mishi irin wannan zantukan? Ranshi ya kai matuka gurin baci, ranar hk suka kwana suna jin haushin juna, abnda basu taba yi ba. Da safe dk suka share juna ko gaida shi batayi ba, shi kuwa ko karyawa be yi ba ya fice abnda ya sama kuwa gidansu ya wuce ya turo kaninshi ya kawo mata. Sai da ya tbbtr sunyi bcci sannan ya shigo dakin, dg sallar asubahi be dawo ba, ranta ya sake zafi. Shedan ya dinga zugata wai ta tafi gidan mamansu tace a kira mata nafisa ta turo direba ya dauketa. Amma wata zuciar tace mata a'a. Tana makaranta ya dawo yai wanka dn suna bikin sulaiman abokinshi, ya aje mata kudi ya fita. Sun kusan sati idon shi be hadu da nata ba. Haule tazo ranar ta sameta zata dora taliya, suna gaisawa tace ke km sai inji shiru? Yaruwarki dk ta dameni kije kije. Ikilima ta debo ma haule ruwa tace ki sha. Ta zauna tana ba khalil nono tare da cewa, mama wlh yaki yarda. Haule ta zabga mata harara. Kin dai ji haushi, bn san meyake tsinana miki ba duk kika nace mishi, dole ne auran? Dubi dakinki, dubi abinda zaki dafa, taliyar hausa. Dube ki, da haka kike? Dk kin kara baki kin tsofe, wa zai ce shekarunki 18 ynxun? Tnda ya hana kin hanu shi kenan, zance mata ta hkra kowa ya zauna mazauninshi. In bnda shashancinki ku kenan mata ku hada kanku ya gagara. In ma kun hada ai kece zaki fi cin moriyarta dn kin san ita abin hannunta be rufe mata ido ba. Ikilima ranta a bace tace ki bata hkri mama, zanje ynxu hk rigima muke kan haka. Tace A to gara dai ki matsa mishi. Shi fa namiji in ka sake mishi yaga gadon bccnka shikenan, ka zama ta bakin ku yan boko kuka ce sori. Ta kada knta tai gaba. Daren ranan ta zauna sai ya dawo suyi wadda zasuyi. Sha biyu ya dawo, hakan ya kara kona mata rai. Wato sai ynxu ma zai dawo. Ciki-ciki ta amsa sallamar shi, bayi ya nufa ya watsa ruwa sannan yai shafa'i da wuturi yazo kan kujera ya kwanta tace kai fa nake jira muyi magana. A zaton shi hkri zata bashi sai kawai yaji tace kan maganar tafiar ne. Cikin mamaki ya dube ta fuska daure. Irin daurewar da bata taba gani ba. Gabanta ya fadi sai km tai shiru. Yace ina jinki. Tace dama hkri zan baka sannan ince inje? Ya ce Eh kije mana ba tntuni n2e kije ba? Yaro ne kawai be ze je ba sannan ki daina min zancan nan bana son ji. Zatayi magana ya daka mata tsawa har ta firgita yace ki kiyayeni tnda na lura ke baki san zuru ba. Ya mike ya fita abin shi, ita km ta nufi uwar daki rai na zafi. Kai-kawo ya dinga yi gani yake tmkr ba ikilimar shi bace wadda daya ce kaza zata ce to in yai fushi ta lallashe shi, ta kwntr masa da hnkl dama haka halin mata yake? Su zuma ne ga zaki ga harbi? Ynxun ya ze mata? Ita kuwa rigingine tai kan gado nata ganin be mata adalci ba, shi kansu na hade da danginshi ita ze rabata da nata kenan tnda yana fushi har ynxu be daina son nafisan ba? Sunyi kwana uku suna 'yar shariya,gashi kwana biyun babu aiki ba ya kawo komai,duk ya damu. Ita kuma yanzu hankalinta ya dawo ta gane bata kyauta mishi ba,amma ba sa haduwa bare ta ba shi hakuri. Sammakon fita yake yi sai sun yi barci yake dawowa,in kudi ya dan samu zata tashi ta ga ya aje mata,kuma bai cin abincin ta. Hankalin ta bai sake tashi ba sai ranar da wani yaro ya shigo yace wai ana kiran mahmud inji wata. Ta dafa kirji tare da kwantar da yaronta a kasa "kai kace wata?" yace eh ta suri hijab "muje in ganta" sai gashi ya shigo ya aje mata kudin hannunshi ya canza kaya zai fita tace cikin kidima "ance wata na nemanka" yace na ganta,ba tare da ya kalli gurin da take ba ya fita. Kishi kumallon mata nan ta soma tunanin cewa budurwar shi ce? Kasa cin abinci tayi ta zauna zaman jiranshi,sai da ya tabbatar tayi barci yanzu sannan ya nufo gidan. Zaune take kan kujera ta zabga tagumi ya dube ta sai ya wuce da kudurin in ta dame shi zai tura ta gida don mahaifinta yayi mata fada. Wanka yayi ya fiti ya kwanta ta matso "baban khalik dn Allah idan baza ka damu ba ina son muyi magan ta fahimta. Yace ina jin ki."ba tare da ya dube ta ba tace ni ban ki kayi aure ba ko ka nemi budurwa ba amma ka bari mu dan warware. Ya dube ta ban gane ba? Tace "budurwarka da ta zo dazun". Bai san sanda ya saki murmushi ba don ya tuna Sa'Ida ce budurwar muktar ta zo neman shi sun dan samu sabani ne da muktar din ya share ta shi ne take so yayi musu sulhu. Ya sake daure face "ai ba yanzun bane auran dama sai mun dan warware din. Ya yi nufin zolayarta. MABUDIN WAHALA 2***8 Ta matso "me yasa kake son yin aure yanzu alhalin ba kullum bane muke dora tukunya? Kuma ma ba kayi min alkawarin cewa ba za ja kara aure ba? Yace "to ai naga kin canza ne yanzu kin fi son tashin hankalina" tace to in don ta ni ce kayi hakuri nina fa daina don Allah. Ya kauda kai don kada yayi daria "to ya ya zan yi da ita? Ta hau jikinsa "taje can ta nemi mijinta wannan nawa ne". Yace,shine kike gaya man magana son ranki? Tace to ni na zata akan gaskiyata nake. Yace,haka ki ke gani? Tace,to ni ai ina ganin kamar ya kamata komai ya wuce tsakaninta da kai. Yace,to ni raina ne bai kwanta ba da tafiyar. Tace,to shi kenan,maganar tafiya an wuce gurin,da dai ka min bayanin haka ne tuni da ba'a kai ga haka ba. Yace,ni ko in na kalle ki ne sai na ringa tuno yanda ki ke iya gaya min magana gashi kina da ilimi. Tace,ai ba wanda ya wuce kuskure,ka yafe min. Yace to na yafe miki,duk da raina bai so abubuwan da ki ka min ba,amma da na tuno halayan kirkinki sai naji na miki uzuri. Suka yi dariya,ranar dai sun tabbatar sunyi missing din juna don msgs ba sauki. Nafisa ta matsa ma haule da waya,haule tace,dama kin daina damun kanki,ta ce mijinta ya hanata. Nafisa ta ciji yatsa ta koma gurin boka ta shaida masa,yace to tunda haka ba ta samu ba ki bari zamu yi ta gwada sa'a in an samu sabani ko mantawa ba suyi adduar ba zamu dace. Sun manta Allah ne mai kare bawa,matsawar yana addu'a. Allah ka kare mu daga sharrin masu sharri. Duk kwanakin a gida take ganin Alh jamilu ya rage yin tafiye-tafiye,y au ma tana bacci wayar shi

Chapter 12 of 20